Showing 6001 words to 9000 words out of 274760 words

Chapter 3 - KYAUTAR ALLAH

10 Sep 2025

14598

din ya idar kenan yna jero addu'ur'insa na yau da kullum KYAUTAR ALLAH ta danno kai cikin dakin.. Sanye takeda doguwar rigar abaya kalar brown light, me matukar kyau anyi mata ado da wasu irin duwatsu masu mugun kyau, se walkiya sukeyi.. Abayar ta amshi jikinta, se kalarta ta kara kyau da sheki, yayindata yane knta da dankwalin abayar. Maida murfin Kofar dakin tayi ta rufe, a hnkli ta karaso ta zauna gefen gadonshi, ta zuba masa ido, yyindayaketa jero addu'ur'insa ga mahaliccinmu. kallo takeyi masa cikeda so da kaunarh.

Byn ya kammala addu'ur'insa ya shafa ya miqe ya qaraso inda take fuskarshi daukeda murmushi. "Abbanarh kyimin adduarh?" KYAUTAR ALLAH ta tambayeshi idonta na knshi.

Karasowa yy ya zauna kusa da ita, ta kwanto jikinsa. "Ai kullum sallahta biyar se nyi kiki adduarh my fineness.."

Murmushi tayi tace, "Tnks alot sweet dad..da gaske daddy zakayi 1week a nan?"

Murmushi yy yana shafar knta yace, ''Knasone inyi 1week?

"Ai kasan inason kasancewa, dakai Akoda yaushe my dad.."

Murmushi yy kalamanta na masa dadih a zuciyarsa..."Zanyi 1week amma da sharadi kn yarda?"

Sauri tayi tace "Yeah na yarda amma ka gyamin sharadin inji..."

"Se knyimin promise innayi 1 week zaki bini muje abuja.."

Zaro ido tyo hadi da fadin. "Kai kai kai..ai matsalar Annah ce bazata yardaba..kumani ina tsoron anty ihsan.." Domin Raslan ya taba zuwa da ita, Ihsan ta rinka zaginta, raslan dayazo ya gani yayi mata ta tas. Abun ya farune tin kafin takai hk shine abun ya tsaya mata a rai har ynzu, .

Raslan yace "Kai Bbyna bakya mantuwa.."

KYAUTAR ALLAH tace, "Daddy bazan iya mantawaba,..wlhy daddy na tsani Anty ihsan.."

Raslan yace "Banace kidena cewa kn tsani mutumba.."

"Am sorry dad bazan karaba..."ta fada cikeda nadama.

"Yau baza kije isilamiyya bane.."

Zumbur ta miqe tana fadin "Au na mnta ma yau akwai isilamiyyah.."

"Jeki shirya inzo in kaikai.."

Cikeda murna ta matsa ta manna masa kiss a kumatu, tace "Yauwa daddynarh.." Ta juya ta fice a guje tabar dakin.

Murmushi yy yabi bynta da kallo cikedaso da kaunarh. Kyn jikinshi ya cire yasa wasu kananan kya masu jahilin kyau, nan ya kara hadewa yayi kyau dashi kmr balarabe.

Fitowa yy falon ynata zuba kamshi, ga walkiya ynayi kmr wani dawisu, hannunshi rikeda car key, se dyn hannun nashi rikeda wayarsa kirar I phone 13Pro,se karama kirar nokia baka, wadannan sune kanana a cikin wayoyin nasa.

A zaune ya samu KYAUTAR ALLAH tna ganin fitowarshi ta mike zumbur .. sanye takeda kayan isilamiyya Kalar ash colour, hijjb ne dogo har kasa se wandonma ash, rigar jikinta farace, se dankwalin dake kanta farine shima. Uniform din ya amsa jikinta ainun, se fuskarta ta fito shar da ita, hannunta rikeda jakar isilamiyyar itama ash colour,. Annah tayi musu a dawo lafia, suka fito suka shiga motar Raslan yaja motar sukabar gidan. Direct Tamfatsetsiyar isilamiyyar suka nufa, me suna *Markazil sikafil islam safana* makarantar benece me matukar kyau, irinna yayan masu fada aji domin larabci akeyi zallah a makarantar, shiyasa bakin KYAUTAR ALLAH inta juya ta fara larabci kai kace bakar balarabiyace. Raslan na sauketa ta shige mkrntar shi kuma ya juya ya shiga gari, da niyar in an tashi ze dawo ya dauketa.

