Showing 87001 words to 90000 words out of 173457 words

Chapter 30 - A BAKIN WAWA (AKANJI MAGANA) COMPLETE

30 Oct 2025

3932

acikin gidan su,tunda suka taso suke fuskantar matsala, tafiyar su Spain ya Dan lafa suna dawowa komai ya cigaba, daga karshe suka dawo gidan Kakar mu ananne suka Samu freedom bayan an koresu daga can gida,

Murmushi kawai uncle yayi Yana cigaba da kallan su,
Wani Abu ya fito da Shi a cikin Dan box box din ja ce mai ba'a kuma ganin abinda yake ciki, ya mikawa Binaif

yace' wannan abun shine abinda aka gani acikin towel din da aka yar Dani bayan sun duba sun gani Ka rike Ka hada Shi da takardun wajenka, maybe zaiyi amfani gaba,

Meyasa Kai bazaka rike ba?

Inaji kamar wani Abu zai faru,kamar wani Abu zai sameni, godiya ta ga Allah dayace dayasa na ga 'yan uwana da yasa nasan gaskiyar komai, Ka rike Shi a wurinka abun Yana da mukulli amma babu key din haka suka ga abun, ko ya fadine Basu sani ba, box Mai kyau gashi karami kamar na zobe na zobe ma yafi girma karba yayi yasa a aljihu bekara magana ba daga nan, suka zuba musu Ido suna kallan su. Waya akayiwa ganin Baba yasa Shi dagawa,

yace' Baba an wuni lafiya,

Daga can ummu tawaikwayi muryan Baba irin shine din nan,
tace' Lafiya qalau yarona,

Yace' ummu ranki zai baci, fa

Tace' Uncle saban labari su besties sun dawo fah tunda safe sai ga su sunzo Amma fa Wanda yasa ce su ne ya kawo su sannan kuma Ance kar Abie yaji donmma Kar yayi wani bincike kasan halin Abie da Dan Karan bin kwawwafi daga karshe de yaushe zaka dawo, Amma idan zaka tafi can London tana nan zaka wuce sannan kuma Kai daya zaka koma Allah sarki My Uncle,

Yace' kekam Ummu bazaki canza ba ko? Daga dawowar su har kindawo normal,yanzu bakin Anty zai fara ciwo,

Laaa kaga ni bazan iya Bama kwasar su zanyi inkai su gidan Hajja yalwa itace babu ruwanta ko fada bata maka idan kayi lefi sai dai

tace' yanzu Kaine kayi kaza kayi kaza to kar ka kuma Zan Zane Ka idan kayi,
Cikin sanyi take maganar shiyasa itama tayi magana yarda takeyi,

Murmushi yayi yace' hmmm ba ruwan keda Umma idan taji ki,

Yaushe zaka dawo de,

Gobe Insha Allah zuwa rana haka? Zan dawo

Tace' Haba de Rana ai yayi nisa dayawa ina laifin zuwa safe haka kayi break fast anan dakaina Zan girka maka abinda kake so,

Shikenan Zan duba nagani,idan nazo akwai labari dayawa,

Kai Amma naji dadi sosai sai kazo idan Ka zo kamin waya da wannan wayar Baban, Amma kace ni kake nema Kar Ka Kira Shi ku fara gaisawa kaji ai?

Numfashi yaja yace' Naji second mom din na,
Sannan sukayi sallama murmushi fal fuskar Shi,

Ummusalma ce tazo ta zauna tace' nagaji dayawa,nayi gudu, tana sauke numfashi,

Mus'ab ma zuwa yayi ya zauna shima, mas'ud kuwa wasan sa yayi tayi da yaran sai da Iyayen su suka zo suka dauke su sannan shima ya dawo yana Nishi,

Binaif yace' ku tashi mu tafi gida magariba ta gabato,

Mas'ud yace' sai da kukaga nazo Zan hutar sannan za'ace a tashi a tafi gida?
Wannan in justice ne, daman nasani ba'a Sona ku Duka kuwa,

Babu Wanda ya kula Shi Dan sun San halin sai uncle shikadai ne ya masa magana sannan ya tashi, sai da sukaje inda sukayi parking Binaif ya juyo ya kalle su,

yace' kubi bros ku tafi baza'a takura min ba, a tafiya na rage hanya a komawa kuma bazan rage ba,

Kallan juna sukayi sukace' mekenan?

