Showing 6001 words to 9000 words out of 173457 words

Chapter 3 - A BAKIN WAWA (AKANJI MAGANA) COMPLETE

30 Oct 2025

3922


Basu dawoba sai 11:30 yusseer sunyi bacci,dakinsu ta kaisu ta rage masu kayan jikin su ta musu addu'a ta fita wanka tayi itama, coffee ta dafa ta kaiwa Abba Yana zaune Yana aiki da system,a gefenshi ta ajje,
?
"Thanks". yace sannan ya daura dacewa banga kun dawo da sameera ba,
Kasancewar bada mota daya suka dawo dashi ba,

?? Tace, "ai sameera tun dazu tamin waya tadawo".

Gyada Kai yayi cike da gamsuwa sabida yasan Sameera nada hankalin uwa uba kuma ga ilimi.
Haka de sukayi tattauna,har sukayi bacci.

? ? ?

? ? Tashi tayi,ta zauna ta jawo wayar taga 1:30am gaban tane ya fadi

tace, "kardai har yanzu Basu dawo ba".

Da sauri ta taso kofar ta bude ta ziro kanta waje ta leka, ahankali ta fito,don ba laifi akwai tsoro, a dakin Sameera ta Shiga dake opposite danata fitila ta kunna Amma bakowa,tsorone ya kamata ta fito, lokaci guda ta tuna sometimes tana kwana a gidan yayar mamansu? da gudu ta Shiga dakin su yusseer ganin su da tayi sun dungule suna baccinsu hankali kwance,wata wawar ajiyar zuciya ta sauke sannan ta koma dakinta ta kwanta,bata jima da kwanciya ba taji motsi, kasancewar dare kuma ko ina tsit, maimakon ta koma ta kwanta sai ta fito taga waye,a kasan parlour take Jin motsin sbd haka nan ta nufa Sameera tagani a kofar parlourn tana kullewa,mamaki tayi bakadan ba ita bata karasa sauka ba kuma bata komaba ganin zata hawo yasata cigaba da tafiya,maimakon ma ta Mata magana ko kallan ta batayi ba ta wuce kitchen.
Sameera kuwa gaban tane ya fadi Allah yasa bata ganta ba tana rufe kofa ba.Ruwa tasha ta koma dakinta,tana tunanin ko daga ina take Oho?
??
***********************

? ? ? ? Washagari? kamar yarda ta Saba duk asabar tana Riga su tashi kafin su tashi tayi wankinta,tayi gyaran dakinta wanke toilet ta gyara duk inda ya dace ta gyara tayi tagama,sai tagama tayi wanka wani sa'in ma sai taci abinci sannan suke tashi wani sa'in kuma ko wanka ma batayi suke tashi.Tana kitchen taji motsin su yusseer suna fada Akan remote. Chips da kwai tayi sai sauce mai kifi aciki, fitowa tayi taga yarda suke fadan wannan na fada dayan ma na fada girgiza Kai tayi baza su canja ba sukam,Wucewa tazoyi.

Tace, "yusseer abinci".

Bada karfi tayi magana ba Amma sunjita. Wucewa tayi dagudu suka bita summa Rigat? Shiga dakin balcony suka bude suka zauna itama nan ta nufa, bayan ta dauko masu lemo, Yusuf ne ya dauko masu cup,suna ci suna Santin abinsu
?? Yaseer

yace, "Yusuf nifa yau bazani tahfeez ba gaskiya nagaji nidai".

Yusuf yace, "bawani ka gaji kawai kace baka iya hadda ba, kuma idan baka jeba amaka duka biyu Dana hadda nakin zuwa".
?
"Islamiyya kawai zanke zuwa ta yamma ai itama ana hadda".

"Oho de nikuwa dole sai kaje ko nafadawa Abba".

