Showing 66001 words to 69000 words out of 173457 words

Chapter 23 - A BAKIN WAWA (AKANJI MAGANA) COMPLETE

30 Oct 2025

3953


Jitayi kamar ana taba lilon kusa da ita bude idanta tayi,ta kalli gefenta ganinsa da tayi akai shima yayi yanda tayi daidai,, da dukkan alama baima san tana wurin ba ko itace batasan yana wurin ba da tazo, numfashi taja ta sauka ko takalmi bata saka ba taje ta zauna a kusa dashi, hannunsa ta kamo ta saka masa zoben,bude ido yayi a hankali yana kallanta ita kuma tana kallan yatsan da tasa zoben,bata dauke idanta a wurin ba, shima bai dauke idansa a kallanta ba,sun jima a haka tana kallan yatsansa dake cikin hannunta shikuma yana kallan fuskarta,

tace' Dan uwan bracelet di nane, kana so?

Sai yanzu ya kalli hannunsa zoben ya kalla ya kalli bracelet din dake hannunta dake rike da nasa, banbanci kawai nata ya jima a hannun ta nashi kuma sabone amma hakan ba yana nufin idan kagan su zaka ce ba iri daya bane iri dayane komai da komai,

tace' kyauta ce zuwa gareka amma idan kana so,
Shiru yayi hakan yasata cewa' ohh baka so Kenan?
Namma shiru yayi,

tace' okay nagane,
Dayan hannunta tasa tafara kokarin cirewa damke hannunta yayi cikin nasa,

yace' kyautar rowa ko?

Ai naga naka so,

Ni na fada maki?

Gashi kuwa ina ta magana kayi shiru,

Shirun ya karayi yana kallanta,wato shi duk maganar da yake mata tana daga masa kai fa, sai ita ce taza Sami magana, murmushi a zuciya yayi,kallansa tayi kawai ta fara kokarin tashi sai dai hannunta dake cikinnasa yasa ta tsayawa janyota yayi,

yace' ina zaki je ki bar mij...ohhh abokinki anan,

Shiru tayi ba amsa
yace' to dawo ki zauna,dawowa tayi ta zauna taki kallansa,
to naji nagode da kyauta sosai, amma waya baki ?

Kauda kai tayi tace' Neena,badan Yana kallan bakinta ba sai yace batayi magana ba,dukda yasan me tace amma

yace' What? Nuzaif?
Harda su waro Ido, kallan sa tayi da dan karfi,

tace' Neena,Neena nace,

Ohh sai naji kamar kince Nuzaif,

Da Nuzaif sunane?

Ahh nasani? Duniya fa da fadi,

Daga nan suka cigaba da hiransu dukda rabin hiran shiyakeyi amma tana bashi amsa sosai,shike lilasu har magriba sannan suka tashi don gabatar da sallah.

('('('('('

Bayan sati daya sosai abubuwa suka canja cikin kuwa harda wata irin shakuwa tsakanin Binaif da Ummusalma sosai suka shaku, idan tana zuba zance ma zaka ce Big girl din da ce da kasani, sai dai tsantsan irin zaman da sukeyi ne, bata so yana magana tana masa shiru bata san bacin ransa batasan dalilin hakan ba, kamar yanda shima baya san bacin ranta shiyasa kowa yake kaffa kaffa kar ya batawa juna rai, ta bangaren Anty safiya kuwa shirye shirye take sosai, yaje ya kai kudin lefenta da komai, Anty safiya ta dire tace gida ma shi zaiyi to Allah ya taimake Shi yana da gidan sa tun Yana aiki ya saya daya a Abuja daya kuma a Kano,Daddy ne ya yace zai mata furnitures.
A bangaren su yusseer sun kwantar da hankalin su sun aan ba fita ba zasuyi sai dai tunanin da sukeyi ne yasa suka rame suka yi wani irin farin rama dukda suna ci suna sha kuwa,
Binaif ya fara zuwa company Yana aiki batare da ta sani ba, duk wani Abu da za'ayi anyi an kara? modernizing abun da suke sarrafawa sunayin madara da kuma sugar, da yake company din hade yake da gonar shanu harda shi ya hada ya saya, Sannan ya kara da sarrafa sugar da ya fara, sosai abubuwa suka masa yawa,ga gyaran gida da ya taso masa don ma Daddy ya bashi gudunwa haka ma Baba Usman shima ya bashi,to da su ya hada yake yin aikin gida da kuma aikin company,sunan companyn ma ya canza ya dawo UMMU LTD.

