Showing 102001 words to 105000 words out of 274760 words

Chapter 35 - KYAUTAR ALLAH

10 Sep 2025

14616

biyar kna yasha exotic ya danyi 30mnt a zaune yna duba system dinsa daga bisani ya tashi ya nufa toilet yayi brush ya fesa mouth perfume. kna ya dawo ya kashe system din ya mayarda ita gun zamanta, duba phones dinsa dayake using a nigeria yy yagansu duk a kashe, a kashen ya barsu.. Kunna wayarshi dakeda Sim din USA, yy already dmn sim din nada rijister din dazeyi Amfani ako ina.. KYAUTAR ALLAH ce ta fado masa rai, murmushi yy hadi da fadawa kn faffadan gadonshi ya shige cikin blanket dinsa me uban laushi ya runtse ido , bb abinda yke gani se kyakyawar fuskarta,,, "my fine ness.." Ya fadi hkn a fili cikin siririyar muryarsa me kamada sarewa, nan da nan bacci me jahilin dadih ya kwasheshi, dmn idanuwan nasa a buqace suke da baccin, a hnkli yake shakar iskar Nigeria yna baccinsa me cikeda kwanciar hnkli ammafa kwanciar hnklin 43% ne sam bekai 100% ba, rabi na gun tunaninta...

A hnkli Annah ke hayewa kan upstairs din duk step daya seta tsaya tayi 5mint ta huta kna taci gaba.. "Allah dawaran baturen da yy wannan benen, uban meye a cikinsa inba whlaba.." Cewar Annah dake hayewa da kyar Still taci gaba da mita"amma kou wannan yarinya anyi yar kan babbar bura uba..to karfe nawa takeso muje gun bikin, oho! inba isknciba da kutmar uba, ace tin dazu in shirya Amma ita har ynzu bata gama shiriba, uwar lab'o lab'o, sekace kwai ya fashe mata a ciki..Allah ma yasa ba bacci takeyiba .." Annah ke fadar hkn dai-dai ta iso kofar dakin KYAUTAR ALLAH, kwancema ta sameta da wayarta a hannunta tanata dealing number din daddynta Amma baya picking.. "Wa'izubillahi!" Annah tace hadi da karasowa cikin dakin ta tsayawa kyautar Allah a kai wadda ta ajiye wayar a gefe ta zuba mata ido.. "Meya faru kk cewa wa'izubillahi!" KYAUTAR ALLAH ta tambayeta

"Kan babbar bura ubakine ya faru..shegiya, dankinga kin fara nono tuzu tuzu, shine kk kawowa mutane raini..dan bura ubaki tin dazu in shirya ina jiranki kizo muje gidan bikin Amma kinki, ashema sam baki shiryaba,knsan ynzu karfe nawane..karfe Ukune da rabi ,.."

KYAUTAR ALLAH ta zubawa Annah ido wadda ke sanyeda doguwar rigar lace, dinkin bubu, rigarma abai-bai tasata, dankwalin kuwa tayi daurin ture kaga tsiya, duk furfurarta Ana gani ta baya.."Wani gidan bikin? Aka gaya miki yau ke zakije, kefa se ranar biki, yaufa rnr kauye day ne.."

"Aiko dani za aje dan ubanki, yau kauye din, aiko rnr muce, zaki tashi mu tafi ko kuwa sena tafi na barki.."

Dafe kai kyautar Allah tayi tace "Annah yara nefa ke zuwa gun.."

"Kince kn bura ubaki keda Yaran,ni nawa nake, zaki tashi ki shirya mu tafi ko kuwa senaci bantan ubanki,shegiya yar buzaye kawai...."

"Ynzu mafa ba a faraba se 6:pm ake farawaba..Hba Annah, kije ki kwanta kiyi bacci ba inda zanje dake.."

"Durun uwarki keda baccin! Ba inda zakije dani din ubanki ni qaramar yarinyace daxakice ba inda zakije dani,ko kuwa kama min hannu zakiyi..aiko in nima bazanjeba to kema bazakijeba, kenan..inkin shirya kya sameni a falo, karki kara bari in hawo wannan matsiyacin benan naki, inna kara hayowa wlhy jikinki ze gaya miki, danse nayi miki duban kawo wuqa, karkiga kin fara nono, ni kadan daga Aikina in daukeki in bugaki da kasa.."

