Showing 306001 words to 309000 words out of 388641 words
dashi na ganin duk wanda ke a sashen da suke kula da shi ya gano ruwan da suka sakama Jay ya ƙare har jininsa ya fara zuƙa yana komawa cikin robar ruwan, shikam sam baima luraba saida Nurse ɗin ya kama hannunsa yana cirewa sannan suka gani shi da Bilkisu. Idanu taɗan ware waje na alamar mamaki, shikam sai ya lumshe nasa idanun ya maida bayansa ya jinginar kamar yanda yake da.
Nurse ya kammala komai sannan ya fita su Abbu suka shigo duba Jawaad ɗin. Sannu sukaita jera masa da addu'oi, shi kuma yana amsa musu da kai dan harshensa ya masa nauyi sosai har yanzu baijin zai iya furta wata kalma ga kowa idan ba Umm-Anun ba. A rikice Nurse ɗin dake tare da Umm-Anun ta shigo tana sanar musu ta farka itama amma bata cikin hayyacinta.
Rige-rigen fita aka dingayi a tsakaninsu, dan hatta da Jay ba'a barsa a baya ba shima. Tashin hankali kenan, yanda Nurse kusan biyar ke riƙe da Umm-Anum zai baka matuƙar tausayi, a take duk suka rufu a kanta banda Abbu dake tsaye kawai yana kallon yanayin nata cike da nazari, ajiyar zuciya ya sauke kafin yayma Nurse ɗin Umarni akan su sallamesu zasu koma gidan ciwon nata addu'a yake buƙata. Basu musaba dan sunsan shiɗin babban likitane mai bada magungunan musulunci wanda akema ɗakko marasa lafiya daga wata ƙasa mai nisa a kawo garesa balle matarsa kuma.
A take aka shirya musu maidata gida. Hankalin Jawaad yay matuƙar sake tashi ganin mahaifiyarsa ta koma cikin asalin halin hauka kamar yanda tabar gida a wancan lokacin, su kansu su Anuwar ɗin hankalinsu a tashe yake dan basu taɓa ganin Ummunsu a wannan irin halinba, sundai san tanada wani rashin lafiya da takan fita hayyacinta lokaci-lokaci amma basu taɓa sanin dalilin motsawar ciwon nataba suma, da kuma Abbu ya dage kanta saita dawo normal kamilar mace. Anuwar yasha tambayar Abbu amma bai taɓa sanar masa komaiba sai yace lokaci na zuwa da zai sani.
Da isarsu gida Abu-Siddiq da Abbu suka rufi kan Umm-Anum da karatun Al-Qur'ani mai tsarki, hakanne ya ja hankali su Jawaad suma duk sai suka ɗaura al'awa suka zauna sunayi su duka har Bilkisu da Anum, kai harma da ama'aikatan gidan da Aunty Mahfuzah da yaranta itama dukda ƙanana ne ba'a barsu a baya ba. A hankali Umm-Anum ta fara lafawa daga bige-bigen da takeyi, ta buɗe idanunta dake jajur tamkar garwashin wutane a cikinsu tana binsu da kallo. Ba ƙaramin tsorata idanunta suka basu ba, amma hakan baisa sun dakataba suka cigaba, maidawa tai ta sake lumshewa tare da kwanciya jikinta na wani irin masifar rawa, sai kuma ta fashe da matsanancin kuka. Turaren magani Abbu ya tashi ya kunna, hayaƙi ya fara fita yana baje ɗakin. Wani irin gunjin kuka ta fara maiban tsoro tana magana cikin muryar da dagaji kasan ba tata bace. “Ku daina ƙonamu, dan ko zaku shekara dubu kuna ƙonamu bazamu bartaba, zamu gama jiyyane a jikinta batare da mun bar aikinmu ba, alƙawarine rubutacce zamu kasance da ita har ƙarshen rayuwarta, dan haka kuma bar wahalar da kanku babu inda zamuje, bazamu taɓa saɓama shugabanmu ba har abada dan shima bai taɓa saɓa manaba bisa umarninmu...!!”. Sam su Abbu basu sauraresuba suka cigaba da abinda sukeyi, hakama su Anuwar basu fasa nasu karatunba, yayinda Abbu ya cigaba da zuba magani kala-kala na hayaƙi a cikin Burne. Tun suna ihu har suka koma kuka da magiyar a daina ƙonasu kar'a halakasu suba laifinsu bane sakasu akayi. Zuwa wani lokaci kuma sai tayi shiru sai uwar zufa take tamkar an jiƙeta da ruwan zafi. Abbu bai dakata da abinda yakeba har saida yaji ta kirayi sunansa cikin sanyin murya. Ajiye abinda ke hannunsa yayi ya ƙarasa gareta ya ɗago, faɗawa tai jikinsa ta fashe da kuka mai ban tausayi. “Abu-Anuwar yau cikin mafarki naga wani abu maiban mamaki da al'ajabi, naga mai kama da Anuwar wanda tabbas inada alaƙa dashi”.
