Showing 105001 words to 108000 words out of 173457 words

Chapter 36 - A BAKIN WAWA (AKANJI MAGANA) COMPLETE

30 Oct 2025

3952

bayar,
Bata jira cewar su ba tayi gaba tayi shigewarta daki,

Khadija ce ta buda jug din batasan sanda wata uwar ashar ta fito ba daga bakinta ba tace bakin ruwa,ruwan fanfo, ruwan girki ruwan flower shita bawa 'yan uwan mijinta Bura uba ma,

Zai dawo ai zai hadu damu,ni ai yayar Shi ce Dan uban Shi dole yayi abinda nake so,

Ummusalma kuwa kiranshi tayi,kamar jira yake yadaga, shiru tayi shima shirun yayi,

yace' sai yanzu kika tashi?

Tace' uhm,uhm,

Yace' ohhh damba a kusa nake ba ko?

Tace' menayi?

Bakiyi komai ba,
Yace' kin tashi lafiya?

A,ah,

Subhanallah me ya faru ?

Ba Kaine ba?

Ni fah? Danayi me?

Kaine ka,..ka..Ka wannan,

Murmushi yayi ya jingina da kujeran da yake Kai,Yana shafa kansa,
yace' na me? Fadi ma?

Ka wannan fah uhm uhm Naga de,

Yace' shikenan tunda kinki fada,abinda za'ayi shine Bari nazo gidan sai ki fada ko?

Zan fada fah,

To inaji,

Daman fa kawai jikina ke min ciwo,

Ikon Allah sannu to,sai ina kuma?

Shiru tayi tana jinsa,Yana magana yarda yakeyi a hankali kamar ma baya so,bata San maganar ta ce ba tasa masa kasala,

yace' kin yi shiru,

Tace' idan zaka dawo Dan Allah Ka taho da ruwa,

Yace' Okay sai me kuma? Da magani ko?

Murtuke fuska tayi tace' um,um, dade cookies biscuit da chocolate,

Yace' to yarda kika ce haka za'ayi Mi Amor,
Adi?s,

Sai da ya kashe ta tuna bata ce masa sunyi Baki ba,tabe Baki tayi, ta Kira Maman Sadiq,

Maman Sadiq tace' kinji ni shiru ko?

Tace' a,a bakomai, kun dawo lafiya?

Maman Sadiq tace' lafiya qalau alhamdulilla, ina fatan wurin aikin naki normal de,

Murmushi tayi tace' Maman Sadiq Baki sani bako?

Mefa? Ai sai anfada min zan sani,

Tace' nafa yi aure,

Ke, auren gaske ko na wasa?

Dariya tayi tace' na gaske mana,daman ana auran wasa ne? Sai kinzo zaki ji,

Amma Dana fi kowa Murna, kuwa, yau ko gobe zaki ganni kuwa,

Daga dawowan ki?

shima Baya nan, kuma daman nace masa ai Zan fita gaida Yan uwansa kinga na biyo ai,

To shikenan Amma ba biyowa zakiyi ba, zuwana na musamman ne,

Dariya tayi tace' to shikenan yarda kika ce,
Sallama sukayi ta kashe,tana kashewa ana banko kofar,

Anty Mariya ce da Khadija suka zo,tana daga kwance tagan su,
Tace' lafiya?

Uwarki nace,

Khadija tace' ko baki jiba na Kara da ubanki,

Kallan uku saura kwata ta watsa masu
tace' Dan kunga ina rabuwa da Ku shine zakuyi ta zagar min uwa? Yanzu kuma harda uba? Taaab,
Ta juya ta cigaba da latsa waya,

Bata ankaraba suka fardota daga Kan gadan sai data bige sosai a hannu da kafa,dayake ta iya boye emotion dinta ko a fuska bata nuna ba, har suka kawo ta parlour suka sata a tsakiya wannan ya dungura wannan ya dungura, bata tanka masu ba, ita dai tana zaune a tsakiyar su tana Jin zagin debe albarka da suke bata, ko digon damuwa babu a fuskarta balle tayi musu kuka, kamar daga Sama sukaji ta zuduma uban ihun ta fara kuka ta kuma takure a gefen kujera,
????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? tace' Dan Allah Anty Mariya kuyi hakuri Dan Allah,kuyi hakuri,
Duk abinda ya faru cikin second din da beze wuce uku zuwa hudu ba Dan kifta ido sukayi suka ganta ahaka,

Ai kamar Kara masu tayi Khadija tace' shegiya to wallahi ko uban ki da uwarki sunyi kadan tsinanniya kawai,

Mabruka ta daga hannu zata zabga Mata Mari taji ita an zabga Mata wani lafiyayyan ajiyayyen mari, a fuska, a tare suka juyo ganin waye,

Anty Mariya tace' Binaif?