Ummusalma kuwa bata ma San me yace ba Dan har ya Shiga mota abinta shima shigowa yayi ya kyalesu suna sun hangame baki,

Tace' yanaga Baka shigo da suba?

Yace' kyalesu sun fiye sa Ido ganawa zanyi da mi precioso,

Shiru tayi ta kyale shi bata San mezata ce ba,
yace' Kinyi shiru lafiya?

Tace' uhm

Uhm kadai?

Wasa wasa fah Surutu dakai

Ohh really?

Shiru tayi bata Kara magana ba, itama ta kyale shi kawai,
Har suka zo gida babu maganar arziki a tattare da su.



Sai da ya sauka a airport ya Kira numbern Baba Yana Kira tana dagawa

yace' gani fah nazo nama kusa zuwa gida kinji ?

Tace' Amma ai da nazo na daukeka,

Karki damu nama kusa gani nan,

To shikenan sai Ka Kara so, Allah ya kawo Ka lafiya,
Ta kashe wayar tace' Baba wai har yazo,ina so yaga besties dina sun dawo lafiya sai dai sun rame fah,
Baba yace' hmmm ke bakya gajiya da magana,

Dukansu suna parlourn sunsa abinci a gaba Shi kawai ake jira yazo yaci,ummu ce tayi abincin kuma ta hana kowa ci Baba kuwa ya biye Mata sai yazo din,? hira sukeyi mai cike da annashwa babu wata damuwa a wurin su,

Wayar ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????Baba aka Kira ganin sunan Uncle yasa Shi dagawa, beyi magana ba daga can akayi magana,

yace' Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un, wanne asibiti aka kaisu?
AAA hospital, ne asibitin Shine,
Yace' gani nan zuwa kuwa yanzu nan, ya kashe wayar,

Dukan su Ido suka zuba masa,suna San Jin ba'asi,
Yace' wai Abokina ne yayi accident Wanda zai so muyi magana dashi yanzu Yana asibiti, Zan Kira yarona?? sai ya wuce mu hadu acan din,kun gane?

Umma tace' Allah ya kiyaye,
Yana sauri ma be amsa addu'ahr ba, sai dai duk jikin su yayi sanyi qalau a haka suka ci abincin su tunda ba zai zo ba asibiti zai wuce...



Sameera ce a zaune a parlour tana kallo babu abinda take tunawa sai abinda ya faru jiya waye Shi? Duk iya tunanin ta takasa samu waye Shi kaf samarinta idan ta hada babu mai kamar shi, bata taba yin mai kalar Saba ma, ya zatayi? Gashi ko sunansa be fada ba, tana zuwa Kaduna suna party amma takasa Nemo Shi, ajiyar zuciya ta sauke,ga kuma wannan yace zata gani mezata gani? Anya ba tarko aka Dana Mata ba kuwa? An rabata da saurayinta daman de bawani San Shi take ba, tanda Wanda take so tana ganin shine daidai da rayuwar ta, shine Wanda zata tsayar a mijin aure nan gaba, ga kuma ya zo, ya zatayi yanzu?

Mamace ta fito da tun daki take kwala Mata Kira Amma a banza tajiba sai da ta fito ta daka Mata tsawa Sannan ta dawo hayyacinta,

Mama tace' me kike da ina kiranki Baki ba ?

Allah ya taimaketa American film din da ake mai fada ne shiyasa,

Tace' mama kallo nake, banjiba ne yi hakuri,

Kallo ta watsa Mata tace' wuce kije ki gyara dakinki da nawa ki wanke toilet tas jiya bakiyi ba yau kuma dole kiyi wuce, banasan kazanta a jima kuma kizo ki daura abinci,

Batayi magana ba ta wuce ita dai kawai a kyaleta tayi tuna Wannan bawan Allahn, sai data Gama tas ta sauko ta daura abinci lokacin? 11 da 'yan mintuna ta daura abinci ta kafin daya ta gama abinda ta girka ta jera a dining, sannan tayi wanka ta kwanta wayarta taji tana Kara dauka tayi ganin number yasa ta ajjewa bata daga ba, sai da akayi four miss called ana biyar din ta daga kuma tayi shiru, daga can,

yace' Assalamu Alaikum,

Tace' Hello?

Bakya amsa sallama?

Bada muwar Ka bace,

Nasani sosai Amma kuma ai zaki samu lada, ko bakya so?

