Showing 57001 words to 60000 words out of 173457 words

Chapter 20 - A BAKIN WAWA (AKANJI MAGANA) COMPLETE

30 Oct 2025

3949

musu har ayi arba'in,

Cikin mamaki tace' Alhaji wannan wanne irin batune haka? Ka kwasan mekake cewa? Anya ba kasan me kakeyi kuwa?

Yace' ehh sanin nasan abinda nakeyi ne yasa nace kar a gayyato mutane,

' to amma meyasa?

' saboda idan mutane suka san cewan 'ya'yan mu sun rasu,za'a tambayi dalili ko mun boyewa na waje bazamu boyewa na ciki ba, kuma na cikinne zasu sanar wa 'yan waje,shima Wanda aka sanar wa ba shiru zaiyi ba idan yayi gaba zai sanar,daga karshe kuma kiga an fara posting a social media,kuma dole labarin zai tashi daga ainahin labarinsa ya koma wani kalar labarin shiyasa nace muyi shiru bakin mu Alaikum,

Sosai ta gamsu kuma ta yarda da wannan shawara tasa,

tace' mu kuma haka Allah ya kaddara mana rashin 'ya'ya har biyu a lokaci guda.
Kallanta yayi kawai baice komai ba don yasan har yanzu batayi hankali ba,idan ma ya fada Mata cewa zatayi Wanda ya sace sune,shikuwa tun ranar da aka neme su aka rasa sai an turo masa da text har yau da? yake kwana uku da dauke su,kuma Kala Kala wani ya gane me ya kusa wani kuma sai an mai bayani, Yana tunanin l bema San ta tafi ba. Kwanciya kawai yayi ya rufe ido,Yana tuba abinda ya aikata a shekarun baya.

?? Koda Mama ta sauko sai taga ummu a zaune a parlour gaidata ummu tayi, mama tace' Ummu sai dai hakuri haka Allah ya kaddara mana fatan Allah ya bamu ikon cinyeta,
Daga Mata kawai ummu tayi tace' Bari na Shiga dakin su zan dauki handout din a,
Daga Mata Kai kawai mama tayi,
Tashi tayi ta Shiga dakin datasan san anan suke ajjewa kayansu kuma ana suke karatu, table din karatu uku ne a dakin sai gado a tsakiya don wardrobe din dakin itace ta zuba littafi da tarkacen su, wurin table dinta ta duba taga babu ta duba ko nasu ma shima taga babu, wardrobe ta duba anan ta handout dinsu tasu ta kwasu ta ta ajjeta akasa tana dubawa, sai data zare ta ta ajje ta Kara da Wanda zata dauka, a Sama ta dauko kawai sai ta ajje a kasa,har zata rufe sai kuma tayi tunanin ta mayar inda ta dauka, taje daukowa ta hado da wani littafi sai da mayar ta zare littafin zata Maya dashi taga kamar diary "' Kona waye ? Ta furta sai kuma tace' to ko su suke rubutawa? Dauka tayi ta hada da abinda ta dauka ta rufe wardrobe din ta fito, sallama tayiwa mama ta wuce gida,
??
? ?? Tana shiga taga uncle Yana cin abinci wucewa tayi ta Shiga daki, sai da tayi sallah tukunna tazo ta kwanta, diary din ta dauko,

