Showing 63001 words to 66000 words out of 173457 words

Chapter 22 - A BAKIN WAWA (AKANJI MAGANA) COMPLETE

30 Oct 2025

4036

eanda akayiwa auren gatan nan basa rike matar da daraja Umma aganina a barshi yayi komai da komai yarda zaiji jiki kudin sa zaiyi kuka kinga idan ya tashi zai rike ta hannu biyu kuma ma Babansa ya fada min labarin ta kinga kuwa wannan ne kadai gatan da zamu bata,Umma mazan yanzu ba irin nada bane nima zan iya yiwa Binaif komai kodan bashi ba kodan albarkacin mahaifiyar sa,Umma kiyi hakuri don Allah,

Jikin Umma ne kuma yayi sanyi da wannan kuwa don wannan tana gani ma nan da aka yiwa wani yaro aure a kusa da ita ma yaran ko wata biyu ba'ayi ba ya saki yarinyar? gaskiya ne auren gata ma yana sawa a ki daraja mace
tace' shikenan to ai kece daman uwar 'da, kuma ki jamasa kunne idan ya kuskure ya tabo ni wallahi sai dai ya wayi gari yaga matar sa a can Ilorin baruwana ni ato,

Haba Umma kiyi hakuri mana kefa ana maki lefi wataran a rasa ma me aka maki don Allah kiyi hakuri ku rabo? lafiya Umma,

Hmmmm to naji,
Daga nan kuma aka fara tattauna yarda zasuyi daman wurin aiki zata je nurse ce kuma sai karfe biyu zatayi shifting shiyasa ma tace zata zo yau din.

A dakin kuwa sosai yarinyar ta burgeta gata da surutu ganin kanta a tsafe gashi kuma tubarkallah dashi yasa tace' ya sunanki?
Yarinyar tace sunana Rukayya Amma ana cemin Ummi shikuma? uncle Binaif haka yake cemin wai Anty Ummi,
Murmushi tayiwa yarinyar tace' sunan maman sa ai kikaci shiyasa yake cemaki Anty,
Yarinyar tace to yanzu tana ina?

Ai ta tafi bazata dawo ba har abada sai de muma mu bita,

To yaushe ta tafi?
Ta jima da tafiya ai,
Tace' kinga Bari na maki kalba ko? Kinga kanki ba kitso kuma karfa Monday tayi a duke ki a school ko?

Da zafi fa nidai bana so ta fada tana niyyar tashi ta tafi janyota tayi tace' a,a Anty ummi zan fa baki alawa dayawa kina so?

Daga kai tayi amma badan tana so ba, tashi tayi ta dauko Mata Allah yasa tana da sauran Wacce ta taho da ita daga London tama manta da ita sai da ta ganta a cikin Jakarta sannan ta tuna da ita.
Bata tayi tace' amma sai kin yarda idan baki tsaya ba bani Kaya na zakiyi, ribbon din da ya sayo mata ta diba tayi tayi mata kamata Mata Kan dashi ta shafa Mata mai, kan yayi kyau sosai gashi mai laushi itama yarinyar har aka Gama batasan anyi ba don alawar ta take sha ba ruwanta.? Kallan kallanta tayi a madubi tace' laa kinga nayi kyau yimin hoto,
Murmushi tamata sannan tayi Mata hoto sukayi wani tare,itama ta cire mayafin kannata a haka sukayi ta hotuna abin su sai da? Goggo safiya tazo tukunna suka dena,

tace' lalle kin ciri tuta irin wannan gyaran kai haka,
Samun kanta tayi da murmusawa irin naji kunyan nan kamo hannunta tayi ta zaunar akan kujera itam ta zauna,

tace' sunana Safiya zaki iya cewa Anty safiya ko sister ok?
Shiru tayi kafin tace' Ummusalma nasan cewan Binaif zai rike ki da mutunci da amana, kema don Allah ki rike shi dahakan,
Dagowa tayi ta kalleta, murmushi tayi tace' selfish ko??
Shiru ta kuma tayi daga bisani kuma,