KYAUTAR ALLAH na shiga hrbr mkrntar taci karo da qawarta fatima, itace qawarta duk duniyarnan fatima farace sol tanada matsakaicin kyau, fatima yar minister din katsinace, a kalla zatakai 14yrs ta girma KYAUTAR ALLAH da 2yrs. Jinin KYAUTAR ALLAH da fatima ya hadu sosai, tin rauda, suka hadu har ynzu, suna ziyarar gidajen junayensu, har zumuncin nasu yakai zuwa gun iyayensu, Fatima tasan raslan, yana mugun burgeta,harma takan fadawa KYAUTAR ALLAH, sede KYAUTAR ALLAH tyi murmushi kawai, don ita batamasan meye soyayyaba.

Fatima na ganinta ta karaso cikeda murna. "Qawata yau knyi late.."

KYAUTAR ALLAH murmushi tayi tace, "Abbanah ne yazo, ni bnmaso zuwaba, dande ya matsane..."

Wani irin farin cikine ya lullube zuciyar fatima, tace, "Kice Wallahi yazo?.."

KYAUTAR ALLAH tace, "wallahi, shinema ya kawoni, yace ze dawo ya daukeni zaki ganshima ai.."

Farin cikine ya qara lullube zuciyarta yyndata kasa boyewa tace, "Tom..mu qarasa aji, malamin fiqihu, yazo, ynata tambayarki.."

KYAUTAR ALLAH ta yamutsa fuska, tace, "Yana nemana in masa me?"

Zunguri fatima takai mata tace, "Ai dole ya nemeki, tinda knsande duk ajinmu babu wanda ya kaiki kwakwalwa, hknne yasa duk malamin daya shigo seya tambayeki.."

Turo baki KYAUTAR ALLAH tayi, tace, "Uhmmm, ke daga ina kika fito.."

.fatima tace "Uhm na fitone ina jiranki nga bngnkiba gashi nabar wayata a gida.."

KYAUTAR ALLAH ta watsa mata harara ta sigar wasa, tace, "Uhm kede qawa bakison zaman aji se anzo exams kiyita raba ido.."

Fatima tace, "Najidin..." Daga hk suka dungumo zuwa ajinnasu.


6:pm yayi packing car dinshi a bakin get din mkrntar, yayinda dalibai keta fitowa ta get din suna shiga motoci don zuwa gida.

Raslan da yy packing dai dai wayarshi tayi ringing dubawa yy yga numbar din ihsan ne, seda tayi ringin ta katse kira na Uku kna ya daga ba tare da yayi mgnaba, daga dayan bangaren Ihsan tace. "Hello my husban darling..kna ina ne.."

Seda ta kara maimaita tambayar kna Raslan yace, "Kmrya.."cikeda yatsina.

Inda sabo ihsan ta saba da miskilamcinsa, don hk sam halinsa be damunta. Tace "Ynzu na duba side dinka, bangankaba, kuma ai nga yau saturday ne baka fita,.."

Tsuki yaja ya katse wayar, yna gani ta kara kira yaki dagawa, karshema ya kashe wayar baki daya. A fili yace "Stupid girl, bata iya komiba ma miji se aukin shirme.." Yaja guntun tsuki, bkrmin haushi take bashiba.

Dai dai suka karaso bakin motar itada fatima hannunsu cikin na juna, direct KYAUTAR ALLAH takai hannu ta bude murfin motar, juyowa yy da idonshi knta, aidukse yji bacin rnshi ya gushe. "fineness, meyasa baku tashida wuriba, har 6:15 pm.."

KYAUTAR ALLAH tace, "Malamin sirah ne ya riqemu.."

