Showing 270001 words to 273000 words out of 274760 words

Chapter 91 - KYAUTAR ALLAH

10 Sep 2025

14604

tasan RASLAN ne ze gaya mata bata da lafia.. Dauko yaran tayi duka suka fito falon bahbah lantana na biye dasu , har suka iso dinning ta zauna da yayan a cinyarta , bahbah lantana tayi serving dinta, ta fara cin abincin yaran na kallonta ta sa musu a baki suka cinye, dan suna dan cin abinci zuwa ynzu. Bayan ta gama cin abincin ta basu nono suka kama cikin zumud'i ta zuba musu ido zuciarta fal adduarh ALLAH ya tsare mata yaranta daga fadawa abinda ubansu ke aikatawa. Ranar wuni tayi zuciarta da dan sassauci. da lokacin data keda lecture yayi tayi wanka ta shirya ta fice a gidan nan gida ta bar yaran nata da bahbah lantana.... Da rana ya dawo yafi a kirga be gantaba tana school ya addabeta da kira taki dagawa kuma tana gani, hk ya koma office dinsa jiki babu dadih. Da daddare ba gidan yakeba amma seda yazo kmr maye, ina dakina na rufeshi gam da key yazo yayita bugawa inaji nyi bnza dashi ya gama magiyarsa ya fice a gidan zuwa gidan ihsan gashi yna cikin tsananin bukatuwa kuma hnklinsa baya kwanceba, ya samu ihsan da niyar ya rage zafi ita kuma bata da lafia ciwon ciki ya tasata gaba kwanan nan ga jinin dataketa zubarwa babu kakkautawa , ta fada masa yace su shirya suje asibiti gobe. Washe gari da safe suka shirya sukaje asibitin, likita ya didduba ihsan nan ya gano maganin hana daukar cikin datasha ne a baya, ya lalata mata mahaifa (ta denasha ynzu danta samu haihuwa) dr Hussain ya zayyannoma RASLAN bayani dallah dallah, yace Dole ynzu sede a cire mata mahaifar ma baki daya. RASLAN ya juyo ya kalli ihsan tayi kasa da kanta. "Ashe kin dade kina cutata? To bani kika cutaba kanki kika cuta..." Ya fadi hkn a matukar hasale, be tabbatr ihsan munafuka bace se yau. Fashewa tayi da kuka kmr ranta ze fita se ynzu take nadamar abinda ta aikata a baya gashi tajawa knta, babu ita babu haihuwa har abadan. Tashi yy ya fice a office din a fusace, ta mike ta biyoshi tana Kuka, suka shiga mota suka fice a asibitin a motar ma se kuka takeyi, RASLAN beyi packing a ko inaba se a gidansu ihsan, ta juya ta gansu a kofar get din gidansu. " na sakeki saki daya.." Ya fadi cikin bacin rai. Ta juyo ta kalleshi a razane ta kara fashewa da kuka kmr ranta ze fita. "Dan ALLAH kayi hakuri, karka sakeni ..." Ta fadi a gigice. juyowa yy ya zuba mata ido, yauce rana ta farko data taba bashi hkri a tsawon zamanshi da ita
, haka kawai ya farajin tausanta a ranshi ganin yadda taketa kuka kmr ranta ze fita, gudun kada zuciarsa ta karaya yasashi daka mata tsawa "banason kukanki! Ki fitarmin a mota nace, na sakeki saki daya!!" Ta kara fashewa da kuka hadi da masa magiya, ya daka mata tsawa tsole ta fice a motar tana kuka ta shige gidansu, RASLAN ya jima a bakin kofar get din kana yaja motarshi yabar harabar gurin.