Yau ya dawo a gajiye so kawai yake yaji shi a kan cinyarta ta,har wani Allah Allah yake yazo gida ya ganta, yana zuwa kuwa ko jakar Shi bai dauka ba ya shiga parlour, Umma yagani,

yace' Hajiya Umma sannu da hutawa,

Umma tace' a,ah dan nema Kaine Ka dawo? Ya aikin?

Lafiya,yace Yana wucewa ciki,Yana Shiga yaga bata nan duk a zatansa wannan lokacin yawanci idan ya dawo tana kwance ko tana bacci ko kuma tana danna waya, amma ganin bata nan yasa Shi zuwa kofar toilet nanma bata nan sai yayi tunanin kila tana kitchen, toilet ya Shiga yayi wanka ya kwanta har bacci ya dauke shi baisani ba,dayake yamma ne be tashi ba sai magriba a gurguje yayi alwala ya tafi masallaci koda ya dawo ya tarar da Umma da mai aikinta suna kallo suna cin abinci Zama yayi,

yace' Umma wai ina take ne,

Umma tace' wa Kenan?

Mata ta,da wa zan tambaya kuwa?

Umma tace' afto danaga ba ajiyar ta kake bani ba idan zaka tafi shiyasa ai, amma dazu kamar naga ta fita I.......

Ta fita, ya katseta,
Yacigaba to ina taje? Da zata fita? Sata nayi kome? Kuma kina kallanta ko?

Umma tace' ehh wallahi kuma baza ta dawo ba sai nan da sati uku shiyasa ma ta tafi,

Umma banfa gane ba,

Ai bazaka gane ba ina magana Ka katsene sai Ka samu wanda zai karasa maka ai,

Saukowa yayi yace' ummi don Allah kiyi hakuri ina taje?

Uwarka ta zo ta dauke ta tafi da ita bani da ikon hanawa tunda uwarka ce,

Yace' bangane ba kina nufin Anty safiya ta tafi da ita?

Zancen kake so yaro, ta fada tana kai lomar tuwo bakinta, bata Kara kulashi ba,shima tashi yayi ya Shiga daki,dukda a azababbiyar yunwar da yake ji haka ya hakura baici ba,juyi kawai yake yi akan gado, Yana tuna? idan yazo kwanciya ko ya zaiyi? Wayarza yaji tana ringing dauka yayi batare da ya kalli sunan ba,jin mus'ab na cewa"' bb kazo ka dauke mu,tun dazo muke jiranka amma shiru,kama manta da mu gashi kuma kasan wurin uban nisan masifa babu mai adaidaita kazo please,

Tsaki yayi ya kashe wayar ya tashj ya dauki key ya fita,a mota kuwa ya jera tsaki yafi dubu kafin yaje airport fita yayi yana hangosu ya nufa wurinsu suna ganinsa suka rungume shi, shima rungume su yayi amma bayi magana ba sune sukayi ta haukar su don yau hauka zaice masu basu birgeshi ba dukda kowa yayi missing dinsu,sakin shi sukayi suka nufa wurin mota, Mas'ud

yace'? wai bb me yake faruwa ne?
Naga kayi shiru ko wani abu muka maka ne?

Girgiza masu kai kawai yayi yana shiga mota suma shiga sukayi yafara ja, suna tafiya Mus'ab yace' to ko wani abu Hajiya tama,
Nanma dai girgiza masu kai yayi daga nan shiru sukayi basu kara magana ba, suka ci gaba da tafiya har suka iso. Suna shiga sukayi kan Umma gaba dayan su rungume ta sukayi suka sa ta a tsakiya,

tace' 'yan albarka sun dawo,sannunku sannu,ya hanya

Mas'ud yace' lafiya qalau Umma,ya kafarn naki,

Kayya dan nan kafa ai daman ta tafi tsufa ne fa da kuka samu ma ban tsofeba ina dad dan jika Wanda ya kusa candy ai dole kuga haka daman,

Daga nan kuma hira ta barke tsakanin su,Shi daman binaif be shigo ba masallaci ya wuce, sai tara ya dawo Koda ya dawo suna nan suna hiran su,sai dai sun canja Kaya Kenan har sunyi wanka sunyi sallah bai kulasu ba ya wuce daki,

Mas'ud yace' wai Umma me aka yiwa bb ne?

