Showing 42001 words to 45000 words out of 173457 words

Chapter 15 - A BAKIN WAWA (AKANJI MAGANA) COMPLETE

30 Oct 2025

3955

password din,Naga menene acikinta nagaji da zaman jira sai yaushe ne wannan lokacin da zaiyi million ashirin wasa ce ne akace maki?
Daga nan kuma bataji me yace ba alamar ya gama wayar, sai taji kuma Yana wata wayar daban Yana bude wardrobe din,da turanci yake, Yana fadar yarda safe din take da iya adadin letters din da take dauke dashi,sai taji kuma Yana cewa yanzu de sai Friday zaka iso Kenan? Daga haka kuma sukayi sallama,ya rufe wardrobe din ya fita Amma be rufe dakin ba,alama ce ta nuna zai dawo,tana Jin ya rufe kofar parlourn yasata ta fito, ganin kofar a bude a zuciyar ta sauke tana mamakin ashe bai san password din ba,to ya akayi ita tasani, bata da wani lokacin tunanin mai tsayi yasata kawai bude safe din da tasan itace ta takardun data gani waccan ranar idan bazata manta ba,aikuwa tana budewa taga itace, takardune aciki dayawa,gabadaya ta kwaso su a hannunta ta ajje a kasa ta rufe safe din da wardrobe sannan ta kwashe su ta koma ta buya,Yana zuwa shikuma kawai ya dau abinda ya zai dauka Wanda shima yanzu yake Dan ajjesu abubuwa aciki sannan ya kulle wardrobe din ya janyo kofar ta fita Allah yasota bai rufe dakin ba,sai ta tabbatar da ya fita daga gidan gaba daya sannan itama ta fito ta hada zufa sosai, dakin ta bude ta fito, sai dai kofar parlourn a rufe ta batadamu ba ta bude window ta fice ta sauka kasa shima? ta window ta fita,sai da taje waje ne kuma ta Rasa da wacce kofar taza fita,Amma ganin kamar sakata ce kawai a kofar yasa ta budewa ta fita sai da tafi kuma tarasa yarda zatayi ta rufe,wayar ta lalubo ta Kira mai adaidaita shine yazo ya Shiga ya rufe sannan ya hauro katanga ya sauko, sannan ta sami wani relief,
?? Sauri kawai take taje taga menene acikin wannan uban takardun haka, har yanzu basu dawo ba,bakowa a gidan, direct garden ta nufa can ciki inda tasan ma masu gidan basa zuwa ta tafi da kujera, ta zauna ga wurin yama fi ko ina iska a garden din sobda yanayin bishiyon wurin ga sanyin ruwa,Zama tayi ta fito da takardun daga cikin hijibi,. Tunda ta shigo harabar gidan tana sauri yake ganinta, fitowa yayi don yaje yasameta ko yaji dadin abinda yake ji,kullum da tunanin yake kwana yake tashi tun ranar da ta sanar masa yake kasa bacci sai dai dayake bacci barawo shine yake sace Shi,ganin ta kadai yasashi jin nishadi ya manta da komai,hakan yasa Shi zuwa ya nemi shawararta kuma ya tambayeta,sai dai ganin inda ta dosa yasata shima bin bayanta, a Kan kujera ya ganta ta daura? takardu akan Dan dandamalin nan na flowers mai tsayi, tana dubawa daya bayan daya, a hankali shima ya taho Yana dubawa Dan tunda daga nesa yake? ganin kamar na company company haka, bata lura ba kuwa taga mutum yasa hannu ya dauki daya, Yana dubawa hannun kawai ta kalla tasan Mr lizard ne,kallo ya bita dashi kallan tuhuma, zaiyi magana amma baisan ma mezai ce ba,kuma wannan takardun original dinne na irin sun jima sosai sai dai kasancewar a ajiye suke yasa Basu ji jiki ba. Dakyar ya buda Baki,

yace' meyasa???
Please don Allah ki sanar dani ko ke Wacece ko Zan zamu salama please, ummussalma,

Katseshi tayi tace is Ummusalma not ummussalma ,
Sannan tacigaba

tace' suna nan Ummusalma mahmud ...