Shiru tayi bata tanka masa ba,
Yace' Baki San Hadithin manzan Allah SAW ba? Dayake cewa a bazaku Shiga Aljnnaba har sai kunyi Imani baza kuyi Imani ba har sai kunso junan ku,
Yake cewa shin bazan fada maku wani? Abu ba? Idan kuka aika tashi zaku so junanku, sannan yace...

Ta katse Shi da cewa' Afshus salama bainkhum, kaga nasan wannan sai me kuma? Mema ya kawo wannan? Kawai Dan ban amsa ba? Ina ruwank Dani?

Yace' subhanallah ba kawai bane kinyi hasara babba samun lada fah idan kikayi ko kika amsa, meyasa zaki ce haka?? Gashi kince kinsani, tunda kinsani sai kike aikatawa kinji?

Wai Kai Dan Allah waye kazo Ka takura min me kake Dani ne wai?

Yace' am sorry bansan Zan takura maki ba ai, da kin amsa min sallama ta da duk haka bata faru ba, abinda nake so dake shine kiyi hankali da duniya, duniya makaranta ce.
Ki huta lafiya,

Ya kashe wayar bin wayar tayi da kallo tana tunanin waye Wannan din? Ya ilahi.


A asibiti kuwa Har yamma Baba be dawo ba shida uncle sai yanzu da ya Kira su yace' su kawo abinci su Dukan su suzo su duba Shi su koma, hakan kwa akayi Yusuf ne ya jawo su Umma na nuna masa hanya har suka iso asibitin, sude jikin su yayi sanyi tun wayar dasuke Kira ba'a daga wa sai da Baba ya kirasu, suna zuwa yazo ya masu jagora suka fito da kulan abinci suka nufa dakin marar lafiyar Dayake Baba ne a gaba sai ya tsaya a bakin kofar yace'? Banda kuka,Banda kuka,Banda kuka, duk Wanda ya min kuka zai koma,

Yusuf yace' Baba ina Yaya banganshi ba yana ina ? Ko ya fita?

Baba yace' Yana ciki, ku shigo,

Umma ce a gaba sai Anty Ummu da Yusuf a tare suka Shiga yaseer ne na karshe, gaba kidayansu saranda sukayi suna kallan shi kamewa sukayi suka dena aiki?? jininsu yadena zagayawa kwakwalwar su ta dena motsi zuciyar su ta tsaya komai Ido yadena kiftawa kunne yadena ji kaface kawai ta tsayar dasu tamkar statue haka suka tsaya cak sakamakon ganin Abdullah Abdullah a kwance babu mara barshi da gawa oxygen a bakinsa badan zuciyar Shi da suka ga tana harbawa ba tsab zasuce beda Rai,ga karaya a kafa Duka biyun da hannu guda daya, Duka kansu babu Wanda yadawo dai dai Saida sukaji kukan yaseer sannan Suma suka dawo sai kuma sukayi kansa ganin zuciyar sa tana nema ta tafi zero ga wani tari da yakeyi ji sukuyi abin Yana 'DI'DI? 'DI'DI alamar ya tafi zero,

Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un.......=?-?=?-?=?-? uncle >?'?=?-?

By: '''Hijjart''' '''Abdoul'''
? ? Cwthrt=??
[ ? ? ?? Akanji magana
? ?

