Showing 108001 words to 111000 words out of 173457 words

Chapter 37 - A BAKIN WAWA (AKANJI MAGANA) COMPLETE

30 Oct 2025

3935


Batayi mamaki ba tasan zai aikata,

tace' Ai beda komai shiyasa yanzu yake so ya fara mallakar Takardun gaskiya,

Binaif yace' me kike nufi?

Gogen hawayen ta tayi tace' yanzu beda shago, ya siyar, shagunan sa Duka ya sayar ya dawo namu, yanzu kawai wannan companyn ne guda biyu sai orphanage kuma yafi samun kudi a business dinsu na Lagos, sabida haka dole companyn sa na?? can zai tsaya cak.
Murmushi tayi ta tashi zaune ta Dora kafa Daya Kan Daya,
Ta kalli Binaif tace' ya Kai karar Ka, muma zamu Kai tashi.

Yusuf yace' kamar ya?

Tace' kamar yarda abin yake,

Ummu ta kalla tace' Ina uncle dinki,
Gaban Binaif ne yafadi Ashe fa bata San yayi accident ba,
Shiru sukayi hakan ya tabbatar Mata da wani Abu ya same Shi, murmushi kawai tayi batayi magana ba,

Kowa shiru yayi Yana sakawa da kwancewa a ransa,

Yaseer ne ya katse shirun, yace' Ummu kinga abinda nagani kuwa, yau akwai harka fah,

Dariya tayi tace' Ai nagani shiru kawai Nayi akwaita Kam,

Yusuf ya balla masu harara yace' kwadayayyu kawai,

Yaseer ne ya tashi ya dauki tray din data kawo ya baje kafa ita ummu tashi tayi tazo ta zauna suka baje suka fara ci, sai da suka ci dayawa,

yace' Yaya Zan iya ci kuwa?

Balla masa harara tayi tace' karkaci Ka zauna,

Yace' ai lemon ne ba sanyi shiyasa, wallahi Alhaji kazo kaci nidai ba ruwana tam,

Ummu tace' nan gidan mune yayar mu da yayan mu, koka ya kace Dan uwa,

Ai maganar ki haka take, yaya kawa,yayane, ta o ina mu ba ruwan mu mun hada,

Binaif girgiza Kai yayi ya tashi ya bar masu wurin, Allah yasa ba Mas'ud,duk ranar da Mas'ud ya dawo sum a suka zo yasan akwai ciwon kai.

Yusuf zuwa yayi ya dauka lemu ya fara sha, yana yi Yana hadawa da cincin, sai da sukayi nak,
Tana zaune tana kallansu ji take kamar a mafarki yau gata ga yusseer,

Yaseer ya matsa Kuda Ummu yace' samana a jaka alkhakin kinji?

Tace' to, Kar ace mun fiye hadama,

Shiru yayi shidai beyi magana ba, ya kwashe ya mayar Kan table,
Yusuf yace' Ku tashi mu tafi,

Cab tafiya? Yanzun?

To gidan ku za'a maka?

Ummusalma tace' Yaseer, kaza tuna wani Zane Dana taba zana maka?

Yace' wanne Kenan?ai dayawa,

Wani Zane,na wani mutum,

Yace' awww Yana nan ma Zane, qalau dashi, zanen fah Mai gadin school din mu ne lokacin da kika zana min ma befi da kwana daya ba ko biyu ne ? Ya bar makarantar,

Numfashi taja, tace' ok,
Yace' lafiya?

Bakomai kawai yanzu abun ya Fado min,

Yusuf yace' finally yanzu kin dawo kamar da ko?

Murmushi kawai tayi tace' da dimma bansan mezanyi ba, Amma yanzu nasani,ji nake Bana da damuwa Sam,

Sai da suka Dan taba hira sannan suka tashi suka tafi, lokacin har an kusa magriba, part din shi ta shiga tagan Shi a parlour Yana aiki a system, wayar taje ta dauko ta zauna a kusa da Shi ta daura kanta a kafadar Shi tana kallan abinda yake, aiki yake a cikin system Dinshi kamar na office Dan harda Zane Zane? tagani yanayi,
Waya tayi take Kira shiyasa batayi magana ba, kuma ba'a daga ba, zata Kara Kira aka Kira, daga can aka ce,

Talaka kawai meyin flashing kinsan mu kudin wayar mu Baya karewa, menen zaki kirani eh? Kizo ki kafa yiwa mutene dinkimkim kina yin shiru ehh? Baza kiyi magana ba?

