Showing 183001 words to 186000 words out of 212110 words

Chapter 62 - Ragon Miji

10 Jul 2025

8353

abinda ke damunki ne? bayan laulayi "

faseelat tasaki murmushi tace "Dan Allah yaya karka damu kanka wlh ba abunda ke damuna, cikin ne kawai kuma lokaci ne nanda wasu watanni kome zezama labari "

yayi shiru yanata kallonta but he smell something fishy,

Fadeela tafito tanata faraa tace"sannu da zuwa anty maraba "

faseelat tabita da kallo har ta zauna tayi fesss Abunta tayi mulmul cikin kankanin lokaci,

Faseelat tace "yawwa anty, ya gida ya kuke? "

fadeela tace "lpy lau ya jiki jiki? Allah yaraba lpy"

faseelat tace "amin" tana harararta tace"anty kema fa akwai Alamar tambaya kode yaya yagama cika aiki? "

fadeela ta dukar da fuska tana dariya,

faseelat tajuya wurin omer taga yanata murmushi yana wa fadeela kallon kasa kasa, tai murmushi tace "hakane ko yaya? Munkusa samun baby"

yace "ihhm amma not very soon"

faseelat tace "I'm happy sis akula da mu sosai"

Fadeela ta bugar da maganar ta hanyar cewa "me zaa kawomiki akwai white vegetable rice da stew akwai sakwara, sobo zakisha ko kunun aya ko mango juice? "

faseelat ta zaro ido tace "anty kuna shagali walla wannan jerin abincin fa shiyasa duk kukayi kiba"

omer da fadeela sukai dariya ta cigaba da cewa "toshi ke tayaki ko? "

fadeela tace "anty duk shi ya girka tayashi kawai nake baya bari na yin kome "

faseelat tai murmushi tace "yar gata, to yanzu ni a koshe nake sede duk inda naga kunun aya bana bari akawomun nasha nasa albarka"

fadeela tai dariya ta Tashi,

Faseelat tai shiru se tunanin soyayyarsu da fahad ya fadomata yadda yake tayata abubuwa kullum yana fadin banso kina wahala,

Omer yaga ta tafi tunani yace "hmmm I knew it theres something behind it"acikin ranshi,

ya tashi ya haye sama yanajin haushi yasanta komun nacinshi bazata fada ba tunda tasan baya yin mijinta, tunda Allah yadora mata wahala base tai tayi ba,

Fadeela ta dawo ta ajiye plate da cups asama da robunan Faro biyu cikeda kunun ayar, itako tanata tunani,

ta koma ta zauna tace "anty ga yanan "

faseelat tai sauri ta dawo tace "OK nagode" ta dauka ta shanye roba daya, tanata santi,

Sunanan ta daga kai ta kalli agogo 3:30 tasan yanzu Sun daga,

se karfe 5 tafito ta tafi gidan baba babba sannan tadawo gida seda akai ishai takoma gidanta,

gidan tsit se tsoro ma yakamata katon gida ita kadai aciki ,ta tsaya tunani gidansu de ba yarinya gashi ma bataso asan bakowa gidan seita don duk Wanda zeji yasan baa kyauta ba tunda bata lpy,


Hakanan ta daure ta haye sama tayo wanka tai shafai wuturi sannan ta dauko kurani tafara karatu daga bakara da niyyar tanason ta sauke tunda yanzu tanada lokaci available,

Tanata karatu har 11 sannan tayo alwala ta kwanta bacci kuwa ya dauketa,

suko su fahad tuni suka isa Sudan jikin abba de gashinan sede ace dasauki, umma koda taganshi da Aisha tayi tunanin don faseelat bata lpy ne bazata iya tafiya ba,

Data tambayeshi ita seyace tana gidansu wannan ya kwantar mata da hankali,

ranar sunyi saa khadija da lady da safiyya sunzo sunanan,

dasafe suka wuce Malaysia,

Tunda faseelat ta tashi tai salla tai karatu ta gyara gidan ta dan kwanta bacci tana tashi batajin yunwa tai wanka ta kunna data se kuma ta sauka tafita garden shan iska,

gidan jinshi take badadi samm ashe har gwara tana ganin shi yana wulakanta tan da rashin ganinshi gabadaya, kewar shi data addabi zuciyarta ne yasa kullum tana like da waya tana kallon pic nasu da nashi shikadai dana marigayiya amira,

