Showing 195001 words to 198000 words out of 212110 words
da nai maso haka ba don baruwana ko auren ko rabuwar"
Anty salma tace "yaran yanzu akwaisu da kwallafa soyayya just kiyi mata addua amma inajin tausayinta"
Mommy tace "dole ne"
Karfe 7 Aisha tatashi tabude ido tarikabin dakin da kallo anty salma,da mommy da Sadiya sukayo kanta,
Hawaye na zubar mata zuciyarta na mata zafi tace"ruwa mommy kubani ruwan sanyi zuciyata ciwo sosai"
Anty salma ta fiddo ruwa a fridge ta matsa tatada ta tana bata,
Ta dansha tabari jin bawani sauki shan ruwan da takeyi,
Ta medata ta kwantar daita,mommy tace"sannu Aisha Allah yabaki lpy"
Hawaye na zubarwa Aisha tace"mommy yaya ya sakeni ko? Ina yaya dan Allah mommy kubashi hakuri wlh bazan iya rayuwa in babushi ba ,ku kiraminshi dan Allah "
Mommy tai tagumi tana kallonta,
Anty salma tace "kiyi hakuri Aisha be sake kiba kuma kinsan baze zo dubaki ba yanzu kibari adan kwana biyu ze hakura"
Aisha tafashe da kuka tana danasani tace"mommy I cheat myself nacuci kaina da kaina wlh mommy ko yaya yamedani baze soni ba nasan yanzu ba wacce ya tsana sama dani,mutuwa zanyi mommy kutayani addua Allah yagafartamin nasani nan dawani lokaci zani mutu"
Kowanensu yanata hawaye Sadiya tace"anty kiyi hakuri zaki cigaba da rayuwa in Allah yaso kicire abun aranki kuma kita istigfariii Allah zeyafe miki"
Aisha tajuyar dakai ta cigaba da kukan nadama ,mommy ta zuba tea akatada ta zaa bata ta kauda kai tace"banaci banajin yunwa kubarni dan Allah"
Mommy tace"toshi cikin naki bakison yarayu ne?ki daure kici abinci don shima yayi kwari "
Hawaye masu zafi suka zubowa Aisha tace"mommy I'm regretting plsss forgive me ban dauki shawaranki ba ,ban tsaya dogon tunani ba nabiyewa shedan yanzu mommy what of in inada cuta wayyo Allah na"
Mommy tace "bakida ita bakida wata cuta aysha ki sawa ranki hakuri ko kinsamu lpy ki cigaba da renon cikinki"
Dan dole Aisha ta dansha tea din ta dauke kai,
Yunwa ce tatada faseelat daga bacci tara saura ta sauka kasa kamar taci babu tabude fridge ta daga robar nutri yoghurt ta banbameta ta shige kitchen dasauri abincin jiya ta dumama a oven ta zauna ta cinyeshi tasss ,
Sannan tatashi ta soyawa fahad kwai da dan Irish da plantain kadan ta kai kan dining da ruwan tea ta shiga toilet tai wanka tasaka blue duguwar riga me adon baki ajiki dankwalinta baki ,bawani makeup don daka ganta tana cikin tashin hankali, ta sauka tafara goge inda yakamata agyara agidan, dakyar tagama tana zufa sannan ta zauna a palon tanashan iska,
Se 10 saura fahad yatashi yanata ya mutsa fuska kanshi na mugun ciwo ya shiga toilet yayi abinda zeyi yafito yasaka kaya ya fito daga dakin ,ba inda idanshi yafara sauka se dakin Aisha ,idanunshi sukai jawur yawuce ya sauka kasa jiki mace,
Faseelat na ganin yafito ta tashi tsaye tana mai kallon tausayi ,
Yazo ya zauna kan kujera ya rumtse ido ,
Faseelat taje gefenshi ta zauna tace"kayi hakuri hero kazama me daukar kaddara me kyau ko akasinta,ka daure kaji mijina ,banason wani Abu yasameka "
