Showing 48001 words to 51000 words out of 173457 words

Chapter 17 - A BAKIN WAWA (AKANJI MAGANA) COMPLETE

30 Oct 2025

3946

banki ta fara zuwa ta Mika check aka bata kudin ta ta fito, mota tashiga ta tafi can bayan gari sannan ta kira numbern nan, gabanta sai faduwa yakeyi, ana dauka taji wata sassanyar murya mai fita a hankali taji muryan tace mata,

' ya Akayi ne?

Muryan ta na rawa sosai tace kudin ne na kawo Bansan inda Zan ajje ba,

Yace' yawwa ashe de kina san raguwa 'yar ki,ki Shiga daga ciki gefen hagun ki zaki bi,ki mike kadan zaki ga wani kango ki Shiga ki ajje kudin. Kit aka kashe wayar,
Fita tayi tana waige waige ta je ta bude booth ta zuba kudin da ta dauko a banki sannan ta dauko katuwar Ghana most-go din, dakyar take tafiya ,daga baya ma janta ta farayi har ta iso inda aka ce mata, ganin rigunan su ya tabbatar mata da anan aka akashe Mata 'ya'yan ta,kuka ne ya kufce mata tayi sauri ta share ta ajje bakkon a lungu, ta tattare kayannasu a hannunta ta rike,ta fito tana kuka, a mota ma ta jima tana kuka sannan ta tafi gida.

? ? Shima Abba sallah yayi kawai ya fita banki kudi ya debo sannan yaje inda aka fada masa ya ajje koda ya ajiye samun wuri yayi ya buya ko wai zaiga wanda zaizo ya dauka, tun karfe 8 yake tsaye a wurin amma har Azahar babu wanda yazo wurin hakura yayi kawai ya tafi.


Yaya kaga na fika iya acting gani fa yanda nake narkewa,muna komawa zan shiga film wo ni wo ni yaseer Dan Mahmud,

Banza yusuf yamasa, ko kallansa baiyi ba abinda yake ji ma kawai ya ishe shi,kwana biyu kawai Amma ya gaji so yake yaga ummu yasan tana cikin wani hali ko abinci tana ci ma?? Bai ankaraba yaji hawaye nabin kuncinsa,da sauri yasa hannu ya goge gudun kar yaseer ya gani sai dai yaseer juyowar da zaiyi don ya masa magana yaga yarda hankalinsa bama ya kansa yana wani wurin, gashi kuman hawaye a fuskar shi,tasowa yayi ya zo kusa dashi,cikin muryan tausayi,

yace' Yaya nasan tunanin da kake bai wuce na halin da Ummu zata shiga ba, don Allah kayi hakuri Yaya na wani lokacine komai zai wuce kamar ma ba'ayi ba,
Rungume Shi Yusuf yayi yace' nasan na wani lokacine amma nasan tana cikin wani hali,mukuma nan muna cikin kwanciyar hankali,a haka zan kwantar da hankali na? Kaima nasan fada kawai kake amma ka matsu da ka ganta, sannan kuma ga Yaya salama again nasan tayi ta jira amma taji shiru?
Shima yaseer rungume shi yayi tare da sakin wani kuka kawai yana daurewa ne,kar Yusuf yaga gazawar shi,shike lallashinsa, sunjima ahaka daga bisani kuma suka zame suka kwanta, daya a kasa daya kuma akan kujera kasancewar a parlour suke, a haka bacci yayi gaba dasu.


Daddy tsaye a bakin kofar part din su Binaif yana knocking,ya jima a tsaye a wurin tun yana yi ahankali har sai da yayi da karfi tukunna, yaji alamar tafiya sannan ya hakura,Yana budewa yaga daddy tsugunna wa yayi ya gaidashi, maimakon ya amsa? sai,

yace' meye sunan??

Kallanshi yayi alamar be gane ba,

Daddy yace' ita waccan kurman,ya sunanta,

Bakinshi na rawa ya furta Ummusalma Muhammad,

Iyayenta ba,

Sun rasu daddy,

Daddy be jira cewarsa ba kawai yasa kai ya? juya ya shiga mota, binaif yana tsugunne har Daddy da driver suka tafi, sannan ya tashi ya koma ciki daman wanka yake,Yana so ya fita ya shaida mata, abinda ake ciki, jiya har ya kwanta yaje ya karbo yar karamar wayar da ta turawa Daddy sako, Sannan ya karbi address din tsohon gidan su,yaje ya zauna a wurin masu gadin unguwar wanda yawanci da daddare suna zama suyi ta fira anan ya zauna yaturawa Mama text,Yana nan zaune yaga police ko ba'a fada masa ba kuma yasan tracking numbern akayi.