Yace' na'am Mariya,

Fuskar nan tayi jajur da ita ya Ciro ya waya ya Kira Daddy, ya fita sai da suka gaisa,

yace' Daddy kace su Mariya Kar su takara tako min kofar gida bare su shigo min cikin gida, meza sumin Bana bukatar su,

Daddy yace' 'yan uwanka ne fah, Binaif idan Basu zo ba waye zaizo ?

Yace' Daddy Yan uwa fa kace? Daman ina Dan Yan uwan da ya wuce Mas'ud da Mus'ab? Banda su, su kadai ne kawai Yan uwa na,

Daddy yace' Binaif me haka kake fada ne wai?

Tsabar bakin ciki har wani hawayen takaici yaji ya zubo masa,
yace' Daddy haduwa sukayi dukan su suna zagar min Mata,ba iya zagi ya tsaya ba harda duka,idan na fada maka bazaka yarda ba, nasani ai, idan ma Baka dau mataki ba akai ba,to ni Zan dauka, daman ai bansan suba,
Murmushi yayi yace' kodayake ni ba DAN SO bane ba kuma za'a soni ba, sani nasan da haka, Amma daga yau Daddy kasani wannan shine Karo na farko daman Dana taba fada maka Ka dau mataki wannan kuma shine Karo na karshe da Zan sake fada maka wani Abu daya dagance ni, Nagode Dad,
Dad kayi hakuri da abinda na fada Ka huta Lafiya,
Ya kashe wayar sa tare da goge hawayen sa, ya Shiga ciki, tanan yarda ya barta bata motsa ba sukuma sai zaginta suke,be tankawa Daya daga cikin su ba, yaje ya daga ta ya dauke ta cimak ya wuce dakin sa da ita.

Sakar Baki sukayi suna kallan sa, Zakiyya tace' shikenan angama da shi,an masa kulla kulla daman nasani ai ba'a banza ba, wallahi,

Shiru sukayi babu Wanda ya tanka Mata samun wurin sukayi suka zauna suan jiran fitowar su.

Aka gado ya ajjeta yafara goge Mata hawayen ta,
yace' kiyi hakuri kinji?
Murmushi tayi Mai kyau tace' bakomai ai, komai zai wuce,
A zuciyar ta tace komai zai wuce idan na koya masu hankali, zasu San sunyi da Ummusalma,

Murmushi yayi Mata ya zauna a kusa da ita ya tallafo kanta har suna Gogan hancin juna suna Jin numfashi juna,ita de kulle idanta tayi sabinin Shi dayake kallanta, dankwalin ta ma ya zame Mata Shi,muryan can ciki ciki,

yace' kin hakura?

Daga masa Kai tayi,
Murmushin mugunta yayi, don kawai ya mantar ta damuwar dake damunta,
yace' namaki magana kina daga min Kai ko? Dazu kince min uhm uhm, mekenan?

A hankali ta bude ido tayi sauri ta mayar ta kulle ganin irin kallan da yake mata,
tace' a,a fah,

A,a me?
Wai mema yake damun kine?

Nifa bakomai,

Bakomai?

Daga masa Kai tayi,

Wani murmushi yayi yace' laifi biyu, kinki kallo na kince na koma dodo, na biyu kince....

Ware ido tayi tace' a,ina? Yaushe na fada?

Yace' ya Zama uku,

Tace' wallahi bance ba,babu abinda nace,kawai kace wai nace,

Yace' naji wannan,

Yarda fah?

Ahhh shima ai,naji na kasa yarda?
Yace' yawwa jikin yadena ciwo ko?

Har ta daga Kai,tayi sauri tace' ehh ya jimama da denawa ai, kwantar da ita yayi ya bi shima ya kwanta ya Dora kan sa a kirginta ya rungume ta kamar yarda take masa, ya kuma Kara Dora Mata kafa ya kanainayeta
yace' Tunde jikin ya dena ciwo yau akwai new harka, what I mean,basai na fada ba, kin gane,

Tace' ni wallahi bangane ba,

Daman haka nake so karki gane, Amma kina so ki gane?

Daga masa Kai tayi da sauri tace' eh,eh,

Kamshin jikinta gabadaya yasa masa kasala,har wani gyara kwanciya yake, shiru yayi itama tayi shiru ganin fa ita take cutuwa,

tace' Ka dagani, zafi,ciwo,

Banza yayi da ita,sai ma Kara gyara kansa da yayi,
Tace' Ka daga ni, ciwo fah,

Yace' kedawa kike magana,haka?

