Showing 93001 words to 96000 words out of 173457 words

Chapter 32 - A BAKIN WAWA (AKANJI MAGANA) COMPLETE

30 Oct 2025

3939

yo mukayi fa nemanki fito kizo fitowa tayi suka fita.

Da yamma akayi kamu yayi kyau sosai da sosai ya kuma Ka yatar kowa ya yaba, washegari akayi walima,akayi wa'azi Wanda ya fadakar musamma ma su 'yan kauye Wanda ba addinin akasa gaba ba kawai miji ya kawo ayi abinci a haihu shine kawai abin su ga bautar aure kamar kamar me,dai dai basuyi ruko da addini ba kalilan s suka San hakan damma suna yanzu suna karatu shine ma saukin abin.? Sosai aka fadakar kowanne bangare kuma an Karo sosai.

Washegari da wuri suka fara shiri Wanda zasu Kai amarya, Basu wani yi gayya da yawa ba, mota biyu ce karfe tara mai kyau suka dau hanya. Awa Hudu suka diba suna tafiya direct gidan su Binaif aka wuce da ita a parlour akayi masu masauki sannan Hajiya ta fito tana wani yatsina tana cika, suka gaisa, Anty ma haka suka Dan gaisa de sama sama, Matar Baba Usman,
tace' to Allah ya kawo mu bikin Binaif? ga kuma amarya Ummusalma, ba'a bude muka ku ganta......

Manage pls....

By: '''Hijjart Abdoul'''
? ?? Cwthrt =??: ? ? _Akanji magan_



Not Edited
POST 2020
REPOST 2023

??
? ?? 33

Umma tace' a,a dakin barshi ma,
Ita duk a Nata tunanin 'yar kauye ce shiyasa,

Anty tace' Allah yasanya alkhairi ya Basu zaman lafiya,

Dayake duk sun San halin su, sai wata daga cikin matan,
tace' Ameen Ya Allah, Allah ya rabasu da sharrin masu sharri ya kare daga sharrin masu hassasa da Kasaita,

Wata kuma tace' Allah yasa de har zuci, ku tashi mu tafi,

Rai Anty da Hajiya ya Kai koluuwar baci,Amma gudun kar ayi sai suka yi yake kawai, suka tashi,
Daga nan gidan Anty safiya aka kaita dayake tare suka taho a gidan suka yada zango, wasu daga cikin matan suka fara tambayar 'yan uwanta, Anty safiya kuwa tace' suna London dayake su sunyi nasu bikin a can,shine aka kawota Suma suyi nasu, daga nan kuwa shiru kakeje damma tunda aka fara shagalin suke cewa Basu ga 'yan uwa ba,Umma tayi banza ta kyalesu dayake an San halinta da jaraba sai Suma sukaja bakinsu sukayi shiru,

Da daddare Anty safiya ta shigo dakin Nafisa su biyu ne kawai a dakin sauran duk sun koma Bauchi sai matar Baba Usman da yarta mace guda Daya dayar kuma tayi bata zoba bata da lafiya, sune kadai Basu koma ba,

Anty safiya tace' Nafisa tashi kije parlour, zamuyi magana,
Fita tayi ta baso waje, Anty Safiya Zama tayi a kusa da ita ta kama hannunta, sai ga Mom yagana matar Baba Usman itama tazo,

tace' Ummusalma kinga yanzu yarda Allah yake lamarinsa, kinyi aure har zaki tare a gidan ki,ki Kula da mijinki, yanzu kece komai nashi, ke zaki masa komai basai na fada ba kin sani, sannan zaman aure sai hakuri,Idan babu hakuri to babu zaman lafiya sannan ko yakike ciki da mijinki karki Bari kowa da zaizo gidan ki yasan hakan,Karki fadawa kowa kada kowa yaji musamman kawayenki, sannan Ummusalma zaman aure na har abadane babu ranar denashi kamar yarda ba'adena sallah haka shima ba'a denawa ki rike amanar Shi ki rike sirrinsa kiyi biyayya, bansan kuma me Zan kuma cewa Amma wannan Kalmar hakuri ita Zan fada maki,bazaki Ganeba yanzu sai kin je kin gane da zaki San me ake nufi kinji ko?