Shiryawa yayi cikin bakaken suite ya bade jikin shi da turare,ya dau yar jakar ya fito, direct dakinta ya nufa lokacin tana kwance babu abinda takeyi sai tunaninsa a wannan lokacin, knocking yayi a kofar dakinta,hijabi ta dauka ta fito ganinsa da wannan shigar yasa,

tace' ina zaka je haka? Ba Daddy ya hana ka fita ba?
Wani irin makirin murmushi yayi,

yace' fita ta zama dole,kuma batun Daddy kawai kyaleshi yama manta,? takardun nan zaki bani,na company guda daya,

Juyawa tayi ta dauko masa bata gani na kowanne bane kawai daukowa tayi wanda tasan na company daya ne, bashi tayi ya kalleta cikin ido ya sakar mata murmushi

yace' sai na dawo,
Tsayawa tayi a wurin,ta daskare wannan killer smile din dayayi ya tafi da imaninta, juyowa yayi

? yace' Ba Allah ya kiyaye ba adawo lafiya ko? Shikenan to tunda ba za'a min ba,bari nayi,
Muryar ta ya kwai kwaya

yace' Allah ya kiyaye Allah ya dawo da kai lafiya Allah kuma yabda sa'a byee sai Ka dawo,
Bai jira cewar ta ba ya tafi kuma daman yasan ba abinda zata ce,

Batasan lokacin da tayi murmushin ba, sannan ta rufe kofarta ta.
zama tayi a bakin katifar ta,tana murmushi,

tace' wai shi bai yarda ba magana ta yayi to nidin haka nake magana ne? Kawai sai tayi dariya abinta,
Yanzu kam ta lura yana abu kadan zatayi dariya idan ma batayi dariya ba zatayi murmushi, ko jiya da daddare sai da yasata dariya, kwanciya tayi tana cigaba da murmushin ta ita kadai.

? ?? Yana fita ya ansa key a wurin drivern gidan ya fita,bajjima da fita ba yaji wayarsa na ringing ganin sunan Daddy yasa shi dagawa yana dagawa kuwa yaji Daddy yace' duk inda kake kayi gaggawar zuwa masallacin bayan layin mu yan zunan kayi sauri ina jiranka kar ka bata min lokaci,
Ya kashe wayarsa,kwana kawai ya karya ya shiga bayan layinsu mutane yafara gani a wurin masallacin tun kafin ya karasa, karsawa dai yayi yasamu wuri yayi parking sosai yaga motocin mutane da dayawa a wurin babu abinda ya kawo sai ko daurin auren abokin Daddy ake? Ba mai bashi amsa haka ya shiga cikin mutanen har yayi nasaran shiga cikin masallacin yafara hangen inda zai gano Daddy amma kuma yana cikin mutanen hakan yasa shi neman juyawa ya koma don har ya shigo cikin masallacin sosai, Daddy kuma ya hango shi, hakan yasa yayiwa liman magana, yana dhirin fita yaji an ambaci sunanshi kara daga kafar da zaiyi yaji ance Ummusalma Muhammadu guri kuwa ya kaure da fatiha, idan kunansa yaji dai dai cewa akayi an daura masa aure da ita. Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un.
Shi bama ta tashi yakeyi ba ta ita yake yi kawai tunanin ta yafarayi hankalinsa bai dawo ba sai da yaji wani kawunsa nacewa ai ga angon ma. zo nan ayi hoto, suka janyo shi,wani kuma yace' ohhh yaran zamani ranar aurenka da kayan nasara aka yi shi ni bantaba gani ba sai kace bikin kiristoci kai jama'a,
Wani yace ango ranar aurensa dariya yake shikuma wannan dakum-kumin murtuke fuska yayi, yana jinsu dai suna jansa har aka fito harabar masallacin,hoto akayi ta dauka wani yayi yake wani kuma kawai gashi nan dai ga shinannan ne.....

