Showing 90001 words to 93000 words out of 173457 words

Chapter 31 - A BAKIN WAWA (AKANJI MAGANA) COMPLETE

30 Oct 2025

3945

ku, zaiyi maki amfani, kuyi masa addu'a Allah ya bashi lafiya itace kawai addu'ar,

Shiru yayi yace' yanzu kuma itama taje tayi Mata kukan, hmmm,

Yasa Kai ya fice Jin ana kiraye kirayen sallah, sun jima a wurin don sai da aka kusa idarwa sannan suka tashi suka tafi, a masallacin sukayi alwala Dan kar ma su Kara makara.
Saida sukayi Isha sannan suka dawo 'yan gidan sun handeme a parlour damma yanzu sun warke Amma Aneesa har yanzu kugunta ciwo yake, darurarta daya Allah yasa ba illa ya jawo Mata ba, suka shigo suka wuce kowa yayi dakinsa, a kusan tare suka fito,yau bejin San Jan mota shiyasa yabawa Mus'ab key din yaja shikuma ya Shiga Baya, ya lumshe Ido so yake kawai yajita a jikinsa wata kasala yakeji da kewanta yarasa wanne daga ciki ya rinjayi daya, idan sa a rufe sukuma sunyi shiru ko radio babu balle waka damman Shi ba kunnawa yake na kar gwara radio Yana saurara, har suka isa yayi parking sannan suka fito parlourn Baban su Nafisa suka Shiga na bangaren ta ganin parlourn ta da Baki shiyasa suka wuce suka Shiga,Anty safiya ta gansu kuma sai taga kamar wani Abu nadamun su,ta taso Dan taje taga kiranshi, tashi tayi ta Shiga parlour gaisawa sukayi,

tace' lafiya?

Binaif da ya kwanta yace' lafiya qalau yunwa mukeji kawai ASA akawo min abinci su inaga sun koshi,

Mas'ud yace' haka muka ce ma?

Yace' haka nagani de,

Anty safiya tace' to Bari masa Nafisa ta hada maku ni nayi Baki,

Tashi zaune yayi yace' Nafisa kuma? Ina take ita?

Sarai tasan wayake nufi tace' kaga ni Bani da wata gidannan kowa Yana da sunan shi Bari naje,

Tatashi tafita, mas'ud da Mus'ab kuwa hada Ido sukayi suka basar Sarai ya gansu ya koma ya kwanta ji yayi ma Shi ba dadi wallahi, Shi kadai yaka fa Jan tsaki,ya jima beja tsaki ba daman,aikuwa ya fara Mita shikadai a ransa,

Nafisa kuma bata nan tana wurin Hajja Dan yanzu wayancj suna can har itama Ummusalman tana zuwa Amma ba sosai ba,sai dai yanzu suna can su Duka, don haka tayi hanyar part dinta, da sallama ta Shiga, Hajja ta amsa, suka Dan gaisa,

tace' Nafisa tashi kije ki hadaw su Binaif abinci su uku ne Maza ki Kai masa,

Hajja tace' a,a zancen me nakeji? Ina kince min wannan ce matar tashi salamatu?

Tace' ehh itace,

Hajja tace' to iya zata Kai masa,Maza tashi kije ma ki hada masu anan, Nima nayi tuwom ai,

Nafisa tace' kinyi tuwo ko kuma kinda anyi tuwo?

Hajja tace' kome kika dauka duk haka ne,ja'ira kawai,

Badan Ummusalma taso ba itama tashiga kitchen din Hajja Nafisa ta taimaka Mata, ta jera komai a tire sannan ta fito ta kofar baya ta shigo sabida mutune dake parlour, ciki ciki tayi sallama idan sa a rufe har tazo ta dire a gabansa besani ba,sai dai yasan anzo Dan wani kamshin turaren wuta yaji mai sanyin dadi Yana tashi, sai ya Kara lafewa a jikin kujerar, ajjewa tayi zata fita har taje bakin kofa,