Tace' ohhh Dan na yabeka kayi aiki mekyau shine zaka kake fada min magana ko? Ta kaci gaba kasan Idan Ka bata Mata Rai zai fada ma kabata hakuri,

Yace' Haba lil sis kinsan yarda nake kaunarki kuwa,

Kake kaunar ta de,

Ahh Dan Allah ruga min asiri ba haka bane ba, wallahi Bana Santa bamma San mene San ba,

Tace' to naji,
Ya akayi? Kaje?

Yace' najeni,wasu Kaya ne za'a shigo da wasu,yau din nan aka kawo su, engines ne da machines, sai kuma wani sabon business da zasu fara iya su manya,na Kaya Sawa Suma sunzo, sannan kuma company din ya samu karbuwa har a Chicago to yanzu sun hada hannu da su, shine fah Akan wannan aka wani ce babu aiki, yau,

Tace'? okay, a wannan aikin da zakuyi na satin nan Ka tabbatar da anyi komai ba daidai ba,yarda wa'ancan zasu ji labari,nasan sunsa kudi,dayawa dole kuma sai an biyasu kudin su, sannan ka tabbatar business din nan ba'a fara ba,

Taya Kenan zanyi hakan?

Kai kasani, kuma,
Tace' kaifa physics Ka karanta ina?

Yace' ehh,

Tace' to kayi aiki dashi mugani anan,
Ta kashe wayarta,

Ta Kira Mus'ab sai da suka gaisa cikin mutumci yace' komai Yana tafiya yarda Muka tsara lokaci kadan ya rage komai ya kwabe,

Tace' hakan yayi kyau glip kaci gaba da kokari,

Yace' ok,ina mijinki?
Yana jinka,
Ki gaidashi,
Sukayi sallama ta kashe,

Tace' wai daman kana aiki ne?

Yace' ehh mana,

Tace' yayi kyau, wannan ginin na meye?

Yace' tambayar fah?

So nake nasani,

Yanzu fah kinfiye magana dayawa,

Tace' idan kuma Nayi shiru ace Nayi shiru ko?

Yace' a,a,
Yace' yanzu kin danne min kafada idan na Rama ace ba haka ba,

Tashi tayi tace' kama ji an kira magriba Ka tashi Ka tafi,kuma karka jima,
Ta tashi ta tafi dakinta, tayi alwala tayi sallah bedawo ba har tayi Isha tayi wanka ta Shirya tadawo parlour ta zauna? tana Zama suna dauke nepa takaici ya kamata,ta cika tayi fam, ta leka dakinsa shiru, kwafa tayi ta koma daki ta kwanta ta kashe fitilar wayar ta Kenan taga an medo da nepa,kin tashi tayi ta kashe wuta ta rufe ido taji ya turo kofar dakin, ya shigo daga Shi sai vest da gajeran wando, gadan ya hawo,

yace' Lafiya?
Banza tayi da Shi,

Yace' ok Bari nagani ko wurin da aka ce Yana zafi ko ya dena,

Tashi zaune tayi rufe Ido ta fara ruwan masifa yafita ya barta ita kadai a gida, ba kallo ba komai, bata Kai karshe bata ji ta hade bakinsu, Yana Mata wani irin salan Abu data kasa fassara Shi,Tama kasa gane kansa, su Ummusalma anji bakon yanayi tuni ta fara karbar sakon itama,abunda yake? Mata jiya nafila jiya batani komai ba Ashe kukan dadi jiya tayi yau tayi na dalili yau tazama cikakkiyar Mata jiya kawai sha'ani aka sha,bata sani ba, yau ake bidiri.


Tana kwance tana juyi a Kan gadan dakin tun sanda suka sato ta bata Kara ganin fuskar ko Daya daga cikin su ba, yau kwana biyar zuwa hudu Kenan kullum sai dai a kawo Mata Kaya abinci, yakasa gane inda aka kawo ta. Tayi tunanin sune suka sauya mata wuri Ashe basu bane, Tambayar ta anan shine INA AKA KAWOTA??