tace' yanzah haka yaseer ne uban hauka zai wani kafa rubuta diary kome zaice oho masa,
Page farko ta bude taga wani zane kamar jariri iri an wulgar a cikin towel, sai kuma daga kasan zanen wasu yara ne su biyu kamar su daya da uniform a jikinsu, daka kasa aka kuma zane wata yarinya? 'yar karama tayi tagumi, sai kuma can kasa aka zana gida ya kama da wuta, kuma kowanne Zane da rubutu a jiki amma ita bata wani gane komai ba tunda rubutun a wani style akayi Shi Wanda ya rubuta ne kawai yasan me ya rubuta a jiki, Kara bude page na biyu tayi shima zane ne bata tsaya kallon me aka zana ba ta bude wani shafin, ganin mai sunan a jikin yasata waro Ido Ummusalma Muhammad?
Ai tuni ta Kara bude wani page anan taga rubutu da yawa,daga nan tafara karantawa,daga farko labarin very interesting amma da taje tsakiyar Shi da karshe tuni ta fara kuka,har kawo sanda ta zata tafi? London,kifa littafin tayi,tayi rufda ciki ta cigaba da rera kukanta,
? Uncle da tazo Kiranta don taci abinci kuma ya fada Mata su Umma sunzo, ganin tana kuka yasa Shi zuwa ya daga ta Shi a tunanin sa kukan besties takeyi,ya Dura kanta cinyarsa ya fara rarrashinta besan dalilin dayasa bayasan kukan 'yarshi ba,ko Shi yasa kuka to ana jimawa zai rarrasheta sai dai kuma ita Allah yayi da tsokana shikuma bayaso ga Dan Karen surutu, ganin taki tayi shiru yasa shima ya dakata Yana nazarin kukan nata, littafin da yagani shima yasashi dauka, page din karshe ne inda zata tafi London daga nan ba'a cigaba ba, farko ya karanta kadan sai kuma karshe karshe karshe da ya? Karanta, dukda be Karanta complete amma ya fahimta abinda zai fahimta,bema iya magana ba ya sauke kanta a pillow ya tashi ya fice,
??
?? Wata irin tsanar Mama da Abba yakeji lokaci tsanar da besan ta Shiga zuciyar sa ba lokaci guda,Yana daf da Shiga parlour yaji Anty na,

cewa'? har yanzu ba'a Sami labarin yarinyar ba, ina tsoron a fada masa wani ciwon ya same Shi,don Allah Baba kumu Bari sai mun tabbatar hoto kawai nagani,
Baba yace' wato zainab Bana ki ta taki bane inasan na kawo karshen wannan abun ne ina son na Gama da Iyaye na lafiya? kulluma Baba da Inna da ciwo suke kwana suke tashi, banje ba Amma kulluma ana bani labari,

Umma tace' ya kamata ace a wannan shekarar munje Bana iya bacci sai nayi mafarkin su,kuma kinga Adda itama an nemeta an rasa kosama ko kasa an bincika ko ina babu ita har sun fitar ma da ran Kara ganinta a duniya sun hakura sannan kuma muda muke ran suka San inda muke sun haramta mana zuwa inda suke wannan Karon kome zai faru sai dai faru,iyaye ba abin wasa bane,

Anty tace' naji zakuje kuma Nima zanje Amma don Allah ku taimaka kar ku fada masa har sai idan munje don Allah ku min wannan alfarmar Baba Umma please,
Numfashi taja yace' shikenan zainab bakomai, Fatana Allah yasa kar su koremu kamar koda yaushe idan munje,
Babu Wanda ya amsa sabida zuciyar kowa da irin tunanin da suke,
?
? Uncle dake corridorn da zai sada Shi da parlour Yana tsaye Yana jinsu,kowaye suke zancen sa kuma oho,fitowa yayi yaje wurin Baba ya zauna kusa dashi ya kalleshi kawai sai???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? ya rungume shi,Yana sauke ajiyar zuciya, idan da sabo ya Saba da irin wannan abun nasa,anacewa Da yafi saboda Uwarsa to shide yafi saboda dansa,
Yace' Babana mai sunan ,jika na, ya akayi ne?
Uncle da Baya iya boye damuwar Shi ,

yace' Dad wani abun al'ajabi na karanta,
Tashi yayi zaune yace' Anty ina wannan yarinyar nan? Bejira cewar taba ya Dura yace' labarin ta na Karan ta,a wurin Ummu gashi can ma tana kuka, daga nan ya Basu iya abinda yasani,
Babu Wanda ya iya magana don kowa yaji labarin ta dole a tausaya mata,kuma ma mace fa da tausayi.


Suna zaune suna buga game,an kawo masu komai duk wani da suke so ana yi musu matsalar kawai wayace babu,kuma ko akwai ma bazasu Kiraba suna San rayuwar su,suna so kafin su mutu su Hadi da Yaya.

?? Yusuf yace'? kasan lokacin da muke game da Yaya?

Yaseer yace' lalle ma nasani mana, wayace ma,wai meka mayar ni ne?

Yusuf yace' ahh yaro mana mekuwa na mayarka,

Yaseer banza yamasa idan Yana game Baya iya magana yanzu sai a cinye Shi gashi daman mutul combat ne aikuwa de ba Ankara ba yaga yusuf yamasa penalty .
Haushi ne yakama Shi yace' na fasa idan ba tsoro ba a koma ball kasan sai na maka 10-0,

Nikuma gani Wawa sai na tsaya kamin,akoma mana aga Wanda zai cinye,

Ball suka koma suna bugawa babu Wanda ya cinye har lokacin sallah yayi suka dawo suka cigaba abinsu.