Girgiza kai KYAUTAR ALLAH tayi ta fara goge uban miyaun da Annah ta tofeta dashi a fuska, duk gurin matsifarta..

Hartakai bakin kofa ta juyo tace "Kifa tashi ki shirya, muje kauye din din, in kika bari na kara hawowa saman nan sena bata miki rai wlhy.."ta karasa ficewa daga dakin tana dogara sandarta,tna mita...

"Ai dole in tashi, kada ki dawo ki cinyeni da fada.." KYAUTAR ALLAH ta fadi hkn hadi da miqewa ta dauko kayan gyaran jikinta ta fara shafawa, seda tayi 10mnt kna ta shiga bathroom din danyin wanka.

Tin 11:30 am daya kwanta baccin be tashiba se around 4:pm, cikin hnzari ya miqe sbda ganin time ya tafi, direct ya nufa bathroom, yy wanka ya fito daureda Alwala, jallabiya ya zura kna ya jero sallar azahar da la"asar tareda neman gafarar Allah na hada sallarh da yy... Shiryawa yy cikin mnyan kaya wani jahilin yadi yasa me kyau,Amma beda nauyi se uban tsada, kalar yadin kalar farine sol, rigar dai-dai guiwa, me hannun links wandon ya zauna dai-dai da kafafuwansa. Sumar kansa ya gyara ya shafa hair cream, nan da nan ta hau walkiya, dmn gata baki kirin.. Ya dora sabon watch dinsa me maballin botir, watch din yayiwa tsintsiyar hannunsa kyau, kou ince shiya haska watch din. yasa takaln cober shoe diddigensa a waje. A gaskia innace beyi kyauba na tsula karya..wato yayi ainihin jahilin kyau. Feshe jikinsa yy da perfume dinsa me shegen dadih. Fitowa Yayi falon hannunsa riqeda wayoyinsa guda shida mnya hudu qanana biyu da jakar system dinsa. Se zuba kamshi yakeyi,.. direct dining area ya nufa saboda yadda yakejin cikinsa na kiran curona.. Already dmn an hada masa abinci iri iri..zaunawa yy hadi da jingina bynsa da byn kujerar..

Wayarsa ya dauka ya kira Joshua ba jimawa yazo a guje yayi serving dinsa, da shinkafa da miyar kaza, spoon hudu yy ya koshi ya kora da ruwan faro kna ya goge bakinsa da tissue,..miqewa yy ya nufa inda Aka tanada dan wanke hannu, brush yayi kna ya wanke hannunsa da abinda aka tanada dan wanke hannu. Wayoyinsa ya kwashe da bag din system dinsa dya ajiye a kn dining din. Kna ya fice a falon, zuciarshi na kn babynsa.

Already an shirya car din daze fita da ita, katotuwar jeep ce kirarta kirace me kyau,ba duk kowa keda irintaba a nigeria. Kalarta kalar milk color ce,...

"Sannu da fitowa sir ya gajiyar hnya!.. Sannu da fitowa sir ya gajiyar hnya!!...sannu da fitowa sir ya gajiyar hnya!...sannu da fitowa sir ya gajiyar hnya...barka da fitowa sir ya gajiyar hnya.. Barka da dawowa yallabai!" Shine Abinda ke fitowa daga bakuna daban daban na duk ma'aikatan dake aiki a gidan.

"Alhmdllh.." Shine amsar da yke basu babu yabo babu fallasa, a tattare dashi. Bude masa handle din motar akayi mazaunin baya ya shiga ya zauna sanyin ac na ratsashi, hadi da kamshin perfumes din mota..

Dreva ya shiga mazauninsa, guard dinsa yusuf ya shiga mazaunin me zaman bnza.. Tayarda car dreva yy nan da nan aka wangale get din gidan kusan gets shida, suka fice daga gidan...

"Sir ina zamuje?" Shine tambayar da Yusuf yy masa.

"Katsina..." Ya bashi Amsa.

