Showing 27001 words to 30000 words out of 173457 words

Chapter 10 - A BAKIN WAWA (AKANJI MAGANA) COMPLETE

30 Oct 2025

3958

tashi tsaye?

yace' meyasa, meyasa,meyasa Baki karbo numbern ta ba? Ke kika bata tamu ? why,why zakiyi haka ehh?
Itakam Sam tunanin Amsar numbernta bezo mata ba,kawai numbers dinsu ta bayar harda Tata,ai tasan zata kira,

tace' ai tare ma da ita muka........
Sai ta tuna abinda ta fada Mata? tace kar tafada tare suka dawo "ohhh God tafada kasan makoshinta, tana dafe goshi,
Da sauri Yusuf yadawo

yace' tare da ita kuka dawo ko? Fada min ehh? Tare ne ko?
Ganin tayi shiru tana kallansa yasa

yace' nasan tare ne ai,nasani tunda kika ki karasawa nasani,me tace maki?
Yafada kwalla ta cika idansa, shikuwa yaseer hotan kawai yake gani yana kuka,? tuno rayuwar su da ita,
Kallansu tayi ganin halinda suke ciki, don kawai suna son ji labarinta,su Basu da saurin kuka koda kuwa an dakesu Amma,zata iya cewa bata taba gani sunyi kuka haka ba, numfashi taja sannan Ta Basu yarda Akayi suka hadu,da labarin da ta bata da komai da komai har kawo dauko su a airport.

Wani irin kuka suka hade Kai da gwiwa sunayi,ita de kawai kallansu take yi itama ta Dan share hawayen ta, a ganinta farin ciki zasuyi Amma sai akasamu akasin haka,suna kuka to kukanne batasan na meye ba. Bayan ta share hawayen ta

Tace' to wai kukan na meye haka? A ganina na farin ciki ne ai,
Yaseer ne yace'" farin ciki? Kinsan kukan da mukeyi ne? Kuka ne na danasani,kuka ne na danasani,yanzu kinji ?
Danasani kuma? Ta maimaita cike da mamaki,
Yusuf ne ya dago a zuciye

yace' ehh danasani, Shi mukeyi don Allah ki tafi ki barmu mungode,don Allah,.
Yafada yana hade hannayensa wuri daya, ya cigaba da kukan sa,

Tace' nifa ba inda zanje sai kun fada min, danasanin meye kuke kuka haka? Maimakon kuyi farin ciki ta dawo,Amma ku zauna kuna kuka?
Wannan Karan yaseer ne ya hada gumi sharkafi ya dago da kansa Yana jan majina

yace' danasani ne na rashin bin drivern ku dauko ki,da'ace munje mun dauko ki kamar yarda mukeyi kullum da mun hadu da ita ai, da kuma ace munbi maganar Anty( maman ummu). Da duk haka bata faru ba,daman ance binna gaba bin Allah,gashi nan fushi da zuciya ta kaimu ta baro.yaya kiyi hakuri ki dawo don Allah,

Sai yanzu ta gane Inda maganar sa ta dosa tabbas kuwa mama ta fada Mata Amma batace tace su bi driver a dauko suba.

Tace'to yanzu ku daina kuka kunji ko? Tunda tazo basai mu fadawa umma ba(maman su) a bincka ko abada cigiyar ta ba kaga sai a samu ta dawo gida ai ko?
Da wani speed Yusuf ya dago cikin wata irin murya mai Kara

yace' kina hauka zaki fadawa mama? Ida kika fada Mata Tou ko sun samota cazasu ce Basu ganta ba, su turata ga halaka, wannan Karan na tabbata kungurumin daji zasu kaita,damun daji su cinyeta, shikenan mu kuma kin samu a uku ko?
Kanta ne ya wani uba daurewa bata gane Inda zancen ya dosa ba, zasu Kara sa turata ga? halaka??? Mekenan? Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un bata gane ba,