Dakai mana,

Yace' a,a bade Dani ba,

Tace' Haba Mai gida,Ka daga ni mana Allah da zafi gashi kaki kwanciya daidai,

Yace' ina haka kike min kema?

A,ah de,kaji ma an Kira sallah Ka tashi Ka tafi,daman Baka taba zuwa ba,

Yace' bakomai ai bansan wurin ba shiyasa,
Amma to da kike cewa na daga ki ciwo da zafi,idan har kin nuna min wurin Zan daga, idan ba'a nuna ba kuma nacigaba da kwanciya,
Yafada tare da gyara kwanciyar sa, a jikinta,

To kada gani Zan fada,

Dariya yayi yace' yarinya Kenan sai da na bushe anan gidan duniya sannan kikazo,Dan haka ba wannan zancen,

Wayyo kadaga ni, to, Allah zafi, kuma wani iri nakeji ba.....
Sai tayi shiru bata karasa ba,

Dago kansa yayi ya kalleta, ganin yarda take wani juya kai a Kan pillow idanta a rufe,ta Shi zaune yayi ya Dora hannunsa a Kai irin besani din nan ba,

yace' to ai Naga meye kike juyi da Kai irin dadin ko?

Hannunsa zata cire ya rike hannun
yace' babu wannan zancen, dorawa hannu fa kawai Nayi shima hannun zafi?

Daga Kai tayi, tan lumshe Ido, wannan ai cuta ce, matsawa yayi yace' daga Kai ko?

Bude Ido tayi ta tashi zaune tace' Allah da zafi kawai Kai sai kayi ta wannan kayi ta wannan nidai a,a,

Sauka tayi tace' nidai Sallah zanyi, da Ido ya bita sai da ta Shiga toilet ya kwanta ya lumshe Ido

yace' zakiyi bayani, wasan yara akayi,bakin ki garau ba, hmmm.
Yana kwance ta fito daure da towel ta yafa wani akai, tasowa yayi,
yace' meye na wanka kuma? Kuma ni Banji kamshin soap ba, kuma Naga de babu abinda akayi,

Turbune fuska tayi tace' zafi naji fah,shine kawai na kora ruwa,

Zafin ne harda su Kai kuma?

To mene na tambayar wai?
Ta daure fuska kamar ba yanzu zatayi kuka ba,

Yace' Ana aasfi ya Madam,

Shima ya shiga, yayi wanka lokacin tasa jallabiyar da wacce tasa da asuba, ta tayar da sallah shima goge ruwan jikin sa yayi ya tayar da sallah, sai da suka idar yace Yana zuwa ya fita,

Yana fita yagan su a parlour ya daure fuska
yace' Mariya Ki kwashe iyalanki Ku barmin gida,koda wasa koda wasa koda wasa wallahi kada Ku Kara tako min koda kofar gate din nane, Idan ba haka ba,hmmmm duk abinda na maku ku kuka sani,

Tace' Binaif ni yayarka kake fadawa haka? Kasan me matarka ta mana kuwa?

Yace' kome ta maku kuka sani, abinda na gani kuma nasan zaku aikata dashi Nayi amfani ku tafi nace,kafin kuga Yara Ku da Ku kanku a titi,

Khadija tace' lalle dole kace haka mana, banza mijin tace Ku tashi mu tafi aikin banza a hofi kawai,

Sun tashi hae sunje bakin kofa yace' kuma wannan abincin da yaranku suka ci fah? Sweetheart ce taci da zan kwashe ko kuma 'ya'yan Ku?

Habiba ce ta dawo tace' Ai kasan bamu san kitchen din ma shiyasa, yace' sai Allah yayi nasan ku da sa'ido ko a kwashe cikin salama ko kuma de....hmmmm ya koma ya barsu a tsaye a wurin sunyi shiru, Habiba ce ta kwashe sannan suka tafi.


Bayan sun gama waya ya jima Yana juya maganar Binaif me Kenan?.. ?? _Akanji magana_

??
??
? ? 38

Ya Rasa yarda zaiyi? Yasan Yana San Binaif,Baya so yake nuna son sa,yanzu ma Daya aka Kaya??
Shiru yayi Yana tuna abinda yace masa yanzu,dole ya dau mataki kafin yazo yayi wani abun.
Har lokacin meeting din su na jam iya Yana nan Yana tunanin mafita, sai da yamma ya nufo gida.



