Showing 39001 words to 42000 words out of 173457 words

Chapter 14 - A BAKIN WAWA (AKANJI MAGANA) COMPLETE

30 Oct 2025

4039

Abu,tun suna magana suna tambayar suwaye har suka dena magana.
??
? ? Basu tashi tashi ba sai shida da rabi na safe yaseer ne yafara bude ido, ganinsa a saban wuri yasa Shi bude ido da kyau, daki ne dan madaidai ci,da gado shima gadan bawani babba bane ba sai kuma mirrorn da bakomai akai, dakinde yayi kyau daidai misali Amma idan aka hada da nasu to ko rabin kwatar nasu beyi ba,ga Shi komai na cikin sa sabo ne,kamar de dakin amarya, dakyar ya tashi ya jingina da gadan da yake Kai, ya kuma lumshe ido ya bude a hankali kuma ya fara tuno abinda ya faru har zuwa lokacin da aka Shaka masu abu, yusuf ya kalla yaga yarda yake motsi, alamar Yana son ya tashi, yajima Yana motsi daga bisani ya tashi zaune ganin ba dakinsu ba yasashi kallan yaseer kamar yarda shima yaseer din kallansa yake,daganan kuma ya karewa dakin kallan tsab, har ya tuno abinda ya faru dasu, kofar da yagani yasa Shi ya nufa, toilet ne sai dai dan karami ne toilet din compare to nasu, babu bathtub sai rariya kawai, sai toilet sit, saidai dukda kasancewar sa karami toilet din ya masa kyau Jin wani kamshi Yana tashi, Ahaka yayi abinda zaiyi ya fito, shima yaseer Saida yagama karewa komai kallo Sannan ya fito, carpet din dakin akai sukayi sallah,

Yaseer yace' ko me muka musu da zasu sato mu? Ko yanka mu za'ayi ne?

Wani irin kallan baka da hankali yusuf ya masa yace' da yanka mu za'ayi akace maka za'a barmu muyi sallah ne? Ko akace maka zamuyi magana?
Kawai Sato mu akayi,kamar yarda ake satar mutane,

Yaseer yace' ina wayar ka? Mu Kira Abba yazo da police a fitar da mu,

Sai a sannan ya tuna yana da waya, aljihunsa ya duba amma babu daman three quarter ne a jikinsu da shirt,to a aljihun yasaka kuma babu,alama Kenan sun dauke ta, yusuf

yace' yanzu ya zamuyi?
Nima bansani ba, yaseer ya fada,

Zama sukayi sukayi su kayi shiru kowa da abinda yake sakawa,su mamaki ma suke wai su aka sato sai kace wasu kananan yara, abin mamaki, suna nan har karfe 10 basu motsa ba, Rasa ma abin yi sukayi gashi windown ba irin casu bane wannan harda wani karfe ajikin sa, dakin kuma ba komai bare su samu su banbare karfen su gudu,to Idan ma sun fita daga dakin sun san yanda wajan yake ne?

Knocking din da akayi yasa su tashi a zabure suna kallan kofa,? wani ne yazo hannunsa rike da kaya niki-niki, ya ajje Yana kallansu,Zama yayi a bakin gadan sannan,

yace' da kunyi hakuri kun zauna,ba abinda zamu muku kawai de abinda muke so daku shine hadin kai zaku bamu, idan mun samu abinda muke so zaku tafi cikin sauki, idan kuma kukayi mana gardama kuma kuke kokarin guduwa to kusan cewa daukar rai bakomai bane a wurin mu, kashe mutum har lahira bamu dauke Shi komai ba, kuma ba mutuwar sauki muke ba,Idan mun muku mutuwar sauki ai kunji dadi bamu muku azabar Wanda yake kokarin guduwa ba, abinda nake nufi shine,idan zamu kashe mutum to yau zamu yanka masa kafa an jima mu yanki fatar sa anjima mu yanka Shi,tsantsar azaba ce zata sa mutum mutuwa, kuma bamu da imani,
? Ya karashe Yana zaro wata zarbebiyar wuka sai kyalli take don sun gano fuskar su ta jikin wukar, tunda ya fara kuma suke zare ido tashin hankalin su basu San? wanne irin hadin Kai yake nufi ba, ga kuma zancen mutuwa da suka ji ana ambata, da irin azaba idan sukeyi laifi su kashe mutum, Basu Kara Shiga tashin hankali ba sai da ya zaro wannan wukar,da kana gani kasan yanka daya ne naman ka ya fita, Basu ankaraba suka ji yana,