"Okay sir.." Cewar yusuf..dreva ya fara qoqarin daukar hnyar katsina..

Jim Raslan yy kna yace "sorry Muje gidan Ummih..."

"Okay sir" cewar dreva hashim,shima sojane.

Wayarsa ya jawo ya danna nan yaga calls har hudu a sama, jawo saman yy yaga bbynsace,murmushi yy hadi da dealing number dinta.. Dai-dai ta gama shiryawa cikin kyn kauye day kenan Tana shafa lipstick don bata kwalliya sam Amma fuskarta tayi kyau fayau da ita, dinkin doguwar rigace a jikinta na Atamfar back up fish shine Ankon kauye day din. Wayarta dake kn mirro tayi ringin da hnzari ta jawo wayar ta daga ta kara a kunnenta tana murmushi.."daddy ina wuni?"

Muryarta ta daki dodon kunnensa ya lumshe ido yace "Lafia lau bby me..Am sorry kn kirani ina baccine.."

"Okay...shine duk yau bka kiraniba in the morning ko daddy.." Tafa cikin shagwaba.

"Am sorry sweetheart, ina baccine tin tini knsan in ina ido biyu bn iya wuni bnyi waya dakeba..yakike?"

"Lafia lau sugar dad dina..jia nyi mafarkin kadawo nigeria?"

Yar daria yy Yace "mafarki ba gaskiaba.."

"Allah yasa ya zama gaskia..daddy wai bkada shirin dawowane pls.."

"Inadashi mna kodan inzo in gnki tinda kn gnani yin video call dake ingnki inji ddh..kinsani a kewarki,da open teeth dinnan naki,me kyau.."

Murmushi tayi tace "nima nyi kewarka da dimples dinka.."

"Kin rama ko.." Duk suka kwasheda daria..

"Bakije isilamiyyaba why?" Ya tambayeta

"Ba Annah ta haniba,da school ma.."

" why?"

"Waini mtr Aurece,wai kuma kaine mijina, da gaskene.." Ta tambayeshi murya cikeda yarinta

Yar daria yy yace "Eh mna ke mtr daddynkice.."

Tayi murmushi tace "Ai daddy bya Auren yarsa..Annah ma tace ai duk rnr dakazo seka sakeni wai,in samu wani mijin inyi Aure.."

Murmushi yy yace "Aiko bazatama ganniba.." Ya fada a rnshi a fili, yace "Ke kinaso in sakeki?"

Yatsanta tasa a baki ta fara tsotso tace " nimade bnsaniba.."

Daria yy yace "Zaki sani Ai.."

"Tom yaushe.."ta tambayeshi

"Gobe.." Ya bata Amsa..

Daria tayi sbda ta mayrda mgnr wasa. "Daddy zamuje biki, kuma kauye day."

"Bikin wa akeyi?" Ya tambayeta

"Bikin Farhan mna,yayan qawata fatima.."

"Waye farhan.." Ya tambayeta ynason tunano inda yasan me sunan ko ince mkamancin me sunan.

"Farhan dinnan wanda ya taba zuwa gidanmu, wanda da Annah tace, in Aureshi, shine zeyi Aure,..."

Nan da nan Annurin fuskarshi ya gushi rnshi ya baci, "Waya baki izinin kije bikin?" Ya tambaya ranshi A matukar baci.

"Annah ce tace muje Ai, mommynsu ta gayyaceta..kuma fatima ta kawomin intervention card.." Ta bashi Amsa ba taredata lura da bacin ran nasaba.

"Nace karkije kou!" Ya fadi hkn cikin tsawa, seda dodon kunnenta ya kusan fashewa tace "Tom..." Cikin sanyi

"Bye zamuyi waya Anjima.." Ya fadi hkn dai-dai akayi packing car dinsa a harabar gidan ummihnsa.

"Daddy Are angry kou?" Ta tambayesa cikin shagwaba.

"Nop..." Ya fadi hkn ynajin ranshi fayau sbda yadda ta tambayeshi nan da nan yaji ya sauka..

"Tom..i love you.." Ta fadi hkn cikin dadin muryarta.

