Showing 126001 words to 129000 words out of 212110 words
na kaiki different wuri"
Abakin wata private hospital suka tsaya suka shiga bayn Sun samu ganin likita sukamai bayani ya aunata bp dinta ya hau sosai ga ciwon zuciyarta da take bugawa da karfi ya rubuta musu drugs ya zauna yanabawa mommy advice akan adena bata mata rai akiyaye duk abinda ze bata mata rai sannan ta kula da drugs dinta kuma she's normal kodawane lokaci tana iya daukar ciki, sannan suka fita bayan aishar tasha wasu drugs din,
Daga asibitin gidan anty salma suka wuce suka shiga me aikin salma tahau bene tafada mata ta sauko tana faraa tace "I'm very surprise yaushe rabonki da nan anty"
Ganin fuskokinsu duk a dakune yasa tabata fuska itama taje takamo hannun Aisha dake kwance ta jinjina ta Kalli mommy tace "anty mi kefaruwa haka? "
Mommy taja tsoki ta kwashe komi tafada mata a karshe tace "kawota nai kibata shawara tunda ni batajin tawa ta watsar da wata soyayya da kishin banza ta zauna lpy, tade riga taiwa kanta tsiya seta jira ganin ikon Allah "
Anty salma tace "yo anty haka zaku zuba ido tazo tafara haihuwa agidan ai dole a dauki mataki wurin boka kawai zamu a zubar da cikin araba su "
mommy tace "a, a salma ni ban taba zuwa wurin boka ba bakuma zanfara ba ban kuma yadda taje ba kide bata shawara kawai "
salma tace "toni iyakar shawarar da zanbada kenan daganan kuma sede nabata hakuri kawai "
Mommy tace "Allah yasa taji tashi mutafi ai duk ke kikaja"
Salma tayo masu rakiya suka tafi takoma tana fada "wai anty bazataje wurin boka ba tasan kishiyar tata ko dacan ta dogara saboda abun yayi yawa ai munanan de watarana kundawo hanya "
Su mommy gida suka wuce tanata rarrashin Aisha abinci ma abaki tabata tana ta kwantar mata da hankali,
Se 1 dawani abu faseelat taji sauki sukayo wanka suka fito tana kokarin shiga kitchen ya hanata yayi waya aka kawomasu abinci daga motel suka zauna sukai feeding juna tana gama cin abincin tasaka cingum baki,
Daga masallaci ya wuce gidan umma yayi saa har daddynsu nanan bayan sun gaisa umma ta tambayeshi jikin faseelat yafada mata dasauki kanshi kasa yace "daddy dama akwai wata magana da nakeso muyi "
Daddy Yace "go ahead,"
Fahad yace "akan Mansura da safiyya ne, dan Allah daddy ayi hakuri da school dinsu amusu aure Sun ida karatun agidan aurensu,"
Daddy yace "lpy kake maganar aure kosu suka fada ne naga de yaranan ko fira basayi"
Yace "daddy Mansura aure takeso kuma wani friend dina ya nunamin yanasonta kuma I know him sosai idan Sun dedeta se akara bincike akai "
Umma tace "wlh batun yanzu na fahimci tanason aure ba nadeyi shiru ne Allah yasa bawani abu tayi ba? "
Fahad yace "batai komi ba umma "
Daddy yace "dukda a tsarina ba wacce zanwa aure seta gama school amma saboda kayi magana zan amince da auren sede duk wadanda zasu aura se Sun amince zasu barsu su wuce school "
Fahad yace "nagode daddy insha Allah ba matsala "
Sannan ya masu sallama ya fita yana niyyar fita Lady ta shigo ta dukar dakai ganin yanata mata banzan kallo,
Ya dauke ido yace "kowane lokaci zakiga kira da bakuwar number bata kasar nan ba ki mutunta shi ki soshi he's my friend"
Mansura ta daga kai tawuce dasauri fahad yaja tsoki yace "nonsense"
