Showing 15001 words to 18000 words out of 173457 words

Chapter 6 - A BAKIN WAWA (AKANJI MAGANA) COMPLETE

30 Oct 2025

3929

ita ta dena taki,ko kallanta ma batayi bare ta tanka Mata ganin haka yasata yin shiru......


?? ~_Nigeria_~

? ? Yusuf da yaseer ne a dakin Ummusalma suna dauka abinda suke so na Zane da kuma hotunansu sosai suke jidar kayan sunayi suna leka window ahaka suka kwashe suka Kai mota suka dawo suna Zama kuwa mama nashigowa

tace, "yawwa yau zamu tashi daga wannan gidan mukoma wani,ku dau abinda kuke so ku dauka,kunji ko?

Kallan juna sukayi suka ce tou
Sama tahau gani Suma tashi sukayi don su haura Saman gani sukayi tana rufe dakin Ummusalma,dakin su suka Shiga, yaseer

yace,"yanzu dabamu ji zamu tashi daga gidan nan ba shikenan ko?
Yusuf yace, "sai kuma Allah yasa munji".

Zama sukayi suna buga game,abinsu
Mama ce ta leko ta gansu

tace, "au wai daman ba haWa kayan kuke ba?

Kallanta sukayi yaseer

yace, "a Kira Indo ta haWa mana kayan mana,ni banzan iya ba".

Ya faWa ya turo baki.

tace, "ehhh tunda Indo ce tasan abinda kuke so ko? To idan tazo gaba daya kayan zata kwashe ta bayar,na bata kayan duka,shiyasa nace ku debe abinda kuke so,kuma Bana San tarkace kunji ni ai?

tafaWa tana barin wurin,kallan juna sukayi sannan suka dauko school bag dinsu suka sa games dinsu aciki sai abinda ba'a Rasa ba wasu ma a hannu suka riko,suka fito,mota suka Kai kayan suka dawo, kallan su mama tayi

tace, "kuje Driver ya kaiku gidan".

Tashi sukayi suka fita. Gidan ya haWu iya haWuwa zaka iya rantsewa ma ba'a ?asar ya?e ba don haWuwar sa? yayi kyau sosai Saida muce Masha Allah,
Sun yaba tsarin gidan sosai kuma ya musu kyau bakadan ba,don harda wurin buga ball,yayi kyau sosai da sosai. Suna gama zagaye gidan suna parlour suna ?ara ganin gidan, Mama ta shigo wannan karan Wakinsu a kasa yake,da parlour aciki sai Dan karamin kitchen da toilet a parlourn,su kuma kowa da dakin shi,sukam sun Saba da Zama daki daya,tunda Basu taba rabuwa kuma basa Jin zasu rabu,fita sukayi suka dauko kayansu a mota,suka dau daki daya suka zuba kayan da suka dauka a dakin Ummusalma,dayan kuma suka saka kayan su anan zasu zauna acewar su.
?? Sosai suke baza hajarsu agidan suna watayawa. Makaranta ma ancanza musu wata sunso ace sai zasu Shiga js2 asake tunda yanzu suna js1 kuma second term Amma a haka aka sake masu,basu so ba,haka sukayi mitar su suka gama,sunyi ?awaye maza da mata abinsu don akwai wata ?ar anguwar su suna cemata Yaya wani sa'in sabida wai sunan Ummusalma ne da ita,ita kuma ba laifi akwai san girma,sosai suka sha?u da ita wataran ma tare ake Waukosu ko akaisu tare,har suka dawo idan aka kaisu agidan wannan to wani satin za'a kaisu a gidan wannan haka suka zama. Kuma hakan bai sa iyayen zumumci ba.........


By: '''Hijjart Abdoul'''
? ?? Cwthrt=??*A BAKIN WAWA* ? ? ?? _Akanji_ _magana_

? ??
Not Edited
POST 2020
REPOST 2023


? ? ? ?? 8

?? A bangaren Ummusalma kuwa balaifi don ita yanzu ta saba sosai da hakan da take,kuma bayan wanke wanke da take a restaurant,yanzu har girki takeyi,takan gani wani sa'in yarda sukeyi da haka ta koya,aikim Zane ma ba laifi yanzu takan zana ma takai ko ba'a ce ba tunda sun fi son zanen nature,kudi sosai takeyi abinta.
Gashi yanzu sungama year one zasu Shiga ta biyu,kusan kowa sun tafi gida sai yan kadan kamar wancan lokacin. Ahaka ta cigaba da zuwa aikin ta kasancewar ta dena zuwa da weekend yasa take karatun da za'a masu nan gaba sosai kuma take ganewa.
Yau ma de tana zaune a bakin campus da yamma tana sanye da wando sai jacket datasa da baby hijab,karatu take yau weekend ba taje ko'ina ba,tana nan zaune taga wani ya zauna a kusa da ita,yana waya kuma da Hausa yake wayar wani sa'in Yana hadawa da Spanish,bata kalleshiba kawai taci gaba da abinda take kallanta yayi

