Showing 30001 words to 33000 words out of 173457 words

Chapter 11 - A BAKIN WAWA (AKANJI MAGANA) COMPLETE

30 Oct 2025

3954

kwanta don tafiya kam na fasata, Zan fadawa su umma.
Anty tace' ai wani satin Suma zasu dawo, Basu fada maka ba?
Yana tafiya yace' Basu fada min ba da sai dai naje kuma mudawo.
Itama bata Kara maganaba ta dawo ta zauna, kasancewar a three seater suke da space a tsakanin su,Zama tayi a tsakiyar su ta daura kansu a shoulder dinta tana shafawa

tace' kudena damuwa Insha Allah komai zai wuce,kamar ba'ayi ba ,kowa da irin kaddaransa,kuma bazamu iya tsallake kaddaran mu ba,duk abinda kukaga yafaru da bawa an rubuta zai faru dashi ne tun kafin yazo duniya, bacin ga haka kaddara tana cikin rukunan Imani, kun tuna da haka?
Bata jira amsar suba taci gaba da cewa,walau me kyau ko marar kyau,idan kuka ga bawa Yana da kudi,kada kuyi tunanin Allah ya fifita Shine Akan wasu a,a Allah Yana jarabtar sane yaga taya zaiyi amfani da kudin? Ta hanya mai kyau ko akasin haka, idan kuma kuka ga Bawa Yana cikin talauci shima jarabtace,shin zai iya rike talaucin sa ko kuma zaiyi wani abun da zai sabawa Shari'a. Allah Yana jarabtar mu ta hanyoyi da dama, batare da munsani ba, Idan Allah ya jarabce mu da kowacce iri ce fatanmu mu mutu Mina masu dacewa .
Haka Allah yasa kuma Haka yaga dama , Allah yasan hakan Shi yafi alkhairi,Amma acikin 100% kalilan ake samun masu fada. Abinda nake so daku shine ku kwantar da hankali ku kunji ko? Bana San hankalin ku ya tashi,ina sanku tamkar 'ya'yan da na Haifa a cikina, daku da ummu duk daya ne a wuri na, a haka ta cigaba da lallashinsu tun suna kan shouldern ta har suka zame suka kwanta a cinyarta,wata nutsuwa na Kara Shigar su tanayi tana shafa kansu har sukayi bacci.? Hakan yasa ta kalli ummu Wace ta zauna a kasan kafarta ta daura kanta kan center table itama tayi baccin.
? ?? Ajiyar zuciya ta sauke ta jingina da kujeran ta rufe idanta, wata kwalla taji tana zubo Mata,aduk sanda ta tuna da wani babban al'amari,tasan duk Daren dadadewa dole Gaskiya zatayi halinta. Hannu tasa ta share hawayen,ganin lokacin na tafi yasa ta ajiye kansu a hannun kujeran, ta tashi ta Shiga kitchen don daura abinci.
? ? ?? Basu farka ba sai bayan Azahar, bayan sunyi sallah suka ci abinci,sosai suka ware kamar ba abinda yake damun su, sai da magariba sannan suka koma gidan su,suna Shiga suka ga Mama tana zaune tana kallo kuma tana? waya, Zama sukayi Suma suka Dan fara kallan, Mama ta kallesu,

tace' ya hakuri kuma?
Yusuf ne yace' hakuri an gode Allah mama,
Yaseer kuwa kawai kallansa yake me yafaru kuma, Yusuf kuwa ganin irin kallan da yake masa na irin karka bada mu,beyi aune ba yaji yaseer nacewa" mama kin ga yarda yayi mutane kuwa, Kai mama Allah yasa muma muyi? kyakykyawan karshe , daman fa Shi ba ruwansa, kuma Yana Karatun Qurani ya rasu, gashi ma kuma, maraya ne Akayi adoubting din shi iyayensa sukayi, amma haka suka rike Shi tamkar dansu, Koda suka haifa nasu, sun cigaba da sansa, Hmmmm ai ba'acewa komai mama,
? Kallansa tayi tace' Ya sunansa kuma,
Abdul sunan sa ai, munji mutuwar nan ta girgiza mu,?? mama, ni har na fara komawa ma ga Allah,yaseer yafada,

