Showing 135001 words to 138000 words out of 388641 words
girmamawa. Nima gaidashi nai, ya tambayeni jikina cike da kulawa. Naji daɗin ganinsa sosai, nakumaji daɗin alhinin daya nuna akan halin dana tsinci kaina, sai dai nayi ƙoƙarin daƙile alwashinsa na buƙatar nabar aikin, danshi kam ya fara tsorata dajin cewa wannan aikin namu da gaske bai dace da ɗiya mace ba, musamman ma irina da nake yarinya ƙarama.
Cikin murmushi da girmamawa a garesa nace, “Dad addu'arku kawai muke buƙata, idan har zamu cigaba da sakawa a ranmu mata basu dace da irin kowanne aikiba saboda matsalolin cikinsa, to lallai yankinmu bazai daina fuskantar koma bayaba, hakama sauran mata masu tasowa bazasu daina fuskantar ƙalubale na daƙile burinsu akan kansu da ƙasarsuba”.
Sosai Dad yay murmushi, ya shafa kaina da cewar, “ALLAH yay miki albarka kinji, lallai tunaninki ƙyaƙyƙyawane Bilkisu, ALLAH ya kiyaye gaba to, nabiya ta wajen likita, ya baki sallama yanzu haka, sai dai ya tabbatarmin daga office ɗinku an turo ɗaukarki, ɗan aiken na hanya kuma, dan haka ni zan wuce, dama daga nan airport na dosa”.
“Dad badai har zaka sake wata tafiyar ba?”.
Murmushi yaymin mai ƙayatarwa yana jinjina kansa, “Hakane bilkisu, masu iya magana nacewa na kwance baiga gariba, muma addu'arku muke buƙata tamkar yanda kuke buƙatar tamu kinji, wannan karon kuma bazan jimaba, dan sati ɗaya kacal zanyi, idan na wuce hakan kuwa bazan zarta gomaba”.
“To Dad ALLAH ya tsare hanya, ya kuma bada nasarar abinda za'a fita nema mai albarka”.
“Amin ɗiyata, nagode sosai”.
Itama Ummie tai masa addu'a, ya amsa mata da kulawa kafin ya ajiye mana kuɗaɗe masu kauri ya fice daga ɗakin”.
Koda Dad ya fice fuskarsa ɗauke take da murmushi tare da ɗunbin tausayin yarinyar a ransa, shidai haka kawai ALLAH ya dasa masa ƙaunarta a zuciya, yaɗan juya ya kalli ɗakin yay murmushi kafin ya cigaba da tafiya........
Gaff sukaci karo da mutum, Gimba yay saurin fara jero kalamun ban haƙuri a gareshi. Batare da Dad yay masa wani kallon arziƙiba yace babu damuwa, yay wucewarsa. Binsa da kallo Gimba yay cikin wani tsagwaron mamaki da juya abinda ya gani a cikin zuciyarsa, sarai ya gane mahaifin matar Boss ɗinsace ta da, kuma mijin Gwaggonsa, afili yace, “To mikenan? Mi yazo yi nan? Minene ma'anar wannan kallon da yayma ɗakin nan? Minenema haɗinsa da ɗakin?”. Bashi da mai amsa masa wannan tambayoyin, dan haka yaja bakinsa ya tsuke dan bai dace ya shiga abinda babu ruwansaba, Boss na yawan masa nasiha da kiyaye abinda ba huruminsaba koda a inane, kuma koda akan minene.
A ɗaki kuwa bayan fitar Dad yabo Ummie ta shiga jero masa, yayinda Bilkisu ke tayata tare da ƙara buɗe ƙyawawan halaye na Dad waɗanda Ummie batasan da suba. A haka gimba yay sallama a ƙofar ɗakin, sai da na suturta jikinna kafin mu bashi damar shigowa, dukda bamusan shiɗin waneneba.
Mun gaisa da juna cikin girmamawa, sannan ya kora mana bayani akan cewar Boss ɗinsa Jawaad ne ya bada umarnin yazo yakaimu gida dan an bani sallama.
