Showing 141001 words to 144000 words out of 173457 words

Chapter 48 - A BAKIN WAWA (AKANJI MAGANA) COMPLETE

30 Oct 2025

3931

da take ba, amma? nasan ana wurin take"

Amina tace'' to mu Shiga daki????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? daki muna dubawa"

Haka suka yi suka fara Shiga Daya bayan Daya suna duba wa Baffa na rike da Inni,

" Wai ita wannan aljanar meya same ta?"

Mus'ab yace'' ba tare muka shigo da Shi ba bare ka mana wannan tambayar"

Anty safiya tace'' ai Mas'ud ya iya tambayan renin hankali, tun dazu yake wannan tambayar muna bashi amsa yaki hakura, yanzu Ka tashi kaje wurin doctor Shi yasan me yake damun ta"

Zubura Baki yayi yace'' daman nasan ba Sona ake ba"

Kallan Binaif yayi da ya zauna Yana ya rike hannun ta Yana kallan Shi, Nafisa kuma tana zaune a gefen ta,taji sauki sosai daman ciwon ciki ne kamar baza tayi ba, sai da tasha allurai da drip tukunna Allah yayi, taji sauki ba laifi.

Anty safiya da Umma kuma suna zaune a Kan tabar ma,sukuma su Mas'ud suna Ka Kujera,

Yace'' bb wai me yasa meta ne"

Ko kallan Shi beyi ba, bare yasa ran amsa, ganin haka yasa Shi yaja bakin sa yayi shiru be kara magana ba,

Umma tace'' Kai jama'a a tashi a kaini gida,nagaji da zama anan nazo ganin marar lafiya Ashe ta warke sai na bige da zaman wacce ta kawo ni, a tashi a maida ni gida"

Anty safiya tace'' to Umma tashi mu tafi na ajje ki a gidan Binaif din, sai na wuce gida,sunce zasu dawo kinga sai na sanar da su muma ana jimawa zamu dawo"

Tashi Umma tayi tace'' Haba mutum de yayi ta Zama,zaman jinyar ma da bansan da ita ba"

Gaba tayi tana dogara sandar ta,
Mas'ud yace'' Umma ga mukullin, mu muna nan sai aljana ta farka"

Anty safiya ce ta ansa tare da kwada masa, tace'' Ka manta ba aljana ba, bulokiya ce"

Tafiya tayi zata tafi Nafisa tace'' Momy Nima tafiya zanyi gaskiya, tunda na warke ina San zuwa islamiyya ma kuma"

Bata Hanata ta dauko Hijabin ta suka tafi, ya rage sai su,

Mas'ud yace'' yawwa daman kunyan Anty safiya nakeji Bari na Kira budurwa ta muyi waya da ita"

Mus'ab yace''? mu ai Baka Jin kunyar mu,Amma kana Jin ta bb Ka tuna dazu da kace..."

Da gudu yazo ya rufe masa Baki yace'' kaifa ba'a sirru da Kai,meye na fada kuma? Karka fada Dan Allah kaji my Twinny"

Cire hannun sa yayi yace'' dalla sake ni, Kuma wallahi Ka Bini a hankali tam"

" Eh naji yi hakuri, Yaya Mus'ab"

Tashi yayi ya koma kan gadan take yace'' idan Ka biyo ni Kuma anan zan fada,daman kaga ogan basu da lafiya kaga idan Ka tabo shi, shikenan komai zeeeeerrrro"

Yana so yayi magana Amma yasan Mus'ab tsab zai fada,hakan yasa ya koma ya zauna ya sunkuyar da kansa looking so innocent,

Mus'ab yace'' bb me yasa meta"

Shiru yayi ba amsa har? fitar da ran za'a amsa masa don Mas'ud shima matso da kujerar sa yayi kusa da su, zaiyi magana, yaji Binaif yace cikin low voice,

yace, "Taga Abban ku"

Kallan juna suka yi, Sannan,
mus'ab yace'' to meyasa bata masa magana ba"

Kallan shi yayi da idan sa da yayi ja dan tsabar takaici, sannan ya dauke kansa ya maida Shi kanta Yana kallan ta, cikin bacin Rai,

yace'' ba magana ta masa, she was so? happy da taga Baban ta, amma shi ba hakan ba ne ba a wajen sa"

Shiru yayi Yana Kara tunano abinda ya faru, yace'' he was asking Wacece ita, bayan dukkan alamu sun Nuna yasan ta,Amma wai yake tambayar Wacece ita?
Hmmm abin da ya bata mamaki Kenan da firgice shine ta shiga wannan condition din"

Mas'ud yace'' to me yasa zaiyi haka?, Besan ta ba, I think zai yi farin cikin hakan"

Mus'ab yace'' Kode besan ta ba"

Tsawa Binaif ya daka yace'' kuma shaukin da na gani acikin idan sa nace me? Besan ta ba kome"

Zaiyi magana yaga ta fara bude Ido a hankali da'alama kuma maganar Shi ta tashe ta, a kansa ta bude idan ta fes, Kara rike hannun sa tayi dakr cikin nashi,

tace'' dagaske be sanni ba?"