Ihsan na shiga gida ta fashe da kuka ta sanar da mahaifiyarta komi, hajiya hadiza ta fashe da kuka ta kira ummih ta sanar da ita, ummih tace karsu damu zata kirashi, aiko ummih tayi kiran duniarnan RASLAN yaki dagawa, kuma yna ganin kiran ummihn saboda yasan kwanan zancen ne yasashi yaki dagawa, direct office dinsa ya Nufa,be tashiba se 6:pm ya nufa gidansa zucia dauke da fargaba, ya shigo gidan tana zaune a falo, jikinsa na rawa ya karaso idonsa na knta, tasa wasu riga da wando najan magana, ya zauna kusa da ita ya rungumota jikinsa. Kmr an tsunguleta ta mike ya zuba mata ido "Me ke faru ne pls? Ko jikin ne? Ya jefo mata tambayar jikinsa na rawa, batabi ta kan ma me yake cewaba ta fice a falon ta nufa dakin yaranya ya biyota , tayima dakin key ta zauna gefen bahbah lantana wadda ke riqe da twins RASLAN yahau buga kofar dakin ta hana bahbah ta bude masa, itama taki budewa harya gaji ya wuce jiki bb laka. Bahbah lantana ta tambayi kyautar Allah me yasa ta masa hk, murmushi tayi tace "Ba komi bahbah, muna yar wasane nidashi..." Bahbah ta jita ne kawai. Hk tayita gwara masa kai, sam batabi ta knsa, a ynzu har tsoronta yakeji, ya rasa ina zesa rayuwarsa yaji dadih. A hk sukayi sati daya a dakin yaranta ma take kwana bahbah ta mata tambayar duniarnan kan meyasa hkn tace mata bakomi. KYAUTAR ALLAH na ankare dashi ynzu be zuwa gidan ihsan ko meyasa bata saniba. Kullum cikin adduarh take ba dare ba rana sannan bata rintsawa da daddare kwana take tana gayawa ALLAH damuwarta hadi dama iyayensa da Annahrtah da duk "
Al'ummar musulmi Adduarh.

Ihsan taje aka mata cs din aja cire mata mahaifir, tayi jinyarta harta warke aka sallamesu, suka koma gida. Kullum ihsan cikin kukan rashin RASLAN take, batasan yanada muhimmamci a rayuwartaba se a ynzu da basa tare, kullum cikin kiran lambarshi take baya dagawa, sede tayita kiran ummih, ummihn na bata hakuri, dan itama be daukar wayar tata.

Mahaifin KYAUTAR ALLAH yazo ya dubata dashi da Anty fahima rnr nan suka wuni se yamma suka hau hnyar komawa kaduna. A yan kwanakinnan se baki iri iri KYAUTAR ALLAH keyi dan hk dmwarta ta ragu, bata taba barin kowa ya gano damuwartaba ballan tanama a tambayeta meke damunta. Anty sadia ma tazo ta wuni nan, ta kawowa KYAUTAR ALLAH magungunan mata masu kyau ta amsa ta mata godia sosai itama nan ta wuni kana ta bar gidan domin laulayin ciki takeyi.