Mom tace' Ummusalma Abu na farko da zakiyi shine gudun bacin ran dayanku, duk wani Abu da yake so Shi zaki fara sani,da abinda Baya so, sannan danginsa koda sunzo idan sun Nuna maki wani Abu kada kiyi fada masa ma anyi bare yasani, Abu nagaba biyyaya i Nayi Bari na Bari, tsabta, girki, kyautatawa ba Shi kadai ba bar danginsa kinji ko?
Daga nan suka Shiga Mata nasiha mai ratsa jini da Kashi tare da duk wani lungu da sako na sassan jiki bata San sanda wani hawaye ba ya taho mata, tambayar ta anan shine shin? daman haka akeyi? Idan za'a Kai amarya? Koshine dalilin kukan nasu daman?

Umma ce ta Kira wayar Anty safiya ta daga tace bata, a speaker tasa wayar, daga can,

Umma tace' Salamatu na daukeki 'ya? kamar 'ya'ya Salamatu ina kaunarki har zuciya ta kamar yarda nake San nawa,na dauke jika kuma 'ya,
Daga nan fa itama ta daura nata nasiha, tayi kuka kamar ba gobe daga nan Daddy yazo aka fito da ita parlour shima yayi nasa nasihar bashi kadai na har mijin Anty safiya da Hajja sai da sukayi Mata Suma taso, taga gata iya gata tayi kukan dadi, sannan tayi kukan rashin Uwa,sosai kukan ya hade Mata guda biyu,

Daddy ya Ciro kudi ya bawa Antu safiya
yace' ga sadakinta kya bata,daga du???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?k suka tashi suka fita,wanka mom tasata tayi da turare mai kamshi,ba'a Mata wani kwalliya ba don har yanzu kuka take yaki ya tsaya Mata, sai datayi sallahn Isha aka Shirya ta acikin liffaya tayi kyau sosai, Nafisa da Anty murja ne zasu kaita su kadai,ita kanta Anty safiya taji ba dadi Zama da Ummusalma akwai dadi bata da matsala ko kadan bata kuma da kiwar yin aiki, kwalla taji zata zubo Mata tayi sauri ta koma daki, haka suka sata a mota sukayi Gidan Abdulshakur Binaif da ita.
? ?
? ? Gidane palate mai kyau da Shi na daidai zaman Mutum daya a wadace sai wani barin daga gefe,kamar de part biyu ne a gidan sai dai Shi be Kai nata ba, sai compound shima daidai ba wani girma sosai ba daga can Baya kuma garden Wanda bishiyar lemu ce kawai ta girma sauran abubuwa duk Basu wani girma ba wani ma ya mutu alama basa samun kulawa,
?
? ?? Daki daya aka kaita ana ma Anty murja ta Kara yimata wata nasihar dayake da Rana sunzo sun? Kara gyara mata sai kawai suka taso suka fito Dan Daddy yace suna kaita su dawo Shi yaso shine ya tafi da ita.
?? Tayi kuka kamar ba gobe, ita kanta a yanzu da suka tafi suka barta batasan na me take ba, na farin cikin tayi aure ne? Ko kuma na farin cikin kudirin su Abba bai hau kanta ba? Kanta kwa ciwo yake Bana wasa ba,ga gajiya ga kuka ga yunwa,duk sun tarar Mata tun abincin da Umma ta matseta a daki taso Dura Mata tun safe bataci komai ba,koda Anty safiya ta Kai mata bata ciba, kwanciya tayi ta kudundune ita kadai a saban wuri haka? Dakyar ta samu hawayen ya dena zuba ga lifayar da aka nade ta dashi bata iya kwancewa da ta kwance, bacci ne ya fara ya daukata batare da ta Shirya ba,

??
? ('('('('('('('('

Yana zaune a gaban Daddy,Daddy Yana masa nasiha kamar yarda yayi Mata,haka ma Anty safiya harda Baba Usman, kowa yayi tashi,

Daddy yace' Binaif ina Mai Kara ja maka kunne kada Kake muzgunawa yarinyar mutane,bata San halinka ba, koni Dana haifeka Bana ce Ka ga halinka bare kuma ita, Ka koyarda yarda zata San halinka Banda fushi Banda zuciya banda bakar magana. Binaif Dan Allah Ka Kula masu da yarinya, tamkar marainiya haka take kazama gatan ta Ka Zama mahaifinta Ka Zama aboki,kazama yaya,kani,abokin wasa, Binaif kake kulada yarinyar mutane Binaif, Binaif kada kaje Ka Kara tafka kuskuran Dana tafka a Baya Binaif duk wani motsin ta idan bata da lafiya ko kuma batajin dadi ko ranta ya baci kayi kokari kayi Shi Binaif Ina Santa kamar yarda nake Sanka 'yace a gurina kamar yarda kake a gurina, Binaif Bana San ka maimaita abinda na maimaita a baya, na rashin Kula ga iyali,

