Showing 63001 words to 66000 words out of 212110 words
haifamin kai da kullum abinda kake samu kanta zaya kare? "
Khalil na shiga gida ya iske jamila tsaye tagaji da jira, cikin rarrashi yace "kanwata amin hakuri nadawo daga gidan hjya mashin dina yayi faci"ya mata karya.
Tace"karya Kake wlh wai haka ake kasan kanada iyali Amman kaje kai zaune wurin hjy ni kabarni ni kadai, wani lokaci ma senayi barci zaka dawo nide wlh ana shiga hakkina "
Yana mata wani kalar kallo dukda beyi mamaki ba don ita bata wani tsayawa tauna magana takeyinta kuma bata barin abu cikinta setai magana, yace"nike karyar jamila? "
Tace "eh karantse faci kayi"
Yace "hmmm "
ya mika mata kazar ta yace "ga sakonki "yawuce,
Ta ansa tana maganganu Kasa Kasa ta dauko plate kitchen ta dawo falo ta bude sega rabin kaza,
Ta bata fuska ta dan iba ta meda miyau tabishi daki yana fitowa wanka kenan tasameshi tana ya mutsa fuska tace "ya naga rabin kaza? kasan de tamin kadan "
Yace "eh nasani kiyi hakuri da wannan banda kudine shiyasa "
yawuceta tabishi tana cewa "amma kasan de baa seda rabin kaza ko? Kawai kace hjy ta raba shine "
Ranshi ya baci ya juya ya zaro ido yace "eh hjy ta raba se meee "cikin tsawa
taja baya ganin yadda ya tasomata ta juya tana kunkuni, yaja tsoki ya saka rigar shi ya kwanta,
Wanshe kare da ze fita tace asiyo mata tsire yace "banda kudi "yayi hanyar fita
Tabishi har zaure tana bashi hakuri hardasu zukunnawa itade yasiyo ta samu taci, badan ita ba yace ze siyo albarkacin cikinta,
Bayan kwana ukku
yau tunda karfe 5 na asuba jirginsu ya sauka Nigeria, suna isa gida suka fara gyaren gidansu sannan aisha ta dafa masu indomei suka ci seda suka kashe arna bacci ya kwashesu,
Karfe 12 ya farka har lokacin aisha na barci a gaggauce ya diro yayi wanka shaf shaf ya shirya ya sauka kasa,
yaje ya bude jakar tsarabarsu ya fiddo wani akwati ya fice ya bude motarshi haryanzu kayanda yamata shopping sunanan ya fiddosu ya meda a motar da ze fita daita ya shiga motar yayi hanyar gidansu faseelat,
Faseelat ko jiya tata kiranshi bata shiga dan kwana goma yace ashe basu taso da wuri bane se yau,
Tagaji ta hakura Amma ta cika tai famm,
Tana daki tana charting dan yau gidansu hutun girki suke abba yasiyo fura da yoghurt da kwakwa daita zasuyi lunch dan sungaji da abincin,
Ummi na waje itako tana yankan farce yaro ya shigo gidan yace "ana kiran faseelat inji wani me mota "
Ummi tace "jeka ce gatanan zuwa "
Tamike ta leka ta window faseelat nata charting dinta hankalinta kaf yana kan wayar ummi na kallonta cikin zolaya tace "tsuntsuwar soyayya"!
