Showing 81001 words to 84000 words out of 274760 words

Chapter 28 - KYAUTAR ALLAH

10 Sep 2025

14629

meyede oho.." Cewar Annah

"Farhan yake.." Cewar UmarTsufa se a hnkli.

."touh touh,..ku yaran ynzu Ai bakuda sunayen Arziki, se sunayen Arna kuke sawa daga bedi se Ambedi se faifam.." (Bedi na nufin baby, Am bedi na nufin Am baby faifam na nurin farhan..)

Duk jikojin Annah dake falon seda suka kwasheda daria..Annah ta tsani daria a rayuwarta "kunyiwa iyayenku mata daria.."

Na'im yace "A huce hk.."

"Dan kan babbar bura ubaka ruwan zafi ceni dazakace a huce Hk..she me siffan yan wuta.." Annah ta Antayowa na'im nasa.

Na "im ya kame baki yace "yan wuta har suffa garesu kenan..touh Godia nke.." Cewar na'im

"Durun uwarka waccen bakar.." Ta nuna Anty Asiya..itako se tayi qasa dakai..

Na'im yja bakinshi yy shiru sbda yaji Abun babbane..


"Wannan tsinannun yaran, sesu haukatani..wainishin wabi dan kam babbar duduwar bura ubanne yace a kira taronnan da yarannan..Allah yasa in krajin bakin wani shege..ku kuma kuci gba da mgna ina jinku,daga dukannin Alamude bakuda gaskia, Amma inajinku.."

Musa yaci gbada koro byani knshi na qasa.. "dalilin dayasa muka fasa bashi Aure sbda ya kasance fatsikine, mara tarbia yna lalata da yaran mutane.. shiyasa Allah ya tona masa Asiri tin wuri sbda yaga zuciyoyinmu..." Nan ya bata lbrin yadda Farhan ya Ajiye Na'ima yarinyar deputy govenor of kaduna state ya lalata mta rayuwa kuma ma A takaice Aikinshi kenan lalata yaran mutane, ga shaye-shaye ynayi..

Raslan yji wani sanyi a ranshi harda ajiyar zucia yy.. ''Tanbas biri yy kma da mutum.." Raslan ya fada A rnshi..

itakama KYAUTAR ALLAH wani irin ddh taji harda kara lafewa tyi a jikin daddynta, dmn ta tsani farhan.. A bngaren ummih kam ji tyi zuciarta na tsananta bugu, ta gaza zama se muskuce muskuce takeyi..A bngaren ihsanma hknne ya faru gabanta se faduwa ykeyi, ga sanyin A.C Amma tini ta fara nemanyin gumi..

Annah kam fashewa tayi da kuka harda fyatar majina tana fadin "Hba biri yy kma da mutum, shegen yaro dan iska dakaga idonshi kaga idon karuwar namiji,.. Allah yasoni bnyi gudun garaba na fada gidan zago, aje ayita haifamin tattaba kunne yan iska da karuwai..dana shiga uku! Babban bala'inma ya kwaso ciwo ya Sakawa jikata, Shege dan iska karuwar namiji kawai insha Allahu a hk ze qare..Amma Albasa batayi Halin ruwaba, ga uwarsu ba ruwanta wlhy hajia zilai.."cewar Annah dake fyatar majina da gefen zaninta..

"Daddy to dawa Aka dora.." Cewar na'im danshi be samu halartar daurin Aurenba sbda byanan daga dubai yayonan, sbda Annah tasa ido ma duk wanda bezoba ya bani a gunta..

Annah ta miqa masa dakuwa "Kaci kan bura ubaka! Shege dan iska Me kmada karuwar namibi! Ka zabga uban kwalli sekace bazawari! mnya na mgna kunasa baki, kaida shegencan babana kuna sakowa mutane baki marasa tarbia kawai, shaggu!"

Na'im yayi daria kna yace "Godia muke..daddy dan Allah ku fadi, Allah yasa dani Aka daura Aurenma nifa dmn inasonta.." cewar na'im uban yan tsokala.