Shiru Yaseer yayi bai Kara maganaba yasan halin Yusuf tsab zai fada,Amma kuma ya kudurta bazai jeba. Ba Wanda ya Kara magana daman shine mai dauko maganar har suka gama suka kwashe kayan suka tafi dashi. Bayan sun fita tunaninta ta fara har ko yaushe ta jima a wurin sannan ta tashi ta fita, tasan yanzu suna parlour su duka saboda haka dakin Abban su ta nufa,safe ta bude taga kudin ba yawa rufewa tayi ta fito har taje bakin kofar parlourn sai kuma ta dawo tunda take bata taba Shiga dakin ba kullum a rufe,yau kam sai ta Shiga tasan yau Yana gida? maybe a bude yake ,? komawa tayi ta murda handle din aikuwa abude yake,Shiga tayi taga wardrobe ne mai kofa uku kawai a dakin sai bedside drawer guda daya, wardrobe din? ta bude taga safe? guda uku a jere,buder sauran kofar wardrobe din tayi? sauran ma haka ne aciki,
Gwada bude daya tayi Amma be budu ba sunnanta tasa namma bai budeba,tasa sunnan kowa a gidan namma haka,kuma password ne ba pin ba,sunaye tayi tasawa be bude ba,gajiya tayi kawai zata rufe wata zuciyar tace kisa ummu,sawa tayi badan tasan zai bude ba,tasawa safe din ya nuna correct,dadine ya kamata,a hankali taga safe din Yana yin kasa Yana budewa kudine aciki dayawa,kudi Bana wasa ba,da sauri ta gwada sauran Suma duk kudi aciki guda daya ce kawai taga takardu? rufe me takardar? tayi, dankwalinta ta shimfida? ta fara jidan kudin a cikin? kowanne safe,ita kanta batasan yawan kudin datake jida? ba kawai jida take,dayawa ta kwasa sannan ta rufe,ta kulle dankwalin ta fita daga dakin,Jin za,a shigo parlourn yasa ta buya a bayan labile,Abban ne yashigo,zama yayi ya ciro da wayar sa har ya Gama abinda zaiyi sannan ya tashi ya kulle dakin da tafito ya Shiga dakin sa,Yana shiga itakuma tana fita dakinta tashiga ta Adana kudin,ta kwanta.
?

? ??
Ranar Monday ta Gama shirinta tsab, dauko jakarta ta tayi? zuba dubu dari dayake ta kirka dari dari ta ajje duka one million ne da duba dari biyu,wayarta ta dauka ta fita,bakowa a parlourn ta sa Kai ta wuce abinta
? Banki tace ya kaita,bata fada masa wanne ba kawai taga sunyi parking a access,fitowa tayi ta Shiga kasancewar da wuri tazo yasa aka Mata da wuri? account ta bude tabada dudu Dari amata transfer cikin account din,
Gobe kace tazo ta karbi atm card.
? Daganan park tace ya kaita ko zata ji dadi don kwata kwata bata ra'ayin zuwa school yanzu sabida ba Neena,
Ahaka ta karashe ranar har yamma yadawo ya dauketa.
? ? Washagari ma haka bataje ba daga karban atm park ta wuce,tayi zamanta har yamma.sai Wednesday ne taje amma badan tasan me ake cewa ba kawai tunani take ahaka de satin ya cinye kullum sai ta ba driver dubu dari ya kai banki an Mata transfer a account dinta.

??

? ??
? ??

? ?? Haka ruyuwa ta cigaba da tafiya a wurin Ummusalma kullum ba dadi,kullum cikin kadaici take duk da su yusseer na debe Mata kewa Amma ita kam bata gani haka,haka idan taje makaranta ji take kamar Neena zata dawo Amma kuma baita ba labarinta kuma bata Saba ba,yanzu abin kadan zata tuno sai tafara kuka, musamman idan Neena ta tuno,abin har mamaki yake bata,tayi bakin kokarinta ta daina kukan Amma inaaa bata iyawa sam. Gashi har sun Gama waec da neco yau watan su 1 da gamawa saboda haka maganar tafiyarta kawai ake tayi. A yanzu tunaninta ya karu kuma kwakwalwar ta takasu kusan uku da tunani na daya neman mafita nabiyu kuma abin da zata karanta na uku kuma Neena,wannan abin yabin yana damunta kwarai da gaske batasan ya zatayi ba.

? ?? Fitowa tayi kasancewar yau Friday bakowa a gidan sai ita, parlour ta sauko badan tasan me zatayi ba,idan ta Akan TV ta sauko tamanta yaushe rabon da tayi kallo hakan nan yau taji tana so,kunnawa tayi ta zanja Channel zuwa india,film din dake kallo ne ya fara Jan hankalinta,na shahid Kapoor mamanshi naso yayi police shikuma naso yayi film,wani tunani ne yazo Mata,da sauri ta tashi ta kashe kallon tasami mafita Kenan, Da daddare yaseer ya kirata yace Abba na kiranta,bayan shi ta biyo har parlour inda Abba yake zaune Zama tayi batare da ta kalle shiba,shima Bai damu ba.

yace, "wato Ummusalma kinsan mu muka haifeki,kuma kunfi kowa sanki sabida haka badan bama sanki ba zamu tura ki wani guri mai nisa ba,sai dan muna sanki kiyi karatu mai zurfi,ki taimaki alumma gaba daya kinji ko".
? Kallan Shi kawai take bako kiftawa tsayawa tayi kamar statue tana kallon shi,
Mama dake gefenshi tacigaba

Tace, "muna matukar kaunarki kinji ko ?ata,abinda nake sodake Shine kiyi kokari ki maida hankalinki, kiyi rayuwar ki tamkar da kiyi hulda da jama'a sosai.
Sannan kuma zaki karanci gynecologist kinji ko Shi aka samu,don har babanki ya Gama komai da komai da ya kamata har hostel kinji ko?

