Showing 168001 words to 171000 words out of 212110 words

Chapter 57 - Ragon Miji

10 Jul 2025

8335

irin kanni taji tanayi,ahaka taita cakular abincin amma bata ciba can zuwa taji amai tai sauri ta tashi ta matsar da kujera tana toshe baki duk sukabita da kallo tana isa jikin sink da ke nan dining ta dukar dakai taita sheka amai,

fahad hankalinshi ya tashi yayi sauri yaje wurinta yariketa harta gama aman,

Aisha nata kallonsu zuciyarta na harbawa, saboda taga kamar ciki ne da faseelat,

Yanata mata sannu ya wanke mata baki, duk ta galabaita tana ta nishi ta dafe ciki, ya dauketa yahau sama daita,

Aisha tabisu da kallo hawaye suna tarar mata,


yana shiga ya kwantar daita yace "sannu honey bari nakira doctor"

Tai shiru idonta lumshe don juwa take gani,

ya dauki waya yakira Mary ba jimawa tazo Aisha tabude mata kofa tashiga,

ta dudduba faseelat sannan ta debi jininta tana ta kallonta don tayi wani irin fari nafitar hankali,

ta kalli fahad da yakasa ya tsare tai murmushi tace "congratulation sir madam is pregnant"

ya fiddo ido yana murna dadi ya rufeshi besan lokacin da yarika sakin murmushi ba yace "thank you doctor "

tace "welcome yanzu zan je nayo test din jininta zamu gane ko how many weeks ne sannan ga drugs nan asiyo da drip zansa mata ruwa "

fahad yace "thanks "ya amshi takardar mary tafita,

faseelat jin tanada ciki taji dadi sosai amma hakanan taji gabanta na faduwa,

ya rungumeta yana dariya yace "thank you honey nagode miki da kika samu Ciki adede wannan lokacin nagode nayi murna Allah ya saukeki lpy I really love you "

Faseelat tai murmushi tana ta kallonshi yaushe rabon dataga yana farinciki yana annashuwa se yau,

Ta dora hannu jikinshi tace "I love you too kaiwa Allah godiya "


Fahad yayi murmushi yace "alhamdulillah"



yana rike daita kamar kar ya barta ya tashi ya fito yana ta faraa ,Aisha ta tashi gabanta na faduwa tace "meyasa meta ne yaya? "


yanata sakin murmushi yace "faseelat is pregnant"


saura kirisss numfashin Aisha ya dauke tasamu tai yake tace "I'm happy Allah yaraba lpy "

yace "amin bari naje drip zaasamata yanzu "

yafita yanata annashuwa koda ya kalli kayan wasan amira se yayi murmushi yace "sooon "



yasiyo magungunan ya dawo ,ya rungume faseelat kamar ze medata ciki yanata faraa da fadamata yadda yakeji,

Har mary tadawo da result tana shiga ya tambayeta how many weeks,

tai murmushi tace "it's only 2weeks dole se anrika kula daita sosai har yayi kwari"


Ya kalli faseelat yasaki murmushi ranar da yarasa wata ranar yasamu wani,

mary tasa mata drip tafita,


Aisha daki takoma taita kuka shiru shiru fahad be fito ba seda ze fita masallaci yashiga yasameta kwance yace "Dan Allah Aisha kitashi ki dafa wa faseelat mint tea kisa zuma aciki saboda zuciyarta ke tashi ni kuma zan fita masallaci kar na rasa salla "

zuciyarta cunkushe tace "to"

yajuya yafita dasauri,


tana hawaye ta tashi ta nufi kitchen acan ta dirji kukanta dole yayi rawar kai yanzu bakowa gabanshi yanason yara kuma abun yafito daga jikin gimbiyar zuciyarshi,tadora hannu akai tace "nabani na lalace ni Aisha "
➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰







By







*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*




✍🏽✍🏽 *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍🏽✍🏽✍🏽

We are bearer's of so golden a pen🖊
We write assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative golden pen🖊
Be hold our words
A product of our pen🖊
Savour our words
For it will cause you no pain.✍🏽