cewa'" idan baku yarda ba da hadin Kan da zaku bayar yanzu nan zan kashe ku,kisa mafi sauki a wuri na,
Yafada yana tashi tare da matsowa inda suke,ai kuwa suma suka fara matsawa yana matsowa suna matsawa,ganin ya daga wuka zai fille masu Kai a tare,yasa su cewa,mun yarda fa mun yarda wallahi, Allah mun yarda wallahi, acikin lokaci kankani suka hada uwar zufa sunga mutuwa yaseer harda guntun fitsarinsa a wando, Yana ganin kuwa ya ajje wukar ya arta a guje a don Shiga bayi,

Yace' yawwa good boys Ashe kuna San ranku haka, yanzu kuke kirana da Oga kunji ai,
Kamar kadangare? yusuf yake daga masa Kai yana hadiyar yawu,dakyar gashi ya makure ajikin lungun bango, ya durkusa,

Yace' kuma inaso ku kwantar da hankalin ku kamar kuna gida, ga Kaya nan na kawo maku idan kuna bukatar wani abu kuyi knocking kofa zanji zan zo,ga abinci na kawo maku kuci ku koshi kunji ko?
Bai jira amsar suba ya maida wukarsa yayi gaba, yaseer yana Jin ya fita shima ya fito, ya zube a gado,vl basu da wata mafita face su bashi hadin kai dari bisa dari yaseer ya fada Yana suke ajiyar zuciyar a akai akai, shi kuwa yusuf baima iya bashi amsa ba saboda yanda yaji kansa wani iri kawai haskowa yake an fille masa Kan nan da yanzu ya farka ido yaji ana cewa man rabbuka, taaab lalle ne abinda yake gani a film ashe anayi a gaske,wuyansa ya shafo ya ji,ya sannan ya sauke wata ajiyar zuciyar da baitaba yi ba tunda uwarshi ta kawo Shi duniya, daga bisani ya zame ya kwanta, basu san iya adadin da suka kwashe ahaka ba,Amma Jin ana kiran sallah yasa ya tabbatar musu da Azahar ce tayi, yaseer ne ya fara tashi ya bude ledan Kaya ne sosai dayawa sai ledan abinci, kayan ya fitar ya gani sosai kayane masu? kyau kusan? Duka iri daya ne har colour.

Sai dai wasu ban bancin colour din, kwashe kayan yayi ya zuba su a cikin wardrobe din dakin duka kayan kanana ne, sai singlet da boxers Suma duka wayanci iri daya ne, bai wani shirya su ba kawai, sai wata leda da gani itama,zazzage ta yi ganin su brush Maclean ne da kayan amfani yasa yakai toilet cikin karamin cupboard din da yagani yasa Shi zubawa,daga nan yayi wankan sa tare da alwala da brush ya fito, shima Yusuf ganin yaseer ya dan kwantar da hankalinsa yasa Shi kwantar da nashi hankalin
Sai da sukayi sallah sannan suka ci abinci gudun kar suje yunwa ta masu illa. Daga nan kuma aka fada tunanin gida, babu wacce suke ji irin ummu, yau?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? zata shiga makaranta ko a,a.
Bama sajin mama akan yanda suke jin ummu daga nan kuma suka gangara tunanin yaya, sun san ta zuba ido ta gansu amma shiru. Suna nan har la'asar suka tashi sukayi wanka,aka kawo masu abinci suka ci, har dare yayi, oga ne yace su fito su zauna a parlourn zasu tattauna, suna fitowa kuwa sukayi arba da kattai manya manya, a daddare suka samu wuri suka zauna,ganin haka yasa ogan sake masu sosai yayi wasa dasu yayi ta jansu da hira saida yaga sun sake amma ba can ba sannan ya fada masu abinda yake so, su duk a tunanin su wani mugun aikin ne,amma dukda haka basu ji dadi ba sai dai tunda zasu iya abarsu sukoma da ransu kuma a sake su to yafi komai dadi.