Tace' kunga ku ganar Dani mana meke faruwa ? Bangane ba? Naga de sunan baban ku daya,kuma yar gidan ku ce? Ba Abba bane ya haifeta ba?
Yaseer

yace' Yaya itace cikwan farin cikin mu,yaya itace komai namu tun muna kanana,da yaya muka fara bude ido muke gani a matsayi? mai Kula damu,dukda Yusuf ya girmeni da shekara daya,itace ta reneshi har aka haifeni, ta hada Dani dashi ta rena,bata da wani buri Sama data faran tamana koda zata bakan tawa wani ko ita kanta, she's sacrifice alot of things for us, shes can do anything for us,yaya tun muna yara take Kiran mu da Yusseer wato Yusuf and yaseer, yaya ce ta fara koya mana karatu,dukda ita bata maida hankali Akan karatunta amma kome aka yi Mata ta iya,indai har zata tsaya ta koya din,Amma kuma bata tsayawa tanayi ba ruwanta da karatu Bama taso,kuma mama bata Mata fada Amma mu tana mana fada sosai musamman akan karatu. Ada ba abinda ta iya sai mana wanka da shirya mu,suka dai mukasan ta iya don ko? kunna gas da bata iya ba, Akan mu ta iya mota saboda fitar da muke any how,ita zata kaimu school sai ta dawo ta shirya taje Tata,bata damu ba don ta makara,abinda tasani shine karmu makara,daga makarata take wucewa ta dauko mu ,Idan mundawo ta samu muyi sallah tamana wanka, tasa mana kayan islamiyya, sannan ta kaimu,sai ta kaimu islamiyya sannan zata cire uniform dinta, tun muna yara tayi damu mudena fada mukaki jinta , tace nake cewa Yusuf Yaya naki fada, kullum sai tai rabiyar fada idan ba ita ba ba wanda ke iya raba mu, bata da? lokacin kanta sai namu, Yaya taje cell saboda mu,ba Wanda yasani saI mu sai Allah,bata damu ba, yaya ba ruwanta,tana da tausayi,kuma bata da mutunci,don kaf ma'aikatan gidan tsoron ta suke ji.
? Watarana zata kaimu islamiyya har mun Shiga ta manta bata dauko kudi ba kuma bamu dauko abinci ba, wataran muna tafiya dashi sai tabi ta kofan baya don ta dauko abincin,komawan da zatayi bata dawo ba sai gajiya mukayi muka taho don mu ganta,Jin numfashi a garden yasa mukaje wurin,muka Kira mama,tundaga wannan rashin lafiyan ta koma wani rin shiru bata magana,dazaki Mata magana dubu to nodding Kai zata maki sau daya,tun muna damuwa har muka saba, da shirunta,ta kuma rage kaimu park da duk Friday da Thursday idan an dawo daga school Bama Zama muna park,da can ita ma bata San zuwa gidan kawayen Mama, shiyasa wani zabin muke wuni a park wani zubin kuma mu yi a gidan kawayen ta,
Alokacin da zata tafi karatu mama tace mana idan ta tafi bazata dawoba,koda na fada Mata tace min zata dawo,amma kar na fadawa kowa sai Yusuf, munyi kuka har Abba Saida ya zane mu,a lokacin Yusuf ke fada abinda mama tafada lokacin muna bacci tace,wai yaya bazata dawo ba kuma zamu manta da ita a rayuwar, abinda Yusuf yayi tunanin zata mana irin abinda akayiwa wani abokin mu,muka dena yarda tana zuba mana abinci sannan kome tabamu bamu ci,ko ta tambaye mu yaya sai muce bamu Santa ba, saboda ita aka tashi daga wancan gidan muka dawo wannan gidan.
Ya kifa kansa Yana cigba da kuka,

Yusuf yace' Akan me zaki ce mu fada mata, cewar yaya ta zo?

Kwallan dake zuba a idanta ta share

tace' me zai Hana to mu nemota?
. taya zamu ne mota? Ya tambaya,

Zamu ne mota mana indai a fadin garin nan take?

Yaseer yace' ehh haka ne zamu iya nemota,amma dole sai ta temakon Isiya driver (drivern ta)

Isiya kuma ? Wayeshi) ta tambaya tana kallansu,
Yusuf ne yace' drivern yaya ne,Amma meyasa kace haka,
Ya tambaya Yana goge hawayen idan sa yana kallan yaseer shima yaseer din hawaye yake gogewa

yace' lokacin da zata tafi London tana yawan fita,idan zaka tuna har tambayanta muka sha yi Amma bata Kula muba, Shi zai tamaka mana,

Amma de kasan baya gidan ai ko?

Wannan duk mi sauki ne,zamu iya nemansa ko ta wurin mai gadi ne ,nasan suna gaisawa ai.

Tashi tayi tace' ni Bari na tafi ,kunsan tare da uncle mukazo,idan anjima kuzo ku gaisa dashi,daman Baku taba ganin sa ba bako?

Wanda mukace Yana kama da yaya? Yaseer ya tambaya

Ehh,Shi sai kunzo,ta fice.