Kwankwa sawa suke babu sararawa, yusuf dake cikin mota me yake inba dariya ba, addu'ah ma yake Allah yasa Kar a bude,

Yaseer yace' wannan amarya? ina, bata hadu ba,

Ummu tace' Ina kuwa ta hadu tazo ta rufe gida ko wayace Mata ana rufe gidan Amarya?

Yaseer yace' cigaba da kwankwa Sawa,Bari ma asa dutsi yarda zata ji,

Dutsi suka dauko suke yi, sukeyi shiru, tsayawa sukayi Dan hutawa, Ummu tace' Allah ya so mu ma yamma ce da tuni ta shanya mu,

Yaseer yace' so take ta looser sweet da chocolate,

Ummu tace' mu kuma mu looser Alkhaki?

Dariya sukayi, yace' nifa najima banci ba,

Tace' Nima haka,

Kamar daga Sama sukaji ance, ku gyara a bude maku,

Juyowa sukayi a tare suka ce Yaya?

Murmushi yayi yace' to ku matsa, bazata ji ba tana can ciki,

Bude masu yayi yace' ina Yayan naku,

Yaseer yace' Ka ganshi can a mota, yayi parking a kofar gidan can wai Dan kar ace tare muke,

Murmushi yayi yace' Bari na bude masa gate sai ya shigo da motar jeka ce masa ya shigo,

Zuwa yayi ya fada masa shikuma ya bude gate din, Ummu ta hau kan Dan step din dake kofar parlourn ta tsaya shima yaseer zuwa yayi ya tsaya
yace' kinga gidan nan harda wurin yin ball? Zakiyi ?

Tace' daga zuwan mu ko? Sai an nuna halin,

Yace' kuma basa bawa zamuyi da matar ba? Kinga sai muke zuwa,

Tace' kaima kasan hakan bazai faruba,kasan yayan Fati ne kuma yusuf bazai zo ba,

Zaiyi magana yayi shiru sabida ganin su da yayi sun taho, karasowa Yayi ya bude musu gidan suka shiga wani kamshin dadi sukaji su Duka sai da suka ja ajiyar zuciya daman daga makaranta suke,sun gaji sai sukaji daman su kwanta su huta,

Yace' ku zauna bari na Mata magana,

Zama sukayi Ummu da yaseer a kujera Daya shikuma babba aka a one seater aka wani kame? Yana latsa waya, Ummu ta matsa kusa da yaseer cikin Dan rada rada,

tace'? Dan Allah gidan nan be maka kyau ba?

Shima cikin rada radar ya Mata magana,
yace' nifa duk field din yafi min kyau,zamu ke zuwa da weekend Muna buga game ko?

zatayi magana yusuf yace' dalla malamai kuyiwa mutene shiru,kunzo gidan mutane kuna masu gulm, kude baza Ku canza ba,kun girma Baku san kun girma ba,

Hada sukayi zasu kwashe da dariya sai kuma aka gimtse aka kowa ya matsa, Yana Dan kunshe dariyar sa,?

Yusuf yace' Munafikai, kamar na Allah,
Basuyi magana ba suka kyale Shi.

A daki Yana Shiga ya ganta ta kwanta inda tayi sallah, ta fara bacci, zuwa yayi yada gata yace' ba'asan baccin yamma fah,

Turbune fuska tayi tace' to bakai bane, kaje Ka zauna?

Yace' to naji,nadena Zama,gaisawa mukayi da mutane da najini masallaci kuma sai muka an taba hira, shine na taho,?

Yace' ba wannan ba kinyi Baki,

Tace' Nayi Baki ko munyi Baki?

A,a wannan bakin na naki,kuma na musamman ne, sannan ni na kawo su, wanne tukuici za'a Bani,

Murmushi tayi tace' Zan Baka wani special Abu, Mai kama da.... Guess what?

Kallanta yake yarda take murmushi yasan na mugunta ne, tashi yayi yace' Bari naje na sallame su tou,

Tace' a,ah Zan Baka fah,

Yace' ai Naga kamar wani mugunta za'a ban shiyasa,

Murmushi tayi ta tashi tace' Bari naje ni nagansu ko lemun ba Baka siyo ba kuma nace Ka siyo,

Riko hannunta yayi yace' ahaka zaki fita? Kallan kanta tayi ganin jallabiyar sa, tace' to ai Banda Kaya,

Yace' Zan ara maki, wata Riga Amma fa ina one condition,

Tace' eh inaji kaga mun bar su a parlour suna jira kuma na dadi,

Sakinta yayi yaje ya dauko Mata wata doguwar Riga Mai Dan Karen kyau,veil din ta ne kawai karami,