Mama na zaune a parlour ita a tunanin ta su yusuf sun fita tun jimawa,ganin yanzu har goma tayi kuma tasan suna da school . Itama yau batajin zata fita Sameera ce ta fito ga dukkan alamu baccin be ishe taba, da kayan bacci a jikinta ta sauko, Zama tayi,

tace' mama yunwa nake ji,

Mama tace' to saidai ki tashi ki girka don,na bayarwa masu aiki,kuma kila sun tafi dashi,
tashi tayi badan tana so ba,saidai don ba yanda zatayi, indomie ta girka ta fito,tana cikin ci sai ga Ummu nan tazo da sallama ta shigo har kasa ta durgusa ta gaida mama ta gaida Sameera,

tace' Mama su Yusuf fa? Nakira wayan yusuf a kashe shikuma yaseer baya picking ince dai lafiya gashi kuma muna shirin makara.

Mama tace' a,ah daman wai basu tafi ba ? Nifa zataci tun tuni sun tafi,jeki ki duba,

Tashi tayi ta nufi dakin,yanda suka barshi ahaka ta same Shi, wayan yaseer akan gado ga missed calls dinta nan rututu, dubawa tayi part din nasu Basu ba alamar su, nan fa ta fito ta fadawa Mama sosai hankalin mama ya tashi,Sameera

tace'? jiya dana sauko don Shan ruwa wurin shadaya saura nagansu suna rigayen fita na zaci ma wurinki zasu zo,

Ummu tace' wanne wuri na kuma da daddare haka?
Mama bata tsaya Jin ba'asi ba ta fita waje wurin mai gadi,

yace' ai Hajiya Bansan sun fita ba sai karar bude gate danaji ko da na fito har sun tafi sun bar gate a bude nama zaci wani ne ba lafiya shiyasa,

Aikuwa ta fara surfa masa ruwan bala'i wani abinmma batasan tana fada ba,dakyar su ummu sukayi controlling dinta suka maida ta ciki,waya ta dauka ta kira Abba ta fada masa, bai? wani dade ba ya karaso, sosai shima hankalin sa ya tashi kafin kace me gari ya karade ana neman yaran 'ya'yan M & M da U & U,? sai? dai babu su babu labarinsu, babu kuma wani evidence da suka bari ko kadan ba, kuma ma dadin dadawa har motar aka dauke, a iya bincike Yan sanda sunce sai dai idan barin garin sukayi tunda gashi ko me irin kalar motar su babu, dajin haka? kuwa yan jarida suka fara tambayoyi akan me zai saka su gudu? Shin me aka musu zasu gudu su bar garin, batare da ansani ba? Abba dukda yasan an sanshi a gari Amma baizaci haka kowa yasanshi ba infact baimasa cewan ansan yana da yaya ba sai da wannan abu ya faru, Idan hankalinsa yayi dubu to ya tashi yarasa inda zai sa ransa yaji sanyi.
? ? Yana daki aana kwance yaji wayarsa tayi kara alamar shigowar sako, kamar bazai daga ba sai kuma yadago ko labarin 'ya'yan sa ne sai dai abinda ke rubuce a jikin message din ya fi ma batan 'ya'yan nasa tada masa da hankali, zufa ce take karyo masa ta ko ina babbar rigar dake jikinsa ta jike sharkaf da gumi, Ya karanta sakon yafi a kirga, bawani Abu bane da sakon Amma Shi a ganin sa wani abu ne, Mamace ta shigo ta ganshi da kuma waya a hannunsa batayi magana ba ta karbi wayar ta ga abinda ke jiki,

tace'. Alhaji banga komai a cikin wayar nan ba dazaka kara tada hankalin Ka,

Kallanta yake irin bakisan me kike fada ba, kallanta yayi na kallan Baki da hankali kallo na ma'anoni daban daban bema San ya fassara kallanta ba,gani yake ma idan ya bata amsa Yana da lokacinta,
Ganin kallan ya ki karewa ne ya sata,

