Showing 81001 words to 84000 words out of 173457 words

Chapter 28 - A BAKIN WAWA (AKANJI MAGANA) COMPLETE

30 Oct 2025

3941

ita, sannan ta nuna masa dakin,
Shiga yayi parlour har yayi Dan Kura danma wai ba sanyi ake ba, kofar kusa dashi ya bude yaga kitchen ya bude na opposite yaga toilet ne,sai ya bude na gaban Shi daki ne na tarkacen su, Wanda yake opposite dashi ya bude yaga dakinsu Shiga yayi yafara duba abu sai dai babu koda? Paper dayane sai hotanta, wayar yaseer ya daya gani akan gado yasashi dauka ganin ya kunna yaga bata kawo ba alamar akashe take,? a aljihunsa yasa ya fita, Basu dawo bakuwa Saida ya juna a charge sannan ya fita yin sallahn Isha sai da yaci abinci ya koshi yayi kallo zuwa 9:30 ya tashi ya kashe kallon ya dauki mukullin motar dayagani a Parlour yaje ya daukk Atm dinshi sannan ya fice zuwa store Dan siyo kayan bukata.

('('('('('('('

A wani store yayi parking yace' bazaki fito ba?

Tura Baki tayi gaba tace' ice cream,

Yace' idan Baki fito ba to bazan siyo ba,

Kara tunzura Baki tayi tare da kumbura Baki murmushi yayi,
yace' da'alama de kinsan Abu nan ma dazu ko? Mai dadin nan?

Kallanshi tayi tace'wanne Abu Kenan? Meye mai dadin?

Kawo kunnanki kiji rada Mata wani Abu yayi ai bashiri ta bude kofa ta fice tana murmushi Tama Riga shi Shiga store din sabida haka sai tayi hanyar ta, shima da yazo sai yayi hanyar Shi tana cikin tafiya taji tayi gware da Abu dago Kan da zatayi sukayi four eyes da uncle Baki bude take kallanshi kamar yarda shima yake kallanta, murmushi karfin hali yayi

yace' can I have your contact please?
Yafada yana Mika Mata wayar Shi,wayar tabi da kallo sannan ta karba tasaka masa, murmushi yayi yace' thank you,
Sannan yace' Ummu ta Shiga damuwa saboda rashin bestie dinga am I mean Yusuf da yaseer, bayan sun so su nemeki amma Allah beyi ba Sai kaddara ta Riga fata,
Yace' idan bazaki damu ba inasan zamuyi wata magana,
Duk maganar da yake a sanyaye yake yinta Kala kalar tausayi, a yarda ta lura ma kamar Yana cikin damuwa damuwa mai wuyar fassara wa,

Kasa magana tayi tsabar ta Zama speechless batasan haka Abu yake ba bata san zata cutar da Ummu ba da batayi ba,? wayarta ta daga ta Kira Binaif amma bedaga ba, maybe wayan na mota har ya wuce ta da sauri ta sha gabanshi tace' baka kirani ba,

Murmushi yayi yasan gudun kar ayi ta ta ta da ummu ne shiyasa tace haka, kiranta yayi taga number samun kanta tayi da Saving with Yaya,
Shikuma yayi gaba abinsa, Binaif ne yazo wurin ta Yana neman wani Abu hankali kamar ma be ganta ba sai duduba? mutene yake zuwa tayi wurinshi,

tace' lafiya? Wa kake nema?

Rike hannunta yayi yace' Neena

Kallanshi tayi dakyau tasaki Baki shida besan Neena ba,? Kara maimaita wa yayi,
yace' Ehh Neena nagani Amma banga fuskarta ba tana cikin store din nan,

What?.......



#team Umsha
#team yusseer
#team Mussab????

More comments =?e? more _typing_
'?
'?



By: '''Hijjart''' '''Abdoul'''
? ?? Cwthrt=?? ?? _Akanji magana_

? ?
? ?? 29

Itama fara neman ta tayi Saida babu ita babu dalili ta gajiya tayi,

tace' Ka saya abinda zaka saya mu tafi,

Yace' nagama siyan kayana, muje ki dau ice cream dinki mu tafi,

?? Fitowa sukayi bayan ta dauki ice cream din ya biya kudin, tunda ta fito kafin su karasa wurin motarsu taji ana kallanta daga Baya tsaya tayi ta juyo Amma ba kowa,gaba tayi ta duba namma bataga kowa ba zuwa yayi?
yace' lafiya kuwa?