"Love you 2 bby me.." Sukayi sallama kowa ya ajiye waya.. Mayafinta maroon ta dauka tasaka da bag dinta maroon itama tasa shoe dinta shima maroon, nan da nan ta haska tayi kyau sosai dukda ba kwallia tayiba Kyaun natural ne. Ita sam tma mnta yace kada taje. A hnkli take saukowa daga upstairs din. Ta krso falon hannunta riqeda hand bag dinta da wayarta.. dinkin doguwar rigar me lafewa a jikine gashi ya matseta tsam ko ina ana gani A jikinta, wato me nuna shape ne.., tayi kyau iya kyau harta gajida kyau. Krsowa tayi falon taga Annah zaune kn kushin 3sttr tanata bacci ta hangame baki.. "Gani nan na fito! Aise ki tashi mu tafi!.." Tadan fada da dan karfi

kyar Annah ta bude idonta hadi da kulle bakinta tahau gyara dankwalin knta, da tini ya subuce sbda bacci. Ta zubawa kyautar Allah ido kana ta washe baki tace "masha Allahu, gaskia knyi kyau KYAUTAR, tubar kallah.."

"Ngde Annah Amma kyn sun matseni kou? Kunyar fita nkeji dasu.." Tyi mgnr tana kallon knta

Annah tace "Ah'ah ki barsu hk Ai sunyi dai-dai kenan, wannan ai sune dai-daike wasuma Ai wanda yafi hk suke sawa, wannan kam ai yy dai-dai yadda ya dace..

Murmushi KYAUTAR ALLAH tayi tace "Tom Annah ta..tashi muje.." Dai-dai wayrta tayi ringing dubawa tayi taga number din Fatimace dagawa tayi tace "Kn fara kirannawa kou.."

Daga bngaren fatima tace "Ai dole na qosane in gnki knsan kece babbar qawata.."

Murmushi KYAUTAR ALLAH tayi tace "Gamunan zuwa nida Annah.."

Fatima tace "Annah kuma.."

Annah dakejin komi tayi carab tace "E Annah din, dani za azo ko akwai wata matsalarne,..."

Fatima tace "Ah'ah wlhy bkm Annah, Aini nji dadihma dazakizo zan gyawa mommy.."

"Ai ko bakiji dadihba se hkri hknan zanzo.." Cewar Annah.

Fatima ta jinjina kai kna tace "ALLAH ya kawoku lafia..." Kna sukayi sallamah.

Miqewa Annah tayi da jakarta me kamadata wanzamai ta rataya, ta gyara mayafinta katoto me kyau dashi, amma tasashi Abaibai. Ta dauko sandarta ta dogara tace "Muje.."

Kare mata kallo tyi kyautar Allah tyi tace "A hk.''

"A hkn mna hina kyau kikayi, ynzude ko gasar kyau za ayi na tabbatr sena miki warwas.." 🤣

KYAUTAR ALLAH tace "Gaskia kam hkne ga Alama nan na gani..knsa kaya Abaibai riga Abaibai, gyale Abaibai, duba dankwalima abaibai, knyi wani dauri duk Ana ganin furfurarki, ga jaka sekace wata wanzamiya.."

Karewa knta kallo ta shigayi kna tace "Bura ubaki keda wanzamiyar, shegiya da ido kmr agolar nufawa..tin shekara ta dubu dari bakwai dasha bakwai, nke kwallia kafinma asan za a haifi uwarki dan ubanki.."

KYAUTAR ALLAH tace "tom..ynzude muje in gyara miki rigar gaskia.."

"Naki baxan jeba in zaki wuce muje ki wuce muje, insa kaya dai-dai kicemin abai bai dayake ke makauniace.."

"Sede in kece makaubiar..Dubafa ki gni,wlhy Abaibai kika saka hba Annah.."

"Ubankine makahon! Kuma Karya kkeyi dan ubanki dai-dai nasa kayana in zaki wuce mu tafi ki wuce mu tafi,.."

"Gaskia Annah ki tsaya in gyara miki kyn jikinki pls.."