By: '''Hijjart Abdoul'''
? ?? Cwthrt =??. ? ? _Akanji magana_


? ?? 39

Abba babu abinda yake zirga zirga a daki shikenan yanzu beda wani shago,sai company biyu da kuma business din da yake Wanda ko matar Shi batasan Yana yi ba, Zama yayi Yana tunanin mafita, mama ce ta shigo,

tace' Alhaji wai Dan Allah bazaka fada min abinda yake damunka ba? Tun jiya kake cikin damuwa fah,

Numfashi yaja yace' saratu bazaki gane ba,

Kamar bazan gane ba?? Sai dai idan ba'a fada min ba,

Yace' kinsan de munsai da shagunan mu? sannan kuma mun fara gina katafaran asibitin mu,kinsan idan mun Gama zamu Sami kudi sosai a cikin sa, to orphanage din dake Lagos Ai kinsan Shi shine wani bature daga can Paris ya taya Shi, wai ya taba zuwa shine aka bashi number ta,kuma beda lokaci sanda yazo Amma yanzu zai zo? sai mu zauna,

Tace' indai ya taya da kudi dayawa inaga ai ba matsala,

Yace' kudin, a dollars ma zai bayar da kudin,

Tace' to kawai a sayar mana,

Yana zaune aka masa waya, dagawa yayi, abinda aka fada masa yayi saurin mikewa, dandanan zufa ta keto masa ya tashi tsaye bema Gama Jin abinda akace ba,ya kashe wayar ya Fadi? reras a Ka gado, mama tayi kansa tana Kiran sunansa Mahmud Mahmud Alhaji Ka tashi mana, ruwa ta zuba masa shiru babu motsi ga Yara duk sun tafi makaranta? da gudu tayi dakin Sameera itama bata nan bata dawo ba, fita tayi ta Kira driver yazo suka kama Shi suka a mota da gudu ta koma ta dauko hijabinta tana kuka, suka tafi asibiti.

? ? ? Abba >?'?

('('('('('('

Dakyar ta tashi ta Shiga kitchen sauran kayan da bata Adana ba ta karasa sa su inda suke, ta hada masu breakfast lafiyayye ta haddan tea yasha kayan Hadi shayi, ta jera a dining, tayi wanke wanke ta gyara inda tayi girki, gidan ta tsab yake shiyasa ma bata tarki Shara ba kawai turaren wuta tayi ta fesa Freshener shikenan, abinda tayi, daki ta Shiga taga har lokacin bacci yake wanka tashiga tayi ta fito ta shirya kayan Sawa ta Rasa Sam ta Rasa wanne zata saka, ita bata San wannan kayan ganewa ce ba'ayi ba, dakyar ta samu wani Riga da skirt English wears masu Dan Karan? kyau tasaka ta hada karami bakin Vail ta daura akanta ta Kara fesa turare, ta kalli taga goma saura, yake ta uban bacci ko baza Shi wurin aiki bane.
?? Gadan ta hau ta kwanta ta shige jikinsa, a hankali ya bude idansa ya ganta rungume ta yayi ta baya,

yace' Mi Amor,

Tace' uhm, Ka tashi ko bazaka aiki ba?

Yace' Amma de kinsan ba tashi na kika so yi ba,

Tashi tayi daga jikinsa tace'? Ka tashi tou,

Yace' ya jikin?

Harara ta Galla masa tace' bansani ba,

Murmushi yayi yace' to shikenan ni Bari na duba na gani ko ya....

Da sauri ta tashi,sai dai bata Ida tashi ba tace' washh Allah zafi wallahi,

Zuwa yayi yace' sannu baki Shiga ruwan zafi bako?

Turbune fuska tayi tace' Naga de da zafi,

Yace' to naji, taso muje ki Shiga,

Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da bracelet din hannunta tana cuno Baki, sunkuyawa yayi daidai kunna ta yace' hala kina so a Mai maita?? ko?

Juyowa tayi da sauri sai? suka hada goshi sukayi gware kowa dafe goshin sa? yayi, atare suka ce

yace' kinga ko?

Tace' kaga ko?

Hannunta ya kama suka tafi ita de tana dafe da goshinta tana mulmulawa taji zafi ba laifi, har dakin sa ya kaita,

yace'? jeki hada min ruwan ka,Naga kin warke harda su gyaran parlour,

Marairaice wa tayi tace' komai fah a hankali nakeyi, daurewa nake,

Shi kansa yasan tana da dauriya,kuma tayi dauriyar Amma sai, yace' a haka?
Ai bangani ba,

Fakar idansa tayi Yana cire Kaya ta Kara Galla masa harara, ta shige toilet ta hada masa ruwa zata fito sukayi kicibus shikuma zai shigo matsa masa tayi sai da ya shigo zata fita ya rufe kofar, kwalalo Ido tayi zatayi magana,

Yace' Wana kama?