tace' kiyi hakuri da halin Binaif bani na renashi ba kanwata ce labarinsa kawai nakeji daga wurinta duk wayar duniyar da za muyi sai tace Binaif kaza Binaif kaza tana mutukar San shi, ita tafi kowa sanin halinshi sai kuma ni da take bani labari,Yana da dadin zama idan ka iya zama dashi,wani lokacin Yana da san barkwanci wani sa'in kuma magana ma baya so, baida san kanshi ko kadan sannan idan ranshi ya baci to bazaiyi magana ba koda kuwa yana Jin yunwa kuma bazai je ya zuba ba, haka yake wani irin juyyayyen mutum ne shi, abinda nake so dake shine Don Allah kiyi hakuri da kome zaki tarar ko mekyau ko marar kyau, hakuri shine komai, dan hakuri shine auren ma gaba dayansa musamman na yanzu maza basu da tabbas bazan yabe shi ba don? Yana 'dana? sai dai cikin kaso tamanin haka halinsu yake, kiyi hakuri wannan hakuri Shi kadai zan iya baki shi kinji ko?

Batasan mezatace ba magana zatayi tace ta karba kome? Me kuma take son ji game dashi ? Abinda yake so? Me yake burgeshi ? Kome?? Kallanta tayi ahankali kamar me tsoron magana

tace' me yake so kuma?

Murmushi Anty safiya tayi,
tace' a bangaren abinci Yana san dambun cuscus,tuwo, yadai fi san abincin gargajiya, Zan iya fada maki sauran kya gane da kanki na Baki hint,
Hannunta ta kuma kamawa tace' taso muje parlour,
? ? Parlourn suka koma Anty safiya ta je dakin Umma sai gata da? yar jaka ta fito tana Kiran mai aikin Umma zama tayi tace' sauko kasa na maki kitso, babu yarda ta iya haka ta sauko ta zauna badan taso ba sai don bazata iya musu ba, mai aikin kuwa da? lalle ta fito a hannun ta,

Umma tace' ki mikar da kafar a miki kunshi,?
Shima mikewa tayi aka fara Mata, ummi da tun dadewa ta fito daga daki tana kan kujera tayi nan tayi nan bata zama wuri daya sai kace rainan Maza.


Ji yayi ma zuwa gidan ya masa nisa gabadaya wani tashin hankali yake ciki wani irin zufa ce ta jika masa kayansa babu abinda yake furtawa sai Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, har ahak??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a yazo gida ko jira agama parking beyi ba ya fito ya Shiga gida,bakowa a parlour sai TV dakin Mama ya wuce fitowar ta kenan daga wanka ganin yanayinsa

tace' Alhaji lafiya kuwa?

Yace' wanne lafiya? Mutane ashe daman kawai kiwon mutane suke haka? Yau kinji tambayar da aka min ne? Bazan iya tantance maki tashin hankalin da na Shiga ba,daman da ace ba a gaban su nake ba wallahi sai na shako su sun fada min uban wa ya fada masu wannan maganar, wannan ai tozarci ne,
Fada yake bilhakki da gaskiya,

Mama tace' haba Alhaji Ka fada min me ke faru mana ba wai ka? daureni ba da jijiyata ba, yi min bayani meke faruwa,
Banza yayi da ita ya fara zirga zirga sai da ya lafa sannan ya fada Mata abinda ke faruwa,

tace' Alhaji baka? ganin kawai 'yan adawa ne da basa son ci gaban mu?
Tace' kuma beyasa Ka sai da company bacin bamu da takardu a hannu,

yace' dalilin shine,zamu sami riba biyu kinga ga kudi sannan kuma ga companyn mu zai dawo gare mu, kinga idan na bashi takardun karya da shi zai dogara kuma kinga bayan kwana biyu sai naje da shaidu na kinga daga nan zai dauko waccan takardar a matsayin shaida kuma ta karyace shikenan zai dawo hannuna idan ma ba'a ci tarar sa ba,

Tace' to da kasan da wannan wannan zancen banza zai daga maka hankali kyalesu kawai sai mu dauko 'yar gidan Yaya hajjaty dake Cyprus kaga shikenan kuma ita Salma ba Ummusalma ba,

Jin wannan batu nata yasa Shi cikin farin ciki tuni yama manta da batun 'yan jarida kuma zaiyi maganin su amma ta yaya?