"Wlhy tlhy na rantse da kwaran kwatsi dubu bazan tsayaba , in zaki wuce muje ki wuce muje, kawai tinda ba akan uban wani nakeba.. Babu siriki babu sirika ballan tana qanin miji dan banza!." Cewar Annah. Hk nan ta barta suka fito compound din gidan,ma aikatan nata kallonta suna daria qasa qasa.. Dan liti dreva na ganinsu ya rugo a guje yace "Sannu da zuwa ajiya.." Cikin mgnrsa ta bebaye.

"Sannu da zuwan ubarka, mun fito zamu fita Anguwa kina mna sannu da zuwa, gidan uwar ubanka mukaje Da har muka dawo...." Cewar Annah

Ya matso daf da Annah sbda bejima me take cewaba "me cihcahceehh?" (Me kikace)

"Durun uwaka nace, shege dan gidan abun kwari!.. " ta kraa danna masa zagi.

Sam bejiba ya kara matsowa daf da ita yace "Uwatarrhh!..."shine kawai Abinda yy qoqarin ji

Annah ta mangaresa, ya hantsila gefe Abinka da dan siririn mutum. "Dallahcan beban bnza kawai..wuce muje ka kaimu gidan biki.."

Nanma bejiba, seda ya qara matsowa KYAUTAR ALLAH ta maimaita masa, kna yace "Tooouhh ajiyah.." Nan ya fito da car suka shiga, zuwa gidansu fatima dmn yasan gidan sbda shike kai KYAUTAR ALLAH.


Fitowa yy daga car din direct ya nufa side din mommy..

Anty sadia da ihsan ne zaune suna kallon zee world, jefi jefi sunawa juna habaici kmr kishiyoyi, ko kishin sauri, tsabar rashin haduwar jini ne.. ya shigo bakinshi daukeda Sallahma ... Kmr daga sama sukaji sallamarsa a firgice ihsan ta juyo dan tabbtrwa da idonta Abinda kunnenta yaji. Tabbas shi dinne idonta ke gni.. Hk itama sadia ta Juyo t kalleshi, nan ta saki murmushi "oyo yo mutanen USA.. Gaskia USA dinnan ta Amsheka ka kara fresh matsalar dyace ka rame..kuma nasan dalilin ramar.." Ta fasheda daria.. Krsowa yy ya zauna kn kujerar kusa da Anty sadia yace "Kai small mom ynzu harkin karemin kallo.."

"Ba doleba sweetheart,ya hnya, saukar yaushe.." Cewar anty sadia

"Alhmdllh, wlhy yauda Asubah.." Ya bata amsa yna kallon ihsan itama shi take kallo, Amma sam bakinta be iya gaisuwarsaba, haushinsane ya rufeta..ta wani fannin taji ddh sbda tasan yau za ayita ta qare, don tnada tabbacin seyaje katsina gun knwar uwarsa. Kallo dya yy mata ya gano ramar da tayi da duhun da tayi, hk kawai se yji ta basa tausai sbda yasan kishine ke cinta.

"Ina ummihnar?" Ya dawo da dubansa kn Anty sadia kna ya jefa mata tambayar.

"Tna side din daddy.."

"Okay daddy na nan ne?"

"Eh.."

Miqewa yy still idonshi na kn Ihsan yace "Ina small khair fa?"

"Tana gun Innah baccima takeyi.."

"Baccin yamma.."

"Eh tna mura ne..''

"Okay..allah ya bata lafia..''

'Bataredata Amsaba tace "ina zaka.."

"Side din daddy.."

"Okay..hope kaci Abinci?'' Ta tambayesa cikeda kulawa.

"Yeah naci small mom, tnks for the care.."

Smiling tayi kna tace "kad'e kawomin tsaraba ko?"

"Insha Allahu, Anty in bn kawo miki tsaraba ba aisena koma USA.."

Daria sukayi ita dashi a tare kna tace "ai ka fadi dai-dai,mgnrka bb gyara.." Dariar ya danyi still idonshi na kn ihsan, itakam dauke knta tayi daga knshi.. Direct ya nufa hnyar dazata sadashi da side din daddy.

