Showing 135001 words to 138000 words out of 173457 words

Chapter 46 - A BAKIN WAWA (AKANJI MAGANA) COMPLETE

30 Oct 2025

3940

abota ko?"

Yusuf yace'' shiyasa muke abokan juna ai"

Ummu tace'' yaya salama yunwa nake ji"

Ummusalma tace'' aikuwa ba'ayi abinci ba, Nima na koshi nayi ba, wata indomie aka dafa mana, ba kwai ba komai sai shegen yaji, kuma babu lemun hada wa,sai de kije ki dafa maku wani abun"

Yaseer yace'' daga mana wake da shinkafa yau indomie muka ci fa da safe"

Tashi tayi tace'' haka za'ayi Dan uwa na"

Yusuf banza yayi dasu sunsan Baya son Shinkafa da wake shine zai ce a dafa Dan neman magana,

Yusuf yace'' kasan yayamu ko? Wannan yaran kullum sai sun bata min Rai, narasa me na tsare musu"

"Ai haka Yara suke aboki na, Nima haka nake fama da wannan yaran abin sai addu'ah kawai"

Mus'ab kawai Kai ya girgiza, Mas'ud kuwa yace su fita suyi ball, fita sukayi su duka Banda Ummusalma da tashi ta Shiga kitchen ganin ummu na aikin Dora abincin yasa ta dauko fruit salad tace'' Idan kin daura kizo ki Sha wannan, kafin kuci abinci,ki kuma daura da yawa basai an kuma yin wani abincin ba"

Ummu tace'' to shikenan"

Yoghurt ta dauka ta fito waje, ganin su suna ball amma Banda Mus'ab Shi Yana zaune Yana kallan su.

Zama tayi a kusa dashi, ta taba Shi,sai da ya juyo ya kalleta,

tace'' Wacece ita?"

Kallan ta yayi dakyau ita kuwa bashi take kallo ba, su take kallo,

yace'' banga ne ba?"

" Tunda kaji abinda nace ai shikenan, sunanta?"

Kallan sa ya koma zuwa wurin su, cikin muryan alamar dake nuna tsantsanr damuwa,
yace'' ban san taba, ban san sunan ta ba, ban san gidan su,Dan uwa, kawa, bansan komai ba, kawai ina ganin ta de a unguwar Dana zauna dake Abuja, tana yawan wucewa da yamma, tana cikin damuwa, ina San taimaka Mata,ban san ta inda Zan fara ba, kuma na dena ganin ta, naza ci kawai taimakon ta zanyi, Ashe ba haka bane, Son ta nake ban Sani ba, sai da na dena ganin ta a unguwar kwata kwata,I love her"

Cigaba da sha tayi tace'' da Ka fada Mata tun wuri da duk haka bata faru ba, yan zuma lokaci be Kure ba, Insha Allah za'a samu solution"

"But please don't tell Fav please! Ina san Naga shima ya samu wacce yake so"

Shiru tayu ba tayi magana, sabida ya tuna Mata da Sameera har yanzu tana can tana dankwan san, Wanda yanzu ya tabbata ya manta da ita, ajiyar zuciya ta sauke kawai tana ci gaba da kallan su, ji sukayi an turo gate an shigo da Kaya niki niki an kawo an ajje, drivern gidan Daddy ne,

Mus'ab yace'' Malama Musa kayan waye?"

Yace'' na Umman Alhaji ne ai" sannan ya koma, aikuwa sai ga tana ta shigo,

Mas'ud Yana ganin ta ya kwasu da gudu yazo ya rike ta, saura kadan su fadi badan ya rike ta ba da tuni sun hantsila, cikin bala'i,

tace'' Kai kaji yaro ne, yanzu Dana Fadi ba, ai sai dai wata mai tagwayen sunan bade wannan zainabun ba"

Sandar ta ta dauka zata kwala masa ya rike, yace'' Haba Hajjaty murna ce fa hakan, ai kinsa Dan da uwa idan maman Shi ta dawo haka fah yake Mata"

Kwace sandar tayi ta kalli su Ummusalma da mus'ab tace'' ehh gwara Kai ai, Dan albarka akan wasu da ko kallo Basu ishe ni ba, kuma a gidan nan Zan zauna ko ana suna ko ba'a sona, aji ma dakyau yawwa ana nuna min daki na"

Binaif da yazo yanzu dayake ba'a mota ya fita, ganin ta da yayi yasa ya turbune fuska yace'' ai banyi da dakin ki ba, kima koma inda kika fito Dan nidai baza ki zauna ki mayar min da gida gidan jarababbu ba"

Wani salati ta dauko ta rabfa, Kai mace wani ya mutu, tace'' yanzu ni zaka fadawa haka? Au..au..du..audu shakuru ni? Nice fa na haifi babanka,na haifi Ubanka,na haifi babar Ka, sannan nazo na haifi uwar Ka da ta koya maka rashin kunya, Allah ya jikanta, shine zaka ce min jarababbiya ko? Har kace mema yace?