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/





8⃣2⃣






*Bazan manta da wadanda sukamin alheri ba daga fara buk din zuwa yanzu tundaga wadanda suka sa kudi a account dina, da wadanda sukamin data,da wadanda suka samin recharge card,da wadanda sukabarmin kudinsu time din da raggon miji ya zama free, bazan manta alherinku ba ina rokon Allah yakara maku budi na alheri yakara maku lpy da tsawon rai me amfani godiya ta tayi kadan sede nai maku addua,wannan page din naku ne jimla, ku zauna ku mike kafa kusha karatu naku ne halak malak son so harabada💓*




Tasha kuka har tagama ta wanke fuska ta hau sama don kaiwa faseelat tea din,
Ta shiga da sallama bakinta, faseelat na kwance ruwa nata shiga jikinta ta amsa tana kallon aishar koba afada ba tasan tasha kuka don fuskarta da idonta sun nuna,

Taje ta ajiye tea din akan bedside ta juya zata fita batare da tace komi ba,

Faseelat bataji dadin ganin ta ahaka ba don hakanan taji cewar kishin cikin jikinta ne takewa kuka,

Ahankali tace "anty ki kara hakuri akan jarabawar rayuwarki ki mika lamarinki ga Allah insha Allah ze haska miki rayuwar ki a lokacin da bakiyi tunani ba "

Aisha dake tsaye bakin kofa tana jinta ta karasa fita daga dakin tanajin mugun haushinta ,

Faseelat ta lumshe ido sam batajin dadin yanayin zamansu da Aisha meyasa bazata yi hakuri ba meyasa bazata dauki kaddara ba se yaushe zasu fuskanci juna ne?

Aisha daki ta wuce tashiga toilet tayo alwala tazo ta kabbara salla tanayi tana hawaye, data gama sosai ta daga hannu tana adduar Allah yabata wasu yaran nan kusa,

Fahad na shigowa dakin faseelat ya wuce da dubara ya tada ta zaune tana jikinshi yabata tea din yanajin matsanancin sonta na ratsa koina na jiknshi ya dade beji shaawa ba amma yau segashi kallon ta da yake tayi yasa yaji joy stick dinsa ta motsa,

Faseelat jin abu yana zungurinta ta dauke kai ahankali tace"nakoshi kwantar dani "

Ya medata ya kwantar da ita yadora kanta akan cin yarshi,

yanata kallonta yanajin shi some how,

ya dora hannu acikinta yana shashafawa yana lumshe ido yace "honey alkawarinki na nan fa triplets plss "

amira ta fado mata arai idonta cike da hawaye tai shiru kawai,

Ahankali ya rika matsawa da hannunshi zuwa kasa yatura shi cikin skirt dinta,

faseelat ta rike masa hannu tace "kabari plsss bana so "

yace "nike bakiso plss kibari bawani abu zanyi ba "

Tace "a, a katafi wurin anty plsss wlh banajin dadi kokadan katafi wurinta kabarni nayi barci "

Yace "ba inda zanje inanan ke ko missing dina bakiyi ba 2wks fa "


faseelat tace "hero se yaushe zakagane bako yaushe mutum ke son irin abubuwan nan ba nazata 2wks dakayi yasa kagane haka, hero plsss ka temakamin awannan karan kabarmin ciki na karkayi wani abu daze tabashi don wlh bazan jura ba na roke ka "se kuka,

Jikinshi yayi sanyi yasa hannu yana share mata hawayen in cool voice yace"im sorry, faseelat inasonki sosai kome da yafito agunki inasonshi wlh waccan karan bansan nayi ba, kuma na miki alkawari bazanyi wani abu da ze taba lpyan cikinki ba, abinda baki sani ba shine yanzu nafison cikin jikinki akan ki inason yara honey, kiyi hakuri ki bar kuka "

Tai shiru tana ajiyar zuciya,

Dukkansu sukai shiru kowa da abinda yake sakawa aranshi,

har ruwan suka kare ya cire mata ya dauketa ya yo mata wanka yanata hadiyar miyau,

ya dora mata zane ta hau carpet zatai salla,

tana kabbarawa yabar dakin ya nufi dakin Aisha,

yasamu tayi bacci yaje ya kwanta bayanta yafara zuge zip dinta tabude ido, ya sakarmata murmushi yace "gwara nakara bada himma ko kincikamin gidan da yara,inafatan kema soon kisamu "

tai karamin murmushi yace "I miss your sweet hQ "

tai murmushi yanata kallon idonta yarika matsar da fuskarshi gunta har suka hade ya kama lip dinta yana kissing,