Ummu ta tabe Baki tace' matar Shi aka dauke shine yake cika yake batsewa ko magana ma yaki yayi,

Mus'ab yace' yaushe akayi auren bamu sani ba?

Tace' ai da yake auren kawai aka daura bakowa ya sani ba sai Nanda sati uku za'ayi tariya ai, Nima gobe zanje kauye a can ma za'ayi bikin ai al'adar can za'ayi Wanda zaije yaje Wanda baze jeba ya zauna huta roro,

Mus'ab yace' habade hajjaju kema kinsan zuwa dole ne ai, daga can ma kika Sani ko mu San kamo maki sirika?

Kai amma wallahi da nafi kowa Jin dadi,daman ita wannan daga ita har mijin nata, yarda kuka san mezan ce haka suke basa dariya Kai ko ita ko magana batayi,amma Naga yanzu tana Dan murmushi shima iya kan lebe ne, wani lokacin kuma zaka ga wani abu ya Loma idan tayi Kenan tayi dayawa, ahakan, amma ni naga hakori da sunan dariya bade ZAINABU ABU mai tagwayen suna ba,

Dariya sukasa mas'ud yace' Kenan itama matar haka take?

Mus'ab yace' taab zanso nake zuwa gidan nan ko zanci dariya ita dikim shima dikim,

Umma tace' su haifo yara dikim Kim,
Suna cigaba da dariya abunsu suna hira, duk Yana jiyo su haushi su ma yake ji Suma din, da aka Basu dalilin kinyin maganar sa Amma suke masa dariya, tsaki yaja ya dau waya wai zai Kira amma beda numbern ta ai, tsaki yaja ya garar da wayar Akan gado, daga nan kuma yadena jiyo maganar su kenan ma suna sane sukayi da karfi,kwafa yayi ya kuma juya kwanciyar sa,


Tana kwance a Kan gado gaba daya ta kasa bacci tunanin Shi kawai take tasan yanzu yakai kololu a bacin rai,abinda bata so game dashi Kenan, wayarta ta dauko da tun sanda tazo take son Kiransa amma takasa gashi yanzu kowa yayi bacci Banda ita, wayarta ta janyo ta tana kallan sunansa da tayi saving dashi ko ta Kira? Danna Kiran tayi ta runtse ido tanaji tayi di sau daya tayi sauri ta kashe, tana sauke numfashi Kara dannawa tayi namma haka, sai da tayi biyar idan tayi ringing daya sai ta kashe,

Yana kwance Yana tsuka Jin wayarsa tayi wani munafikin flashing yasashi Kara Jan tsaki da karfi, sai kuma yaji anayi ba'a dena ba janyo wayar yayi Yana kallan number idan aka Kara Kira sai ya Kira yayi rashin mutunci wallahi,aikuwa ji yayi tayi wannan karan haske kawai wayar Shi tayi ko Dan ringing din ma batayi ba aka kashe, a zuciye kuwa ya Danna Kira,

Tana ganin Kiransa gabanta ya fadi? mezata ce masa,har Kiran ya katse ba a dauka ba,wani Kiran ne ya kuma shigo sai da ya kusa katsewa ta daga tana saune numfashi,beji sautin komai ba sai numfashin da ta sauke, shiru yayi itama haka sai can ganin batazayi magana ba ya Shi

cewa' da kinsan Baki da ta cewa kika kirani ? Kika katsemin bacci na mai dadi?

Wani Abu taji ta hadiye me kama da bacin rai, itama

tace'? tunda ni nafi kowa hauka sai na kiraka yanzu ko? To Bani na Kira ba, inaga Nafisa ce don ni ina parlour ma kallo nake sai yanzu dana shigo Naga wayan Yana ringing ita kuma ta Shiga toilet,

abinda ya hadeye yafi nata daci Jin maganar yayi wani iri wato Bama ita ta Kiraba,Shi Yana nan ya kasa bacci ita kuma tana can tana kallo,Jin yayi shiru alamar ya Shaka dayawa yasata cewa' kayi shiru nikuma kallona zanje inci gaba daman Abu nazo dauka Naga wayar na ringing,

Takaicine ya sashi kashe wayar,zata sani ne ai zaya dawo ko? Allah ya kaimu lokacin,

Itama ajje wayar tayi wato tana nan tana tuna halinda zai Shiga shikuma Yana can yana bacci ko?? Addu'ah tayi ta rufe Ido aikuwa bacci ya dauke ta,

Shima dakyar baccin ya dauke shi,don ma gobe weekend daya kwala....