By: '''Hijjart Abdoul'''
? ? ? Cwthrt=?? _Akanji magana_


19


Driving yake amma gaba daya jikinsa yayi sanyi hankalinsa kuma ba'a driving din yake ba, tunani yake akan wannan auran, yadai san Daddy be sanar Mata ba, akan me kuma zaiyi wannan abun, aure fa ba abin wasa bane haka kawai 'ya ba tashi ba ba komai ba, "Ya ilahi Daddy why??
Abinda da ya furta lokacin da yayi parking a bakin gate dinsu, sai dai kuma ya kasa fita yana zaune kawai ya dafe kanshi da yafara ji yana sara masa, horn yayi aka bude masa ya shiga ko gama parking baiyi ba ya fito key din ma a jiki ya barshi, a parlour ya baje ya kwanta yana wani irin tunani na daban, shikadai yasan me yake sakawa yake kwancewa.
Ya jima a wurin ahaka har wurin 12 yana nan bai motsa ba jin wayarsa na ringing Allah yaso bai barta a mota ba ya tuna sanda Daddy ya kirashi da ita ya fito a mota,shi dai baisan sanda yasata a aljihunsa ba sai ji yayi tana ringing.
Daukowa yayi ganin number da har zai share sai kuma yayi tsuka ya daga, abinda aka sanar dashi yasashi saurin mekiwa,bayan ya kashe wayar shi yama manta da abinda ya fita yi badan an kirashi an tuna masa ba, daki ya Shiga yayi refreshing sannan ya fito key yafara nema sai kuma yayi tunanin ko ya barshi a mota ne .


('('('('('


"Yanzu Adamu abinda kayi ka kyauta Kenan ko me? Uhm, yarinyar nan fa ba 'yarka bace, sannan da kace min iyayenta sun rasu ita bata da me riketa ne ko me? sannan kuma wannan yaro ba mace bace da zakayi masa auren dole, Ka duba mana wannan lamarin, gashi kuma kace min yarinyar kurma ce,kawai don san a cuceta ko kuma me?

Kanshi a sunkuye yake bashi da daman tankawa yasan bai kyauta ba shi kawai abinda zuciyar sa ta Raya masa Shi yayi,

" Ba magana nake ma ba, kana jina kayi shiru ka kyale ni ko? Wato yi ki gama ko?

Bude Baki yayi yace' amm... amm.. umma ki..

" Rufe min baki wani amm amm umma,daka san zaka bani hakuri ka aikata ?

Wani mutum ne dake gefen Umma,

yace' kiyi hakuri kuskure ne mun rigada munyi,kuma kinga bamu da ikon da zamu warware wannan aure, har sai mijinta ya saketa tukunna, Allah kuma baya san saki, umma kiyi hakuri kuma watakila ma dalilin aure nan sai kiga Allah ya shiryeshi,...

" aww da mai yake aikatawa? Ta kastse shi,

Daddy yace' umma nema yake ya lalata masu yarinya fa a idona nasha ganin hakan tana faruwa shiyasa ma kikaga kawai na yanke wannan hukuncin.

Umma tace' ehh lalle ne shi Audushakurun Kenan? To bari kaji ko duk jikina kunne ne bazan yarda ba,kawai dai ka cuci yarinya kawai shine magana. Kai kuma dan kaga inajin maganar ka shine aka dauko ka kana can wata uwa duniya amma kadawo saboda wannan auren ko? To shikenan ya zanyi kun dakeni kun hanani kuka bazanyi magana ba,kun nuna min ni ba abokiyar shawara bace shikenan ai aikin gama ya rigada ya gama.

Sai tayi shiru,Suma shiru sukayi babu wanda ya kara magana, sai can ta kalli Daddy,

tace' kaje ka dauko min ita yarinyar,bazan laminta ba zamanta wannan gidan,kashe ta zasuyi daman ga aba kurma,

Daddy yace' umma da kin barta acan din inaga hakan...

Zaifi ko? Yanzu ma ja zakayi dani ko? Baka sanar dani ba auren sannan kace zamanta a wannan firin din zaifi. Bana boka bana Mallam amma ko kaffara banayi na tabbata wallahi wannan shegun matan naka ne suka hada tuggunsu da munafinci suka fada maka,Kai kuma ka hau dokin zuciya ka dauka. To billahillazi bazan dauka ba,kai da kaina ma zani gidan bari gari yayi sanyi zanje na dauko ta,kuma yarda baka fada min kayi masa aure ba koda subutar Baki karka kuskura kafada masu tam.
Tashi tayi tana dingisa yar kafarta

tace' idan kun tashi ku kashe min kallon kuma a tabbata an rufe min kofa. Ta wuce abinta ko waiwayowa batayi ba.