Kwallace ta ciko idansa ya goge,bazai iya cigaba Dan yanzu sai yayi kuka yana San dansa Allah ma yasani bayasan ya biyo halinshi na rashin kulawa da iyali gani yake rashin Kular sa ce yasa Mahaifiyar guduwa, gani yake rashin damuwa da damuwar ta ne yasa hakan ya faru, tashi yayi zai? fita, sabida tuno wani Abu yaji an rungume Shi ta baya tare da sakin kuka ko be fada ba yasan Binaif ne,juyowa yayi shima ya rungume shi,Karo na farko kenan a rayuwar Shi da ya rungume dansa,Karo na farko da yaji tausayin dansa, Karo na farko Daya ga dansa na kuka,raban da ya rungume Shi tun Yana yaro shima ba wani sosai ba, kukansa kuwa be taba gani ba tunda ba'a gabansa aka Rene shi ba,
? Sunjima a haka sannan Daddy ya bubbuga bayan sa be iya magana ba kawai yayi breaking hug din ya fice,

Baba Usman ne yazo ya kama hannun Binaif
yace' ya Isa haka kukan kaji son?
Goge masa hawayen yayi bayan ya zaunar dashi sannan shima ya masu sallama ya wuce,
Anty safiya tace' kayi hakuri kadena kuka, yanzu idan kaje kana kuka ita tana kuka waye zai rarrashi wani kuma?

Tunawa da ita ma kukan take yanzu haka,ba shiri ya Kara goge hawayen sa, Basu wani jimaba ya tashi zai tafi,

Anty safiya tace' Ka Bari su Mus'ab su kaika de,Naga tare kuka zo, karkace Kai su zaka Kai sannan Ka wuce,kaji ko?

Da to ya amsa, tace' muje na fada masu don ba wai na yarda da Kai bane,

Tare sukuje ta fada masu, Mas'ud ne kuwa ya karba key din suka tafi,
? Awani slow motion yake tafiya ga wata waka dake tashi a hankali itama lumshe idan sa yayi Shi kawai so yake ya bude ido ya vanshit a gabanta,ko ta dena kukan? Ji yayi sun tsaya a zatanshi sunzo sai ganin su yayi a bakin wani wuri, tsaki yaja ya rufe idansa ya kwanta,?

Mas'ud Yana dawowa bayan sun fara tafiya
yace' fav kar Ka manta idan zai fita Ka hada Shi da wannan ledar,

Mus'ab yace' Naji,
Yace' wani twinny ina event din da kace zaka hada mana ne?

Tsaki yaja yace' kaidai fav barni na so na hada wani event din ai Amma ba lokaci tund kaga aikin nan yamana cikasa gashi ni gobe ma Zan koma, Sai wani weekend din idan na dawo dole ne fa a shirya wata hadaddar Dinner ya kake gani?

Mus'ab yace' lalle kam zaka Shirya Kai daya,Kai fa wani sa'ilin kanka Baya ja,taya za'ayi ub an gayyatar ya yarda bacin Yana kagane ai,

Mas'ud yace' kaina kam Baya Dan wallahi ban gane ba mekake nufi ba,Dan fada min kaga shikenan bazan hada ba,

Matso da kunnansa mus'ab yayi ya rada masa wani Abu,? atare suka sa dariya suna cafewa,

Mas'ud kanka naja wallahi,kana kawo light kuma fa haka ne, taab kace tun yanzu an fara wataran ma Bama Shiga ba,Amma ni dai ko da ta Sama ne sai na Shiga ko an hanani,

Mus'ab yace' Kawai wannan weekend din kar mu dawo gida mu Basu privacy Ka de gane ai,

Mas'ud yace' wallahi kana kawowa sosai fa,Nima de Zan fara kawowa nan ana Abu Zan dago jirgin karka damu,

Ahhh ai daman Kai ne kake kwafsawa ina so na ma signal amma nasan ba ganewa? ba zakayi,