Akan hanya ya kira Hussein yafada mashi yayi ta murna yana fadin "alhamdulillah"
fahad ya tura mishi number lady,
gidan mommy ya wuce da tsarabarta dana sisters yana shiga yasamesu zaune a kasan carpet kan Aisha kan kafafun mommy sisters nashi zaune akujeru sadiya na shan yoghurt while ramlat na chart ga drugs nan gefen mommy,
Jikinshi sanyaye yaje ya zauna ganin banzan kallon da mommy ke masa da be saba gani ba
Yace "Mommy ina wuni "
Mommy tadaga mai hannu tace "karka wani gaidani marar mutunci ,saboda kayi aure shikenan seka nemi kashemin diya a
da tarin kayan takaicinka, ka dauketa kuntafi uwa duniya amma seda ciwon zuciya da hawan jini zata dawo? To kayi dede ka rubuta mata takardarta ka saketa ta huta "
Fahad ya zaro ido ya shido kasa,
Aisha tai wuff zata tashi jin mommy tace Saki mommy ta danne ta, tai shiru zuciyarta takara gudu,
Fahad ya sadda kai ya rasa me zece mommy takalli ramlat tace "ke tashi kije ki daukomin tests da akamata suna jakana "
Ramlat ta dauko ta dawo tabawa mommy, mommy tawtsa su jikinshi tace "read them kakuma saketa ai inason diyata bawai banasonta bane na dauka nabata a tunanina kowani kaga zesata awani hali bazaka bari ba se gashi kaine ka jefata ciki "
Fahad ya dauki papers din ya karanta ya kalli aisha ya lumshe ido yabude, shide ganin kokarin kanshi yake he's trying his best,
Da ladabi yace "mommy Dan Allah kiyi hakuri wlh ina kaucewa bacin ran Aisha saboda inasonta sosai kishi ne ke damunta bansan bata lpy ba dani ne zan kula daita "
Mommy tace "ba abinda na tambayeka kenan ba ban bukatar bada hakurin ka just divorced her "
Fahad ya dafe goshi zuciyar shi na zafi yace "mommy Dan Allah kimin hakuri zan gyara zankara bata kulawa fiyeda da wlh bazan iya rabuwa daita ba inasonta sosai kuma itama tana sona "
Su ramlat se tunzurar baki sukeyi sunajin takaicn shi ze halaka masu yaruwa,
Mommy tace "ko kanason ta seka saketa ita kuma ta mutu da sonka dan kagane tana sonka shiyasa kake kuntata mata "
Yace "wlh aa mommy kiyi hakuri plsss "
Taja tsoki" ka saketa yanzunnan nace "
Ya dago kai arazane idanunshi Sun cika da hawaye yace "I can't bazan iya ba wlh I love my wife "
Ya matsa kusa daita yana hawaye " dan Allah mommy kibarmu tare we love each other bazan kara sakaci ba "
Cikin zuciyar mommy tace yayi dede ,
ta kalleshi tace "this is the last time da zanga Aisha awannan halin na barmaka ita, ka kiyaye inason kayata amma kullum ina bayanka yanzu bazan bari bakin ciki ya kashe ta ba kanajina ai"
Yadaga kai yace "thank you mommy "
Se yanzu Aisha taji dede batasan lokacin da taja doguwar ajiyar zuciya ba,
Mommy ta ajiye ta ta tashi ta haye sama yawatsa wa su ramlat harara duk suka mike sukai sama ya meda kan Aisha kanshi duk busassun hawaye a fuskarta ya mata kisss yace "sorry Aisha ki kara hakuri dani I will change kinji? "
Ta daga mai kai ta lumshe ido,
Ya dade nan sannan ya tafi office,
Da dare suna wurin dinner faseelat takasa cin abinci yana dan kaucewa be tabata ba yace mata me takeso tace quaker oats ya tashi yaje ya hadomata ya bata ahannu yakoma ya zauna, har suka gama kasancewar Aisha ce kedashi yaje yawa faseelat seda safe ya fito yanata jin kamar ya kwana acan.