ita kadai take rayuwa kuyum kamar mayya, wani lokaci su Mubarak sukan leko ta,

Itake fita tasiyo abunda take bukata 5million de itace taketa amfani daita, Kafff maganinta sun kare taje tasiye wasu da abubuwan da takeso,

cikin sati biyu takeyin saukar kurani bayaga nafilfili datakeyi duk dare,


Bayan wata daya,



Lokacin kuma cikinta yana wata ukku cifff sosai yake motsi damuwar da take ciki bata hanata kula da kanta ba hakan yasa tatafi asibity donyin antenatal bayan da aka duba cikin akai mata blood test da alluran da akeyi se akamata scanning tana kwance tana kallon abinda ke wakana acikin TV din,

Itakam ta gansu rututu abun yadan bata tsoro har takasa kilga yawan abinda take gani, bayan angama ta tashi akabata results nata, they're 4 in number dadi yagama kasheta taita ma likita godiya kamar shi yabata baby's din sannan takoma gida,


Kullum jira take taga fahad ya kira amma shiru wata daya da sati biyu bawasa bane, yanzu takan samu sauki kafin ciwon ya motsa mata hakan yasa takanji bukatar mijinta akusa daita, kuma ba yadda taiya sede ta hakura

Zaune take a garden tai zaman dirshan kafafunta mike tana ta kallon pic na Hero awayarta, tana ta hawaye yadena sonta yanzu bayayin ta idan bahaka ba bayadda zaai yakai haka beko ji muryarta ba,

Tana kallon pic din take rera wakar novel din raggon miji wadda shalele ta raira wadda taiwa suna da *(kewa)* wakace me ban tausayi da karya zuciya tana wakar tana hawaye, ga kadan daga cikin baitocin wakar"duniya babu tabbaci, rayuwa seda hakurii,ni faseelat ya zanyi ne da raina, don fahad yadena so aguna"
*(fans shalele naji daku dan jindadinku na rera muku waka zan turomuku ita bayan kunsha karatu kuji ta zakuji ta very sweet muryar cakwai😂se abi ahankali banda group na maza don kar asamu matsala🤣seriously waka donku fans💃🏼*

abun gwanin ban tausayi,

tadade nan sannan ta tashi takoma bedroom ta kunna sunna TV tana kallo, idan tana kallonta takanji saukin abinda ke damunta saboda malamai dake waazuzzuka da dama,

Tana cikin kallo ne wani malami(sheik gombe) yana waazin mata, akan bin bokaye Wanda ya gabatar a sokoto abun yadaga mata hankali,

yace" se kina zaune da miji lafiya lokaci daya kiga ya sauya ya tsaneki anjuya mai kwakwalwa anjuya mai tunani bakomai bane ankaishi wurin boka ne kowani ka surgumin dan tsubbu yahadashi da bakaken aljanu sunata watangariri da rayuwar shi, mata sekun dage da addua dake da yaranki gabadaya dan wasu cikin ku shedanu ne basuda imani ko kadan, zasuiya yin komi dansu samu biyan bukatarsu"

Waazin yake ita kuma tana tunani da zuciyarta take shawara"akwai fa alamar tambaya akan al'amarin fahad daga samun yar matsala se sumar dani se tsana haka kawai? to idan asirinne wazai mashi asiri? duk nan kusa ?"

Tace "to nasan abinda zanyi nasan komin laifin da nai masa bazaace ya kwashi 2month baya ganina ba kuma ya dawo da fushi dani ,Nide nasan mijina na sona bazemin irin wannan kiyayyar ba kuma baze iya 2month bama batare dani ba ,zanjira lokacin dawowarsu I wish ba asirin bane ,"

Shiru tanata kewar mijinta har ,2weeks sukayi kuma basu dawo ba hakan na nufin 3month zasuyi yanzu kam abun yamata yawa kukan ma ta dena ,

Takoma awo cikin is 4months amma yayi girman ban mamaki ga yawan motsi, fatar cikin tabude tayi wasu line kugunta yakara girma ,she complain about the movement doctor yafada mata lpy lau cikinta yake sede tarage damuwa don bp dinta yahau sosai ,

Bayan 1 month takoma awo su fahad jirginsu yasauka Nigeria batanan lokacin kusan karfe 11 na safe ita kuma tun 9 tabar gidan ,sunyo kibarsu hankalinsu kwance,