"Okay.." Yace tareda maida idonshi kan fatima wadda tin tini shi take kallo kmr zata lasheshi. Kallo dya yy mata ya dauke idonshi, wai danma tnason KYAUTAR ALLAH ne yasa har tasamu matsayin kallo daga garesa.

KYAUTAR ALLAH tace, "Daddy kaga fatima.."

Daga kai kawai raslan yayi, cikin isada kasaita. Fatima tayi saurin cewa, "Ina wuni .."

"Lafia.." Ya amsa a takaice dmn hk yake amsa gaisuwa, wai a hknma tasamu matsayine.

Fatima se tji wani sanyi ya mamaye dukkannin rayuwarta. Don wasu lokutanma baya amsa gaisuwar tata."Qawah bye maybe zanzo anjima, kou gobe...knga ynzu ga dreva na ya karaso.." Tyi mgnr tana kallon gefen inda dreva dinta yayi packing car dinta.

Farin ciki ya ziyarci kyautar Allah jin cewar qawar tata zatazo..KYAUTAR ALLAH tace, cikeda murna. "kice wallahi, zakizo qawa.."

"Zanzo insha ALLAH..." Cewar fatima.

Farin ciki ya rufe KYAUTAR ALLAH yayin dataketa daria har wushiryarta ke bayyana, ido Raslan ya zuba mata shima se yji farin ciki ya rufeshi. Fatima tayi musu sallahma tajuya ta nufa motarta inda dreva ke jiranta, tana shiga drevan yaja sukabar gun.

Shima gogan tada car din yy yabar harabar gurin. "Daddy kasan meye.." KYAUTAR ALLAH tayi tambayar byn sun hau kan kwalta.

Daga mata kai Raslan yayi, hnklinsa na kn driving din da yakeyi.

"Daddy knajikou..."

Ya kara daga mata kai..

"Fatimafa tace in gya mata kna burgeta," ta fada da faraarta

Shiru yy kmr bejitaba,..sanin hali, don inda sabo ta saba da miskilancinsa.

"Daddy bakajibane.."

Shiru ya karayi mata,,, tou dmn gidan miskilancince itama, se tayi shiru bata kara tankashiba.

Direct gida suka nufa, ynayin packing ta bude murfin motar ta fita, shima bude murfin yy ya fito, nan ma aikata suka fara miko masa gaisuwa da masa barka da zuwa, dukkannin ma'aikatan dake aiki da Raslan, suna mugun jin dadin aiki dashi saboda ynada kyautatawa sam abin hannunsa be rufe masa idoba, a kullum hannunshi a bude yake.

Direct ya danno kai cikin falon be ganta a falonba, se Annah dake zaune da carbi a hannunta tna lazimi, lami me mata tausa, tana Zaune bisa carpet Kafar annah na kn cinyarta, tna mammatsa mata kafafuwannata. "Sannunku da dawowa.." Annah ta fada idonta a kn Raslan.

Zaunawa yy a kn kujerar dake kusa da ita tsaf yajita amma yy mursisi kmr bejiba. Annah ma tasan hali don hk batafi ta knsaba.

Jingina bynshi yy da kujerar idonshi na kn kafar Annah dayaga alamar kmr tadan tasa. "Annah, kinashan magungunanki kuwa..?"

Annah tace, "inasha wallahi, meka gani.."

"Kafanki kmr ya dan tasa.." Dayake tnada ciwon kafa,da hawan jini shine ciwonta.

Annah ta tabe baki tnabin kafar tata da kallo tace "Uhm kaide bari tsufane kawai, lokacin ya tafi..ai Alhamdulillahi munmayi tsawon rai.."

