Showing 168001 words to 171000 words out of 173457 words

Chapter 57 - A BAKIN WAWA (AKANJI MAGANA) COMPLETE

30 Oct 2025

3948

data San zai taimaka Mata Shi tayi sai da taga taci abincin da ya karbo a wurin Binaif ta sha magani sannan ta fita, tare da rankwashin sa aka.




Rayuwa Mai dadi wannan family din suka fara ta kowanne Bari Basu da matsala Maman Binaif ta tare bayan ya sauya musu gida sun koma nasarawa kusa dasu Umma sai dai da Dan nisa tsakanin su, haka su Saima suna Jin dadin Zama da ita. Sameera kuwa ta bawa Ummusalma labarin abinda yafaru har barin mama gidan su yusseer Basu fada mata tasan ba labari bane me dadi. Su ummu sun koma makaranta inda yanzu cikin ta ya tsufa wata ran taje wata ran kuma tayi zaman ta duk da su Binaif ne suka dauki nauyin gidan su Yusuf batare da Abban yasan hakan ba haka ma asibitin da yake zuwa idan ciwon Shi ya tashi duk su suje biyan komai kafin su Yusuf su tafi zasu tabbatar da sun tana dar masa abin dayake bukata wata ran kuma? shike musu girki idan sun dawo ciki sun rage zuwa gidan su sabida Samum kaluwar da suke bawa Abba, Abba kuwa wataran yaje kasuwa yaga wani kamar Muhammad hakan yasa yaje wurin Shi ganin bashi bane idana a daurin auren Sameera yaga wani ma kamar Shi sai dai kafin yaje shikuma ya tafi haka nan yaji a jikin sa Muhammad be mutu ba Yana nan da ransa kamar kullum yau ma ya dawo daga kasuwa Yana tunanin Wanda ya kuma gani kamar Muhammad Yana tunanin har yazo gida babu abin da yake sai tunani kitchen ya Shiga Dan tana da abinda ya siyo kawai yaji ya fara tunanin haduwar su tun suna yara da irin Abubuwa da yayi ta yi masa har kawo abinda ya saka masa dashi hawaye ya fara yi sosai ya Dade kirgin sa Yana ambatan Allah

Allah yasa su Yusuf dawowar su kenan suna neman sun shigo kitchen din suka gan Shi a haka da gudu sukayi Kan sa suna Kiran sa, sai asibiti kafin su zo asibitin kuwa? ya Suma. anjima a kansa sosai kafin a samu ya farfado Yusuf ya Kira Sameera ya sanar da ita sai gasu sun zo ita da Mas'ud sosai hankalin ta ya tashi bakadan Sai sanda ya farka bata dakin ta tafi tayi sallah iya sune a dakin kawai.

Abba ganin mijin Sameera a gaban sa tare da su Yusuf yasa Shi cire oxygen din da aka sa masa da sauri sukayi kansa hannu ya daga musu sannan Mas'ud ya taimaka masa ya tashi Yana numfashi dakyar ya riko hannun Mas'ud hakan yasa ya zauna, cikin muryan dake nuna alamamun Yana cikin ciwo ya fara magana.

"Ba kasan wanne irin siriki Ka samu ba".

Dukda mas'ud yasan abinda ya faru kuma yasan dalilin sa na fadar haka Amma.

yace, ''Abba bangane abinda kake fada ba kadena Dan Allah".

"Mas'ud baza Ka gane ba sai na sanar da Kai komai".

Ya kalli su yusuf dake Kan sa suna kallan su yaseer sarkin kuka kamar mace.

" 'ya'ya na idan sukaji abin da na aikata ina ga dena Kula ni zasu yi".

Hawaye ne ya zubo masa beda mu da ya goge ba.

"Akwai wani babban Abu da na aikata a rayuwa ta Ummusalma da Iyayen ta sai dai duk abinda nayi matar danayi dan na faran ta mata ta tafi ta barni bacin ita ce Wacce ta zigani da nayi hakan haka ma Mahaifiyar data haifeni wacce itace silar faruwar komai yau gashi ta mutu ta bar dubiya batare da ta Nemo yafiyar abinda tayi ba".