yace' Hello,
Bata tanka masa ba ta dan juyo ta kalleshi da sauri ta maida kallanta ga books dinta saidai gabanta da ya fadi,Amma Sam bata nuna ba,meke faruwa da ita ne???abinda tace a zuciyar ta Kenan,mai fuskar Baba ga kuma mai fuskar NEENA mekefaruwa???
Katse Mata tunani yayi ta hanyar

cewa" hey can I ask u?
Shiru tamasa,sai ma Kara Dan kallansa da tayi,zuwa yanzu taji zuciyar ta tadena bugawa shiyasa ma ta Kara kallansa,tabbas sunyi kama da ita sosai,amma Neena farace bata Kai hasken shiba,shikuma ja kuma jikinshi ya samu hutu, sabanin Neena. Ganin ta tafi tunanin ya kuma

cewa" please,
Dauke kanta tayi daga kallansa ganin haka yasa Shi cewa a fili" To ko kurma ce ne bata magana??
Daman tasan za'a rina indai cewa kurma badaga kanshi aka fara ba,sabida ko haushi ma bataji bare kuma tayi magana.
Joyuwar da zatayi taga ya fara Mata zancen kurame ikon Allah haka ake zancen kuramen?
Ganin irin kallan da take masa na irin mekakeyi?
Yasa Shi sararawa ya Ciro wayarsa ya kira wani bata sai ji tayi Yana

cewa" Nidai yunwa nake ji,ni banga kowa ba,sai wata kurma kuma nayi nayi ta gane takasa ganewa Itakam wannan a kurman ma ina ga ajin karshe ce,
Ita dariya yaso bata wai a kurman ajin karshe ce,hmmm kawai tace,batajin me aka fada amma da duk kan alamu lallashinsa ake,ganin yarda yake hade fuska, kallanta yayi,ya dauke yaci gaba da fadin bazaka gane ba ne yarinyar daman tayi kama da ifiritu gata da manyan ido kwala kwala da su irin na twiny gata da dan wani matsitsin bakinta in fada maka wannan badan kurma bace marar kunya za'ayi inaga ma ko a kurman ma bata da kunya,nifa tana min kama da twiny wallahi,Dan kamar ta baci ma,ya kareshe yana wani ya tsine fuska,
Batasan me aka ce Saida ganin yarda ya hade Rai Ya nuna fada ake masa, bayan ya kashe wayar ya juyo ya kalleta,

yace' yunwa nakeji ki taimaka min kifada ko ki nuna min cafeteria ko restaurant ni bako ne masters aka kawo mu yi nida Dan uwa kuma baida lafiya yana can adaki kuma wai shine? aka kawo mu tun yanzu don an tsanemu please ki taimaka kinga ni Yayanki ne ko? Duk maganar da Hausa yakeyi irin ita tace tana Jin nan yazage yana surutu,ita ta tambayeshi me yakawo shine ko kuma de kawai San asani wai gaida uwar miji a kasuwa,saida ta tattara kayanta na wurin, jakarta ta bude ta ciro wata leda,sai da ta tashi ta? Dora masa a kan ciyarsa,har tayi gaba sai kuma ta dawo

tace' bakai na bawa ba Dan uwanka na bawa.
Kawao tai gaba ta barshi a wurin,Baki a sake yake binta da kallo bai taba tunanin ta iya Hausa ba kuma daga ji ba wai koya tayi ba can dama ta iya,baid daina kallansa ba har ta hau sama ta Shiga dakinta sannan ya saki wata ajiyar zuciya,
yace' Ashe ba kurma bace, Kenan taji duk abinda nace taaab,kawai sai yasaki wata dariya,