Raslan yayi murmushi, Hadi da miqewa yabar falon ya nufa dakinshi, wanka ya qarayi, ya canza wasu kyn na hutu. Ya fito falon daureda alwala time din anata kiraye kirayen sallah magrib. Bega kowa a falonba, Hkn ya bashi tabbacin Annah taje sallah ne. Ficewa yy ya nufa masallacin dake kusa da gidansu, nan yayi sallarh magrib seda yayi sallarh isha'i kna ya dawo gidan, A falon yga bega kowaba.
Direct saman upstairs din ya nufa don a nanne dakin KYAUTAR ALLAH yake, gabaki dya saman mallakintane, tin daga matattakalar abin kallone, har ya zuwa falon dake saman ya hadu iya haduwa, komi dake falon Maroon ne and white, falo ukune a saman kou wanne da yanayin tsarinsa kuma duk mallakin KYAUTAR ALLAH ne. duk inda ka wulga ido, se kaga teddys saboda KYAUTAR ALLAH nason teddy, duk bangon falon hotunan KYAUTAR ALLAH ne itada Raslan, wani kuma raslan dinne shi kadai. Wani picture ne yafi daukar idon Raslan inda KYAUTAR ALLAH take ita kadai lokacin tna 1yrs, murmushi yayi yayin daya tuna wanibabu a ranshi.. Direct bedroom dinta ya nufa, wow! Hasbunallahu wani'imal wakeel!! Bedroom din ya hadu, iya haduwa, zan iya rantsewa da Allah ban taba ganin daki me kyauba kmr nata, Komi yaji an narka dukiya, domin gadon dake dakin dan gadone na danyar azirfa, madaidaicine gadon, na kwanan kyautar allah ita kadai, komi na dakin adon maroon ne and ash colour, roy ne Amma komi na azirfane. Fans dakin ya hadu. Gadonta gaf cike yakeda teddys, dakinma duk inda ka wurga ido teddy ne takou ina se hotunansu itada Raslan, A dakin hotunan Raslan yafi yawa, kmr yadda a dakin raslan pictures din kyautar Allah yafi yawa.

Kwance ya sameta a kn gadonta ta rungume teddy dinta daya kawo mata yau, Sanye takeda riga da wando irinna yan hutu, kalar milk,sun amsheta sosai, kanta babu dankwali yayinda sumar knta irinna larabawa ya kwanto Bisa bayanta baki wuluk dashi. . yatsunta guda biyu na kusa da qarami dana tsakiya,sune yatsun datake tsotso,suna bakinta tna tsotso. Ido ya zuba mata, yayindayake kallonta cikeda burgewa, Yanaso yaga tana tsotson hannu hkn na burgeshi, kou abinci bataci sosai, saboda tsotson yatsun datakeyi, inma za a barta bazataci abincinba sede tayita tsotson yatsu. Tsaf taji shigowarsa juyuwa tayi ta zuba masa ido da yatsun a bakinta.

"My fineness.." Ya fada cikedaso da kaunarh.

"Naam.." Ta amsa still yatsun na bakinta tna tsotso,don intasa yatsun a baki, bata cirewa kouda zatayi mgnane. Tna tsotson yatsun tna wani lumtshe ido.

Smiling yy yace, "Meyasa kika zauna a daki ke kadai.."

"Bakomi.." Ta fada a takaice.

Tashi muje inyi feeding dinki dinner..

"Na koshi.."

Zaunawa yy a gefen bed dinnata, rarrafowa tayi ta kwanta a jikinsa, hannunshi ya dora a knta,yna shafar sumar knta, "gobe zamuje saloon..."

Girgiza kai tyi ba tare da tayi mgnaba..

Murmushi yy danyasan batason kitso sam. A hnkli yake janta da hira, na bn dariya tna kyakyatawa,, kna daga bisani ya gojota suka dawo kasan nan suka samu Annah a kan dining tna dinner. Raslan yace "kaga tsohuwarnan zata cinye abincin ba taredata nememuba.."

Annah kmr tana jira tace, "Yooh ina zan tsaya jiranku, aise yunwa ta nemi nakasani.."

KYAUTAR ALLAH ta zubawa Annah ido, yayinda hansa'u ke serving dinta, da tuwan shinkafa miyar kubewa danya, Abincin da Raslan yafi kauna kenam, shiya koyawa KYAUTAR ALLAH son abincin, itama tanason tuwon miyar kubewa danya. Krsawa dining din sukayi da knshi yy serving dinsu kuma yy feeding bbynnashi, seda ya tabbatar ta koshi kna ya faraci shima. Dmn dukkanninsu ba kwanayen cin abinci bane,loma biyu uku sun koshi. Farfesun naman kaza sukaci kna suka bar dining din suka koma tsakiyar farlo, Suna kallon cartoon don inhar KYAUTAR ALLAH na falon tou basuda abun kallo se cartoon.

