Showing 66001 words to 69000 words out of 212110 words
zanzo ganin yata anty ma tace tayi missing dina "
yace "gobe munada special guest kenan Allah yakaimu "
Tace "amin bari natafi se munyi waya"
Yace "ammmmm"ya fiddo 1000 rafas biyu daga gaban motor ya mika mata yace "kibawa yara "
Ta girgiza kai tana murmushi tace,"bana son kudinka kai nikeso"
Yaji dadin maganarta ya lumshe ido ya bude kafin yace wani abu tabude tafita tana mai murmushin dauke numfashi,
ya rumtse ido gam yanajin yadda zuciyarshi ke harbawa saboda tsananin sonta,
sannan ya bude yana kallonta har ta shiga gida, seda ya dau 10 mnt sannan ya tada mota ya tafi,
Yana kan hanya yamata transfer na 500,000,
faseelat mamaki ya cikata da tagani tanata tambayar kanta koshi bejin wuyar fidda kudine oho, ta nunawa ummi, ummi tace
"duk kan gyaranki zasu kare ai"
faseelat tai dariya
Next day tunda wuri faseelat tagama aikinta tatafi super market, ta kwashi kayan kitson yara danginsu beads ,robber band,robar kitso ,Brazil wool dasauransu sannan taje wurin kayan wasan yara,
Wata big teddy me kyau ta baby ta burgeta ta dauka taje tabada ATM suka cire kudinsu kusan 50 thousands teddyn yakama tana dauke daita ta hau napep zuwa gidansu Aisha,
Me napep na ajiyeta ta biya tai knocking ta gaida baba tsoho ta shiga,
Amira na wurin wasanta ta hango faseelat da gudu taje ta rungumeta,
Faseelat na dariya tace"daughter I really miss you "
Amira tai dariya tanakai hannu kan teddy faseelat tabata tace "dama nakine gashinan "ta mika mata amira ta rungume babyn,
Faseelat tace "ina anty? "
Amira hankalinta na kan teddy dukda tana da wadanda suka fisu setaga wannan tafi mata tace "she's inside "
faseelat tace "OK zo mushiga ciki "ta jawota suna tafiya tana kallon kitson kanta da yadan tsufa,
Suka tsaya bakin kofa faseelat ta danna door bell shiru takara dannawa seda akai 15 mnt sannan aisha tazo tabude tana murmushi tace "maraba da anty "tana kallon kayan jikinta,
Faseelat ta shigo tana murmushi,
faseelat ta gaida aisha, ta amsa tana mata kallon up and down tace "a, a! Jawara kinfaso gari kinga yadda kika kara kyau kuwa? "tana dariya
Faseelat tace "anty bawani kyau kina zaulayata ne "
Maman amira tace "Allah kinsauya gaskiya bazawarinki na kula dake "
Faseelat tai dariya tace "anty very soon de zanyi aure nahuta da kirana jawara da kike "
Aisha tace "Allah yakaimu muna murna ai, saboda mune kirjin biki "
faseelat tai murmushi,
Aisha ta mike "baride nakawomiki drinks, inkoma ciki daddyn amira nanan, bacci ma muke kika tadamu "
Faseelat tace "ok"
Aisha tatafi kawo mata drinks ita kuma ta bude jaka ta fiddo kayan kitson amira ta dauki wasu da zatai amfani ta ajiye sauran ta ajesu a kasa, tafara wa amira tsifa,
aisha nadawowa tagansu tace "yau ranar ta amira ce kenan naga harda katuwar teddy aka siyomata "
Faseelat tace "eh dan ita nazo "
aisha tace "to Nagode "ta ajiye mata ta haura sama,
Seda tagama mata tsifa ta danzuba drink tasha, ta daga kai tana kallon benen jin aisha shiru, wani malolo yatsaya mata a makoshi ta daure ta farawa amira Twisting,
Irin manyan nan ne masu guda ukku shaf shaf tagama mata aisha shiru bata fito ba, abun yabata mamaki kusan 1hr,
Cikin dabara ta kalli amira tace "kitsonki yayi kyau jeki gwadowa mommy "
Amira ta gudu tana taka step,
Ba jimawa segasu sunfito Aisha rike da hannun fahad shi kuma ya dauki amira yana tambayarta wa ya mata kitso dan besan faseelat bace har tazo,