tace' haba Alhajina yanzu me aka rubuta a jikin wannan Abun? Abinda ya dace shine mu nemo 'ya'yan mu daga baya sai mu nemo wannan,nasan wanda ya sace su to tabbas shine zai turo wannan sakon, mene na tashin hankali kuma?
Shi baimayi wannan tunanin ba tabbas ya yarda da ake cewa mace tana da hikima kalakala amma ake cewa sune masa karamar kwakwalwa,dukda haka dai bayarda yayi ba don shi wani tunanin ya dauko Wanda yasa ita bata kawo Shi a ranta ba,kuma bazai fada mata ba har sai ya tabbatar da gaskiyar lamarin.
Beyi mata magana ba ya cire babbar rigar ya tashi ya shiga bayi, wanka yayi ya fito ya shirya ya kuma fita,? don jin labarin ko an Samu wani abun kuma, sai dai har dare babu su babu labarin su.
Mama kuwa idan ta kwanta to batasani ba don ko shingida batayi ba abinda take cewa kawai shine yaranta ina suke? ( Sai kace Wanda akace Mata an San inda suke anki fada ).

('('('('('('('

? Tana komawa gida tun daga bakin gate ta saki wata uwar Kara sai da yasa kowa ya fito tana karasowa kuwa parlourn ta zube tana kuka, tana cewa an sace su an sace su shikenan an yanka su,sun mutu, sai da Anty ta tsawatar mata tukunna tayi musu bayani, tana gamawa kuwa ta kuma zubewa tana kuka, daga karshe ma hotunan su ta rungume a kirjinta a haka tayi bacci, sallah kawai yake tada ita daga inda take tana parlourn a rakube kallo daya zaka Mata ta baka tausayi sosai. ( Allah sarki ummu).


Yau ta tashi cikin wani irin farim ciki dukda fuskarta tana nan kamar kullum ba fara'a amma ita a yarda take ji wani irin dadi da nishadi ne yake kwasarta, batasan dalili ba, musamman idan ta tuna Mr lizard ( Binaif), akan abinda ya faru jiya,sai ta samu kanta da murmushi ga kuma su yusseer wanda basu zo ba a jiyan, a haka ta gama aikinta taje taci abinci tayi wanka, koda ta fito gidan bakowa tsit yake, lokacin har sha biyu tayi kasancewar yau bata tashi da wuri ba, kitchen ta shiga ta daura abinci ta dauko silalliyar kaza ta daura ta don ta narke ta soya,tunda tazo ake cin dafaffiyar kaza yau kam ko suna so ko basa su sai sun ci soyayyiya tunda ita tana so, sai da tayi ta soya ta, ta bade ta da yaji, ta dauki na dauka ta rufe sauran a flask, Naman rago ta dauko ta wanke ta daura,tuwo ma zasu ci yau.
Sosai tayi tuwon semo da miyar kubewa bushshiya Tasha manja da nama, Saida ta gama ta kuma gyara kitchen din, bude Fridge tayi ta dauko lemo mai sanyi ta dauko namanta ta fito bakin kitchen din da kofar dakinta tasa takalmi ta baje tana cin nama tana korawa da lemo tsabar dadi har wani lumshe ido take irin yaushe rabo, zuwan shi kenan don yasanar da ita abinda ke faruwa ganin wani sinadarin farin ciki a tare da ita yasa Shi tsayawa Yana doubting ya fada mata ne ko mar ya fada, gashi yanzu sai cigiyar yaran ake, tunda yazo ta lura dashi amma tayi kamar ma bata ganshi ba, karaso wa yayi ya tsaya akanta,dago Kai tayi ta kalleshi, ta maida kanta ga naman da take ci,kujera ya dauko ya zauna yana kallanta, tashi tayi ta Shiga kitchen bata jima ba sai gata tafito dauke da kwano a hannunta tuwo ta zubo masa da naman da ta soya, beyi musu ba ya karba, ta zauna ta cigaba da ci, shima sauka yayi daga kujerar ya zauna a kasan tiles din wurin ya nade kafa yafara zirawa,sosai yaci Saida ta lura ya kusa koshi,

tace' inaji meke tafe da Kai?