Kallon juna mukai ni da Ummie, kowanne baki a hangame, sai dai bamu da damar bin ba'asi akan wannan umarnin, dan kuwa dai yana sama damu, mizaisa mu tuhumesa da abinda bamu da bakin zarensa. Haka muka shiga kimtsawa har Doctor ya shigo, ya ƙara mana bayani akan yanda zan kula da cuwon saboda gudun karya zarta haka, tare da kwanakin da zan ringa zuwa asibitin domin tabbatar da ingancin kulawar da nake bashi.
___________________________
JAWAAD
___________________________________
Zaune suke a office ɗinsa su huɗu, aminan juna kenan da sukejin kansu jini guda, sannan abokan amanar juna masu taruwa wajen magance matsalolin juna da ƙarfin zuciya dana aljihu.
Sunyi nisa cikin tattauna abinda ya faru a yammacin jiya ne, domin dai da gaske Jabeer ne ya haɗa cinkoson jiya da gangan saboda son cimma burin kama tsagerun da suka biyo, amma sai suka ɓace musu, ganin zasu rasa wannan damarne Jawaad ya bama Jabeer umarnin nuna ƙwarewarsa kasancewarsa masani sosai ta ɓangaren na'ura mai ƙwaƙwalwa.
A take kuwa ya nuna gwarzantakar tashi, ya haɗa cinkoson da su Bilkisu suka riska saboda tabbacin nan kaɗaice hanyar da masu laifin zasubi su tsira da wuri, ita kuma Bilkisu tayi tarar aradu daka akan abinda bata da tabbaci.
Aliyu ne ya fara faɗin, “Maganar gaskiya na daɗe banga jarumar mace mai ƙarancin shekaru irin yarinyarnanba, a yanda labari ke fitowa da ga bakunan mutane na yanda ta tari motar mutanen da suka fara ganin farkon al'amari da yanda ta tunkari mutanen zai baka tabbacin da gaske tanada kaifin zuciya akan aikinta”.
Cikin jin jina kai na tabbaci Jabeer yace, “Lallai maganarka tana akan gaskiya wlhy Aliyu, nifa abindama ya sake birgeni da ita shine, dukda mugun ciwon da taji, amma saita dake dan tabbatarma da duniya lallai ita ma'aikaciyar tsaroce ta gaske ba ƴar burgaba”.
Fuska shimfiɗe da murmushi Hafiz yace, “Sosaima kuwa Jabeer, dolene ƙaimin yarinyar ya burge kowa, dan kuwa da ƙwaƙwalwa tai amfani wajen fahimtar motar tana da alaƙa da rashin gaskiya, ta kuma nuna himmarta na sadaukarwa koda hakan na nufin zata cutu a wajensu, ta cancanci kowanne irin jinjina ga hukumarnan tamu, musamman idan akai la'akari da shigowarta cikin aiki jiya-jiya kawai, bana tunanin kuma an taɓama fita da ita wani aiki makamancin haka koda sau ɗaya”.
Duk wannan zance da suke faman zubawa akan yabon Bilkisu da jinjina himmarta Jawaad na zaune shima a cikinsu, yana sanye cikin baƙaƙen suit kamar sauran da a kullum suke ƙara masa kwarjinin kasancewarsa ma'aikaci, sai dai ya cire rigar sama, yana zaune ne kawai da baƙin dogon wandon da rigar ciki mai dogon hannu kalar kore mai haske, maɓallan rigar uku a buɗe, hakanne ya bayyana singlet ɗinsa kaɗan fara tas, yaci zanzaro, ya tsuke ƙugunsa da belt kalar shirt ɗinsa.
Abinda zai baka mamaki ko tari bai yiba akan maganar, baima nuna ya fahimci mi suke tattaunawarba sam, yana zaune ne ƙafa ɗaya kan ɗaya tamkar wani basarake, kansa sunkuye yanata faman danne-danne a cikin tab... ɗinsa ta kamfanin Apple, sam fuskarsa babu wata walwala, kuma ba'a tsuke take sosaiba.