Idanta ya cicciko da hawaye,
tace' indai da gaske? Neena kake tunanin Ka gani to tabbas itace kuma yanzu ma itace take kallona,idan baza zo inda nake ba nagama nemanta a rayuwa ta har a bada ko naganta Zan nuna ban Santa,
Ta karashe? tare da goge hawayenta ta tafi ta barshi a tsaye, Saida taje wurin motar Yana kallanta sannan shima ya yafi,
Sun dau hanya,

tace' taya Ka gane Neena ce bayan kuma kace bakaga fuskanta ba,

Yace' ina tsaye a wurin cashier wata tazo bazata wuci kiba a tsayi sai dai da Nikaf a fuskarta itama ta tsaya tana jiran a Gama min itama a Mata zoben hannu na ya gani,
tace' Zoben Ka yayi kyau a'ina Ka siya don Allah,

Nace' ba siya Nayi Bani akayi,

Tace' Zan iya sannin don Allah waya Baka?

Kinsan data min tambayar nan sai da ta kalleta??

Nace' meyasa Zan fada maki?

Tace' kawai ina San sanine Naga de zobem kamar na Mata,tunda yawanci irin wannan Yana zuwa da bracelet shiyasa, to bansani ba ko Kai naka yazo iri guda daya ne,

Nace' Bani akayi,kuma itama bata akayi,

Budar bakinta sai ca tace' irin na Ummusalma sak, sannan ta tafi ko gama biyan kudin ma batayi ba, sai da ta tafi wani tunani yazo min, nace' tabbas itace shine fa na fara duba???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? mai irin kalar hijabinta,

Yace' kuma kinsan Nima nakaina nayi mamakin yarda na zage ina zabga Mata surutu Bana tantama itace,

Murmushi Ummusalma tayi,bata ce komai ba ganin sun dawo hanyar gidan Umma yasa,
tace' lafiya?

Yana karya kwana yace' kinyi mantuwa,

Ni babu abinda na manta fa,

Idan munje zaki gani ai,

Shiru tayi don itakam yau taga ta kanta daman ma bata zo ba, a waje yayi parking, ya zagayo ya bude Mata,
yace' fito,

Tana kumbara Baki ta fito tare da gunguni be kulata ba ya shige suna Shiga parlour suka tarar da Hadaimai suna kallo suna cin abinci Basu fito ba sai da suka tabbatar da sun tafi sannan suka lallaba suka fito, sauran abincin da sukaci suka rage shine suke ci, ko kallan inda suke basuyi ba kamar yarda Suma Basu kalle su ba, sai da suka ce Saima,
tace' shegiya karuwa mai kama da ifritu,
Sairai Ummusalma taji ta kasancewar itace a Baya shine a gaba, bata tanka Mata Har suka Shiga daki, yaja? ya tsaya

tace' mena manta to?

Zama yayi Akan kujera
yace' a haka zaki tafi? Bata ganki ba sanda kika fito?

Tace' wa?

Anty safiya,
Yafada Yana Danna wayar Shi,

tace' to daka dawo Dani mezanyi?

Yace' to shikenan Bari mu tafi idan tagano munyi wani Abu kinga gobe ina zuwa zata Bani ke, Bari mu tafi,

Itadai harga Allah bata gane Kan zancen sa ba, to me
Sakayi ganin ya Kai bakin kofa yasa ta bishi har zata bude itama ta fita wani Abu ya fado ranta, ai bashiri ta koma? ta canza kayanta data zo dashi ta fito tana tamke fuska, ta Shiga mota dariya ce cinsa Amma ya Maza yayi murmushi kawai sun fara tafiya,

yace' ai dakin koma da wancan kayan meye laifin su kuma?

Banza tayi dashi, Tama kawar da kanta daga gareshi,
yace' fine, kici gaba kinsan ba ganin ki kikayi a parlourn Anty ba ko?

Yana rufe Baki
tace' Haba Mai gida yanzu menayi? Kawai de maganar ce ban gane ba shiyasa,
Ta karashe da yake a fal fuskarta ita dai burin ta ta ganta a gida,

Shiru yayi be Kara magana har suka kusa zuwa, yaji
tace' Ummu tana cikin damuwa sabida sace su yusseer gobe zasu koma,

Wacece hakan?