('('('('('('

Umma na zaune a parlour taga sun fito,

yace' Umma zamu fita,

Kallansu ta da kyau? tace' idan Banda de yaran zamani ina kaga an fita daga daura aure ? Jiya fa aka daura auren ko kun manta ne?

Yace' Umma ba jimawa ba zamuyi ba,yanzu zamu dawo,

Umma tace' ina ruwana to,mude a zamanin mu idan aka Kai mace gidan mijinta ko leka kofa batayi sai tayi shekara cis a dakinta, Kai wata ma sai ta haihu,wata kuwa bata haihuwa sai ta shekara biyu,uku,hudu Kai har shida ma sannan wasu zasu fita shima sai an zubda wanka,kuma idan mace ta fita a ranar take dawowa gidan ta ba irin yanzu ba,

Yace' Haba Umma da kikace da da dayanzu ai ba daya bane komai ya canza,

Tace' Allah ya Baka hakuri fada maka nayi ai,ko kaima zaka yiwa matar haka, sai kun dawo.

Ummusalma tace' sai mun dawo,
Shikuwa ko magana beyi ba,
Ya Riga zuwa hakan yasa ya bude mata kofa shima ya zagaye ya bude ta Shi,Shiga tayi tana mamakin wannan labarin da Umma ta basu,anshe da sun shade wahala.
?? Bayan sun dau hanya ta fada inda zasu,suna tafiya shiru babu mai magana ita tana kalle kalle shikuma yana tuki, katse shirun yayi da cewa'

' Kinsan wani abu?
Sanin da ita yake ta girgiza Kai,

yace' anfa Bani shawara,kuma shawara ce mai kyaun gaske nake fada maki,

Ganin kamar Yana so yaja da magana,kuma da alama de bayansa shirun nan nata,

tace' Wacce shawara ?

Yace' ahh wacce Umma ta Bani mana,

Tace' dayaushe?

Yace' yanzu da zamu fito,kinga daga yau bake ba fita sai kin haihu,

Kallanshi tayi dakyau tace' sai na haihu kuma?

Yace' yes,of course,idan kin haihu a shekara daya to kina so ki fita idan ma kin haihu a shekara biyu Kinsan fita,Amma Baki haihuba a wannan shekararun bake ba fita,wasu ma har sun manta dake,

Kumewa tayi tace' wai maganar nan dakeyi daga zuciyar Ka take fitowa kokuma daga bakinka,nakasa fahimta,

Yace' zuciya tamana sannan Baki na yake fada ,kinsan ana cewa abinda babba ya hango ko ya hau ina ne bazai hango ba,

Banza tayi ta kyaleshi,har suka karaso unguwar

yace' kinde San ni ba aljani bane da Zan San ko ina ko?

Da hannu ta fara mai kwantance,samun wuri yayi,yayi parking
Kallanshi tayi dakyau
.
tace' lafiya?

Yace' Naga kin Zama kurma,ni kuma banzama ba,shiyasa gwara kawai mu zauna haka,

Tace' amma de kasan ai yamma tayi yanzu ko,kuma yanzu magariba zatayi daman bamu fito da wuri ba,

Yace' to Ashe kina magana haka,

Bata yi magana tama juya tana kallan wani wuri,motar ya tada,

yace' Madam ina muka nufa,
Nuna masa hanya ta fara yi har suka isa, fita tayi ta Shiga gidan da yake opposite dana Maman Sadiq, Sallama tayi aka amsa sai da suka gaisa,

tace' maman Sadiq ce ta aikonj Zan amsa key Zan dau sako,
Zasuyi sa'anni da matar gidan,

tace' eh ta fada min Amma meye sunanki?

Tace' Ummusalma,

Tace' ina zuwa,
Koda Shiga sai ta Kara Kiran maman Sadiq ta shaida Mata, sannan ta dauko key din ta bata,?

Fitowa tayi janye da? trolley dinta da kuma wata jakar a hannun ta, fitowa yayi daga mota ya zo ya ansa jakar ita kuma ta maida key din,
?? Gidan dake kusa da na Maman Sadiq ta kalla da ta Shiga gidan Maman Sadiq taji haniyarsu da'alama ball suke a tsakar gida, mota ta Shiga ta zauna,

yace' kinsan masu gidanne?

