Showing 165001 words to 168000 words out of 173457 words

Chapter 56 - A BAKIN WAWA (AKANJI MAGANA) COMPLETE

30 Oct 2025

3924

Daya da oo".

Mus'ab ne ya tashi ganin wayar sa na kara Mas'ud yace ina zaka je?"

"Kasan ni ba yaro bane ina waya da mata ta wani kuwa har yau banji Yana wayar ba Ande ji asara".

Biyo Shi yayi da gudu suka sauka kasa wayar ma har ta Riga da ta tsinke.

Inni tace, "meye haka? Bafa nasan shashanci da hauka meye na gudu haka?".

A tare kowa ya nuna Dan uwansa.

"Ai daman baza'a taba samun waye ba Kun girma Baku San kun girma ba ko? Ku wuce ku ban wuri".

Kamar jira suke tafada suka Kara mannawa da gudu girgiza Kai kawai tayi ya shige kitchen.


Biki sosai aka fara gudanar wa ta kowanne bangare daura auren Muja aka fara zuwa daga nan akaje na Sameera Baffa babu abinda yace? da aka sanar dashi waye sai ma farin ciki da yayi hakan. Ba laifi 'yan uwan su Sameera sun zo a bangaren Abba sunzo sosai Ashe suna da 'yan uwa iya Abba yake sada zumunci da Shi kadai sai da bikin nan suka dan San juna sosai akayi biki har auren Daddy an daura, babu abinda akayi bangaren amare ne kawai sukayi kamu kuma da daddare za'a kai amare Mas'ud duk zumudin Shi sai yaji Baya son barin gida gaba Daya ji yayi auren ma ina kuka kawai yake so yayi Shi ko yaji sanyi, duk da yaji dadi sosai da yin auren yasan da badan Ummusalma ba da komai ya watse yasan hakura kawai zaiyi hakuran da zaiyi? kuwa dai-dai yake da Mutuwar sa Shi yasan wannan.
Ta???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?re suka dawo gidan lokacin anyi Azahar sai da suka tsaya sukayi sannan suka dawo gida kayan su iri Daya inda su Binaif sukayi iri Daya Suma har su yusuf amma su basu biyo su ba kawai da aka daura na Sameera suka tsaya a can Ummu ma tana can ita ce kawa.

Suna Shiga gidan ya kaca me da surutu hayani ya kawai hutunan aka yi suka wuce gidan Baba ba kowa sai su Ummusalma da su Fati Neena ma ta tafi inda ake harka ita da ummu.
Basu ma San suna gidan ba sai da suka je suka gansu kowa harkar sa yake Yana Danna waya.

Ta fito daga kitchen Kenan hannun rike da cup ta gansu.

Tace, "a'ah Alhaji Chatty an daura auren fa ko?"

Kallan Binaif yayi da idan sa da yaji zai kawo ruwa.
yace, "can I hug her?"

Murmushi Kawai Binaif yayi tare da Gama masa Kai.

Tace, "wacce gulmar kake".

Ganin sa da tayi kawai ya rungume ta Lemar da taji ya taba ya bata tabbcin kuka yake...

BY: ```Hijjart abdoul```
? ? ?? Cwthrt=?? ? ? ?? Akanji magana
? ??

? ? ? ? ? ?? 61
? ? ? ? ? *_last page_*

Abin ya bata mamaki sosai da dayan hannun ta ta rungume shi,du sai taji ba dadi sai da ya gama kukan ya dan share hawayen sannan ita kuma tana bubbuga bayan sa alamar rarrashi can ya dago, ya kama hannun ta ya zaunar a Akan kujera shikuma ya tsugunna a kasa ya kama hannun ta yana kallan ta.

Yace, "bansan ta ina zan fara ba, ban kuma san da wanne iri abu ne zan gode miki da shi ba. Abinda zan iya kawai shine...

Shiru yayi yana goge hawayen sa sannan ya kuma kallan ta.

"Thank you".

Kurban abinda ke hannun ta tayi.
Tace, "chatty lafiyan Ka kuwa?"

Murmushi yayi Yana kallan ta yace, "lafiyar ce ta kawo haka, da'ace bake to da bansan ya zanyi ba da tuni ta jima da Zama matar wani but..."