Faseelat tadago tana zumburo baki ummi na dariya tace "ga tsuntsun soyayya can yazo yana jira "
faseelat tafashe da dariya tanajin dadi ta mike ba shafa komi ta jawo katuwar hijab dinta tasaka tafito tanawa ummi dariya tafita,
Ummi ta girgiza kai "ansamu wanda akeso inyazo zaafita ana dokin ganinshi "
faseelat nafita ta hangoshi tsaye bakin Ash din motarshi yana sanye da dark Blue Jeans da red shirt,
Bakaramin kyau yayi ba setaga har fari yakara sede yadan rame tundaga nesa take karemishi kallo ,shima yanata kallonta,
Tana karasowa kusa ta sadda kai,
Sheik kabir gombe yace πsu mata munafukaine tundaga nesa suke karemaka kallo da sunzo kusa su sadda kai,
[7/12, 11:01 PM] Maman Mamy: β°β°β°β°β°
*RAGGON MIJI*
β°β°β°β°β°
By
*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
βββββββ
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
βββββββ
*~βWe beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
4β£5β£
*dedicated to Dr fatee the writer of matar bahausheπ*
Tana zuwa tai tsaye ta sadda kai, yanata kallonta kamar yau yafara ganinta dariya taso kufcemishi ganin doguwar hijabin data saka abun dariyar abunda ake boyemishin de sunfito dan hijabin roba ce tsawonta yakara sa saman yayi shape,yana kara kallon tudun breast dinta yace "enter the car mana kinyi tsaye "
Ta dago tace "a, a daga nande "
Yana mata wani kallo yace "wlh zanzo in daukeki nasaki ciki da tsiya, gwarama kishiga"
Ta tunzuro baki ta bude marfin motar ta shiga, shima yabude yashiga yana kallonta yace"yanzu ni na zama abin tsoro kamar ba fahad naki ba "
Ta dago ta kalleshi tai murmushi, shima ya murmusa yana juyawa ya jingina jikin kofa dan yaji dadin karemata kallo yace "kinbani wahala cutie dan kinga inasonki da yawa ko? "
Ta harareshi, wanda hakan ya matukar birgeshi tace "munsha wahala, zakace kasan yadda nai missing dinka kuwa? Nasha kuka many times saboda shareni da kayi "
Abun ma yabashi dariya yadan shafi sajenshi ya kalleta yace "ke zakice haka? Kira nawa nai miki kikai ignoring dina dubi duk yadda nafada saboda tunaninki, kincika taurin kai tunda nabada hakuri ai shikenan amma se lokacinne ma kika kara hawa kawai dan na "se yayi shiru ya saki murmushi yana shafar kanshi da hannu ya dan kalleta yaga tanata watsa mai harara, yayi dariya yace "bada gangan nai hakan ba, nide inarokon ko hakan yafaru anan gaba amin hakuri, wlh kamshin turarenki kanshi rudani yake "
Ta balla mai harara "Allah karka kuma dan bazan daukeshi a kuskure ba tom "
Yayi dariya "kinganki ko, hmmm ki koyi hakuri dani shiyafi miki "
Ta turo baki gaba, yana dariya yana nuna setin breast dinta da hannu yace "harda jibgo hijab amma dukda haka ga yan albarkannnan sunfito gaidani "
Dasauri tadora hannu biyu saman breast dinta takare su, ya kwashe da dariya itako se kallon saman hannun take taga wai dagaske ne,
Ya sassauta dariyar yace "to yazakiyi ne tunda suna sona kome zaki sa se sunfito sede in a akwati zaki rika sakasu "
Ta zumburo baki tana so tayi kuka,
Yace "I'm sorry,im joking, nadena amman kicire hannunki plsss kibari ko daga cikin hijab din nasamu narika meda miyau na,"
Taki cirewa yace "kicire kigani wasa nake yi "
Ta zame hannun tana kallon gaban nata ashe dagaske yake sunfito tai sauri tameda hannuwan akai,
Ya dafe goshi "oh ni bakina yajamin dama nai shiru na cigaba da kwasar romo na "
Su duka suka fashe da dariya,
Yanda take dariya bakaramin burgeshi yakeba, yayi shiru yana kallonta cikinso da kauna,
Jin yayi shiru itama tai shirun ganin ita yake kallo suka kure juna da kallo dukkansu sunajin feeling like to hug thereself,
itace ta dauke ido, sannan shima ya dawo tunaninshi cikin inda inda yace "I love you cutie "
Ta kalleshi ta sakarmai murmushi tace "I love you more"
Jiyayi kamar yakai mata kisss yayi sauri ya dukar dakai kamar me nazari,
Faseelat na kallon sumar kanshi dake kwance takatse shirun da "where's my angel?"