8:30pm Zaune take a falonta da charbi a hannunta se lazimi takeyi yaranta na gun bahbah lantana sunyima baccih, tana shirin mikewa kenan ya shigo falon, sam batayi tsammanin zezoba tasha yana gidan matarshine. Ta juya da sauri tana kokarin barin falon ya karaso ya kamo hannunta, ta fisge ya kara riqo hannun nata gam a cikin nasa. "Dan dan darajar iyayenki kiyi hkri ki bani mintina biyar inaso ne muyi magana..dan Allah da manzanninsa badan niba, nasan na miki babban lefine saboda fushi kikeyi dani..." Ya marairaice kmr ze fashe da kuka. Ta gefen ido ta kallesa taga yayi wata uwar rama yayi baki, duk ramar datayi bata kaishi rama ba se taji tausansa ya cika mata zucia. Jin tayi shiru ya bashi karfin guiwar Kamo hannunta ya zaunar da ita a kn daya daga kujerun dake falon, ya raba gefenta ya zauna ya kamo hannayenta duka biyu, jikinsa har yana kakkarwa. "Dan ALLAH ki gayamin lefin dana miki, nayi miki alqawarin bazan karaba har abadan, sannan zan rokeki gafara, dan ALLAH ki gayamin lefin dana miki, axabar dakikeyimin ta isheni haka, kin sani a uquba, kin hanaki ganinki, kuma kin hanani saduwar aure dake, har ta kaiga kin hanani ganin yarana dana haifa dake kanki, wannan azabar ta isheni, Wallahi kwara kimin komi a kan wadannan abubuwan dakike yimin, kin hanani jikinki bayan na saba dake, inajin dadinki, kin hanani, nasan ba banzaba, na qurekine saboda kinada tsananin hakuri, ki gayamin me na miki yau dan Allah dan darajar mutumcin iyayenki?" Ya karashe mgnr kwalla na tarar masa a ido. Kanta na kasa ko kallanshima batayi ba, haushima taji ya fara bata saboda abinda ya aikata ya dawo sabo dal a zuciarta. "Ni bakayimin komi ba," ta bashi amsa a takaice. Ya zubawa karamin bakinta ido, da kirjinta dake cike taf. "Kawai kinasone ki wulakntani?" Ya fadi murya cike da rauni, dagowa tayi ta kalleshi bata tabbatr namiji beda kunya ba se yau, wai tanasone ta wulakantashi bayanshi wulakncin daya mata bazema faduba, ko a mafarki akace mata ze iya bawa wata mace jikinsa bazata yaddaba ashe ba hakan takeba, shiyasa akace namiji, bakin maciji. "Hmmm..." Kawai tace idonta na knsa. Hmmm din nata ya bashi ma'ana daban daban sannan ya kara tabbatr masa da lefinsa babbane, duk zurfin bincikensa ya gaza gano wani lefi ya mata. Zamowa yayi kasa ya tsugunna a kan guiwowinsa ya kamo hannayenta duka biyu ya fashe mata da kuka yana fadin "Dan darajar iyayenki ki gayamin me nayi miki..dan ALLAH, ki yafemin dan darajar ma'aikin ALLAH ki yafemin , bazan karaba, na tuba! na tuba! Wlhy na tuba!! Nasha wahala! In kika kara azabtar dani mutuwa zanyi!!!"' Ya fadi hawaye na zirya a kan kuncinsa, yana saukowa bisa hannayenta. Bin hawayensa dake zirya a kn hannayenta tayi da ido, ta dago ta kalli kwayar idonsa da gaske kuka yake mata, ji tayi zuciarta tayi sanyi amma batajin zata iya yafe masa, duk abinda take masa tanayi ne danya gaji ya saketa ta huta da auren sa na mazinaci... Ya cigaba da mata magiya tayi shiru kawai tana jinsa harya gama ya zarce da romances dinta kmr mahaukaci, duk abinda yakeyi sam taki tayashi dukda tana cikin bukatuwa dashi, yayi juyin duniar nan taki mayar masa da amsa, shi yayi kidinsa yy rawarsa se iface iface yakeyi jikinsa na bari, shima dan bata da yadda zatayine, ta fashe da kuka saboda haushin knta ma taji data yadda ta bashi jikinsa. Duk duniar dayake ciki hkra yy ya cire burarsa a gindinta ya shiga bata hakuri,. Batama sauraresaba ta nufa bedroom dinta ta fada bathroom nan ta fashe da kuka tayi kukanta ma'ishi kana tayi wankan tsarki. Tin daga ranar ma bata kara bashi jikintaba, shida ita se kallo, aiko ta kara haukatashi danta masa dandani haukace. ana hk akasa ranar saif da fatima, ashe tini sun dinke se ynzu mgna ta fito, ansa