Showing 162001 words to 165000 words out of 173457 words

Chapter 55 - A BAKIN WAWA (AKANJI MAGANA) COMPLETE

30 Oct 2025

4037

"Mama kome zaki fada min Zan fahim ce ki sosai".

Tsab ta kwashe komai ta fada duk da ta sani amma bata katse ta ba har barin cikin ta da tayi har samun wani cikin da komawan Rukayya gidan ta anan tayi shiru haweye na zuba a idan ta da'alama ta tuna abu mafi girma shiyasa ta zubar hawaye.

"Dawowar Rukayya gidan yasa na dena aiki ita take yi idan kuwa zanyi to tare zamuyi shakuwa Mai karfi ce ta Shiga tsakanin mu harta kai da bama maganar da Hausa sai da fulatanci babu abinda take so irin taga na haifi abin dake cikin na ga wata irin son yayan ta da take yi haka shima Yana san ta wannan abin yasa aka hadawa Rukayya tarkon sata Hajiya kuma ce ta hada wannan abun ba kowa ba hakan ya mugun bata min rai kuma nasan Hadi ne tun daga nan ya dena Kula ta sosai duk wani Abu Idan aka nema aka Rasa sai a zo dakin da take kwana za'a same shi tun yana Mata magana har yazo ya dena ko ta gaishe Shi Baya ansawa bata taba fada ba ta rike abin tsakanin nida ita har ciki na yayi girma yazo watan haihuwa muna zaune kullum da irin abin da ake fada masa muna cikin damuwa sannan ni kuma Bana iya fada masa sabida wannan zurfin cikin nawa da beda amfani ko kadan.
Kwatsam wata Rana da daddare suka zo? lokacin har na fara bacci dayake ba a daki na yake ba ranar suka tashe ni ita da kawar ta Hafsa tace zabi biyu zasu bani na farko idan na haifi yaran nan zan tafi na barshi su zasu Kula dani za'a nemi ni a rasa na biyu kuma idan na haife Shi ban tafi ba zasu yi ajalin abinda na Haifa sannan kuma suyi ajalin Alhaji sannan kuma suce nice nayi wannan abun. Nasan zasu aikata hakan yasa na yanke hukunci tafiya na barshi a ranar da na haife shi ina fito wa da ga asibitin aka dauke ni aka kaini can wani gida Ido na a rufe aka ajje ni gidan gidan kasa ne daki daya ne sai ban daki ba kitchen ma ko baranda babu ga zafi gidan a haka nayi rayuwa ta gidan ya kwarabe musamman da damuna amma sai dai suzo suyi faci facin sa da kasa suyi gaba duk wata suna aiko min da kayan abinci sai dai kadan ne Baya isa na wata dayan sai dai na can cana haka Ida ana ruwa babu inda zanyi girki sai dai nayi daki na sha wahala ni kadai tun ina damuwa har nazo na dena hatta ruwa shima na wata ake kawo min har na wanka da komai da komai fita kuwa kulluma a kulle nake sannan suka ce bani ba fita duk ranar da na fita to nayi ajalin yaro na da hannu na".

Anan ta tsaya ta goge hawayen ta.
tace, "gashi yanzu bansan wanne hali rukayya take ciki ba bansan ko ta shirya da yayan ta Mai son ta ba bansani ba ko yaran ta nawa? Allah sarki Rukayya she did a lot to me, Iyaye na kuma nasani Suma zasu ji haushi na sosai bansan ya zanyi ba ga yaya na".

Shiru sukayi Ummusalma ta Rasa abin fada ta Rasa taya zata ganar da ita cewan ita ce tasa aka dauko ta aka dawo da ita nan, ko kuma tace itace matar yaran ta ba yau ta tsici bakin ta yayi nauyi shikuma Binaif abinda yake tunanin akan ta daban ne dana kowa besan sabida tsananin son datake masa ya rayu bane hakan ta faru, numfashi taja ta ajje sannan.

Tace, "Mama ina ganin Anty ummi taji komai shiyasa ta dauki yaran ki ranar da kika haife Shi ta Hana kowa koda tayi aure tare dashi ta tafi ta bar kasar da shi ita ce ta reni shi har ya girma sai dai Allah be bata yaro ko Daya ba sai yaran da rike sannan kuma sai dai muyi hakuri".