Annah ta gallara masa harara ta kalleshi up An down ta zubda miyau gefe tace "dallah rufemin baki dan durun uwa kai! kai nan Akwai wata tsinaniar dazata Aurekane, inba waccan shegiyarba nasmimi take ko ubanwa! Shegiya me siffar yan good evening.." Ta karashe mgnr tna kallo nasreen mtr Na'im dake gefenshi zaune ita uwar yn soyayyah.. "Mtwss Allah wadaran nka ya lalace dubeta fuska kmr tsohon biri, da bakar fuska kai kace bakin na zunubine , zunubinma babbah, Allah yasoni baka haihuba da an bani, Wannan sede a haifa gawayi ko,.." Wasu a falon suka kwasheda daria..nasreen ta hada rai..

Na'im ma yasha mur kna yace "karki, kuskura ki zagarmin mata shan koko kwanciar rai hk ngni nce inaso kmr yadda kakanmu jibril ya ganki yace ynasonki.."

"Kai! ungo naka nan.." Cewar Alhaji umar ya miqawa Na'im daquwa.

"Am sorry daddy.." na'im yace yna rissina kai.

"Bar yan bura uba, a hkde Ai nafi uwayenku yan bura uba kawai...ai dka barshi yaci gbada zagina dan kutmar ubansa, ynzunnan se in tashi in babballashi in jefashi bayan layi, karnuka su cinye.." Cewar Annah data hasala

Kallo na'im ya bita dashi dariama ta bashi wai zata karyashi, kou ta ina zata fara kakkaryashi oho, ita da duk kasusuwanta sun rakwarkwabe rami kawai suke jira..

"Ayi hkri Annah.." Cewar harun.

"Dole kace Ayi hkri tinda baka koyawa danka tarbiyar Arzikiba ...inajinku gayamin dawaye Aka daura Aure da jikata,a gayamin mna inji ko uban waye, Allahde yasa ba a familynnan ykeba sbda bnason Auren zumunci sam...kai ni dman an barshi kawai da ba a doraba, ni nma hkra da Auren A barmin ita tayi kratunta, likitancima nkeso ta krnta...duk nama kra Tsinkewa da lmrin maza.."

Dukkanninsu seda gabansu ya fadi dajin klmn Annah, Ita knta KYAUTAR ALLAH tafiso Ace ba ayi Aurenba, itafa btason Aure sam ,daddynta kawai tkeso a rayuwarta, da da hali dmnshidin ta Aura..alhaji harun yayi jim ya rasama ta ina ze fara mgnr..

Raslan ya zubo musu ido ynajirn yaji dawaye Aka daura Aure da bbynshi.. "Su abbah Akwai karere.." Ya fada a rnshi.

Alhaji musa yayi kukan kura yace "An daura Auren da Muhammadurraslan..."

diffff! Dimmmm!! Dimmmm!! Gaban Annah ya yanke yy wani irin jahilin faduwa, seda knta ya Amsa nan da nan ta farajin jiri.. Kan kace kwabo firgice da dimauta ya bayyane a a kn Fuskartaba,tsabar tashin hnkli seda ta taune harshenta zafine ya ratsata da hk ta dawo hayyacinta, glashin dake manneda idanuwanta ya fadi kasa, da hnzari Anty rukayya ta dauka ta miqa mata, amsa tayi jiki na rawa ta manna a idonta, murya cikeda firgici da tashin hnkli tace "dan gidan ubN waye muhammadun...ku fahimtar dani don Allah! Wlhy bn fahimtaba!" Ta tambaya cikin rudu, Adduarh taketayi A rnta Allah yasa ba Raslan din data sani bne..

"Muhammad raslan dan gidan Umar.." Cewar musa, daya qara yl kukan kura ya fadi hkn kawai kwara a wuce gurin, cewarsa..

ba Annahba gaf Duk Me ran dake falon seda ya razana, Dajin klmn Alhaji musa, Ummih ta lumshe idonta ta bude tna kaiwa knta duka, Itafa a ganinta mafarki takeyi, firfita tashigayi da gefen mayafinta, sbda tashin hnkli, nan da nan zuciarta ta shiga up up , tanada tabbacin daza a dubata a Unzu hk tnada hawan jini....