Yusuf yace' kuma mama wallahi idan kinga yarda suke sansa ca zakice dansune,muma bamu saniba sai a wurin mutuwan nan mukeji,munyi mamaki sosai, Akan wani shikuma da ajimmu da rikonsa ake,
Ya kalli yaseer yace bata labari,
Yaseer kuwa

yace' ai mama ko wallahi mutane suke Jin tsoron Allah,shikuma wai fa rikonshi fa ake don kawai babansa da mamanshi? sun? rasu, sai ya koma gidan kanin mahaifin Shi to matar gidan bata bashi tarbiya, ta batashi ga kashe kudi,tun muna js2? ya fara shan taba, yanzu kuwa tsabar abin yayi nisa har club yake zuwa abinsa,kuma ba kullum yake kwana ba a gidan, ai lamarin Shi gaba yakeyi, ga yanzu india zai tafi,hmmm Mama tsoron duniyar nan nakeji,
Yafada Yana dan share hawayen kamar gaske,
?? Mama kuwa tunda yaseer yafara take hada wata uwar zufa, taab ashe itama ta tafka kuskure fa a rayuwar ta, ita har mantawa ma takeyi da abinda ta aikata,koda yake bazata taba kiranshi kuskure ba, ba abinda ma ta aikata ai.
Kallan juna sukayi Yusuf

yace'? Mama lafiya kuwa?? Ko Baki da lafiya ne ?
Bata ji shiba ma itakam ai ta lula duniyar tunanin shin daidai ne abinda tayi ko ba daidai bane?
Suma tashi sukayi suka Shiga daki suna Shiga yaseer

yace' wai ca kace wa mama mutuwa akayi ne?

Yace 'ta shigo kana wanka tace me yafaru taga idona yayi ja haka kamar Wanda nayi kuka? Shine nace mata ai wani abokin mu ne ya rasu shine fah,abinda nace Mata,Kai kuma da tuni ka kwafsa mana dan ma dai ka iya tsara zance da Kai da waccen parrot din Bansan wa fi wani ba.
Yafada Yana hayewa kan gadan, tambilin yayi a gadan??

yace' Mama fa ta tsorata wallahi,
Kawai ya saki dariya,

Yace' wai Kai yaseer sai yaushe zakayi hankali ne ? Baka da aiki sai dirifkiya a kan gado ko? Du kabi ka sawa mutane ciwon jiki,banza kawai,

Ikon Allah,wai Dan Allah dame ka fini ne,da shekara dayan?

Koma da second daya ne na fika de,kuma dole a kirani da yaya Yaseer a toh,

Kai Ka sani,mutum de bazai kirani yaro ba tunda shekaru na 16,16 kuwa ai ba wasa ba.

Dariya kawai Yusuf yayi ya tashi ya Shiga toilet.

? ?
Hajiya wannan itace mai aikin naki,kamar de yarda na fada maki ita din kurma ce,tana ji Amma bata iya mayarwa,
Kallanta Hajiya tayi ganin yarda take kalle kalle yasa ta daka Mata tsawa

tace' ke kurma,
Dukda taji ta,Amma ko gezau batayi ba,kawai tana kallan girman parlourn da za'a ce kullum sai ta share tayi mopping,tunanin irin ciwon bayan da zatayi kawai take yi.

Kara daka Mata wata tsawan tayi sai? a sannan ta jiwo ta kalleta,

Hajiya tace' kinaji na ina maki magana,
Girgiza Kai tayi alamar a,ah,kallan iya ladi Hajiya tayi

tace' bacin rashin magana harda na rashin ji ma,ni kuwa bazan dauka ba ki sanar da ita tam.

Itakuwa Ummusalma a zuciyar ta tace idan nayi maganinki zakisan Bana ji Bana magana ai.

Kuma yanaga fuskarta a murtuke bata fara'a ne? ko kuma saban iskanci ne?
Iya ladi ce me bada hakuri,daga nan ta sallame ta, sannan tace ta kaita dakin ta,Wanda yake bayan jikin gidan amma kofar ta waje ce window dakin kuma daya a ciki zaka iya hango parlour dayan kuma a waje,garden zaka hango. Katifa ce kawai a dakin sai pillow ba bedsheet bare kuma a samu blanket sai wata munafikar wardrobe? ta jikin bango siririya da ita, Allah sa Akwai toilet adakin, iya ladi ta kalla,