Cikin mamaki take kallan ta kafin.
tace, "taya kika san itace? Bamma fahima ci inda zancen ki ya dosa ba".

"Mama wata Antyn Mijina ta taba bani labari irin yarda kika Bani komai naku shiyasa nasan kece kuma nasa itace yarda na fada maki haka ne naji labarin ta".

"Amma ke to Wacece?"

"Mama zaki san komai, amma Dan Allah kibini mu tafi".

Mama zatayi magana taji wayar Ummusalma na Kara shiyasa tayi shiru bata yi magana ba ga kuma Pretty da ta fara kuka, kawaici tayi ta ta daga wayar ganin Binaif ne".

Yace, "kina ina haka? Baki ce zaki jima ba ya kama ta kidawo fa".

"Nace to ko zaka zo Ka dauke mu, muna gidan Mamaan Sadiq".

"To ganin but wait, ba kukan Pretty nake ji ba bazaki dauke ta ba?"

"Wayar Ka ce tasa ai".

"Irin wannan Marta bawa haka? Zaki biye ni zuwa jibi ai ganin nan".

Murmushi kawai tayi ta kashe wayar mika ita mama tayi ta ansa gaba Daya sai taji kunya ta kama ta takasa shayar da ita a gaban ta. Haka nan Mama taji yarinyar ta burge ta sabida kunyar ta.

Tace, "ki bata mana sai kuka take amma ki Dan rarreshe ta tayi shiru kadan ba'a san shayar da yaro Yana kuka Sosai ki tashi ki Shiga parlour".

Tashi ta wuce Kan ta a kasa sai da dan rarreshen ta sannan ta bata ta koshi sai bacci goya ta tayi ta fito ganin tana wanki yasa ta je ta fara taya ta wanki ba yawa da wuri suka gama.

Mama tace, "gaskiya ba lalle bane na biki Bana san wani abu ya sami yaro na".

Murmushi Ummusalma tayi kawai bata kuma cewa komai ba ta tashi zata tafi Kenan wayar ta tayi Kara ganin shine yasa ta daga.

Yace, "ina kofar gidan Ku fito".

"Ka shigo to ni ina gidan kusa dasu Ka shigo nan din me farar kofa nan please!"

"Ohh! Keko?"

"Please".

"To ganin nan".

Dayake bayan sunyi wankin ciki suka koma ita kuma a waje tayi wayar shiyasa itama ta koma ciki sauko da pretty tayi ta kwantar da ita ita kuma mama kitchen ta shiga ta kawo Mata snacks da lemu.

Tace, "kiyi hakuri ko ruwa ban kawo maki ba".

Murmushi Jin kunya tayi tace, "laa bakomai dayake ai daga gida nake shiyasa".

Mama tace, "nikam ina Shan kunya sai kace wata sirikar ki".

Murmushi ta kuma tayi ta, tace, "Mama inaga gashi nan yazo zaku gaisa".

"Tou! Jeki shigo dashi Bari na dauko mayafi"

Tashi tayi ta fita ita kuma tayi hanyar waje bude masa kofar tayi ya maka harara ita kuma tasa dariya kawai tayi gaba da sauri ya shigo Yana kwafa har parlour ya shiga ya zauna a kusa da pretty sannan ya dauke ta.

Yace, "kawai ki kafa ajje ta a gidan mutane salan ta fado ta fasa Kai".

Waro Ido tayi tace, "yarinyar da ko cikakken juyi bata yi?"

Harara ya balla mata, murmushi tayi murmushi kasa kasa tace, "wallahi zanyi Zama na a gida ko na tafi Adamawa nayi wayon arba'in acan sannan nadawo".

"Naji wannan".

"Yarda fa".

"Banyi ba".

Shiru ganin Mama ta fito da murmushi a fuskar ta ta karaso zata zauna Kenan ya dago dan ya gaita da ta gaisuwar da ba'ayi ba Kenan kowa ya kame ita kuma zaman da batayi ba sai ma Kara Mike wa da tayi.