Tashi Abu-Siddiq yay ya fita dan ya basu waje.
Abbu dake shafa bayan Umm-Anum yana murmushi yace, “Ba mafarki kikeba zahiri ne”. Zumbur ta miƙe zaune tana kallonsa, sai kuma tai saurin dafe kanta da taji ya sara mata. Kamata yay ya kwantar yana faɗin, “Kiyi haƙuri ki kwanta ki huta zuwa anjima ko da safe idan ALLAH ya kaimu sai muyi magana, Alhmdllh nafahimci mun samu wani haske saɓanin da da bama ki taɓa makamancin wannan maganarba”. Umm-Anum dai batace komaiba hannunta na dafe da kanta, ahaka barci mai nauyi yay awon gaba da ita, dukda anata kiraye-kirayen sallar magriba bai hanataba.
Sai da ya tabbatar barcin ya ɗauketa sosai sannan ya fito falo, Bilkisu da Anum yace su shiga suyi salla a ɗakin dansu dinga kula da ita, shi kuma suka fita tare da su Abu-Siddiq salla masallaci. Tunda suka fita salla Abbu ya fahimci Jawaad bayajin daɗi, dan daya kama hannunsa sai yaji zafi alamar zazzaɓi na neman rufesa. Baice komaiba sukai salla suka zauna har isha'i itama suka gabatar sannan suka koma gida. Har lokacin Umm-Anum nata barci, su Bilkisu da suma suka idar da salla suna zaune sun zuba mata idanu cike da damuwa.
Sashin baƙi Abbu yasa aka gyara, aka kaima su Jawaad abincinsu can, Abbu yace Anuwar yaje ya raka Jawaad itama Bilkisu Anum zata rakota.
____________________________________
★★★★★★★★★★★★★★★★★★★
____________________________________
Duk wani masoyin su Momy hankalinsa a tashe yake akan ɗauke Shahudah da ɗan fir'auna yayi, abin ɗaure kai da ban mamaki shine duk yanda ƴan sanda suka bazu nemansa basu samu koda mai kama da shiba, dai-dai da wayarsa an kasa samunta ta kowanne yanayi, dama ita Shahudah tata wayar na nan bai bari ta ɗauka ba, duk kuma inda ake tunanin samun ɗan fir'auna anje babu shi babu abokansa.
Hankalin kowa ya ƙara tashi, Momy kuka take kawai tana zazzagama Dad masifa ta waya akan ya dawo ita tashin hankalin nan yamata yawa, sannan ya saka Qaseem ya taho shima. Shidai lallashinta kawai yakeyi dan shima hankalin nasa aiba a ƙwance yakeba, yana matuƙar ƙaunar Shahudah fiye da zaton mai hasashe, shi da yake nesama dasu ya fisu tashin hankalin. A ranar ya sanarma Qaseem ya shirya ya koma gida zuwa gobe saboda halin da ake ciki. Qaseem dai ya amsa da “to” dan zuwa yanzun bai iyama Dad musu akan komai, duk abinda yace yayi shi yakeyi koda bai masaba. Tun a daren ya fara shirin komawa ƙasarsa ta haihuwa, dan dama hankalinsa bama a kwance yakeba a China'r saboda wata cuta da aketa raɗe raɗin ta ɓillo a wani yanki na ƙasar chain mai suna Corona virus, mutane duk a tsorace suke, daƙyar ya iya danne ransa yaje yayo wata ƴar sayayya da yake buƙata ya dawo hotel ɗin da yake ya kimtsa kayansa, insha ALLAH jirgin farko na gobe dashi zai tashi zuwa ƙasar Dubai cikin birin Abu-dabi, daga nan zai hau jirgin da zai sadashi ƙasarsa.
Ɗan-fir'auna ka sakamu a cakwalkwali😣🙄😏😒😠🚶🏻.
