Showing 258001 words to 261000 words out of 274760 words

Chapter 87 - KYAUTAR ALLAH

10 Sep 2025

14623

bincika zuciarta dan farin ciki...duk wanda yazo ganin bby fah Annah taki bada babys ta kamasu ta riqe a hannunta gam babu me amsarsu da ance ta kawosuma seta dura maka zagi, hk kowa ya hakura ya bar mata baby, aka basu zam-zam kafin nono yaxo, da nonon yazo kuwa suka cafke suka hau tsotso RASLAN se kallo yakeyi tanata yatsina fuska saboda zafi Amma hakanan ta jure bata da yadda zatayi Anty Rukayya ta sata a gaba... Satinsu daya a asibitin aka sallamesu zuwa gidan Annah suna zuwa sukaga an canza komi na gidan ansa sabbi masu kyau da tsada an canzana gidan penti da de sauransu, duk aikin RASLAN ne, Annah tayita sanya masa albarka. Nan aka fara shirye shiryen suna daza a gudanar nan da sati me zuwa. .... Raslan ya saki kudi na fitar hayyaci dan gudanar da bikin suna, yayi other din manyan zannuwa da laces daza a raba ga duk wanda yazo bikin sunan, ciki Hadda mota kirar 206 da de sauran motoci na mata za a raba game rabo, da gidaje, duk daga bangaren Alhaji musa kyautar gida da motan suka bullo. Ummih na nan da ita za ayi shagalin sunan ta sanar da hajiya saude ta kd tace itama zatazo, duk ummih tayi tata gayyar. Ihsan kam data samu lbrin haihuwar a gun humaira matar saif, karamin haukane kawai batayiba taje ta samu bokannan ta rinka sirfafa masa zagi, da kyar maryam ta lallasheta, ta jawota suka dawo gidanta tayi zaman dirshan a kasa ta fasa ihu, maryam ta shiga rarrashinta, rnrfa seda maryam ta kira malamin anguwarsu yama ihsan rukiya ko aljnune, malam ta gaji da karatun iskokan basu saukaba ya yayyafa mata tiraren aljanu amma duk basu saukaba hakanan ya barta tanata haukanta, maryam ta zauna ta raf uban tagumi ta zuba mata ido saboda tayi iya nata amma bata hakuraba, dan haka ta batta inta gaji dan kanta ta bari, ai kuka ba kida bane, ko kidama aka gaji ballan tana kuka.....






*saura kirisss....... Tnks for the love fans.😍*
[8/24, 19:43] Sa'adatu Bintu Abdullahi: 🅿️59

*PAID BOOK...500 ONLY...08136349646*

SAADATU BINTU ABDULLAHI✍🏽

Ranah bata karya sede uwar diya taji kunya! (Inji bahaushe) Ranar jumma'ah akayi bikin sunan yaran KYAUTAR ALLAH da alhaji RASLAN, inda hassana taci sunan Annah wato Aisha aka lakaba mata (Meead) ita kuma hussaina taci sunan Rukayya (wato mahaifiyar KYAUTAR ALLAH kuma sunan KYAUTAR ALLAH) ana kiranta da (Hannaah) kowa ya hallara dangi da abokanayen arziki, hadda na tsiyarma duk sun hallara, Ciki kuwa hadda ihsan Da qawarta Maryam wadanda gulma da kallon kwakwaf ne ya kawosu. Fatima da mamanta ma sun hallara, sun kawo kyaututtuka ba gani na fada, hajiya saude ma tazo da kyautar ta me tsoka, da matar saif dashima Saif din, duk sunzo da sha tara ta arziki.