Ya fada tana kallan Mas'ud, Mas'ud yace'' haka yace baza ki maida masa gida gidan....

Karaso wa yayi ya kai masa naushi ya goce yaje ya buya a bayan ta,

tace'' yau a gida nan zan kwana,Kai Bama kwana daya na, anan za'a jana'iza ta, Dan uban Mai gidan da matar mai gidan ko suna so ko basa su"

Takuma cewa'' kaga nuna min daki, a cikin gidan masu gidan nan"

Mas'ud kuwa kayan ta ya dauka ya, yace'' shigo na kaiki dakin ki"

Tana tafiya tana Mita, tsaki Binaif yayi ya zo ya zauna, Yaseer ya Kara so yace'' yaya Wacece?

Mus'ab yace'' kakar muce"

Yusuf yace'' amma tafiye masifa''

Ummusalma tace'' Idan taji ku kuda ita ne,Kar ku sani a ciki"


Suna cin abinci Umma tace'' wai ba ruwa a gidan nan ne?"

Yusuf yace'' jiya suka dawo, inaga yau kuma aikin gida sukayi"

Ummu tace'' ehh inaga yanzu zasu je su siyo"

Umma tace'' ai ni ina San haka, nayi tambaya,ayi farat a fada min amma masu gidan nan hmmm sai addu'ah"

Girgiza kai Binaif yayi, kawai ya tashi ya tafi dayan parlourn ya zauna, Umma kuwa daga murya tayi tace'' azo a siyo min ruwa dan kaniyar mutum"

Mas'ud yace'' Bari mu Gama daman za'a siyo wasu kayan sai muje"

Sai da suka sha fruit salad sannan suka fita Banda su ummu da suka wuce gida, aka bar Mas'ud da Umma kawai sukuma suka fita.


Sun Gama siyayyar su Ummusalma tace'' ina zuwa bari naje na dauko wani Abu"

Mas'ud yace'' so kike mu tafi mu barki,daman kin daddar mu"

Binaif yace'' muna nan kiyi sauri"

Wurin turare tayi, zatayi kwanar da zatayi ta hango Sameera ita da ummu suna zaba, kallo Daya tayi mata ta hango kwantacciyat damuwa a tare da ita, da wani irin speed ta juyo, ta dawo,

mas'ud yace'' ina abinda kika dauko?"

Matsowa tayi kusa dashi tace'' na kasa kuma banga masu aikin ba, zo muje Ka dauko, ina bb?"

" Ya tafi mota, muje ni na dauko maki,gaba yayi ya barta a baya, ita kuwa a Baya ta tsaya tana tafiya a hankali, tana binsa shikuwa har ma yaje, wurin sai kace yasan me zata dauka, kallan kayan wurin ya fara yi a hankali idansa ya Kai kan wani turare mai kyau dashi hannu yasa zai dauka, itama tasa zata dauka, dago da kan da za tayi kawai ta makale a haka,ita bata dauka ba kuma bata janye hannun ta ba, shima dagowa yayi ganin Wacece haka, ganinta da yayi yasa kirgin sa dokawa,gashi shima ya makale a hakan,kuma ya kasa dena kallan idan ta.

A hankali ta saukar da kanta ta janye hannun ta, ta kakaro wani munafikin murmushi,

tace'' Ashe ana ganin Ku"

Shima janye hannun sa yayi sai dai be dena kallan ta ba,

yace'' uhm"

Tace'' Allah yayi zamu sake haduwa,kafin nayi aure"

Dan dagowa tayi ta kalle Shi,yarda ya kafe ta da ido yasa ta kawar da kanta gefe tana kallan wasu Kayan, dakyar ya furta "aure zakiyi?"