Kama biyu take hangowa a fuskar Shi Daya kamar ta Daya kuma kamar Wanda ko mutuwa tayi ta dawo zata gane shi shikuma babu abinda yake hangowa sai tsantsan kamar shi ga kirginsa da yaji Yana wani irin dokawa kamar ya fito zuciyar sa wani irin sanyi sanyi yaji tana yi sai faduwar gaba haka nan yaji ya kasa dauke idan sa Akan ta itama haka.

Ummusalma tace, "Mama Zaikai ga Baban Mai sunan ki".

A tare suka maida Idan su Kan ta
kowanne da alamar tambaya a fuskar Shi.

Binaif yace, "mekike nufi Kenan? Wannan ita ce kika Sawa pretty?"

Gingina Kai tayi alamar tabbatar wa.
Lineage Ido yayi ya Bude cikin a kanta.

Yace, "a'ina kika samu ta? Mene hadin mu da ita".

Kanta ta mayar kasa tana wasa da hannun ta.

"She's your mother".


Ba shiri ya mayar da kallan sa ga kanta itama Shi take kallo sun jima a haka babu Wanda ya iya magana daga bisani.

Yace, "Nasan kin san komai kin kuma san dalilin barin ta ta barni bayan Anty ummi tace min ta rasu please tell me everything".

Mama kuwa takuwa wurin Shi tayi tana kallan sa hawaye na zuba a idan ta ita de ko ba dan ta bane da gaske zata ke daukan sa yaran ta har ta bar duniya, kawai ta rungume Shi shida pretty dake hannun sa? lumshe Ido yayi ya Bude su akan Ummusalma dake kallan su. Jin yarinyar ta fara motsi alame zata tashi yasa tayi breaking hug din sai anan yani bugun da zuciyar sa take masa yaji ta dena sai wani sanyin dadi Mai kama dana Jin dadi dake ratsa jikin sa.

Ummusalma tace, "a lokacin da su Mas'ud suka bani labarin su tare da naka haka nan naji ban yarda su Hajiya ba hakan yasa na fara aiki a gidan saboda abu biyu na farko sabida Kai na Biyu kuma saboda idan ina aiwatar da komai nawa babu Wanda zaiyi tunanin nice sabida ina aiki a gida.
Zuwa gidan sai ya zama naji abubuwa da yawa Dan game da Kai da Maman ka, sannu a hankali nagane duk wata duk wata suna zuwa wata anguwa duk da wata na Daya a gidan da satittika nagane hakan sabuda zancen da suke yi ga kuma abina suke kulla maka wani zancen ba da Hausa take ba da yaren Bole take kasance war ta yare sai akayi sa'a na iya yaren sanda ina junior sosai kuma Dana ji sai naji ban manta ba duk wani abu da za suyi nasan dashi har business din da Daddy besan sunayi ba nasan suna yi ita da Anty da taimakon kawar su Bari na gidan sai ya Zama na bana Jin komai sai dabara ta fado min na nasa iya ladi aiki a gidan take dauko min maganar su idan da Hausa sukayi zata sanar min idan kuma da yaran su tayi zata yi recording ta kawo min a boye a haka har wata yayi ranar da za'a kai mata nasa Saminu Wanda suka ce su yusseer suka bita har gidan a daren kuwa aka? dauko ta aka kawo ta nan".

Shiru sukayi kowa Yana kallan ta ta dago ta kalli Binaif tace, "Sanka ne yasa ta tafi bar Ka bata a lokacin kana tsananin bukatar ta San ka ne yasa tayi haka bakomai ba babu uwar da zata haifi yaran ta ta tafi ta barshi a ranar Ka godewa Allah Ka samu Anty ummi wacce ta rike ka a matsayin uwa".

Wani hawaye ne ya digo daga cikin sa a diga akan Pretty yarinya sai ta fara kuka irin tana taya Baban ta kukan farin ciki kallan yarinyar yayi ya tashi ya kai mata ita sannan yaje wurin Maman shi ya zauna a kasa ya Dora kansa akan cinyar ta sai kuka kasa jurar kukan sa tayi ta tashi ta fice daga gidan ma gaba Daya ta koma gidan Maman Sadiq tana zuwa Ummu ta karbe ta ta goya ta Zama tayi itama ta fara ci abinci.