Ya dago yayi murmushi yana jindadin yadda takeson yarshi yace "tana gida, tana missing naki sosai, wani lokaci takanwa mommynta kuka akaita gum anty ita "
faseelat tai murmushi tace "I'm missing her too, inaga zanje ganinta very soon "
yace "baki tsoron aisha tagane muna soyayya? "
Faseelat ta girgiza kai tace "a, a banajin tsoro, bana tunanin akwai abinda zeban tsoro inde akanka ne, anty nasona nasan zata fahimceni, "
Yace "hmmmm"cikin ranshi yana cewa "bakisan true colors na aisha ba"
Ta katseshi da cewa "komiye de ni inasonta saboda ta dalilinta na sanka, and saboda kana sonta saboda inason duk abinda kakeso "
Ya cije lips yace "really? "
Tace "eh, insha Allah nida anty zamu zauna lpya bawanda zeji kanmu "
Yayi murmushi ya girgizakai yace "I wish so "amman yana ganin wuyar abun,
Sunata fira kusan 40 minutes ya zaro akwatin zoben da yasiya mata ya bude, tace "Wow" tana zaro ido da rufe baki ganin haduwar zoben na diamond me shegen kyau,
Yakara matsawa kusa daita yace "here's our engagement ring,plsss let me put it on your hand"
Tai mai wani kallo tana murmushi ta make kafada tace "nagano wayon naka, so kake katabani hankalinka ya kwanta"
ya kalleta yayi guntun murmushi yace "don't take me wrong Allah my intention is not to do that ,kawai I want to put it on you "
Tace "ban yarda ba "
Ya rufe akwatin ya dora akan cinyarta yace "alright have it "ya dauke kai
Ya tamke fuska tatsaya tana kallonshi feeling sad ya juyo yana kallonta yace "I want to go back home"
Tai fuskar tausayi ta dauki zoben ta dora a kan lap dinshi ta dora hannu kan dayar,
Tana mishi good look tace "feeling happy now? "
Yayi murmushi ya bude akwatin ya zaro zoben ya dago hannunta yanajin wani diffirent soft ya saka mata zoben,
Ta lumshe ido har yasaka mata tanajin nice bazato taji yayi kissing din hannun ta bude ido dasauri jin yarrrrr jikinta,
Idanunsu suka hadu yana mata love looking yace "will you marry me? "
Tanata kallonshi batare data saniba bakinta ya furta "I'm ready to marry you "
Fahad ya Saki dariya yana kallonta tai sauri ta dawo tunaninta ta rike baki not knowing me tace yake dariya,
Ya dago "inasonki me kyau da duk wani abunda kikai "
Tai dariya ta rufe fuska yace "yanzu zankoma, very soon zan aiko parents nawa yanzu mufita inbaki tsarabarki "
Tace "thank you "tana kallon hannunta
Yace "u r beautiful kome kikasa dole yamiki kyau "
Tai murmushi ya bude yafita itama tafito ya bude gidan baya ya dauko ledar ya mika mata,
Ta amsa tace "Nagode "tana murmushi
Yana mata kallon shaawa yace "I'm going "
Tace "bye take good care of yourself for me "
Ya daga kai kurum, taki tafiya yace "just go sekinshiga gida zantafi "tai murmushi ta juya tana tafiya,
Yabi kugunta da kallo da suke sababurna baburna ππ€ ya lashe lips yanata kara kallonsu, harta kusa shiga gida ta juyo ya sakarmata murmushi ta daga mai hannu tana murmushi ta shiga gidan, ya girgiza kai yana kara cusa lip abaki ya shiga mota yabar unguwar,
Faseelat nashiga gida taga ummi tsaye bakin kofa da hijab a hannu tace "ummi lpya inazaki? "
Ummi ta harareta tace "wace irin fira ce kuke haka har 1 hr Allah da bakishigo ba sede kiganni awajen"
Faseelat tace "yi hakuri ummi bawani abu fa dan Allah kiyarda dani ummi "
Ummi tace "bahaka bane ba rashin yarda bace ai se anayi ana duban bakin gatari ko faseelat "
Faseelat tace "hakane umminmu zan kiyaye, kinsan ummi muje kiga zoben da yabani da kayanda ya siyomun a Italy da yaje "
Ummi tace "hmmmm marar kunya muje nagani "suka wuce ciki,
Suka zauna suka fara fiddo kayan, wasu dogayen riguna biyu da turare da agogo, se dayar ledar sweet ne kala kala tun wadanda ya taba semata,
Ummi tace "kaya sunyi kyau, zobenma yayi yanzu idan abbanku ya dawo se anuna masa "
Faseelat ta kwantar da kai kan cinyar ummi tanajin dadi tana ta kallon zoben hannunta,
Ummi ta kalleta itama she's happy ganin faseelat din na son abun awannan karan,
Anahaka abba ya shigo ummi ta nuna mai kaya yagani,
Yace "naga kaya Amman waye wannan ya sunanshi aina yake, saboda inyi bincike kanshi donke ba budurwa bace da zaaita jan jiki gwara in dagaske yake yafito ayi aure shine "
faseelat kanta duke tace "sunanshi fahad dawood kuma a GRA gidanshi yake "
Abba yace "yanada mata kenan? "
Tace "eh "kanta kasa,
Ummi tabata fuska, "wai wannan yaron da bewuce 30 ba shine yake da mata har yana neman ta biyu? Gaskiya nikam abun ya siremin "
Abba yace "wannan ba matsala bace inde beda matsala, kuma ke faseelat ai kina iya zama da kishiya ko? "
Faseelat tai sauri tadaga kai ummi ta watsa mata harara tace "tashi kiba mutane wuri sakarai ni nan kinganni da kishiya ne? Kike wani murna zaki auri me mata "mtsssw
Faseelat ta tashi ta shiga daki
Abba ya duko kasakasa yace "angayamaki ita irinki ce me shegen kishi "yayi cikin zolaya.