By:? '''Hijjart''' '''Abdoul'''
? ? ? Cwthrt=??25

Washegari? koda ya fita ya gansu a parlour babu Wanda yayiwa magana,? sune da suka ganshi suka gaida Shi sai dai ko kallo Basu ishe Shi a bare ya su samu ya amsa ya wuce su yayi tafiyar sa,

Mas'ud yace' Hajjaju wai ku mayar masa da matar sa mana kinga ni tunda nazo banga yaci abinci na kar ulcer ta kamashi,

Umma tace' naci kwal uban gidan su baza'a mayar ba,olsar ta kamashi a haka zai kare shegiyar zuciyar Babansa(usman) ne duk zuciyar ubansa bekai ubansa Adamu? ba sai kace shine ya haifo shi,

Mus'ab yace' Allah sarki Umma wallahi ni tausayi ma yake Bani,da'alama Yana san matar Shi,

Umma tace' kunga meye aciki Nanda sati uku mai kyau za'a bashi ita, ya cinyeta. Wannan da zaima iya ce Mata Yana sannata ne,

Mas'ud yace' a,a fah ai irin wannan sun fi iya soyayy....

Rufa min Baki marar kunya kawai,
Tafada tare da wurga masa ludayin?? hannunta da take Shan kunu,

Mas'ud yace' haba Hajjaju da yanzu Bana roba bane da tuni kin min asarar Dan Baki nan nawa,kin rage min farashi,

Ummu tace' na lura Kaine Ka koyawa waccan dinkimkim din rashin kunya idan Ka kuma magana wallahi rainka zai baci tam,
Shiru sukayi Basu Kara magana ba har suka gama cin abinsu.

Koda ya fita gidan Shi yaje yaga ankarasa gyaran da yakamata ayi komai angama daga nan kuma sai ya wuce company shima Wanda tuni an kusa gamawa befi kadan ba aiki sune bana wasa ba, duk inda ya kamata?? gyara an gyara hatta sunan companyn an canza ya koma UMMU LTD.? Yafi so Nanda? wani satin sun gama, anfara aikin da yakamata na sarrafa madara da sugar dayake da iya madara ce yanzu kuma harda sugar yake so ayi, da zai sai companyn harda gonar shanu ya hada ya saya. Sai da ya Gama zagaya ko ina ya dawo cikin office da yake Sama window ya bude dayake na glass ne kuma babba Yana ganin komai abinda ke faruwa a kasan office din na iya yankin wurin, dawowa yayi ya zauna, ya dauki waya ya Danna Kira,

yace' nasan yanzu hankalin sa ya kwanta,kuyi duk abinda ya dace,
Bejira amsa ba ya kashe wayar sa, jakarsa ya dauko ya bude takardun Yana neman na company tunda company biyu ya gani sai gidaje da fili, Yana cikin dubawa ne wani rubutu yaja hankalinsa? ? janyowa yayi yaga rubutun kadanne ajikin wata paper anyi stapling dinta da ta fili Zuwa ga Dana Umar Muhammad da date sai kuma signing date din daya gani yanzu shekaru talatin Kenan, numfashi yaja ya zaro takardar ya ajje ta a gefe cigaba da dubawa Yayi ganin Ummu yasa Shi dakatawa ya tuna da ya taba dubawa du haka yagani yawanci a takardar Kara Nemo na Company din da yake nema yayi sannan yayi copy guda daya yazo yaciga da dubawa Yana mai nazartar takardun wasu Basu Kai wasu tsufa ba dukda Duka sun tsufa sai dai kuma yanayi na ajjiya mai kyau yasa Basu ji jiki ba, biro ya dauko ya rubuta Umar, Ummusalma, mas'ud da mus'ab,