Gida nane,tace
Kuma Baki Shiga ba,tace' su yaseer ne fa a ciki,
Kunna motar yayi ya fara tafiya,
?? A cikin wani store taga sunyi parking,

yace' zaki Shiga ne?
Girgiza Kai tayi alamar a,a, fita yayi ya shiga,har ya shige tana kallansa, sannan ta maida kanta jikin kujera ta rufe Ido, ita abin ma Mamaki yake bata wai itace da Miji abinda batayi tsammani ba, gashi kuma ko kadan daga cikin mission dinta bata kammala ba, dole ta dage idan har tana so ta cimma burinta, amma taya zatayi hakan?
Kamar ance Mata ta bude ido ta? juyo wurin windown ta, idan ba gizo idanta ya Mata ba Neena tagani fa, ai da sauri ta bude kofar ta fito sai dai kafin ta karasa har ta fice ta hau a daidai ta sunyi gaba tsayawa tayi tana kallan masu adaidaitar tabbas Neena tagani,dawowa tana mamakin ganinta da tayi Ashe hassashenta daidai ne Kenan ba barin garin sukayi ba,suna nan acikin garin amma ai gari da fadi a,ina ?? Security din wurin ta samu,

tace' don Allah wacce ta wuce yanzu nan daga ita babu Wanda ya fito tana zuwa nan wurin sosai ne?

Securityn yace' taya za'ayi na gane Wanda suke zuwa fa dayawa,

Tace' ehh nasani amma idan mutum Yana yawan zuwa dole zaka Santa,

Yace' munsan wasu ma dayawa Amma gaskiya itade bansanta ba,
Numfashi taja tace' to ku nawane masu shifting din nan wurin?

Mu uku ne,daya bezo ba ga daya can kuma daga ciki, godiya ta masa ta nufi wurin na cikin,Yana zaune taje tayi masa sallama

tace' am wacce ta wuce nace don Allah ko kasanta ? Tana yawan zuwa haka?

Yace' Wacce Kenan Aminatu?
Ita kadai ta wuce ai,yanzu sai kuma Maza da suka fita yanzu,

Tace' ehh Kasan tane?

Yace' ai unguwar mu daya da kafin su tashi, ni kuma ana nake aiki, to gaskiya kwanan ina yawan ganinta tana zuwa kuma indai tazo tana zuwa mu gaisa,indai ina nan.

Tace' to shikenan yanzu zaka Bani numbern Ka duk ranar da na samu lokaci Zan kiraka,
Numbern Shi ya bata tasa a wayarta,ta Ciro kudi ta bashi,sosai yayi godiya mota ta dawo ta zauna har yanzu be dawo ba,
Ji tayi an bude kofa an shigo,gani Shi da ya ajje kayan hannunsa a baya,

Tace'? ice cream,

Yace' da kinsan kina San ice cream kikayi shiru ban siyo ba kuma bazan koma ba, kuma kema bazaki fita ba,

Kumbura Baki tayi tace' da nace Zan fita ne?
Batasan a fili tayi maganar ba,

yace' me kika fita yi? Naga kina magana da wancan security din?

Tace' Neena na gani fa, Amma ban Mata magana ba ta hau abin hawa ta wuce, shine na tambayi security yace tana Dan zuwa akai akai kwanan, shine na amsa numbern sa watakila yasan inda suka koma ko?

Gingina Kai yayi yace' hakan yayi,Amma kar ki sake magana da wani sai da izinina kinji ai?

Daga masa Kai kawai tayi, alamar taji,
Suna tafiya aka fara Kiran magriba, suna zuwa gida wasu masallaci sun idar,Kayansa ta kwasa ta fita da su,bakowa a parlourn sai Tv shikuma masallaci ya wuce daga nan,
? Itama sallah tayi ta zauna tana Azkhar bayan ta Gama kuma ta tashi ta Shiga wanka tana fitowa Yana shigowa da akwatinta bata ma lura dashi ba ita sai da tazo tsakiyar dakin ta ganshi, murtuke fuska tayi ta janyo hijabinta a Kan gado ta rufe jikinta, ta wuce wurin mudubi,

Yace'? ikon Allah, to mene na rufe jikin kuma? Ke kina sani de,ya ajje mata Jakarta har zai fita sai kuma ya dawo ya bude ledar da ta shigo da Shi, comp ya dauko da main kitso da ribbon yazo ta bayanta

yace' tunda Allah ya hadani da wacce batasan gyaran gashi,ni Bari na gyara mata,
Ta jikin mirror take kallansa bata iya musu ba,ita kuwa zata ga ikon Allah Namiji da gyaran gashi.....