KYAUTAR ALLAH ta cancare cikin lace me tsadar gaske kalar maroon color me flowers milk, cikin kayan da Raslan yase mata, wuyanta kuwa gold ne kawai ke magana, haka hannunta tako ina de tasha ado ga kunshi hannu da kafa, sumar kanta tasha gyara, ta hadu iya haduwa kmr a saceta a gudu, hatta takalmin data saka a kafarta abin kallone, haka suma jariran duk an musu ado na fitar hankali kafa hannu wuya duk gold ne a jikinsu, an ninka tsaro matuka a gidan dama duk anguwar saboda sunan cuteness din RASLAN. Shima knshi angon karni ba abarshi a bayaba se cancara ado yakeyi, da kyautar ALLAH ta canza kaya shima ze shiga ya canza kaya haka suma babys se canza musu kaya akeyi, a awa daya sun chanza kaya yafi kala goma, duk inda sukabi masu videos nata binsu suna daukarsu, anty Rukayya da Anty sadia suke riqe da babys din. Annah ma ta cancare, ta cakare taci ado cikin dankareriyar shaddarta me walwali,,, ihsan de duk inda sukayi se binsu takeyi da ido ita da qawarta maryam Zuciyar ihsan se barazanar tarwatsewa takeyi, musammanma dataga anata hidimar arziki RASLAN ya balle hannu se barin kudi yakeyi kmr besan zafinsuba, daddyU yazo ya sauke kudi kirar dala dalah jaka daya yace na bbys sannan da company dinsa dake Lagos guda biyu yace duk na babys, DaddyM kuwa tashi KYAUTAR ta gigitace company dinsa na hada jirgin sama yabawa jariran kyauta, daddyH kuwa gidajensa manya manya guda biyu dake waje ya bawa jarirai kyauta da makudan kudade, Alhaji abdullahi KYAUTAR motoci ya basu masu kyau da tsada se kudade... Duk wanda yazo a family seya ajiye tasa kyautar zuciar ihsan kmr zata fashe nan taji tana sha'awar itama ta haihu kodan wadannan kyaututtukan da KYAUTAR ALLAH da yayanta sukasha, abunfa zar sha'awah ga masoya amma abin bakin ciki ga makiya...abinci kuwa anyi yafi kala talatin, ko ince ana kanyi, sannan ga drinks iri daban daban se abinda kkeso zakaci zakasha masu serving ma daban akayo hayarasu sunfi mutum arba'in, saboda yawan mutanen dake gidan ba kadan bane (knusan mutanenmu na yanzu da kwadayi inba kana dashiba babu meyi dakai, ko sha'aninka ba azuwa sena masu shi, saboda kwadayi da son abin dunia, pls mu gyara halinmu talauci jarabawace hakama arziki jarabawace, Allsh yasa mu dace) A cikin taron jama'arh nan da Annah ta kyallara ido taga ihsan tasha zagi da habaici har ce mata ta rinkayi juya, wadda bata haihuwa... Sosai ihsan ta kule Amma de ta shanye saboda bata da yadda zatayi... Tin safe akayi walima aka rarraba kyaututtuka na fitar hankali wasu gida suka samu wasu motoci wasu atamfofi wasu laces wasu kuma riguna jallabia wannan KYAUTAR daga hannun ummih ta fito, wasu kuma kyautar kudade, wanda ya fito daga hannun Anty Rukayya.... Da yammaci RASLAN ya kama tamfatsetsen hall a can kuma aka yada zango, Sukayi shiga ta Alfarma shida KYAUTAR ALLAH da cuteness dinsu, aka kira mawaka daban daban ranar kam daloline ke magana, bandir bandir aketa ballesu ana watsarwa... RASLAN ya shifa watsi da bandir bandir na dollars yanama KYAUTAR ALLAH liki dukda ba rawa takeyiba, hajiya Annah kuwa se gyada kai takeyi Anty Rukayya na mata liki,, Ihsan kam na gefe zuciarta na barazanar tarwatsewa... Ansha hotuna daban daban da video iri iri,..basu suka bar hall dinnanba se 12:am suka nufa gida daman KYAUTAR ALLAH duk a gajiye take, kwancia kawai tayi tayi baccinta tabar su Anty Rukayya da anty sadia da cuteness dinta. Ihsan kam daganan asibiti suka nufa ita da maryam saboda a mota ta zube a sume saboda bakin ciki...

