Showing 159001 words to 162000 words out of 388641 words

Chapter 54 - KWAI CIKIN KAYA

10 Sep 2025

20708

iya ce mata na amsa na fito. Koda na fito sai na roƙi Nabeelah tazo ta rakani, catai ALLAH naje ni kaɗai, dan inhar mukaje mu biyu cazai anmasa gayya.
     Badan nasoba

na nufi saman ni kaɗai, addu'a nake a raina Oga Jabeer yazo mu wuce. Sai da nai knocking ya bani izinin shiga sannan na shiga da sallama, kaina a ƙasa ban yarda na kalli ko inaba sai gabana, saida naje dab da shine sannan na kallesa sau ɗauya na ɗauke idona, har ya saka kaya, baƙin wando da yellow ɗin riga folo, yana zaune ne a bakin gado da waya a hannunsa, hannunsa ɗaya dafe da kansa yanzu ma, nidai na ajiye tiren a gabansa ina faɗin, “Gashi inji Ummah, tace kanason wani abune?”. Banji ya tankaba, bankuma damu da yace ɗinba dama na miƙe zan fita.
       “Zonan” ya faɗa a hankali. Dawowa nai ina jan numfashina da ƙyar, dan duk a takure nake, danma zuwa yanzu kamar naɗan fara sabawa da kasancewarmu tare zuciyata ta sassauta min wajen bugun da takeyi idan har muna tare. Nace, “Gani”. Shiru yaymin kamar ba shine yay kiranaba, sai da yaja wasu sakanni kafin ya nunamin dogon table ɗin dake a gaban gadon ta gaba, “Ɗauka waɗancan keys ɗin, kije Gimba ya kaiki station, zaki ɗakkomin abu a office”.
      Duk yanda naso daurewa sai da gabana ya faɗi, ta yaya zanje na buɗe office ɗinsa nikam? A matsayin wa? Na shiga uku, mutumin nan nason jefani a matsala shidai na lura......
      “Miemaa!” ya faɗa a ɗan tsawace ganin dukma bayanin da yake mata hankalinta baya tare da shi. Firgigit na kawo numfashi tare da kallonsa, yanda ya danƙaramin harara ya sakani saurin duƙar da kaina. “Ina miki magana kina wani banzan tunani”. “Sorry sir” na faɗa da sanyin murya, dan harga ALLAH banji miya faɗaba”. Ƙaramin tsaki yaja, ya miƙomin waya batare da ya ce min komaiba, amsa nai ina jiran ƙarin bayani, amma sai ya shareni yama ɗauki tea ɗinsa ya fara sha.
        “Tashimin a kai kafin na canja miki kalar fuskarki”. Fuska na kumbura na juya na fita ina ƙunƙuni a raina.
       Jawaad dake binta da harara yay ƙaramin tsaki da faɗin, “Miskilar banza kawai”.

        Banason zuwa ni kaɗai, hakan yasani cema Nabeelah tazo muje ya aikemu, da yake batasan gaskiyar zancenba sai ta bini muka bar Ummah na haɗa masa abinci. A jikin mota muka iske gimba da alamar yasan da tafiyar, zai buɗe mana mota nace ya barsa kawai, murmushi yayi ya shiga mazaunin driver yana tambayarmu “ya jikin boss ɗin” da sauƙi, muka faɗa kusan a tare sannan muka gaidashi.
       Tunda muka tafi Nabeelah ke zuba mana surutu, Gimba nata biye mata, nidai murmushi ne nawa idan sunyi wani abun dariyar, har mamaki nake yanda Nabeelah bata gajiya da zance saikace wata akku. 
       Nidai har Gimba yay fakin addu'a nake ALLAH yasa karna haɗu da Yah Qaseem, gefe kuma ga maganar shiga Office ɗinsa bansan yanda za'a fassarani ba, sauƙinma na taho da Nabeelah ne, tunanin zuwa office ɗin Oga Aliyu ko Hafiz nayi, saisu kaimu office ɗin, a ganina hakan sai yafi, jan Nabeelah nai zuwa Office's ɗin nasu sai dai munyi rashin sa'a duk a rufe alamar bamasa station ɗin kenan................✍

“Team Bil-Qas & Jay-Hud. Saura wani yace sunan baiyiba😏😜😂”


Fatan alkairi a gareku baki ɗaya😍😍😘👌🏼


ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.[11/30/2020, 12:58 PM] HASNA✍🏻: Bilyn Abdull 📚:
Page 12