By:'''Hijjart Abdoul'''
? ? ? Cwthrt =??A BAKIN WAWA* ? ? _Akanji magana_
? ?





22

Yana Jan Jan Dan ya taje, ta rike hannunsa,sabida wata irin masiffan zafine daya ratsata,

tace' a hankali fa ake bi,

Yace'? Madam a hankali fa nayi,

Wanne hankali kasa duka karfin Ka kaja,sai kace Ka damu gashin doki,

Yace' to naji sake min hannu, zanbi ki a hankali bazan yi da zafi,

Promise?

Promise,

Sake masa hannun tayi,tana kallansa yarda ake kunshe dariya,aikuwa ta Kara hawa gashi yace Mata Madam, ahankali yake bin Kain yarda bazata ji zafi har ya taje Shi tsab,ya kawo mai ya shafa Mata,ya kuma tajewa,ya dauko ribbon,

yace' to ki juyo mana a kulle kinsan bazai dauro ta haka ba,
Batayi musu ba ta juyo shikuma ya daure Mata kai,

yace' kinma fi kyau haka,kyanta kitso aka min,a yarda suke haka sai sun fi kyau,

Tace' ban taba kitso ba.

Yace' to juya kiga yarda na iya gyaran gashi na tabbatar ko ke bazaki iya ba,
Juyawa tayi ta kalli kanta a jikin madubin ta kalle Shi yarda yake murmushi irin nayi abin arziki? nan,

Tace' sai kace wata yarinya zaka min three babies?
Ashe shiyasa yace da kitso ne sai yafi kyau, kallon Shi tayi,

tace' wannan ai damuna zasuyi,

Shidai Yana tsaye Yana kallanta ta jikin mudubin, yarda take cuno baki tana kumbura Baki,shifa abin arziki yayi a ganinsa Ashe na yara ne, kuma fa tasan tayi kyau amma take kushewa shikam Allah ya hada Shi da Mata, a Dan zaman da sukayi da ita ya gane 70% a halayarta.
Sunkuyowa Yayi daidai fuskarta suna kallan juna ta cikin madubi,

yace' kinyi kyau mi precioso,
Ya kaimata peck a kumatu ya fice, murmushi kwance a fuskar Shi,
Kallanta ta dawo dashi wurinsa har ya fice,ta dawo da kallanta ga madubin murmushi tagani a fuskar ta har dimple dinta duka biyu ya lotsa, shafa inda yayi mata peck din tayi tana mai kallan kanta a madubi, Idan aka ce Mata zatayi murmushi nan gaba to zata karya ta mutum,bare kuma ace tayi dariya? Ada tana tunanin yaushe zatayi Kara Jin farin ciki a tattare da ita, sabida? damuwar da take ciki kuncin da bakin cikin da take ciki, shekara bakwai ta ta wuce,a tunaninta ma tayi bankwana da dashi, sai kuma yanzu rana daya kwatsam wani daban yasata dariya alokacin da bata shirya a lokacin da batayi zato ba, dukda shima Yana cikin damuwa ahaka yake danne damuwarsa don yaga annashwarta to ita Akan me bazata danne ta ta damuwar ba itama ta dawo kamar kowanne mutum??
?? Ajiyar zuciya ta sauke,ta cire hijabin da yafawa jikinta ta karasa shafa mai,tana shafawa tana tunano ranar da suka a London har yanzu ta manta inda suka fara haduwa amma Shi kamar ya tuna hakan,
Sai da tagama tsaf ta feshe jikinta da turare, har ta Kai hannu zata cire three babies din da ya mata ko me ta tuna kuma oho ta barshi, wurin trolley dinta ta nufa ta? dauko kayan bacci masu laushi Riga da Wanda? tasaka ta kuma fesa tureranta, sannan ta jera kayanta a dayan side din, ta jera komai da komai,ta zuke jakar ta sata a kasan wardrobe, kayan bakko ta dauko shima ta dau muhimman abubuwan ta, ta rufe ta ajje, ta fita

Suna zaune a parlour ta shigo kusa da Umma ta samu ta zauna da yake Umma a kasa take,
Umma tace' ashe kun dawo ko? Ina sallah,

Tace' eh,

Umma tace' to ki tashi ki zuba maku abinci ni naci nawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login