Annah kam tini tyi musu seda safe,tanufa bedroom dinta ta kwanta, don ita akwaita da saurin bacci.

Suna nan suna kallo a kn carfet yynda kyautar Allah ke kn jikin Raslan, har Bacci Ya kwashesu a falon ba taredasun saniba,se wajajen 2:am Raslan ya farka, yaga KYAUTAR ALLAH kwance bisa cikinsa tnata bacci yynda yatsunta ke cikin bakinta. Ido ya zuba mata sam bya gajiya da kallon kyakyawar fuskarta me cikeda annuri a garesa, in yna kallonta, babu Abinda yake tunawa se mahaifiyarta, da kuma Amanar data basa na KYAUTAR ALLAH.

Seda ya dauki 20mnt yna kallonta kna daga bisani, ya miqe ya dauketa ya nufa sama da ita bedroom dinta, a kn gadonta ya ajiyeta, yayi mata adduarh ya lullubeta ya juya ze tafi ta riqo hannunsa, cikin magagin bacci take. "Daddy,,kada ka tafi ka barni.." Ta fada murya cikin bacci. Murmushi yy ya juya da niyar tafiya ta kara riqo hannunsa,,, matsawa yayi daf da ita yayi kissn dinta a kuncinta,, murmushi tayi dukda a cikin bacci take. A hnkli ta furta masa a "Love you.." Cikin wani irin voice me sumar da zuciyar me saurare.

Ajiyar zuciya ya sauke, ya wani lumshe ido, yayinda kalmar data furta masa ta fara yawo a cikin jininsa da bargonsa har takai ziyara zuwa, hantar cikinsa, yayinda hantar tasa ta fara bawa jinin jikinsa kalaman nata..nan da nan dukkannin jikinsa ya dauka..azabar son dayake Mata Baze misaltuba. Dauriya yy ya kwace hannunshi cikinnata ya juya yabar dakin zucia fal sonta da kaunarta.

Kakkashe wutar gidan yy kna ya nufa dakinshi dake kasa. Idonshi fal bacci dan hk yada zango yy a kn faffadan gadonnashi. Lumshe ido yy nan da nan bacci ya kwasheshi...kmr a mafarki yaji mutum kwance a kn faffadan kirjinshi, ..a hnkli ya bude idonshi meze gani? KYAUTAR ALLAH ce ta baro dakinta tazo nashi dakin, don tin fitarshi ta farka, sam bata iya bacci inhar ba a jikinshiba, sede kuma in bata ganinshi.

Murmushi yy don yasan sam bata taba yadda su raba makwanci inhar yna garin. Rungumeta yy, nan da nan bacci me nauyi da dadih yayi awon gaba dasu.

Share and vote๐Ÿฅฐ
[8/4, 19:30] +234 913 133 0334: ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
*KYAUTAR ALLAH*
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ


SAADATU BINTU ABDULLAHIโœ๐Ÿฝ (Marubuciyar boyeyyen al'amari)


*wannn book din na kudine game bukata 300 ne kacal trnsper 0542703718 SAADATU ABDULLAHI GT BANK. kou mtn card ta wannan sim din 08136349646. Ga masu bukatar book dina inso cuta ne complete 300 ne sena jiku*

Free Page3

Bacci sukeyi me cike da kwanciyar hnkli kai daganin yadda suke baccin kowannensu fuska dauke da farin ciki da Annashuwa, kallo daya zakayi musu kasan ba komi dayake damun rayuwarsu, sun samu duniya, Abinda ya rage su nemi lahirarsu, Allah yasa mu dace.