('('('('('('('

Bashi ya dawo ba sai karfe uku na rana? kasancewar yau juma'a akwai cunkoso shiyasa ya jima be dawo ba har uku, gaba daya ya gaji rigar bayan ya cire? ya riko a hannu ya daura a kan kafadar shi dayan kuma ya riko Leda? ya shigo gidan,a Kan kujera ya zube ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya rufe Ido yayi ya bude dakyar ya tashi ya Shiga daki tana kwance kamar me bacci sai dai ba bacci take ba tunanin sa kawai take har yanzu bai dawo ba kuma ta kasa kiranshi kawai sunansa ta zubawa ido wayar a hannun ta take Idan ta a rufe kanta a bude? kitson ya zubo har kafadar ta ta sha riga da wando sun Mata kyau sosai kallanta kawai yake? baima San ya karaso ba sai ganinsa yayi a Kan gado gefen ta yasa hannu ya fara shafa gashinta kanta, a hankali ta bude ido suka hada Ido kasa dauke nata tayi sai ma kara zuba masa su da tayi samun kanta tayi da,

cewa' ina kaje? Baka tashe ni ba?
Bai dena shafa kannata ba cikin muryan nuna alamar gajiya kuma a hankali,
yace' Baki min sannu da zuwa ba zaki fara tambaya ta?

Tace' Baka fada min ba,kuma sannan Ka tafi kana fushi dani,

Hawayefa yake hangowa kwance a idanta yana daf da zubowa. ji yayi bai kyauta mata ba ya fada laifinta atleast yasan zata gyara, ganin idan tasake magana hawayene zai zubo mata yasa ya sunkuya daidai fuskarta ya furta? am sorry,
Ya fada yana lumshe ido,
Tashi tayi zaune tana goge Dan hawayen da zai zubo mata,ta tashi ta shiga toilet bata jima ba ta fito,

tace' na hada maka ruwan Ka kaje kayi,
Ware ido yayi irin really......

By: '''Hijjart''' '''Abdoul'''
? ? ? Cwthrt=?? ? ? ? ?? _Akanji magana_
? ?

? ? ? ? ? ? ? 24

Yace'? thanks,

Haka nan ta ji dadi a zuciyar ta tare da wani farinciki, bayan ya Shiga wanka,itakam tasan indai tana tare dashi ji take gaba daya damuwar ta yayewa take baza ta iya fassara yarda take ji ba, kitchen taje ta zubo masa abinci har lokacin bai fito ba ajiyewa tayi a akan center table din dakin komawa tayi ta dauko ruwa tare da cup ta dawo ganinsa daure da towel yasa ta saurin dauke kanta taje ta ajje zata fita taji ya rike hannunta, gabanta taji ya fadi janyota yayi,

yace' ina zaki kinga mijinki ya fito a wanka shine zaki fita ko??
Fuskarsa? ya daura a kan wuyanta ya zagoyo da hannunsa ta cikinta,

yace' ina magana,

In ina tafara tace' am zan dauko wani abu ne fa,
Tana yi tana kyafta Ido,
Zaiyi magana wayarta tayi kara sakinta yayi taje ta dauko wayar amma yana sakinta tayi waje harda hadawa da gudu, murmushi yayi yaje zai shirya jin wayar na kara har yanzu yasa shi zuwa ya dauka, yasata a silent Chatty yagani a jiki, dauka yayi ya kara a kunne muryan Wanda yaji yasa shi sakin boyayyiyar ajiyar zuciya daga can bangaren akace

" Wai ke kam ina kika shiga ne muna ta kiranki amma kinki dagawa mutane waya ke bazaki Kira ba kuma idan an kiraki Kiki dagawa ko? Kuma Sarai nasan kinga missed calls,

Be yarda ya dage sai masifa yake,amma yasan da tana gabansa bazai iya mata wannan abu Yana farawa ma zai dena,kashe wayar yayi ganin hotanta da ummi? yasashi Kara kallan sosai ko gidan suka zo ya furta,sosai tayi kyau,Kenan Anty ce ta mata kitso murmusawa yayi ya bude wardrobe ya ciro three quarter da? shirt yasaka ya fesa turare wata iska yaji tana shigarsa bacci kawai yake so yayi amma yana Jin yunwa kuma yasan breakfast ne da beci ba,da yaci duk wannan gajiyar ba jinta zaiyi ba, Zama yayi Yana kallan abincin da ta zubo komai biyu ta dauko,aikuwa idan ba'a bashi ba bazai ci ba, ya rufe Ido Kenan ta shigo rike da lemu a hannun ta ajiye,