______________________________________
((°•°))((•°•))((°•°))(())(())((°•°))((•°•))((°•°))
______________________________________
Iya ƙofar ɗaki Anum ta tsaya tai min saida safe, kaina kawai na iya ɗaga mata batare da nace komaiba. Ƙofar na tura na shiga da sallama a bakina, falone madaidaici da aka zuba komai cikinsa, sai ƙamshi mai daɗi ke tashi a ciki. Na sauke kumburarrun idanuna akan boss dake kwance cikin doguwar kujera idanunsa rufe, nai masa kusan kallon mintuna biyu kafin na ƙarasa inda yake, durƙusawa nai gaban kujerar na ɗaura hannuna saman goshinsa, wani irin zafi naji zauu dan haka na rimtse idanu da sauri. Jin ya ɗaura hannunsa saman nawa na buɗe idonuna, hannunma akwai zafi shima, a rufe idanunsa suke har yanzu, “Yayanmu baka da lafiya ne?”. Baice min komaiba sai idanunsa dake jajur ya buɗe yana kallona. Hawaye naji sun cikamin idanu, yaɗan lumshe nasa idanun ya sake buɗewa a kaina da girgiza min kansa alamar kar nayi kuka. ban ankaraba naji sun silalo kawai, hannunsa ya ɗaura saman kumatuna ya shiga sharemin batare da yayi magana ba. Kusan mintuna biyar muna a haka kafin ya buɗe baki da ƙyar yace, “Kukan ya isa mana, haɗamin ruwa maiɗan zafi nayi wanka kozanji ƙarfin jikina”. Kaina na jinjina masa sannan na yunƙura na miƙe. Ƙofar dana gani a falon ya sakani tunanin itace bedroom, can na nufa kaina tsaye, koda na tura sai naga ƙaramin kicin ne, rufewa nai na nufi ɗayar ƙofar, itakam ina buɗewa nai tozali da bedroom babba. Numfashi naɗan sauke na shiga, ban wani zauna ɓata lokacin kalle-kalleba na shiga bathroom ɗin da shima ya kasance babba, komai tsaf an gyarashi, sai ƙamshin fresheners masu daɗi. Dai-daita ɗumin ruwan nayi yanda zai masa daɗi sannan na tara masa, komawa falon nayi na taimaka masa ya tashi zaune, dan da gaske bayajin ƙarfin jikinsa, amma duk da haka yamin nauyi sosai, haka dai na daure har muka isa bedroom ɗin, taimaka masa nayi ya cire kayan, ya rage daga shi sai singlet da boxer kawai, a haka na sake taimaka masa zuwa bayin. Duk yanda naso na zame na barsa yay wankan shi kaɗai bai yarda ba, yace na taimaka masa jikinsa sam babu wani ƙarfi, gashi yanajin jiri. Dole na daure nai masa yanda yakeso sannan na sake taimaka masa muka fito, har kayan barci an kawo mana dan haka na taimaka masa ya kimtsa yasha shayi da magani ya kwanta, bargo naja masa na rufesa na zauna gefen gadon ina kallonsa, shima dai idanunsa a kaina, bamu jima a hakaba barci ya kwashesa, ajiyar zuciya na sauke a hankali ina share ƙwallar da suka cikamin ido, duk wanda ya aikata al'amarin nan yacika baƙin azzalumi mai busashshiyar zuciya. Nima shayin kawai nasha, na ɗauki abincin na maida sashensu Umm-Anum sannan na dawo na shiga wankan nima. Gasa jikina nai sosai sannan na ɗauro alwala na fito, nima nai shirin barcin na haye gadon na kwanta tare da shigewa jikinsa da har yanzu yake zafi zau. Lumshe idanuna nayi ina sauraren yanda bugun zuciyarsa ke harbawa, a haka nima barci ɓarawa ya saceni.
WASHE GARI
Bayan mun tashi daga barcin da muka koma na safe wanka mukai, muna cikin tunani da zullumin kayan da zamu saka saiga sallamar Anuwar, boss ne ya amsa masa tare da zira jallabiya ya fita falon, babu jimawa sai gashi ya shigo da akwatinmu. Kallonsa nai da alamar tambaya, sai dai baice komaiba ya ɗora akwatin saman gadon tare da buɗewa ya ɗauka kayansa nima ya fiddomin nawa. “Kitashi ki shirya suna jiranmu, su Takawa ma sunzo” yay maganar cikin dasashshiyar muryarsa da tun jiya bata dawo dai-dai ba. Kaina na ɗaga masa na miƙe.
Tsaf muka fito cikin shiga ta kamala munata zabga ƙamshi, mun iske Anum a fallon su Umm-Anum zaune ita kaɗai da alama mu take jira, da girmamawa ta gaida Boss daketa faman kallonta ko ƙyafta ido bayayi. Nima muka gaisa sannan ta sanar mana duk suna falon baƙi mu ake jira.