"Chatty enough please! Ya isa haka Ka tashi kaje Ka zuba abinci naji bansan Jin wani zance kuma".

Binaif ne ya zo ya daga Shi Yana daga Shi shima Yana rungume Shi, zaunar Shi yayi a kusa da ita ya kamo ya kama hannun Mus'ab shima ya zaunar.

Yace, "Bari ayi muku hoto".

Tace, "Kasa ango chatty Yana? kuka ranar Auren sa zai rabu da kauwar sa".

Dariya sukayi shi kuma ya maka harara aikuwa Binaif ya dauko su sunyi Dariya shikuma ya maka mata harara daga ana suka fara hotuna kowa da kowa har sosai sukayi hoto harda pretty tana bacci chatty ya tashe ta wai sai ta bude Ido du Shi ya rike ta akayi tayi sannan aka zauna aka fara cin abinci sun gama Kenan sai su Mariya yayun sa su Duka biyar din Banda hunaifa suka zo ko waccan su ta bada hakuri sosai Yarda suka mata uwar mijin su ta fara uzura masu da kannai Ashe Ummusalma ce ta hada wannan abun da ta bincika taga duk wayancin? siblings din mijin su sunyi makarantar Daya dasu shine ta kitsa ta hada wannan abun takuwa nuna ko a jikin ta? ba abinda ya faru komai ya wuce.

Mariya tace, "Saima ko san inda su Hajiya suka tafi kuwa?"

Saima tace, "wallahi bamu san Inda suke ba, wayar su bata Shiga tun sanda nayi waya da Hajiya tace min wai suna Dubai daga nan zasu wuce China bamu Kara waya da su ba".

"Kuma kin kira su bayan nan?"

"Ai bata shiga".

"Allah de yasa lafiya".

"Daddy de yace zasu dawo Amma kinji shiru".

Kowa shiru yayi sukuma suka ci gaba da rahar su Basu, basu wani jima ba suka ko gidan biki.

Da daddare aka tara su gaba dayan su aka musu nisaha mai ratsa jiki da bargo kowa sai da ya musu ba iya su kadai har su Binaif aka hada.

Daddy yace, "Mas'ud Mus'ab gidan danace Zan Baku Ashe ma wai yayan ku ya riga da ya gina muku tare Sai dai muce Allah ya bar zumunci ya kuma kare mu daga sharrin masu sharri".

Da ameen kowa ya amsa, suna fita.

Mas'ud yace, "Finally!"

Ummusalma tace, "kayi aure saura haihuwa nan da gobe ko?"

Rufe idan sa yayi a bayan uncle.
Uncle yace, "fito nan naganka waye Kai da zaka ji kunya ai baka isa ba gaskiya ta fada".

"Haba Dan Allah yaya kunya kuke Bani".

Girgiza Kai kawai Mas'ud yayi ya fice ya Shiga mota haka ma uncle sune a gaba su kuma a baya Ummusalma kuwa sai yazo zasu tafi.

Mas'ud yace, "Yana ga Ka dau hanyar gidan Ka nifa ba yau nayi shirin zuwa na kwasa Kaya na ba sai nan da kamar sati haka hudu zaka ganni a gidan Ka".

Mus'ab yace, "gaskiya ce nima haka".

"Ai shine ni duk zumudi yabi ya cika ni Kai ma haka kaji?"

Gashi daman ba gudu yake ba sai ya Kara rage gudun Yana tafiya a hankali yau shine har da su sa waka yana tafiya.

Mus'ab yace, "hafa bb yada haka? Kayi gudu mun fa gaji muje muga Amaryar mu".

"Dama ban shigo motar nan ba".

Banza yayi dasu ko tanka su beyi ba sai ma tsaya wa da yayi yab fita.

Mas'ud yace, "shikenan tana can tana jira yau na ga ta Kai na".

"Kai dai bari daman ma Uncle ne ya amsa tukin".

"Uncle ka ansa tukin kaji ko".

Incl yace, "tunda Ka taba gani na a kitchen ina tuka tuwo ba?"

Binaif ya dawo hannun sa rike da Leda guda hudu ya ajje musu biyu a Baya suma ya ajje musu.