A bngaren Ihsan kam tin a mgnr farko ta dimauce ta biyun kam gigitata, tayi, kadan ya rage tayi hauka na bin bola, kn kujera take Amma seda ta zamo qasa tim!, tayi zaman dirshan a qasa, i mean zaman yan bori, dukda sanyin dake falon se kawai zufa ta fara karyo mata,tuge dan kwalinta tayi ta Ajiye A gefe, nan uban gashin dokin dame knta ya bayyaba a gadon bynta..

bngaren Raslan kam abinda yaji baze misaltuba, hk kawai ya tsinci knshi a farin ciki, mara misaltuwa ya rasa dalilin hkn, Harga Allah yasan ynason bbynshi so me gigita zucia da gangar jiki "Alhamdulillahi..rabon kwado.." Ya fada a rnshi..KYAUTAR ALLAH kam dukta rude ta yaya zan Aura mahaifina.." Ta fada A rnta.. A bngaren Alhaji Umar ma yaji ddh sosai yy farin ciki Ainun.. Hk Anty sadia ma farin cikine ya lullubeta, ta kalli Ihsan datayi zaman yan bori a kasa, kai bb dankwali kai kace mahaukaciyace sabon kamu..

na'im ya dafe goshi shifa yaso ace shiya samu small bbynnan Amma bkm aiduk dyane ya fada a rnshi,tsaf matarshi ta lura dashi tin a mgnr farko dyace ynadon KYAUTAR ALLAH, amma ta dauki hkn wasa,...

a bngaren Anty rukayyah taji ddh Ainun..hk anty fahima,duk fam din Alhaji Abdullahi sunji ddh,.. Kowa se cewa ykeyi perfect match.

Annah ta tuge dan kwalin knta ta ajiye a gefe ta sosa knta rai a bace zufa se aikin bin goshibta takeyi,kai kace qarya tayi..nan ta shiga katse zufar dake keto mata tna yarfarw..

Yarannata se kallon reation dinta sukeyi hnkli a matukar tashe..

"Jar ubannan kan yasa! Durun uwa inji baban lantana! Wai kuna nufin Muhammad dan gidan zainabu da ummaruru nawa?" Ta kra tambaya dan tabbatrwa

Duk sukayi jim tabbas sunga tashin hnkli a kn fuskarta..

"Dan kan babbar bura ubaku badaku nake mgnaba!" TaYi mgna a fusace..

"Eh shi...shima knshi besan da Aurenba Annah, inada tabbacin shi knshi se ynzu yakejin mgnr, ...hk Alhaji umar ma.."cewar Alhaji Abdullahi.

"Rufemin baki munafuki!" Tacewa Abdullahi... "Innalillahi wa'inna alaihiraju'un Allahumma ajirni fi mutsebati wa akalifni khairan minhan!.." Shine abinda Annah ta fada kawai ta zube nan sumammiya, sbda tsabar firgice.. Nan hnkli ya dawo knta amma bnda ihsan dan nata tashin hnklin yafi na Annah zuwa lokacin ta fara kuka ma.. duk wanda ke falon dawowa sukayi suka tsaya knta Alhaji harun da musa zucia cikeda nadama sbda suna neman su kashe uwarsu da knsu..KYAUTAR ALLAH ma tini ta isa inda Annah ke kwance sumammiya ta fada jikinta tna kuka,...Alhaji harun ya dauko bottle water na faro a frij yaxo ya bude ya fara yayyafa mata, Ajiyar zucia ta sauke Amma bata farfadoba...Raslan na ganin hkn yy wani irin murmushi ynabin kyautar Allah da kallo, kawai ya juya yabar falon, Ya tsallake Ihsan wadda sam btama gnshiba sbda tashin hnkli..ba Wanda ya Ankare da fitarsaba se Anty sadia.. Zuciarshi wasai kmrta jarirai..Anty sadia ta biyoshi waje itama tna farin ciki tace "Son!" Ta kwalo masa kira, juyowa yy yna kallonta murmushi ta sakar masa hk shima ya sakar mata murmushi.. Hannu ta kawo masa suka gaisa cikeda wasa tace "Congratulation! Congratulation!! Congratulation agains,my son Na tayaka murna..kasha shagali nawan knada sa'arh,,,maza kyi hnzarin barin garinnan tin Annah bata farkaba daga suman datayi.." Se kuma ta kalli time tga kusan 10:pm ne "kode zaka bari gobene..."