Ya daga kai kurum tace"muje nabaka abinci sekasha magani ka kara hutawa "
Ya lumshe ido yace"banason ci kibarni plsss"
Tace "tom nima nakoshi kowa ya hakura da abincin"
Ya riko hannunta yace "hey kefa kinsan problem naki karki wahalarmin da babies dina plsss eat ur food"
Tace"tonaji kaima sekaci tukun kadaure "
Ya daga kai ,ya tashi yana rike da hannunta suka tafi dining, tunda ya tunkari wurin yake kallon seat na Aisha dana amira ,
Yaja seat ya zauna yakurawa seat din Aisha ido ,faseelat tafara zubamai tana hadiye hawayen idonta don itama abinda yake fado mata kenan,
Yana tuna lokacin da suke cin abinci awurin suna feeding juna time amira na da rai da time dabasu haifi ko amira ba yaduke jikin table yana kuka zuciyarshi na zafi ,
Faseelat ta ajiye zuba abincin ta duke itama tana kukan tanata kuka take cewa" meyasa nashigo rayuwarku meyasa nakamu da sonka? ina dorawa kaina alhakin komi saboda ni anty tai haka,dama bansan anty ba dama kome yadawo baya"tana kuka mecin rai,
Fahad ya dago da hawaye kan fuskarshi yana kallonta yace"kidena cewa haka u r my wife shiyasa hakan tafaru idan da batasanki ba maybe ba yadda zaai muhadu"
Ta dago tana kuka tace"look at the house bakowa saini yazanyi in manta baya yazan in manta rayuwarmu dasu anty "har numfashinta na daukewa ,
Fahad ya goge hawayenshi ya matsa gunta yafara gogemata hawayen yace" kidena kuka ,haka Allah ya kaddara ze faru ,barin gidan zamuyi donmu manta rayuwar da mukayi dasu kiyi hakuri kinji "ya cigaba da share mata hawaye,
Tai shiru tana kallonshi sotake tace mai yayi hakuri Su zauna don atunaninta ze sauko watarana amma abinda take gani yasa takara ganewa baze hakura yamedo Aisha ba,
Ya debo abincin ya kai fork bakinta ta kauce ta ansa tarika bashi yanacin abincin kamar madaciya,
Beci sosai ba ya dauke kai tacigaba daci tana ajiyar zuciya,
Fahad ya fiddo waya yakira sabeer yanason yabashi sako to office don se bayan week ze koma aiki,
Suna zaune a falo TV kashe sunyi zugum kowa yana tunani ,sabeer yayi knocking ta tashi tarufe kai taje tabude ,
Sabeer yashigo da faraa yace" amarya bakya laifi "
Tai yake, tace"ina kwana"
Yace"lpy lau "yana kallonta
Tajuya ciki sannan yashigo shide he love faseelat shaawarta ma ce yasa ya auro fatouma dan Suna kama amma they're different fatouma zuciya tana iya sati tana fushi in ta gadama ,shiyasa yafison radiyarshi itakuma Jan class amma bata saurin hawa ,
Daace lpyar fahad lau dabaa bunda ze hana ya zage sabeer tasss saboda kallonda yake mata,
Ta zauna gefen fahad shiko yazauna kujerar dake facing nasu fuskokinsu duk ba annuri sema jawur dasukayi,
Yana raba ido yace" lpy kuke ko?meyafaru?"
Fahad yace"lpy lau" ya mikamai wata small laptop yace "kabawa manager banjin dadi senan da week zancigaba da aiki"
Sabeer ya zaro ido yace"amma kasan hakan naiya jawo maka problem kuma wane irin ciwo ne wannan?"