Not Edited
POST 2020
REPOST 2023


?? 31

? ? Da wani irin sauri Daddy ya Danna alarm sai ga doctors sun zo, fitar da su akayi waje suka hau kansa, a waje kuwa Yaseer ne kadai mai kuka Banda Shi babu wani mai yin kuka a cikin su, sunana har akayi magriba shiru akayi Isha,sun dawo daga sallahn Isha sun zaci sun fito Amma suka ji shiru sai anan Ummu ta fara kuka gani ma take duk laifin ta ne ita tace masa yazo da safe da duk hakan bata faru ba, ta manta da cewan indai Allah ya ?addara Abu babu Wanda ya isa ya kawar dashi, Basu suka fito ba sai Karfe 10 na dare da wasu mintuna sannan suka fito Baba dayake matsayin sa na likita shima kansa fitowa yayi bazai iya yiwa dansa komai ba, Dade ace ma Zainab ce zai iya Basu wani shaku da ita ba kamar yarda ya shaku dashi, Baba da Umma sai Anty su kadai ne sukaje wurin likitan Yaseer da har yanzu kuka kawai yake Bama ya iya magana bare ya tashi yaje yaji ba'asi Ummu da Yusuf kuma basa san suji abinda kunnansu Baya son ji, ga kuma doctors din Basu fito da fara'a ba,
? Office sukaje na likitan,
yace' sai dai kuyi hakuri yaran ku Yana cikin wani hali numfashin sa na barazanar daukewa sannan kuma Yana inner bleeding, sakamakon bugun da zuciyar sa tayi Allah yasa bata fashe ba, sai kuma kansa dashi ma ya bugu yanzu de anyi masa aiki, sosai fatan mu daya Allah yasa kar ya Shiga comma idan kuwa ya Kai kwana daya zuwa biyu be tashi ba zamu karayi masa wani aikin, muga yarda Allah zai kaddara Allah ya sauwake, numfashi Baba yaja wannan al'amari da yafaru sai kace a mafarki? Ikon Allah Kenan, fitowa sukayi babu Wanda ya iya magana, Baba ya kalli su Ummu da yaseer da suke kuka ya kuma kalli Yusuf da ya zabga uban tagumi,

Baba yace' kudena kuka kudena duk wani tunani haka Allah yake ikon sa, ki maida komai ba komai ba, mu godewa Allah da be mutuba da sauran ransa a gaba kuma muna fata Allah zai bashi lafiya yanzu da kuke kukan nan kunyi masa addu'ah ko sau daya ne?

Girgiza Kai sukayi, yace' to kungani? Amma kun zauna kuna kukan da beda amfani ko kadan,yanzu da mutuwar yayi haka zakuyi ta kuka? Shine zai nuna kuna San Shi? Zaiyi alfahari ne daku? Bazaiyi ba, ku maida komai ba komai ba, ku dauki matsayin yayi tafiya mai nisa,tafiyan da bai Fadi ranar dawowar saba, kude na tunanin wai Yana kwancen a asibiti, kunji ko? Hakan da zakuyi shine zai nuna kuna kaunar sa kuci gaba da walwalar ku mutuwa ma bata Hana komai bare kuma jinya, duk Wanda na Kara gani yayi koda tunani to zuwa dashi ma bazan karayi ba,yanzu ku tashi mu koma gida,

Jiki kowa a sabule babu kwari haka suka mike sai dai anyi nasaran da Yaseer ya dena kuka haka ma ummu sai dai sunyi shiru ne kawai, walid Baba ya Kira yazo ya tafi da wasu shima ya dau wasu koda sukaje gida sai da Baba ya Kara masu nisiha sosai sannan suka da ware harda suncin abinci Basu suka kwanta har shabiyu suna nan suna jimamami Amma a zahiri kallo suke, a parlour yusseer da Ummi suka kwana batare da sun Sani ba, washegari Banda su aka koma Shiyasa suka ware suke abubuwan su, ahaka sai da akayi kwana biyu bai tashi ba, zasu sake wani aikin Baba yace a barshi zasu koma dashi London acan za'a cigaba, aikuwa haka akayi ya nemi visa da komai ranar Wednesday zasu daga zuwa Londo sukuma su Ummu su dawo gida don makarantar su, ranar da zasu tafi jirgi daya suka hau,don su Baba a Abuja zasu tashi,sukuma sai sunje Abuja zasu wuce Kano,
?
? ? Suna zuwa suka zarce gidan Anty, sai da suka taya ta aikim gida tsab komai da komai suka huta? sannan suka wuce nasu gidan, fargaban Shiga suke Basu San bezao faru ba kuma, lokacin da safe sukazo Amma Basu fito ba sai da yamma? a hankali suka tura kofar gate din suka Shiga babu kowa a harabar gidan suka sa Kai suka Shiga ciki, Sameera ce a parlour tana waya da Wanda bata sani ba Wanda tasa Maza preacher mutane ta gani kamar su yusseer mantawa ma tayi tana waya
? ?
tace' Wa....w...a.na..ke...ga...ni?
Mama ta kwalla Kiran mama,
Mama ki fito wallahi Mama ki fito da sauri Mama!!!! Ta Kara kwalla Mata Kira,

Fitowa mama tayi tace' ke banasan shirmen banza da hofi ba,meye kike wani kwal.....
?? Wanda tagani ne yasata saurin karasowa tace' yu...u ..yu..yu. Si..f,

Yusuf yace' wai ca aka ce maku mun mutune ko yaya?