Sosai yayi mamakinta, Kenan tasan da magana a bakinshi,? sai da yacinye tuwon tas ya kai kayan kitchen ya dawo ya zauna

yace' bansan ta ina xan fara ba ai, cewa zanyi an sace Kannan ki ko ya zance?

Kallanshi tayi tace to me Zan masu don an sace su sai me??
Ni zaka fadawa kome ko kuma nice ubansu kaje can ka fadawa babansu amma nani ba,
Dukda cewa ahankali take magana amma sai yaga kamar ranta ya baci daya fada mata din dan yayi wani iri bacin rai yake hangowa karara a tare da ita, tashin da tayi zata Shiga dakinta ya sashi saurin riko hannunta a sukwane ta juyo zatayi magana ya riga ta

Yace' meyasa? Meyasa zakiyi haka? Why?? Fada maki nayi fah don kisan halin da ake ciki amma shine zaki min haka?
Bata Kula Shi ba tace' menace ma game da rike mun hannu?
Sakinta yayi ta wuce ta tafi ta barshi a tsaye ,ya rasa yazaiyi da ita yana so su Saba kodan tarin tambayoyin dake kansa ya sauke mata su.
Tana Shiga ta kwanta a katifa tana tunanin. Tana Jin? ya tafi? tazo ta kwashe plate, wanke kayan da suka bata tayi,ta koma bata Kara fitowa ba gudun kar su Kara haduwa dashi, tana Jin yan gidan suna mitar tuwon da tayi Amma bata fito bama bare a zagi iyayenda bata san su ba.
? ?


? ? ? Washegari da yamma ta shirya ta fito kasancewar Yan gidan basa nan ta lura jiya da yau basu zauna a gida ba, kuma Basu dawo da wuriba,hakan yasa itama kulle dakinta ta fita,tana fitowa taga mai adaidaitar ta fada masa inda zai kaita tayi, tana masa kwantance har kofar gate din, cewa tayi ya jirata tana fitowa ta tura gate din,a bude kuwa yake, sai dai ganin mota da tayi a wurin yasata tunanin tabbas zuwa akayi shiyasa ma taji gate din a bude, zuwa tayi wani lungu ta makale tayiwa mai adaidaita message cewar ya jirata a bakin layin, sannan ta dauko wata Nokia key pad tayi message,ta mayarda ita cikin jakar ta,lallabawa tayi ta Shiga gidan,kallan gidan take tamkar batayi rayuwa acikin sa ba,wani irin tsanar gidan take ji Yana taso mata,dukda ba mutane Amma yana samun gyara akai akai, Jin motsin tafiya yasata saurin buya a dining wurin wani dan lungu ta makale, leko da kanta tayi taganshi yana saukowa, yakara kiba da fari,kana ganinsa zaka san Yana cikin daula da kwanciyar hankali sai dai kuma daga jiya zuwa yau ya zabge ya rame, kallansa takeyi tana tuna abubuwa da dama,Jin ya kusa saukowa yasata saurin Kara labewa har ya sauko ya fita,Yana fita kuwa ta tattare hijabinta da wani iri gudu ta haye sama dakinshi ta Shiga don taga dalilin zuwanshi gidan da suka tashi suka Bari batare da sun zuba yan haya ko sun saida gidan ba, dakin sa ta Shiga sai dai bakomai a dakin hakan yasa ta fito ta Shiga dayan,Yana nan yarda tasan Shi banbamcin kawai ansake? wardrobe ne, Shiga tayi ta bude taga wannan safe din zata bude Kenan taji Yana waya ashe be tafi ba, wani dokawa kirjinta yayi,cikin sauri ta shige bayan wardrobe din data ganin wani dan space, Allah ya taimake ta bata da kiba, shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya a hankali,tare da numfashi, ji tayi Yana,

cewa' yanzu million ashirin fa zan Kai, akan yaran nan million ashirin fa,ba yarda za'ayi a kama Wanda yasace ne??
Bataji me ake cewa ba Amma tasan da Mama yake waya, jitayi yace' kinga ni ina? tsohun gidan mu duk abinda za'ayi saidai ayi don kira zanyi ayi hacking din wannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login