tace' haka Zan zauna ba abin shimfida? Ba bargo?
Iya ladi tace' Bari naje na tambayota, naji ko za'a samu.
Batajira amsar taba ta fita,tana nan tsaye kuwa saiga ta tadawo da bedsheet sai karamin bargo mai laushi, itakam a ganinta daga bedsheet din har bargon ba Wanda yamata,Karba kawai tayi a rashin babu,kudi ta kawo ta bawa iya ladi sosai tamata godiya ta fice.
?? Bayan ta Kara kallan dakin,babu K'ura a ciki da'alama ana gyarashi, Ghana most go dinta tasa acikin wardrobe din, daga kasa taga tsintsiya da Dustbin karami sai parker, toilet ta shiga shima ba laifi dukda ba bathtub Amma akwai ruwa, kuma akwai kayan wankewa.
Fitowa tayi ta Kara share dakin tsab sannan ta shimfida bedsheet din,ta zauna abakin katifar,tana Zama ana kiranta,
??
? ? Hajiya tace'? sunanki salamatu ko?? Daga Kai tayi, taci gaba to aikinki a gidan nan shine gyaren Parlourn nan, Dana Sama,sai abin da ba'a Rasa ba,muna da mai girki da wanke wanke, sannan Bansan kazanta ko kadan kina ji ai?
Daga Mata Kai tayi alamar ehh,
To tashi ki Bani wuri, sum sum ta tashi ta koma daki, jakar kayanta ta dauko ta ajje lungun katifar,ta bude ta Ciro wayar ta, missed calls din maman Sadiq ta gani, kasancewar sunyi exchanging phone numbers,kiranta tayi bayan sun gaisa maman Sadiq

tace' maganar gidan nan ne mai gidan yace dari takwas zai Saida,gidan kuma karami ne ,kuma dakunan a jere suke,kamar namu na da,

Ummusalma tace' Shikenan bakomai,Zan turo maki kudin idan yaso sai a mayarshi Bungalow kamar naku? Amma two Bedroom nake so,
Shikenan ba matsala,

Tace' account numbern karki manta,
Daga nan sukayi sallama,

Kwanciya tayi Akan katifar tace' tunda nake ban taba kwanan katifa ba sai yau,
Tasaba tajita a Sama tana juyi yanzu kuwa sai dai tajita a kasa idan batayi wasa Bama taji ta mirgono kasa, tana zaune? har magariba sannan ta tashi tayi alwala tazo yin sallah ba abin sallah, fita tayi ta ga bakowa a parlourn tsaki taja ta dawo ta cire dankwalin ta tayi sallahn dashi, tana nan har Akayi Isha, Jin tafara Jin yunwa yasata tashi,tana nade dankwalin, ganin kamar mutum yana zaune a garden yasata lekawa,yana zaune ya lumshe idan sa ya daura kafa akan Akan table din da dayake na gossiping chairs din, tana kallan Shi kasancewar windown da yake facing kuma da haske sosai a wurin shiyasa ma bata kunna fitila ba, matsowa tayi jikin window tana kallansa, damuwace sosai a tattare dashi, kuma da'alama mafita yakeso ganin yanda yake karkada kafarsa da kuma bubbuga hannu sa da yakeyi, bata San iya adadin lokacin da ta dauka tana kallansa ba kamar yarda shima baisan adadin lokacin da ya dauka a wurin ba,sai da yabar wurin itama ta juyo ta ajje dankwalin kanta,ta fita don cin abinci, kitchen ta Shiga tunda daman sai tabi ta kitchen zata Shiga cikin parlourn warmers din ta bude taga sauran abincin kadan ne ya rage,don haka ta zauna taci ta koshi ta kora da lemu harda cake abinta, ta koma dakinta har zata kwanta tadawo ta rufe kofar ta bar key din a jiki, kayanta ta cire tasa yar rigarta ta kunna fanka,ta janyo wayar,tana dannawa taga time 11:45,ita a tunanin ta yanzu bai wuce 9 ba haka,tayi mamaki sosai, contact ta shiga taga numbern su Yusuf batasan ta Yusuf ba batasan ta yaseer ba duka yusseer tasa masu,sai ta ummu kuma,sai numbern su chatty da glip ta 9ja,da maman Sadiq,sukadai ne daman suka bayawa ba ,sai number sahr da wurin aikinta shikenan contact dinta, what's app tayi downloading ta bude, badan komai ba sai don kawai ta ga su yusseer yasata budewa, aikuwa de tana shiga sunansu taga Dukan su online,
Batayi masu magana ba ta kashe tayi addu'ah sai bacci.
? ? ?
?? Washegari da wuri ta tashi? ta shirya ta fara aikinta, tas tas share ko ina ba ha'inci ba komai ta gyara ko ina da ko ina har windows ta buge,tayi mopping sannan tasa turaren wuta ganin burner da tayi a parlourn sama,ta rufe ko ina ta Kara fesa air freshener, ta kunna na tsinke kuma,sosai gidan ya dau kamshi mai dadin gaske,ta kunna ac, sannan ta shiga dakinta,tana zuwa ta baje a kan katifa ta gaji over gabadaya jikinta ciwo yake abinda bata Saba ba sai dai tayi kadan, janyo wayar ta tayi ta duba time ganin Tara saura yasata Kara gyara kwanciya, sai bacci,
? ? ? ?? Sosai gyaran yayiwa Hajiya kyau a zuciyar ta, abinci aka kaimata ganin tana bacci yasa aka ajje mata, bata farka ba sai shadaya,ganin abinci an ajje a gefe yasata Shiga wanka,bayan ta dau sabulun ta.
?
Abincin ta bude bayan ta shirya, chips da kwai da bread sai shayi,shayin kam ya huce shiyasa kawai taci chips da kwai, ta kwashe ta kai kitchen.