Tace'' eh aure zanyi nanda wata uku zuwa hudu sai anjima"

Ta gefen Shi ya rabe ta wuce,wani siririn hawaye Yana zubota. Kulle idan sa yayi besan dalili ba amma wannan abun da ta fada cewam zata yi aure tamkar an Sami garwashin wuta ne an watsa masa a cikin zuciyar sa haka yaji,

Ummusalma tazo tace'' hey na dauka fah, mu tafi"

Kallanta kawai yayi yaga kuma tayi gaba, hakan yasa kawai ya bita ba Dan yasan me tace ba, a mota ma suna ta surutu shikuwa besan me yake ciki ba.





Waya yake amma Baya Jin abinda ake cewa sosai sabida hankalin sa yayi gaba, kashe wayar ma yayi sai da ya shigo yaga dakuna, ya manta wanne tace masa ma,
Wata zuciyar tace'' kamar ten tace"

Hakan yasa Shi tura kofar kusa dashi ya afka, bakowa a cikin dakin sai wani daya gani, Yana kwance kamar ma na Rai a jikin Shi,Amma ganin bugun zuciyar shi yasa Shi matsawa a Hankali ji yayi zuciyar Shi na bugawa da sauri da sauri, gani me kama dashi sak, photocopy din Shi,ban bamcin shi ya tsufa dayan kuma yaro ne, wani Abu yaji Yana masa yawo a cikin zuciya, a Hankali ya mika hannun sa ya shafi fuskar shi,

yace'' da yanzu ina da da kamar wannan"

Kara shafa fuskar yayi sannan ya juya ya tafi, Yana fita zuciyar uncle ta fara bugawa da sauri da sauri, Yana fara wa kuma su Baba na shigowa suka Kira doctors.

Baffa kuwa na fita ya hadu da Amina tace'' laa Baffa nine fah nace, shigo.

Beyi magana ba,ya Shiga ciki ya zauna,Yana Shiga su baba na zuwa,

yace'' an siyo mata maganin ta ne?''

Tace'' yanzu zanje na siyo Kar ta tashi ko tana bukatar wani abu Shiyasa"

"To shikenan kiyi sauri karki zauna"

Fita tayi Shi kuma ya dawo kusa da ita ya rike hannun ta gam, Yana kallan fuskar ta, gaba Daya tausayin ta yake ji, yasan dalilin 'ya'yan ta ne wannan ciwo ya same ta kullum sai tayi kukan rashin su, kullum kwana take tana binsu da addu'a, 'ya'yan da bata san suna da Rai ko Basu da Shi ba, dalilin su ta koma wata silent da ita, ajiyar zuciya ya sauke ya Kara damke hannun ta, Yana tuno fuskar Abdullah.



Saida komai ya lafa, Doctor ya kira Baba yace'' ansa mu cigaba don da alama yaji wani abu ne, shi yasa,kuma da ace an cigaba da magana to ba makawa sai zai iya magana, Bama iya magana ba har tashi zai iya yi"

Baba yace'' to yanzu ya za'ayi?"

" Ya kamata kuke debe masa kewa ko hakan zai sa yake Jin maganar ku har ya tashi,tunda Yana jin, magana ce bazai iya ba da bude Ido"

Shiru Baba yaya yace'' daman Shi Baya gani?"

" Baya gani sai dai yaji,kasan wasu Idan Shiga comma magana ce kawai basa iya yi,wasu kuma basa iya bude idan ma bare su gani, amma suna ji"

Numfashi yaja ya sauke, ya mikawa doctorn hannu suka gaisa sannan ya fito,da ya zo yaga wani a kofar a dakin waye ne yazo?"
Amma ai da'alama ba wurin Shi aka zo ba,tunda yaga dakin da aka Shi Wanda yake kallan nasu ne, dakin ya koma ya duba Shi an masa allurar bacci, kallansa ya kuma to sannan ya fita.

Yana fita Baffa na fitowa Baba a Baya Baffa a gaba, a haka suka fita har suka zo harabar asibiti babu Wanda ya lura da Dan uwansa kowa hankali yayi gaba.


('('('('('('('



Ummusalma ganin yau Mas'ud ko abincin arziki beci ba,bare yayi hira da tsokana, gashi ana gama breakfast yayi part din su kamar jira yake a Gama, Umma tayi tayi ya fada Mata,Amma yace kansa ke ciwo kawai.