Rasa ma abinda zai fada yayi,
Mas'ud yace'' kinga ya sanki,zai zo ma idan anjima zai zo kinji ko,ki kwantar da hankalin ki eh?"

Mus'ab yace'' baza su zo ba"

Ji sukayi an turo kofa an shigo, gaba Dayan su Ido suka zuba wa kofar Banda Binaif da yake kallan ta, Yana kissima abubu a Kan ta, yasa a yanzu babu abinda take so irin iyayen ta, amma su kuma bata ita sukeyi ba, maganar Inni ce ta katse masa tunanin sa,

Tace'' Wali..da"

Ita Inni Bama taga su Mus'ab ba,kawai idan ta Akan Ummusalma ya sauka,? sai da taji,

mus'ab yace'' Ina kunce Baku San ta ba? Me kuka zo yi Mata"

Ummusalma kallan matar da ta Kira ta walida tayi,ita daba walida ba?

Baffa yace'' munzo ganin 'yar mune"

Binaif yace'' kunzo ganin ta ko kunzo Kara sata?"

Amina tace'' ya kama ta kasan da wa kake magana"

Mus'ab yace'' hmmm sanin dawa yake magana nanne yasa Shi ya bashi amsa, shakarar nawa tayi tana neman sa? Sai Rana tsaka ta ganshi kuma yasa ita ce sannan yake tambayar Wacece ita?
To Bari na fada masa ita din Wacece a yanzu, bakowa bace sai 'yar Adam Dan Lami, Matar Abdulshakur Adam, Shikenan haka yayi ko kuna San karin bayani?"

Inni a hankali ta? tako har wurin sa, ta shafi fuskar sa tace'' Mus'ab?"

Ta kalli Mas'ud tace'' Mas'ud"

Kawai ta hada su ta rungume, tace'' na kasa, na kasa,jure rashin Ku, Ku gafar ce mu, Ku yafe mana abi sa abinda muka aikata Ku yafe mana"

Tana fada tana kuka, sai yanzu Binaif ya dago da kansa ya kalleta, ganin irin hawayen dake zuba a fuskar ta, yasa Shi tuno da tashi mahaifiyar, babu abinda yazo masa Rai Sai ko tana,
"Sona?"

Besan afiki ya fada ba, kuma Ummusalma taji Shi,batayi magana ba, sai Kara damke hannun ta datayi acikin nasa, sukuwa kasa hakurin Jin kukan ta sukayi hakan yasa suka rungume ta gam gam,suma suka saki kukan, Baffa ne ya tako barin Ummusalma ya sunkuya ya kamo hannun ta,

yace'' kiyi hakuri 'yata,am sorry,am so sorry,am sorry, am so sorry...

Haka kawai yake fada, kallan Shi tayi ta kalli Binaif ya daga Mata Kai, sannan yasake Mata hannun ya tashi ta fita, itama Amina fita tayi ta Basu wuri.

Sai da suka Gama komai,komai ya lafa, sannan Inni ta tambayi labarin su, Mas'ud tsab ya kwashe ya fada Mata komai, har haduwar su da ita, zuwa auren su ta da Binaif, sosai abin ya bawa Baffa da Inni mamaki, yaran su da suka bata lokaci daban daban sai gashi yau Allah ya hada su a Rana Daya kusan lokacin Daya, ikon Allah yafi karfin wasa,

Suna cikin wannan haka sai ga Daddy ya zo shida su Baba da Umma? da su Anty da mijin ta, sun shigo sosai Daddy yafi kowa nuna farin cikin Shi,? sai da aka nutsu Ummusalma ta juya taga Baya nan, Mas'ud Daya dawo kusa da ita Akan gado ta zungure Shi da kafar ta, kallan ta yayi irin meye?

? Da Ido ta masa alama yana ina?
Yace'' me kika ce?"

