Showing 72001 words to 75000 words out of 173457 words

Chapter 25 - A BAKIN WAWA (AKANJI MAGANA) COMPLETE

30 Oct 2025

3943

muka nufa?

Tace'? ADAMAWA

('('('('('('('

Da sassafe yayi shiryansa tsab ya fice agidan beyiwa kowa sallama bare ya su San ya tafi, hanyar Jigawa ya dauka,bashi ya isa ba sai goma sabida irin tafiyar da yake yi address din da ya rubuta yake bi har ya karaso wurin, kana gana zakasan company ne karami don ko Rabin Wanda ya siya beyi ba,
Knocking yayi mai gadi ya fito,sai da suka gaisa,

yace' don Allah shugaban wannan company din nake nema,

Mai gadi yace' to kaga de yau lahadi bazaka Sami kowa ba,

Yace' to ko Zan iya samun sa a gida?

Ehh zaka iya, samunsa Baya zuwa ko ina idan na uzuri ne ya taso ba,

Yace' am ina ne gidan nasa?

G9 zaka je,

Ai Bansan G9 din ba,ni bako ne,

To kuma kaga bakowa anan kusa da sai nasa a raka Ka,amma Ka jira kadan wanda zai karbeni zaizo sai mu tafi in nuna maka,

To shikenan nagode badamuwa Bana jira din,

Basu wani jima ba dayawa wani yazo ya karbeshi, suka tafi,tafiya suke Yana nuna masa hanya har suka isa kofar gidan nan sa,sai da suka fita sannan mai gadi yace' to ga gidan nasa,ni na wuce,
Kudi ya Ciro ya bashi ya kuma yimasa godiya,

Karasawa kofar gidan yayi tare da knocking,Jin shiru yasa ya karayin wani namma de shiru karawa yayi sannan yaji ance waye?
Shi besa ba da wani waye ba,hasalima yasaba kawai door bell zai Danna yazo a bude,
Amma wani waye? Shiru yayi don besan mezai ce ba,

Zuwa tayi ta bude masa, yace' mai gidan nan?

Eh Yana nan,

Kice yayi bako,

To,

Ta koma bata jima ta dawo tace' ance Ka shigo,ita ke masa jagora har cikin parlourn sannan taje ta kawo masa drinks da snacks, duda da safe ne.

Wani mutum yane ya fito kamili babba dashi, wuri ya samu ya zauna suka gaisa sai kuma sukayi shiru,? mutumin yace' ban shaida kaba,

Binaif yace' ai baka sanni ba, amma wala'allah idan na Baka tambaya zaka iya tambaya hadina da komawa waye,

Mutumin yace' wannan wacce irin tambaya ce haka?

Murmushi kawai Binaif yayi,
yace' game da companyn ka, bayan Kai waye shugaban Ka?

Sosai mamaki ya bayyana a Saman fuskar mutumin nan, yace' Kai waye din Muhammad ne?

Fadada murmushin sa yayi yace' Sirikinsa ne, nasan daman tambayar Kenan,

Yace' siriki? Kai yaro Muhammad daga har 'ya'yan sa guda biyu da matar sa sun rasu, da dansa kace min? ne ma Zan yarda,

Binaif kamar yarda na fada maka ni sirikin sane kuma Ka yarda dani, 'yar sa nake aure Ummusalma koba ita bace?

Sosai mamaki ya lullubi mutumin yace' 'yarsa? Bata mutu ba? Tana ina? Ina take?

Yace' bata mutuba,Abu daya nake so da Kai shine Ka fadamin Kai waye din shine? Aboki ? Dan uwa? Kode wani Abu haka?