By: ```Hijjart Abdoul```
? ? Cwthrt=??: ? ?? _Akanji magana_


Not Edited
POST 2020
REPOST 2023



? ?? 16

Gefen takardun ya zauna sannan ya kalleta yace' Mahmud or Muhammad,

Bata bashi amsa ba taci gaba,

tace'. Ummusalma Mahmud, na kasancewa yarinya mai farin jini,walwala,fara'a, surutu,tsiwa,masifa,duk wani kalan rashinji,to na dame kowa na shanye, bana Jin magana koda kuwa ta iyaye na ne, ina da shekara uku? a ka haifi Sameera,sai dai tunda aka haifeta, duk wani Abu da zanyi a gida ba'a min magana a lokacin an sani a makaranta sai dai bana zuwa Islamiyya sai dai boko kawai, sai dai kuma bana san karatu kwatakwata wasa ya min yawa,ansha kawo karata daga makarata amma ko dan yatsa Abba baya daga min, bare kuma Mama, ahaka na taso a wani sangarce, ina da shekara shida aka haifi Yusuf tunda aka haifeshi kullum ina dakin,ina ganin yarda ake masa wanka, babu abinda nake so sama dashi,idan naga yana kuka to tsab zan masifen ce mai aiki ba ruwana daman Bana daga masu kafa,ahaka nake daukan sa tun ban iya ba har nazo na kwaya, makaranta kuwa daman sai naga dama, kuma Mama bata taba damuwa ba, ina da shekara bakwai ita kuma Sameera shekara hudu aka haifi yaseer sai yazamana bani da wani lokacin sai nasu,idan na dawo daga makarata ina tare da su a haka suka fara wayo tun ina karama nake masu wanka tun ina sa masu kumfa a ido a min magana na daina, amma da naci sai da na koya masu wanka, sai ya zamana da suka fara baki ni nake koya masu wakokin makaranta #children rhythms,? babu abinda na tsana Sama da karatu sana San karatu,Amma saboda su ne yasa na dan fara maida hankali sai naga ashe duk abinda Akayi ma ina iyawa,daga nan kuma sai na dena maida hankalin,a haka na taso ga wani uban kudi da ake bani ina kashewa koda kuwa ban da bukata, ra'ayimmu ya sha bambam da Sameera we are parallel da ita, idan ni nayi gabas to ita tayi yamma, Sameera tana da mutunta mutane,bata da wulakanci gata da San karatu,duk kankantar laifi idan tayi za'ayi mata fada, sabanin ni da ba'amin fada ko me nayi. A haka na taso cikin so da kauna, har na zo js3, lokacin school dimmu boys and girls ce, ina da friends Maza da Mata banda mu ba,kowa ma ni nawa ne,ina da harka da kowa bana ware kowa, ga kuma uban kudin da ake bani ina kashewa hakan yasa ake min taken big girl,? ? indai a school din kake to tabbas kasan big girl idan ma baka san ta ba to kana Jin labarinta. Ina js2 na matsa aka koya min mota, Abba beyi musu ba yasa driverna yake koya min har na kware, tsayi na baya kaiwa naga gaban mota to sai nayi ciko,ahaka na koya lokacin da na shigo js3 na kware abuna, duk weekend? ko Thursday and Friday ina dibar su Yusuf mu tafi yawo,
??
?? Wata Rana za'ayi birthday din Dan class dimmu,? kasancewar mazan class dimmu akwai sha'ani ba laifi, dukda cewan duk wani birthday idan za'ayi to a class ake yinsa, Amma shi sai yace ai baban sa ya yarda yayi a club, ni nafara cewa zanje, ganin ba Wanda yayi magana sai ni yasa nace" ya haka ku baza kuje bane?
Abinda sukace shine"' a gida za'a mana fada,
Nikuma nace" Naga sai da yamma basai muje har gidan naku ba kowa mu gayya to Shi ba?
Basu ce komai ba sukayi shiru,ana tashi daga school kuwa bayan na dauko su yusseer kasancewar haka nake ce masu banma Shiga da su gida ba,na fada bin gidajen kowannan mu ina fada,ba laifi kuwa duk an barsu.
Da yamma wasu suka biyo min muka tafi club,shine Karo na farko da na taba zuwa club wani wuri aka ware musamman saboda taron birthday dinshi, tun 5pm aka fara ba'a gama ba sai 12:30am a hakan ma bawai angama bane kawai gajiya nayi nace Zan tafi, tare da su sauran friends dimmu muka fito sosai munga abubuwa abinda bamu taba gani ba koda kuwa a film ne, bamu Kara tsinkewa da lamarin ba sai da muka fito waje ganin dahu yayi sosai kuma lokaci ya ja sosai muka tsorata idan anje gida me za'ayi mana ga goben zamu fara zana jarabawar mu ta BECE ni ce kadai kowa gida ban koma gida ba sai 2:30am, dukda na tsorata Amma na kasance mutum wacce bata nuna emotion dinta, a haka na Shiga gida,ina Shiga naga Abba da Mama a tunanina zasu min fada ko duka ma kamar yarda nake ji za'a zane wasu daga cikin mu daga bakin su, Mama