Tsaki taja ta tabo mus'ab ta masa alamar Yana ina?
Mus'ab tuni ya gane,
yace''? ya fita, ina gani shine ma ya Kira Daddy"

Tace'' to Kira min Shi, yunwa nake ji"

Tashi yayi ya fita, yana fita ya ganshi shida Amina a zaune suna hira, da'alama kuma ita keyin Rabin maganar, tafiya yayi zaije wuri Shi yaga Mas'ud yazo ya wuce Shi da gudu ya isa, Yana zuwa,

yace'' bb matar ka yunwa take ji fah, kuma naji ma Daddy yace kazo Ka dauke ta Ka maida ta gida Shi zai tafi da su Inni gida tare da mu"

Mus'ab ya karaso yace'' sai kace Kai aka aika"

Girgiza kai ya tashi ya tafi, Amina tace'' ba magana ko?"

Sai nan suka lura da ita, Mas'ud yace'' kut, twinny wallahi na canza wannan ce twinny na,Kai daman kafi kama da aljana"

Taske keyarsa yayi yace'' with respect har yanzu baka samu matar Ka ba"
Zama Mas'ud yayi yace'' Allah ya bawa yaya Mus'ab hakuri"

Tafiya yayi ya barshi a wurin, ya Shiga ciki,
A kusan tare suka Shiga shida Binaif, kansa a sunkuye ya Shiga babu Wanda ya lura dashi sai Baffa, wurin ta yaje ya zaune,

yace'' me zaki ci"

Tace'' kaje dakin da aka kwantar da uncle dakin na goma na ajje fruit Ka dauko min..."

Sai kuka tayi shiru, tuna wani Abu da tayi, kallan drip dinta tayi taga ya saura kadan,?
tace'' cire min"

Beyi musu ba, ya cire Mata, ta tashi zaune ta kalli mus'ab tace'' a Abuja wanne unguwa Ka zauna"

Yace'' gidan Daddy dake garki"

Murmushi tayi Mai kyau sannan tace" bb muje dakin yaya"

Kama ta yayi suka tashi, sannan suka fita, dakin suka je, Anna suka ga su ummu suna zaune Shi Baya nan, Zama tayi ummu ta kawo Mata Tasha ta dayawa sai da taji garau, tayi sallah sannan,

tace'' Ina mus'ab? "

Yusuf yace'' bezo ba, iya bb ne kuma shima ya tafi,kina sallah"

Tashi tayi ta hango su, su hudu har Binaif Shi Yana tsaye Yana waya sukuma a zaune Amina da Mas'ud sai zuba ake shikuma Mus'ab Yana binsu da Ido, wuce tayi Basu lura da ita ba, ta wuce male ward har wurin gadan su Muja,

Muja na ganin ta, ta taso ta tarbe ta, suka karasa, sai da ta zauna,
tace'' kuma Baki tsaya ba"

Muja tace'' Ina Zan tsaya kuwa"

Murmushi kawai Tama ta tace'' to shikenan,daman nazo duba ki ne, numbern ki fah"

Muja tace'' Banda waya sai dai numbern Abba na"

" Kash,kinga ban taho da waya ta ba"

" To muje mana, sai na sa maki,wayar Abban ma ma charge bare nace ki saka min Zan Kira ki"

Hakan ya mata dadi, fita suka yi daman ya samu yayi bacci, har suka zo wurin zasu wuce Basu lura da ita ba, a saitin wurin ta tsaya,

tace'' Glip Dan ban Aran wayar Ka"

Dayake amfani yake da ita ya kawai ya miko Mata ta, juyar da Kan da zaiyi kusa sukayi four eyes da Muja, Dan murmushi tayi

tace'' Ina wuni?"

Mas'ud yace'' lafiya qalau"

Shidai be amsa ba,Amma Yana kallan ta, ita kuwa,
tace'' kamar na Sanka,Amma na manta a'ina? "

Janye idan sa yayi, beyi Mata magana Dan besan me zai ce ba,

Ummusalma tace'' zaki iya sanin sa, Dan ya zauna a unguwar ku, a Abuja, haka yake magana bata dame Shi"

Murmushi tayi tace'' Kannan kine?"

Mas'ud ta kalla yarda ya wani wurgo mata harara a fakai ce, tasan da namiji ne yayi maganar sai ya maida masa da martani Amma sanin macece yasa yayi shiru sai boyayyiyar harara, murmushi tayi tace'' a'a yayu na ne, wannan ce kawai kauwata"

Ya fada tana nuna Amina,

Muja tace'' Allah sarki, sannu"

Amina tace'' ina? wuni,yi hakuri bamu gaisa ba"

"Bakomai"

Mika Mata tayi wayar tace'' Samin"

Amsa tayi tasa mata sannan tayi musu sallama ta wuce...