Numfashi mutumin yace' sunana Munir Yakubu, Dan asalin garin Gumel mahaifiya ta rasu tun ina yaro Babana Shi ya rikeni dukda mitar yayi aure da ake masa Amma yayi biris da zancen kuwa, Shi yaciga da Kula Dani har na Kaiga nagama Nce dina,Amma babu aikinyi a lokacin Babana ya fara ciwo kafa dayake Nika yake yi sai naciga dayi sabida aikin da za'a masa
Gashi kuma injin bayayi kullum Yana cikin gyara wayanci shike cinye mana kudin,kawai na saidashi na tafi Lagos don samu kudi,sai dai kuma kasan cewata sabon Shiga aka sa cemun kudi ga babu wurin kwana ga yunwa da wahala zafi komai ya hade min,nasami gafen titi na zauna kwatsam wata mota tazo ta bigeni tayi gaba Allah ya rufa asiri ma banji ciwo ba sai dai naji jiki,jiki ya kama ciwo Bansan meke damuna ba, idan nace zanyi dako kafin na dauka har andauke anyi gaba,ga ciwon kafa Ashe nayi tagade ruwan da zan shama aiki ne, ina kwance a gefen titi awannan lokacin mutuwa kawai nake bawa kaina,sai ga Ya? Muhammad da Matar sa Sunzo sun taimaka min sun kaini asibiti bayan na warke suka tambayeni inda nake na fada masu na kuma Basu labari,shine ya biya kudin aikin sannan yace zai Samar min aiki a kusa da gida don nake zuwa ina Kula da mahaifina,banyi musu ba na yarda bayan anyiwa Babana aiki yazo da kanshi ya daukeni ya kawo ni nan garin ya nuna min komai da komai da shagunan sa da inda yake da Zama gidajen sa komai nashi wai gudun bacin Rana, koda na tambaya shi Baya tsoran na cuce Shi? Sai yace duk Wanda ya cuci wani kansa ya cuta ba Shi ba,da wannan Babana kullum yake Kara min nasiha Akan kar na yaudareshi na rike amana ko a zuciya ta Bani da buri cutar sa, a haka muka shafe shakara uku ina masa aiki duk wani Abu da yayi sai ya fada min, sai dai Mahmud Baya San haka ko kadan Amma be taba nunawa ba,ya daukeni tamkar kaninsa haka itama matarsa, lokacin da ta samu ciki ya sai wani fili yace duk Wanda aka haifa yazama nashi, ranar da ta haihu ranar amaida wannan fili sunan Dan da Umar don ni har na manta ma da anyi zancen, sai dai washegari da za'a sallame mu a asibiti aka nemi da aka rasa daga karshe aka gano sace Shi akayi kuma ya mutu, bayan anyi hakuri suka kuma samun wani ciki suka haifi twins mas'ud da mus'ab sannan suka dawo Abuja inda ya cigaba da kasuwancin sa,Iyayen matar sa sune suka rike Shi don Shi? don Shi a hannun matar uba ya tashi mahaifinta ya daukeshi da suke unguwa daya a yarda ya ban labari Kenan, sai da twins suka shekara hudu Allah yasake a zurta su da Ummusalma suna Santa, tana da shekara biyu a duniya aka nemi yayunta aka rasa kosama ko kasa ba'a gani ba, anyi haka da sati daya gidan su ya kama da wuta, inajin labari washegari na tafi Abuja ganin gidan su ya kone kuma babu kowa da yake zaman makoki yasa na tafi kafancan Inda Iyayen su suke sai dai na iske babu kowa a gidan sun tashi, haka na dawo jikina ba dadi, ga kuma wani labari da ya riskeni cewan Mahmud ya mallake duk wata kadara ta Shi,banyi mamaki ba don nasan zai aikata hakan, sai dai bai san shagunan sa na nan ba? da wani dake Paris shima besani ba Dani da Wanda yake Kula Dana Paris muka cigaba da Kula da komai dake hannun mu bayan na fada masa halin da ake ciki.
Shiru yayi na wani lokaci sannan yace' gashi kazo Kace min Kai siriki sa ne taya?

Binaif da labarin ya Dan daure masa Kai Yana so ya bi komai a hankali ne, numfasawa yayi,

yace' shine ya dauke ta ya so ya lalata Mata tarbiyar ta,? sannan ya turata karatu don tarbiyar ta ta war gaje, sai dai Allah ba nufa ba hakan bata faru ba, sannan Yan uwanta Suma duk suna nan da ransu Umar ne bansan inda yake ba,Amma shima na tabbata Yana da rai,

Taya zakace Umar na Rai?