Zaune suke kn kujerar 3sttr shida Ummih, kwanin ban shawa'awa, gaban daddy karamin table ne na glass an cikashi da kyn fruits iri daban daban. Dai-dai ya cako kankana da fake yakai baki ummih na masa fira Raslan ya shigo bakinsa daukeda Sallahma, knshi na qasa, ko kadan bejin alamar faduwar gaba a tattare dashi.

A tare duk suka kai dubansu garesa suba zuba masa ido, kallo daya biyu suka gano kyaun daya kara, a lokaci daya suka gano ramar da yayi..Musammanma UMMIH. "saukar yaushe kakana.." Daddy ya fada cikin so da tsantsar kaunar dannasa.

Karasowa yy ya zauna kasan carpet yace ''yau da asubah, muka iso daddy.. Ina kwana?"

"Lafia lau Kakana, yaya hnya?"

"Alhmdllh, daddyna.."

"Masha Allahu ande samu Abinda ake nema kou?" Daddy ya tambayesa. Haushi ya rufe UMMIH sbda taga sam bema nuna masa kuskurensaba na tafiyar da yy ba tareda izininsuba.

"Alhmdllh daddy.. UMMIH ina wuni.." Ya dawo da duvansa kn UMMIH wadda ke cikeda haushinsa.

"Ka gama shawagin ka dawo.." Shine abinda ta fada ba tare data amsa gaisuwar tasaba.

Alhaji umar yayi carab yace "shawagi kuma shi jirgine? Aikifa yajeyi.."

" Wani irin aikine zeje ba tareda izininmuba.."

"Shifa namijine, kuma magidanci.."

"Hba alhaki ynzu a memakon a nuna masa mistake dinsa shine zakace hk...shikenan.." Miqewa tayi tabar falon ta shige bedroom din daddy. Daddy bebi ta kntaba suka cigabada hirarsu shida dansa..dmn Raslan yasan beda case da daddy UMMIH ce cases dinsa.."daddy inaso naje katsina.."

"Katsina a yaushe kenan?"

"Yau daddy..." Duba time yy yaga 5:30pm yace "ynzufa 5:30pm ne, a kunyi gudu ku isa 9:pm beyi dareba?"

Sosa keya yy harga Allah baze iya wuce yauba be gntaba, sede kuma in yy dare, dole ze hkra da sassafe ya kirata su hadu.."beyi dareba daddy.."cewar Raslan

"To shikenan bb dmwa..Ammafa kada ka sake kaje gidan Annah, domin ta matsa kn ka saki Rukayyah, ynzu hk jiran dawowarka takeyi, wallahi idonka idon Annah, to tabbas seka saki Rukayyah..ko baka sontane?"

Sosa keya raslan yayi knshi kasa yna smiling Allah yasani tin tna jaririya ykesonta kawai ya boyene..

Murmushi daddy yy jin yy shiru yace.. "aiko kanada case kaida Annah, wannan case dinma yafi karfinmu, mu namu Adduarh, .."

"Aiko zata mutu, tinda Aka dora Bb wanda ya isa ya sani sakinta.." Ya fada a rnshi.

"Kaga matarka kou?",daddy ya tambaya Raslan

"Eh na gnta daddy..''

"Madallah, kayi qoqarin adalci pls, ka tafi kusan 1month katunafa Akwai haqqinta a knka, kada ka zalintar musu yarinya pls kajinko?.."

"Toh daddy.."

"Ka tabbtr ka sauke haqqinta kafin ka tafi garin katsinar.."

"Insha Allahu.."

"Tashi ka tafi kada kyi dare, Allah ya tsare gabanka da bynka.."

"Ameen sweet daddy.." Ya amsa tareda miqewa yace "Bari inje gun UMMIH rigima.."

Yar daria daddy yy yace "matan kenan.."

Direct ya nufa bedroom din Daddy zaune ya sameta gefen bed ta jingina bynta da byn gadon, bb Abinda take tunani Se yadda zata Bullowa mgnr auren Raslan, din.. Krsowa yy ya zauna a kasan kafafuwanta kn carpet ya dora knshi a kn cinyarta..

Ido ta zuba masa, tin shogowarsa,.

"UMMIH kina fushi kou..Am sorry pls, in kna fushi dani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login