By: ```Hijjart Abdoul```
? ? Cwthrt =?? ? _Akanji magana_


? ??
? ? 53


Daki suka koma ita da Binaif suna Shiga sai ga Anty safiya tazo Dan su tafi gaba Daya ganin dakin ya cika da bakin fuska yasa ta gaida kowa suka gaisa,

Daddy yace'' ya kamata a samu aje a tafi haka nan ga Shi ana neman ayi la'asar"

Baba yace''gaskiya Kam, ya kamata a tafi"

Inni da Baffa dakin su suka koma sannan Baffa yaje yaga likita daga nan aka Basu takardar sallama, Baffa ne ya Kira Amina a wayar ta, tazo ta tattare kayan su sannan suka fito, kowa ya fito inda sukayi parking,

Daddy ya kalli Binaif yace'' Ka kaisu gida daga nan sai ku wuce gida Ku kuma"

Hakan akayi suka shiga, Baffa yashiga gaba su kuma a Baya, Su yusuf daman ba tare suka zo ba, kuma Basu San abinda ya faru ba sunma wuce tun da Dade wa, kowa Shiga yayi ya tafi,

Baffa na nuna masa hanya har suka je, unguwar su da bacirawa can ciki ce, har kofar gidan su, suka je, dukan su suka Shiga bayan yayi Parkinson, gida ne Karami na Mai kyau parlour Daya da two bedroom sai kitchen a waje, da 'yar bishaya Mai a tsakar gidan, Shiga sukayi suka zauna, Baffa da Binaif sukuma daki suka Shiga dan Inni ta huta tana bukatar hutu dukda tana cikin farin ciki,

Binaif yace'' Baffa kayi hakuri da duk abinda nayi maka,bamma san da bakin da zan Baka hakuri ba, ina Mai Baka hakuri nasan bai Zama lalle Ka yafe min ba, kuma zaka dauke marar..."

Baffa ne ya katse Shi ta hanyar cewa'' Baka da laifi, tabbas nine Mai laifi, kasan ma dadi naji? Kowanne uba yana so ya aurar da 'yar sa ga mijin da yake so, naji dadi sosai, wannan ya nuna kana son ta,ya nuna zaka iya kare ta, koda kuwa babu mu, daman babu mu din Ka aure ta kuma Ka zauna da ita,bansan me Zan maka ba, Yana suna Ka?"

Binaif yace'' Abdulshakur ko Binaif"

Murmushi Baffa yayi ya taso daga wurin sa, ya zauna a kujeran dake Binaif ya jingina, ya shafi kansa cikin kulawa, yace'' Kai ba siriki bane, kaji ko? Kai yarona ne, baka da banbanci da su, bansan sirikin nan kaji ko?"

Binaif ji yayi wata nutsuwa na Shigar Shi, gashi yarda yake shafa masa Kai,irin rarrashi a hankali ya zame ya kwanta a cinyar Baffa,

Baffa yace'' tell me more about you,and my children, mamanka ta rasu ne"

Yace'' Taya akayi san haka?"

" I can see, kayi rashin Uwa, kana son uwa, Naga wannan acikin idan Ka"

Kwalla ce ta taru da idan sa yace'' Baffa bansan ta ba,bansan sunan ta ba,ban taba ganin ta ba, but she's gone, ta tafi, I don't know ko tafiya tayi, ko kuma mutuwa tayi, but she's gone forever"

Shiru sukayi babu Wanda yayi magana, Saida ya natsu sannan,
yace'' Mas'ud ya fiye tsoka, Mus'ab kuma ya fiye hakuri"

Murmushi Baffa yayi yace'' Mas'ud tun Yana yaro haka yake,ga Dan Karen tsoro, shiyasa kullum suna fada da Ummusalma basa jituwa sam ita tsokana shima tsokana ga San girma me hali Baya fasa wa"

Murmushi Binaif yayi yace'' har yanzu basa jituwa, ga rashin hakuri haka itama"

Jin ana Kiran sallah yasa su tashi Dan gabatar da sallah, a waje sukayi alwala sannan suka tafi.