Mas'ud yana turo baki yace, "ranar auren naka ma ace wai sai an bata maka rai ni da yake Allah ya zuba min hakuri da juriya bakomai nayi aure ai Nima za'a ake faran tamin rai".

Uncle yace, "kasan har yau bata ci kazar Amarci ba kullum Mita ake min".

Murmushi Binaif yayi yace, "Ku ai ban taba Jin irin Naku ba kafa birgeni mutumi na".

"Ahh dawa zai zauna taab ba gashi an sallame ni ba, dafa sai na warke ras harda wani karani bed rest na sati kaji fa".

"Wai me ake cewa naji ana wani Amarci kaza me yake faruwa".

"Ni ba wannan ba please bb Ka taka Mota mu tafi".

Binaif yace, "revenge ne ai".

A tare suka ce "revenge?"

"Ehh revenge ne Nima haka kuma min har Gwara nima ina dan sauri".

Koma suka yi suka kwanta sun tuno abinda sukayi can.

Mus'ab yace, "Amma ai Twinny ne Bani fa fav ne yake tukawa ai".

"Naji wannan".

Shiru sukayi suka rabo dashi Mas'ud ya cika ya cika yayi fam.

Uncle yace, "yanzu idan mukaje gida kamar minti nawa zamuyi sai Ka kai ni sannan sai Ka kaisu ko inaga haka zaka ai ma".

"Uncle hakan za'ayi yanzu kallan ball zaka yi ni kuma na huta".

"Haba bb Haba bb this is cheating wallahi".

Banza sukayi suka rabu su sukaci gaba da hirar su, ganin sun tsaya a gidan farko uncle yaje ya bude suka Shiga yasa su mamaki komai iri Daya dana bb marabar kawai su ba Field Shi kuma da akwai beyi parking ba ya tsaya ya kalli chatty.

Yace, "Chatty Ka gidan Ka nan zaka iya fice mun daga mota na kawo Ka".

Rasa bakin magana sukayi Basu taba tunanin nanne gidan su ba kusan Kullum sai sunyi maganar gidan daga waje iri Daya ne su uku a jere Ashe harda daga ciki ma iri Daya nanne ga shinan ko ina haske. Jiki a sabule ya fita shima uncle fita yayi Dan sunyi waya da Ummu tace tana gidan Mas'ud hakan yasa ya fita tare da daukar ledan Mas'ud guda daya suka Shiga cikin gidan.

Haka ma gidan Mus'ab shima iri Daya ne kasa jure wa yayi ya rungume Shi bayan ya fito, shine ya raka Shi har parlour shine ya Shiga ciki sai ga su sun fito da Neena gaisa wa suka yi yayi musu dan nasiha sannan suka tafi shida Neena gidan Mas'ud suka wuce be Shiga ba? suka fito suka tafi, Neena suka Kai mayar sannan Ummusalma ta tafi da ita da pretty suka tafi.



_Gidan Mas'ud_ .


A Hankali ya tura ya shiga tana kwance bayan tafiyar su tana tunanin Jin muryan sa da tayi....

Ta rufe fuskar ta mayafi bata San san da ya karaso har ya tsugunna a saitin fuskar ta ba, sai da yasa hannu ya Bude faskar ta ta sannan ta bude ganin sa da tayi a gaban ta yasa razana lokaci guda kuma tana neman guduwa hannun ta ya rike gam ya dawo da ita shima ya zauna rungume ta cikin kunne ya rada mata.

"Your husband is here".

Sai anan ta samu wani irin nutsuwa sai kuma tasa kukan da tasan na farin ciki ne wani irin yanayi suka tsinci Kan su a ciki dakyar ya iya ce su tashi suyi sallah.