.............Babu yanda na iya dole naja hannun Nabeelah muka nufi office ɗin, sai dai tunma a hawan farko aka dakatar da Nabeelah, ni kaɗai aka bari na wuce, kamar na fasa kuka haka naji, sai dai nayi mamaki a raina yanda babu wanda ya tambayeni mizanje yi?.
      Office ɗin na nan tsaf, duk da yau ba'a gyaraba tunda baizoba babu wani datti, yau kam ban cuci kainaba saida nagama ƙare masa kallo gabas da yamma kudu da arewa, hatta da hotunan saman tebir ɗinsa sai da na gama kalleso, tsabar jan magana irin tawa na zauna saman kujerarsa ina gwada yanda yake zama, nakai kusan mintuna huɗu ina shirirtata kafin kira ya shigo wayar da ya bani, ƙurama wayar ido nayi tamkar mai tsoron ɗauka har sai da ta kusa katsewa sannan na ɗauka nasa a kunne batare da nayi maganaba. Daga canma shiru anƙi cewa komai harna tsahon sakanni.
       “Baki iya sallama bane?” muryarsa ta daki kunnena a bazata, idanu na zaro waje dan wlhy banyi zaton shi bane, nace, “Sorry Sir” bai amsa minba sai cewa da yay, ki buɗe ƙaraman drawer na jikin table akwai faran leda da kwali a ciki ki ciroshi” na amsa da “to”. Ina ƙoƙarin jawo ledan kwalin ya fita a ciki, hakanne ya sani cirosu ɗai-ɗai shi da ledan, haka kawai na tsinci kaina dason karanta abinda aka rubuta a kwalin, dan da alama na magani ne, shaf na manta da wayar a kunne take bai kasheba, na hau karatun rubutun jikin maganin ina faman zaro idanu saboda fahimtar danai maganin na miye. Daga can Jawaad da yaji a jikinsa akwai abinda ta nutsu takeyi wanda ya ɗaura zarginsa akan maganin cikin sanyin murya yay magana saboda cikinsa dake murɗa masa a lokacin, “Bincike kike mini?” a bazata naji maganar tasa, shiyyasa na saki kwalin ƙasa batare dana shirya ba, cikin rawar baki, nace, “A...a'a sir” shiru Jawaad baice komaiba idanunsa a lumshe yana faman cizon lip ɗinsa na ƙasa, sai da ya lafa masa sannan ya sake maida hankali akan wayar, nikam duk a tsorace nake, gani nake tamkar ya gane mi nakeyi, cigaba yay da lissafo min duk abinda yake buƙata, na sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya jin yabar waccan maganar, na ɗauka kwalin maganin na maida a ledar ina cigaba da ɗaukar duk abinda yace, inda kuma ya faɗa anan nake ganinsa, bayan na haɗasu na zuba a wata leda baƙa na fito.

       A ƙasa na iske Nabeelah ta cika tai fam da haushi, taban dariya, hakan yasa na murmusa ina kamo hannunta, ƙwafa tai tace, “ALLAH yayanmun nan ko, saina rama abinda yay min”. Nace, “Miyay miki?” ta sake yin ƙwafa, “Bakiga yasa a hanani shiga office ɗinsa ba, ALLAH nima duk randa na fara aiki bazan bari yazomin office ba”. Yanzunkam kasa jurewa nai saida na dara, “Oh Nabeelah yaushe ya hanaki shiga Office ɗinsa, jami'anmu dai sun hanaki”.
       “Kutt wlhy bakisan halinsaba ne, nasan shine yace karsu barni”. Nace, “To kiyi haƙuri, Yaya yayi laifi”. Tunanin zamu dawo yanzu da oga Jabeer yasa ban shiga ko inaba, Mun isa wajen Gimba ya ɗaukemu muka koma, yanzu kam a falon ƙasa muka iskesu harda su Aliyu, mamaki ƙarara na gani a idanun Rose saboda ganina, a tare na gaishesu gaba ɗayansu na ƙarasa gaban sarakin dake kwance a doguwar kujera, cikin girmamawa na ajiye ledan da keys ɗin da wayar a table ɗin dake gabansa nace, “Gashi”. Idanunsa dake rufe ya buɗe ya zubasu a kaina, “Dama tare da Nabeelah na aikeki?” yay maganar yana hararata. Ƙasa nai da idanuna ina girgiza masa kaina alamar a'a. Ƙwafa yay ya ɗauke kansa, ganin hakan yasani barin wajen da nufin bar musu falon ma. 
          “Waye zai ɗauke miki kayan nan”. juyowa nayi, kafin na ƙaraso wajensa Rose dake zaune a kujerar dake inda ƙafafunsa suke ta miƙe ta ɗauki ledan da cewar, “Ƙyale shashasha boss ina za'a kai?”. Banza yay bai tanka ba, niko na sake juyawa zan fita. “K! Ina wasa dake ko?”. Nazata da Rose ɗin yake hakan yasa nai yunƙuri cigaba da tafiyata Aliyu ya kirani.
       “Momi zoki amsa ki kai masa sama kinji”. “To” nace, na dawo na miƙama rose dake ɗauke da ledan hannu alamar ta bani, wata banzar harara ta zubamin ta dangwarar da ledar ƙasa ta koma ta zauna, bance da ita uffanba na ɗauka ledar da keys ɗin na nufi sama, dama duk abinnan da ake tuni Nabeelah ta haye tund