Seda akayi sati cir ana bikin sunan a sati na biyune mutane suka fara watsewa kowa ya kama gabanshi amma banda Anty Rukayya wadda tace bazata koma gida ba se KYAUTAR ALLAH tayi arba'in, ... RASLAN kam ya zama kmr wani na mamajo tin kafin yan biki su watse yaketa bin KYAUTAR ALLAH duk inda tayi seya bita mutane se binsa sukeyi da ido ciki hadda ummihnsa, daya samu mutane suka watse kuwa ai nan abun nashi ya karu yaci uwar nada..... Sati daya period din KYAUTAR ALLAH yayi ya dauke, anty rukayya na ankarewa da hakan kuwa tacema KYAUTAR ALLAH kada ta kuskura ta bari RASLAN ya gano hakan, danta kula rawar kanshi yayi yawa, a hakanma dukya kosa su kebance ta bashi gindi yaci gaba da gabza,,, Anty Rukayya ta matsa sosai gun gyarama KYAUTAR ALLAH jiki da kayan gyara masu kyau da inganci daman tini ta tanadesu, musammanma na matsi dana karin ni'ima dukdade bada kanta ta haihuba Amma ai tanada bukatar gyara, Aiko ta fara shan gyaran dan a sati daya taji jikinta ya canza kullum cikin canza pant take saboda yoyon datake tayi kmr an kunna famfo... ALLAH ya bata lafiyar shayarwa se feeding babys dinta takeyi da nononta dayake tanada ruwan nono sosai, sannan kullum cikin mata kunun kanwa takeyi... ALLAH ya daurawa Anty Rukayya son jarirannan ita da Annnah bnsan gwaniba, da kuma fahima da sadia kullum cikin kira suke suna tambayar lafiyar cuteness.


Kwanan ihsan biyu a asibitin ta kira RASLAN tace masa bata da lafia tana asibiti, yace ALLAH ya kara sauki..tayi jim kana tace "Baza kazo kaga jikin nawa ba,kwana na biyu fa ina kwance.." Da kmr zece eh se kuma yace "turamin adress din asibitin zanzo anjima.." Yana fadar hakan ya katse wayar, ba jimawa kuwa ta tura masa da adress din asibitin. Da yammaci ya shirya cikin kananan kaya wadanda suka amshi jikinshi yayi kyau ainun. Ya fito falon se sheki yakeyi jikinsa nata barin kamshin perfume dinsa.. Zaune take a falon ita da anty rukayya wadda ke riqe da Meead ita kuma tana riqe da hannaah tana bata nono, Sanye takeda doguwar rigar atamfa me zip a gaba saboda bada nono Aka mata zip a gaban rigar, kanta babu dankwali sumar knta se sheki takeyi, ya karaso falon idonshi na knta, itama dagowa tayi ta zuba masa ido kallo daya ta masa taga yayi mata kyau Ainun. Karasawa yayi ya amshi hannaah dake hannunta ya amshi meead dake hannun anty Rukayya, duk ya manna musu kiss a kumatu ya rungumesu a jikinshi duk abinda yakeyi idonshi na kan KYAUTAR ALLAH, wadda ke maida nononta zuwa cikin riga., lashe baki yayi saboda idanuwansa dasuka sauka a kan nononta dake zubda ruwa, saboda hannaah ta jawoshi bata shanyeba ya amsheta. "Zan sha nono.." Ya fada a hnkli ta yadda ni dayace zanji, kasa nayi da kaina danni a sorace nake dashi Anty Rukayya tacemin ina bari ya kusanceni zanyi wani cikin , niko banaso saboda nasha matukar wahala.. Murmushi yayi idonshi na kaina ya kara kissn yaranshi kana ya mikawa anty rukayya Meead ni kuma ya dawomin da hannaah. "Zan fita ne.." Ya fada idonshi na kaina, dagowa nayi na kalleshi kana nace " ina zakaje?" Shafar sumar knsa yayi yace "ihsan ce babu lafia tana asibiti, zanje inga yaya jikinnata..." Ido na bishi dashi harya gama mgnr, seda ya idar na dauke kaina a knshi saboda ji nakeyi kamar in tashi in haushi da duka, kishinshi ya turnikemin zucia, dauke kaina nayi daga gareshi,, inajinshi yayima Anty Rukayya sallahma ya fice a falon, Dai-dai Annah ta fito daga bedroom dinta tazo ta dauki hannaah dake cinyata, na mike na bar falon na nufa bedroom din Annah saboda zuciata zafi takeyimin kmr zata fashe, kwancia nayi a kan bed a zuciata se ayyana abubuwa da dama nakeyi, gani nakeyi kmr inyaje zeyi sex da ita ne har ina ganin abun a idona wai yana cinta rinte idona nayi gam inajin kaina na azabar ciwo,..Anty Rukayya ta shigo dakin ta zauna a gefen bed din duk bansaniba, ta tabani, firgigit na bude idona a kanta, hannunta rige da Meead wadda keta bacci ta kwantar da ita akan bed din. Kana ta zuba min ido, tin tasowata ta kula da abinda ke damuna shiyasa ta gaza hkri ta biyoni. "Me kike tunani?" Anty Rukayya ta tambayeni, shiru nayi na wasu yan daqiqu kana nace mata "bakomi mommy.." "Ba gaskia bane.. Gayamin me kike tunani?" Na kara ce mata ba komi. "Ni nasan me kike tunani mijinki kou?" Na zuba mata ido taci gaba da magana "Kishin mijinki ke damunki kou?" Ta kara jefo min tambayar idanuwana suka shiga kokarin kawo ruwan hawaye na shanyesu kana nace " kinaji fa Anty Wai zeje gun matarshi..." Kawai na fashe da kuka. Ta shiga rarrashina danta kula ina cikin jerin mata masu bala'in kishi. "Kukan me kikeyi? Me kike nema a gun dana miji da baki samu ba a rayuwar aurenki dazaki zauna kina kuka a bnza a kan kishiya? Meye ba yayi miki, kullum a gigice yake saboda ke, shine zaki damu kanki a kan wata kishiya? Tin wuri ki kwantar da hnklinki inba hkba seki rame a bnza a hofi..." Shiru KYAUTAR ALLAH tayi tana sauraren kalaman Anty Rukayya, haka kawai taji zuciyarta tayi sanyi.... "Ki kwantar da hnklinki knji?" Anty Rukayya ta kara fada mata cikin tafshin murya KYAUTAR ALLAH tace "to mommy shikenan..."