Koda suka shigo gidan kwasss dashi ,hannuwansu cikin na juna suka shiga dakin fahad wanka kawai sukayi suka kwanta da niyyar yin bacci fahad beiya baccin ba seda yadan huta da aisha,

Karfe 12 faseelat tabaro wurin doctor tadawo gida ganin sabuwar mota fa ke yasa tagane sun dawo farin ciki yarufeta don ganinshi kawai takeso tayi kotaji dede aranta,

Dasauri ta shiga ciki bakowa falon ta wuce daki ta fesa wanka ta saka doguwar riga black color ta fesa turare sannan tafito ,tasan karfe 1:30 dole yafito zuwa masallaci ,tashiga kitchen ta dafa kuskus fari already tanada stew takwashe ta kai dining sannan ta zuba tafara ci domin yunwa takeji don yanzu bata iya 30 mnt bataci wani abu ba ,

Tanaci tana duba wall clock dake jikin dining ,

Bayan ta gama takoma falo ta zauna ,

1:35, segashi yafito ta naganin yafito tamike tsaye ko kallonta beba zewuce tace "sannu da zuwa"

Yaja dogon tsoki yafita,hawaye suka gangaro mata yanzu kenan asirin aka mishi takoma ta zauna tafashe da kuka mecin rai ,tana kuka take cewa"waye yamin haka ?saboda me ? Ya cutar dani ya cutar da hero dina Allah yaisa bamu yafeba"
Seda tasha kukanta sannnan ta tashi ta haye sama dasauri dukda hawan step namata wahala segashi tafito da hijab jikinta da key na motor a hannu tazo bude kofa yabude yashigo beko kalli inda take ba yawuce tabi bayanshi da kallo zuciyarta na zafi,hawaye suka zubo mata ta sharesu da hannu ta fita ,

Tashiga mota tafita ba inda ta tsaya se arriyad islamic center ,ta shiga tayi saa tasamu malan yahya tamishi bayani yace"asiri ne akamishi amma insha Allah zamu temaka ze samu lpy"

Yabata magunguna masu hadi na sha,na turare, dana shafawa,ta amsa tai godiya akai list kudin maganin nera 15k kamar anbata kyauta taita godiya tafita, tana ta Sauri ta koma gida ,

Da shigarta tasamu aisha zaune a main falo aisha tajuyo tana kallon cikinta da yayi kato kamar me cikin yan biyu wata tara ,ta dauke kai zuciyarta na zafi ,

Faseelat ta shigo ciki da ledarta rike ahannu ta matsa wurin aisha tace"anty kundawo lpy ?"

Aisha tace "lpy lau"inshort

Faseelat tajuya ta haye sama ,don ta dena mamakin Aisha tunda tana gani kome ke faruwa,

Hijab kadai ta cire ta fidda sauran maganin a ledar tabar nashan tafita kitchen ta wuce direct ba drinks daze rufa asirin magungunan inba zobo ba ta hada zobo tajuye magungunan ciki ,tahada shi sosai yaji kayan kamshi takai fridge,

Akan dining kulas kadai tagani sun cinye abincin ta dauka ta meda kitchen,tawuce daki tai laasar tana fitowa taga aisha da keys zata fita ranta yayi dadi,

ta shiga kitchen ta dauko jug takoma daki tanada ganyen magarya tasan amfaninshi bayan sit birth,guda bakwai ta tsinka ta wanke tazubasu a jug cikin ruwa tamurje su ,ta bude kurani ta karance suratul bakara kafff aciki ta rufe tatsaya tunanin yadda zatai dasu tunda wankan dole se awuri me tsarki,dabahaka ba da a tanki zata bawa baba tsoho ya zuba kowa yaita wanka, ta tashi ta sa a fridge tana fatan in yadan fara dawowa dede tabashi yayi wanka dasu,

Kusan karfe5:40 tsit da alamu duk basunan ,

Tashiga kitchen tadora girki da man habbatus sauda da zaitun ta soya miya domin hadasu cikin na shafawar tahada tuwon shinkafa miyar ganye a wahalce tagama ta dora dining tahaye sama ta sake wanka tai Maghreb ta dauko kwalin maganin da akace na hiyaki ta aje kwalin tafita dashi,

A falo ta jona burner seda tai ja sosai ta kwarara maganin falon ya turnuke da hiyaki ta dauka tana haki ta zagaye wurin dining dashi zuwa sama dataje dakinshi seda takara zubawa sannan ta kullo dakin ta fito ,