Mas'ud yace' ya zaki tafi Baki zubawa mijinnaki abinci ba? Kinsan fa ajebo ne,

Ai bashiri ya tashi zaune Jin ance miji aikuwa itace da Shigar ta ta kulluma bata da Kaya sai doguwar Riga sai kace mai ciki(=??) a yarda yace, dawowa tayi tana gallawa mas'ud harara, ta tsugunna ta zuba masa ta Mika masa,Yana kallanta it's komai nata da sanyi takeyi Amma ta iya fada da sauri har tana kamar ta sarke Dan bala'i, ganin ta miko masa bata ko kalleshi ba yasa Shi kin karba, ganin be karba ba yasata karawa ta mikawa su mus'ab mas'ud ne ya karba tare da daukan spoon,

yace' fav zomuyi nan,
A tare suka fita, Kara zubawa tayi ta Mika masa bata kalle Shi ba, namma kin ansa yayi dagowa tayi suka hada Ido ya kauda kansa gefe,

tace' Ka ansa,

Yace' nagani ai, Amma gani nayi ba'asan naci abincin shiyasa,

Tace' ni banceba,

Nima bance kince ba ai

Gashi kuwa Ka fada?

A,ah nace gani Nayi,Alana nagani ai shiyasa na fada hakan,

Tace' Wacce alama Kenan?

Kinga na farko kinzo ba sannu da zuwa ba gaisuwa ba ya aiki ba ya gajiya ba komai, sannan sai da aka fada maki aikinki tukun kika dawo kika yi sannan kuma the worse ko kallo na ma babu,

Tace' to naji, na gyara ina yini,ya aiki,ina gajiya,kazo lafiya?

Yace' lalle ma ke din nan haka ake ?
Ba fadar sunana bakomai taab, koda yake daman ni fa Ashe Kai ake cemin sai kace Mai karaton kai,

Gajiya tayi da tsugunna da mitar Shi,Zama tayi a kusa dashi,

Yace' kinga?

Menagani?

Ko iya Zama ma bakiya a kusa da miji,

Tace' wai dan Allah ya kake so Nayi ne?

Yawwa ba wahala abin, nakoya maki?

Daga Kai tayi, yace' good, na farko za'a fara da Zama ne,idan zaki zauna to a kusa na zaki zauna kingane?

To yanzu a,ina na zauna?

Taab kallafa ratar ai dayawa,

Nikam nagaji yunwa ma nakeji,

Yace' Nima haka ai,
. Abinci ya dauko ya matsa daf da ita ya debo a spoon yace' haaa

Bude bakin tayi ta zuba Mata Yana yi Yana zuba zancen Shi har ta koshi,shima ya Mika Mata batayi musu ba ta ansa ta bashi Yana Gama ci Anty Safiya ta shigo

tace' yawwa daman ina San na fada maka cewan Umma ta Kira tace gobe na kaita,Kai kuma sai ana sauran kwana biyu sai kaje,

Bata fuska yayi yace' kika ce kuma sai saura kwans hudu?

To ta zanja shawara haka tace da Baka zo Bama tafiya zamuyi, ta tashi ta tafi abinta,

Kwanciya yayi a cinyarta yana kallanta itama kallan Shi take, a hankali tasa hannu ta fara shafa masa sumar sa da har yanzu be rage ba,shikuma ya rufe ido kallan sa kawai take Jin yarda yake sauke numfashi a hankali yasata yi masa peck a goshi,zata dago Kenan yasa hannun sa ya dunkufar da kanta tare da

cewa' ba'a nan ba,

Zaro ido tayi tace' daman bakayi ba bacci?

Yace' Nayi mana wani Abu naji Wanda ya tada ni shiyasa,

Tace'to ni sake min kaina, zaka.....

Jin wani bakon al'amari tayi Yana Wanda ya fi nada,Ashe bakomai Akayi ba.

Bayan sati daya


By: ```Hijjart Abdoul```
? ? Cwthrt =??: ? ?? _Akanji magana_

? ??


? ?Not Edited
POST 2020
REPOST 2023

??
? ? ? ? ? ?? 32

Kawo yanzu abubu sun tafi da yawa zuwan su Ummusalma Bauchi da kuma samun aikin su Mas'ud, komawa makarantar su yusseer Dade sauran Abubuwa, a bangaren Uncle kuma ba? sauki? dan an tabbatar da zuciyar sa ce? ahalinda ake ciki ma ya Shiga comma, du bayan kwana biyu suke zuwa gano Shi Baba da Umma sai Ismail da yaje shima ya ganoshi, kuma baza'a tabbatar da aikin da aka masa yayi ko beyi ba har sai sanda ya farfado sai dai cigaban da aka samu karayar ce kawai take warkewa sabida ba'a taba wa bare a taka,