Tin kafin ya karaso maryam ta shiryawa ihsan tuggu iri iri saboda maryam tafi ihsan wayau ta wannan fannin, ita gam take rige da mijinta A hannu... Yusuf ne ya kawoshi asibitin seda suka tsaya a gun siyayya ya siyo mata kayan dubia masu dunbin yawa, kana suka iso asibitin... Yana shigowa dakin ta kara langwabewa yusuf ya gama shigo da kayayyakin dasuka siyo ya gaidata ko amsawa batayiba, daman be tsammaci hk daga garetaba ya juya ya fice a dakin. RASLAN ya karasa bakin bed din datake kwance se kara narkewa takeyi ya zauna haka kawai yaji tausanta ya ratsashi , yace mata ya jiki ta amsa da dasauki dakyar, irin ita a dole mejin jikinnan. RASLAN ya juya ga maryam suka gaisa ta tambayeta ya jiki ta amsa da dasauki,,, ya miqe kmr ana tsungulinsa da zumnar ya tafi ihsan ta riqoshi tace "ai dr yace yanason ganinka, pls karka tafi ka bari ya dawo ya fita ne, tin safe yake tambayarka..." RASLAN yace okay, ya koma ya zauna se shafarshi takeyi ita a dole ga karuwa,, shiko nan da nan jikinsa ya fara saki, ya mace ma gabaki daya....Da kissa da kisisina ihsan ta rikeshi a nan har tsakiyar dare ga bacci na idonshi karshede nan bed din datake kwance ya raba ya kwanta bacci ya kwasheshi, ihsan ta saki murmushin mugunta, ta koma ta kwanta da wayarshi a hannunta ta danna screen din taga picture dinsa ne shida KYAUTAR ALLAH da cuteness dinsu , dukda ita makiyiyace Amma tasan sunyi kyau sosai, kmr a sacesu, Ammafa kasan zuciarta ji takeyi kmr ta kashesu har lahira...dubawa tayi taga Maryam tini tayi bacci a kan gadon me jinya.

Har dare KYAUTAR ALLAH taga be dawoba, se dubawa takeyi Amma ina har kowa yayi bacci ya batta tana jiran dawowarsa be dawoba, har 2:am, ta dauki waya ta kira lambarsa bugu daya biyu akasa mata busy ta kara kira, akasa mata busy, kira uku tayi anasa mata busy kuma duk aikin ihsan ne bakin ciki ya turniqe zuciar KYAUTAR ALLAH saboda ga zatonta RASLAN dinne kesa masa busy... ranar fa kwana tayi bata rintsaba kawai ta riga ta ayyanawa kanta yanacan yana making love da ihsan ne shiyasa yaketa sa mata busy hk ta kwana bata rintsaba zuciarta kmr zata fashe...