abu a duhu abba wayasani ko itanma hakan take π€£
ai comments ko infasa auren fahad ehe π
[7/12, 11:01 PM] Maman Mamy: β°β°β°β°β°
*RAGGON MIJI*
β°β°β°β°β°
By
*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
βββββββ
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION~*
βββββββ
*~βWe beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*
4β£6β£
*another page for you rukayya haroun(maman nour)* *and erminatou*
Ummi tace "gaskiya alhaji bazan kai diyata gidan kishiya ba "
Abba yace "haba asiya be kamata kina magana irin haka ba, ita ai ba budurwa bace jawara ce kinga mawuyacine tasamu saurayi, dan Allah kibarta tunda tanasonshi karki sage mata gwiwai "
Ummi tace "ni ban iya kishi ba bare ita hakanan kaje aimaka wani mugun abun kana zamanka lpya "
Abba yace "shikenan tunda zancen kikeso bari nabaki wuri inkingama mitar kikawomin fura ta "
Ya tashi yabata wuri, ummi tace "shikenan se inki magana, yanzun intayi auren ko nima hankali na ba kwanciya zeba bare ita, tunda taji tagani shikenan Amman dole na dage mata da gyara na musamman in inaso tai daraja "
Ta tashi ta nufi dakin abba,
Faseelat nashiga daki ta haye gado ta kunna data cikin farin ciki,
Messages nagama shigowa tabude na maman amira wanda yanzu ta meda number ta da my anty , ta bude message nata "wai antyn amira kinmanta danine?ko duk zawarcinne ya boyeki?har munyi tafiya mundawo, in bazaki zoba kibani address naki zanzo ni saboda yarki ta matsamin "
Faseelat tai dariya ta tura mata "zanzo insha Allah zuwa jibi de nima ina missing naku "
Tafita tashiga contact na fahad ta turamishi "masoyi naji dadin kyautar ka, Allah yakara maka budi ya kareka daga sharrin makiya, kanata kara kyau miye sirrin ne?"
Ta turamishi tana murmushi ta kashe datar se barci,
Da laasar fahad ya kirata suka kara shan vedio call sannan sukai sallama,
Se dare ta samu tabude data bayan sunyi bankwana da habibinta, ta shiga message din maman amira "ππΌππΌππΌthank se kinzo inanan ina zuba eyes"
Faseelat ta tura mata "don't mind"
Tafita alokacin fahad ya turomata reply kamar haka "amin cutie karki damu da kyauta da namiki bakomai bane danko raina kikeso zanbaki, kinason kisan sirrin?"
Faseelat tace "thanks eh inaso inji "
Cikin zolaya yace "aisha ce sirrin tana kula da service dina duk lokacin dana bukata ana bani "
Faseelat ta tura mishi "π To yayi kyau ,tunda ta isheka me zakai dani "?
Yace "I'm joking fa naga kinhau I just test you kinga kema kishinne dake zuwa zakuyi kuyita hadamin zafi "
Faseelat tace "aini bazanyi kishi da anty ba "
Yace "hmmm Allah yasa, gobe inanan zuwa fa, don kullum zanzo sekin gaji dani "
Tace "ai bazan gaji ba kazo yanzu ma "
Yace "kina tsoron nawa da rana ma yaaka kare? "
Tai murmushi ganin ya sauya zancen tace" good night sleep well π"
Yanagani yayi murmushi ya cigaba da aikinshi.