A hankali ta turo kofar parlourn su Yana kwance Akan kujera, Yana kallan saman parlour gaba Daya Yara sa taka maimai meyake ji, kuka ma Shi yake so yayi amma ya kasa, waya kawai yake kifa wa Akan cikin sa da dayab hannun sa,dayan kuma yayi pillow da Shi. Har ta shigo ta zauna besan tana yi ba, center table ta dauko ta zauna a saitin kansa tana kallansa, hannun ta Kai ta shafa goshin sa,

tace'' me yafaru chatty?"

Dauke hannun ta yayi yace'' ki barni,Dan Allah karki Kara samin damu wa"

Murmushi tayi ta kuma maida hannun ta shafi goshin sa zuwa kansa,

tace'' tell me, me yafaru meke damun Ka please! Idan ba so kake Nima na Shiga damuwa ba,Haba mana chatty"

Kulle Ido yayi ya bude suna kanta yace'' aure zata yi, nan da wata hudu or what oho but aure zatayi fa..."

Sai hawaye besan ma yayi ba, kawai ta kifa kansa a cinyarta,bata Hana Shi sai da yasai saita, ya koma ya kwanta ya rufe Ido Yana ja majina,tare da sauke ajiyar zuciya,

Tace'' Wacece zata yi auren?"

Wani kallo ya wurga mata,cikin wani irin kunar zuciya yace'' ita wacce kika hada ni da ita, Sameera nake nufi idan ke bakya gane wa"

Tace'' ohh! Wai Sameera? Shine daman kake wani damun Kan Ka? Naga Baka Santa? Meye abin damu wa? Me zata ma? Tunda gasu Yusuf nan suma ai zasu maka abinda zata yi maka"

Kulle idan Shi yayi gam,ji yayi wani iri sam be kyau ta ba, hawaye ne ya zuba masa ya goge,

yace'' please Ummusalma stop joking, this is not time for joke, ehh?"

Tace'' okay fine, let her go"

A sukwane ya tashi zaune yace'' What?"

Tace'' yes! Let her go...



~This page is for u cwthrt =?? Happy birthday to you Baeb.

By: ```Hijjart Abdoul```
Cwthrt =??: ? _Akanji magana_

??
? ?? 51

Kallan ta yake yi Wanda Shi kansa bazai ce ga taka mai-mai na meye ba, bare kuma ita da akeyi wa, wani hawayen ne ya zubo masa Mai ciwon gaske, yasa hannu ya share.

yace, "Na barta ta tafi fa naji kin ce? To where?

Hawaye na kuma zubo masa,
yace, "To somebody's wife? Uhmm are out of your sense?? Kinga please go. Jeki kawai".

"I said go".

Ya faWa tana masifa yana goge hawayen sa.? "Bansan Kara ganin ki, ki fice kawai, ina daman kin tsane ni ko? To je ki na kusa mutuwa".

Ajiyar zuciya ta sauke,ta kamo hannun sa,ya fizge, yace'' I said go!''

Kara kamo hannun tayi tace" ohh! Wai Santa kake?"

Fizge hannun sa yayi cikin daga murya yace'' ki fita nace"

Ita dariya ma yake ba, Ashe haka ya iya fada bata sani ba, this is the? first time da ta ga? jarumta hade da fushi a ciki idan sa, sai yanzu tasan shi Win ma ashe? namiji ne, murmushi tayi mai kyau Wanda dimple Win ta ya loma.

tace'' Chatty, Sameera loves you too"

Kallan ta yayi, yace, "banga alamar hakan ba, da tana so na ai da ta faWa min".

"Macen da ta? amsa sunan ta, macen da take da aji Chatty babu yarda za'ayi tace tana San wani da namiji koda kuwa zaiyi ajalin ta, tambayar anan shine menene dalilin da yasa ta fada maka cewan zata yi aure? Sai tana Sanka hakan zai faru, da'a ce basan Ka take ba, zata ja Ka da surutu ne kuma baza ta fada maka ba sanda zata yi aure ba sai auren ya matso kusa sosai zata? sanar da Kai, abinda yasa ta sanar Kai saboda kayi wani Abu akai"

Wani irin farin ciki farin ciki yake ji, har wani irin dariya dariya ya fara yi da hawaye na zubo masa.

yace'' dagaske kike fada kuwa?"

"Da karya nake fada"

Rufe Ido yayi ya Bude yace'' kina fa nufin tana Sona kena?"