Yarinyar da suka zo gidan ku ranar nan,

Yace' ohh nagene, me dinsu ce?

Kawar suce,

Waya fada maki halinda ta Shiga,

Wanda muke nema,nafada maka daman niece dinshi ce, kuma baya ga haka ma gashi an barsu abubuwa dayawa a school, na zalince su,

Bakomai, Insha Allah komai zai daidai,kin ansa numbern Shi?

Ehh ya Bani,

Saida yaje gidan mai vadi ya bude masu suka Shiga yayi parkin,
yace' Bani numbern,
Bashi tayi yasa a wayar Shi, sai anan yaga miss called din ta, beyi magana suka fito tare da daukan kayan da ya siyo sukayi part din Anty safiya,
Dukan su suna zaune a parlourn 10:30 babu Wanda yayi bacci har Ummi suna kallan king of heart Ahmad ma yana nan sun kwalalawa tv Ido basa su seen daya ya wuce su idan ba talla aka tafi ba, Da sallama suka shigo amsawa sukayi Amma idansu nakan kallo,
? Saida ta? zauna ta kalle su yarda kowa ya kwalalo Ido yana kallan yarda abin zai kasance inda roushini tayi accident Shabnap ta dauko ta Amma ba a Nuno fuskar ba shima Binaif tsayawa yayi daga tsaye Yana kallo kawai ta canza channel zuwa sofiya the first, su Duka juyowa sukayi Nafisa ce ta fara magana,cikin marairaice wa,

tace' Haba Anty? don Allah ki bayar mana ankusa gamawa saura talla biyu agama Dan Allah please kinji ?

Anty safiya ta fito tace' a,a kundawo Amma de yanzu nan don yanzu na tashi naje nayi waya,wai kar in zauna anan basa sun abinda ake fada sunayin missing word,

Ummusalma tace' yanzu nan nadawo Nayi sallama babu Wanda ya amsa shine na canza,

Binaif shima zuwa? yayi ya zauna kusa da ita,
yace' har wani yanzu kika zo ca zaki ce yanzu makazo nida mijina,

Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un Sam Baya kunyat fadar wannan kalma ita kuwa nauyi take Mata abakin wai mijinta,

Anty safiya girgiza Kai kawai tayi,
tace' can gidan kikaje ne?

Yace' a,a haduwa mukayi da ita a traffic suna cikin adaidaita sahu ita da kawarta suna Rabin IV shine fa Mata waya suka dawo mota ta nake kaisu shine na kaita gidan su kawar tasu da suka Gama kuma sai yanzu tace nazo na maida ta gida,?

Anty safiya ta yarda 100% da zance shi,ita kuwa Ummusalma sake Baki tayi tana kallan ikon Allah wannan zubit ma'aruf din ai,mintsinta yayi tare da Mata signal din tadena kallan Shi,

Nafisa tace' dan Allah ki mayar mana muga Wacece, kinji?

Shine ya dauki remote din ya makiwa? Nafisa yace' gashi yi kallan ki, tazo ta takura maku haka akeyi?

Ummi da ta kwalala Ido tana kallan cartoon aikuwa tasa kukan baza'a canza ba,
Yace' lala aikuwa Nafisa sai dai kiyi hakuri baza'a canza ba, mayar da Aljanunan,

Nafisa tsabar takaici harda su kwalla,tashi ma tayi ta bar parlourn ta Shiga daki,

Anty safiya tace'kin gamu da aiki kuwa na tsani wannan kallan da Baya karewa, Abu a yi tayi de bazai kare ba?

Itama Ummusalma tashi tayi ta bar wurin sai anan ya gaida Anty safiya sannan sukayi wata hiran yace gobe da yamma zai zo ya dauketa su fita.

Kwanciyarta Kenan taji wayanta na vibrating daukowa tayi taga Yaya dagawa tayi suka gaisa sannan kowa yayi shiru sai can,
yace' Kinyi aure ne?

Waya fada ma?

Shine ya kirani yanzu yana so mu hadu gobe,

Ok, ina ummu?

Tana Adamawa Nima yau nazo rabon zamu hadu ne,

Tun yaushe Kenan?