Duk suna zaune an baje abinci kala-kala a tsakkiyar falon, yanda muka samu Umm-Anum zaune cikin kamala ya sakamu sauke ajiyar zuciyar jin daɗi muka bisu ɗai-ɗai muka gaisar.
Gaba ɗaya hankalin Jay akan Umm--Anum yake, kamar yanda itama nata hankalin na agaresu shi da Bilkisu, sai dai batace komaiba dan an bari sai anci abinci sannan ai zama akan hakan. Lafiyayyen breakfast ne da kowa ya tsinci kansa cikin jin daɗin cinsa, sai dai boss tsakura kawai yakeyi. hakama Umm-Anum bata wani ci sai kallon Jay take.
Bayan an kammala aka gyara wajen tsaf sannan kowa ya nutsu waje guda..............✍😓
wayyo idona wayyo yatsuna😢🚶🏻
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[1/16, 1:48 PM] HASNA✍🏻: Typing📲
ƘWAI cikin ƘAYA!!
Bilyn Abdull ce🤙🏻
BOOK TWO
Page 50
.................Shiru kakeji falon ya ɗauka bakaji motsin komai saina ajiyar zuciyoyi dana AC dake aiki. Sai da Abu-Siddiq yay doguwar addu'a kafin kowa ya sake maida hankalinsa ga takawa da yay gyaran murya alamar zai fara magana. Wata gyaran muryar ya sakeyi kafin yay sallama a garesu duk suka amsa, Cikin nutsuwa Takawa ya sake gyara zamansa.
“Alhamdulillahi ala kulli halin, duk da dai bamu da tabbacin har yanzu Umm-Anum ta gane Jawaad matsayin jininta ina ganin ya kamata na fara warware abinda mu muka sani game da ita kafin muji abinda zai fito daga nata bakin yanzun”. Jinjina kai kowa ya shigayi cikin gamsuwa da jawabinsa.
“Mun tsinci Umm-Anum a wasu shekaru da zan iya ƙiyastasu da kusan shekaru ashirin da takwas idan ban mantaba, a lokacin nazo gida daga india domin halartar bikin salla babba kamar yanda na saba a duk shekara, saukar dare nayi a ranar, dan sai kusan tara na dare ma na iso, amma kamar ko yaushe na iske sarkin mota na jiran isowata a airport ɗin. A gajiye nake matuƙa gaya dan haka bamu ɗau lokaciba muka bar airport ɗin, tafiyar mu bata wuci ta mintuna goma ba akan titi sarkin mota yaja wani wawan birki. Sosai gabana ya faɗi saboda ƙarar da aka ƙwalla mai nuna tabbacin mun bige wani, daga ni har shi fita mukai cike da tashin hankali. hakama mutane dake ɗan kai kawo a titin harsun fara taruwa a wajen. Ganin mace ce kuma cikin shiga ta kamala duk da babu lulluɓi tare da ita sai muka fara bincikar mutane ko akwai wani nata a wajen?, amma babu wani mai alaƙa da ita. Mun ɗauketa zuwa asibiti, duk da gajiyar da nake ciki bamu bar asibitinnan ba sai da muka tabbatar ta samu dukkan kulawar da ake buƙata a daren sannan muka wuce raina duk a dagule. A dalilin bige baiwar ALLAHr nan gaba ɗaya bikin sallar nan baimin daɗi ba, dan tun bayan farkowarta daga magagin ciwon bugetan da mukai sai muka fuskanci tanada taɓin hankali ma, taɓin hankali irin mai ban tashin hankali, dan duk da cikin halin ciwo da take ƙoƙarinta kawai ta gudu daga asibitin ita dai, dalilin hakan takai har sai da aka saka mata hand corps a hannu da ƙafa sannan aka samu ɗan kwanciyar hankalin ta, a hakanma fisge-fisge take ita kawai a barta ta tafi duk ta jima hannayenta ciwo da ƙarfen ankwa dana gado. Doctor ɗin shine ya faɗamin gaskiya da tabbatar mana cewar matarnan akwai wani babban al'amari tattare da ita, mizai hana mu haɗata da malaman musulinci. Wannan shawara tasa itace ta zame mana haske a kanta, sai kuwa na samu abokina Muftahu akan ya bincika min malamin da zamu kaita wajensa, shine kawai ya bani shawarar mizai hana mukaita Saudia wajensu Abu-Siddiq. Na amshi shawarsa da hannu biyu babu ɓata lokaci mukai duk wani ciku-ciku dagyar muka samu damar fita da ita zuwa