Yace' wai ni Twiny ina Sameera kuwa kwana biyu,

Wannan yarinyar wallahi Allah ma ya gani tsoron ta nake ji,a waya tsakani na da ita fadar gaskiya shine kawai kuma Tama sani a blacklist,bansan kuma ya za'ayi ba,

Mus'ab yace' za'a San yarda za'ayi sai mundawo ai,

Daga kuma Sukaci gaba da maganar su iya su,Yana jinsu ne tanka masu Dan beda ta cewa, zasu hadune ai. Har sukaje gidan, dayake babu mai gadi a gidan Mus'ab ne ya fita ya bude, yashiga ya rufe yaje ya dauko ledar Shi, ko kallansu beyi ba ya Shiga cikin gidan Suma binsa sukayi a parlour yaja ya tsaya,

yace' lafiya? Sai bina ake?

Mas'ud yace' matar zamuje mugani mana,

Kallan irin Baku da Kai ya masu, yace' bade kun kawo Mata mijinfa lafiya ba? To Allah ya tashe mu Lafiya,? Allahu ya kawo ranar dena tuzoranci,

Juna suka kalla Mas'ud da Baya shiru yace'? dame Ka fimu? Mufa har yanzu bamu Kai 30 ba bare ace mana wani Abu ku .......
Taske masa keya yayi yace' fita, bazaka zo Ka min rashin kunya ba anan,
Kuma ku bani key Dina,

Mas'ud Yana Dan gunguni yace' wanne key? Taab ai dashi yazamu tafi idan kana da bukatar wani Abu Ka Kira mu,
Suka tafi shima binsu yayi don ya rufe kofa? sai dai suka fita yana rufe gate mas'ud yafito da gudu,
Yaje saitin sa ya rada masa Abu sannan ya dawo da gudu ya koma, girgiza kansa kawai yayi mas'ud beda kunya kokadan Allah ya kawo ranar da zai shiryu. Sai da ya rufe ko ina sannan ya Shiga daki, tana kwance tayi nisa cikin baccinta sosai Kara sowa yayi kusa da ita ya durkuwa a gabanta Yana kallan fuskar ta wacce tayi ja sabida kuka,sai ajiyar zuciya take saukewa alamar har yanzu besake ta ba.......




By: ```Hijjart Abdoul```
? ?? Cwthrt =?? ?? _Akanji magana_
?
??

Not Edited
POST 2020
REPOST 2023

??

? ? ? 34

Kallanta yakeyi bako kiftawa tunanin da yake ya tasheya ko a'a yama Rasa me zaiyi,sai yayi kamar ya taba ta sai ya fasa ga wani nannadewa da tayi ta rungume pillow kuma ta kwanta a kanshi sai kace bata da Kashi, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya tashi ya fita a dakin,wanka yaje yayi ya saka kayan bacci sannan ya dawo, wardrobe ya buda ya dauko Mata kayan bacci ya zo fara kunce liffayar jikinta, shikaidai ya fafa mita,"'? da haka kawai azo a saka wa mutum wannan Abu, shiya ce Yana so ne kome ko kuma ita tasaka oho,
Ganin tana motsi yasa Shi yin shiru kar ta tashi a hankali a hankali yake bita da ita har ya wareta Sannan ya cire Mata kayan bacci kawai yasa Mata doguwar Riga mai laushi sannan ya kashe fitilar yaje ya kwanta Yana sauke numfashi, Sai da ya nutsu ya daidaita kanshi ya masu addu'a ya jawota jikinshi,duk bidirin nan bata San anayi ba, shikuwa samun kansa yayi da murmushi tare shafa bayanta yayi missing moment nan ba kadan ba, tunani ya fara yi, wai yau shine da matar sa kuma a gidan sa? Abinda be taba kawo sa ranae faruwan hakan ba,ina ma Anty ummi tana nan,
Numfashi yaja yana shakar kamshin turarenta maganar Daddy na Kara dowa masa akai, me daddy yayi? Baya kula da Matar Shi ne? Meyasa yace? masa Kar ya maimakon abinda ya maimaita? Ya ilahi,? tunanin kawai yake ya Rasa mafita, tunani yake idan yaje don ya fada masa ko shin zai fada masa? Ko Baba Usman zai samu??

Kwanciyarta ya gyara mata Jin tana motsi,zata tashi, tashin kuwa tayi sabida yunwa ga bacci fal idanta, jinta da Yayi ta tashi zaune yasa Shi kunna bed side lamp,

yace' lafiya?

