Showing 147001 words to 150000 words out of 173457 words

Chapter 50 - A BAKIN WAWA (AKANJI MAGANA) COMPLETE

30 Oct 2025

3936

nawa.

Zansu yayi suka Shiga ciki, Umma na zaune ita kadai tana kallo, abin ta,

Tace'' sai yanzu zaku dawo?"

Binaif yace'' wani abun farin ciki ne ya same mu Dan Allah yau karki yi fada kinji Umma"

"Jarababbiya Ka maida ni Ashe bansani ba Ka kyauta"

Binaif yace'' ai idan ana neman masiffiya an same ki"

Cokalin abinci ta dauka ta wurga masa tace'' Dan zakaraw'a kai yanzu zaka cewa Safiya jarababbiya ne? Ka rena ni, gidan nan Zan Bari bazan zauna ba"

Tabe Baki yayi yace'' Dade yafi dan Bana so daman ki zauna yaran su koyi fadan ki, kinga Baban su Mas'ud yau muka hadu da su da maman su"

"Alhamdulilla, Alhamdulilla, Alhamdulilla, Allah Kaine abin godiya, taya hakan ta faru?"

Binaif tsab ya bata labari, Umma tace'' Kai kaga, Abu sai kace almara, Ikon Allah Kenan, azo a kaini Naga Iyayen 'yan albarka"

"Haba Umma da Daren nan? Ai sun rufe gida yanzu"

"Allah ya kaimu gobe"

Mas'ud yace'' bb banga Ka Shiga daki ba"

Mus'ab yace'' bafa ta nan"

Umma tace'' ahaf ina zai Shiga daki ba mata Ashe shiyasa bata dawo ba tana nac wurin Iyayen ta hakan ma yayi kyau ai"

Banza yayi dasu ya koma doguwar kujera ya kwanta ya rufe idan sa, Yana Jin su suna masa tsiya ya kyale su, a haka bacci ya dauke Shi yasan idan yaje daki ma ba bacci zaiyi ba, har suka Yana kwance a parlour ranar nan yayi bacci.


Washegari da safe suka tafi gidan Baffa har Umma sai da aka daura auren ummu sannan su Baffa suka wuce Umma ta koma gidan ta, Daddy kuma ana daura aure ya wuce airport ya tafi Adamawa sunyi murbab zuwan sa sosai shine yake fada masu auren da aka yi da kuma samun Iyayen su sosai hakan yasa su murna,be wani jima ba ya dawo, kasancewar tafiyar jirgi ce befi mintoci ba yasa yayi sauri,

Matan sa ya gani a zaune suna hira tare da 'ya'yan su guda hudu, ya kallo yaran kawai girgiza Kai,

yace'' Ku same ni a Sama"

Ya wuce dakin sa, sai da yayi wanka ya shirya ya fito ganin su da yayi a parlourn sa ga kuma abinci, ya zauna ya dauki remote ya fara zanja channel sai da ya Kai labarai tukun,

yace'' Mas'ud da Mus'ab Wanda suke gida nan ada kafin su koma gidan Umma nasan da cewa kune kuke aika ta komai..."


By: ```Hijjart Abdoul```
? ? Cwthrt =?? ?? _Akanji magana_

??
? ??
? ? ? 55

Shiru yayi tunawa da wani abu da yayi mafu soyuwa a zuciyar Shi, kafin ya lumshe Ido ya bude.

Hajiya kuwa da Anty Rasa abin fada suka yi ji kawai suji ya gama abinda zai fada su fadi nasu.

Yace ''Hafsat, Zuwaira nasan duk wani kallu kullan Ku, a yanzu ni tsoro kuke Bani, sabida haka ga wannan kowa yaje yayi business din sa da yake so kowa ya kama gaban sa".

Ya fada Yana Mika masu wata envelope mai kyau da ita, har zuciyar su suka ji wannan Batu jiki na rawa Hajiya ta amsa ta dauki nata ta bawa Anty.
Anty harda durkusa wa ta fara godiya itama Hajiya haka.

Hajiya tace ''Alhaji mun gode sosai Allah ya Kara budu".

Anty tace "Allah yasa kaci wannan takarar deputy governor din da kake nema".

Dariya suke bashi sosai, dukda Baya san yayi amma sai da yayi murmushi ya.

Yace ''Idan zaku tafi, ku tafi Ku kadai kubar min yara na".