Har suka sauko falo ahaka faseelat tunkan bene take kallonsu tanajin haushi,
Fahad na dago ido yaga faseelat,
Tayi kyau tana sanye cikin milk hijab da brown atamfa ya dan dauke ido daga kallonta,
Aisha tace "yaya kaga teddyn da faseelat ta siyowa amira nan gashi harda kitso tai mata "
Faseelat cikin jin haushi tace "inayini "
yace "lpy thanks for your care for our child "
Tai banza dashi ya juya yacewa Aisha "sena dawo "
Ta matsa tai masa kisss a cheek tace "take care of yourself"
Faseelat ta cika tai famm yana satar kallon faseelat ya fita,
aisha tazo ta zauna tajawo amira tana duba kitson tace "gaskiya kinyi kokari har kingama cikin sauri kiyi hakuri nabarki ke daya wlh se yanzu mukai wanka tundazu muna kwance "
Faseelat tace "badamuwa "tana yamutsa fuska tace "tafiya ma zanyi "
aisha tace "tunyanzu kitsaya mudanyi fira mana "
Wayar faseelat tahau ruri ta ciro ta duba taga fahad ne batare data dauka ba ta kalli Aisha tace "jirana akeyi dama nacika alkawari ne kawai "
Aisha tace "to shikenan Nagode kwarai faseelat Allah yabarki da masoyinki naga yanaji dake har iPhone 8s kike riko yanzu "faseelat tai yake,
Aisha tace "bari nakawomiki tsarabarki "
Faseelat tace "dan Allah anty kibarta ina sauri "
aisha tai dariya tace "aikuwa har gida zan kawomiki wasu English dress ne masu kyau nasiyomki naga zasuyi kyau da jikinki dan Allah kima bari nakawomiki daukosu kawai zan yi "
Faseelat tace "tom"
Aisha ta juya faseelat taja tsoki,
Can zuwa aishar ta dawo da ledar ta amsa tai godiya shaf shaf ta fita daga gidan,
Tana fita taga motar fahad awaje tana sauri tai gaba yabi bayanta da motar,
haryakai setin ta ya rage glass yace "kishigo in kaiki "
Tai banza takara sauri,
Yakara binta yana cewa "meyafaru ne wai? Kishigo mutafi "
Takarayin gaba, cikn fushi yakashe motar yafito yabita yajawo hannunta tana ta kokarin kwacewa ya sakata motar yaja yabar unguwar,
Faseelat ta duke tafashe da kuka me cinrai,
kujimin iko seta hanashi soyewa da matarshi π
team faseelat de π
[7/12, 11:01 PM] Maman Mamy: β°β°β°β°β°
*RAGGON MIJI*
β°β°β°β°β°
By
*MAMAN MAMY*
*SHALELEπ€ΈπΌββ*
βπ½βπ½ *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*βπ½βπ½βπ½
We are bearer's of so golden a penπ
We write assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative golden penπ
Be hold our words
A product of our penπ
Savour our words
For it will cause you no pain.βπ½
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
4β£7β£
Yana tuki yana jiyowa yana kallonta saboda mamakin abinda yasakata kukan kawai yake,
Ta cigaba da kuka tana sheshsheka, cikin jin ciwon kukunnata ya gangara gefen titi yatsaya, ya kifa kai jikin sitiyarin motar zuciyarshi na zafi,
Faseelat batabar kukan ba don wani mugun kishi takeji yanda suka fito tareda aisha says it all sunacan suna soyewarsu ne,
Ya dago yana kallonta cikin jin haushi yace "wai me yafaru ne?hakanan sekita kuka ninasan banmiki komi ba, kifadamin mekikewa kuka "
Ta cigaba da kukanta tana rage volume din,
Ya matsa ya dago fuskarta yana kallonta,
Bata kalleshiba ta cigaba da zubda hawaye,
Yana nazarinta yace "cutie kifadamin damuwarki plsss banajin dadin kukanki "cikin rarrashi,
Ta daga ido ta kalleshi tana ajiyar heart tace "bakome kaina ne ke ciwo "
Ya girgizakai kawai yafara share mata hawayenta da hannunshi sannan yace "kishi ko cutie?"