tace' Ah ah salama sai yanzu? Ya birthday din?

Abba kuma yace' ya kika tsaya gobe ma ki dawo duk lokacin da kike so, soyayyar mu a gareki ita ce komai kiyi duk abinda kike so koda kuwa zaki kwana ne bai dame mu ba kinji?

Wani dadi naji kasan ance kuruciya dangin hauka, jinayi duk duniya babu masu sona sama da iyaye na, da gudu na zo na rungume su nace"? nagode Abba na,
Yace' ai bakomai salama komai munayi ne saboda ke farin cikin ki shine namu farin cikin, ina kaunarki yata,

? ? Washegari danaje school friends dimmu wayanci an Zane su, musamman mata kowa yana fadar abinda aka masa suna cewa bazasu kara ba har abada,ganin irin kukan da suke sha da danasani yasa ni jan bakina nayi shiru bance uffan ba koda suka tambaye nace ni ba amun komai ba,daya daga cikin kawayen na tace' gaskiya iyayenki basa sanki,kikai wannan lokacin a waje kuma ko fada ba'a Miki ba? Anya su suka haifeki ?
Sosai mukayi fada da ita kaca kaca akan furucinta akan iyayena gani nake duk duniya babu wacce iyayenta suke so sama dani, dakyar aka raba mu da ita,
Tundaga ranar duk wani birthday da za'ayi ko a'ina ina zuwa bakuma na dawowa sai sanda naga dama,sai dai idan naje bana shan ko lemu ko cake din bana ci kawai rawa nake zuwa yi abuna.

? Abba Yana da company,idan na zauna nida shi na riga cewa kenan idan nagama makaranta zai bani company daya Nima nake aiki aciki,burina Kenan kawai na zauna a kujera nake juyawa,abinda nake so kenan tun ina karama, a lokacin yakan bani labarin wani abokinsa mai suna Muhammad dashi da Mama suna yawan bani labarin mutumin nan shine ya cucesu ya sace masu yar su sannan ya kashe masu 'ya'yan su,kafin ni sun haifi 'ya'ya uku amma duk Shi ke kashe su, tun daga nan naji na tsane shi, idan muka zauna basu da labarin da ya wuce nashi da irin muguntar da yayiwa Abba, koda na tambaye Shi nace yanzu yana ina ca