Tana murza idanta tace' yunwa nakeji,

Tashi yayi ya fita,Yana fita ya hango ledar da Mas'ud ya siyo masa dazu, Godiya yayi wa Mas'ud ya wuce kitchen ya dauko plate da cup,da babu Abu da yanzu ko me zai bata?? Wata zuciyar tace sai Ka fita ka siyo,wata kuma tace ina motar,
A fili yace' salan ma na kirasu su suzaci wani Abu ne,

? ? Yana Shiga ya ganta ta komawa ta kwanta ta Kara kudundune wa abinta, karasowa Yayi,

yace'? sauko kici?

Make kafada tayi tace' a,a anan zanci,

Girgiza Kai yayi ya hawo gadan yace' to jeki wanke bakinki,

Tura Baki tayi gaba itafa yunwa takeji, ganin bata da niyya yasa Shi ya daga ya kaita toilet da kansa ya wanke Mata ita sai layi fuskar da ya wanke Matane yasa ma baccin Dan sakinta,dawowa sukayi ya zaunar ta a kasa ya Shiga Baya kazar da Yogurt tana ci har ya koshi,bawani koshi can sosai ba bacci ne kawai fal idanta kuma yasan duk gajiya ce komawa tayi ta kwanta shima beci wani sosai ba ya tashi ya mayar ya dawo suka kwanta,sai anan bacci ya dauke Shi.
?
?? Da Asuba ta Riga Shi tashi,jinta a jikin mutum yasa ta kalli fuskar sa da kyau bata ganin sosai, kasancewar babu haske sosai,a hankali ta zare hannunsa Daya rungume ta dashi ta kunna bedside lamp ta juyo tana kallami zata sauka ta tuna da lifata ce fa ajikinta to waya cire Mata? A hankali kuma ta tuna sanda yake bata abinci, juyowa tayi ta kalleshe dakyau sannan ta tashi ta shiga tayi alwala, ta fito kuma sai ta Rasa yarda zata tashe Shi,kusa dashi taje ta sunkuyo har ta sa hannu zata bubbuga pillown sa sai kuma ta tuno indai zai tasheta to iska yake hura Mata sanda suna gidan Umma, Amma ai ba barinta yake kallo ba gashi an kusa a Kira a Shiga sallah, kamar yasan me take nufi sai gashi ya juyo barinda take, daidai fuskar Shi taje sai kuma ta kasa tasa hannu ta fara shafa masa fuska har ya bude Ido ya saukesu akanta ,ita dai tasan tana shafa masa fuska Amma bata San tunanin da take ba harda su murmushinta mai tsada take aikawa dashi,
Shima murmushi ya mayar Mata ya rike hannun Yana tashi zaune,

yace' duk acikin shaukin ne? Har an Shiga sallah bakiji ba?

Ai bashiri ta tashi tana sunne Kai,Shi dariya ma take bashi idan tayi wani abun, tashi yayi yaje yayi alwala ya dawo har lokacin batayi sallah ba tana neman Hijabi bata gani ba,shine ya dauko Mata sannan ya jasu sallahr sun jima suna Azkhar har gari ya fara wayewa sannan,ya tashi zai kwanta,

Tace' Ina kwana?

Saida ya kwanta, yace' zo,

Ba musu ta tashi taje kusa dashi ta zauna,jawota yayi,tare da cire Mata Hijabin, suka kwanta tare Yana shafa kanta,

yace' ina kwana kawai? Ba mi amor ba komai? Ina laifin ma kice dear shine ba laifi,Amma kice ina kwana kawai ai sai nazaci ma ba Dani kike ba,

Shiru tayi batayi magana ba,batasan korafi da Mita, tasan idan tayi magana to yanzu zasu fara shikuwa bazak gaji ba ita kuma tanasan tayi bacci, matseta yayi hakan yasa,
tace' to kayi hakuri, bazan karaba,

Yace' good girl,

Tace' Mai gida ina kwana?

Takaici ne ya isheshi kawai ya rufe Ido irin nayi baccin nan,

Murmushi tayi ganin be amsa ba,tasan maganin Shi idan ya takura Mata,itama rufe idan tayi sai bacci.
? ?
? ?? Karfe takwas ta tashi sabida tayi bacci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login