A daki kuwa Ummusalma a gata ga Inni haka suka kwanta, tana kallan tana? tambayar ta wasu abubuwan na rayuwar ta, a haka bacci yayi gaba da Inni ita kuwa kasa baccin tayi dan yunwa take ji, ji take kamar tayi amai Dan tsabar yunwa amma sai taji bakin ta yayi nauyi tace tana Jin yunwa a bata abinci, gashi Amina tana so tayi mata magana bata, bata dama ba bare ta saurare ta, a hankali ta tashi ta fita alwala tayi tayi sallah a parlour ta idar da sallah kenan,

Amina tace'' Salma"

Banza tayi mata, sai ma jingina tayi da kujera ta rufe ido, tana cigaba da tasbihin ta,

Amina tace'' Haba salma maganar ne bazaki min ba?"

Ummusalma tace'' na'am Neena, shikenan?"

" Ya kamata ace at least ki fada min abinda na maki "

"Mtsww"

Tashi tayi ta kwanta Akan kujera, zuciyar ta ta cigaba da tashi, su Baffa ne suka dawo gani su tayi tare su Mus'ab,
Mas'ud Yana shigowa ya zauna a kusa da Ummusalma,

yace'' dalla can tashi, ki koma gidan Ku,kin wani zo kin zauna mana a gida kowa ya tafi gidan su idan ba tsoro ba"

Baffa yace'' ai itama gidan su ne,sai dai Kai Ka tafi gidan Ku"

Binaif da ya zauna a wurin Kan ta,kamshin turaren kawai taji tasan shine, bude Ido tayi, tace masa "yunwa nake ji"

Dayake kallan ta yake yasan me ta fada, haka ma Amina, tashi tayi ta fita, ta daura abinci sannan ta fice,

Mus'ab yace'' Yawwa Baffa fada masa nan gidan mune"

Baffa yace'' Mas'ud bazaka taba girma ba,Naga ranar da Zaka girma Kai kuwa"

Binaif yace'' Ai Baffa ya kusa girma fa, shida zai yi aure nan da wata biyar?

Baffa yace'' ikon Allah, amma naji dadin wannan maganar sosai Mus'ab fa"

Mas'ud sunne kai akayi irin kunyar nan, besan kunyar tasa dariya take bawa mutane ba, abinka da ba'a Saba ba,

Baffa yace'' mus'ab fa"

Mus'ab sosai kai, yayi ya kalli Ummusalma ko zata yi magana,ita kuwa dauke Kan ta tayi, irin ba ruwan ta Kenan, sosai keya yayi,

yace'' inaga tare za'a hada"

Mas'ud yace'' inji uban wa? Baza'a hada biki nada Yara ba, Kai da budurwa ma Baka da ita,da kama iya zancen ?"

Baffa yace'' Mas'ud!"

Ai tuni ya tashi ya nufi kofa har Yana neman bigewa, ya fice,

Girgiza Kai kawai Baffa yayi, mus'ab yace'' to Baffa kadan Ka gani Indai wannan yaran ne"

Amina ce ta shigo tace'' Ya Mas'ud ya na ganka anan, azaune"

Yace'' kedai bari,leka min kika Baffa Yana nan?"

Shiga tayi taga Baya nan, hakan yasa ta juyo ta girgiza masa Kai, taso wa yayi ya shiga ya gan su suna hiran su Banda Ummusalma da idan ta yake a rufe tsab zaka ce bacci take, zuwa yayi ya zauna, Yana wani daure fuska,

Amina ajje coolern da ta shigo dashi tayi a gaban Ummusalma tace'' ki tashi kici, awara na siyo maki"

Bata tanka Mata ba, ta tashi ta sauko kasa, tare da cire Hijabin ta, ta zauna ta baje kafa tasa coolern a tsakani kafar ta, ta fara ci, gawani yaji Mai dadin gaske, data kawo Mata, gashi awaran da zafin fa Tasha kayan Hadi, ta fara ci tana zirawa,

Mas'ud yace'' Lalle ma Neena mu ina namu"

Dago Kai tayi ta kalli Binaif tace'' mi amor zaka ci?"

Murmushi yayi ya girgiza Mata Kai, yace'' kici ki koshi"

" Ke Neena wai ba Kiran ki nake ba"

Daga waje yaji tace'' Ina zuwa"

Mus'ab yace'' Lalle samun wuri, wai ni nayi kauwa"

" Oho de ba kauwar wani bace, twinny Dinna ce, Daman Ku Kala kuke da aljanu"

Ita de cin kayan ta take sai da ci tayi nak, ta cinye tas saura Daya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login