Usaman Wanda yake gaba da Daddy kuma shine na farko a wurin Umma, ya matsa ya dafa Shi,

yace' Karka damu kasan halin Umma kuma kasan duk wannan zafin da ta dauka be wuce na yarda aka daura auren nan ba'a fada mata ba kayi hakuri,

Daddy yace' umma baza ta taba saukowa ba, kaima fa kasan da wannan, kunyar kace fa yasa batayi min fada dayawa ba,nadauka laifina ne,gashi kuma tazo da maganar dauko ita waccan yarinyar,idan na kalli dana inajin dadi ganinsa nake tamkar mahaifiyar sa yaya yazanyi don Allah,

Har wata kwallace ta taru a idansa,ga muryan shi da ta fara rawa alamar neman yin kuka ganin haka yasa Shi yin shiru,ya sunkuyar da kansa,shikadai yasan me yakeji a zuciyar shi, zuciyar shi zafi take masa, amma baisan wazai fadawa ba yaji dadi, kuma baisan me za'a fada masa ba yaji dadi.

Shima Dan uwannsa shiru yayi ganin halin da kaninsa yake ciki,besan me zai fada masa ba shiyasa ya zabi da yayi shiru don shi magana bata dameshi ba tunda can ma. Sunjima a hakan hannunsa nakan kafadar shi alamar rarrashin,daga bisani kuma

yace' ni Bari na koma idan umma ta fito kace na wuce sannan kuma kace mutan gidan na gaida ita



Zaune suke su uku suna tattauna yarda abin zai kasance daya daga cikin ma'aikatan ne,

yace' yanzu Oga namu baya nan amma duk sanda yazo office zan sanar dashi,duk yarda mukayi dakai zakaji Insha Allah.
Murmushin dole ya kirkiro

yace' thank you,yafada yana mika masa hannu,shima mika masa hannu yayi,haka ma dayan, daga nan kuma suka tashi don tafiya.

Koda ya dawo gida bai shiga wurinta ba,wanka kawai yayi yasa kaya marasa nauyi ya kwanta yunwa yake ji beci komai ba tunda safe gashi yanzu ana nema ayi la'asar,shafa kansa yayi Mai cike da suma sannan ya shafo cikinsa, ya lumshe ido yana tuno Anty ummi bata taba barinsa da yunwa bare kuma tabarshi da damuwa, a fili ya furta" Allah ya jikanki Antynah.
Jawo jakar da ya fita yayi,don yayi wani abu ganin ya fara tunani dukda kansa dake ciwo amma haka ya daure ya fito da takardun cikin jakar tashi yayi zaune dakyau takardun company din da ta bashi yasa shi dauka, dubawa yayi yaga yama fi na company daya ta dauko masa, sannan kamar harda ma takardun fili da gidaje, dubawa yakeyi daya bayan daya sai dai kuma kowanne yana ganin signing din Ummu da yake rubutawa a jiki,amma idan ba lura kayi ba bazaka taba gani ba, sosai ya nutsu yana kara nazarin takardun,Yana cikin dubawa wata karamar paper ta fado a ninke take sai dai kamar harda wani dan jajaja a jikinta, warwarewa yayi ya bude, ganinta da yayi tana da tsawo papern ashe nadinne aka yi karami sannan kuma rubutune a jikinta dayawa sai dai rubutun bawai a tsare akayi shiba, nadeta yayi yarda take ya mayarta inda ya gani. Jin sosai yunwa yake ji yasa shi tattarawa ya ajje a gefe guda ya fito, fridge ya buda ya ciro malt ya fito don nemawa kansa abinci, ta wurin dakinta ya zo wuce sai kuma ya dawo da baya azuciyar Shi yace"' kome take yi yanzu?,
Samun kansa yayi da bude windown ta kadan, tana kan katifa tana faman taje kanta, gashinta yana da cika dayawa don yama fi karfinta saidai yana da tsayi amma bawani can tsayi na'azo a gani ba, sai dai ace Masha Allah, tana sanye da t shirt sai zani da ta daura sai da yagama mata kallon tsab sannan kuma ya kawar da kansa,a zuciyar Shi yace'" haka kawai nayi ta kallanta ba muharrama taba ba komai ba" har yayi gaba yadawo yakuma lekata a fili yace' ashe fa kedin halali nace, yafada yana yar karamar dariya,ganin bakinta na motsi yasa shi kara gyara tsayuwa ya zuba mata na mujiya Yana kallo,