Ahaka tayi wata a gidan bata fita ko nan da waje sai dai zubar da ruwan mopping amma bade ta zauna ba,daga daki sai parlour shima tana gamawa take komawa daki, Hajiya kuwa zagin da take Mata kuwa ba'a magana,har wani yar Rama tayi daman gashi ita ba kiba ba, kuma kullum cikin bambamta Kaya take bata taba sa complete Hajiya tayi mitar tayi masifar a banza beyi aiki ba ,kuma idan tasa zani saita tattarshi yadawo Sama kauri a waje, ba abinda ya dameta,wataran tana Shiga dakunan su Duka? ta gyara sosai yanzu kuwa ta Saba ma da gyaran da masifar Hajiya bama Hajiya kadai ba duka yan gidan basu da mutunci ko kadan har abokiyar zamanta kuwa.
A zaman ta da Hajiya da kuma kishiyarta yarda suke abunsu babu kishi ko kadan na zahiri, ga kuma duk lokacin da suke zance suna ganinta zasuyi shiru,ranar da sukayi Baki taje kaima su lemo sunayin zance tana shigowa,sukayi shiru, bakin ne suka ce ita wannan bata sallama idan zata shigo wuri ne ko yaya? Hajiyar ce tace' ai kurma ce bata magana,
Dayar bakuwar tace ai irinsh ake so a masu aiki,kinga ba Wanda zaiji sirrin ki,tana fita kuwa ta labe, taji abinda suke cewa,tundaga ranar take yawan Shiga dakin Hajiyar,itama Hajiya tadena wani boye boye ko ta ganta,sai wani yare da? takeyi abinta, hankali kwance.

? ? Yau aiki take Amma ba kamar kullum ba bayanta ke ciwo sosai,alamun period dinga na gab,babban tashin hankalin ta be wuce yarda bata da pad ba,kuma ita ba magana ba, kuma bata Jin akwai wani shago a kusa,dauriya kawai takeyi, yau ko turaren da take sawa ma bata saba,so kawai take taje ta kwanta,ko zata ji saukin abinda take ji, saukowa takeyi ahankali hannunta rike da bucket din da tayi mopping, sai da taje tsakiyar steps din ta rike bayanta da dayan hannunta dayan kuma tana rike da bucket din tana cikin tafiya sai ji tayi tayi tuntube da bucket rufe ido kawai tayi tana jinran taji zafin fadowar da zatayi,Amma Jin kamar an riketa kuma ga wani sanyayyen turare da take ji yasata bude ido fes ta sauke idan ta cikin nasa, dukda ba rokota yayi ba,tokareta? yayi da hannunsa Duka biyu,
Kallanshi kawai take kamar yarda shima ita yake kallo, babban abinda yasa bata fita kenan bata so su hadu,dukda ita tana yawan ganinshi a garden? , shikuma tunani yake me yakawota gidan su,mekuma takeyi? Dukda kallan da sukeyiwa juna hakan be Hana su wannan tunanin ba, yayinda zuciyar ta ta fara abnormal bugawa sakamakon wani yanayi da ta tsinci kanta aciki,shima hakanne a wurinsa, sun jima suna kallan juna yayin da idan ta kifta ido sai yaji an tafi da numfashin sau dubu, Baiki su dawwama a haka ba,

?? Hajiya ce fa fito don zuwa kitchen ta hado Breakfast ganin su ahaka yasata ta saki wani ihu tare da salati,

tace' na Shiga uku ni Hafsatu mezan gani??
? ? Banaifu Kaine rungume da? mace haka a kirjinka, lahawwala wala quwwata, jama'a ku fito kuga abinda idona yake gane min,