ranar biki 1 month aiko humaira kmr zata haukace, da kyar aka samu ta natsu. RASLAN ya kira anty Rukayya ya sanar da ita abinda KYAUTAR ALLAH ke masa, ta kirani ta tambayeni me yayimi nace mata ba komi ,nan ta rufeni da fada hadda zagi kmr Annah part 2, ganin ta harzuqa yasani saukowa na hkra kawai nasawa kaina salama amma ina kallonshi da abin sannan in mukazo kwanciar aure bn tabuka masa komi, wasu lokutan har kuka yake yimin. Ana hk bikin fatima ya matso tin ana saura 3days na masa mgna kan ya barni inje gobe, ya amince da wuri dan yana tsoron bala'i ballan tana ma da muke a dotsane nidashi. Washe gari muka nufa garin katsina nida yarana da nanny dinsu, dasu jummai da laraba, sosai RASLAN ya cikani da kudi yusuf nema ya kawomu. A gidan Annah muka sauka washe gari mukaje gidan biki dmn munyi ankon bikin duka. Ansha shagali sosai. RASLAN ma yazo ranar daurin aure a nan garin Katsinar aka daura auren. Nan gida abuja aka kawo amarya a gidanta madaidaici da saif ya gina mata, sosai aka mata natsiha kana kowa ya watse. KYAUTAR ALLAH ma da mijinta suka dawo gidansu byn sun kai amarya da ango. A gajiye suka shigo gidan wuraren 11:pm. kyautar Allah ta ajiye wayarta a nan falon ta shige bedroom din yaranta da meead a hannunta hannaah na hannun bahbah lantana. Wayarta dake gefen RASLAN tayi ringing ya jawo wayar yaga Anty Rukayya ce itama tazo bikin yau ta koma, picking call din yayi suka gaisa yace mata kyautar taje shimfidar dasu meead, anty Rukayya tace "Okay...daman inaso ne inji kun koma gida.." Raslan yace "Shigowar mu ynzu kenan..." Anty Rukayya tace "Okay, to A gaidata intazo, Allah ya huta gajiya .." Raslan ya amsa da "Ameen..." Daga hk sukayi sallah ma ta katse wayar, ya shiga gallery da niyar ya kalli picture din dasukayi yau a gun biki, hannunsa ya subuce ya danna videos kawai yaga wannan video din nasa, yayi Playing video din yaga tabbas shine kuma samha ce ta masa video din be saniba se ynzu yagano lefin dayasa KYAUTAR ALLAH ke fushi dashi kwanaki, be tabbatr da yarinyarnan tanada hnkli ba se yau shi knshi seda jikinsa yy sanyi , tabbas ta isa mace ta kai duk inda mace ke kaiwa ta zama sirrinsa, bako wacce mace bace zatayi abinda tayi dukda karancin shekarunta. "Zanci kutmar ubanki samha!" Ya fadi cikin bacin rai, kana ya maida wayar ya kashe ya ajiye a gefensa dai-dai- Ta karaso inda yake ta dauki wayar tata ta nufa bathroom dinta saboda tayi wanka ta kwanta ta huta. Ya biyota dakin dai-dai zata shiga bathroom din ya zauna bakin bed dinta ya bita da ido ta shige bathroom din, yana nan zaune har tayi wankan ta fito daure da bathrobe ya zuba mata ido, tazo zata giftashi yajawota jikinsa ta fado masa ya rungumeta sosai a jikinsa. "Ina sonki iyalina, ALLAH ya miki albarka, yasa ki gama da dunia lafia.." KYAUTAR ALLAH ta amsa da ameen. "Yau na gano dalilin fushinki, Lallai kin isa mace, kuma kin zama sirrina, ina me baki hakuri nasan nayi miki lefi babbah Dan Allah ki yafemin, Amma wlhy bn taba sanin wata diya maceba bayan ku matana na sunnah, Wallahi bnsan sadda na aikata abinda na aikata da wannan yarinyarba, Dan Allah ki yafemin..." Ya marairaice mata kmr zeyi kuka, jinjina Kai kawai tayi, zucia taf mamaki, tasan a wayarta yaga komi. A halin ynzu babu komi a zuciarta a dmn rayuwa ai ta gaji hk ko Allah muna masa lefi ya yafemu ballan tana mu yamu yamu. "Na yafe maka har abadan mijina.." Ta fadi cikin kissa, ya rungumeta jikinsa nan suka afka duniar dadih da annashuwa... Hk rayuwarsu taci gaba cikin aminci komi na RASLAN ya mallalawa KYAUTAR ALLAH da yaranta rayuwarsa rankatakaf ta koma a hannun KYAUTAR ALLAH ita kejan ragamar rayuwarsa, KYAUTAR ALLAH taci gaba da zuwa makarantarta masha ALLAH tana fahimta yadda ya dace.