Tun ranar da kika taho daga can,Ranar muma mukaje,

Jinjina Kai kawai tayi, kamar Yana ganin ta,

Yace' Saida safe nakirane nafada maki ne daman,

Ok shikenan,Saida safe,



Kun Shirya Duka kayan naku?

Yaseer yace' mun shirya,Amma oga ina zaka kaimu haka da safe kaga fa 8 ma batayi ba,

Oga yace' Zan canza maku wurin zamane bazai iyuba ace kuna zaune wuri guda ba,

Sabida haka ku kwashe kaf kayanku har ps dinku idan kunaso,

Yusuf daman beyi magana ba kume beda niyyan yin magana daki kawai ya Shiga ya dauko jakar su wacce suka hada kayan su tun jiya da aka fada masu,

Shima yaseer wurin TV yayi ya hada ps din yasata a kwali yasa a cikin Leda ya rike, suka nufo kofar parlour ji sukayi an rufe su masu Ido da bakin Abu, an karbi kayan hannun su, nasuyi musu ba suka bisu ba, ana masu jagora, motar daf take da kofar gidan suna fita aka sasu a cikin sannan suka dauki hanya Basu San ina ake tafiya ba sai da aka bude musu fuska suka gansu a airport an San sa musu fuskar wasu mutene sannan suka fito kowa,harda ticket dinsu suna zuwa basu wani jimaba jirgi ya daga har suka isa inda zasuje su de Ido ne kawai nasu,

Tana kwance kamar kullum yau hoto take gani su uku a ita tsakiya sanda sukayi birthday dinta babu Wanda yazo sai su kadai Anty ma ca tace baza tayi ba shine su suka Kira mai hoto da kudin su ma suka sai cake din lemuka kuma a gida suka kwasa dukan su suna dariya sun goga cake a fuskar su, tayi nisa cikin tunanin ta Inna ta shig, cikin fada,

tace' ke! Fita waje bazan iya ba yau zaki koma gidan Ubanki ina dalili haka?

Bata tanka Mata ba don tasan kwanan zancen tagaji da biyota da abinci har daki shikuma Baffa kullum sai yace a kawo Mata shiyasa yau tazo da wannan tijarar harda zagin uba, tashi tayi ko Dan kwali babu ta fita tsakar gidan ta zauna a kusa da Baffa ta fara cin kosan badan Yana Mata dadi ba sai kawai Dan jarabar Inna data lura kullum karowa take, dayan da ta dauka a hannun ta shine bata cinye ba,kamar tana cin magana me da Karen daci haka takejin sa a hankali ko magana ne ma ai zakayi sauri Ka tauna haka take ci, sallama akayi tare da shigowa ko Suma tayi ta farka wannan muryan bazata taba bace Mata ba, daga Kan da zatayi kuwa tayi tozali dasu wani wawan ihu ta daka ta Mike a guje ta rungume su,Suma rungume ta sukayi sai suka saki kuka a tare .(>?'?)


Mama ce zaune a parlour tana kallo kamar ma babu abinda ya faru da ita hankalin ta nakan? kallanta, Sameera ta zo tace' Mama ina kwana?
Da fara'a ta amsa Mata suka gaisa,
Mama tace' lafiya naganki a shirye haka? Ina zaki kuma?

Sameera tace' a,a mama zani gidan su kawata tun jiya nace maki zani fah,

Mama tace' Sameera Bana San fini fah,ki Rasa yaushe zaki je gidan su kawar sai da wuri haka? Ina laifin ki Bari sai da yamma sai kije,

Sameera ta turo Baki gaba tace' Haba mama tun jiya fa na fada maki zani, kuma na fada Mata ganin nan kinsan daga nan Zan wuce gidan Hajiya Yaya fah datazo ta, kuma yau juma'a kinsan de gidanta yafi dadi da yamma kowa yazo Mata ayi ta hira,

Mama tace' da wannan kuma,to Kide kiyaye Bana San fitina banasan tarkace tarkace damma kuma Naga yarinyar tana zuwa Amma yawon ki ya isheni haka, tam kuma kidawo da wuri bazan Kara Bari Bama kike kwana a wani wurin,

Sameera tace' Insha Allah mama Zan dawo, ke yau bazaki fita ba?