Sabida ta taba ganin wani, ba wannan ba ina so ayi wani abu? ,ya saida min da company guda daya dake Kano ya kuma bani takardun karya a matsayin sune na gaskiya nikuma ina da na gaskiyar a hannu na ina so mu hada karfi da karfi mu yaki karfe,kayi wannan sadaukarwa ga abinda ya maka,

Koba baka fada ba yaro, zanyi komai Insha Allah indai komai Nasu zai dawo, bawan nan ba gidan marayun dake Lagos ya sayar dashi yanzu duk yaran da aka Kai can to idan suka taso kasar waje ake tura su, wasu suna aikin miyagun kwayoyi wasu kuma fashi, Mata kuma a tura su bauta gida Jen aikin reno wanke wanke da dw sauran aiki,sa'ar daya ce basa bata Mata masu rayuwa sai dai Basu San inda zasu tsinci kansu a ciki ba,ga kuma yunwa da suke fama da ita,
Ina so mu fara daga nan kafin muyi komai,?

Binaif yace' to shikenan Insha Allah daga nan zamu fara amma abinda nake so daki Ka fara nemo mana wanne percentage ake bashi,

Taya Zan iya Nemo percentage din da ake bashi? Baya ga haka ya sayar dashi,

Murmushi Binaif yayi yace' koda ya sayar dashi bazai Bari haka kawai ba, dole za'a bashi wani Abu daga ciki, zaka iya nemowa tunda ka iya sannin an sayar dashi,

Zan duba na gani,

Cigaba da magana sukayi har? biyu tayi masu sani ba, bayan sunyi sallah Binaif yace' zai tafi
Dakyar ya tsaya yaci abinci sukayi exchanges numbers daga nan ya dau hanya Yana tafiya yaji Karan shigowar sako be Kula ba, wannan Karon yayi gudu a hanya don uku da rabi ma acikin kano tamasa kafin ya karasa gida anyi la'asar Yana zuwa bakowa a parlour jakarsa ya dauka ya Shiga ciki sai da yayi wanka yasa kayan shan iska yayi sallah sannan ya kwanta ya janyo wayar sa ganin message din ta yasa Shi budewa,

? ? Nayi tafiya zuwa Adamawa, take care.

Besan abinda yaji ba don bazai iya fada ba, take care Shi yafi bashi haushi ma, ba gaisuwa bakomai sai take care juyi kawai yake Yana maimata take care din nan ina laifin ma ta Dan masa message din na morning ko yaji sanyi a ransa,Amma sai take care da ce masa,tsaki yaja a Karo na ba adadi wayar ma ajje tayayi Yana tunanin su Mus'ab ne suka shigo banza yayi masu ya cigaba da abinda yake,

('('('('('('('('

Bayan sun tsaya sunyi sallah tayi tunanin tura masa message shiyasa ta tura masa Amma ba reply daman tasan bazaiyi ba mene na damun kanta, sai yamma lis suka isa da tambaya sukaje unguwar har suka karasa kofar gidan, gida ne matsakai ci na rufin asiri gefen? sa kuma gidane mekyau? ba laifi, sallama tayi a kofar gidan aka amsa shigowa tayi matar dake zaune ta tashi tana Mata lalle da fillanci ta bata wuri ta zauna ta kawo Mata ruwa mai sanyi ta ajje mata suka gaisa cikin fillanci, cikin fillancin matar tace Mata '" ban gane ki ba Bingyal daga ina?

Itama cikin fillancin ta mayar Mata tace' Baki sanni ba, sai dai ina tambaya nanne gidan Abdullah Abdul shakur? Da matar sa Mariya ? Suna da 'ya'ya biyu zulaihat da kuma Abdallah,

Cikin mamaki matar tace' eh nan ne ke wace??

Wani dattijo ne ya fito Yana dogarawa yace'wai me nake ji ne, ji nayi ana anbatar zulaihat da kuma Abdullahi,
Matar ta tashi ta karaso da Shi ya zauna sannan ta fada masa abinda akace da kuma tambayar da ta Mata,shima yace' fada mana ke wace?

Ni matar jikanku ne wanda 'yarku ta tafi ta bari,

A tare suka ce? a tare suka ce TASHI KI FITA..........

? ?? Tofah =?3?=?F?
@&?

? ? ? ? ~*Ayi sallah lafiya~*>?p?>???
? ?

By: '''Hijjart''' '''Abdoul'''
? ?? Cwthrt=?? ? ?? _Akanji magana_

??

Page 26 yayi missing kuyi hakuri kuyi manage a haka. Nagode.