daganan suka cigaba da romancing suka fara sex,


faseelat nagama salla tajuya taga wayam babushi se tajiyo ihunshi daga dakin Aisha ta tabe baki ta girgiza kai, ta koma kan bed ta kwanta hannunta daya kan maratta dake dan motsawa kadan,

ita kadai ke ta tunani she wish tasamu mace asa mata amira amira tadawo su cigaba da rayuwa she's missing her everyday every time,

bayan Sun samu natsuwa fahad ya rungume Aisha yana shafar gashinta yana kallon fuskarta yace "wai miye sirrin? Se kara dadi kike kin sauya sosai yanzu fa kullum da wet kuma kema kinajin dadi unlike before da bakiji ,sosai kike rikitani yadda kike nunamin kinajin dadin wani lokaci fa har sambatu kike (ahhhhhh immmmmmm ashhhhh thank you God for giving me the best man in the world)"

Aisha tafashe da dariya ta rufe fuskarta da hannu tace "kai dinne kaiya rikita ni, ina jindadi sosai u r d best"

yanata kallonta yanajin dadi yace "Aisha kece? Kece kike fadin haka"

tai murmushi yace "naji dadi sosai heart beat kicigaba da fadamin haka I love it "

tace "anything for you my hubby "

yayi dariya ya dauketa suka tafi toilet sukayi wanka sunata wasanni,

Suna fitowa a gaggauce ya shirya ya fita wurin faseelat Aisha ta tabe baki,


da daddare girkin faseelat ne gashi bata lpy, shi kuma ya fita se dare yadawo wayam ba komai a dining ,

dakin Aisha yashiga tana kwance tana chatting yace "Aisha meyasa baki mana dinner ba? "

hankalinta kan wayarta tace "ai ba girki na bane"


rai bace yace "kamar ya?amma Kinsan bata lpy ai ko? "

ta dago ta kalleshi tace "eh bata lpy amma hakan baze hana ta bude ma kafa ba don haka ita zataiwa kanta girki tunda har tana iya sex girki bazeyi wuya ba "

yanata kallonta yanajin kamar yaje ya mazgeta yanxu tunda taga yadena bugunta shikenan komi yafito bakinta se ta fada masa yace "I don't care karki girkin amma kirika kula da abinda zaki rika fadamin,idan kinga dama inbaki ga dama ba seki cigaba amma bazakiji da dadi ba "ya juya ya fita

Tace "matsalarka ai gwara narika rage takaicinka inba haka ba bakin cikin ka ze kasheni yau akafara samun ciki a gidannan duk kabi ka rude ko cikin amira bakai murna haka ba "

fahad yafita ya shiga dakin faseelat yana bude dakin yaga wayam se wani kamshi medadi da ya bugi hancinshi ya lumshe ido yakarasa ciki duk ta gyara dakin gadon yayi luff yaje ya kwankwasa toilet yana kiran "may I come in? "

Yaji shiru ya kanga kai yaji shiru ya tura kofar yaga bata nan,

yafita yashiga kitchen se yasamu tana shirin dora tukunya,

yaje ya rike tukunyar ya meda ya aje ya kalleta daka ganta kasan batada kuzari yace "meyasa zakimin haka? kirika ba kanki wahala hakanan, kibar girkin zan fita yanzu me kkso kici? "

tai murmushi tace "da kabarni nifa kishin cin abincin waje nake na anty ma don yazama dole kaci da bazan bari ba, kabari bawani abu me wuya zan makuba "

yace "naki tunda kince haka bari naje na kwabe nazo nayi girkin ,kefa me zakici? "

tai shiru tana murmushi,

Yace "ehmmm me kkso?nasan special abune kinsan abincin masu ciki is very special "

Tai shiru tadan sosa kai, ya rungumeta ta baya kanshi akan kafadarta yace "tell me mana "