4:30am ya tashi a hnkli ya zameta daga jikinshi, ya nufa bathroom yy wanka kna ya fito daure da alwala ya saka jallabiya milk me mugun kyau, wadda ta amshi jikinshi na yan hutu, direct ya fito ya nufa masallaci, byn sun idar da sallarh ya dawo gidan, har zuwa lokacin bacci takeyi, a hnkli ya karasa ya tasheta, ta bude idonta tangaran a knshi, yayinda still yatsunnan na bakinta, dasu ta kwana ta tashi. "My fineness, tashi kiyi sallah knji..." Ya fada yna kafeta da ido shima yayinda yaga ta kara masa kyau. Murmushi ta sakar masa a hnkli ta sauke kafafuwanta a kn lallausar carpet din dake dakin. Bathroom ta afka Tyi wanka tayi alwala ta fito daure da towel a kugunta.

Yna zaune a gefen bed din yayinda system dinsa na kn cinyarsa yna duba wasu Aiyukanshi, a duk ma'aikatarsa, komi ta system sukeyi. sam Raslan bema kalli inda takeba... Direct Waldrop ta nufa inda kynta suke, domin rabin kayanta na dakin Waldrop dintama daban a dakin. Budewa tayi ta dauki doguwar riga ta material me kyau tasaka kna ta dauko hijjb dinta ta zumbula ta nufa gunyin sallah.

Rabin hnklinshi na kanta, harta idar da sallarh ta iso inda yake ta sugunna ta gaidasa cikeda kauna ya amsa. Hayewa kn bed din tayi don cigaba da baccinta, yatsunnata suna bakinta. Nan da nan bacci ya kwasheta, don tnada son bacci kwarai. Ajiye system din yy ya cire mata hijjb din dake jikinta ya ninke ya mayar Waldron din. Kna ya dawo yaci gaba da abinda yakeyi a system dinsa. Yna gani Ihsan na kiransa, tin 5:30am taketa kiranshi har 6:30am seda tayi masa 26 miss call yna gani karshema ya kashe wayar gabaki daya haushinta ya kara rufeshi, kou ubanme zeyi mata inyana nan ohon mata. Komawa yy ya kwanta, KYAUTAR ALLAH njin duminshi tayi maza ta matseshi kmr mage, don ita akwai shegenson jiji. Rungumeta yy yna shakar kamshin jikinta..se wajajen 10:am suka tashi KYAUTAR ALLAH ta nufa bedroom dinta, can tyi wanka, shikam gogan wankan ya kryi ya fito ya gaida Annah dake zaune a falon. Direct ya nufa dining don har cikinsa ya fara kiran ciroma. Seda ya kira KYAUTAR ALLAH ta fito sannan sukayi break din a tare, Shi yy feeding dnta kmr kullum.

Annah na zaune tana binsu da ido, A gaskia tna tsorata da yadda suke kwana daki daya, Kawaide tna kauda kaine, sbda gudun bacin ran KYAUTAR ALLAH, Amma zuciarta fal tsoron Abinda hknze haifar, tnade Adduarh Allah yasa hkn ya haifarda da me ido.

Wajajen 12:pm Fatima tazo gidannasu. A falo tasamesu duk suna zazzaune suna kallon tv, KYAUTAR ALLAH na jikin Raslan. Ai tna ganin fatima ta miqe a guje taje ta rungumeta. "Oyoyo qawatarh.." Ta fada cikeda nishadin ganin fatima.

Fatima tayi murmushi tace, "Qawata yakike.."

KYAUTAR ALLAH ta saketa tna fadin. "Bnsaniba, byn jiya kikace zakizo bakizoba, inata kiran num dinki yaki shiga.."

Fatima tace, "Uhm dmnde nace miki maybe ai..ke jiya mafa, Yah farhan ne ya dawo knsanshi da takura, shine y hanani fita wlhy.."

KYAUTAR ALLAH tace, "yayanki dinnan wanda ke karatu a malesia.?"

Fatima tace "Yeah shi...jia ya dawo da yammarh" cewar fatima

Annah dake zaune tace, "Maraba da fadima, Ku karaso ku zauna mna inyaso seku cigaba da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login