a muka shigo ta gaida su Hafiz ta haye abinta.
        Bily na gama hayewa Jawaad ya miƙe cikin dauriya ya ɗauki ɗaya daga ruwan da aka ajiyema su Hafiz yabi bayanta yana tafiya a hankali, dan inhar yace zaiyi hanzari dolene a fahimci matsalarsa, ca yay musu yana zuwa. Rose ta bisa da kallo a wani irin yanayi maisa ƙuna a zuciya, a ƙufule ta kalli su Aliyu tana faɗin, “Wai miye haɗin wannan yarinyar da Boss ne?, shishshiginta yayi yawafa” dukansu da mamaki suka kalleta, duk da sun fahimci tsagwaron kishi tattare da zancenta, Jabeer ya kare bakinsa da hannu yana dariya ƙasa-ƙasa, sai da Hafiz ya hararesa sannan ya haɗiye da ƙyar, ya kalli sama sannan ya maido dubansa ga Rose data sake cika fam. “Wai Rose kina nufin sonta yake?”. Da sauri tace, “Itaɗin banza, kaima kasan Boss ya wuce da ajinta, kawai dai itace ke shishshige masa”.
       Hafiz yace, “Humm” Aliyu dake murmushi ne ya bata amsa, “Toke tunda kinsan haka miye na damuwar, dan ya sakata aiki sai ya zama wani abu, sau nawa ke ya sakaki ayyuka da sukafi wannan?”. Baki ta taɓe, cikin hausanta da bawani fita yakeba tace, “Amma tunda muke nama taɓa zuwa nan gidan ne? Itako daga gani tana nan tun ɗazun”. Cike da jin haushi Hafiz yace, “To idan ya sakko saiki masa wannan tambayar kuma ai”. Harar Hafiz tayi, dan tun dama can basa shiri, baya shiga sabgarta sai dole, dama sunfi ɗasawa da Jabeer duk cikinsu, Aliyu kuwa baida yawan hayaniya, dan harma yafi Jawaad rashin son magana. Babu wanda ya sake cewa komai, sai Rose daketa kallon hanyar benen tana cika da batsewa da sauke tagwayen ajiyar zuciya.

        A sama kuwa koda na isa Nabeelah na bama kayan akan yace takai masa su ɗaki, har Nabeelah ta amsa zata wuce sai gashi ya hawo, hakan yasani saurin riƙo ledan saboda wata uwar harara daya sauke min, Nabeelah ta juyo zatai magana itama ta samu rabonta na harar, sakarmin ledar tayi da sauri tana barin wajen, ni kam dai ƙasa nai da kai kawai.
       Duk abinda sukeyi Ummah na zaune tana kallonsu, sai dai tayi kamar batasan sunayiba.
      Jawaad ya wuce ɗaki batare da yace komaiba, dan shikuma baima lura da Ummah ba, bayansa nabi gudun karna sake wani laifin. baice dani komaiba harna ajiye ledan nai hanyar fita. Na sauke numfashi ganin na fito lafiya, a raina ina mitar  ‘mutum sai baƙar takura’ matarka dai taga banu yasin, a can ƙasan raina kuma tunani nake yanada mata to miya haɗashi da shan magani irin wannan?, nifa dukma sai naji inajin kunyar abun yasin, nikam bazan sake yarda idona ya shiga cikin nashiba, wannan abun kunya har ina haka. Muna a falon Nabeelah na fama dani akan abinci data zubo ya fito, bai kalli kowaba a cikinmu ya sauka ƙasa.
       