Raslan ya sosa keya yace "nop ynzu zan tafi Anty ...Ai kasarma barinta zanyi, wannan tsohuwar case ce.."

"Good my son..kyi tunani, Don Wlhy Akwai kura..Allah ya tsare.." Cewar sadia

"Ameen my sweet mom.." Har bakin car ta rakoshi ya shiga yna shiga ya kashe gaf wayoyinsa dreva yaja suka fice dga gidan se smling din mugunta ykeyi, ya tabbatr yau yasawa Annah dull tension..

Byn tafiyrsa Anty sadia juyowa tayi ta dawl falon, zuwa lokacin Annah ta farfado byn An zuba mata gorar ruwa har uku kna ta farka a hnkli ta bude idonta tna Ajiyar zucia, tna bin kowa da idonta da bta gani sosai dan tini glashin ya fadi, Anty sadiace ta dauko tasa mata...nan ta qara kurawa kowa ido, Abinda ya faru ya dawo sabo a rnta... Fashewa Annah tayi da kuka tna fyatar majina "Ynzu ni zaku cuta ku ha'inceni ina uwarku indau cikinku, wata tara da kwana tara, kai musa seda kyi wata goma da kwana goma sha daya a cikina kna na haifeka Amma hk zakuyimin? Wanda ya bada shawarar daura Aurennan da babana Allah ya.."Anty rukayya tayi sauri ta rufe mata baki "Dan Allah dan Annabi kada kiyi Allah ya isa, pls Annah bakin uwa beda kyau.." Cewar Anty rukayyah

"Gaskia kam Annah Ayi hkri Dan Allah, qaddarace wadda ta rigayi fata.." Cewar Anty fahima.

Kwace bakinta tayi daga Hannun rukayya tace "Ki barni kawai Rukayyah nikadai nasan me nkeji a raina wlhy yarannan sun cuceni Abinda na guda shiya faru jinin Zainabu Wlhy bna kaunar jininta sam, kmr yadda bn kaunarta...."

Wani irin zafi Ummih taji a rnta ta rasa me tayiwa Annah ta tsaneta har haka..nan Ummih taji ta qara tsanar Auren, kyautar Allah da danta Raslan..

"Ayi hkri dan Allah Annah.." Cewar Abdullahi..umar da harun da musa suka hada baki gun bata hakuri..

Fashewa da kuka Annah ta qarayi, "bana kaunar Aurennan ko uban hkri za a bani ba hkriba, jikata baxata Auri sauran waniba kwara ta dauwama bb Aure, Ni bnasonshinema kwata-kwata, me sonshima bnasonshi...."

Lumshe ido Ummih tayi sbda yadda klmn Annah,ke mta zafi a zicciya..

"Amma Annah butuluce..raslan ya sadaukar da komi nasa ya raini yarinyarnan amma sakayyarta shine ta tsaneshi..gaskia hkn beyiva.."Na"im ya fadi da a hnkli a hnkli mtrsace da ummih kawai sukaji.. Tsabar takaici seda hawaye me zafi ya digowa Ummih..

"Ina wannan d'an.." Cewar Annah.

Harun yace "Gani nan.."

"Ina musalle.."

"Ganinan.." Cewar musa.

Annah tayi jim kna tace "Ina ummaruru.."

"Gani nima Annah.." Cewar umar.

"Ina yke shi baban nawa, dan uwarsa.." Cewar Annah.