? By: '''Hijjart''' '''_Abdoul_'''
? ? ?? Cwthrt=?? ? ? ?? _Akanji_ _magana_
??

Not Edited
POST 2020
REPOST 2023

? ? ? ?? 5

Kawai kallansu take yi,ba ko kiftawa, idan suka ce suna Santa wani irin bakin ciki takeji,wai suna Santa. Abba ne? ya mika Mata envelope

yace, "gashi takardunki ne da komai da komai mun ajiye copy a wurin mu,abinda nake so dake shine kiyi karatu,shine ya kaiki,banasan shirmen banza kina jina ai".
? Batasan mezatace ba shiyasa ta zabi da tayi shiru,Amma har yanzu bata dauke idan ta akansu ba kallon su kawai take kallan irin kun tsaneni dinnan

"Tafiyar kuma Nanda sati daya ce kinga saura kwana takwas kenan,sabida haka sai kifara shiri kinji ko".

Muryar Abba taji ya fadi haka,
Ganin sungama magana sun dauko wata yasa ta tashi ta fita,dakinta ta koma ta zauna a balcony, envelope din ta bude ta zaro takardun ciki ta dudduba komai, su biyu ne a dakin,don har sunan dayar akwai saidai ba musulma bace daga ganin sunan,maidawa tayi ciki,ta jingina da kujerar tana tunanin tafiyar kuma da dukkan alamu ita kadai zata tafi ina laifin ma su tafi tare sai su dawo Amma zata tafi ita akadai sai kace wani namiji,kuka takesonyi ko zata ji dadin abinda takeji amma yau taga bata da alamar yin kukan,tana zaune anan bata San iya adadin lokacin da ta dauka ba tana tunani, da?yar ta tashi ta rufe kofar, alwala ta dauro ta fara sallah tana rukan Allah yasa da alkhairi a cikin tafiyar ta kuma,tare da shiriya.
Tana kwanciya bata jimaba aka fara Kiran sallah dakyar ta tashi da aka shiga sallah,tana idarwa kuwa ta koma bacci. Ba ita ta farka ba sai shaWaya shima su yusseer ne suka zo suka tasheta zasu wuce tahfeez yau za,ayi hakan yasa akace suje goma? Amma sai suka ce sai shadaya akace? suje, zuwa sukayi suka tasheta suka Mata sallama sannan suka wuce, tashi tayi ta gyara dakin,yaukam sanyinta ta Kara karowa don Saida takusa awa daya da rabi Dana gyaran dakin tanayi tana tunani,ta wanke toilet tayi wanka,batajin zata iya wanki shiyasa ta hada takai laundry.
Lemo ta dauka da biscuit taci ta koshi, fitowa tayi ta Shiga parlourn Abba bakowa a parlourn sai tv dake aiki,dayan dakin ta shiga? kudi? ta dauko ta dawo dakinta? kirga? su tai sannan ta zuba su ajaka key din motar ta dauka guda daya Wanda yake wurinta ,sarkan gold dinta ta dauko da receipt dinsu ta hada ta dauko wani key din motar ta Wanda yake a wurinta guda daya shima ta hada.

?? Bayan tayi sallahn la'asar ta hada su Duka ta sa acikin jakarta, ta fito sameera kawai tagani a parlourn da'alama yau bata je islamiyya ba,wucewa tayi ta fita harabar gidan, drivern ta na ganinta ya taso da Dan gudunsa,yazo zai gaisheta saidai kafin ma karaso ta karasa wurin motar,budewa tayi ta Shiga, shima Shiga yayi sannan suka fita,inda zai kaita ta fada masa,sarkarta ta siyar,ta dawo kudin ta Mika masa,tace ranar Monday yasa Mata a account,daga nan ya kaita park,ta zauna sai dab da magriba suka dawo gida,har zata fita ta bude jakar ta Ciro mukullin motar

tace, "kasiyar da biyu ka samun kudin account".

Ta juya ta wuce. Kallanta kawai yayi to wacce zai siyar tunda ya gane motar take nufi,Bari kawai ya siyar biyun a ajje Mata sabuwar Amma Allah yasa kar yayi laifi.