yace' sai yanzu ?
Yana ganinta da zata shigo sai da ta leka ko ina sannan ta shigo,
Batayi magana ba ta kawo ta ajje? ta janyo plate ta zuba masa abinci itama ta janyo ta zuba sannan ta zuba masa lemu ta tura gabansa tace' gashi,
Ita kuma ta zauna a kasan carpet ta fara ci ji tayi shima ya sauko kasan kusa da ita ya janyo plate dinta ya hade abincin a plate daya ya jingina da kujera,

yace' bazan iya ci ba,idan nagaji bana iya cin abinci da kaina bani ake,
Harda su lumeshe ido, yace' idan kuma ba'a bani a baki ba to har gobe bazan ci ba shikenan sai na fara rashin lafiya, juyowa tayi ta kalle shi yarda ya Jingina da kujerar kallo daya zaka masa daman kasan ya gaji, spoon din hannunta ta dauka ta kai bakinsa,bezata ba sai jin abinci yayi a kusa da bakinsa ai tuni ya bude ido ya zauna dakyau,tana bashi yana aikin kallanta saida? yakusa cinyewa? yaji ya koshi,ta kawo zata bashi ya kalli hannunta shi sai yanzu ma ya lura da lallan da aka mata,karban spoon din yayi ya kai bakinta, ba yarda ta iya ta bude bakin yasa mata,

yace' yau dai da'alama so ake a kashe ni idan ba'ayi wasa ba,
Waro Ido tayi waje ta kalleshi

tace' kashe Ka kuma?

Yace' manta kawai,
Zatayi magana wayarta tayi kara, tashi tayi ta dauko ta dawo ta zauna abincin yasamata sannan ta daga wayar Glip ne

Yace' fav bro ya kira ki wai bakiyi magana ba, kuma baki ma daga ba,

Tace' damuna zaiyi shiyasa ma ban daga ba,

Yace'kuma kin daga kinyi shiru,

Tace' ni kuma?
Sai kuma ta kalle shi dage mata gira daya yayi,

tace' yanzu de menene?

Yace' daman wani albishirne,

Wanne albishir?

Karban wayan Yayi yasa speaker yacigaba da bata abincin,

mus'ab yace' Mun kusa dawowa mun sami aiki a company nan fa,amma sai dai ba aiki daya bane kuma ba gari daya bane ni a Lagos fav bro Abuja zamu zo interview Nanda sati daya shine daman kiran,

Tace' amma naji dadi,

Yace' idan munzo ina zamu sameki?

Kallansa tayi taga ita yake kallo ya miko mata Loma baki,
Daga can Mus'ab yace' ehh ?

Tace' amm idan kazo kawai Ka kirani zanzo na dauke ku,

yace' a,a kema kinsan bb ne zaizo daukan mu ai
Tace' okay sai anjima?

Jitayi ance ehh da yake shine an dau wayar amma ni kuma ko oho ko?

Damuwar ka, headache kawai,

Takashe wayar cigaba da bata abincin yayi saida ta koshi tukunna ya dauko lemo zai bata ta karba tace Zan iya sha da kaina,kaima nasan haka ne tunda ka koshi har kana bawa wani ko?

Murmushi yayi kawai ya matso kusa da ita sosai har suna gogan juna yace' nagaji da yawa bacci nake sonyi kuma ina kwanciya za'a la'asar gashi kuma ba'asan baccin yamma ya zanyi ?
Tashi ta tattare kayan

tace' ina zuwa
Bata jima ba ta dawo wannan Karan ya koma kan gado zama? tayi a gefen gadon ta lankwashe kafa daya daya kuma ta kasa, shikuma rufda ciki yayi ya juya kansa, Ta jima tana kallansa batasan kuma me take kallo ba juyowa yayi don ya mata magana sai dai Jin idanta a cikin idansa yasa Shi manta mezai ce mata, dakyar yasa hannu ya janyota ta itama ta kwanta suna fuskarta juna,shafa kitso kanta yayi,

yace' wa ya maki?

Anty safiya,
ta bashi amsa kamar yarda yayi maganar Shi,jiyayi gaba daya ma ta kara saukar masa kasala, hannunta ya dauko,

yace' wannan fa? Du itace?