Neena tace, "ina kika je?"

Harara ta zabga mata tace, "inda kika aikeni".

"Haba Salma Dan Allah wai tunda muka hadu fa babu wani zancen arziki da ya taba hada mu wai laifin me nayi maki Dan Allah".

"Mtsww tambaya ma kike? Bakiyi komai ba".

"Haba dan Allah idan dande naganki har sau dayawa ban maki magana ba kiyi hakuri komai ya wuce ai yanzu".

Banza tayi mata bata amsa ba wato har sau dayawa ma ta ganta amma ba magana hakan yasa ta Kara kume wa da ita kadai tasan tayi abin ta sai da maman Sadiq tasa Baki sannan tace ta hakura.


Mama kuwa itama kukan take ta kasa hanashi bare itama ta Hana kanta,dakyar ta samu.

tace, "kayi hakuri Abdul am sorry".

Kukan ya tsayar ya dago Yana kallan ta, goge mata hawayen yake yi itama ta fara goge masa a tare suka sakar? wa da juna murmushi.

Tace, "yaro na Ka girma ko?"

Murmushin Jin kunya yayi ya dauke Idan sa daga gare ta, ya maida kan sa cinyar ta ya kwanta yasa da'a ce Anty ummi ce Kan sa zata fara shafawa haka ma Ummusalma sun San abinda? yake so, murmushi kawai yayi ya lumshe Ido.

Tace, "bansan irin godiyar da zan yiwa matar Ka ba ban san mezan ce mata. Amma Ka rike matar Ka dakyau ta Kai duk inda ake so mace ta Kai ya hada komai kuma ta maka komai ba kowacce bace zata ji labarin Ka ta shigo cikin rayuwar Ka ba amma ita tayi hakan, Abdul idan ka butulce mata baza ta Kara yarda da kowa ba ka, itace ta silar hada mu, tasa sunana tun kafin ta hadu dani, and Abdul Karka biyo ni halina na zurfin ciki beda amana beda dadi sai cutar da Kai da wauta da sa mutum nadama duk Mai irin halina Ka bashi shawara da ya dena".

Shiru tayi bata yi, sannan ta kawar da duk wani Abu da take ji.

Tace, "labarin Ka fa".

Murmushi yayi Idan sa a rufe yace, "labari na Mai dadin jine amma labarin ta beda dadi ji sai dai na Baki shi idan zaki ji".

"Nace bazan ji ba? Ina san ji".

A hankali ya bata labarin ta tsab har kawo haduwar su da Iyayen su komai ya fada mata.

"Allah sarki sai gashi yanzu kamar ma ba'ayi ba haka rayuwar take".

Dagowa yay ya kalli inda take ganin bata nan yasa Shi maida kansa cinyar ta labari suka shiga yi be fada mata anty ummi ta rasu ba sai dai tana san tambayar sa amma tayi de shiru sai aka kira magriba suna nan sai dai idan an Kira sallah suje suyi tare suka ci abinci tana bashi a Baki du sai yaji wani iri be sababa Amma da matar sa wannan normal ne kawa ita din ce be sa ba sai Duka gama.

Yace, "ya kamata mu tafi nasan ana ta kirana wayan na mota ki taso mu tafi".

Baza ta iya musu musu ba tace, "to Bari na hada Kaya na".

Yace, "wanne Kaya kuma Mama? Ki Bari kawai tunda gidan zaki Bari".

"Sabbin kaya tasa a din kamin fa kwati har uku kayan sallah ma akwati guda aka min kuma kace na barshi?"

Yace, "to muje na dauko maki".

Sai da suka fito da kayan Duka ya zuba a but sannan ya Kira ta yace su fito su tafi,
Suna tafiya ya Kira Daddy yace si hadu a gidan Baffa yasan su Baba na can tunda safe suka je kuma yasan sai dare zasu koma suna, sude su Neena daga Kaida da Sukayi shikenan Basu kuma ba.