NOT EDITED
POST 2020
REPOST 2023


? ? ?? 27

Baba be saurareshi yaci gaba,
yace' ranar da muka tsinceka acan wani kauyen ne, kusa da Adamawa ba nisa, mun tsaya don zainab tayi fitsari taje zatayi taga wani jariri a wuri dayake yarinya ce a lokacin sai da tayi fitsarin ta dauko yaran ta kawo tace Baba kaga a can wurin na ganshi,karbar Shi nayi na Kare masa kallo, ya kurkurje kuma idan ba lura kayi ba dakyau tsab zakace Baya numfashi, da kuma hannu sa Wanda ya kumbura,dayan hannun kuma shaida ce ta daga asibiti aka dauko Shi Wanda ake mannawa yara shaida, da number, ita mahaifiyar ta ma tazaci ya mutu,? mukaje muka duba ta nuna mana inda taga yaran ga kuma towel can a gefe, daukan towel din mukayi,ta rufe Shi tace ya mutu,nine nace Mata be mutu ba,gashi kuma bakowa a wurin mu ba gidan dagaci muka sani ba, tausayin yaran yasata cewa mu tafi dashi,haka ma zainab banki ta tasu ba muka dawo dashi Amma sai da mukaje asibiti aka bashi taimakon gaggawa tukunna, sa'a Muka wucs gida,sai muna zuwa gida labari yasha banban, tsab ya kwashe komai ya fada masu har zuwan da yake yi da kuma zuwan Shi na karshe sa'a nan yayi shiru,

? Tunda Baba ya fara yake sauraran Shi be taba sanin saboda dashi ne basa zuwa wurin Anfa da Fendo, hawaye ne ya fara zarya a kumatunsa Shi shikenan beda uwa be da Uba? Gashi de wulgar dashi akayi ai kuma mutane sun shaida haka? Sun San basa son sa meyasa suka haifeshi da hanzari ya dade da mutuwa da ba'a ceci rayuwar Shi ba,tunda aka fara ya fara comparing rayuwar sa da ta Ummusalma beda iyaye kamar yarda itama bata da iyaye inama zai ganta.

Anty ce ta kwantar da kanshi a cinyarta,
tace' lokacin da naga hoton Ummusalma na hango tsan tsar kamar ku, sai dai Kai Baka ga hakan ba sam,tun a sannan na dasa ayar tambaya a kanta shin Baku da alaka ne? Har hotan na turawa Baba shima kuma ya gani sai dai yace' min yana yawan ganinta a airport din London tana raka wata ita kuma sai ta dawo, Ashe shima Yana tunanin kamar yarda nake, daga baya ne yadena ganinta besan dalili ba, beyi wani Abu akai ba Shi a zatan sa 'yar can ce. Koda yayi bincike a kanta sai ya tarar ba haka bane ba, ba iyayenta bane sai dai be tsananta binciken ba ya barshi iya haka.?

Baffa dake sauraran kowa yace' ita wannan din da kuke fada Wacece?
Anan suka bashi labarin abinda suka sani, sannan ummu ta Basu kaf diary dinta da ga karanta sosai kuwa abin ya Basu mamakin haka ga kuma news din da sukaji ranar Saturday Amma ita ummu bata ma San anyi ba. Shiru kowa yayi Yana tunanin wani Abu ransa, shidai Uncle abinda yake ji kadai ya ishe Shi,
?
Ummu tace' Baffa da mukazo naji kace Kanwar Shi kun Santa ne?

Baffa yace' tabbas tazo anan ta kwana, yau da safe ta tafi kuma bakowa ne yace ta tafi ba sai ni,nine tun farko naja komai me ake da zuciya irin tawa?

Baba yace' Anfa kadena fadar haka mana, Wacece ita har tazo nan?

Baffa kasa magana yayi gani yake duk Shi yaja komai da ace bece ta tashi ta fita ba da duk haka bata faru ba,

Inna tace'? Yarinyar tazo gidan nan,itace ta fara ankarar mu abinda babu Wanda ya fada mana, itace ta daidaita komai tsakanin mu da ku, itace silar komai, gashi ta tafi, sai dai tace' ita Sirakace a gare mu domin Dan zulaihat take aure.