? ? A bangaren su Abba kuwa ya Sami lawyern Shi ya masa bayani ya kuma biya Shi kudi sunyi duk abinda ya dace,gashi company sai wani cigaba suke samu daga fara aikin su Dan kayan su yana da kyau da kuma inganci Ada ana zuwa 7-7 Amma zuwa Shi ya maida zuwa 8-6 hakan yayiwa ma'aikatan daidai sannan kuma salary din za'ake Basu according to yarda aka samu riba,tunda yau da samu gobe akasin haka,kosa yayi na'am da wannan zancen kuma sun yarda sun gamsu, be yarda da kowa ba bare wani PA shikadai yake gudanar da kudurin Shi masu shawarar Shi su Mus'ab ne sabida beda wani aboki ko daya kuma duk sa'anin Mata ne shiryawa.
?? Su yusseer kuma sunyi neman numbern ta Amma bata Shiga sunje har unguwar data fada masu Amma shiru har tambaya suke da nuna hotan ta a unguwar amma babu Wanda ya Santa a haka suka hakura suka dena nemanta,

? A yau takama alhamis ranar da za'ayi kamu,kamun su iya Mata ne Maza basa zuwa iya Mata ne sai kuma 'yan yaran da baza'a Rasa ba,
Ummusalma da sa'anni ta Wanda duk sunyi aure sai Wanda suke karatu ne basuyi ba, kuma dayake gidan Umma na kauye Family house aka mayar Shi shiyasa kowa yazo jar Baba Usman shima yazo da iyalin Banda Hajiya da Anty har 'ya'yan su? kuwa babu Wanda yazo acewar su suna bikinne Suma ai,? suna zaune a babban parlourn gidan anyi Mata doka an Mata kwalliya irin tasu ta amaren can tasa kayan Fulani, sun sata a tsakiya wannan nayi wannan nayi, Umma itama tana yi don harda ita, itace ma ke Basu labarin auren da, suna dariya daga nan sai a daura zance idan anyi anyi sai taci gaba, ana cikin haka har kazo Kan matsalar idan miji yamaka laifi kar Ka horashi da yunwa kode da wani Abu,

Umma tace' ku tsaya kuji,

Kowa shiru yayi, umma tace' Sanda Malam Yana da Rai idan yamin laifi sai nayi abincin da Baya so, Baya san tuwon dawa sannan Baya San asa nama a cikin miya ko asa wake ba'a daka ba, Baya San wannan, nikuwa idan ya min laifi sai ya kawo namansa na tashi Nayi miyata nasa nama a cikin miyar na kawo wake nasaka a ciki, sannan Nayi Tuwon dawa abuna,
Shiru tayi tace' Allah sarki bawan Allah haka zai kwasu yunwar sa daga kasuwa wani lokacin ma hae cikin Bauchi yake zuwa ya dawo Amma hakan idan na kawo Yana murnar zaici sai yaga abin da Baya so,haka zai zauna sai ya tsince wanken tsa ya dauke Naman sannan yaci, nikuwa ina kallansa ko magana Banayi,
Tace' Kai Allah ya jikan malam,

Ameen duka suka amsa,sai dai Dan hawayen da suka ga tayi namma fa aka fara tsokanar tuno da sahibi, shiru tayi ta kyale su sai can,

tace'? Sanda ina 'yam Mata bana daukan reni duk kauyen nan an sanni Bana wasa gani jarababbiya shiyasa kowa yake gudun masifata naki auruwa nikwa ko a jikina sai Malam,Malam Yana da hakuri sosai, Allah ya Baku 'ya'ya masu hakurin Shi,

Suka amsa da Ameen, Kiran wayar Ummusalma? akayi yasa suka bata dayake sunyi hotona shine ake tura Mata, karba tayi ta tashi ta fita daga parlourn shima de tsakar gidan da mutane yasa tayi bayan parlour lokacin har ta katse, Kira tayi, daga can bangaren akace," tazo gidan, kuma naji suna maganar karshen wata yazo,

Tace' wanne kalar Kaya ne a jikinta?