Shiru yayi numfashin sa yana yin Sama Sama Kara damke hannun Mas'ud yayi ya kulle ido, tiryan tiryan ya zayya no musu komai har kawo Sace su da akayi da tura Ummusalma karatu sai da ya Gama.

Yace, "Lokacin Dana fara ganin Ka na gano kamar Muhammad a tare da Kai sannan Maryam, amma kuma ganin Baka da alaka dashi Kai din Dan Adam Dan Lami ne yasa ban kawo komai a rai na ba sai dai har yau idan na kalle Ka Shi nake tunawa, Inaji a jiki na be mutu ba ina Jin wannan a jiki na amma bansan inda Zan ganshi ba ban San inda Zan same Shi ba".

Shiru yayi na wani lokaci sannan yace.

"Ku Kira min Sameera tasan waye mahaifin ta, tasan mahaifin ta be cancanci yafiya ba daga gare Ku da wannan mutanen".

Mas'ud yace, "a,a Abba basai an kira ta ba tun da bata sani ba Dan Allah a bar komai anan yayi ya kare Wanda kake fada kuma nasan shi Zan Kan Ka wurin Shi Insha Allah Abba kadena fadar haka kaji ko? Mutanen kuma sun jima da yafe maka kayi hakuri Ka kwantar da hankalin Ka".

Cikin mamaki yake kallan sa.

"Kasan su? Kasan sun yafe min? Ka kaini wurin su yanzu nan Ka kaini kawai bansani ba ko shine yasa har yanzu nake raye".

Kokarin tashi yake amma suka rike Shi shikuwa ya dage sai an kai Shi wurin su babu yarda suka iya.

Yace, "Abba Bari naje nagani ko za'a Baka sallama".

Sameera dake bakin kofa ta rigada taji komai tun sanda ya fara labarin sa farkon ne bata ji ba ga mugun mamakin abinda taji ya fada tasan tayi dacen miji tun sanda sukayi be taba bata Mata Rai ba kullum Yana cikin faran ta mata haka itama Jin zai fito yasa ta tayi saurin komawa bakin ward din ta fara tahowa tana goge sauran hawayen ta gware sukayi dashi ya dago Yana kallan ta ita kuma kanta a kasa, murmushi yayi Mai kyau.

Yace, "crying baby ko pretty bata Kai ki kuka ba ina ga sai nakai ki an zuke hawayen nan ko zuciya ta ta huta da gaba Daya".

Yarda yayi maganar ne dole ya baka dariya murmushi tayi kawai bata iya magana ba shikuma yasa Kai ya wuce binsa tayi da Ido har ya fita, cikin dakin ta Shiga babu abinda Abba take cewa sai su yafe shi.

Yana fita ya Kira Ummusalma ya sanar da ita komai gashi doctor Baya nan bare su tafi.

Tace, "to Ka Kira su Baffan mana kace suzo asibiti nasan zasu zo ai muma gamu nan".

"Ke ki kirasu mana".

"Chatty Ka kiyaye ni".

"To Inni aljana kawai".

Ganin kamar bazai Kira su ba yasa ta kira Inni Ashe har ya fada wa Baffa ma,? Binaif ta Kira da Mas'ud sai uncle suka taho.

Basu wani jima ba kowa ya hallara ana jiran dalilin kiran sai ga Mas'ud din nan ya fito ya zo ya Shigar dasu.

Baffa yace, "wai waye ba lafiya kabi Ka daga mana hankali".

"Baffa kazo mana zaka gani ai".

Suna zuwa kofar dakin ya kama hannun Sameera suka zame suka fita.

Baffa ne a gaba ya tura dakin ya Shiga Yana kwance idan sa a rufe Yana tunani yaji sallamar sa Bude Ido yayi ya sauke su a kansa koda ace? zai sauya sau dubu to tabbas zai gane shi, shima Baffa tas ya gane Shi sabida ya ganshi a biki.

Kokarin tashi yayi Baffa ta yayi sauri ya karasa ya Ida daga shi Abba besan sanda ya rungume Shi ya fara kuka ba kukan dayake kuka ne na taba zuciya da tsantsar Nadama Inni ita kanta ji tayi hawaye zai zu bo mata da sauri ta maida shi tana komawa baya,
Dakyar Abba ya iya Bude Baki Yana kuka sosai.