yace' Allah sarki ohhh wataran tabbas Zan sha Duka idan na cigaba dayin abinda nake,
Ya jima a wurin Yana yiwa kansa dariya,daga nan kuma ya tashi ya tafi.
? ? Tana kallansa yana magana Shi kaidai Yana dariya, dariyarsa iri daya da Neeena,ita mamaki ma abin yabata duk abinda ya fada akanta bata ji wani haushi ba. Koda ya tafi tajima a tsaye a wurin, balcony ta nufa ko zata sha iska,Zama tayi ta rufe idonta? tana hango abinda ya faru tsakaninta dashi,tashi tayi ta zauna sannan ta kalli kayan Zane jitayi tana sha'awar zana shi,tashi kuwa tayi dauko kayan ta fara zane,mutane Biyar? ta zana, kuma duk sai taga suna kama da juna, sunaye ta saka asaman kowanne,Neena ce ta farko sai Baba sai AA da? Chatty(Wanda suka hadu) sai ita kuma a karshe,kallan Zane ta tsaya yi,tabbas sai yanzu taga kamar su suna kama da AA sosai haka nan da Baba Neena kuma nakama da Chatty,ta jima tana kallan wa'yanna fuskokin, zuciyar tace ta fara saka bata wani abu da sauri ta kauda tunanin tana girgiza kai,tana cewa bazai mata ba iyuwa ba hakan baza faru ba. Tana zaune a wurin har lokacin magriba, tashi tayi tai sallah tayi karatun Qur'ani, har lokacin Isha, fridge dinsu ta duba ganin bakomai lemo yasata Jan tsaki,kuma ita yunwa takeji gashi tayi burgar aiki ta bayar da nata, da hijabin jikinta har kasa ta ta fita Wanda tayi sallah dashi, tafiya take a hankali harta iso cafeteria, tagama? siyan abinda zata siya juyowar da zatayi kuwa sukayi Karo da Chatty lemon dake hannunshi ya zubar Mata a hijabi shi besan ita bace kawai ya dago zai bada hakuri har ya bude baki sai kuma yayi shiru ya tsaya kallanta

yace' Baki iya bada hakuri bane ?
Gani take idan ta kuma dagowa ta kalleshi to ai matsayi yasamu,ko kallo bai isheta ba,ta sa Kai tazo zata fita,ji tayi an riko hannunta, a masifen ce zata masa magana saidai ganin Wanda ke rike da hannunta yasa gabanta faduwa,ta zuba masa na mujiya kawai tana kallansa,shima ita yake tabbas wannan badan ita kadai taji an Haifa ba zata iya cewa dan biyunta ne sabida kamar su ta baci ba kadan ba,komai nasu iri daya banbamcin sa da ita kawai tana da tusar jaki shikima bai daita ta fishi karamin baki,ta kuma fishi eyelashes,wata zuciyar ce tace Mata kawai kama ce bakomai ba,sannan ta sauke wata Ajiyar zuciya,shima kallanta take kuma besaki hannunta ba,

yace' Ina mai baki hakuri da abinda fav bro ya maki dazu da kuma yanzu kinji?
Yarda yake magana zaka san baida lafiya,gakuma hannnun Shi da ya riketa,zafi kau dashi,ganin tana kallansa yasa dayan?

cewa' in fada maka bazata maka magana ba ai,wannan da Ka ganta tafi BB miskilaci wallahi gwara ma ka kyaleta Ka barta,kar Allah yasa ta hakura din,daman bani na Baki hakuri ba shine ,
Kallanshi tayi bata ce komai ta ajje ledar hannunta ta sa hannun ta cire hannunsa batare da tayi magana ba tayi gaba ta kyalesu,tabe baki Chatty yayi

yace' dakai daga fada maka kamanninta shikenan sai Ka gane ta kallansa yayi

yace' yarda kabani labarinta,yarda kayi ta fada Mata magana bata tanka ba nasan itace wannan ganin yarda ka bata Mata hajibi kuma kayi magana Amma bata tanka ba.
Dariya yayi Yana Zama

yace' Kai mai tsoron Mata ne fa da ace ta tanka maka akan abinda Ka Mata dazu,to yanzu idan hakan ta faru nasan da da gudu zaka bar nan wurin,ya karashe da dariya sosai Duka ya kai masa ya goce

yace' Kai kuma fa? Har gwara ni ai Akan Kai,ya karashe yana bata fuska,tashi yayi ya fita wai ko zai ganta,Amma bai ganta ba shima fitowa yayi daga nan suka fita.
? ? ?
? ? Tana zuwa daki ko hijabi bata cire ba ta dauko zanen ta ta zana dayan tasa masa glip a sama sunansa. Sannn ta ajje tazo taci abinci tayi shirin bacci ta hau tunanin,ita Allah yasa ma kar su Kara haduwa da su.
*********
? ? Washegari da wuri ta shirya ta fice wurin aiki,wanke wanke ta farayi sannan ta fara taimakawa ana yin abinci, haka sukayi har lokacin tashin su yayi,tana fitowa tagansu zasu shigo,ko kallan inda suke bata kallaba bare su hada ido tayi masu magana, Chatty ne ya hangota zata wuce da sauri yasha gabanta