yace' Yana Abuja, gidan sa ne ya kama da wuta,
Ban wani tambaya ba sosai,a lokacin na tsani ma Jin labarin,na tsana yaudara da cin amana,karya gabadaya na tsane su.
? Ahaka na cigaba da zuwa makaranta ta da islamiyyan da ake min a gida dukda malamin yana hakuri dani idan yazo tun four to sai five ko six zan fito ina fitowa zance aya daya zai Kara min, lokacin banfi hizbi biyu ba da aya daya daya din da yake karamin, dukda malami na ne amma madam yake cemin bama shikadai ba kaf masu aikin gidan nan madam suke cemin idan kuwa basu fada ba to kayiwa aikinka korarka zanyi ba ruwana,ina da tausayi amma kuma Mama takance ba'ajin tausayin talaka,talaka bashi da mutunci,idan kayi masa rana to Shi dare zaiyi maka, sai ta kawo min misalin Wannan mutum mai suna Muhammad shima talakane, ya cuci Abba,da haka tayi tasiri akaina, na dena Jin tausayin wasu, amma ba duka ba idan na fita indai naga kana neman taimako to Zan baka shi.
Akwai watarana nakai yusseer park lokacin ina ss2 munje da su,suna fada da wani yaro suka tarar mai suka masa dukan tsiya sannan suka ji mai ciwo a gefen idan sa, ashe yaran dan dpo ne aikuwa babansa yazo yana zuwa kuwa yace sune suka ji masa dan zuwana kenan daga siyo ice cream bansan me yafaru ba kawai gani nayi za'a tafi da su yusseer aikuwa nace nice, aikuwa aka tafi damu har su,aka rufe ni aka Kira Abba sai ca yace' baya gari,Mama aka kirata itama tace' bata gari tare suka tafi da Abba kuma zasuyi sati ne a can,sai suka ce a mayar da su yusseer gida ni kuma a barni a cell,? sai da nayi sati biyu a cell sannan Abba yazo yayi bailing dina, yana ta ban hakuri,ko kallansa banyi ba,?? sai da ya fada min uzurin sa sosai sannan na yarda na hakura.Tun ina ss1 aka dawo dani makarantar nata kawai ni nace inaso saboda frienda dina wasu sun dawo ta,? zamushiga ss3 aka min repeating Amma bandamu ba na bisu na cigaba da karatuna tare su har akayi hutun Frist term...........


By: ```Hijjart Abdoul```
? ? ?? Cwthrt=?? ?? _Akanji magana_

Not Edited
POST 2020
REPOST 2023




? ? 17

?? Washegarin da akayi hutu shine ranar birthday na, mun fito don na kai su yusseer islamiyya,daga can na wuce nayi siyyayar abinda babu, naga Yayar Mama ko kallanta banyi ba saboda nuna min kiyayyar da takeyi karara, dukda bana haduwa da ita sai dai ta waya kawai, ko da muka fito sun? manta abincin su, sai nace Bari naje na dauko masu sai na bita kitchen harda hadawa da gudu don kar su makara, ina shiga sai naga ba abincin a kitchen na fito don naje dining sai dai Jin an ambaci sunana? yasani komawa da baya don naji me ake cewa, Yayar Mama ce,

tace' Wai ni? saratu wannan yarinyar ya batun ta ne?

Wacce yarinyar Kennan?

Ummusalma mana? nake nufi,

Awww Yaya Kenan ai mungama da shafin yarinyar nan, saboda kwata kwata mun lalata mata tarbiyar ta, mun cusa mata kiyayyar Mahaifin ta don tun bata Kai haka ba muka cusa Mata kiyayyar Shi, in takaice maki yanzu kusan? kullum sai ta fita birthday a club bata dawowa kuma sai kusan asuba, kinga kuwa babu wanda zai dora idan sa akan wannan budurwa? ya barta indai a club ne.

Yayar Mama tace' bangane ba taya kuka cusa mata Kiyayyar mahaifin ta meyasa kukayi haka?

Mama tace' hmmm yaya kenan, ai fada mata mukeyi irin cin amanar da mahaifin ta yayi wa Alhaji,ita fa a tunanin ta mu muka haifeta,alhali kuwa ko renonta banyi ba, idan wannan yarinyar ta kwanta acinyata ji nake kamar wani gagarumin karfen da aka sa shi a wuta haka nake ji,kawai zuciya ta nake dannewa don mu cimma burinmmu,

Yayar mama tace'?? yana ina ne shi mahaifinnata ko nace makiyin ta don kun gama komai, cusa kiyayyar d'a da mahaifi ba karamin Abu bane.