          Ban sakko ba har saida suka tashi tafiya Jabeer ya ƙwalamin kira, lokacin dana ƙaraso duk sun fice daga shi sai Jabeer ɗin, inda yake Jabeer ya nunamin alamar yana kirana, na ƙarasa gabansa dan yanzu ya tashi zaune, batare da ya kalleni ba yace, “Ranar lahadi ƙarfe goma na safe kije ku haɗu da wannan yarinyar, Jabeer zai baki address ɗin wajen”. nidai nace masa to ina jiran ƙarin bayani, sai dai bai sake cewa komaiba, oga Jabeer yace, “muje to, Boss ALLAH ya ƙara sauƙi”. “Amin” ya faɗa akan laɓɓa, nima nace ALLAH ya ƙara sauƙi nai gaba batare da jiran ya amsaba, dan yaban haushi.
        Ni da Jabeer a motarsa muka koma, su  Aliyu kuwa suna a motar  Hafiz da sukazo a ciki, ina kallon yanda Rose keta bina da baƙar harara nai tamkar ban ganiba.
        Munzo fita daga layinne naga motar Mom zasu shiga su kuma, nace, “Lah ga mom can”. Jabeer dake tuƙi yace, “Ƙila itama zataje ganin boss ne ko?”. Kallonsa nai nace, “ganinsa kuma? Wai da gaske Ƴan uwansu ne?” dariya yay yana harba motar kan titi, yace, “Momin mu kemafa na kula akwai shiririta wani sa'in, bakiga gidansu ɗaya bane, ai da mom da Abban Jay babansu ɗaya, sannan Jay shine ya auri Shahudah kafin su rabu”.
       Mugun waro idanu nayi baki a hangame, nace, “Wai dan ALLAH oga kana nufin dama shine mijin aunty Shahudah?”. Jabeer dake murmushi yace, “Ƙwarai kuwa, ammafa a da kenan, amma ke yaya kuke dasu Shahudah da har bama kisaniba?”. Daƙyar na iya ce masa

kamar yanda Mom suke da Abban Boss, nima da Abbansu Aunty Shahudah da Mamana babansu ɗaya”.
      Kai Jabeer ya shiga kaɗawa yana faɗin, “Tab cakwakiya kenan, kice shiyyasa Qaseem beson kowa ya raɓu dake? Kodai ƴar gida zamuyi?”. Murmushin yaƙe kawai nai masa bance komaiba, danni gaba ɗaya kaina ya toshe, koda wasa ban taɓa kawo cewar boss mijin aunty Shahudah bane ba, to yama akai na kasa fahimta? Koda yake bai taɓa zuwa gidanba ina nan, bankuma taɓa ganin koda hotonsa ba a gidan, amma kuma inban mantaba nasha jin sunan Jawaad a bakin ƴan gidan, ‘ya salam, miya toshe min kaina haka?’. Har mukaje station wannan tunani ne keta kaikawo tsakanin ƙwanyata da zuciyata batare da nasan ma'anar hakanba, shima kuma oga Jabeer bai sake cemin komaiba saima redio daya kunna.
       Koda muka iso office nabi oga Jabeer kamar yanda ya umarceni, ya bani ƙaramar takarda ta address ɗin wajen da boss yace sannan na fito. Na iske su ummie sunata shirin tashi, dan biyar tayi, ALLAH ma ya soni nayi sallar la'asar yanzu da muka koma gidansu boss, nima ɗaukar tarkacena nai muka fito tare, dan Ummie zanbi, na leƙa office ɗin yah Qaseem bayan na fito daga wajen oga Jabeer na iske bayanan ya fita wai. Daurewa nai na cire alaƙar Aunty Shahudah da boss data tsayan a rai ba gaira ba sabar na biyema Ummie mukaita hirarmu, har gida ta kaini, sai dai bata shigaba iyakarta gate na sauka ita kuma ta juya.
       Na iske su a falo aunty Shahudah kwance Doctor na saka mata ƙarin ruwa, ba hurumina bane tambayar abinda ya sameta, na gaishesu tare da mata sannu cikin jimami sannan na wuce ɗaki abina. Bansan miyasa na tsinci kaina cikin rashin jin daɗin komaiba, nai wanka na canja kaya, ganinma magrib tayi saina bari nai salla sannan nai zaman yin azkar har aka kira sallar isha'i, itama tashi nai nayi sannan na fito falon dan sake duba Aunty Shahudah, dan banajin yunwa, tun abincin da naci a gidan boss bai sauka ba, duk da saida Nabeelah ma tai fushi sannan naci bayan ummah ta saka baki.
     Na iske aunty Shahudah ta koma ɗaki, sai yah Qaseem kawai a dining yana cin abinci, sannu da dawowa nai masa, yay murmushi yana min alamar nazo. Ban musaba naje garesa, naja kujera nima na zauna, “Kinyi ƙyau” ya faɗa yana kashemin ido ɗaya, murmushi kawai nayi bance komaiba. Haka yayta ɗan jana da hira harya kammala, ya miƙe domin zuwa yay wanka, nima miƙewar nai nace bara na sake duba aunty Shahudah naje na kwanta na gaji.
          Zaune na isketa Aunty Aamilah na bata magani, na sake mata sannu da ALLAH ya ƙara sauƙi na fito, ɗaki na koma nai kwanciyata duk da nasan gobe idan ALLAH ya kaimu babu aiki, amma inason na kira Dad da safe idan ya bari sai naje gidan Inna Zainabu na gaishesu, da wannan tunanin barci ya kwasheni.