yace' yawwa wana kama? Dabaki fada min? ? wurinba na Allah basa karewa sun fada min? Glip ne ya karaso

yace' haba mas'ud meye hakan wai?
Kaga mus'ab kyaleni,ni zatayi ma banza ina Mata magana ?
Kallansu kawai take yi,yo ita badan duniya bama da ta sauya mata? akwai Wanda ya isa yadaga Mata murya ne bare kuma har ya tsereta Yana fada Mata magana?
Wani banzan kallo tamasa tare da Jan wani wawan tsaki,ta wuce bata tanka masa ba,ai daga mus'ab din har mas'ud? cikinsu ne ya duri ruwa Basu iya tankawa ba,dakyar mus'ab

yace' kaga ni ko?kaga abinda Ka janyo mana,to wallahi nikam ba ruwana bazan Kara Shiga sabgar taba ato.
Ya wuce Shi ya barshi a wurin,ai kuwa de yasha jinin jikinsa ai,jiki a sanyaye ya Shiga ciki shima,mus'ab sai ya kalleshi sai ya kwashe da dariya,

yace' kaga wata yarinya can jeka ka tambaye ta inda ake Shan ice cream kaji fav bro,
Ya karshe cike da zolaya, lokacin an kawo masu abinda suka bukata,don haka Saida ya fara ci,sanna ya kalleshi ya kalli yarinyar da aka nuna masa sannan

yace' hmmm kai ai Dan bakaraba wallahi,taab nifa nazaci baza iya yin komai ba.
Wai kaga ma kuwa wani kallo da tayi minne?

Awww Kai kadai tayi wa?tayi mana de zaka ce,
Kasan wani abu lokacin da BB yake cewa shiru shiru va tsoro bane gudun magana ne ban taba yarda ba sai yau,

Jibi ita ba magana tayi mana ba amma gaba daya kallan da tamana yasani Jin Kara tsoron Mata wallahi,

Kai ta k??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????allo take tsakin da taja Kai,

Ni wannan bai dameni ba,wannan kallan,kallo ne na irin gargadin kar ka Kara Shiga harkata,
Dariyan mus'ab yayi

yace' to yanzu fav bro mas'ud dafatan Ka dauki darasi ko?
Shima dariyan yayi

yace' darrussa na dauka,ai

Nikam idan mun hadu Zan bata hakuri daga nan sai mu kulla zumunci tunda da 'alma yar 9ja ce kaga shikenan munyi friend mace de ko?
Tunda yafara zancen zuwa da bata hakuri yake kallanshi tou Shi yanzu ko haduwa yayi da ita ai baya jeba taab.
daga nan yace' Kai kadai zaka kulla zumunci ka Amma Banda ni,

To naji nima Banda ni kadai shikenan?
Ehh shikenan ya bashi amsa,sanna yaci gaba

? Amma nifa twiny wannan yarinyace bata fi bama tafi 17-18 bako?

Kaga fav bro idan kun hadu sai Ka tambaye ta shekarunta inaga hakan yafi ai ko?
Ganin maganar yakeso yasa shi yin shiru Yana cin abincinsa,shima mus'ab din shiru yayi ganin ba'a tanka masa ba.

?
Aikin banza suzo su addabi mutane kawai idan ya kuskura ya Kara Shiga harkata sai na nuna masa true colour Dina tunda Shi beda mutunci,
Ita kadai take mitar ta tana juyi Akan gado,zaman dakin ne ya isheta yasa ta fitowa fita wurin dayan aikinnata,sai bayan magriba ta dawo, wanka tayi,tay sallah sannan taci abinci ta dau Qurani ta karanta, lokacin Isha nayi,tayi ta kwanta.
Washegari ta makara sakamakon ciwon bayan da ta tashi dashi, gashi batayi wani baccin kirki ba,haka de ta shirya ta fito, fuskar nan kamar kullum,tana tafiya taji tayi kicibus da abu dagowa tayi don ganin da me tayi gware,shima ita yake kallo, hada ido sukayi babu Wanda yayi tunanin dauke idon sa, fuskar juna suke karewa kallo,tunanin inda yasan fuskar take Amma yakasa ,itama tunanin inda tasan Shi takeyi Amma kuma ta kasa tunowa,
ahankali ta fara janye idonta tayi kasa dashi,bahaka yasoba yaso ace sun cigaba da kallan juna wani irin yanayi ya tsinci kansa mai wuyar fassarawa,ganin tana shirun wucewa yasa ya riko hannunta,sai da gaban ta yafadi,Amma bata juyo ba shima bai juyo ba