Ita kuwa sai fama take da kanta tana mita ita fa a duniya shiyasa ta tsana zubawa kanta ruwa,kwata kwata bataso shiyasa idan ta kulle shi bama ta Kara kulashi sai wani lokacin kuma,ta tsani tajar Kai itakam,mitar ta take zubawa ba kakkautawa ita kadai,bakinta ne kawai yake motsi, haka ta bar kan badan ya taju ba sai don ta gaji, ribbon tasa ta daure kan shima dakyar sai kuma ta kama tufkar tayi mata kitso, kwanciya tayi ta lumshe ido tare da sauke a jiyar zuciya saidai kuma data kwanta sai taga kamar inuwar mutum a windown ta, kara bude ido tayi ganin bakowa yasata rufe idan ta, knocking din da taji a kofar dakinta yasa ta bude idanta ta zubawa kofar ido,ita fa tagaji wannan kwanciyar ta mata dadi bakadan ba,ji tayi ansake knocking tare da cewa "'ko in shigo ne?

Ai batasan sanda tayi saurin janyo hijabi ba ta bude kofar ta kalleshi sai kuma ta rasa me zatace,ta sunkuyar da kanta kasa kawai hannunta daya ta rike kofa dashi dayan kuma tana wasa dashi, murmushi yayi,

yace' Azo aban abinci yunwa nake ji tun safe banci komai ba, amma baki damu dani ba,
Kumbura baki tayi,amma batayi magana ba don batasan me zatace ba,sai dai kuma azuciyar ta maganar take,ita kadai tasan metake fada,kamar ya San metake fada

yace' aww zagina kike ? Allah ya sauwake ki zubo min ko? Kuma yazo ya dameki kina hutawa har da min Allah ya isa ko?

Zaro ido tayi Jin wannan lamari, batayi kuma magana ba kawai ido ta zuba masa,dafe Kai yayi

yace' kuma tsorata ni dazakiyi da wannan idan naki Masha Allah dashi, don kinga ni bani da su ko? Shikenan bakomai nasan inda zani, shikenan wata rana zaki karasani shikenan ni daman babu mai dona babu mai kulada ni bari na tafi bakomai idan na mutu ki daure kyace Allah yaji kanshi ko sau daya kinji,
Yafada yana neman juyawa,

Itakam tasan idan tana tare dashi to komai nata kuncewa yakeyi,ganin ya juya zai tafi har ya sauka daga Kan barandar zai sha kwana yasa,

tace' Ka tsaya,
Wani irin dadi yaji dabata tsaidashi ba dabai san sai yaushe zaici abinci,dukda yaji dadi kuma har kasan zuciyar shi yakeji,amma a zahira sai yayi kalan tausayi ya juyo, koda ya juyo ma bata nan hakan yasa shi dan yin tsalle ya dawo ya dauko kujera ya zauna, harda suyin tagumi ji yayi an Kira sallah, lokacin ta fito da abinci a plate tare da lemo sai anan ma ya tuna Ashe fa ya fito da malt a hannunsa ko ina take oho, mika masa tayi abinci yaki karba,kallansa tayi,

tace' idan baka so na mayar,
Kar yayi biyun babu ukun zero yasa shi saurin karba ta mikasa lemun hannunta ya amsa,bata jira cewar sa ba ta wuce daki ta rufe sannan ta jingina da kofar tana sauke ajiyar zuciya saida ta dawo normal sannan ta tashi tayi alwala Jin za'a shiga sallah.

Shikuma Allah ya gani ba duka lemo yake sha ba don shi wannan ma basan shi yake ba,tashi yayi wai da zummar yaje ya dauko malt dinsa sai dai kuma ganin gwangwaninta yasa shi tsayawa irin yaushe na shanye, zuciyar shi ta bashi amsa da kana kallanta, shafa kanshi yayi ya koma ya fara zira abinci lemon ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login