Shikuwa bema San sanda ya rungumo ta din ba abinda yasani kawai yasa hannu ya tokareta kar ta fadi Amma yanzu sai ganinta yayi a Kan kirginsa, ganin da Hajiya tamasa baisa yasaketa ba,kuma be kalli hajiyan ba sabida wani irin haushi da yaji ,ta katse masa Jin dadin sa,ita kuwa Ummusalma kunyan duniya ce ta rufe ta,tunda tazo duniya wannan kadan ne zatace taji kunya,Amma bata wani nuna ba a fuska, expression din be nuna ba, sai motsi take alamar yasake ta,Amma ko gezau beyi ba sai ma Kara kallan ta yake yarda take motsi da baki,da kuma kifkifta ido sai abin ya bashi dariya, kawai yayi murmushi.

By: ```Hijjart Abdoul```
? ?? Cwthrt=??: ? ?? _Akanji magana_


Not Edited
POST 2020
REPOST 2023




? ? 13

Ihun da tayi ne da kuma salati yasa kowa fitowa daga daki,suka fito Suma cirko cirko sukayi suna kallan ikon Allah,
?
Hajiya tace' Alhaji nasha fada maka daman yaran nan ga abinda yakeyi,to har masu aiki ma be ragaw ba,bin matan ma shi har cikin gidan ma zai zo ya maka Shi,
Anty(kishiyarta) ta karbe da

cewa' indai sune na Saba kamasu da wannan shegiyar ifrituwar kazama kurma kawai,
? ?
Wani irin tafasa zuciyar Daddy keyi,wai dansa? Shi mamaki yake,gashi kuma yau har cikin gidan sa, yana rungume da yarinya,kuma ganinsu besa yasake ta ba,
Cikin wata irin murya ta bacin rai Daddy

yace' sai nace kasaketa zaka sake ta ne?

Murmushin dake Kan fuskar sa be bace ba,don maganar ma da sukayi zai iya cewa beji ba,sai da daddy yayi magana, ita kuwa taji komai,kuma tayi mamaki furucin Anty akanta, Ashe itama ta tsane ta haka?
Ahankali ya saketa Yana cigaba da kallanta,kamar jira take kuwa yana sakinta tana fara tafiya sai dai ko taku daya batayi ba,santsin ruwan da tayi tuntube da bucket din ya zube, ya debe ta zata fadi don saura kiris taje kasa yai sauri ya tarota wannan Karon har sai da ya tsugunna kadan,
Sakinta yayi ya gyara Mata tsayuwa,Tana Shirin tafiya Hajiya ta Kira

tace' ina kuma zakije,kurmar yar iska,shegiya munafika, kina kurma kina iskanci,.dawo nan bangama dake ba
Daddy yace' ke tsaya zuciyar Shi kawai tafasa take,duk abinda ake fada masa Akan dansa yau ya Kara tabbatar wa dakansa hakanne.
? Bema iya magana ba tsabar takaici kawai ya juya ya koma ciki,
Ummusalma kanta a kasa ta dawo ta tsugunna ,Anty

tace' wannan yarinyar mekama da wancan Dan karuwar( Mus'ab) dole daman ai halinsu ya zo daya ai,
Dago Kai tayi ta kalleta sai kuma taji Aneesa na cewa ai itace babbar yar iska ba'a yar iska mace sai namiji, idan bakiyi wasaba wallahi zai Kai ya baro musha suna abin mu, yafada tana shigewa,
Tasan inda maganar su ta dosa,maimakon ma taji haushi,sai wani murmushi takaici da tayi,iya zuciyar ta,abinda yake damun Tama kadai ya isheta, Abu kadai ne ya bata haushi a zaginsu cewa glip( mus'ab) Dan karuwa, ahaka suka kare Mata zagin kare dangi,suka koma daki,itama tashi tayi, ahankali ta juyo don tafiya sai dai kuma ganinshi da tayi rike da moper Yana mopping wurin don har ya goge Kan step din Yana goge kasan parlourn abin ya bata mamaki,saukowa tayi ta nufi inda yake,ta Mika hannu don ta karba,maimakon ya bata Saima jeho Mata tambaya da yayi

yace' me yasa kika Zama kurma? Bayan nasan ba haka bane?
Kallo daya tamasa ta dauke Kai,takara kawo hannunta zata amsa mopper ya kauda ita daga wurin,

Yace' tambayanki nake, ko sai na Kara maimaita wa?
Gani kawai yayi tayi hanyar kitchen don tafiya dakinta, sororo ya tsaya Yana kallanta, har ta shige kitchen Sannan ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login