      A ɗakin Shahudah kam bayan fitowar Bilkisu Aamilah ce ta sauke ajiyar zuciya tana mai fuskantar ƴar uwar tata da ƙyau. “Sister ga shawara mana” Shahudah da duk tazama kalar tausayi ta jinjina mata kai alamar tana saurarenta. Aamilah ta sake jan numfashi kafin tace, “Ina ganin yarinyar nan Bilkisu zamu iya sakata tai mana wani abu” murya a dasashe Shahudah tace, “Ban ganeba Aamilah ”. “Sister ina magana ne akan Brother Jawaad, da nayi tunanin Broth ne a farko, sai dai daga baya nasan bamai yuwuwa bane, musamman idan mukai dubi da yanda basama shiri tun suna yara, sam jinin Qaseem da Jawaad bai haɗuba, bankuma san lokacin dazai haɗunba, so idan mukace zamu ɗorasa akan ya taimaka mana sai dai ya ɓata komai tunda dama can bason aurenku yakeba, yanzu da yarinyar nan ta shigo, sai naga mizai hana mu amfanu da ita, dan kinsan bata da yawan hayaniya da surutu, sannan mutumin dake da irinki bazai kalletaba da sigar birgewa balle akai ga so, ballantana zuciyarmu tayi tunanin ko zata iya cin amanarmu, ko shi yaji wani abu a kanta”. Shahudah datai shiru tana kallon Aamilah tace, “Maganganunki kawai naji Aamilah, amma ban gane ina suka dosaba sam, wane taimko zamu nema akan Bb?”. “Yauwa, yanzu kikai tambaya mai ƙyau Sisi na, inaji a raina Yarinyar zata taimakemu, sai dai bani da tabbacin wajen aikinsu ɗaya, duk da dai naga kullum tare take fita da Broth, ku

ma Broth da Brother Jawaad wajen aikinsu ɗaya ne, amma wannan ba wani abu bane, zamu iya tambayarta”. Kai kawai Shahudah ta jinjina alamar gamsuwa, Aamilah tace, “ki kwanta ki huta zamu tattauna zuwa da safe, tunda weekend ne tana gida babu inda take zuwa”. Nanma da kai Shahudah ta amsa mata..

★★★★★

       Washe gari da safe na tashi nai ƴan ayyukan dazan iya harda kayana da sukai datti, na gyara ɗakina tsaf nai wanka sannan na fito, babu kowa falon dan har lokacin ma bana tunanin wani ya tashi a jama'ar gidan, kicin na nufa na samawa cikina abinci naci, kafin na sake komawa ɗaki na shiga neman Number dad da ya kirani kwanaki uku da suka shige, kusan duk Numbers nashi na ƙetare inada ita, dan yakan kirani lokaci-lokaci idan yay tafiya tamkar yanda yakema sauran ƴaƴansa, bata shigaba, na sake gwadawa har sau uku saina haƙura, bazan iya zuwa ko inaba bayan wajen aiki saida umarninsa, dan banida wani jagora sama da shi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login