Fahad yace"kayi yadda nace kabashi kuma ciwon zuciyane da bp shikenan"
Sabeer be yadda ba ya kalli faseelat yace"faseelat mike faruwa ?naga kamar anyi mutuwa nasan ba ciwo ne problem dinba"
Tai shiru kanta kasa fahad yace"ni zaka tambaya ba itaba kuma nabaka amsa plsss leave us now"
Sabeer yatashi yanata kallonsu yace"toshikenan Allah yasawwake "ya juya abunshi ,
Fahad yabishi da kallo shide beda problem matansa biyu tunda yakara auren ma kiba da kumatu yake ta ajiyewa,
Sabeer yakaiwa manager ,manager yace seya biya rashin aikin dazeyi tunda bawani akai,kunsan abun turawa,
Shiru gidan yake ba motsi dukkansu sunata tunani had lokacin abinci yayi tatashi tadora sanwa,
Aisha ko basauki hawaye batsayawa aka fidda kowa adakin se ita kadai ba abinda takeyi daga kwancen se istigfaree me tsadan sayyidul istigfari ,
Haka sukaita rayuwar duk badadi,fahad baya bacci sede barawo haka Aisha,
Bayan kwana ukku suka kwashe kayansu suka koma airport way wani sabon gidanshi it's plat house amma kato bawani kayan alatu kamar wancan,tareda megadinsu,
Wanshekare Su Umma suka sauka Nigeria domin jikin daddy yayi sauki har umara sukaje ,
Fahad ya dauki faseelat suka tafi wurin Umma yi musu barka da arziki,
Umma data koma sharrr tanata murna tana ganinsu duk murnar takoma ko zama basuyiba tafara tambayarsu " lpy miyasameku haka?"saboda duk sun rame more especially faseelat dabata gama dawowa Dede ba,
Fahad Yakama hannun faseelat ta zauna ya rumtse ido yace"umma kimin addua ,kimin addua Allah ya cire min son Aisha, Umma Aisha tamin asiri koda mukaje gunki bana kula faseelat for 5month tana zaune da ciki itakadai agidan,randa hankalina yadawo dede wanshekare nabi Aisha wurin boka umma aisha nakama Aisha tana sex da boka"yakarasa da kyar
Umma tace"innalillahi wainna ilaihi rajiun!!! Amma Aisha ta aikata katon laifi "
Faseelat na hawaye tace "Umma kibashi hakuri yadawo daita bazata karaba nasan tayi nadama ,Umma duk ni najawo hakan dana shigo rayuwarsu"
Umma tace"baze dawo daita ba saboda nasan baze hakura ba daya rika zaluntarta gwara yabarta,kidena dorawa kanki laifi"
Faseelat ta dago jikakkun eye lashes dinta tace"haka zakice Umma ?dan Allah kibashi hakuri ciki ne daita kuma tanason yaya sosai"
Umma tace "toyi shiru zai medotan idan Allah yaso"
Ta kalli fahad tace "ina Aishar ?"
Yace "bata lpy suna asibity "
Tace"tom zanje nadubata Allah yabata lpy "
Yayi shiru daddy yazo suka mai ya jiki fahad yatashi yafita be zame koina ba se asibitin yasamu room number wurin doctor yanufi dakin,
Har yadora hannu akan handle yaji kukan Aisha tana cewa"mommy kikirashi nabashi hakuri ya yafemin ,dan Allah kukiramin yayana inason ganinshi"dawata murya me rauni,
Zuciyarshi tarika harbawa dasauri idanunshi jawur yajuya yafita beko ganta ba saboda bayason yaji tausayinta,ko ganintan yakara mai tension danko hakan muryarta kadai tasa yaji tausayinta,
Umma ta shirya ta dubo Aishar tana ta kuka tana rokonta tabawa fahad hakuri harta tafi,
Bayan sati aka sallamesu lokacinne fahad yakoma aiki amma baida wata walwala ,don kullum gani yake kamar ranar abun yafaru,
Aisha gidan anty salma aka medata tanata kuka basauki alamarinta,