?
??
? ?
? ?? Gida ta dawo lokacin wacce zata kaita aiki ta zo,gaisawa sukayi ta fada Mata bukatar ta,dakuma unguwar da takesanyin aiki da gidan idan za'a samu, matar mai suna Ladi

tace' to kinga gidan da kike fada de Gaskiya yan gidan basu da kirki, don nasha Kai mutane Amma suna guduwa bazasu iya ba,bare ace ke, kuma a matsayin kurma ko nace? bebiya kinga kwa ai da matsala, Amma Idan zaki iya bakomai duk mai sauki ne,

Jinjina Kai tayi sannan iya ladi taci gaba da fadin, yanzu zanje gidan Idan tana nema, to kobata nema ma zanyi yarda zatayi? ta? dauke ki aiki.
Kudi ta Ciro ta bata tace tayi kudin adaidaita, godiya tayi ta fice, tace'" naji damus ai yanxu zanje nadawo ma ina dalili taab,watakil ma a karamin,ni ina ruwana koma yar leken asirice be dame ni ba.

? ?? Maman Sadiq ce tace'? Allah yasa de asamu,
Ameen tace, su nan suna hira matar ta dawo bata jima ba,

Tace' ai anyi dace,amma wai aikin ki gyaran Parlour ne Sama da kasa sai daki idan ance kiyi,da kuma aiki haka de,Amma fa Gaskiya akwai wulakanta mutum ato Gaskiya ce,

Ca tace' bakomai,yaushe kuma zamuje ?

Yau da yamma nace Zan kawoki,sai ki hada kayanki,Idan kun Gama zuwa yamma sai ki kirani Fatsima(mama Sadiq),amsa Mata tayi sannan ta fice,
Maman Sadiq tace' to yanzu bari na hado maki Yan tsuffin kayana da zan bayar sai ki tafi dasu ko?
Bata jira? amsar ta ba ta Shiga daki ta kwaso kayan,ta ajje,waje ta fita wani store ta dauko tsohuwar Ghana most go ta goge ta tas ta zuba kayan a ciki

tace' kuma Riga daban zani daban sannan dankwali ma daban,haka masa aikin keyi,wayanci de, bansan mezaki je yi ba Amma koma meye nasan ba abin cutarwa bane dukda Baki fada min ba. ta?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? bude Baki zatayi magana

tace' kinga tashi ki dauko abinda zaki bukata a saka a ciki Bana San godiyar ki,
Kallanta tayi kawai,kuma har ranta take fada,tashi tayi ta dauko man shafa da turare da inner wears daman ita powder ba mutuniyar ta bace,bare kuma jam Baki,sai lipgloss ta zuba aciki, maman Sadiq ta dauko sabulu da klin dayawa ta zuba Mata su,ta zira handbag dinta Suma aciki daukan wasu kayan tayi
tace' taje tasaka,sawa tayi ta fito zanin plane ne kuma bata iya daurawa ba,ita skirt ma baso take ba bare kuma wani zani,a haka ta fito ta tattare Shi Sama tana tafiya, lokacin maman Sadiq ta fito daga kitchen itama,sai datayi dariya mai isarta tukunna ta sarara ta koya Mata yarda ake yi, ita dai wannan kayan wahalar baso ba take ba.
? ?
? ? ? Suna cin Abinci tace' ina San na sai gidan da su Amina suka tashi daga cikin sa,zaiyi nawa kike ganin?
Maman Sadiq ta kalleta tace' idan Abban Sadiq ya dawo zansa ya tambaya maki duk abinda ake ciki zaki jini, daga Kai kurum tayi.....

By: '''Hijjart Abdoul'''
? ?? Cwthrt=??A BAKIN WAWA* ? ?? _Akanji magana_


Not Edited
POST 2020
REPOST 2023



? ?? 12

?? Da sallama suka shigo parlourn, kana ganin su zaka San sunyi kuka, sabida idan su da beyi kama da normal ba,amsa sallaman mama tayi tana kallansu taji jikinta yayi sanyi,saboda ummu tana dawowa ta Basu labari kamar yarda suka bata, tabbas suna San wannan yayar tasu,shin ina zasu ganta? Samun kanta tayi dacewa Insha Allah za ma su ganta.
Katse Mata tunani sukayi ta hanyar gaidata,amsawa tayi,

tace' kuje kuyi breakfast don Naga alama kamar bakuyi ba ko?
Yunwa suke ji bata kadan ba,Amma a halin da suke ciki yasa baza su iya cin abinci ba, Yusuf ne