? ?
Washegari da rana gaba daya gidan suka tafi rakata shopping banda Abba,duk wani Abu da zata bukata,kayan sawa kam an jide su ba laifi,ita kawai ido ne kawai nata, daga nan suka wuce yawo Basu suka dawo ba sai tara na dare, don haka kowa dakinsa yayi ya kwanta. Haka Mama tasa drivern gidan yake kaita gidan kawayenta acewarta tayi masu sallama,ita kuwa duk inda taje ko sallama bata masu bare kuma gaisuwar da daman can ba gaida su take ba,ko ruwa batasha bare aje ga abinci,haka zata karaci zamanta ba magana,idan kuwa zata tafi ba sallama take wucewa abinta,Haka kawayen Mama zasuyi ta kiranta suna Mata complain akan Ummusalma,ko mama ta sameta ta mata fada,bazai hana gobe ma idan taje takuma yin shirun ba,tun mama nayi har tagaji tayi shiru.
? ?
Ya rage sauran kwana biyu ta tafi ta dena fita ko'ina tana gida abinta, Mama kam ba laifi ta Mata snacks da dambun nama sai yaji dayawa, kasancewar tana San dambu da yaji,Sameera ce ta hada Mata kayanta ana gobe zata tafi,tana zaune tana kallanta tana shirya Mata kayan. Tunanin? Sameeran take? a zuciyar ta,yanzu iyayenta bama iya iyayenta ba kadai ba mutane dayawa kallan mai hankali suke mata ga nutsuwa da kokari, gata da biyayya dai daibgwargwado, yarinya mai Shiga Rai indai har kazauna da ita zaka fahimci hakan,Amma kuma anyi ba'ayi ba wai an raka bako ya dawo, iyayenta na bata tarbiya daidai gwargwadon su amma kuma batare da sun saniba suna tufka ana warwarewa ne,ko kawaye Basu bata taba to ta tabbata samari na bata ta.sameeran ce

tace, "Yaya kuma yanzu zaki na dawowa gida?

Nodding Kai tamata alamar a,a

"Taaab har shekara shida ko?

Namma de Waga Mata Kai tayi alamar ehh,
Cigabawa tayi

"Nikam da nice gaskiya zan dawo, Nama Gama hada maki kayan bari na tafi".

Tashi tayi ta fita,tabi bayanta da kallo,har ta fice, ajiyar zuciya ta sauke daga bisani taje tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga tayi rolling tasa takalmi ta rataya jaka ta dau key din mota fita.
Gidan su Neena ta nufa sai yarda ta ganshi ranar da suka zo haka yake babu abinda ya sauya,fita tayi ta Shiga gidan matar da suka Shiga, sallama tayi ahankali tasa Kai ta shiga,matar na zaune akan tabarma tana yanka alaiyyahu, lalle matar tamata tabata wurin zama,bayan ta zauna ta kalli matar

Tace, "Ina yini?

Da fara'arta matar

Tace, "ahhh wallahi lafiya qalau ya mutanen gidan ?

Shiru ba amsa,ta kuma? cewa

"ince de kowa lafiya?

Namma de shiru, ta kuma? yi mata

"To madalla ya hanya kuma?

Girim ba amsa,ganin haka yasa matar cewa.

"Ni kamar Ummusalma?

?aga Mata Kai kawai tayi.

Tace, "to yayi kyau. Kinga kinzo ban baki ko ruwa ba yi hakuri bari na Wauko".?

tashi tayi taje ta Wauko Mata ruwan, Kallanta tayi a zuciyarta

tace,'tafiye surutu ca duk amsar ta dayace amma ta damu mutane ya kaza kaza mtsw'.

Taja tsaki,ruwan ta kawo Mata ta ajje,
Kallanta Ummusalma tayi bayan ta harhado abin fada,
?
Tace' Amina fa?shiru?

Matar kallanta ta Wanyi,yanzu fisabilillahi maimakon tace ya labarin su Amina ansamu ko kuma har yanzu shiru? Amma shine zata ce Amina fa? Shiru?

? Numfasawa tayi tace,"wallahi har yanzu shiru,ba amo ba labari,kuma su ba wayaba, bare a Kira aji ko lafiya?