Yanzu cikin jamila yakai 7month da weeks cikin yayi narkeke kamar zata haihu yan biyu haryanzu dabiar hajya nanan ta rike khalil se 11ko 11 saura jamila har hakurinta ya kare tayi mai magana so baadadi sede yabata hakuri kawai yace watarana se labari,
Yau har 11:15 tsit ba khalil ba alamunshi ta fito tsakar gida tanata sintiri,
Tana ta surutu kunsan masu tsohon ciki dasaurin hawa dama,
takasa hakuri bako tsoro ta fito daga gidan ko tsayawa kullewa batai ba tai hanyar titi,
tana cikin tafiya tasamu mashin tahaye tafada mai unguwar,
Khalil da hjya yau fira tayi dadi dukda de rabin hankinshi nagun jamila, matsakaicin bowl ne a saman shi yana cin dambun kaza sunata labari da angama wannan se ajawo wannan,
Kamar daga sama sede suka ga jamila cikin dakin fuskar nan ta kumbura tai jawur saboda bacin rai hannunta kan kugu,
Khalil yafara slowing da cin naman yakura mata ido hjy ma kallon ikon Allah take duk sunkasa magana,
Rai bace jamila tace "hjya yau shine na karshe da zaki rikemin miji har wannan lokacin, haba kamar baki da imani kinsan inada tsohon ciki ki rikeshi har tsakar dare, koke kika haifeshi ainima inada hakki akanshi "
hjy is very shocked abunda bata tabajin ko labari ba shine yake faruwa kanta ni kaina nakasa gane wane yanayi take ciki,
khalil ko kallon jamila kawai yake yadena taunar naman, ya dade yana tunanin kamar jamila kanta da motsi se yau ya tabbatar,
Jamila tana jijjige jijjige tacigaba da cewa "wlh in kika kara gigin rikemin miji se ranki yayi mummunan baci zan baki mamaki dan zan..... "
Khalil ya furzar da naman bakinshi yana zare mata ido ya kaseta da tsawa" ke!!! bamusan hauka anan "
Jamila tadan tsorata tai shiru yace "bacewa mutane dagani mahaukaciya "
Tafashe da kuka ta juya tafita tana kukan,
khalil ya dafe goshi
Tsittttt dakin yayi har lokacin kofa kawai hjya ke kallo bazaka gane ya take cikiba,
Khalil ya saci kallonta yayi shiru zuciyarshi na zafi he know her bazata bar abunnan haka ba,
Kusan minti biyar sannan murya asanyaye batare da yakalli hjya ba yace "hjya kiyi hakuri dan Allah tanada iskokai I'm sure ba ita bace ba"
Hjya takasa ko motsi, se lokacin ya duba wayarshi 12:00am shaf besan lokaci yaja haka ba ,
Tunawa yayi da jamila kar haukannata ya tillata wani wuri ya ajiye bowl din hannunshi yace wa hjya "seda safe "ya juya yafita dasauri,
Hjya de na zaune kamar gunki , shi ko da yafita ba jamila ba labarinta hankali tashe ya tada mashin yakama hanyar gida.
[8/9, 9:12 PM] SHALELE: ➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*
✍🏽✍🏽 *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍🏽✍🏽✍🏽
*
We are bearer's of so golden a pen🖊
We write assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative golden pen🖊
Be hold our words
A product of our pen🖊
*Savour our words
For it will cause you no pain.✍🏽
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
6⃣8⃣
*bestowed this page to anty hauwa lawal me sunan baba thanks for the love and alheri inata godiya Allah yabar soyayya*
Sedata dau lokaci zaune tanata sake sake zuciyar ta na zafi batasan lokacin da hawaye suka silalo akan kumcinta ba tasa habar zanenta ta share tana ayyana abubuwa da dama aranta ta tashi ta kimtsa ta kwanta sede bacci kasa ko sama ba bushi har kagara tayi gari ya waye,
Titin fessss yake se mashina daidaiku dake kaikai kawo amma ba wata alamar jamila, da high speed ya isa gida beko shigar da mashin dinshi ba ya shiga gidan, tun azaure yaji kuka da ihun jamila, yaja tsoki dan haka yakoma ya shigo da mashin dinshi ciki, ya samu jamila tsakar gida a rashe tana ta kuka,
Ya daka mata tsawa "keeee !!!! Kukan ubanmi kike? "