Hajiya tace ''Haba Alhaji Muda zamu tafi business wasu kasashen saro Kaya taya zamu tafi da yara kuma?"

Anty tace ''su mana me? Su ba Yara ba ba komai ba?"

Murmushi kawai yayi ya Basu wurin ya tashi ya fita yana Dariyan shi shika dai.

Anty tace ''kinga Bari naje yanzu yanzu na duba Naga wanne jirgi ne zai tashi da kudin wuri na nayi booking".

Hajiya tace "tuni ma da me zamu kira kuma tashi zamuyi ai da kudin mu zamu saro kayan ma wannan kuma sai mu ajje sai mun dawo".

Anty tace ''china zani nikam".

"Ahh ni Dubai zani".

Fitowa sukayi kowa ya Shiga daki yayi booking flight Hajiya ita da yamma ta samu,ita kuma Anty sai gobe shima sai taje Abuja. Dayake Hajiya sai sunje Abuja sai kawai? Anty tace zata bita.

('('('('('('('


Suna zaune su Duka a gidan Umma, bayan sun dawo daga daurin auren Ummu,

Ummusalma tace ''yanzu Umma ai da kin koma mun tafi tare".

Umma tace ''ke rabani da gidan da babu rahama babu iska ko kadan, babu wurin shakar numfashi window an kama an garke, labule an sake Shi daki ba Hasken Rana sai na lantar ki, bazan iya ba ga gida na kana waiga wa zaka ji iska, ka fita waje Ka bishoyo nan, idan naci gaba da Zama a can gawa ta kawai za'a dauko".

Mas'ud yace ''hmmm Umma Kenan ai kinga gidan nan takaici ne a cikin Shi fal, damma ba'ayi haki ba kinan nida da nake da Asthma kullum sai ta tashi".

Binaif yace ''kun dame ni fa".

"A tashi a tafi daman banne mi mutum ba sai da aka ga na gyara gidan nawa sannan za'a ce wani abu".

"Matata ta gyara de".

"Muna Mata de, ai wannan ba matar arziki bace".

"Matar tsiya ce Kenan ko?''

"Oho de, ace har yanzu? ba amo ba labarin samun ciki yanzu da a watan da akayi aure a watan ake samun ciki amma banda ita ko nace banda ku ehh nannan wata wacce akayi auren Ku tare a? kauye ciki ne da ita wata hudu zuwa biyar har ya dan tasa abin ta abin sha'awa da ita baku ganta ba wallahi".

Mas'ud yayi karaf yace ''zaki sha mamaki Hajjaju idan nayi aure, ke dai bari sai 'ya'ya sun yi wayo sun girma da wayon sa tukun zasu haifi na fari ai idan nayi aure za'a..."

A tare Mus'ab da Binaif suka jefe Shi Mus'ab da pillow Binaif da remote.

Mus'ab yace ''wai sai yaushe kunya zata ishe Ka ne? Ayi yaro bashi da kunya Sam, Kai da ko nema auren har yanzu ba'aje ba kayi ta cika Baki".

Umma tace "ohh! Dan ya Fadi gaskiya? Shine abu? Gaskiya ya fada ai idan bata yi ciki yanzu ba sai yaushe zata yi? Ku nan zaune kuna kunbiya-kunbiya zai haihu ya barku".

Ummusalma tace "kasan de sarai wani ya raga Ka idan ka manta na tuna fatan Ka Allah yasa a Baka kake wani cika baki".

Kalar tausayi yayi ya zame ya kwanta.

Mus'ab yace ''dayafi de".

Umma tace ''kwaji dashi Insha Allahu babu Wanda ya riga shi 'yan bakin ciki".

Binaif yace''Kunga ku tashi mu tafi ba zai iyuba kawai ayi ta zagina da mutunci na da komai".

"Kufi ruwa gudu kuma koda wasa kar a zo min gida".

Tashi yayi ya fita, ita Ummusalma sallama tayi Mata,

tace ''Umma sai anjima".

"Mu jima da yawa har auren 'yan albarka".

Itade tafiya tayi, shima mus'ab tashi yayi ya Mata sallama haka ma Mas'ud suka tafi suna tafiya Mai aikin ta na zuwa Allahn da ya te make ta taya ta hira.

A hanya suna tafiya, Ummusalma tace ''bama je gai she da Daddy ba?"