A can ma mommy jinya take don jininta yahau kullum se tasha magani,koda fahad yazo ko maganar Aisha batai masa ba shi kanshi abun yabashi mamaki ,amma yabar zancen shima betaba maganarta ba ,
Aisha duk tabi ta rame satin ta daya gidan anty salma tamatsa mommy tabiya masu umara itada Sadiya suka tafi,
Tunda taje bata komi se Neman gafara tana kunyar haduwa da Allah dan se yanzu take kara ganin munin abunda tayi,
Ciwonta ma na nan se abinda yakaru sede bata damuwa da ciwon dan tanaji ajikinta mutuwa zatayi,tanata kewar fahad wani lokaci Sadiya seta kirashi Su gaisa dan Aishar taji muryarshi,tarage damuwa,
Ana haka aka shiga azumi acan Su Aisha sukai nasu faseelat ciki be barta yiba sede ciyarwa akemata,
Ranar salla da fahad daita sune har gidan baba babba koina sunje barka da salla ,
Bayan kwana biyu da salla Su Aisha suka dawo lokacin da Mommy taganta seda ta firgita ta jeme kamar kallemu ,
Dawowar ta gidan yakara mata tension saboda tana ganin shige da ficen fahad dukda beda walwala ,taso tabashi hakuri da tayi niyyar tunkararshi seta kasa inta tuna halinda ya same Su ,
Bayan sati da salla yaje da faseelat gidan yanata nan nan daita ,
Lekowa kawai tayi ta gansu jininta yakara hawa zuciyarta taita zafi ,dan tuni tagane yasaketa kuma gashi batason konawa yamata ba,
Hawaye taitayi tana tarin bakinciki shikenan ta rasa yaya ?sede ta ganshi da wata yana nuna mata kauna,
Sukayi mintoci suka tafi ,
Se dare Sadiya tashiga dakin Aisha domin itakadai ke kara tausaya mata dansu mommy ma haushi take basu yanzu,
Ta sameta tana ta aman jini ta ruga ta kira mommy akatafi daita hospital,
Tunda suka shiga daita ba allurar dabaai mata ba amma takasa bacci sede pain din yarage hakanan aka medata rest room ,
Su mommy suka zagayeta suna kuka ,
Har wanshekare suna nan wurinta,
Aisha da jini ke shiga jikinta hawaye nata bin gefen idonta ta kamo hannun Sadiya tace"mutuwa zanyi kikiramin faseelat nabata hakuri dan Allah "muryar na rarrabuwa,
Sadiya tatashi tafita dagudu tana zuwa gidansu faseelat taita knocking faseelat tazo tabude ,tana ganinta gabanta yafadi,
Tana haki tace" anty kizo asibity anty Aisha bata lpy sosai tanata kiranki dan Allah kitaho "
Hawaye suka cika idon faseelat batasan lokacin da suka gangaro ba bako tsayawa daukar hijab daga ita se doguwar riga da gyalenta suka fita,
Tana cikin motar ta tana bin bayan Sadiya,
Suna isa dasauri tafita harta manta da ciki jikinta suka shiga dakin da Aisha take kwance,
Aisha na ganinta ta mika mata hannu tana hawaye faseelat ma nayi ,ta zauna gefen gadon,
Aisha tace"kiyafemun faseelat nacuceki na rabaki da mijinki for almost 5month ki yafemin ,mutuwa zanyi"
Faseelat tana kuka tace"bakimin komi ba anty nice namiki laifi kiyi hakuri ciwo ba mutuwa bane"
Aisha tace "ki yafemin mutuwa zanyi dan Allah ki rokarmin yaya yayafemin tun kafin na mutu na cutardashi naci masa amana"
Faseelat tace"ya yafemiki since be rike kiba "
Aisha tace"I want to see him before dyeing ki kiramin shi nasan zezo "
Faseelat tatashi tafita tashiga mota tana tukin ganganci taisa maaikatarsu fahad hankalinta tashe kowa se kallonta yake tasamu aka nunamata office nashi tawuce waiter nata mata magana tashige ciki ,