Jamila taci gaba da kukanta ta tashi ta shige daki, ya bita dasauri ya sameta kwance akan bed tana ta kuka sekace wadda aka daka,
Yayi tsaye kanta ranshi bace yace "Ashe baki da hankali kuma bakida tunani ko kadan dan kinada brain din kaji sekije kisamu hjya kimata hauka? Saboda hauka da rashin tarbiyya irinnaki agabanta zakije kina fadamata magana "
Tana kuka tace "nagaji nagaji don me zanyi shiru a rika shiga hakkina kullum, tsofai tsofai daita ta rika kishi dani yarinyar cikinta, wlh ko gobe ka kara kaiwa dare sena je namata warning kafin infara shuka rashin mutunci "
Idanunshi jawur yake kallonta da mamaki da tarin haushi da takaici cikin fada yace "hjya zakiwa rashin mutunci saboda kina mahaukaciya duk wani rashin mutuncinki hjy ta fiki iyawa dan wlh tsabbbb zata nakada maki duka tasa ni dole na sake ki ki koma can kauyanku jaka kawai , ko yanzu ki fara rokon Allah ta hakura ta barki ahaka sakarai marar hankali inba ma da kina mahaukaciya ba mahaifiyata zaki kalla ki ciwa mutunci agabana dan iskanci"
Jamila tace "yo haka surukkan kwarai suke ai ita yakamata ta rika baka shawara ka kula dani amma itace kesaka kana tauyemin hakkina wlh har fin haka zanyi mata"
Yaja dogon tsoki da ace yana iya bugun mace da tuni yaci ubanta, yasa hannu ya ciro waya yace "bari na kira mama da baba nafadamasu abinda kikayi kafinma hjy ta dauki mataki, tunda har nima zakirika medawa magana "
Ya latso suna ya kara akunne ,jamila ta sa kuka "Dan Allah karka fadamasu kayi hakuri zanje nabawa hjyar hakuri kuma bazan sake ba in sukaji wlh har bugu na baba zeyi"
Khalil ya cire wayar daga aljihu yana mata kallon mahaukaciya yace "saboda hauka sekije bata hakuri mtswww mental tokice mata me? "
"Nide zanje nabata hakuri wlh in su mama sukaji fushi zasuyi dani "
Yakara jan tsoki "wai saboda hauka jamila kije wurin hjya ido da ido kifada mata magana, hmmmm yanzu nariga na mata karya nace iskokai ne dake in ta hakura shikenan inbata hakura ba kau akwai matsala, kuma kisani hjy ita ta haifeni tai duk wata dawainiya ta itace duniya ta itace lahira ta tafi duk matan duniya awurina ita nafi so fiye da komi idan har kinason zama dani dole kiyi hakuri da yadda take in bazaki iyaba sena sawwake miki, kamar yadda kike tsoron fushin iyayenki haka nake tsoron fushinta fin tunaninki ma kuma duk abinda zesa ta farinciki zanyi kokarin yi mata shi,kuma dole kirika girmamata inkinason zaman lpy dani useless girl kawai "
jamila ta cigaba da kuka, ya fita yabar mata dakin ya koma dayan dakin ya kwanta, shima yakasa bacci , rabin son da yakewa jamila duk ya tafi se tunanin faseelat da yadawo mashi sabo yadda take kula da mahaifiyarshi kafin taso rabuwa dashi, ya gyara kwanciya ya rungume pillows yana tuna yadda takeyin kasa da fuska saboda kunya da murmushinta idan sukaje gun hjya,sonta se yadawo mashi sabo ya rumtse ido zuciyar shi na zafi
yace "hjya duk ke kikajawo hakan ko alhakin faseelat baze barki ba nasan kema dole zakiyi kewarta, I love her so much babu wacce zanso kamarta tana da duk qualities na mace tagari amma saboda son zuciyarki hjya kikai abinda dole ta sauya hali kinja na rabu daita gashi har yau nakasa cire tunanin ta araina nikan tuno duk wani abu me kyau nata cute face, cute body, cute skin,white lulu eyes good structure ,long hair obedient tasty food and drinks shyness more over light heart and her beautiful smiling "
Ya kara matse pillow ya rumtse ido yana tuno yadda yakejin natsuwa idan ya rungumeta hawaye masu zafi suka zubo mishi ya bude ido yace "I love her I will surely die with her love, ko tana ina yanzu? "(niko nace mishi ai tayi aure 🤣)