Ihsan fa dunia ta juya mata baya kudaden bleaching dinma ya fara karewa dan ba karamin mai take shafawa ba, na miliyoyin kudade take shafawa to ynzu bb hanyar kudi se fita Kawai kudin keyi, gashi maryam ma ta dena daukar wayarta saboda bata da abinda zata bata a halin ynzu, ashe se kanada ma mora mutane ke sonka.

Se kwanan nan ne KYAUTAR ALLAH tasan RASLAN ya rabu da ihsan , shima saboda Ummih ne datazo har gidan ta samu RASLAN din a kan ya mayar da matarsa, yace ah'ah tayi hkri, to a nan kyauta taji mgnr.

RASLAN yabi diddigin layin samha ya gano tana garin katsina har can yasa akaje aka kamo masa ita da duk yan kungiyarsu, sojoji suka sasu a kanta sukayita duka, musammanma samha RASLAN na tsaye anata dukanta seda aka mata jina jina, ba tare da an tambayetaba ta fadi cewar ai farhan matazo ne yasata ta turawa matarsa message dinnan da kuma video din da cewa ma yayi ta kashe RASLAN ita kuma tace baza ta iyaba saboda tana sonshi, sosai RASLAN zuciarsa ta cika da mamaki."ya akayi kikasan farhan mataxo?'' RASLAN ya jefo mata tambayar. Jiki na rawa samha ta amsa da cewa ai abokin tane, a dubai suka taba haduwa last 3 years ago, suka kulla aminan taka , basu kara haduwaba se kwanaki, shiya nemeta ya bata wannan aikin saboda yanason RASLAN ya rabu da KYAUTAR ALLAH shi kuma ya aureta dan kwanakima daya samu lbrin KYAUTAR ALLAH Nada ciki a gun fatima yaji zancen seda ya kwanta a asibiti saboda damuwa, .." Ba bata lokaci RASLAN yace a kamo farhan, ba bata time aka nufa katsina a ranar aka damqo farhan, nan shima aka hau dukansa , dayaji jiki ya fara fadin irin ta'adin daya rinkawa RASLAN wanda yasa yaronshi jan zaki yayi masa..." RASLAN yace a nemo jan zaki. washe gari kuwa aka nemoshi shida tawagarsa aka hau jibgarsu kmr jakai, karshema RASLAN seda ya hada da duk wani me kakin tsaro a nigerian. Sannan yayi record din komi ya Kai ma KYAUTAR ALLAH tana gani ta fashe da kuka musammanma dataga samha sannan taji bayanenta , tsaf ta gane samha. "Dunia kenan.." Ta fadi tana fadawa jikin mijinta.

RASLAN ya azabtar dasu sosai se da kyar dasa baki yasa aka saki Samha da farhan daman tini aka saki sauran yammatan. Jan zaki da tawagarsa seda sukayi wata kana aka sakeshi, aiko duk yy laushi., farhan yayi nadama sosai ya runguma matarsa da yayansa guda biyu , ya dawo ya bawa Raslan hkri sannan ya nemi yafiyarsa, raslan nada tausai tini ya yafe masa kuma ya kaishi ga yan uwan wadanda ya kashewa rayuka ya nemesu gafara, wasu suka yafe wasu suka barshi da Allah. Samha da kawayenta duk jikinsu yy la'asar suka koma gidan iyayensu, samha ma ta dawo ta nemi gafarar RASLAN yace ya yafe mata, har gidansa taje ta nemi gafarar KYAUTAR ALLAH itama tace ta yafe mata. Yammata hutun duk suka samu mazan dasuka lalatasu suka auresu, sede babu wacce tayi bari ballan tana asa ran haihuwa, duksun gama zubda yayansu a titi. ALLAH ya shiryamu, mata a daure a kai mutumci dakin miji kyafi samun daraja a gun yara da miji, Allah ya mana mawafaqa, ameen.

Ihsan ta dosa zuwa office din RASLAN tana nemansa gafara amma sam yakibi ta knta, karshema ya mata korar kare. Byn kwana biyu Ihsan taje gidan KYAUTAR ALLAH, KYAUTAR ALLAH na ganinta taji tausanta sosai, nan ihsan ta roketa kan dan ALLAH ta temaketa ta rokar mata mijinta ya maidata, KYAUTAR ALLAH tace insha ALLAH zata kokarta. Ihsan tayita daukar twins tana musu wasa, ALLAH ya jarabceta dason yaran, a halin ynzu ma se tafiya sukeyi, KYAUTAR ALLAH taji dadin yadda ihsan keta daukar mata yara, kunsan ance me yayah wawane. KYAUTAR ALLAH ta shiga bakin kokarinta kan RASLAN ya dawo da ihsan, a fari ce mata yy bata da hnkli,,amma bata bi ta tasaba ta nace masa har kuka ta masa saboda kusan kullum se ihsan ta kirata a waya dan sunyi canjen number. Da kyar RASLAN ya kara biyan sadaki aka kara daura musu aure shida ihsan dan harta gama iddarta,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login