KuWi ta Ciro ta jakarta ta ajje sannan ta tashi ta fita,da ido matar ta bita?

tace,"ohhhh ni yau fatsimatu kekam wannan daman kurma ko bebeya akayi ki tunda Baki San magana".
?? Ta jima a cikin mota tana kallan bracelet din da Neena tabata,Neena ce mutum na farko data sota Sona tsakani da Allah,gashi yanzu ta tafi ta barta,goge hawayen da ya zubo Mata tayi sannan ta ja motar ta tafi,park ta nufa,Itakam a rayuwar ta tanasan zuwa park duda yanzu ba wasa takeyi ba Zama kawai take tasha ice cream,amma tana San zuwa,
Zama tayi tana Shan ice cream tana kallan yarda yara ke wasan su hankali kwance,sam Basu da damuwa.
Tana nan zaune ganin magriba ta gabato yasa ta tashi ta tafi.
Kamar kullum driving take a hankali,yau kam tunanin take kawai tana driving,da karfi ta ja wani irin wawan burki, sabida jan danjar da aka bayar amam kwata kwata bata luraba,don har ta kusa bige wani dittijon mutum Amma dukda haka sai da ta Dan bige Shi,da sauri ta fito,mutane har an taru anzo kallo,ganin bata wani bigeshi sosai ba kuma zai iya yasa ta koma cikin motar,namma mutane har sun fara magana akai saidai kuma ganinta da kudi yar Rafa guda yasa kowa yaja bakin Shi yayi tsit,kamo hannunshi tayi ta damka masa kudin,ta kalle she bata taba ganin mutum mai kwarjini irin wannan ba,bata taba kallan mutum taji gabanta ya fadi ba sai yau,yau takasa hada ido da mutum,yau itace take Jin zuciyarta na bugawa saboda wannan mutumin,cikin sauri tayi kasa da kanta,samun kanta tayi da magana cikin rauni da taushi gami da nutsuwa, ahankali kuma,

Tace' Baba kayi hakuri,wallahi ban lura bane,amma ga wannan Ka sai fruit ka sha kar Ka zauna haka Baba,
Kara damke hannunta yayi

yace, "Allah yayi maki albarka yata, Allah ya kareki, Allah ya biyaki duniya da lahira Allah kuma ya jikan magabatanmu,nagode sosai ?ata nagode nagode".

Sannan yasa Kai ya fice yabar ta a tsaye tana kallanshi, gani take kamar tasan mutumin Amma kuma a, INA????
Horn taji ana Mata tazo ta zanje motar ta,zuwa tayi ta Shiga,ta tafi,
Lokacin da taje gida an fito daga magriba, parking tayi tafito,so take takira drivern ta amma bazata iya daga murya takirashi ba kawai tadau waya ta kirashi,Yana ganin kiranta ya tashi Dan ma yaga zuwanta,durkusawa yayi

yace, "gani madam".

Mukullin motar ta Mika masa,
Karba yayi ganin zata wuce? dasauri?

yace, "Madam amm daman naga gobe naji ance zaki tafi karatu kuma daman ke kadai nakewa tuki a gidannan,gashi kuma Alhaji ya sallameni,shine nace mezanyi da wannan din?

Tsaki taja a zuciyarta sannan

tace, "dan baka so ka yar".

Tasa Kai ta wuce. Ikon Allah ya furta Shida tunda yake beta tunanin zai samu motar nan ba shine ya bar sabuwar Ashe rabonsa ce Ikon Allah, Kenan cike da zumudi yadawo benchi sauran ma'aikatan ya fada masu,sun tayashi murna kam balaifi.

?? Sallah tayi sannan ta dauko Qurani ta karanta, taso ace tayi sauka kafin ta tafi,Amma kuma hakan ma ta godewa Allah da tasamu,kuma Insha Allah bazatayi sakaci ba,tana nan zaune har Akayi Isha tayi, sannan tayi Shirin bacci,ta kwanta Kenan mutumin dazu ya fado mata rai,babu abinda yafi mata dadi irin addu'ar Shi,batasan idan akayi kyauta haka akeji ba,to ita wama ta taba bawa Abu?Neenace kawai take sai mata chocolate kuma idan ta kaimata ma sai tace' ban gode ba kuma bazan gode ba,amma hakan bayana nufin idan takuma bata takuma cewa hakan ba.ajiyar zuciya ta sauke tana Kara tuno inda tasan fuskar mutumin nan,ganin ba mafita yasata sauka a gadon ta kunna fitilan dakinta, dakin zanenta ta Shiga ta yaye abinda take rufe zanen dashi,zaninka kalakala duk abinda taga ni indai ya Mata kyau to sai ta zana shi,a da tana bawa zanen muhimmanci kusan shine yake cinye Mata lokutanta. Bin zanen take daya bayan daya don duk sunyi kura,Idonta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login