Karba tayi tace' wow tayi kyau,

Beyi magana ba ya bata ya fita, ita ma a gurguje ta zura rigar ta yafa Dan veil din, rigar cib ita,kuma ta Mata kyau fita kitchen tayi ta taga kayan an ajje wasu a Sama wasu a kasa ga Katan na lemu da ruwa da fruit,

Tace' Ashe ya siyo kayan Amma be fada ba, yabarni Nayi bacci, lemun kawai ta dauka da fruit ta wanke tasa 'yar karamar wuka akai, ta dauko masu snacks dayawa ta daura Akan babban tray ta fito parlourn tana dosuwa tafara jin gabanta na faduwa haka kawai, da murmushi a fuskarta tayi sallama bayan ta karaso bata kalle ko Daya daga cikin suba sabanin su da sallamar ta sukaji suka juwa Banda Yusuf dayake Danna waya Suma ganin kwakwaf ne yasa su juyawar sai kuma suka kame,
Sai da ta ajje sannan ta dago da ganta sukayi four eyes da yaseer dake kallanta juyawa gefen yusuf tayi shima ta kalle Shi,ta juyo ta kalli ummu ta kalli Binaif dake musu murmushi, dakyar bakinta ya iya furta

yusseer??

A sukwane yusuf ya dago yaganta,tashi zaune yayi yace' Yaya? Salama? You?

Girgiza masa Kai tayi hawaye na zubowa daga idanta shima kukan ya fara yaseer ya guje ya taho ya rungume ta gam,shima yusuf zuwa yayi ya rungume ta saura kadan ma su Fadi tare Allah ya tsare, kuka suke su Duka dakyar ta samu karfin hugging back,tana shafa kansu babu abinda take tunawa sai sanda suna Yara da suke rungume ta,
Breaking hug din tayi,tana goge hawayen masu hawaye tace' ya isa haka yusseer is enough,
Suma hawayen suke goge Mata, murmushi tayi masu taje ta zaunar su a Kan kujera ta Shiga tsakiyar su,
Ta kalli Binaif tace' a,ina kuka hadu?

Yace' a kofa nagansu,

Ummu tace' zuwa mukayi fah, anan unguwar muke,

Yusuf ya dalla Mata harara yace kunzo kwadayi de,

Yaseer yace' ehh din anzo kwadayin kuma sai muka tarar da wani abu Mai ban mamaki,

Murmushi tayi tana Jin wani farin ciki har cikin zuciyar ta,

Yusuf yace' Yaya,Amma meyasa? Meyasa Baki dawo ba? Meyasa yaya? Yanzu da mun manta ki fah? Kina ganin yin nesa da gida shine solution? Ehh yaya?

Kwalla ce ta zubo Mata tace' yusuf bazaka gane ba, ba....

Tashi yayi ya tsaye cikin fada fada da daga murya yace' mene ban gane ba? Kina tunanin bamu San komai ba? Kome kike so kice?

Tace' yusuf,

Yaya enough please,Nafa sa Jin dalilinki na kin komawa gida, tunda yanzu gani gaki, Amma kisani ko kin koma ko Baki komaba har yanzu ana bibiyarki, har yanzu Abba be manta kiba, infada maki wani Abu ma, Abba Nemanki yake ruwa a jallo, kinsan inda ya ganki?
A park,store unguwa,

Daga ita har Binaif saranda sukayi suna kallanshi bata taba sannin ya ganta ba, mekenan? Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un,

Yaseer yace' yaya,
Sai kuma yayi shiru yana kuka, itama kukan take, Binaif ne ya taso ya dawo kusa da ita ya rungumota jikin sa Yana shafa bayanta,

yace' komai yazo karshe,idan ma bezo ba ya kusa zuwa karshe, komai ya kare Insha Allah,

Yusuf yace' Haka kuke gani Amma be zoba,yanzu aka fara wasan,
Yace' Abba next week Monday zai Kai karar ka koto cewan kaje kayi amfani da takardun bogi kace yasai da maka da company Alhali besan anyi ba,Bama ya gari, sannan kuma ya maka wani mugun sharri Ka Shiga gidan sa kamasa data Ka sace takardun mallakin sa, gaba ki daya,

Dagowa kusa da yaseer ya zauna, yace' ahakan ne komai yazo karshe?

Sai yanzu tunanin Binaif ya kawo masa abinda take nufi da safe,sai yanzu yasan I a ta dosa, tabbas yarda ya fada ne komai yazo karshe.
Wani shegen murmushi yayi na gefen Baki,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login