Mas'ud yace "Bana San zuwa gidan nan nikam".

"Sabida akwai dodannika ba?"

"Dalla can yimin shiru, nasa dake? Bansa da mutum ba ya dena samin Baki a zance na Bana ciki da renin wayo".

"Hmmm haka de za'ayi auren kenan,? thanks God nawa jarumi ne".

"Oho de ke kika sani".

Mus'ab ne ya matso kusa dashi cikin rada.
yace, ''magana fa ta fada maka".

Shima cikin radar yace, ''me tace?"

"Tana nufin wai idan akayi auran babu abinda zaka iya Kenan idan ana yiwa matar Ka wani abu kaga ita nata jarumi ne, tana nufin Kai rago ne ai".

Da karfi Yace, "Kan bala'i wato Dan munafinci yanzu zancen ya koma cikin nadi Kenan bakomai Zan Rama".

Binaif yace, ''mun san wannan word din sai a canza wata as usual sai dai Ka rame".

Turo Baki yayi ya fara gunguni Shi kadai, Yana Mita, har suka je gidan Daddy a bakin gate suka yi parking sannan suka shiga, cikin gidan.

Suna zaune su Duka hudun kowa da waya a hannun sa Banda Fati wacce? take karatu da sallama suka Shiga ko daga Kai Basu yi sun kalle su ba bare su amsa sallamar, saida suka Samu wuri kowa ya zauna.

Binaif yace "Baku ji anyi sallama ba ? Ko kuma iya amsawa ne baku iya ba?"

Sai da ya fada sannan suka dago suka kalli su ganin su tare da Ummusalma wacce take Danna wayar ta bata dago ta kalle su ba suka kalli su Mus'ab da Mas'ud a tare suka ja wani wawan tsaki, sannan.

Saima tace, "ai munga anzo da karuwa ne shiyasa, taya za'a mu ansa sallamar karuwar da ko sallah batayi ita da arba babu banbanci Dan bazan ce Christans ba sai dai arna arnan ma kafirai cikin su".

Ameera tace, ''abin takaici wai karuwa ce ta dake mu fah ko?"

Aneesa tace, ''ai watan cin uwar su ne ya kama tsautsayi ne ya kawo ta cikin gidan nan shima Binaif din ba tsoran sa ake ji ba 'ya Tama na rashin kunya wallahi mu balla ta a gun nan".

Fati de bata ce komai ba, Dan iskancin ta tana da tsoro shiyasa ma ta tashi sum sum ta bar wurin.

Binaif kuwa jira kawai yake su gama duk Wanda yayi magana idan sa ne yake komawa kan sa har yazo wurin fati ya zaci zata yi magana sai yaga ta fita. So calm ya tashi ya nufi remote ya dauko ya tsaya yana Yana kallo ganin channel din da suke kallo Boom tv ta waka kawai, yasa Shi yayi murmushi ya Kara volume ya karade gidan, remote din TV ya hango a tsakiyar Saima da Ameera a Kan hannun kujera hakan yasa ya nufi wurin Yana zuwa ya Basu aune ba Dan Basu yi tsammani ganin sa ba ya Gwara kan su, Aneesa da tana magana tasa earphone sai wani karkade kai take sai Jin saukar sani lafiyayyan Mari tayi.

Duk abinda ya faru befi a cikin seconds ba, gaba dayan su gigice sukayi sun ma Rasa me zasu yi gudu wa ko kuma a kasin haka, kasa ya jawo su ya rinka ball dasu idan yayi ball dasu sai sun ture kujera a cikin lokaci kankani sun har gutsa parlour dan dansa yayi masifar baci kana gani zaka sa dukan da ya jima yana Tarawa ne be shi ba ya bude fridge ya dauko kankarori ya jawo su saitin goshin su ya rinka fasa wa akai ihu suke amma ba'a ji bare asan me suke yi sai da ya Kai ihun ma basa iyawa bare suyi azamar gudu wa ganin sunyi lakwas yasa Ummusalma kallan Mas'ud dake kusa da ita.

Tace "kaje Ka taimake su mana".