5:am ya farka daga baccin daya kwasheshi yana bude idonsa yaga a asibiti yake, shaf ya manta yasha a gida yake, tashi yy jiki na rawa ya dauki wayarsa ya fice a dakin, time din ihsan da maryam duk suna baccih. Seda ya tsaya yy sallah a masallacin asibitin kana yusuf ya jashi zuwa gida. Tana kwance a kan dadduma tana lazimi taji shigowar motarsa ta leka taga shine, ya nufo kofar falon ya hau bubbugawa tanaji tayi bnza dashi, se Anty Rukayya ce ta tashi daga kan daddumarta taje ta bude masa ya shigo direct dakin ya nufo, idanuwansa suka sauka a kan KYAUTAR ALLAH dake zaune bisa dadduma ga alqur'ani me girma a hannunta tana karantawa. Karasawa yayi gadon yaranshi duk ya duddubasu yaga se bacci sukeyi hnkli a kwance ya manna musu kiss tare da adduarh kana ya dawo ya gaida Annah dake zaune gefen bed da carfi a hannunta tana lazimi , Annah ta amsa a mutumce..suka gaisa da Anty Rukayya.. ya gaida KYAUTAR ALLAH taki amsawa kmr ma bata jishiba,.. "Amma de ba gidannan ka kwana ba Yau kou?" Annah ta jefo masa tambayar saboda ta saba ganinsa duk dare yana zuwa ya tofe yayanshi da adduah amma bezoba jia ta yadda akayi ta gane kenan. Sosa keya yayi yace "Eah wallahi.." KYAUTAR ALLAH na satar kallonshi. "Ina ka kwana?" Annah ta jefo masa tambayar. "Asibitih...inata jiran dr ne yace yana son ganina bnsanma bacci ya kwasheniba..." Annah ta bishi da ido ta tabe baki tace "Kawai kace ka hadu da makircin mace kawai tasaka kwana a asibiti..." Sosa keya RASLAN yy hadi da mikeqa ya fice a dakin ba tare daya ce komiba KYAUTAR ALLAH ta bishi da ido cikin bakin ciki da kunshinsa.... Coffee yasha yayi wanka ya koma ya kwanta bacci ya kwasheshi cike da bukatuwa da ita amma ynzu tinda yaga tayi tsarki se yasan yadda yayi ya dangana da gindinta...

Ranar wuni tayi jikinta sakaka ko abinci kadan kadan takeci sabanin da, datake cin binci sosai, shiyasama ta fara narka uwar kiba seta danyi duhu saboda ruwan zafi da Annah ke dundumata dashi kullum 2times take mata wankan jego gashi wamkan towel.

Washe garin ranar su ihsan suka koma abuja, zucia bb ddh, basu yada zango a ko ina ba se a gidan hadiza, ta kwashe komi na shagalin bikin ta sanar da ita, daman already hajiya hadiza ta gani a t.v , haihuwarma a bakin ihsan taji ba a bakin ummih ba, aiko ummih tasha wulaknci a gun Hadiza data dawo daga katsinar. Nande suka shiga shirya ta yadda za ayi ihsan ta haihu itama, suka hau kulle kulle iri daban-daban...

Kwata-kwata KYAUTAR ALLAH ta daukema RASLAN kafa, ko gaisawar arziki basuyi in tana zaune a gu ya shigoma tashi takeyi ta bar masa gurin, duk yana ankare da ita da abin ya isheshi shine ya samu Anty Rukayya ya tambayeta ko yayima KYAUTAR ALLAH wani abune, anty rukayya ta jinjina kai tace "Bana tunanin hakan..." RASLAN yy jim kmr me shirin yin kuka kana yacr "to meyasa take yimin haka Anty? Ko bakiga abinda take min bane..gaskia akwai abinda de na mata dan Allah a bata hakuri ta yafemin bnsanma nayi ba, Amma de tayi hkri..." Anty Rukayya ta zuba masa ido yana mgnr kmr wani mara hnkli, har wata yar rama ya kara a kwanakin nan. "Ka tambayeta ne tace maka ka mata wani abu?" Cewar Anty Rukayya. RASLAN ya kara marairaicewa "Ta ina ma zata, tsaya in tambayeta Anty, danazo gufa seta gudu aide kina gani , kinga kuma se tayita hade rai, bazan iya mata magana ba tsoronta nakeji wallahi Anty ..." Karashen mgnr tasa se

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login