Takoma daki tana ta tunani kanta na matsanancin ciwo har akayi ishai tayo alwala tazo ta kabbara tana salla tana kuka ,

Bayan ishai fahad yadawo daga gun abokanshi har lokacin aisha bata dawo ba ,

Yana bude gidan yaji wani kalar kamshi badadi ko kadan kanshi yayi nauyi,dasauri ya haye sama ya bude dakinshi nan kuwa yafi koina samu yabude windows ya kure fanka shaf shaf ya shige toilet yayi wanka ,ya fito yasa boxer ya zauna bayason fita falon sega aisha tazo ta rungumeshi tana cewa"nadade ko ?im sorry"

Yayi shiru saboda tunda yashigo kanshi yafara matsanancin ciwo,

Tace"ya de?"

Yace"normal kikawo mana abinci anan sama plsss banason fita falon"


Tace"to shikenan"ta juya ta fita ta dauko abincin ta medo sama ,

Tayi serving dinsu a plate daya tafara bashi abaki tana cewa "kamar bakajin dadi?"

Ya samu ya hadiye na bakinshi dakyar yace"im not well"

Tazo zata kara masa ya kauda kai ya dauki jug ya tsiyayi sobo cikeda cup ya shanye ,

Seya fara jin juwwa juwwa ya tashi yana layi yafada saman bed nantake bacci ya daukeshi ,

Hankalin aisha yatashi taje ta birkito shi taga yana sauke numfashi ahankali yana bacci ta gyara mai kwanciya ta koma taci abincinta takoma dakinta tai wanka ta haye bed tana charting se 11 takoma taga har lokacin yana bacci ta juya tafita ,tana ta kalonshi wata zuciyar nabata takira likita wata zuciyar na cewa tajira yatashi,

Takoma daki ta kwanta se bacci ,

Faseelat kam yau kokadan bata rumtsa ba daga zaune take ta salla tana adduoi a sujud tana hawaye ,sosai takejin jikinta ya mata nauyi amma hakanan tadaure tai tayi,


Karfe 4am ya farka da faduwar gaba yanajin kamar.....



What i want u to understand asiri ma ciwo ne bayan addua dole se antashi tsaye da neman magani har Allah yasa adace ,Allah yabawa marassa lpy ,lpy amin.






Karkumanta da wakar kuma banda dariya 🤣
➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰








By






*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*





✍🏽✍🏽 *GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION*✍🏽✍🏽✍🏽

We are bearer's of so golden a pen🖊
We write assidiously perceiven no pain
So magical
Our creative golden pen🖊
Be hold our words
A product of our pen🖊
Savour our words
For it will cause you no pain.✍🏽


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/




8⃣6⃣



*Allah (S.A)yace ku rokeni zan amsa maku*

*Manzon Allah (S.A.W)yace Wanda baya rokon Allah (addua) Allah na fushi dashi*
Bukhari





Karfe 4am ya farka da faduwar gaba yanajin kamar kirjinshi ze fito ,ya dafe kanshi yana ya mutsa fuska ,

Ba tunanin da yafara yi sena faseelat where she's? Ya rumtse ido yafara tariyo baya he can remember every thing that happend ya fiddo ido waje a tsora ce ya sauke kafafunsa kasa "what's wrong with me nine kuwa may be nayi mafarki but ba gaskiya bane abinda brain dita ke fadamin"

Yafita dakin dasauri zuwa na faseelat,

Tagama salla Ta mike kafafuwa domin ciwo suke mata jikinta bakomi daga ita se zane da half vest don bata iya kwana da kaya jikinta yanzu,

Ya murda kofar dakin ya shiga yayi tsaye yana kallonta zuciyarshi na kara gudu ,

Tunda taji budewar kofa ta meda kallonta gun yana tsaye idanunshi jawur yana ta kallonta ,

Hawaye suka cika mata ido suka gangaro tasa hannu ta share ta dauke kai,

Yanata kallonta hijabin jikinta bata iya boye girman cikinta ba he is asking himself "wata nawa yayi besa ta aido ba"

Yanajin matsanan ciyar kunya ya shiga dakin jikinshi mace ya zauna kusa daita ya dora kai a kafadarta ya saki kuka me taba zuciya,

Yana ta kuka tana ta hadiye nata batasan lokacin da ya kufcemata ba ta rufe fuska da hannu tanayi cikin ta se motsi yake ,