Nan suka shiga waige waige, sukaga basu gnshiba.. Anty sadia tace "Ya fita An kirashine a waya.."

yunqurawa Annah tyi da niyar ta zauna, suka kamata ta tashi zaune, rai a matukar bace ta fara mgna "Wallahi kou bngon dunia yaje inya dawo seya sakarmin jikata, bna kaunar Aurennan kou misqala zarratin..ni kwarama Ace dashi mazinacin Aka daura da Ace da Wannan yarom Aka daura,ni A'ee jinin Zainabu,! Allah ya sittiramin, ubangiji ya tsari kakata kuluwa da sarar roko..Wallahi kunji na rantse In har yaronnan be sakarmin jikaba to tabbas sena tsine muku kunbi dunia dukkaninku, kunji na gya muku...dan hk ku nemosbi duk inda yke ya sakarmin Jikata kowa ya huta, inba hkba bb wanda ze huta kunji na rantse..aka gya muku nemn kai nkeda ita...." Tna gma fadar hkn ta miqe ta lalubo sandarta tabar falon tna kwallah, a bakin kofa taga Ihsan na zaune zaman yan bori tana kuka, Annah batabi takaNtaba illa iyaka ta taka mata kafaduwa Ta fice Abunta, cikin zafin rai
...

sbda tsabar bakin ciki dakecin Ihsan batamaji zafin takawar da tayi mataba, zafin dake knta yafi wannan..KYAUTAR ALLAH kam kara lafewa tyi a kn kujera tana tsotson yatsunta, sam hukuncin Annah beyimataba harga Allah, se raba ido take tga inda zataga daddynta, a tunaninta yje ya dawo ne....anty sadia ta kamota suka fice a falon "Anty ina daddyna.." KYAUTAR ALLAH ke tmbyr Anty sadia byn sun fito compound din gidan, zasu nufa side din da anan Anty sadia ke kwana...

"Ya tafi Abuja.." Cewar Anty sadia

"What!" KYAUTAR ALLAH ta fada da karfi..


"Yeah..kada ki damu knji small bby.."

"Tom.." Kawai KYAUTAR ALLAH tace..

Watsewa sukayin kowa yy a falon yaragedaga ummih se Ihsan da kafafuwansu ya gaza daukarsu, ihsan de na nan zaune kmr yar bori, tna hkn sadia dasukazo fita sedata takata..Yawancin duk wanda ya fitama sedaya takata.

Alhaji harun da musa da umar da abdullahi suka nufa wani falon dansu kara tattaunawa.. Tattaunawa sukayi kn yazasu shawowa kn Mgnr KYAUTAR ALLAH da raslan, nan suka ynke shawarar su kira Raslan kawai in besonta ya saketa kowa ya huta...nan take alhaji musa yy dealing number dinsa a kashe, Alhsji umar ya kira sauran lambobinsa duk a kashe, Ajiyar zucia dukkaninsu sukayi suka zauna jingun jingum kmr Anyi musu muruwa.. Nanko kowa da abinda yke saqawa tabbas suna tsaka mebwuya..

Lalubo waya ummih tayi ta fara dealing numbers din Raslan kmr zautacciya, duka Amsa dayace number a kashe.. Goge kwallar dake zubo mata tayi ta nufa inda Ihsan ke zaune tna kuka tna birgima A kasa tna yamutsar gashin dokin dake knta, kai kace mahaukaciace..kamota tayi tna fadin "hba mna sweetheart, meye hk pls.." Ummih ta fada cikin lalama

Fashewa ta qarayi da kuka tna fadin "Ummih wannan wacce iriyar mummunar qaddarace nkeda ita..Wlhy bnason mijina ya qara Aure..ummih haukacewa zanyi, wlhy ynzu hkma na fara hauka, titi kawai ya rage inbi, zanbi bola wallahi ummih! Zanyi tsince tsince, inde mijina yymin kishia..ummih zuciata tnamin zafi taba kiji qonewa xatayi..nashiga uku wayyoo!"ta kamo hannun Ummih ta dora saitin zuciarta, nan ummih taji yadda zuciarta ke beating da karfi,hnklintane ya tashi se bargon tausayinta ya lullubeta, tace "hba Ihsan a kn meye zakisa kanki a tashin hnkli hk..Auren nefa kawai Aka daura Amma ni bnaso hk uwar gayyarma Annah bataso, daga gani wannan kullin na Alhaji Harun ne Da Alhaji musa, kuma seya saketa kinadejin Abinda Annah tace ...pls darling In-low ki kwantarda hnklinki hba in-low.." Ta krshe mgnrda sigar rarrashi.