" Tabbatar wa zaka tsaya yi ko kuma neman hanyar da Zaka bi Ka same ta"

Hawayen sa ya Kara goge wa yace'' a,a hanyar da Zan same ta nake nema"

" Kaje Ka samu bb Ka fada masa, Shi kuma zai fada wa Daddy"

Daga haka ta tashi ta fita,
Wata ajiyar zuciya ya sauke yana godiya da Allah.

Umma na zaune tana kallo, Ummusalma ta Shiga,
Ummusalma tace'' Umma sannu da hutawa"

Umma tace'' yawwa sannu, nace kinga an kwantar da Nafisa a asibiti ta Kira wayar ku gaba Daya bata Shiga ba, nace ko tafi ya zamuyi ne"

" Sai dai network, kuma kinga bamu sani ba, inaga Shi ya sani? be fada ba, Dan kinga dazu ya fita"

Umma zata yi magana sai ga Binaif ya shigo shida Mus'ab, Umma tace'' kai,Kai mai kake? jira kazo Ka Kai mu asibiti"

yace'' daga asibitin nake, sai dai Mas'ud yazo ya Kai Ku"

" Dan jakar uba,Ashe ka sani baka fada ba,wai meke damun ka ne, baza Ka warke ba ko?"

Zama yayi a kusa da matar sa ya daura kansa a cinyar ta,
yace'' nace maki Banda lafiya?"

" Mtsww duk abinda zaka yi sai dai kayi amma nida gidan nan mutuwa ce zata raba,marar kunyar banza,ko nace marasa kunya, karshen lafiya ma kuwa"

Ummusalma tace'' Bani key din, muje mu dawo"

Tashi yayi ya? Galla Mata harara yace'' Baki da lafiyar? Sai dai Mas'ud yazo ya Kai Ku"

" Da dan albarka ma lafiyan Shi qalau da ban ma magana ba,? Tunda tace Ka bata Ka bata mana, ko bakin cikin samun ladan kake min ne?"

Key din ya Mika Mata,ya tashi ya wuce dayan parlourn ya zauna, itama tashi tayi ta dauko hijabin da jakar, Umma kuwa Mayafi aka yafa, suka fito, Mas'ud? daya fito yagan su,

yace'' Umma ina zuwa"

"Za muje duba marar lafiya ne a asibiti"

Yace'' to a dawo lafiya"

" Allah yasa"

Yana kwance ya shigo ya same Shi, zama yayi a kasa, Yana sunne kai,

Yace'' bb"

Bude idan sa yayi ganin Mas'ud a kasa yasa Shi tashi zaune,
yace'' lafiya nagan Ka yau a kasa?"

Kara sunne Kai yayi yace'' da..ma..n..daman am..."

" Kaga meye kake tawani daman daman me?" Nade San ba kunya ta kake ji ba, bare nace wani abu"

Kara sunne Kai yayi ya fara shafa keya,Yana ta motsi da Baki"

Dariya ya bawa Binaif sosai, Binaif yace'' karde kaje,garin sunne Kai,Ka kifa kanka a kasa"

Shiru ya kuma yi sai Dan murmushi murmushi da yake yi,

" kaga nifa ba ca nace Zan Baka, 'ya ta ba,bare kuma kazo kana wani Jin kunya ta, abinda bamma taba gani ba kena, Mas'ud da kunya"

Yace'' daman fah''

Tsaki yayi ya kwalla wa Mus'ab Kira, Mus'ab da yazo a kujeran da Binaif yake ya zauna,

yace'' bb gani"

" Yawwa tambaye Shi, me zai fada min, sai wani sunne Kai yake yi, Yana Jin kunya, idan ya fada maka Ka fada min"

Kallan sa Mus'ab yayi yace'' wonders, yau Kai ne? haka? Kunya fah Kenan"

Mintsi nin Mus'ab yayi a kafa, mus'ab
yace'' kut, lalle ma me na maka?

Waya akayiwa Binaif ya tashi yace'' kunfa ni na fita, idan ya fada maka, Ka fada min"

Yana ganin Binaif ya fita shima yayi sauri ya tashi ya dawo kusa da Mus'ab ya lankwashe kafa daya, daya kuma ya sauke ta a kasa yake facing din mus'ab,irin zaman da yake so Kenan, musamman idan zai zuba surutu Baya Zama normal a kujera,

Yace'' Kai dalla,Ka kusa cemin Yaya Mas'ud, Kai da waccar Aljanar, very soon zaku fara"

Mus'ab yace''

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login