Ya rage nashi kukan ya dago fuskarshi yana kallonta hawaye nata kara wanke masa fuska murya na rawa yace"bani bane I'm not the one ,how could I??"yayi shiru yanajin ciwo yace"yazaai namiki haka ?yazaai na wulakanta rayuwa ta, you're my life wlh bansan yaakai ba ,bansan meyasa meni ba "

Ta cigaba da kuka tasha wuya ta azabtu sosai,

Yace"Truth me sonki baze taba bari namiki haka ba ,yama zaai natafi for almost 3month batare dake ba ,inasonki sosai da cikinki I don't know what come over me,ki fahimceni plsss"

Tana ta kuka na murna dana tausayin kanta yace"kiyafemin faseelat wlh da hankali na bazan iya dukanki ba tuntuni natuba da tunani na bazan iya kauracemiki ba ,bazan dena kula da lafiyarki data cikinki ba i hate my life dana kasance azzalumi I cheat you kiyi hakuri plsss"

Ta share hawaye tana ta hadiyar wani kukan tace"kadena fadar haka bayin kanka bane saka akeyi,before ina tunanin kadena sona ne daga baya na fahimci abun yafi haka nasha wuya hero I'm not eating ,im sleepless ,not enjoying my life for all this time,I cry loudly and silent, "

Ta riko fuskarshi tana hawaye tace" baaso muna tare anmaka asiri hero don katsaneni ka rabudani,u maltreat me hero u had said zaka iya kasheni "tafashe da kuka

Ya rumtse ido yana tuna time din da yafadi hakan tanata zubda hawaye amma beji komi ba,

Yana hawaye yace" I'm very sorry, u have gone through a lot of pain I'm sorry, waye ze min haka waye ze cuceni haka wannan shine mafi cutar da akamin a rayuwa what if something bad happened to you ?wlh faseelat I will not forgive my self for doing all these to you"

Ta girgiza kai tace "I don't know bansa niba abinda kawai nasani shine wasu nason Su rabamu ,wani naso yashiga tsakaninmu,bansan kome hakan ze kara musu ba"

Still fuskarshi na rike da hannuwanta Hawaye suka zubomai yana jan zuciya yace"I'm sorry plsss forgive me for all that I did to you "

Hawaye na cigaba da zubomata tace "stop begging for my forgiveness, before inajin baka kyautamin ba inajin cewa ka zalunceni but tunda nagane u have been charmed sena rika jin tausayin ka don tuni nake karyata kaina nace bazaka iyamin haka ba,nasan kana sona hero kuma nima haryanzu ina sonka ba abinda ya sauya "

Ya kure ta da kallo yana kara tausaya mata,tace"I Love u hero and I will always do"


Ya rungumeta tsam without saying a word,dukansu sunata hawaye suna murmushi,juyin da cikinta keyi sosai ne yasa ya saketa ,ya cire hijab din jikinta yana kallon cikin he can see the movement kobai taba ba,

Abun yabashi tsoro yadda cikin ya tale yayi Kato haka,motsin shima abin ban tsoro ne ,

Ya dora hannu sama yanajin dadi da tsoro, tameda kallo ga hannunshi dake kan cikinta Wanda tai matukar kewa,

Just like cikin na juyi ze fito waje,haka yake ganin abun ,

Ya dago ya kalleta yace "baki lpy ko? naga girman is too much"

Tana ajiyar zuciya tace"lpy ta lau hero yaranka ne suke da yawa"

Ya bude ido yana murmushi yace " my babies? kinsan at that time inata adduan triplet"

Tai murmushi tadora hannu akan nashi dake saman cikinta tace " u ask him only 3 but he add one for you, he love you hero 4child in one time, Allah love you hero he give u all in life beauty, money, well,education and children,

Farin cikin shi yaki boyuwa nishi yake yana fidda ido yace" 4 child for me?all praise be to Allah for all his blessings to me alhamdulillah"yanata murna yana taba cikin yanajin dadi,

Hankalinshi nakan cikin nawani lokaci sannan ya dago yana kallonta,tana ta kallonshi da murmushi fuskarta ,ya zuba mata ido yana kallonta yana murmushi yana karajin sonta fiyeda da,

Faseelat tana ta murmushi tace"I miss u hero ,and everthing about u ,ur smiling ur perfume, sweet word and

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login