Fahad da yayi nisa atunani yadago fuska jin kukanta da kamshinta ya zuba mata ido yana kallon kayan jikinta da katon cikinta da yayi kamar yafashe ,yabude
Baki da niyyar yin masifa ,takarasa wurin shi tana kuka sosai ta zukunna gabanshi tace"dan Allah kayafemata kame data dakinta anty tana cikin ciwo sosai "numfashinta na daddaukewa ,
Ta cigaba da cewa " kazama me yafiya hero dan Allah kasamar mata kodan karamin wuri ne a zuciyarka ko kanaso ta mutu?to wlh idan baka hakura ba anty mutuwa zatai"
Ta mike ta kamo hannunshi yanata kallonta betashi ba tace"
dan Allah hero kazo kaga anty kataso kaga anty yadda ta koma "cikinta yayi wani irin juyi ta sakeshi ta rike cikin tana cigaba da kuka sosai,
Yayi sauri ya rikota yace" muje nagantan kiyi shiru kidena kuka "ya gyara mata gyalen ya kama hannunta suka fita ,yana jin haushin mazan da suka ganta haka,
A motarshi suka tafi tanata kuka sede kallonta yake zuciyarshi na ciwo,
Suna isa asibitin ya fito ya rikota suka shiga tare tanata kuka har time din,
A bakin kofa yasamu Su ramlat sunata kuka yatura kofar yashiga,
Kallo daya ya mata hankalinshi yatashi yanzu sunyi 2month besata a ido ba ,
Ya saki faseelat yakarasa bakin gadon datake kwance Mommy tafita daga dakin don ba karamin haushin fahad takeji ba,ta zubamai ido ne kawai,
Aisha da idonta ke rumtse tanata sallallami ta bude ido ,
Fahad jikinshi ya dauki rawa hawaye na zubarmishi yace" aisha ta Aisha kece kika koma haka?"
AISHA tana hawaye tace"kayafemin yaya mutuwa zanyi kayi hakuri da abunda na maka"
Yanata kyarma ya rike hannunta yana hawaye yace"kidena fadar haka na dade da yafemiki ,kuma bazaki mutu ba Aisha idan kika mutu ya zanyi da rayuwa ta ,zaki samu sauki zamu cigaba da rayuwarmu kamar can baya "
Ta girgiza kai tace"mutuwa zanyi yaya inaji ajikina mutuwa zanyi"
Faseelat ta kara volume na kukanta tana matukar jin tausayin aisha,
Fahad ma kuka yace"kidena fada inasonki aisha har yanzu ina sonki inason nakara rayuwa dake akaro na biyu"
Tai murmushi tana kallonshi yace"I still love u aisha nayi nayi be ciru ba ,I truly love u and I will always will"
➰➰➰➰➰
*RAGGON MIJI*
➰➰➰➰➰
By
*MAMAN MAMY*
*(SHALELE)*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
8⃣9⃣
*Dedicated to my daughter(anti Mamie)* writer of *naga ta kaina,ustaziyya ko yar duniya,and now namijin duniya*
*ina makaranta namijin duniya karki yarda 200 ta hanaki bin buk din dan yanzu yake dadi wlh ga tarin darussa just kibiya 200 ta wannan number 0816 652 6167 ,idan ta bank ne zakiiya tuntubarta don samun account number dinta ,namijin duniya yayi wlh karki bari abaki labari,ina fans dina ku garzaya wurin diyata kusha nata basiran💃🏻*
*akwai wani novel dinta guda daya daban fadi sunanshi ba her first novel duk wacce ta turomun sunan novel din zata samu damar karanta littafin namijin duniya kyauta, amma mutum ukku kacal keda wannan damar hurry up write the name and send it to my what's up number 07063721063,after kinturo zaki cigaba da samu for free ,senajiku, duk meson shalele yaso diyata anty mamie 😘*
Allah subhanahu wata'ala said :- kullu nafsin za'ikatul maut,wa nablukum bishsharri wal khairi fitna,wa ilaina tur'jaun.