nan saudia. A ganin farko dasu Abu-Sufyan sukai mata suka tabbatar mana akwai sihiri tattare da ita, dan kuwa tunda ta buɗe ido daga barcin da take dan allurar barci a kai mata tun da ga can kafin mu taho saboda gudun matsala, sai muka sameta a nutse babu wani bige-bige da takeyi sai dai alamar rashin lafiya na haukan yana tare da ita, alamun hakan na nufin can ƙasarne ba'ason ta zauna kenan ko wani abun daban da bamu da ilimi a kansa. Bayanin da mukaima Abu-Sufyan akanta ne yasa yace mubarta a wajensa na wani lokaci zasu cigaba da kula da ita. Nai masa godiya sosai bayan kwana biyu na koma india nabar Muftahu anan saudia. shima kuma bayan wani lokaci saiya koma. A koda yaushe muna magana da Abu-Sufyan ko Abu-Siddiq akanta da yanayin jikinta, sannan Muftahu nata ƙoƙarin bincike game da ahalinta acan gida, sai dai babu wani haske da muka samu game da samunsu. Bayan wani lokaci jikinta yay sauƙi sosai ta koma normal Alhmdllh, sai dai kuma ta manta komai dangane da kanta, batasan ko itaɗin wacece ba, daga ina ta fito? duk ta manta har sunanta, wannan shine ya ɗarsa tausayinta a zuciyar Abu-Sufyan yace shikam zai aureta har ALLAH ya kawo iyakar komai ta gane ahalinta. Tunda yaymin bayani sai ban musaba, dan uba nike kallonsa bawai yayan aboki kawai ba, na kuma tabbata shine kawai zai iya riƙe amanar baiwar ALLAHr da bata da kowa tunda hatta kanta da sunanta tama manta, ya bada gudunmawa sosai gameda jiyyar mahaifina shima, har kawo yanzu kuma yana badawa a dukkanin al'amurana dana zuri'ata, babu abinda zance a garesu sai addu'ar fatan gamawa da wannan rayuwar lafiya su samu sakamakon aljanna a ranar sakamako”.
Tunda Takawa ya fara magana hawaye kawai kowa ke faman sharewa, Abbu yace, “Tabbas duk abinda ya faɗa hakane, abinda kawai ya manta bai faɗaba shine ciki dake tare da ita, sun kawota da ciki kwantacce da bamusan adadin wataninsa ba, kamar yanda ya nuna, dan sai da muka dage da addu'oi da magani matuƙa sannan ya fara motsi alamar abinda ke cikin yana raye, da alama dai akwai sharrin jinnu a al'amarin kokuma wata hikimar UBANGIJI daya ɓoye game da cikin wadda zuwa yanzu munga ƙalilan daga ciki shiyyasa ya ɓuya a jikinta, tashin da cikin yayi sai yazam watanninsa ya koma baya, dan saiya koma wata uku, sai da tai wata shida sannan ta haihu Namiji, shine yaci suna Muhammad Anuwar gashi nan, bayan haihuwarsa ne mukai aure da ita ta haifi Anum kuma, ga tanan tana da shekaru ashirin da uku, daga ita dai bata sakeba har zuwa yanzun”.
Cikin rawar jiki Anuwar ke kallon Jawaad, sai kuma ya kalli Abbu ya kalli Umm-Anum da ke zaune shiru ta zabga tagumi tana hawaye, dan abubuwa da dama ne keta dawo mata cikin rai tun a daren jiya, hatta da sunanta ta manta sai a daren jiya ta tuna shi. Hannunta dake rawa ta miƙama Jay dake kallonta ko ƙyafta idanunsa bayayi, a hankali ya miƙe ƙafafunsa tamkar an dokesu ya nufota, ta riƙe hannunsa ta zaunar da shi kusa da ita tare da rungumesa ta fashe da kuka, shima Jawaad hawayen yakeyi. A take falon ya ɗauki sabon koke-koke har saida Abbu ya fara musu nasiha akan hakan sannan suka tsagaita. Anuwar ya taso shima ya zauna kusa da Ummu, kafin ya tashi ya koma jikin Jay yana sharɓar kukansa, Jawaad ya rungumesa da ƙyau yana murmushin farin cikin samun ƙanne. Tasowa itama Anum tayi tazo ta zauna ƙasa ta ɗaura kanta saman ƙafar Jawaad, ya sake murmushi da shafa kanta yana lumshe idanunsa da kai hannu ya share mata hawaye itama. Wata irin ƙaunarsu mai tsananice ke ratsa dukkan ɓargonsa