yace' can't you apologize?? U don't know how to apologize right????
Tabbas tasan muryan nan kuma yarda ya fada haka aka taba fada Mata,Amma a'ina ???
Batare da ya saki hannunta ba taji? yace' maybe ma
Kurma ce, da fillanci? yayi maganar,kuma taji abinda yace bataji mamaki ba kasancewar? Shigar hausawace? tagani a jikin Shi harda hula kuma yayi Kala da?? Fulanin,
Hannunta tasa ta tacire hannunsa tayi gaba ta barshi Yana binta da Ido,taxi ta Shiga ta barshi a wurin.
Koda taje wurin aikinta dauriya kawai take yi sosai bayan ta ke Mata ciwo indai zatayi period haka takeji,a daddafe ta Gama aikinta har lokacin tashinta yayi,ta dawo hanya,nufar dayan wurin tayi namma yau akwai aiki,Basu Gama sai dare kusan 9pm sannan ta samu kanta shima a hakan sararawa ce Akayi give zasu ci gaba,tafiya kawai take batare da tasan ina zata dosa ba tasan dw tadau hanyar school dinsu,sai ogan su yace zai sauketa tace a'a, tsayawa tayi tana jiran me taxi ganin tafiyar ta gagareta,mota ta gani ta tsayar Shiga kawai tayi ta Fadi inda zataje, har jikin campus ya Shigar da sai da tafito sannan ta fito da kudin Shi zata bashi hannunta ne ya makale ita bata Mika masa ita bata mayar ba,kawai ta tsaya take kallanshi,mutumin dazu ne da sukayi Karo,fitowa yayi ya zagoyo inda take cikin harshen turanci

yace' da sace mutane nake saidai na sace ki ko? Meke damunki haka?
Ganin bata da niyyar magana yace' wannan motar ta maki kama da taxi ne ?
Bata kulashi ba sai maida kudinta tayi jaka tana neman tafiya da sauri ya riko hannunta

yace' sunana Abdulshakur,ana Kirana da Binaif,sai Naga kamar na taba ganinki Amma ba anan ba zan iya sani??
Hannunta ta cire daga hannushi cikin Hausa

tace' kar Ka Kara tabani,
Ta juya ta barshi a wurin, tabbas ya Santa kuma ya tuno inda yasanta,Amma abin mamakin da ai bahaka take ba meya faru ta dawo shiru shiru haka??
?? Yana nan tsaye ya daga waya yayi kira, fitowa yayi daga cikin campus din ya samu wuri ya zauna ya Dan jima a zaune sai ga su mus'ab nan sunzo,sun jima kuwa suna bashi labarin abinda ya faru bai nuna musu ya Santa ba har suka gama bai kuma yi magana ba.


Tana Shiga daki wanka tayi taci abinci sannan ta kwanta,sai da ta kwanta tafara tunanin shi,
Abdulshakur tace,meyasa ta manta inda ta sanshi? Tashi tayi ta zauna ji tayi? maganar sa tana dawo mata inda yace meke damunki?? Lumshe ido tayi ta bude ba'a taba tambayar abinda yake damun taba,koda can data ke ganiyar kan mulkinta babu Wanda ta taba tambayar damuwarta,haka sahr da suke kwana su tashi tare bata taba ganewa ba sai Shi?? A,ina ta sanshi? Ganin baccin ya gagara yasa ta tashi ta leka window hango su tayi sunsa Shi a tsakiya suna ta maganar su, dariya suke Amma bandashi ga dukkan alamu ya tafi duniyar tunani ne,kallanshi kawai take bako kiftawa, bata San metake ji ba idan tana kallanshi amma koma mene ne hakan Yana Mata dadi sosai. Tashi taga sunyi zasu Shiga mota,kamar yasan ana kallanshi kuwa yatsaya ya kalli saitin windown ta,tasan de baya kallanta sabida filar daki a kashe take, shiyasa ta tsaya,ya Dan jima Yana kallan wurin daga bisani kuma ya tafi.

?? ('('('('('('
? ? ? Tun daganan bata Kara haduwa da suba hakan ya Mata dadi bakadan ba,bata kuma son Kara ganinsu,musamman Shi da tun sanda ta daura idan ta akanshi take fama da tunanin sa, har aka dawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login