yace' a,ah mun koshi sai da muka ci muka fito ma,
?? Badan ta yarda ba sai don kada ta matsa masu,yasa ta barsu, Kiran ummu tayi,ta tashi ta Shiga ciki,
Tana Shiga ummu na fitowa ganinsu a haka kowa yayi shiru yasata karasowa

tace' twins dina sannunku ko nace mako besties? A,ah ba besties ba yusseer kuke so??
Tafada tana kallansu,wata harara da Yusuf ya wurga Mata yasa ta fashewa da dariya,

tace' remember Yaya salama tace ko nayi maku laifi Banda fushi,Banda kallan banza,bare kuma a samu harara ato,
Ta fada tana murguda Baki tare da Zama ta daura kafa daya kan daya,
Ba Wanda ya tanka Mata,don sun san halin kayansu,yanzu suna magana zata ce yaya tace kaz tace kaza,kullum sai ta Kara maganar ta.
? ? Ganin sunyi shiru yasa

tace' yanzu uncle zai fito sai ku gaisa ko. Daga nan sai muje garden mu tsara? yarda za'ayi ko?
Numfasawa Yusuf yayi

yace' mun samu numbern sa,mun kirashi yace yau bazai samu damar zuwa ba,baya garin,kuma sai jibi zai dawo,
Ya fada Yana kallanta,itama kallansa tayi

tace' jibi kuma? Meye wani jibi,nifa kunsan bagane wannan abubuwa nake ba,kumin da yaren da zangane mana kwace mun wani jibi,
Ta karashe da daukar remote tana murguda Baki,
Yaseer da tunda yazo bayan gaisuwa bai Kara magana ba,

yace' muma haka yace mana basani muka yi ba,ya fada Yana hararanta,
Tsabar ta rena masu hankali, idan sun fada Mata sai tace batasani sukuma sai su fada Mata,yaci ace idan karatune to ta hardace,

' tace jibin ce Baku sani ba?to kar kusani,
Tayi shiru sai kuma can

tace' laaaa Monday ce ko? Ita jibin inke nufi?
Bawanda ya daga Kai ya kalleta tv ma suke kallo,suna cikin haka sai ga AA nan yazo zai wuce? har yaje Baki kofa zai fita bawanda ya lura dashi sai ita,tana ganin zai fita kuwa ta tashi da gudunta

tace' uncle Baku gaisa ba da besties din nawa ba,kuma zaka fita,
Sai anan suka lura dashi,basa ganin sa sai bayansa kawai suke gani,

Yace' haba ummu bakya ganin sauri nake Zan fita, so nake naje na gaida mutane kinsan de Sarai gobe Zan koma ko?
Turo Baki tayi gaba tace' nasani Amma ai gaisawa ce kawai zakuyi fa? Bata barshi yayi magana ba ta dinga Jan hannunsa,bata yarda janshi take,juyowa yayi kawai suna tafiya don yasan komin dare yadawo sai sun gaisa shiyasa kawai ya zabi su gaisa din yama huta da mitarta,
Tunda ya juyo ya fara tahowa suka kalli juna suka zuba masa ido, bako kiftawa har ya karaso gabansu ya Mika masu hannu Amma basu san ma Yana yi ba sai da, ummu ta tabosu tukunna, Yusuf ne yayi dan yaken da kana ganinsa zaka san? iya fuska ne kawai,ya bashi hannu,

yace' Yusuf,kawai iya cewa don maganar ma kakarewa tayi,
Murmushi yayi yace wannan duk ganin nawa yasa kuke kallo na haka? Kamar na maku kama da wani?
Ya fada Yana mikawa yaseer hannu,maimakon ya Mika masa sai ya zuro hannu a aljihunsa ya ciro hotonta da sauri ya bude ya dauko guda daya,shidai kallansa kawai yake kuma bai dauke hannun nasa ba ganin abinda ya dauko yasa Shi kallan? hoton, yaseer kuwa tashi yayi ya? Kara hoton a fuskar Shi,

yace' haba ummu Yama zakiyi kice wannan basa kama,suna kama wallahi, kece Baki ga kamar ba, Yusuf mekagani,
Yusuf bai iya magana ba don Shi tashin ma yakasa yi,ummu ce ta matso,

tace' laaa uncle kuma fah hakane kuna kama wallahi,
sai kawai tayi dariya, girgiza Kai AA yayi ya amsa hoton a hannun sa

yace' muga da wacce nake kamar,
Kallanta yayi a fili ya furta? student?
Kasantane? Ummu ta tambaya,ehh nasanta mana a school din da nake lecturing take karatu,bata magana yarinyar sai da na ganku a airport kuna yi ,ashe ta warke yanzu tana magana,
Amma fa ni banga kama ba anan,ya fada Yana kallansu,

Yusuf yace'daman Kai ai bazaka ga kama ba,Amma kuna kama fah.