Da safe abba yaje yasamu baba babba akan maganar fahad yace zesa amishi bincike akansa,
Da marece faseelat taci gayu sosai tasaka kayan da ya siyomata, tafito ummi tace" kinyi kyau gaskiya ina zuwa halan? "
faseelat tace "fahad ne yace yana kan hanya "
Ummi tace "to waike bazaki ce yarika shigowa ba kullum fira a mota? "
Faseelat tace "to ummi zanmasa magana "
ummi tace "kibada asiyomiki dan juice mana kitafi mashi dashi yadansha "
faseelat tace "to bari nabawa Mubarak "
Ummi tace "sekinfa dage yarinya, don ba khalil bane wannan awaye yake kuma yanada mata "
Faseelat tace "nasani ummi bari naje "
Ta juya ummi tabita da kallo rigar duk tafito mata da shape dukda tanada fadi, kuma faseelat dan mayafin rigar kawai ta yafa,
Karfe 5 yazo ya mata waya tafito, be fito daga mota ba ta cikin glass yake karemata kallo, harta zo tabude marfin motar ta shiga,
Yaja numfashi ya sauke ta kalleshi tana turo baki,
Ya lumshe ido ya bude yace "cutie wannan kwalliyar fa?"
Tace "i did it just for you "tana marmara ido cike da jan hankali,
Yayi murmushi yanabinta da ido yace "thank you I'm happy, kinyi kyau sosai "
Tace "thanks ga ruwa"
ta mika mai water melon juice yana kallon kwalin yace "ni bazansha ba sede kibani a baki "
Ta bata fuska tana hararanshi yace "abinda aisha keyi kenan komi yimin take taimin wanka, tasmin kaya, ta bani abinci abaki, amma ke just kiban drink yagagara "
Ta harareshi tace "kabari kaga muyi auren ba wanka ba har goyonka ma zanrika yi "ya kyalkyace da dariya yace "sure? "
Ta daga mai kai yace "to fara tundaga yau mana mugani inda gaskene"
Ta tunzuro baki gaba tace "open ur mouth"
ya wage baki yana jiran tafara bashi,
Tai dariya ta bude marfin ta dora mishi kwalin abaki, ya dage yayita kwankwada, tai sauri zata janye caraf ya rike hannun alamun ta cigaba da bashi,
Ta dora mai yayi ta sha ta fiddo ido tana kallonshi tasss ya shanye yana meda numfashi ,tana mamaki ta sadda robar Kasa bakomi ciki ta dago tace "amma yau anty batai maku girki ba ko? "
yayi dariya yana goge bakinshi da handkerchief yace "yau nidakaina nashiga kitchen, bawani yunwa nakeji ba jindadin juice dinne yasa na shanye shi duka, kinsan duk abinda ya fito daga gunki dole yayi dadi "
Ya kashe mata ido daya,
Ta rufe fuska tana dariya,
ya dauko waya yace "kigyara nai miki pic, badani zaaiba bare kice danna samu na tabaki ne "
tace "OK, amma zamuyi da kai a wayata "
Ya saki murmushi yanajin dadi,
Ta dan fiddo ido ta matse baki ya dauketa, pic din yayi mugun kyau kalar rigarta purple da baki ,
shiru be dagoba yanata kallon bakinta da ta matse kamar zatai kisss,
Tana kallonshi tace "muyi atare mana "
cikin rashin sanin abinda yake yace "wait for me "
Ta turo baki ta matsa ta leka wayar yayi zooming bakinta yanata kallo ta fashe da dariya,
yayi sauri ya dago cikin dawowa tunani,
tana nunashi da yatsa tana dariya tace "Allah kacika jaraba dubi duk yadda idanunka suka koma "
Yayi murmushi ya jingina da seat ya juya ya kalleta yace "kamar kinsani kima shirya "
Ta canza maganar da matsawa kusa dashi ta dauke su pic,
Tana dauka shiko hankalin nakanta tana samu tadauka ta matsa tana dubawa tace "yayi kyau sosai, kasan wani abu zan dorashi a status da insta "
Yayi murmushi yace "idan kuma bakisaka ba ni zan saka akan nawa "
Ta rufe baki "rufani kasayani ban shirya abinda zancewa anty ba, gobe ma