Wama yasani ne, 'ya'yan sa de kinsan ke kika fara wurgar da daya,kuma irin wulgawar da kika masa nasan ya rasa ransa, sai twins din da suka haifa sukuma nace a sace su daga makaranta a yi nesa dasu sannan aka masu kurciya, ashe ma Alhaji yasa a kashe su, ita kuma wannan sai mukaji tausayin ta akalla ma bar masu da daya ai, lokacin ma ai shekarar ta biyu sai muka dauke ta muka cinnawa gidan wuta daman already mun kwashe all important thing din, daga nan kuma sai muka dawo Kano, kinji fa yarda akayi, ai ke lokacin bakya nan kawai wutgar da waccan yaron da kika yi washegari kika tafi Cyprus shiyasa kuma ban fada maki ba,kuma bama samun lokaci sai yau.

Hehehe wallahi kun mun daidai, Nima haka nake gallazawa yayan mijina Amma yanzu ai basa nan yan uwansu sun kwashe su,kuma ko waiwayar su bayayi, hahahaha maganin dan banza, Amma fa naso Muhammadu Amma Allah beyi ba,

Ai da kin aure shi ma dayanzu komai ya dawo hannun mu,

Daban aure shi bama yanzu gashi komai ya dawo hannun ku,riba biyu Kenan,kun tarwatse tarbiyar yarsa kun hanata karatu, kuma kun kwace mata dukiya,

Mama tace' Yaya Kenan ni ba wanan ba so,yanzu tana ss3 kuma burinta be wuce a bata company daya ba, idan ta gama karatu kuma kinsan ko result dinta beyi kyau ba, dole a bata, ina gudun kar taje? ta gano wani abu da zai sa ta fara thinking otherwise,

Hmmmm wannan ai Abu mai sauki ne,kawai ku turata karatu kasar waje,kar ku waiwayeta daga nan kuma kunga shikenan kinga su a can karuwanci ba komai bane ba,idan taji bata da kudi dole ta fada wannan harka ai, don ta biyamawa kanta bukatar rayuwa daman kinga already ta Riga da ta lalace kinga shikenan, ko ya kika ce,

Yaya Kenan wannan shawara taki tayi daidai wallahi,haka za'ayi ma,Amma Zan bari ba yanzu ba sai tana gab da gamawa zanyiwa Alhaji maganar,

Kuma fa infada maki ko dangi bata sani ba,shima iyayensa Alhaji yaje ya hada masu tuggun sun hau sun yarda,bare ma kuma mun cinnawa gidan wuta,

Kai Kai wannan abu ya min dadi wato har iyayensu ma baku kyale ba Kai jama'a wai wai ai hakan yayi kyau wallahi,

Daga nan suka dauko maganar su kuma ta wani abun,

? ? ? Yanda na koma da baya ban San lokacin da na sulale ba a bayan kujeran dake kusan da kitchen,kukan ma nemansa nayi na rasa tunani ma kasawa nayi, Jin suna neman tashi don su daura abinci yasani rarrafawa na bi ta kitchen naje ni garden Bansan ma menake yiba,abinda nasani karshe shine zuwan su yusseer daga nan kuma bansan ma me yake faruwa ba sai gani na nayi a gadan asibiti, duk yarda akayi dani na fadi meke damuna kin fada nayi dan ko kallo basu isheni ba,tun daga wannan rana na sauya, na dauko damuwar duniya na daurawa kaina,kulluma muna kan hanyar zuwa asibiti har hawan jini ya kamani harta Kai ta kawo ko mikewa nayi don na tashi sai dai na fadi,yawan faduwar da nakeyi akace wataran stroke zai kamani,hakan yasan na dan rage damuwa sai dai tunanin yarda zanyi na gyara rayuwa ta danake dakuma samun mafita, a haka na sawa kaina salama sai dai bana fita ko ina daga daki sai daki abinci ma dena ci nayi nadawo cin snacks bansan me za'a samin a ciki ba watarana kuma, gashi ni ko gas ban iya kunnawa ba bare kuma ace na Shiga na dafa, ina zaune kamar ko yaushe a daki ina tunani aka zo aka sanar dani malamina yazo, kamar bazan jeba sai kuma na tuna illar da akamin har yanzu na kasa hada uzu biyu cikakke hizbi hudu Kenan, tashi nayi nasa Hijabi na fita, daman da Qur'anin shi yake kara min shi yake zuwa da komai yamin yakara gaba,Amma yau da naje nace yafara min ta Sama kuma shafi zai Kara min, tundaga nan yafara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login