Lashi ne sai Hijabi kalar ruwan madara sai nikaf,hijabin ba dogo bane, iya Ka gwiwa ne,

To idan ta fito a kirani,

Shikenan Insha Allah,

Bayan sun kashe tayi message sannan ta,
tace' kuyi Maza kuje ku inda na tura maka da address din zakuga wata Mata ta fito daga gidan tana sanye da lace sai Hijabi milk da Nikaf kuyi Maza kar ta fito,
Bata jira amsar su ba ta kashe wayarta, A fili ta furta? Allah yasa hassashena? gaskiya, Ya Allah help me,

Koda ta dawo sai gani tayi an Kara cika a parlourn,sulalewa tayi ta Shiga daki,shima dam yake da jama'a ita tarasa gane wannan taro ko ina kayi da jama'a,duba sauran dakunan tayi dake cikin parlourn suma duk hakane, fitowa tayi ta bi wani lungu sai taga kofa 'yar karama, aikuwa ta Shiga taga parlour da kofa guda biyu acikin sai wata kofar kuma babba ce da'alama ta waje ce, sai ta Shiga ma ta tuna zuna Zama a ciki dakin Umma ne, aikuwa ta fada dakin da suke zuwa su kwanta mafi lokuta da rana, shine mai ac haka Umma zata a su kunna solar idan na nepa suyi barcin su daman ba aikin da suke yi,
Dakin ma data Shiga duhu hasken kadan ne Wanda ba'a Rasa ba sabida safe? safe ne Rana Rana ba yamma ba an kulle ko ina an saki labilaye an kunna ac ga kamshin air freshener dake tashi a dakin, aikuwa ta cire abinda aka murde Shi aka daura Mata da mayafin, ta ware zanen Saman kayan bata da daure Shi ba kawai ta barshi,ta hau gado tayi kwanciyar ta bata jima ba bacci ya dauke sabida kamshin dakin da dadin sa ya Mata dadi.

Acikin gida ana ta neman Amarta kowa yana so ya ganta kafin a yamma a fita kamu Amma ba'a ganta ba,

Wata daga cikin yammatan tace' to aje a duba dakin da Daddy mana da muke Zama ko taje can,

Umma tace' ke kam Indo Sam bakya rabuwa da shirme mezataje tayi kuma bacin Maza yau sunzo mijinta ma yau yazo Shi,da tun jiya zaizo bezo ba da na kirashi jiyan namasa Karan dangin shine yau da sassafe yazo min gida, ita tasan inda ta tafi,daman na lura da ita Sam bata da San mutane sai wani nokewa take wai ita kunya, sai kace tsohuwar muna fikar da tayi sata ana nemanta,

Wata tace' Kai Umma yanzu idan tayi dariya ace bata da kunya,yanzu ma da take Dan nokewar tana nuna kunyarta sai ace Mata munafika? A munafikan wacce tayi sata, Haba Umma mana,

Wata tace' ni wallahi Sam tunda tazo banga wani aibun taba, bata da musu Sam wallahi,

Umma tace' to sai ku titsiye ni,tunda Hajju ta dawo da Rai( mahaifiyar ta)? yo idan? ba hajju ba waye zai maida min magana iye?

Wadanda sukayi magana shiru sukayi Basu Kara ba, wata tace'? hmmmm rashin musunta na banza a Bari ta Shiga daga ciki mana mugani,ai yanzu biyayya zata keyi,

Wata kuma,ai ni wallahi banyarda da ita ba a London fa akace tayi karatu kuma tazo ta har kauye ta zauna tayi sati wajen biyu ma a kauye? Haba de ai da sake wani abun kawai suke nema,

Umma bataji suba tashi tayi ta fita neman Ummusalma, sukuma suka ci gaba wannan yayi wannan yayi, suka ci gaba da abin su, daga karshe, suka cigaba da wasu? harda sharri a dangin miji,

? Dangin miji ba'a iya musu >?&?
@&?