Daddy ya Riga su zuwa sabida Shi a hankali yake tafiya, suna zuwa Kowa ya fita Mama kuwa kallan gidan take tana mamakin ina suka zo su?

Kowa ya fito suka Shiga sune karshen Shiga aikuwa kowa Yana nan har su Fati Umma ma tana nan Daga Binaif sai ita.

Hakan yasa Daddy cewa, "kazo Ka ajjeni anan ina da abin..."

Bama tsayawa yayi ba tashi tsaye yayi ganin wacce yake kallo bakin sa ne ya furta.

"Laihat?"

Sunan da baza ta manta sunan da abin kaunar ta yake yafada Mata Kenan Laihat kowa kallan sa ne ya dawo wurin Ummusalma kuwa Sama ta hau Dan ta huta tayi bacci kafin anjima cikin dare pretty ta tashe ta.

Kowa yayi mamaki sosai da sosai sai da aka nutsu sannan Binaif ya fada musu yarda akayi itama ta fada musu, namma fa kowa ya shiga fada masa sunan sa da waye shi ita kuma kawai tana murmushi sai da kowa ya gama sannan mas'ud ya tashi ya dawo kusa da ita ya zauna a kasa.

Yace, "ni sunana Mas'ud yayan Aljana Salamatu matar bb yaran ki kenan, kuma a matsayi? na sirikin Shi yayar matar Shi baya ce min Yaya har itama sai wani Chatty suke cemin kamar wani cinnaka kuma ko? Na fada maki Mama nanda jibi za'a daura min aure Nima na...."

A tare suka masa rufdugu su uku Binaif da Uncle sai Mus'ab.

Tace, "me yayi zaku jefe Shi haka?"

"Laaaa mama ai indai sune haka suke min da Basu Zane ni Bama? Ai su suke ramar ni".

Murmushi tayi Dan sosai Mas'ud ya birgeta kuma ya Shiga ranta sosai nan da nan suka saba sosai sukayi hira da yaran sannan suka tashi suka hau Sama suka kyale manyan, Baba ne ya nemi da a hada auran ta Dana su Mas'ud tunda gobe su Inna zasu zo bikin zaiyi waya a zo har Baba.

Washegari kuwa sai su Inna sosai anyi kuka anyi dariya sun kuma godewa Ummusalma tare da Iyayen ta Saida komai ya lafa kuma aka hau hira.


Suna Sama suna zaune sai ga Mas'ud da Mus'ab da kayan wasa harda mota ta Shiga irin ta yaran nan sun shigo da ita kowa kallan sa ya fara yi.

Neena tace, "Ya Mas'ud wannan?"

Yace, "dalla ta genios ce ta fara shiga".

Ummusalma tace, "yarinyar da bata fara Zama ba balle ta Shiga a tura shine zaku fara koya Mata gagara ko?"

"Ke 'yar ki ko 'ya ta".

Binaif yace, "Allah ya Baka Hakuri Yaya tuba take".

Zuwa yayi ya dauki yarinyar ya fara daga ta Sama Yana Mata wasa shikadai sai can ya gaji ya zauna.

Yace, "wannan yarinyar Bata dariya ta biyo Aljanar Babar ta".

Ummu tace, "to aka ce maka yanzu zata fara dariyan".

Yaseer yace, "Nima naza ci ai yanzu zata fara Nima nayi nayi tayi dariya bata yi".

Uncle kuwa daure fuska yayi Baya magana, mus'ab yace, "Yaya lafiya kuwa? Naga kayi shiru sai daure fuska kake".

Harara yayi shiru yace, "Duk ba Ummusalma ce ta ja ba? Nida ba haihuwar tayi ba amma azo a wani wannan".

Binaif ne kadai yasan Kan zancen Dan dazu yaje wurin Inni yaji tana masa fada besa kunya kuma matar sai gobe idan an Kai masa ita ya cillo ta yace Baya so, murmushi kawai yayi Yana kunshe dariyar sa Ashe ba Shi kadai bane yake jegon.

Mas'ud yace, "Nifa bangane ba".

"Ina zaka gane Ku kyale ni ko na Karya mutum".

"Allah ya Baka Hakuri Yaya Dan Naga kaima Halin Ku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login