Yace, "Ka yafe min Ka yafeni Ka..ka..".

Kasa karasawa yayi sabida wani saban kukan da ya taho masa har Yana sarke Shi, bubbuga Shi Baffa ya fara yi Yana bashi baki.

Dagowa yayi Dan kallan Baffa yarda yake magana cikin taushi da lallamin komai ya wuce idan sa ya Kai kan Ummusalma da itama wani hawaye ne ya zubo Mata.

"Um..mu..sal..ma".

Ya iya furtawa kawai kasa jurewa tayi take ta rungume Shi tana kuka sosai bema yi magana ba ta fara ta yafe masa haka ma Inni.

Ranar Abba ya zaci karshen mutuwar rayuwar sa ta zo ganin yarda mutumin da be zaci zai yafe masa na sai gashi komai ya wuce idan kuwa ya Bude Baki zaiyi magana da sunan neman yafiya sai kaji sun dauko wani zancen sunayi hakan yasa Shi kawai kallan suya zuba musu Ido ji yayi zuciyar sa tayi fes ta wanke babu wani damuwa bare bacin Rai da bakin ciki Jin sa yake kamar ba'a cikin ciwo ba yake.










_Dubai_



Tsawon wannan lokacin suna Dubai suna harkar su Kaya kawai suke sarowa suna aikowa babu abinda ya dame su da gida bare kuma yaran su business kawai suke zubawa babu abinda ya dame su bare ya sha kansu da kudin su suke bishashar su Saida suka tabbatar da sun turo Kaya kusan na miliyan ashirin sannan suka wuce China anan ma sun jida kaya.

Yau sun tashi Basu da kudi sai Wanda zasu hau jirgi gashi an kawo musu kayan Basu biya kudin ba hakan yasa su Bude envelope din da Daddy ya basu dan ganin check din da ya Basu suna parlourn gidan da suka kama haya suna fadar abinda zasu yi.

Hajiya ce ta fara bude wa taci Karo da wata paper ta zaro tana budewa tana magana.

"Kai Alhaji de wallahi sai a barshi mene na..."

Shiru tayi ganin saki biyun da tayi a Hankali ta fara karantawa tsab ta gani kamewa tayi a wurin a zaune.

Anty ma hakan ce ta kasance kowa kasa motsi yayi da ya ga wannan takarda gashi ko sisin kabo babu a ciki sai yanzu suka San wautar da sukayi sai yanzu suke Dana sun sani sun Bude sunga ko nawa ne Amma meyasa be ce musu komai ba?

Jin ana musu knocking shine ya dawo daga su daga duniyar da suka dulmiya masu Kaya ne suka zo dole kuma yau zasu bada kudin nan babu yarda suka iya kudin jirgin su suka biya dashi da canjin hannun su sunyi kuka kamar ba gobe wacce suke turawa Kaya kuwa dakyar dakyar ta hado musu kudin jirgi da na gidan da suke zaune suka dawo Niger, suna zuwa Basu zame ko ina ba sai gidan sa babu kowa a gidan ko Mai gadi babu Dan gidan ma dankareran Padlock suka gani a jiki acikin 'yan kwanakin nan karamin hauka ne kawai basuyi ba kana gani zaka San sun rame har wani Baki sukayi saki ba Abu bane Mai sauki musamman ma lokacin da Baka shirya ba.

Daga Gidan wacce suke turawa Kaya sukayi suna zuwa aka ce ta tafi saudiyya bayan ta sai da Kayan su wani kuma ta tafi dasu ana Gama fada musu suka zube suka fara kuka wiwi suna tafi ya Akan titi kamar tababbun mahauka ta Gidan Mariya suka je itama Tace tunda suka tashi bata Samu dama taje ba da Rana zasu Sa suje su Duka tayi tayi dasu su tsaya suci abinci amma suka ki suka Tunanin yayi gaba daman su biyu ne anan garin sai Hunaifa, Hunaifa kuwa tana zuwa gidan sosai sai dai suka Samu bata nan ta tafi sunyi tafiya gidan wata kawar su suka je sai da sukaje fada ya kaure a tsakanin su wannan yace kaza wannan yace kaza Abu ya hade musu kwanan su biyu itama tace mijin ta zai dawo idan ya dawo kuma korar kare zai musu hakan yasa suka tattare komatsan su suka tafi gidan su Anty, Tasha fada kuwa a wurin sa musamman dayaji tun yaushe akayi sakin bata nemi gida ba sai yanzu.