Ahankali tace "umma ta taba kawomin tuwon shinkafa miyar gyada shinake shaawa kuma kaga bazan samu ba, kade yi nakun ni zansha tea kawai "

yace"ina sekinci tuwon shinkafar umma ayau dama ban fada mata good news ba yanzu zataji kuwa "

faseelat tai dariya ya fiddo waya yayi dialing no dinta tana dauka yace "hello umma I have good news for you ur daughter is 2wks pregnant "

umma taji dadi sosai tace "wow Masha Allah ,I thank to Allah the giver for giving us another blessing I'm very happy "

yayi dariya yace "umma kuma zai fara baki wahala tun yanzu don tace tuwonki takeso irin wanda kika taba kawomata tuwon shinkafa miyar gyada"


umma tace "wane irin wahala kuma nida aka zaba yabani 40 minutes yananan isowa "


yayi dariya yace "thanks umma we love you so much "


tace "don't mind "takashe kiran tana murna tashiga kitchen,

faseelat taja mishi kunci tace "baka kyauta ba zakaba umma wahala"

yayi dariya yace "bakiji me tace ba, wannan babyn dangata ne ko zaki yace yanaci ubanshi seya kaso zaki yakawo mishi "

faseelat tafashe da dariya harda rike ciki shi kuma yana tayata,


Aisha data sauko zata kitchen tahada indomei taci taji su kishi ya kara tokareta yanzu shikenan ita tazama yar kallo, ta juya takoma daki tai kwance rufda ciki tana hawaye,


a kitchen fahad ya tube ya rage short ya mika wa faseelat kayan ta nufi sama dasu yadora tukunya yanata murna ya fara kokarin dafa simple jellop supergetti,

faseelat nadawowa taji kamshin girkin zuciyarta tafara tashi ta cire dankwalin kanta ta daure hanci ta shiga kitchen din yanata hanata amma seda takama mishi suka gama tahau sama tashiga dakin Aisha,

aishar na kallo daga kwance, tace mata "anty kifito dining angama dinner"

Aisha batako kalleta ba ta juya tafita,

afili Aisha tace "nifa wlh ban yarda da mutuwar amira ba who knows koke kika kasheta don naki dan yazama babba agidan "

tagama surutun ta tafita dining din don tanajin yunwa saboda surkudarta da fahad yayi dukda de bawani cin kirki zatai ba "

tana zuwa taja kujera ta zauna,faseelat ta tashi ta zubamusu suka fara ci, dukkansu bame kallon kowa kuma tun fitowarta fahad ya hade fuska,

Faseelat ta tashi ta haye sama don kiran ummin ta tafada mata labari me dadi,

tana tafiya fahad ya kalli Aisha dake cin abinci haushi ya kamashi ya janye plate din gabanta ya medashi gaban shi,

Aisha ta rike spoon tana kallonshi, ta mika hannu zata jawo ya kara matsar dashi fuska ahade yace"kije ki dafa kici naki wannan nina dafa dakaina kuma be zama dole nai miki girki ba "

Aisha tafashe da dariya ya daga ido yana kallonta,tarage dariyar tace "haba yaya nifa kanwarka ce ina laifi ma kasamu ina cin wanann jagolgolan naka "

yace "so what karki ci mana "

tace "Tom kayi hakuri da maganganun dazu Allah yahuci zuciyar jarumi acikin matanshi"

Ya tabe baki, setaji ana knocking ta tashi taje tabude sega yar aikin umma da warmers kusan guda ukku ta amsa tashiga dasu ta zauna falo, ta bude daya tuwo daya miya daya farfesun kafar sa, ta tabe baki tace "shikenan fa zatai ta tsirface tsirfacen tsiya ita me ciki "ta bude kular farfesu tasa hannu tana yago nama tana ci,

jin shiru bata iso dining ba fahad ya taso yaganta rungume da kula tanata cin namanta,

ranshi ya baci yace "wai mike damunki ne Aisha, kinsan fa banaki bane donme zakici mata abu,ko tausayin ta bakiji aike yakamata ma ki tausaya mata kafin kowa"

Aisha ta tsame hannu tace "ni banga abun tausayi a rayuwarta ba ni din dece abar tausayi ta yaudare ni ta shigo gidana ta mallake min miji ta amshe min diya daga karshe ta kashe min ita, itakuma tayi wani cikin se in wani ji tausayinta, wlh natsane ta bazan dena tsanar taba har lokacin da zan mutu "ta ajiye kular ta gittashi ta wuce, yabita da kallo kamar ya shakota yayi ta jibga,

ya dauki abincin ya kaiwa faseelat lokacin har tagama waya da ummi tafito wanka yashigo,