Taki cewa komi ya kwantar da kanta kan kafadarshi ya jinginar da kanshi jikin seat din motar ya rumtse ido zuciyarshi na harbawa dasauri,
Bayan 3mnt tanata ajiyar heart tadena kukan cikin jin tausayin kanshi yace "faseelat meyasa zakimin haka? yakamata ace kina boye kishinki kefa kikace min bazaki kishi da aisha ba yanzu me kike? Aisha ce fa ,aisharki haba for god sake ni yazan da rayuwata, faseelat akwai kalubale da yawa akaina, kullum cikin tunani nake taina zamfara fadawa aisha wannan batun, momy zata amince koko?ga shawarki data addabeni inason aurenki nankusa na rasa taina zanfara komi ya jagulemin hakanan kike ganina Amman ni nasan me nake ciki, yanzu bazaki temakamin ba ?ki kwantar da hankalinki kicire kishinnan ko nasamu kwanciyar hankalin yin abunda yakamata, saboda inkina fushi dani wlh duk tunani akanki yake tafiya "
faseelat ta daga kanta daga kafadarshi tanajin tasayinshi ta saka hannunta cikin nashi ta damke ya bude ido yana kallonta,
Tace "kayi hakuri plsss bazan sake ba"
Yana ta kallonta yace "yanzu haka zamuyi auren faseelat? I'm not going to take you to somewhere agida daya zaku zauna ya kenan, I want to build a peaceful family,idan kina haka yazaku zauna lpya keda aisha? Itama fa bansan ya zata dauki abun ba fa "
Faseelat tai fuskar tausayi tace "I'm really sorry nadena kishinka are you happy now? "
Ya juyar da kai yace "I'm not, ai bacewa nai kidena kishina ba, cewa nai ki rage ai u have to hide it now "
Ta cire hannunta daga nashi tace "naji nabari, kuma badole naji ciwo ba, nazo kunbarni a palo kuna ciki kuna...... Sannan kunfito harwani kisss zatai maka dan iskanci "
Yayi murmushin takaici yace "to miye aisha cefa maman amira "yaida yana dariya,
Ta harareshi tace "nasan kunayi basekafada minba ai"
Yayi murmushi ze kamo hannunta ta janye tace "kakaini gida ni "
yayi murmushi "ke yarinya kincika wayau time dinda kinason kiji dadin hannu na keda kanki kika rikoni nikuma in inaso seki hana? "
tai murmushi ta rufe fuska tace "kuskure ne akasamu "
Yayi dariya yana tada mota yace "inason irin kuskuren nan,"
yana hawan titi yace "bari muje na kaiki kidanyo shopping ko se nakaiki gida "
Tace "nide kakaini gida kawai banison shopping din "
Yace "I insisted "
Tai shiru yana tuki har suka isa big mall yayi parking ya fita ya budemata tafito suka shiga ciki,
Duk yadda yaso tadauki abunda takeso taki, sede shi yazabar mata kayan makeup da different perfumes dasu kayan tea ,
Yaje yayi payment suka fito suka kama hanyar gida, sunata labari kamar ba yanzu tagama kuka ba,
Suna zuwa kofar gidansu ya tsaya ya kashe motar ya kalleta yace "kigaidamin da kowa se nazo gobe "
Tace "tam Nagode hubby Allah yabiya maka bukatunka na alheri "
Ya lumshe ido ya bude yace "inason adduarki kicigaba damin addua "
Tace "karka damu ahakan bakomai bane akan wacce nakema aduk salla ta"
Yace "thanks Allah ya amsa "
Tai murmushi tafita,
Ya bude back seat din ya dauko ledojin yaji da nauyi yace "muje narage miki aiki banso ki expanding "yana dariya,
Tamai harara irinta masoya ta juya sunatafiya tare har bakin kofar gidan ya mika mata yace "bye"
Ta daga mishi kai kawai ta shiga, yana juyowa abba naiso wa akan mashin,
Fahad ya dakata har abba ya sauko ya zukunna har kasa ya gaidashi,
Abba ya amsa yana kallonshi, sannan fahad ya tashi ya tafi,
Bayan abba yashiga gida suna daki da ummi yace "anyi bincike kan yaronnan"
Ummi tace "to lpy de ko? "