Azuciyarsa yake tunanin,Umar Shi aka fara Haifa sai Mas'ud da Mus'ab sai Ummusalma kenan, numafashi yaja a fili ya furta yace' Tabbas haka yake amma mene dalilin rubuta wannan abun? Yana nan Yana tunanin bashi ya tashi ba sai yamma sai da ya Kara lekawa ya tabbatar da komai normal sannan ya dau hanyar gida babu abinda yaci sai malt da yasha guda biyu restaurant yaje yaci abinci ya dau hanyar gida gabadaya kewanya yake kwana daya kacal be taba tsammanin hakan zaiji ba,Ashe jiya kadanne,Akan yarda yake ji a yanzu da zai koma gida ya tarar bata nan,yana zuwa kuwa ya gansu sun sata a tsakiya suna zuba,ko kallan inda suke beyi don haushin su yake ji,sune suka masa sannu da zuwa wuce su yayi ya Shiga ruwa ya watsa sannan ya fito ya tafi masallaci be dawo ba sai da aka idar da sallahn Isha sun Riga Shi dawowa don har sun zuba abinci suna ci,
Suna kallon film din da Umma ke kallo karangiya ta kalli film din saj tari ba adadi amma duk sanda sukeyi sai ta kalla tana cin dariya abinta, Yana shigowa ya dauki remote ya canza zuwa tashar labarai kallanshi ta budi Baki zatayi magana taji anacewa
Ayau ne mukayi hira da wannan sharar mai companyn wato M & M Wanda ya aka masa tambayoyi game da sace 'ya'yansa da 'yar sa wacce ya tura karatu tsawon shekaru har yau babu ita babu labarin ta ance de waka a bakin mai ita yafi dadi,

A safiyar yau ne mukayi hira da Alhaji Mahmud Isah wato mai company nan na M & M da kuma U & U Wanda muka tambaya sai dai kuma be bamu amsa gamshashiya ba,

Abba aka nuna sanda ya fito daga company ranar da ya saidashi,suna masa tambayoyi,

Dan jaridar ya Kara dacewa sa'an nan kuma munji jita jita cewan yaransa Basu mutu ba yayin da wasu suke cewa yaransa sun mutu,wasu kuwa suka Kara dacewa har gawarsu sungani, 'yar sa kuma wacce ya tura karatu yace beda wata 'ya yaransa uku ne kawai a yarda kukaji yace sai dai kuma Wanda suka je karatu dasu nan gida Nigeria sun tabbatar da tare sukayi karatu da ita kuma tare ya kamata ace sun dawo, tambayar da mutane suke yi anan shine shin? tayi aure me acan? Ko kuma de dagaske ba 'yarsa bace? Ko kuma 'yar Dan uwace da ta tafi kuma sai ta koma wajen iyayenta? Wannan tambaya mutenan suke ta yadawa muma baza muce a gaskiyar lamarin ba, ni Bilal Abdullah nake cewa mu hadu a shiri na gaba,

To kunji de yarda wannan abu ya kasance sai dai muce Allah ya kyauta,
A jiya kuma aka nemi yaran minister aka rasa acikin garin Kaduna sunzo ne ziyara wurin 'yan uwa sai dai kuma ba'a gansu an neme su ko Sama ko kasa anrasa sun bace bat kamar allura, Allah de ya kyaut.

Umma da ta bude zatayi magana sai? sakinsa tayi tana kallo ganin ikon Allah, Suma kansu sunji mamaki sai dai basuyi gigin tambaya ba tunda basuga fuska ba, ko da suka dau wayar su duk zancen ake tun Basu fahimta har suka gane inda zancen ya dosa sai dai kuma Basu San gaskiyar lamarin ba,
Shima be tashi ba sai goma idan wannan tashar labarain sun Gama sai ya Kai wata kuma duk sai anyi labarin Abba kowanne kuma da irin abinda zai fada ahaka ya tashi ya koma daki, don ya kwanta sai dai Yana kwanciya baccin yaki zuwa tunanin ta kawai yake, ganin baccin yaki zuwa yasa Shi tashi ya bude wardrobe dinta ya janyo akwatinta ya bude takardu ya kwaso Duka ya daura Akan gado, ya baje su Yana bi Yana gani ya kwashe tsawon lokaci Yana ganin wannan takardun wasu? gabadaya ya mallakawa 'ya'yansa harda Wanda Bana kasar ba kalilan ne nashi Dana matar,na matar sa ma yafi nashi yawa, ya jima sosai daga nan ya tashi ya dauki paper yayi rubutu a ciki ya dauki takardan da zai dauka ya maida sauran papers

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login