Wayarta taji tana Kara bata ga Mai Kiran sosai ba ta daga Jin ance ga ta nan ta fito yasa ta wartsake ta tashi zaune, tare da kashe wayar,ta Kira tace' ga tannan fitowa a mota civic red,ku Shirya kar ta gane ana binta ko kadan ko alama karta gani,
? Ta kashe wayar,ta ta kwanta sosai baccin ta yayi dadi, gashi anzo an katse Mata ki Azahar ba'ayi ba, kwanciya tayi ta rufe Ido, ya fara daukanta Kenan taji an bude kofa an shigo an mayar an rufe a hankali ta bude idonta gaban ne ta doka ganin Wanda ya shigo, dakyar ta hadiyw yawo ta kulle idanta kamar mai baccin gaske,shikuwa bema Kula da ita ba, gajiya sukayi da yawo shine ya dawo gida, rigar jikinshi ya cire ya rataye ta ya zauna da singlet da Wandan rigar, juyowar da zaiyi ya ganta tana bacci hankali kwance? kitson ya masa kyau,ita kanta ma ta masa kyau din,gadan ya hau ya kwanta kusa da ita sosai, Allah ya taimake Shi don tunda safw da yazo Umma ta hana Shi ganinta sai gashi yanzu tazo har dakinsa kuma yasan batasan da zuwan shiba da tasani bazata zoba, kwanciya ya gyara ya daura kansa a pillown ta Yana kare Mata kallo, ita dai gabanta ne kawai yake faduwa Addu'ar ta Allah yasa kar idanta ya kifta, a hanlyya sunkuyo daidai fuskarta ya daura bakin Shi a Sama nata,a sukwane ta bude ido ta kwalalo su, yarda tayi yasa Shi dariya Amma beyi ba sai da ya Gama abunsa muryan can kasa kasa,

yace' wannan zuwa gaisuwa ya min dadi,
Da wani irin murmushin yayi maganar,

Daure fuska tayi ta kauda kanta, juyo da fuskarta yayi,
yace' sai da aka gama zaki daure fuskan?

Shiru tayi babu amsa, zata tashi yayi sauri ya danneta da rabin jikinsa ya daura kanta a kirginta gaba Daya ya saukar Mata da nushin Shi,
? Dakyar tace' kana da nauyi fah,

Yace' Ba ina maki magana Kina yimin shiru ko kuma ki kumbura fuska ba?

Shiru tayi batasan meza tace ba, yace' kuma Baki ita bada hakuri ba,

Tace' to Ka....Ka..wannan...imm...ka... ha..ku...ri..

Yace' taam haka ake bada hakuri? Idan an hada fa Duka ca kikace Kaka wannan imm hakuri,
Yace' taab ban amsa ba,

To kayi hakuri,

Sai dai na roka shima hakurin ko?

To ai nabaka,Ka dagani dakyar fa nake numfashi,

Yace' a,ah bazan daga ba,

Ya ma Kara gyara kwanciyar sa
Tace' Wayyo kirj.......
Sai kuma tayi shiru,bata karasa ba,

Yace' mene?

Sarai yagane me take nufi Amma ya basar,

Tace' da zafi Ka danne ni Ka daga ni Dan Allah,

Ina yake maki zafin?

Tace' cikina ne, kuma sosai,

Ayyyaahhhh sorry,

Tashi yayi Yana cewa raguwa kawai, itama tashi tayi tana sauke numfashi,

yace' Yana ga kin canza ne? Ko de nan zamu dawo da Zama?

Indai zaka zauna Zan zauna,

Hmmm naji Wannan,

Baka yarda ba?

Nace fa naji,

Batayi magana ba sai ma mayafinta ta dauka zata yafa
yace' Ina zaki je?

Kumbura Baki tayi batayi magana ba sai da ya yafa zata harta sa kafarta zata sauka ya fardota ta dawo?? ta tsorta ainun sabida yarda ya fincikota,

Yace' ba ina maki magana kin min shiru ba?

Marairaice fuska tayi tace' kayi hakuri Dan Allah bansan me zance maka ba shiyasa,

Kada Kai yayi na irin zamu hadu, tace' Dan Allah sake ni na tafi, yanzu haka ana ta nema na a cikin gida,

Sakinta yayi ta dauki dankwalin ta da waya ta taje bakin kofa zata fita,tasamu kanta da juyowa ta sakar masa wani kasallalan murmushi na kwantar hankali ta fice,
Tunda yake da ita bata taba yin wannan murmushi ba, ya tafi dashi, yanzu ma daurewa kawai yayi ya barta Amma yaso ace bata Shi ba sun kwanta tare Shi kawai yanzu wannan kamshin yake so, na jikinta.

Ita kuwa lallabawa tayi ta ta wuce cikin parlour har daki dukda akwai mutene Amma dayake da mutene ba lalle ne a lura ba,can gadan ta samu dan waje ta kwanta kamar me bacci, bata jima ba kuwa Umma tashigo tace' wai har yanzu Salamatu Amarya ba'a ganta bane?

Aka fara ba'a ganta ba,tashi tayi
tace' Umma gani fah,
Harda su kalar bacci irin daga bacci na tashi,

Umma tace'

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login