Bayan sunyi sallah ya sukayi addu'a ya mata tambayoyi sosai kuma ya samu gamshashshiyar amsa hakan ya masa dadi, sai dai hawayen da take yi ne ya kasa sanin takai Mai Mai na meye nan take zuciyar Shi ta bashi amsa da bata Sanka wani irin dokawa yaji kirgin sa yayi nan take yaji babu dadi amma dayake yayi gadan boye emotion sai be nuna ba sai ma ya wani murmushi da yayi ya tashi ya fita ya dauko cup da plate ya dawo tana nan yarda ya barta Zama yayi ya zuba musu madarar ya Mika Mata cup din ta madarar kawai Tasha duk yarda yayi da ita da ta ci wani abu kinci tayi haka ya kyaleta ya Gama ya kwashe ganin be dawo ba yasa tayin wanka ta fesa turare da humra tasa karamar rigar bacci Mai laushi sannan ta kashe wutar dakin ta kwanta tare da kunna lamp sai anan wani saban hawayen ya zubo mata Jin sakamakon zuciyar ta da ya Raya Mata kila ma Abba ne ya mamamika masa ita Baya San ta, sai wani saban hawayen ya kuka zubo mata Jin anbudw kofar an shigo yasa ta tsayawa da kukan tana neman hadiye Shi. Zama yayi a bakin gadan ba ita yake kallo kamar yarda ita ma bashi take kallo ba.

Yace, "kiyi hakuri, bansan ta ina ba zan fara nayi abinda naji zuciya ta yarda da abinda aka fada min kuma Nayi, na bi san Rai na da zuciya ta na auro ki".

Shiru yayi beci gaba ba.

"Bansan wanne irin mutum zaki dauke ni ba all I know is I Love you!"

Jin karshen Kalmar tayi kamar a mafarki shine kuwa yake cewa yana Santa?

"Bansan wanne lokaci bane bansan kuma wanne rana bane naji hakan ya faru dani, my love for you? I know is beyond imagination it's a strange kind of addiction I can't stay without you even for a moment there is something which attracts me to you with you everything is fresh like dew Amor I just want you to know that I will always love you till my last breath I don't know whether my words make you clear how much I love you".

Tashi yayi ya zago inda fuskar ta take ya hau gadan shima ya kwanta suna fuskan tar juna Yana kallan ta tana kallan sa. Bata san me zata ce masa ta wani Zama speechless ta Rasa bakin magana? cewa zatayi tana San Shi? Ko me zata fada ma.
Besan meke Jan Shi na ganin kirjin ta na bugawa da sauri da sauri yasa ya Kara matso da fuskar Shi sosai ya mayar da Kan sa pillown ta runtse ido ta tayi Jin bugun zuciyar na Kara ruwa, shidai besan mene ba haka kawai yake Jin wani iri a jikin sa kuma bazai iya Barin koma mene ba bata Ankara ba kuwa taji bakin ta a cikin nashi ware ido tayi tana kallan sa tun tana iya hana kanta kin biye masa kuma de na biye masa su Chatty ba kanta.


A bangaren Mus'ab kuwa komai ya tafi normal da yake yarda suka tsara abin su sai dai Jin wank bakon Al'amari Muja taji sosai ta sha wahala ba laifi.


Washegari da safe aka aiko musu abinci daga gidan Umma Binaif aka kawo wa ya basu.

Shiga daki yayi Yana cika Yana batsewa.

Ummusalma tace, "a'ah lafiya? Ba drivern gida Umma bane?"

"Shine mana har wani mu baza'a kawo mana abincin ba? Abincin su fa kadai aka kawo".

Tana daga kwance kawai tayi juyi ta koma dayan barin.

Tace, "idan Ka Gama cikar taka ni bacci nake ji".

"Me Kenan?"

Dan juyowa tayi.
Tace, "idan Banda abinka Kai saban aure kayi ko me da za'a wani aiko maka abinci".

"Sabo ne mana almost 70 days".

"Naji wannan".

Murmushi yayi Yana kwanciya a kusa da ita tare da sa Hannun sa ta cikin ta.

Yace, "shiyasa Naga jiya kin..."

Tasa Karshen zancen shiyasa ta juyo a fusace maimakon magana taji bakin ta a nasa sun dulmiya basa Jin kira, sai da suka lafa.

Tace, "Ba bugun kofa nake ji ba?"

Shafa kanta yake Wanda ya sha kananan kitso Yana rike da hannun ta Yana kallan zanen lallen ta.

Yace, "oho koma waye kuma sai munyi wanka".

Ware ido tayi tace, "nidai banzan yi da Kai ba Ka Kara wahalar dani Ka wahala fa kafin kayi yafi dari".

"Dari ko? Naga Darin kike so Kkenan, kuma Naga Fansheke nake? yarda gobe ma idan ance tafi wanka bazaki ba".