"Ummih pls ki kirashi kice yazo ya saketa inba hkba ki tsine masa pls,...way! ummih baxan iya kishi da yarinyarnanba, ba ajina bace.." Ta fadi hkn kmr zautaccia, se wani nishe takeyi knr wadda bura ke wutsil wutsil a cikin durinta..

Tausayi ta bawa Ummih sbda tasan Abinda takeji A zuciarta, kishia kouya take tnada zafi."Yi hkri mna ihsan nasan me kkji a zuciarki Bnsamu numbers dinsa bne kiyi hkri, yau dinnan zan koma garin abuja sena sashi ya saketa sbda nima in samu sassauci mtrnan ta tsaneni bta kaunata sam.inhar be saketaba bazata barninin hutaba nima..." Ta qarashe mgnr tna kallon agogo dai-dai goma da rabi. Da kyar Ummih ta rarrasheta ta samu tadanji dama dama a rnta, amma har wata rma tyi nan da nan duk tyi nadamar dole..cikin daren ummih taso barin garin Abuja daddy ya dktr da ita dole ta kwana katsina Ammafa kwana tayi tna kiran wayarshi shiru bata shigaba, Alllah-Allah ummih tarinkayi gari ya waye,,,aiko 6:am dreva yajasu itada ihsan din, da bby khair taje duba sadiama side dibta bta gntaba tin lokacin ta fita daga side din tana garden hk kawai ta tashi da shaukin hkn..

Ita kuma Ummih setasha tna side din Annah ne, dan hk ummih tyita jaraba a motar... ko daddy be saniba seda sukahau hnya kna ta masa text tnayi masa ta kashe wayar gabaki dya, sbda harshi haushi yke bta...

Raslan kam cikin daren ya iso garin Abuja, a daren ya kira Saif dmn saif bya bacci da wuri.. "Hellow Ango kasha kamshi.." Cewar saif yna kwashewa da daria..

Cikeda mamaki Raslan yace "Wai dmn ka sani Amma shine bka Ankarar daniba.."

"Nasani wlhy, nida Aka daura A gabana a kn sadaki dubu dari uku, Alhaji DaddyM ya bada, shiya hnani in snr dakai..amma ynzu nasan ka sani.."

Raslan yy wani murmushi yna qara juyi a kn gado..

"Uba ya zama uban yarsa Abinda ya rage ya sata ta kalli silin, yyta zungura mata jela.." Cewar saif

Raslan yy suki kna yace "Kai dakikin ina ne..in raini yarinya kuma in cita..lallai bkada hnkli.."

Saif yace "Sannu alaramma, A wani hadisin Akace bazaka zunduma mata jelaba..Dallah malam, Shiga hnklinka ka kwashi kyn ddh..daga gani yarinyarna zatayi dadih..kai harfa nacema daddy a daura Auren dani, danni Inaso.." Yy mgnr da zolayane,

Wani irin mugun haushi ya bawa Raslan yace "Wawa kai..dallah ba wannanba..nifa nan nasan Anacan Ana nemana kmr kudi, ko ince kmr nyi kisan kai.. .."

"Kmrya.." Cewar saif

Raslan ya kwasheda daria yace "Kai Annah fa har suma tayi sbda taji lbrin dani Aka daura auren.."

Saif ya zaro ido yace "Ka rantse da Allah Abokina!"

"Wallahi!"

Saif yace "Kai mutumina! Amma tsohuwarnan itace zata hna ruwa gudu yaseen.."

Raslan yy murmushin mugunta yace "Ita ta isa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login