Yabita da mayen kallo ya ajiye kulolin yafita ,tasaka rigar bacci ya dawo ya rungumeta ya zuba abincin yana bata abaki, so ukku kadai taci tatashi dagudu tashiga toilet Taita sheka amai yabita yana ta mata sannu kamar yayi kuka,

ya wanke mata baki ya daukota ya kwantar daita a bed, yana gefenta yanata kallonta ba jimawa bacci ya dauketa,

Yayi shiru yanata tunani inde irin wancan laulayinne to yabani don jiyake kamar yayi kuka inyaga tana wahala ba kamar wancan ba da bedamu sosai ba,

ya tashi ya meda abincin kitchen a freezer ya dawo yayi wanka ya kwanta, ya rungumeta tsam jikinshi,


da safe shi yayi musu breakfast don faseelat ma da zazzabi ta tashi, tana kwance abed yazo yayi feeding dinta, yanata rarrashinta da nuna tausayinta,
Karfe 9 umma ta aiko mata da danmalele (shashshaka)taji mai da yaji da veggies faseelat miyonta ya guda zuciyarta ta ji shaawar cin abincin sede tana ci se amai harta hanci duk tabi ta galabaitu, fahad kuka ne kawai beba yakasa fita koina,

da rana ko leko falo beba yana ciki yana jinya, Aisha ta fito ta soya indomei da kwai takoma daki taci, dukda bawani cin kirki ba,

Da Maghreb tafito ta dora girki don girkinta ne,

sede faseelat bashi ta ciba don cewa tai bazata iyaci ba tace ice cream takeso ya fita yasiyo mata da yawa yaajiye a fridge,

Shi kanshi bewani ci abincin kirki ba yatashi yakoma gunta ,Aisha tagama takoma daki tai shirin bacci, shiru be shigo ba se 12:am yashigo,

fuska ba walwala yaje ya kwanta,yabata baya, tanata kallon bayanshi tace "yaya baka min adalci kiri kiri kafifita faseelat akaina kana shiga hakkina sosai seyanzu zaka shigomin? "

abun yabashi takaici beko juyoba yace "kede anyi marar imani Aisha kin sauya yaushe zuciyarki takoma haka, faseelat bata lpy ko rantsuwa nayi haryanzu baki mata sannu ba, baki jin ko tausayin wahalar da take yanzu haka nabaro ta tana ta makyarkyata wlh daita ce bazata bari na kwana can ba zata barmiki kwanan amma ke dayake bakida hali har korafi kike Aisha! Aisha!! Anya wannan halin naki ze barki zama lpy, cikin data samu samm baki farin ciki dashi sema bakin ciki da kike lokacin da nasameki ai kuka kike,wanda nasan faseelat bazata miki bakin ciki ba don kinsamu ciki ita batadashi ,adalcin da kike cewa ayi bazaai ba, zuciyata ta fison faseelat ba jikinta kadai nakeso ba harda zuciyarta da halayyarta me kyau wadda ke kika rusa taki, inason faseelat ina tsananin sonta insha Allah zata samu lpy kuma zata haihu lpy lau sede masu bakin ciki su mutu "

tun kafin yadasa aya tafashe da kuka me taba zuciya har sarkewa takeyi tana kuka tace "I pray so Allah yadauki raina na mutu tunkafin bakin cikinka yakasheni u hate me yaya tunda kasamu faseelat baka ganin kyaun komi nawa while abaya kasha yabon halina da komai nawa nagode da wadannan kalaman "

haryanzu be juyo ba yace "kin sauya hali ne Aisha kisamu ki medo kyawawan halinki nada kuma koda zaki medosu wlh faseelat tafiki aguna , saboda tana son duk abunda nakeso, tana sonki Aisha ke kina wulakantata taso amira fiyeda tunani donme bazan fi sonta ba nace I love her I love her badly itace rayuwata "

Aisha tatashi numfashinta nason daukewa tafita tana kuka ta sauka falo tai hanyar kitchen,

Jin yadda numfashinta yasauya yasa yaji tsoro tana fita yabita,

ta na shiga kitchen ta dauko wuka ta dagata sama tazo zata sokawa cikinta yayi sauri yarike hannunta,

Jikinshi har rawa yake saboda tsoratar da yayi saura kirisss ya kwasheta da mari, idonshi jawur yake kallonta,

Itako tanata kuka idonta kulle ta gaji da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login