Yaseer da har yanzu yake kallansa yace' dole akwai alaka a tsakanin ku da ita,
Kallan yaran yayi yace' Ba kune Kannan taba taya kuma zai Zama da alaka a tsakani na da yarinyar nan, ina da nawa iyayen da suka haifeni,itama kuma tana da nata iyayen tunda har tana da kannai.
Yusuf da ya tsani yaji an alakanta ta? da ace iyayensu su suka haifeta,ya tashi cikin wani hargagi ,

yace'?? IYAYE ??Wanne iyaye,? Wanne iyaye take dasu? Bata da wani iyaye.? Wanne iyayen ne zasu nemi tura yarsu karatu batare da an Kara waiwayar taba? Wanne iyayenne zasu nemi halaka yarsu? Wacce uwa ce wannan da bazata bawa? 'yarta tarbiya ba?? Wacce uwa ce da zata tura 'yarta wani wuri tace tana so 'yan uwanta su manta ta? Wacce uwa ce wannan? Idan ita ba 'yarta bace Shi kuma uban? fa? Ai Shi 'yarsa ce ko? To Wanne irin ubane wannan da zai tura 'yarsa? karatu batareda yana tura Mata kudin da zata bukata ba? A yarda yake da wadata meyasa bazai je ya ganta koda sau daya bane ba a shekara? Wanne irin ubane da 'yarsa zata tafi tayi wannan adadin shekaru batare da yaji daga gareta ba kuma hankalin shi bai tashi ba? Fada min sune zata Kira a matsayin? iyayenta ??
?
? ? Kawo yanzu kuka yaci karfinshi, dauriya kawai yake yi kar hawayen su zubo sai dai kuma bai San? da cewar tunda ya fara ba yake zubar da hawayen ba, Saida ya Gama ya zauna,ya dafe kansa Jin yana Sara masa, yaseer ne ya dago dakan sa? cikin wani irin low voice

yace' da'ace nice ita da bazan kirasu da marikana ba,sun san basa santa meyasa suka reneta,sun san basa Santa meyasa Basu wurgar da ita ba,meyasa Basu kaita gidan marayu ba ta tashi acan,meyasa basu bada ita ba ga mai so? Sun manta cewa 'da na kowa ne? Ka fada mana yakayi shiru uncle??
AA kuwa tunda suka?? fara maganar yake kallansu,sai yanzu yasan menene matsalar ta, rashin iyaye,
Zama yayi,
Yana kallan ummu yace itace wacce kika bawa Anty labari?
Daga masa Kai tayi,don itakam sun kulle Mata Kai,ai basuyi wannan maganar da ita ba,koda yake bakomai bane daman zasu fada Mata ba,kuma yanzu taji,.
Kallan Yusuf yayi yace' naji bayan daga wurin ummu tana bawa Anty labari,kuma naji kunce zaku nemota can I join you guys ??
Basu Kai ga magana ba Anty ta fito don fadawa ummu taje tayi gyaran daki,Amma sai ta tarar Yusuf na fadan wannan maganar, kuma basu lura da ita ba,

tace' Idan ba damuwa Nima ina cikin wannan tawagar can I??
Tafada da guntun murmushin a fuskar ta,bawai tayi murmushin bane don kanta,kuma baikai zuci ba,can kasan zuciyar ta tausayin Ummusalma take tare da tausayin su kansu besties din,tasan halin da suka Shiga to itama zata Shiga ko bai Kai Rabin nasu ba, murmushin tayi don kawai ta kwantar masu da hankali.

Daga yaseer har Yusuf kallansu kawai suke Basu iya magana ba, ummu ce tayi magana dukda itama tana tausayawa besties dinta da wani irin murmushi a fuska ta?

tace' wooww my mom?,my uncle?
Kawai tayi dariya

tace' daman mama kina son mu haka? Amma kullum sai kin mana fada Ashe kina sonmu,
Ta karasa tareda rungumo mamanta,
Uncle kawai murmurshi yayi don kullum idan aka masu? fada sai tace ba'a San su, dukda labari yake ji,kuma wataran ana Mata fada a gabanshi.
Tashi yayi

yace'ni Bari na koma daki na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login