Jiya naje babu inda zani, Allah ya kiyaye,

Tace' to mama abani Dan kudi,

jeki dauka a daki a cikin jakata ki dau ki dubu daya ta isheki,

Komawa tayi tadauka takara yiwa mama sallama ta wuce, tana fita ta kira driver ta fada masa inda zai kaita gidan su kawarta bikinta za'ayi shiyasa zasu fara Shirya abubuwa tun yanzu saura sati biyu ya rage bata wani jimaba ta Kira saurayinta suka tafi shan iska sukayi ta yawon su a gari daga nan suje nan daga karshe sukaje park lokacin har yamma tayi yara kowa sai wasan sa yake,




Sai da sukayi mai isar su babu Wanda ya tanka masu har? su Anty da sukaji ihunta daga gidan su Wanda yake Jin na su Inna suka ce baza su koma? ba ana zasu zauna, suma sun zo suna kallan ikon Allah,
Taja hannun su ta zaunar ta Shiga tsakiyar su, Koko da kosan ta kalla,

tace' Inna yanzu fisabilillahi waye ya zubar da wannan abun? Sai kace marar hankali,

Takaici da haushi Inna taji takasa Mata magana Baffa
yace'? idan Banda abinki mai sunan manya ai ke kika zubar kece kiyi wannan ta'asar kina ihun ganin yaran Gobe,

Sude kallanta kawai suke bako kiftawa? yarda da ta rame tayi duhu, kanta tun kitson da suka Santa dashine shine de babu canji,?

Anty tace' ai kece marar hankalin mutum ayi kamar mai aljanu,kunga ki tashi muje kuci abinci kamar nasani yau favourite dinku nayi, Maza ku tashi mu? tafi,

Ummu tace'inaa ai mama wallahi Nima sai naje,yunwa nakeji nima,

Babu Wanda ya tanka mata suka tashi suka fita har sunje zaure yusuf,
yace' haka zaki fita?

Sosa keya tayi tace' ku jirani ganin zuwa,kar ku tafi, ja sukayi suka jiranta da gudu ta koma ta dauko hijabin Inna ta sa a zauren ma ta karasa sawa, a parlour suka zauna Anty ta kawo masu abinci Suma daman Basu ciba su Inna ne de masu ci da wuri kuma kullum? Koko da kosai sai kace Ibada, Suma acan favourite din su ake Basu duk wani Abu ana musu, sosai suka zage suka ci abinci har itama Ummun abinda bata taba yi ba Kenan tunda suka tafi sai yau da suka dawo aikuwa tafi kowa haka sai ci take zuba surutu ita da yaseer kamar babu abinda ya faru Baba kawai Jin su yake tare da nazarin yaran lalle akwai laka Mai karfi a tsakanin su, Saida suka ci suka gyatse sannan Anty
tace' Yusuf ya akayi hakan ta faru?

Yusuf ne ya Basu labrin yarda komai ya kasance har zuwan su Adamawa,

Yaseer yace' a airport muka neme Shi Muka Rasa sai mai taxi ne yazo yace ance ya dauke mu ya kaimu wani wurin dayake bamu taba zuwa Adamawa a jirgi ba yasa bamu San ita bace sai da aka kawo mo kofar gidan nan aka ajje mana kayanmu ya bamu kudi yace inji Wanda ya kawo mu yace amu,

Anty tace'Yanzu baza ku iya gane shiba?

Yusuf yace' Antu babu wani sauran bincike tunda mun dawo lafiya shikenan ai,

Yaseer yace' kwarai kuwa ai Bama za'ayi ba gaskiya kar ma Abie( Baban Ummu) yasan da wannan zancen,

Baba yace' kamar yafa? A sace ku kuma kuce kar asan da wani zance zancen banza Kai,

Ummu tace' kufa bayin Allahn nan kunfiye gardama,tunda sunce yafe a barshi ai shikenan, agarin bincike nan a wannan Karon na tabbata Ida aka sace su sai dai wasu ba suba nikuwa mutuwa zanyi daman,

Kowa kuwa yayi na'am da maganar ta karma aje garin nema gyara akara batawa, ahaka suka ci da hiran su Itadai Anty Ummu ta bata mamaki bana wasa ba ace daga dawowar su har ta ware haka?
Suna nan Basu suka tashi ba Saida suka ji Kiran sallah, Ummu tace' laaa yau nice wai banyi wanka ba har aka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login