Tace, "kayi hakuri kawu dan Allah ni kawai so muke muji me muka masa da zai mana wannan sakin har biyu".

"To zan neme Shi Insha Allah naji dalilin sakin idan ya mayar Ku to idan kuma be mayar Ku ba sai hakuri da dangana".

Daga nan ya fara balbale su? da masifa daman ita can sabida dashi ne bata San zuwa gidan su yanzu kuma da Shi kadai ya rage mata dolen ta ta ne me Shi.

Fita yayi da kansa yaje ya Kira Shi a waya sai da suka gaisa yake sanar dashi komai Daddy kuwa yace ga Shi nan zuwa.

Sai da yazo ya fede musu biri har witsiya da irin kuma abin da yaji suna fada da abinda zulaihat ta kara fada masa game da Kauwar sa sosai shikan sa ya girgiza da irin abinda sukayi gashi kuma a gaban su ya fada babu daman musu.

Anty kuka ta fara tana magiya.

"Tabbas abin da mukayi bamu kyauta ba Dan Allah Kayi hakuri Ka maida mu".

"Da'ace baku furta ba bazan ji ba kunsan ance A BAKIN WAWA".

Kawun ta yace, "akanji magana, Allah ya kyauta kede tawa ce bakuma zan kore ki ba zaki ci gaba da zama ke kuma Hafsa zaki kama hanya ki tafi garin ku

Bazan iya rike Ku ba har Ku biyu Nima nawa iyalin ya ishe ni".

Sallama Daddy ya musu ya tafi sai da ya masa alkhairi Mai tarin yawa sannan sosai yayi godiya.





Abba kuwa ba laifi yanzu ya warke Sosai sunje kafancan mutane sunyi mamaki Wanda suka San su Kenan gashi kuma Baban su sun dawo an sha koke koke da labari kafin wani lokaci komai ya Zama tarihi Baffa yaja Abba a jikin sa sosai haka su Yusseer yanzu a wurin Inni suke ita ke musu komai har yau babu Wanda ya furtawa Sameera komai dukda tasani itama bata nuna ta sani din ma.

Yau ta kama Friday Inda kowa ya zo gaida Inni da Baffa jiya sukaje gidan Daddy yau kuma suka yo nan kamar hadin baki suka hadu anan sai da suka ci abinci suka sha sun zauna ana ta hira Dan har su Inni sunan mazan kawai basa nan.

Mas'ud ya kalli pretty dake kama center table ta mike ga gashin ta Masha Allah mai tsaya da laushi.

Yace, "so nake yarinyar nan ta min laifi na kama gashi na aske ya dawo na Maza".

Ummusalma tace, "chatty ko? Daman Kai ne Ka Sace ta Ka Kai ta aka Mata askin suna kaga yarinya tufarkallah".

Inni tace, "Mas'ud fa da Yana karami shine ya kama Kan walida ya aske itama da tana karama gashin ta yafi na pretty".

Dariya ayi Banda ita da ta cukume fuska ta daure ta tamau.

Yace, "Amma naji dadi Inni laifi tayi ko na aske gashin".

"Na manta me ta maka kawai Ka ko kayan wasan Ka ta bata ne ko me tayi tana bacci kaje Ka sami scissors Ka yanke Shi tas ga Kan nan Mai laushi gwanin ban sha'awa Ka yanke kasa Sheva Ka aske Ka kusa Gama wa nikuma na fito daga wanka na ganka kana aiki nan Baban Ku yace kuma bazan dake ba".

"Daman na jima da sani Baffa na so na irin yafi kowa Sona din nan".

Ummu ce kadai bata zo ba tana can tana fama da cikin ta kasa zaune ta kasa tsaye ita ce tace baza ba, waya ya dauka ta kirashi suna tsaka da hiran su a zabure ya mike ya tashi ya fita ganin haka suka San ba Lafiya sai, Mas'ud zai fita pretty ta fara Kiran sunan sa tana kuka.