Alama ya Mata na Bana ji da hannu ya cigaba da kallan sa Yana gyada Kai, haushi ne ya ishe ta tama Rasa me zata yi kawai ta dungure masa kyeya ya juya ta kalli mus'ab da yasa earphone a kunnan sa ya kwanta Yana Danna waya, tsaki tayi ta tashi taje wurin Shi, rasa me zatayi ta Hana Shi dukan su tayi Shi kansa ya hada zufa ba kadan ba, samun kanta tayi da rungume Shi ta baya tare da hannun sa ta daura kanta a bayan sa tana sauke numfashi.

Runtse Ido yayi ya tsaya da dukan nasu Yana nishi, sai da ya dan saitu sannan ya juyo da ita ya rungume ta sosai kamar zai balla ta, ita rungume Shi din tayi sosai kamar yarda ya Mata, kansa ya kwantar a kafadar ta Yana Jin kamshin turaren ta Wanda a kullum yake Kara sa shi nutsuwa. Sai da ya daidaita sannan nemi remote yaja ta kujera suka zauna, rage volume din yayi sosai sannan ya canza channel,? ya kalle su yarda suke wani tankwashe wa tsabar radadin da azaba kukan ma ya dena zubowa.

Yace, ''inaga biyo Ku zanyi na janyo Ku".

Bashiri suka nemi tashi sai dai ko rabin daga wa ma Basu yi ba, haka ma rarrafe kin yi yayi, sai da tafiyar miciji suja isa wurin shi. Dauke yayi? Yana kallan Ummusalma ya nuna musu ita.

yace ''kunga wannan, Mata ce".

Dagowa yayi ya kalle su yace ''kinsan abind yasa na deke Ku?''

Girgiza Kai sukayi alamar a'a.

"I think dukan be isheku ba kuna nema Kari".

Dasauri suka ce "a,a bamu Santa ba".

"Daga yau Anty,daga yau me?"

"Anty". Suka fada a tare murya can kasa.

"Oohh daga murya zanke yi Kenan ko?"

"A'a".

"Daga yau babu reni a tsakanin Ku da ita babu a tsakanin Ku da Mas'ud Mus'ab babu wannan respect nake so na fara gani kunji ko baku ji ba".

"Munji". Wannan Karan da karfi suka fada.

Daddy yana waje daga Baya Yana Jin disco na tashi yazo Dan musu magana ganin irin dukan da Binaif yake musu yasa Shi ya koma da baya sai yaji kidan ya Ragu sannan ya nufo cikin gidan, a gaban Binaif ya gansu ga parlour an har gutsa sai ya samu kujera ya zauna.

yace, ''Ku kuma duk rawar ce haka kome kunzo kunyi zube a kasa sai kace Wanda aka dake ku gashi kun bata mana parlour lafiya?"

Saima da ta Dan tashi tace, " bakomai Daddy laifi mukayi aka hukun ta mu".

Yace, "Ku tashi Ku gyara parlour nan".

Babu zan cen musu suka tashi suka fara gyara wa dakyar suke aikin Dan sun jigata ba karya.

Gaida Daddy suka yi ya amsa musu Yana tsokanar su, sun jima sosai a gidan tare da Daddy sune har aka Kira la'asar sannan suka tafi.

A mota Ummusalma tace, "ina San na zama ta farko da Zan fadawa Yaya auren sa da Ummu".

"Idan kin isa na make ni zan fada".

"Sai Ka fada mugani ai".

"Ni daman an hada harda ke an zabga Dana ji dadi".

Binaif yace, " idan Baka kiyaye ni ranka zai Baci".

Mus'ab yace, "Gwara tun wuri kayi shiru kafin kaima a Baka naka kasan, don Naga bb idan Yana Duka manta a'ina yake".

"Fav idan aka min wannan dukan ba tabbatar bazan tashi ba woo Kai kaga duka? Daman bb haka kake bamu sani ba taaabb".

"Ai ni babu ruwa na yanzu da Shiga harkar bb".

"Nima de kuwa amma bazan ce wannan aljanar Anty ba a haife ta a gaba na nace Mata Anty ita ko Dan yayan nan bata ce min".

Banza tayi dasu ta kyalesu, Hiran suma suke da Binaif har suka isa asibiti suna zuwa.
Mas'ud ya fita haka ita ma suka bar su Mus'ab a Baya...


By: ```Hijjart Abdoul```
? ?? Cwthrt =??A BAKIN WAWA ?? _Akanji magana_



? ? ?? 56



Har wani sauri yake yi yaga ta wuce ta, Yana gaba tana bayan sa har suka isa dakin a kusan tare suka shiga suna Shiga suka ga su Yusuf a dakin Shi kuma Yana kwance yana kallan su suna fa Hiran su Banda Ummu Dan ca tace baza ta zo ba.