Mai aikin Umma,

Yayi kyau sosai,amma meyasa Baki ce ta miki shuku uku ba?

Murmushi tayi tace' shuku uku fa,haba dai sai kace wata yarinya,

Ohh ke yanzu ba yarinyar bace?

Ehh,

Banga alama ba,

Wacce alama Kenan?

Gashi dai kina da miji amma ba'a iya Kula dashi ba,

Shiru tayi tama dena kallansa, yace' okay na gane, baki dauke ni a matsayin miji ba ko,

Girgiza masa kai tayi alamar a,ah,
Yace' shikenan na gane,to yanzu a dauke maganar miji a ajiye ta a gefe ko?

Daga kai tayi irin eh,
Murmushi yayi sarai ya gane kunya take ji,
Yace' to shikenan yanzu de na zama Neena,na kuma zama Yaya,na Zama Baba wannan matsayin na bawa kaina an bani ko na janye ?

Daga kai kawai tayi,
yace' to naji amma dai kin san ba shiru zaki min ba ko? Yanda na bude baki ina magana sai kace wani loro,a loron ma sabo,
Ya karashe tare da gyara kwanciyar sa ya juyo daidai yana fuskantar ta da kyau,

yace' kuma kallan ma an dena ?

Dagowa tayi suka hada ido ta kuma kawar da nata kan, hannunsa dayake shafawa akanta yasa ta tafara Jin bacci dadi take ji idan Yana shafa mata abinka sabon kitso kuma zafi yake mata shiyasa bata sa mai ba bakuma ta daura dankwali ba,

tace' me loro yake nufi?

Kina so ki sani,

Ehh,da kuma mi amor,da mi precious,

Dariya ya fashe da Shi,
yace' mi me? amor? Precious taab, ba ruwana idan suka jiki, idan Banda abinki ai turanci ne precious din,

Kumbura baki tayi zata tashi daga kan gadan sauri yayi ya kamota yace' Am sorry bazan sake ba,

Ba dariya kake min ba?

Nadena yi hakuri kinji mi precioso, mi amor,

To me yake nufi ,

Karki damu zaki sani ne kinji?

Komawa yayi ya kwanta,
yace'? zoki kwanta a kusa da mij..kusa da Neenanki kinji ko? Daure fuska tayi,
yace' nace fa Neena ko? Kawai ki dauka ni itace kinji ko?
Bracelet din hannunta ta dago ta kalleshi sannan ta mayar da hannunta ta koma wasa dashi sai dai idanta da ya ciko da hawaye,matsowa yayi kusa da ita ganin hawayen ya zuba tana wasa da bracelet din,wani abu yaji ya tokare shi ya kasa numfashi,dakyar?

yace' waye? Shi?

Dagowa tayi ta kalleshi abinda ta hango a cikin idansa kadai ya tabbatar mata da kishi yake, murmushi ne yayi escaping a bakin ta,

tace' Ai naga kaine Neena to mene na batan rai kuma ?

Yace' dariya ma zakiyi?
Goge kukanta tayi ta tashi ta bude wardrobe ta dauko Jakarta a cikin ta dauko wata paper tare da zoben da har har yau bai mata daidai ba, zoben ta dauko ganinsa tayi har yaje bakin kofa ya bude ya? fice, itama Jin ana kiran sallah yasata shiga toilet,koda ta idar ta jima akan sallaya ko zata ga ya dawo amma shiru.
Daukan zoben da ta ajiye akan gado tayi ta fita,dakin Umma ta Shiga sallah taga tana yi da'alama makara tayi,fitowa tayi ta nufi kofa ta fita yau kwanan ta biyu a gidan amma bata taba leka tsakar gidan ba,? tsakar gidan ya mata kyau madaidai ci dashi sai bishiyo shiyasa gidan yake iska saboda wadatar bishiyo wani dan lungu tagani inuwa tamasa yawa shiyasa ta bi wurin kamar wurin hutawa don harda su lilo a wurin irin na zaman nan wurin ya burgeta sosai ga kuma shuke shuke harda su zogale da wasu abubuwa batasan suba, Zama tayi akan lilon? tana kara nazarin wurin tana lilawa ahankali daga karshe kafarta ta nade ta jingina da lilo ta rufe Ido iskar na kadata tare kamshin kasa alamar suna samun ruwa sosai.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login