Gabanta taji Yana faduwa, tace' to menayi?
Tana kif kifta ido,

Yace' laifi biyu, kin harareni dazu yanzu ma kuma kinyi, sannan yanzu kuma kinzo zaki bigeni Ashe ma uku ne ba biyu,

Tace' yaushe din Zan bige Ka?

Ohh kin yarda kin harareni din Kenan?

Juyar da Kai tayi, yace' ga kuma wani laifin,

Tace' babu kyau magana a toilet de,

To shikenan karshen magana kawai punishment dinki shine kimin wanka,

Bata juyo ba, tace' taabb kujimin da mutum Shi Bemin wanka ba daya wahalar dani sai nice karama Dani Zan masa wanka, cib,

Sarai yaji abinda tace, yace' magana kike?

Juyowa tayi ita tazaci a zuciyar ta,tayi maganar da yake a fuskarta,
tace' a,a kawai fah,
Sai kuma tayi shiru, takowa ya fara yi tana ja da baya Yana takowa tana ja Baya, haka sukayi tayi, bayan da zata ja kawai tajita tsudum a cikin ruwa, me zaiyi idan ba dariya ba,

?? Tsayawa tayi sororo acikin ruwan tana kallan shi, yau ta taba ganin sa yayi dariya haka, sai da taga yana murmushi, sai da ya tsagaita dariyan Amma still da murmushi a fuskarsa, ya zauna a bakin bath tub,

yace' tsuntsun daga Sama gashashe,

Daure fuskayia bata yarda ba, babu wasa a fuskarta,

yace' yarinya duk wani cikar ki da batsewa sai dai an...

Ruwa ta watsa masa hakan yasa Shi yin shiru shima ya watsa mata haka sukayi tayi be Masan sanda ya Shiga ruwan ba shima sai dakyar ta yarda yasata a ruwan zafi kuma taji sauki laifi sannan ta fito shikuma yayi wankan sa, kin Zama tayi a dakin ta koma dakin ta, ta shirya atampa tasa bata daura Dankwali ba ta fito, ta zauna a dayan parlourn, tana Danna waya,wani lokacin kuma ta kira, ta jima sannan ya fito cikin kanan kaya sai kamshi ke tashi, sannan sukayi breakfast, sai da suka Gama,

yace' muje na rakaki kiga gidan ki,

Batayi musuba suka fito suna zagaya gidan har part din su Mas'ud suka je, three bedroom ne a ciki sai parlour sai kuma kofar baya, yayi kyau shima, suka zo Garden,

tace' meyasa ba'a Kula dashi?

Yace' Nima bansani ba,haka kawai,

Girgiza Kai tayi kawai, yace' Allah ya shirya ni ko?

Tace' ohh daman idan Ka girgiza Kai abinda kake nufi Kenan?

Yace' kusan haka?

Amma ba haka bane,

Yace' Kai kekam ko?

Menayi?

Babu komai,

Suna tafiya sun zo wurin? field dinsu,
tace' idan umma tazo gidan nan ca zatace gida ba rahama, babu iska, babu sanyi sai sanyin nasara,

Murmushi yayi yace' Umma ai, jarabar ta tafi karfinta,har addu'a nake Kar Allah yabani Dan ko ya masu halinta,

Tace' ba ruwana idan tajika kaida ita ne,

To na nawa kuma, sai dai Kar a kuma,

Tace' wai tsaya kaga wata kofa a can karama, kuma kaga wata ma anan suna kallan juna,ina ne?

Murmushi yayi ya rungume ta, yace' nazaci bazaki gani ba, shiyasa ban fada maki ba,

Tace'ko bangani yau ba,wataran zangani nida gidana?

Yace' haka fah masu gida,

Fadi Ka Kara,
Ina ne?

Yace' muje mu gani ko ina ne?

Zuwa sukayi ya bude da key din hannunsa suka Shiga gida taga ni irinna su komai da komai iri daya tunkafin ta Shiga tasan hakan,

Yace' laaaa ai gidane,

Tace' gidan waye?

Yace' muje muga wancan shima,

Shima zuwa sukayi suka ganshi yarda nasu yake shima haka yake,

Tace' gidan Glip da Chatty ko?

Murmushi yayi ya yaja kumatun ta yace' haka yake,? Sweet Mi Amor,

Tace' idan ba'a fada min mi amor din nan ba Kar a Kara fada min,

Yace' angama Madam,

Tace' Mai gida,

Daure fuska yayi ya matse hannunta dake cikin nasa,

tace' ouch da zafi Mai gida, Haba Malam zafi fah,

Yace' karki Kara fada min kinji ai?