Mas'ud murya kasa kasa yace,? "kun fada masa?"

Yaseer yace, "a'a Ummun ce tace Kar a fada".

Wuri ya samu ya zauna ita kuma Ummusalma fita tayi ta Kira ummu a waya Jin abin da suka ce, tana daga wa.

tace, "me yasa kika ce kar a fada masa?"

Ummu daga can tana kwance a daki haka nan taji yau duk jikin ta yayi sanyi ga wata irin kunyar Uncle da take ji ta Rasa dalili tasan su Baba da Abie ba fada masa zasu yi ba tunda Binaif ne ya ruki da a daura din sun zaci zai fada koma ya fada.

Tace, "yaya salama fa kunya nake ji shiyasa".

Murmushi tayi har hakora ya fito dimple din ta ya loma.
tace, "yanzu de? idan Anty zata barki to ki fito asibiti ki taho min da abinci da freshyo".

"To Allah yasa ta barni idan nazo zan kira ki sai ki shigo Dani".

Murmushi tayi tace, "to sai kinzo".

Juyo wa tayi da murmushi a fuskar ta sosai kana gani zaka san abin ya bata dariya amma maimakon tayi sai take yin wannan murmushin, kicibus suka yi dashi yana tsaye Yana kallan ta ba wayar ta ta yake ba kawai kallan ta yake ta yarda ta Kara masa kyau da fari na musamman.

Daga masa gira Daya tayi tace, "kallan fa?"

Murmushi yayi Yana sa hannun sa a dimple din ta yace, "I miss you".

Ya fada Yana wani lumshe ido,cire hannun sa tayi tace, "kaga asibiti fa muke zake tabani salan wasu su fara thinking otherwise".

"And so?"

"Hmmm let's go".

Hannun ta ya kama suka Shiga ciki ganin su sun tare a wuri daya suna ta hira yasa suka karasa wurin gadan ya zaunar ta shikuma yaje ya tashi Mas'ud ya dauki kujera daya ya koma kusa da Shi ya zauna.

Ummusalma tace, "kunzo kun wani tare kuna damun marar lafiya haka ake zuwa dubiyar su Chatty harda tafa hannu sannu tou".

"Ai daman ni kika Rena ga marenin wayon ki duk wurin nan ki rasa Wanda zaki Kira sunan sa sai ni, Bari de Nayi aure nan duk Wanda Baya respect dina bazai je gidan na ba".

Binaif yace, "wai gidan nan nawa ne da Kai ne? Gidan har yanzu be kare bane ayi ta fada ayi ta fada abar Shi haka mana".

Turo Baki yayi yace, "daman ai Ka kwace min kujera kuma kake fadar haka dole ai wallahi bakomai zaku gani ai idan anyi auren".

"Chatty Allah ya shirya min kai".

"Ji 'yar renin hankali? Sai kace ita ce babba hmmm".

Mus'ab yace, "dude rabu da su kawai let's continue".

Ummusalma ta kalli uncle taga wani annuri a kwance a fuskar sa Yana murmushi kawai Yana kallan su kana gani zaka san kawai yana cikin annash wa da murna.

Tace, "Yaya kana San ummu?"

Kallan sa ya dawo dashi kanta.
yace, ''me yasa kika ce haka?"

"Yaya please kana San ta?"

"Ina san ta mana she's part of me ada nazaci kawai son Da da uba nake mata by the time nasan komai nasan ba hakan bane amma nasan ummu will not marry me because am not..."

Binaif ne ya katse Shi ta hanyar cewa, ''idan kuma itama tana san Ka fa?"

Kallan Shi ya dawo Kan Binaif, Binaif ya daga masa Kai.

yace, "yes".

Tace, "ehh ummu loves you too,kade na? kawo komai a ranka ummu na Sanka sosai kuma Ka yarda dani and kasan wani abu?"

Girgiza kan sa yayi alamar a'a.

Tace, "Yanzu fa Kai na Ummu ne Ummu taka ce".

"Bangane ba? Me kike so ki fada ne haka?"

Binaif yace, "abinda Ka gane Kenan yau aka daura muku aure da Ummu.

Tace, "sabida tana sanka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login