Dan zulaihat ?? Baba ya maimaita,
Jinjina masa Kai tayi tace' ehh haka ta fada mana,

Anty tace' me tace maku sunanta ?

Ummusalma tace, kuma a gaskiya Nima Naga kama sosai da sosai Dan Zama a Iya cewa 'yan biyu ne,

Mijin Anty yace' to ya akayi kuka barta ta tafi?

Inna tace' kayya yaro kuskure an rigada na tafka Shi sai kuma gudun yin wani,

Yace' to Baku tambayeta komai game da ita ba?

Gaskiya bamu tambaya ba, bamu Sami damar yin hakan ba,

Shiru yayi Yana nazarin wani Abu,kowa shiru yayi can ya dago,

yace' kunsan ita zulaihat dinne? Da tace' danta take aure?

Inna tace' 'yar muce zulaihat wacce ta bata shekara da shekaru,

Yace' to ko kunsan inda take? Nufina gidan mijin ta ?

Baba yace' gaskiya bazan ceba,don nikam rabona dashi na manta ko a hanya zai iya wucewa na wuce bamu gane juna ba, ko gidan ma ni bazan iya kaika ba,

Inna tace' Ada suna zuwa daga Baya ne kuma suka dena muma kuma muka dena shikenan zumunci yayi nisa kuma,

Shiru yayi yace' yanzu dole muna bukatar saninin inda gidan yake,dole sai anyi bincike indai muna San mu San idan suna alaka da Abdullah,
Kowa kuma yayi na'am da zancen sa daga nan kowa shiru yayi shidai uncle ba Baka sai kunne Shi bega amfanin Nemo subama tunda sune suka yar dashi ai.?

Sai bayan sallahn Isha Baban Ummu yacet zai tafi hakan, zai barsu anan don su ga 'yan uwa da abokai, tunda Yana da wata matar,ita de ummu bata so ba, gashi lokacin basirar ta ta dauke batace makaranta ba,haka ya taho a jirgi Allah yasa ya tafi da passport din Shi ya barsu ba ranar dawowa .


Yusuf ne da Yaseer suna zaune a tsakar gidan su,kowa yayi jigum Yana kallan wani wuri, suna wani tunanin na daban, gaba daya sun rame sabida tunanin da suka sawa kansu danma suna Dan debe kewa idan da nepa,to yau kusan sati ma babu nepar? Shiyasa suka fito suka zauna,
Yusuf ne ya kalli yaseer,

yace'? kasan menake tunani?

Yaseer yace' a,a sai Ka fada,

Ina tunanin Ummu ne,nasan tadena surutu yanzu sabida rashin mu,

Yaseer yace' nasan dahaka,Amma Kai Baka tunanin Mama?

Murmushin takaici Yusuf yayi yace' me zanyi tunanin akai? Ita da suka raba uwa 'da, uba da 'da?
Karka manta sune suka raba yaya salama da Babanta da kuma yayunta guda uku,har 'ya'ya hudu? Hakan be ishe suba sai da suka nemi su watsa Mata tarbiyar ta a matsayin ta na mace,hakan be ishesu ba suka kuma turata karatu Akan manufar su,ko ca aka ce masu? kowannne dane ake turawa yake watsewa oho, kuma kana min zancen su? Banyi ba kuma bazanyi ba,

Shima yaseer murmushi yayi yace' nagode daka tuna min hakan,Amma kasani no matter how bad they are, they still our parent, don't ever forget mufa maza ne aljannar mu na kasan su,ba Mata bane da aka ce aljannar su na kasan mijin su, koda matanne ma ba'a ce sabawa iyayen su ba, and kuma idan ma duba acikin 100% Maza kalilanne ke bin iyayen su musamman idan basuyi dacen Mata ta gari ba, Mata kuwa zaka samu kusan rabi da kwata basa bin iyayen su, Bana so mu Zama masu sabawa iyaye kuma fa sun bamu gwargwadon ikan su, suna San mu fiye da tunanin Ka,

Murmushi Yusuf yayi yacet ehh lalle Kace min ka girma u know all this,Nima kuma nasani, Amma abinda sukayi sun kyauta ne? Mema ya kawo wani bin iyaye, inama Ka zancen Ummu ne fa,

Yace' nasani na fada maka ne don kar wata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login