Ya girgizakai yace "akwai matsala gaskiya ,wato shi mahaifiyarshi sun rabu da babanshi da dadewa kuma ba rabuwar arziki ba, shi yataso ne awurin matar babanshi, lokacin da babanshi na raye yahana mahaifiyar shi koda ganinshi saboda wulakanta yaron da tayi lokacin tana neman Saki, yanzu da yamutu tanata bibiyar yaron ya yafemata yaki ,saboda ancusa mishi kiyayyarta,yafison matar babannashi akan mamanshi sannan diyar ita matar babanshi yake aure, kinga akwai matsala kenan ace mutum na fushi da uwa, kuma yana tareda diyar ita wadda yakeso kinga faseelat zatasha wuya ne, kuma bazata hada kanta da kishiyartan ba tunda sunfi mu hali ganinake abun zezo da matsala, nima dazun alhaji ke fadamin Amman yace wannan duk ba matsala bace tunda suna iya sasantawa da ita mamanshin nangaba "
ummi tace "a, a gaskiya ni dama banason gidan kishiyarnan, bare ita wannan da yaruwarshi ce ,wlh da maganar da zanmaka ince kungama binciken ace yaturo dan naga ita faseelat ta haukace kanshi yanzu ma daga zuwa unguwa ta dawo da nikinikin kaya yasiyo mata "
Abba yace "Allah sarki ainima mungaisa yanzu har Kasa ya zukunna ya gaisheni "
ummi tace "ai yanzu sede ta hakura don abunnan bazeyiwuba"
faseelat dake bakin kofar daki kan tabarma tana kwance duk tanajin abunda ake wufff tatashi ta shiga dakin abba ta durkushe gabanshi tana zubar da hawaye tace "dan Allah abba karku rabani dashi, wlh inasonshi ni aganina shi abun tausayi ne, ansa mishi tsanar mamanshi kuma bayada wanda ze nuna mai gaskiya, dan Allah abba kayarda in aure shi kodan na temaka mishi "
Daga ummi har abba sukai kasake suna kallonta saboda mamaki, itako she don't care batamasan kunya ayanayin da take ciki ba ,
abba yace "faseelat karfa ai abunnan azo ana danasanin yinshi"
ta girgiza kai "insha Allah abba baabunda ze faru "
Ummi hannunta kan baki tana zaro ido tace "kajimin ikon Allah dama kina labe kinajinmu kenan, kuma yanzu faseelat tunda kinfara soyayya kin tattara kunya kin aje gefe kina ta zuba rashin kunya, bama agabana ba hargaban abbanku ko? "
Faseelat ta girgiza kai "ummi dan Allah kubari na aureshi "
ummi tace "ahaf tunda kinji kingani ai shikenan Allah yasa alheri iyakar abunda zamu ce kenan "
Abba yana kallon faseelat yace "tashi kije "ta tashi tafita,
Ya kalli ummi yace"mutayata da addua kawai Allah yasa hakan ne alheri"
hannun ummi kan gemu tana mamaki tace "amin ya Allah" tana kadakai dan mamaki,
akan hanya fahad se tunanin yadda yaga gidansu faseelat yake duk da ginin cement ne amma ya tsufa, acikin ranshi yake shawarar canzamusu gida daga cikin gidajenshi,
Se marece ya koma gida, kodayaje aisha batanan tafita, yakada kai kurum dama da mommy takirata inde baya gida tafiyarta kawai takeyi sede ya samu batanan,
Se dare ta dawo amira ahannu tana bacci ,yana cikin balcony ya taso ya amsheta suka shiga ciki se akan hanyar shiga takecewa "mommy ce takirani anty kulsum ta haihu shine muka tafi tundazu muna asibity se yanzu muka dawo ,ta samu baby boy "
Yanata tafiya yace "Allah yaraya "tace "amin"
Tunda tashiga take ta kai kawo tai wanka ta shige salloli,
shiko yana saman bed yajawo computer dinshi yana aiki, yana cikin aikin faseelat ta turomishi pic Data dauka da dayan color da yasiya mata ,ya bude pic din yana kallo rigar is maroon irin robar nan ce irin kayansu na yan can tabi jikinta sosai ta mata dasss kamar dan ita aka yisu ga pic din andauketa from head to toe ta dan juya kadan wanda har hips nata ana gani,
ya kure pic din da kallo yanajin many emotions, yana tunanin kila dan takarasa shi ta turomishi pic din,
Yanata kallon pic din bako kyaftawa gabadaya ya rikice hannunshi biyu adunkule akasan habarshi,
Har Aisha tagama sallolinta taje gaban mirror ta shafa perrfumes dinta tasaka rigar baccinta da wando ta juyo tana kallonshi taga baaikin yakeba tunani ma yake, yadda taga yakure system din da ido dukda bata cika bin aikinshiba amma yasa ta zagaya ta bayanshi tai tsaye tana kallon computer din,
Abinda idonta yagani ne ya tada mata hankali gabanta ya rika harbawa fat fat!!!