Yaseer yace' mundawo baza'a yi welcoming namu ba,

Mama tace' kune? Baku mutuba? 'ya'yanah kun dawo gareni?

Sameera tace' kamar ya? Baku mutuba wai daman?

Yusuf yace' Wanda ya mutu idan Yana dawowa to mun dawo,

Yafada tare da zuwa ya zauna shima yaseer zuwa yayi ya zauma,

Mama tace' ku fada mana ya akayi haka?

Yaseer ne ya Basu labarin komai,

Sunyi jimami bakadan ba,
Mama tace' dakunje gidan su Ummu yarinyar nan ta damu,Tama fini Shiga damuwa,

Yusuf yace' munje ai,Basu jima da dawowa ba daga Adamawa uncle dinta ne yayi accident ya Shiga ana zaton ko ya Shiga comma ne ba'a sani ba shine aka tafi dashi London shine yau suka dawo,

Mama tace' subhanallahi dole naje gaskiya Nayi musu jajaje wannan Abu har ina haka? Allah ya kiyaye Amma ni bamma San shi ba gaskiya,

Yaseer yace' mama idan kika ganshi kamar su daya da ya......

Yusuf yace' yaya sameera, yarda kuka ganta haka take,sai dai Shi Baki ne ita kuma fara ce,
Yusuf ya aikawa da Yaseer wata uwar hararan Baka da hankali shima ganewan da yayi me yasa Shi wayem cewa ( yaseer akwai gane Abu =??)

Yace' wallahi Mama Nima da ganshi fa nashiga comfuse sosai,

Yusuf yace' dalla yimin shiru babu wani kama suke ba,ni karya ce Bana so,

Sameera tace'kuma kace muna kama? Shi baki,nikuma fara,

Yusuf yace' a cewar yaseer ba? Haka yake cewa kuma nasan hakan zaice,

Mama sai nan nan take da su haka itama Sameera dukda babu shakuwa a tsakanin su Amma a kwai respect da fahimtar juna, koda Abba ya dawo shima yayi mamaki wannan lamarin.


Da gudu ya fito daga dakinsu Yana
cewa' bb bb fav kuna ina, basa Parlour hakan yasa ya wuce daki namma basa nan sai kawai ya fito waje suna wurin Shan iska da gudu ya karasa

yace'? bros yayi accident wallahi yayi accident Allah shiyasa Bama samun sa, shikenan,
Sai kuka ya rungume bb da suka tashi tsaye tun kafin ma ya karaso Jin Kiran su da yake, shima Binaif din rungume shi yayi

yace' cool dawn, fada min taya kasani,

Yana shashshekar kuka
yace' muna waya da Sameera sai suka dawo kuma bankashe wayar ba lokacin ina typing Abu a system to a speaker nasata shiyasa ban kashe ba, naci gaba dajin zancenta, har na fara Jin zancen su anan naji abinda yake faruwa,

Sai ya Kara fashewa da kuka, shima Mus'ab kukan ya farayi ya rungume bb shima bbn rungume su yayi,Suma sunyi kika ina ga Ummusalma kuma? Ajiyar zuciya ya sauke yaja su ya Kai lilon ya zaunar su shikuma ya tsaya,

Yace' baza ku iya Kula da ita bakena ko?
Shiru yayi sannan yaci Gaba,
yace' kunsan me kukeyi kuwa? Kuka fa kuke? Ko Baku sani ba? Ehh?
Iska ya furzar yace' kun fita shekaru ina ganin zaku fita hankali da tawakkali Ashe nayi kuskuran fahimta,? yanzu idan nace kuje ku fada Mata mezatayin tunanin ya faru idan kukaje kuna kuka? Tunani zatayi mutuwa akayi, shine abu na farko da zata kawo aranta,kuka beda amfani, na farko zakuyi asarar lokacin,na biyu zaku sa kanku a damuwa na uku zakusa zuciyar ku ta cunkushe, na hudu da kukan da kuke inama zaikiri kuke? Kuka ma Kala Kala ne, bako ina akeyiwa kuka ba, akwai abin kuka a lokacin baza ku iya kukan ba Alhali kuna so kuyi Amma ba halin yi,ku tana da kukan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login