"Revenge?"

"Idan Kin fada hakanne".

Tashi zaune tayi tace, "da'alama 'yata ta tashi Bari nayi wanka sai Ka rike ta kafin na fito ko?"

Kafin yayi magana wuf ta sauka ta shige toilet ta fara, tana gasa jikin ta Dan ba laifi ta Saba da ruwan zafi a wannan jegon nata, tana Shiga yarinya ta fara kuka Jin tana kuka yasa tayi gaggawa ta fito dukda ta dan jima tan zuwa ta karbe ta ta fara jijjaga ta ta danyi shiru sannan ta bata ta Tasha sai Shiga anan ya Shiga wanka kafin ya fito ta tafi dakin ta ta Mata wanka ya shirya ta sannan itama ta shirya cikin atampa har yau bata San zani a dole kawai take sawa skirt ta saka tayi kyau abinta sai kanshi suke zubawa ita da 'yar ta shigowa yayi, ya dauki pretty sannan ya karaso Inda take a gaban madubi.

Yace, "bakije kinga waye ba?"

"Nifa na manta ma da ana bugawa kaje kaga waye".

Fita yayi da pretty a hannun sa yaje ya Bude yana Bude wa yaga Chatty.

Hanya ya bashi ya shigo shikuma ya cukume ya daure fuska irin an bata min Rai.

Yace, "bb na shigo ina? Bade niba ina matar Ka ita nake nema wallahi inaga tun 7 nake bugawa ga waya ta bansan inda take ba na koma naje nadawo shine har yanzu".

Tace, "a,a chatty Kaine da sassafe haka?"

"Kinga please it's urgent please zo muje".

"Ina?"

Hannun yazo ya kama zai fitar da ita bishi tayi suka fito ganin sun fito zasu bi ta gate yasa ta tsayawa.

Binaif yace, "ina key din da kayi amfani dashi Ka Bude gate".

Hannun sa ta daga alamar gashi, zuwa yayi ya karba da pretty a hannun sa yaje ya bude kofar ganin gidan sa yasa.

Yace, "bb ko? Daman nan".
sai kuma yayi shiru ya kalli Ummusalma dake kallan sa.

Yace, "wai bazaki tafi ba?"

Koma wa tayi zata koma gidan ta ya kamo hannun ya marairaice.

Yace, "ki gane mana".

Harara ta zuba masa sannan ta shiga tana kwance a cikin bargo da'alama Zazzabi ne ya rufe ta sosai komawa tayi ta dauko wani garin magani da Inni ta bata da kuma magani ta dauki mayafin ta koma.

Zama tayi ta yaye bargon data rufa.

Tace, "Sameera tashi kisha magani".

Muryan mutum Daya ce tasani wannan sai dai yau da asuba ya bata labarin sistern Shi da komai nasa na rayuwa.yace zaije ya Kira sistern shi tasan ita ce wannan.
A hankali ta yaye bargon da rufa ta tashi zaune tana kare wa halittar matar kallo, Kallan ta ta Kai ga Mas'ud dake bakin kofa Yana kallan ta, itama Ummusalma kallan ta take yi hannu ta daga tana nuna Ummusalma.

Tace, "wannan ce sistern naka?"

Daga Mata Kai yayi alamar eh.

Kallan ta takeyi Bako kiftawa kafin.

Tace, "yaya meyasa? Meyasa kika bar gida? Har na manta dake meyasa yaya?"

Murmushi Ummusalma tayi Mata Wanda duk zaman da take da ita a gidan ba taba yi mata tun kafin ta zama kurman shiru.

Tace, "Sameera na gano iyaye na shiyasa ban koma ba Amma kiyi hakuri gashi yanzu mun sake haduwa kin zama in-law kin tashi daga Sameera kin koma Anty Ko yaya sameera".

"Daman Basu Abba bane Iyayen ki?"

"Basu bane Sameera su kawai rike ni sukayi da amana har suka sani a makaranta kin gane".

Murmushi itama ta mayar mata Mai kyau.

"Ya wahalar min dake ko?"

Sunkuya da Kai kasa tayi ta fara wasa da hannun ta, hararan Shi tayi sannan ta wuce toilet duk wani taimako da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login