Jikinta yadau rawa koina tafara ja da baya tana jawo numfashi da karfi,
Jin nishi nishi yasa fahad ya juya yaga aisha nata kyarma tana ja baya,
Cikin tsoro ya mike yana kallonta ,
Har takai karshen bango tanajinta jikin bango ta zukunna ta dora hannu biyu tafasa tsuwwar da fahad besan lokacin da yakai wurinta ba yariko ta yana "sorry Aisha take it easy please "
Jikinta na cigaba da rawa cikin rarrabuwar harshe tace "fa..fa....see.... Lat.... Ce..... Fa......A...com. ..pu.. Ter...dinKa.... KaKe..... Kallon....pic......nata "tadora hannu abaki tana fiddo ido,
Ya rumtse ido ya zukunna gabanta yahade hannu biyu yace "kiyi hakuri Aisha ki saurareni "
Itako kojinshi batayi tana ta tariyo maganganun faseelat, "harna fara son wani daban , anty soon de zanyi aure nima nahuta dakirana jawara da kike "sune maganganun datake ta tariyowa, that means tun tanada aure suke tare, kuma shine Wanda zata aura.
ya jawota jikinshi yana fadin "listen to me aisha "
Tai kukan kura ta tunkude fahad daga jikinta tai waje da gudu tana kuka , yabita yana kiran "Aisha wait plss kitsaya karkifita dare ne "
Koda yafita har tabar gidn ko takalma babu bare dankwali,
Kusan karfe 10:40 tana fita tasamu mashin ta haye tana kuka da rawar jiki tafada mai yakaita malali quarters ,
mashin na ajiyeta ta dira tafara buga gate din gidansu da karfi tana kuka,
megadi yazo yabude da katuwar gorar shi ahannu,
Tabanka aguje ta shiga cikin gidan,
Me mashin ko kotsayawa amsar kudi beba yajuya, don ya tausaya mata
Kannenta biyu na kallo Tawuce su dagudu tafada dakin mommy, mommy na zaune tana waya kan bed aisha tafada jikinta,
Jikinta na rawa tace "mommy mommy kitemakamin faseelat ta cuceni zata auremin miji... ......"
tohwa ana wata ga wata ππ½ββ
inga ruwan comments woooo π€£π€£π€£π€£π€£
Shalele takuce fansπ€
[7/12, 11:01 PM] Maman Mamy: β°β°β°β°β°
*RAGGON MIJI*
β°β°β°β°β°
By
*MAMAN MAMY SHALELE*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
βββββββ
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
βββββββ
*~βWe beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
4β£8β£
*dedicated to firdausi, Fπ§πΌkinsanme? Inasonki sisterπ, kina sona kinga ko dole naso ki hausawa na cewa kaso me sonka,shiyasa nakamu over, fans kutayani son firdausi don nima inasonta, tadamu Dani matuka da zanwuce 9am bana online seta kira taji ko lpya nake, I love you Fπ§πΌ,my masoyiya*
Mommy tarika kallonta hankali tashe takamo fuskarta tace "ban fahimta ba, ki kwantar da hankali sosai kimin bayani"
Tana sheshsheka tace "mommy yaya aure zeyi kuma kawata ce, wlh faseelat ta cuceni ban cancanci haka daga gareta ba"
Momy tafara tafi tana salati tace "nashiga ukku ni faiza, yanzu yazanyi ne? Ke dan ubanki har wata kawa kikasamu wadda bansaniba? "
Ta daga kai tana kuka tana jijjiga mommy tace "dan Allah mommy kice karyayi aurennan wlh zuciyata bugawa zatayi, nide nashiga ukkuna faseelat ta gama da rayuwata "
Mommy tace "keda harkina da guarantee kan kawa? da har zaki saki jiki daita? To yanzu gashinan de kinaso kijamin asara inyi renon banza, nasaki jiki zansamu kudi Amman kinjawomin tsiya, kafin mahaifin fahad ya rasu ya mallaka mishi gidaje da filaye da gonaki da bansan adadinsuba, su ramlat su ukku bazasu samu rabin gadonshi ba shiyasa nasamu nahadaki dashi kinga komi de nawa ne akarshe Amman kinyi sakaci zekawo wata ta ragemin lissafi "
Aisha tace "mommy kihanashi plsss wlh bazan iya sharing dinshi ba da wata "
Mommy tace "aiko sede ki hakuri sanin kanki ne nariga nasaba mishi da goyon bayanshi akan komi, yanzu innace aa to matsala zaasamu saboda yana iya bijiremin gwara na yarda din yafi "
aisha tafasa kuwwa tadora hannu saman kai mommy ta jawota tana rarrashi tace "ki kwantar da hankalinki diyata baabinda ze faru a aurennan kede kirika bin shawarata sannan kirika fadamin duk abinda ake ciki "
Aisha ta cigaba da kuka mommy nata rarrashi tace "dole ki hadiye kishinnan ki nuna mishi kinason abunnan kinga zeji dadi yakara sonki kuma ko tazo