"inafatan ki kara zama Matata akaro na biyu saboda inasonki nine nafi kowa sonki"
Jamila tagaji tai shiru cikinta se juyi yakeyi setaji kuma tana regretting abinda tayi, she love khalil so much bazata iya rabuwa dashi ba, tasan ta bata mishi rai sosai tunda har yayi mata hijira agado ta sauko daga kan bed din tabude fridge tasha ruwa kamar barauniya tana sanda ta nufi dakinshi,
Yana ta kallon silin ta turo dakin ta shigo ta durkusa kasan kujerar da yake kwance tace"dan Allah yaya kayi hakuri wlh duk sharrin shedanne da na zuciya I promise you bazan sake ba kayafemin "
Beko kalleta ba yakira sunanta "Jamila! "
Ta kura mishi ido yace "kin matukar batamin rai da kika nuna mahaifiya ta bakomi take agunki ba nayi zaton zaki bata girma fiyeda nikaina amma bahaka ba, wlh rabin son da nike miki duk ya tafi tunda har kika iya wulakanta min uwata kitashi ki tafiyar ki dakinki tunda kin fadi ta cikinki aise kije ki bacci "
Jamila ta riko hannunshi dasauri hankali tashe tana zubda hawaye tace "Dan Allah kayi hakuri karka dena sona wlh nafison ka fiyeda komi ka dawo da duk sonda kakemin zan gyara kuskurena"
Yaja tsoki a zuci yace madness its true fa jamila kanta da motsin dukda yarinta da kuma hauka,
Tace "plssss wlh zan gyara namaka alkawari zanso ta kuma zan bata girma bazan kara yin korafi akanta ba "
Yayi shiru taita risgar kuka yagaji yace "Dan Allah karkisa dodon kunnena yayi ciwo naji inasonki na kuma hakura shikenan? "
Tace"se kuma kadawo da son nawa da kace ya tafi "
Abun de na yarinta yace "to ya dawo shikenan kije ki kwanta "
Ta share hawaye da bayan hannu tace nima anan zan kwana tare da kai "
Ya dafe goshi yace "OK tashi mukoma dakinki kar jikinki yayi ciwo anan "
Ta kamo hannushi ta tashi suka tafi dakinta suka kwanta
ta matsa ta rungumeshi sosai tana kara bashi hakuri shiko tunaninshi ya tafi akan gobe yadda zasuyi da hjya,
yayi shiru yanaso tasamu bacci ne kawai saboda cikin ta,
wansafe fuska ba yabo ba fallasa yake shirin fita,
jamila tagama breakfast ta shigo ta sameshi tai zaune tana ta kallonshi so take takara bashi hakuri kuma tana tsoron ya dawo yi mata fada,
Jiki amace tace "ga breakfast dinka "
yana saka hula yace "banci ki dauke abinki"
tafara hawaye tace "kacemin ka hakura ni kawai kabarni har ita inje nabata hakuri "
yace "karki kuskura ki kara taka kafa waje bada izinina ba kinga jiya na shareki amma next time wlh sena gwadamiki nawa kalar haukan, ki kwashe kayan abincinki wurin hjya zanje nayi breakfast dina "
Ta dora hannu akai "nide nashiga ukku ni jamila "
Yace "bakwai kika shiga ba ukku ba, mental "
yazo ze fita wufff ta kamo gefen rigarshi tarike tana magiya" dan Allah yaya khalil kayi hakuri na yarda banda hankali, wlh nayi nadama bansan meyahau kaina ba "
ya kalli rigarshi ya kalleta yace "cikani "
Taki Saki ya bige mata hannu ya nufi kofa,
beko samu cikinta ba ta dafe ciki ta duke tafara ihu "wayyo Allah cikina wayyo ya khalil"
da gudu ya dawo wurinta ya duka yana fadin "lpy meyasameki ko mutafi asibity ?"
ta rika yarfa hannu" yaya cikina zaya balle marata "
hankalinshi ya matukar tashi tuni tausayinta ya mantar dashi lefin yace "sannu yi hakuri bari na samo mota mutafi asibity sannu "
ya juya yafita dasauri, ta cigaba da kuka tana kuka tace "inba haka naiba bawai hakurin zeba "
bayan 10mnt ya shigo tai shiru kanta Duke akushin ya wuce ya dauko abaya yazo ya rikota zesa mata sutafi hospital tai fuskar yaushi tace "yadena ciwon ai base munje asibitin ba "
Ya kalleta yace "a, a mutafi likita ya dubaki"
ta girgiza kai tace "kabarshi na warke"
yayi shiru yana kallonta na seconds ya tashi ya fita ya sallami me