(Anbiya'i 35)
Ankabut verse 57:-kullu nafsin za'ikatul maut,summa ilaina turja'un.
"And certainly we shall test you with something of fear ,hunger,loss of wealth,lives,and fruits,but give glad tidings to the patients one's. Bakara 155
" who when afflicted with calamity say truly to Allah we belong and truly to him we shall return.156
Hawaye suka zubomata ta lumshe ido tabude tace "thanks nagode yaya da duk soyayyar da kanunamin"
Ita kadai tasan pain datake going through,
Ta dan juya kai ta kalli faseelat dake tsaye tana ta kuka tana share hawaye da gyale,tace"faseelat nagode da soyayyar da kika nunamin nida amira ,inafatan zaki mana takwara don nima mutuwa zanyi"
Faseelat takara volume na kuka ta rufe fuska tanayi ,Aisha tai murmushin ciwo ta meda kallonta akan fahad ,tana ta kallonshi,
Yanata hawaye hannun ta still anashi yace"I love you Aisha u r part of my life"
Kallonshi take tayi bako kyaftawa,yanata hawaye ,
Lura yayi numfashinta ya dauke idanun basa motsi jikinta ya saki,
Nan take jijiyoyin kanshi suka firfito yakara damke hannunta ya duke jikinshi na kyarma agabanshi daddy ya rasu now Aisha bayan amira,kuka kezo mishi yasamu ya hadeshi,
Ya dago fuska ya juya yana kallon uwar yaya, tanata kuka da alamu batasan ta mutu ba,
Ya tashi jikin na rawa ya tsayar da jinin dake shiga jikinta ya juyar daita sannan ya rufe mata ido ya nufi wurin faseelat daketa kuka ya kamo hannunta batare da yace komi ba ,
Ta kalleshi ta kalli Aisha da aka meda kanta yana kallon bango ,takara kallonshi tashin hankali karara fuskarta ,
Dakyar yasamu Yace "mutafi in medaki gida"
Tace" ta mutu ko ?anty ta mutu"
Tai luuuu zata fadi ya tarbeta sede har ta suma ya ida zauniya kasa yasaki kukan dayake dannewa faseelat na jikinshi a sume ,
Jin kukan yayi yawa mommy ta shigo dakin ta ganshi rikeda faseelat yanata kuka,
Ta kalli gadon Aisha ta kuramai ido gabanta na faduwa taisa tana juyota taga babu rai jikinta ,hawaye masu zafi suka kara wanke mata fuska ,acikin ranta tace "ka kashemun diya son"
Ta zauna ta Dora Aisha jikinta tana kuka shikenan tayi bankwana daita shikenan ta tafi bazata kara dawowa ba,
Kukan Su momy yasa Su ramlat shigowa itada Su anty salma suka samu Aisha ta mutu dakin yakacame da kuka ,
Asibitin dake very silent takacame da sautin kuka nurses biyu suka shigo suka ga abinda ke faruwa sune suka kawo gado suka dora faseelat dake lifeless suka tafi ceto rayuwarta fahad ko nanan zaune yakasa tashi se kukan dayake kamar mace,
Mommy kam zuciyarta ciwo take sosai ,
Anty salma ce ta dauki Aisha datakoma sakwaf bayan sun rufeta suka fita daita ,dukkansu suka Mara mata baya basujira likitoci ba suka tafi abinsu ,
Faseelat kam suma tayi bayan sun samu ta farfado tanata kuka jinin ta ya hau sosai sukasa mata drip da allurai ciki dandanan bacci ya kwasheta ,
Fahad seda yakara shan kuka sannan yatashi yanjin jiri beko leka faseelat ba ya tafi gidan mommy akan hanya yakira wani yaronshi akawo likkafani ,sannan yakira sabeer ,
Sabeer na kitchen gimbiya fatouma tasashi aiki kiran fahad yashigo ya dauka yanata goge zufa yace"dude what's going