Angama mai...aww angama Malam,

Harara ya dalla mata,
tace' laaaa daman Malam Ka iya harara haka? Kaga yarda kayi kyau kuwa, Bari na ma hoto kamin kyau sosai Dan Kara muga?

Banza yayi da ita suka karaso gaban parlourn,
Tace' mu yaba asa mana kujeru ana ba?

Yace' za'a sa,
Bari naje na dauko mana,

Zuwa yayi ya dauko masu, suka zuna suka daura kafa akan table,
Tace' nagaji dayawa,

Yace' ayyyaahhhh sorry Madam,

Tace' idan kace madam din nan irin masu sai da abinci nan yarbawa ko iyya murai haka nake ji, kawai haskoni nake acan,

Dariya yayi yace' ni kuma fah?

Tace'me ?

Dakike cemin mai gida,

Aww Kai ai haka naji ana fada maku,

Naji wannan.


Hajiya ki fito ki Sha iska muma yau zamu bar gidan nan, sabida haka gashi nan an tanadar maki komai, da komai na bukata idan kina neman Abu ki Kira wannan wayar ki fada komai duk abinda da kike so,an mallaka maki wannan gidan halal malak, ga takar dun, sai dai bake ba fita kinsan Idan aka ganki da matsala, idan zaki fita kisa nikaf,?

Tace' yaro Ka fada min mana, waye ya maido ni nan,

Yace' Hajiya Kenan, gaskiya bazaki jiba, abinda aka ce kawai kiyi, sannan zanke kula dake ga kudi ance na Baki,

Tace' ni yanzu mezanyi da su?

Yace' ance na baki ne,
Yace' banda wayo Banda wayo Amma kije ko ina,

Tace' Banda yawo Amma naje ko ina? Idan Zan fita kuma masa nikaf mekenan?

Yace' abin nufi daga Layin nan sai Layin nan,zaki ke ganin mu ai, muna Sami Ido, mude mun fada maki mun fita,

Shiru tayi tana tunani to mene ma amfanin yawo? Ina zataje? Wa tasani? Daman ta Saba rayuwar ta a daki shekara talatin babu fita,

Bayan ya fita ta tashi ta dafa abincin ta a gas ita kadai ta gyara gidan ta tayi komai, ta zauna tana jiran lokacin sallah tayi, Zama tayi tunanin rayuwar ta,
Numfashi taja tace' Allah yagani gareka ni ZULAIHAT ina ganin rayuwa Allah Ka kawo min sauki ya Allah.


Kwana biyu yana yau be ganta jiya da yau kullum Yana ganin ta Amma yau Sam be ganta ya neme ta kuma a Layin babu ita babu labarinta gashi yanzu ana neman Ayi magriba yayi neman shiru tun ranar Friday rabon Shi daya ganta, ya zaiyi? Besan gidan suba, besan sunanta ba, kawai kamarta yasani a shekaru bazata wuce Ummusalma ba koma bata kaita ba, yarinyar nan kana ganin ta kasan wani Abu na damun ta,kullum bata cikin walwala, gashi besan ta.

Numfashi yaja ya samu wuri ya zauna Yana tunanin yarda zaiyi meyasa ma be tambayeta ba?

Wata zuciyar tace kana shegen tsoron zaka iya? Wama yasani ko matar aure ce,
Zuciyar Shi yaji tayi wani irin bugawa Mai kama da tsoro shine Karo na farko hakan ya faru dashi, yanzu meye mafita?

Tofah >??




A asibiti kuwa an ansa Abba cikin gaggawa sai dai duk abinda ya kamata suyi,sunyi ba har yanzu be farfado ba, gashi yamma tayi, koda su Yusuf sukazo babu dison damuwa a? tare dasu bare su nuna, Sunde hi shiru kawai, sun Kira Binaif sun sanar da Shi, ya fadawa Ummusalma batasan zancen da aka fada masa zaiyi jawo wannan abun ba, hakan yayi Mata kyau fatan ta Allah Kar ya karbi ransa a cikin halinda yake ciki tana so yanemi gafar su, tana masa wannan fatan. Tana kuma so taji dalilin dayasa yaci amanar mahaifin su, shine abinda take so.


('('('('('('('


Baffa Dan Allah ku barni na nemi Salma Dan Allah Baffa,

Baffa yace' wacce yarinyar? Ba wacce ta Baki kudi ba? Daman ita kike bamu labari ko? So kike ta bata ki? Kamar yarda aka bata ta? Yarinyar da sam bata da tarbiya?

Tace' Inni Dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login