Dawowa yayi Yana bata fuska.
yace, "ke ban hanaki cewa chatty ba? Papa zaki ce".

Yarinya kuwa ta kuma cewa" cati".

Daukan ta yayi ya dungure Mata hakan yasa shida Binaif ne kawai suka tafi sai au yusuf da suka sulale suka bisu? sukuma suka zauna Zaman jiran tsammani kowa shiru yayi yana tunanin.

Bata fi awa biyu Allah ya sauwake Mata ta haihu bata da doguwar labour Basu wani jima ba komai Normal suka dawo gida Rasa inda zasu je sukayi Kawai suka Kira Anty, Anty kuwa tace suje gidan Inni nan suka je suna zuwa aka taso kowa so yake ya dauki abinda aka Haifa ganin Yara biyu Daya a hannun Yusuf Daya a hannun Yaseer yasa kowa mamaki manya ne suka fara karban su itade ummu dakin Neena ta Shiga ta kwanta sai bacci.

A parlour kuwa bayan kowa ya gama ganin yarinyar Mama da Inni suka tafi daki suka barsu anan.

Yaseer yace, "yes wannan ta hannun Yaya ita ce Mata ta".

Yusuf yace, "ni kuma babbar ce kasan nine babba".

Sameera tace, "dalla can kuyiwa mutane shiru wani matar Ku".

Ummusalma tace, "uwar yaran ma tace baza ta bayar ba wai lokacin sun tsufa bansan uban ba".

Mas'ud yace, "nine uban Yara nan kuma sai na basu wannan a rubuce yake kuji dakyau".

Tashi tayi itama ta bar wurin ta rabu dasu suna bugawa harda Muja itama ba laifi akwai surutu mijin tane de beda meshi ba daga nan kowa ya watse aka tafi sallah. Suna daki Bayan ta farfado Ummusalma tace, "kunga ki fadawa Umma kafin azo a maimai ta".

Neena tace, "wannan tsohuwa da Mita take".

"Wai sai yaushe zaki yi aure ne?"

"Zanyi bakin sa tare za'a hada dasu Anty Saima ba?"

"Bansani ba zamu sha biki".

"Sosai zaku sha Kam".

Muja tace, "kinji wani wuri ko kunya babu ko?"

"Wanne kunya ai ni ko kuka bazan yi ba nifa? ina so".

Sameera tace, "wai mu ba yayunki bane? Ko kunyar mu bakya ji ko?"

"Aff sorry Yaya Sameera yi hakuri kinji kafin ya Mas'ud ya fara Kuli Kuli Dani".

Ummu tace, "Yaya salama kice su dena magana Damu na suke".

Tace, "kudena magana kuna damun ta".

Cigaba hirar su sukayi cikin raha.

Ranar suna yara sunci sunan Anty wato zainab da sunan Umma Aisha, Hajiya Umma ana Jin ansa sunan ta ya kada guda harda Kiran masu kidan kwarya ta taka abin ta.

('('('('('('('


Bayan wani lokaci abubu da yawa sun faru ciki kuwa harda haihuwar Mas'ud da Mus'ab inda Mas'ud ya samu mace shikuma Mus'ab ya samu Namiji pretty tayi wayo sosai har yanzu Chatty take cewa sai dai yanzu tana cewa uncle kullum indai yazo bata fita tana wurin Shi haka idan taje gidan ummu ta nace Sai an bata Yara biyu ta dauke su kuma baza'a karbe su ba da kuka de take baro gidan wata ran kuma ta kwana a can har a gidan Umma tana kwana ko ina inde taje sai ta kwana sukuma su barta sun san bata kuka kuma sannan bata da kiwa.

Yarinyar Mas'ud Sunan Ummusalma yasa amma yace sunan matar yayan su ba ita yake nufi ba inda suke ce mata Banafsha, shikuma Mus'ab sunan Daddy yasa sosai hakan yayiwa Daddy dadi.

Yau ne sunan Ummusalma da ta Kara haihuwa Allah ya bata 'yan biyu duka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login