Aliyu ne yakai dubansa garesa, tare da faɗin, “Ka fuskanci abinda muke tattaunawa game da yarinyarnan kuwa Jay?”...............✍
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.Typing📲
ƘWAI cikin ƘAYA!!
Bilyn Abdull ce🤙🏻
BOOK TWO
Page 4
...............Shiru tamkar bazai tankaba, kusan sakanni sha biyar kafin yay magana batare daya bar danne-dannen tab... Ɗinba balle ya kallesu, “Wace yarinya kenan?”. Yay tambayar cikin nuna halin ko'in kula balle su sami ƙwarin gwiwa akan ya jisun.
Duk kallonsa sukai da mamaki saboda yanda sukasanshi dason mutum mai himma, amma yanda ya amshi maganar ya matuƙar basu mamaki a yanzun.
Jabeer ne yace, “Yarinyar jiya daka bama jini mana Jay”.
“Humm” yace kawai ya sharesu bai sake tankawa ba, tsawon mintuna duk sun zura masa idanu suna jiran ƙarin bayani, dan sunyi tsammanin fara jin yabon yarinyar da ga bakinsa ma kafin su su furta, amma ya share kamar ya manta dasu ma a office ɗin.
“Wai boss lafiya kuwa?” Hafiz yay tambayar a wani yanayi.
Sai yanzune ya ɗago ya kallesu su duka, kallo irin a taƙaice ɗinan ya janye mayatattun idanunsa masu cikar gashi da haske tamkar madara, ya taɓe baki kaɗan kafin ya miƙe daga wajen ya nufin kujerarsa ta zama, dan da suna zaunene a rukunin kujeru da'aka shirya a office ɗin domin hutawa ko ganawa da baƙi na musamman.
Sai da ya zauna sosai ya juya kujerarsa tana fuskantarsu kafin yace, “Abun harinmu a yanzu shine mutuwar jami'inmu da sir Ahmad yamin bayani, minene shawararku akan hakan?”.
Aliyu ne ya samu damar faɗin, “Bincike akan shi ɗin wanene? Tunkan fara aiki a wannan hukumar har zuwa farawar tashi, tare da sanin masu bashi gudunmawa akan aikin da yazama sanadinsa, da kuma sanin a ƙarƙashin wa ya samu umarnin”.
“shawara mai ƙyau” Jawaad ya faɗa yana lumshe idanu da kwantar da bayansa jikin kujerar yana lilawa a hankali fuskarsa ɗauke da murmushi, kusan sakanni biyar kafin ya sake ɗagowa yana kallonsu da nazartarsu. Ya ɗauke idanunsa tare da sake komawa jikin kujerar ya kwanta, “Idan an sallamota daga asibiti zatayi bincike akan dukan bayanan Aliyu”.
Cikin matuƙar mamaki suka kallesa, cikin harɗewar harshe Jabeer yace, “wai kana nufin yarinyar?”.
Kallonsa kawai yay ya janye idanu, sai dai baice komaiba. Sun fahimci amsar kenan, dan haka Aliyu yace, “Amma boss baka ganin aikin zai mata girma? Musamman idan mukai dubi akan shine na farko?”.
Cikin halin ko in kula ya taɓe baki, ba tare daya kallesu ba yaja wasu takardu dake saman tebir ɗin nasa yana faɗin, “Maybe hakan, maybe kuma ba hakan baneba, naga kuma da kanku kun yarda da ƙwazonta, to miye kuma na kokwanto yanzun?”.
Babu wanda ya sake cewa komai. sai dai a ƙasan ransu duk sai suka kasance cikin nadamar kwarzanta ƙwazon yarinyar da yawa irin haka, dan a ganinsu bata kai ƙwarin da za'a sakata a irin wannan babban aikin hakaba mai haɗari, musamman idan sukai dubi da ko rose data daɗe a cikinsu baya bata irin wannan damar.
Takardar da ya maida hankali a kanta ya ɗago saitin Hafiz, “Hafiz wanene da wannan bayanan haka?”.
Tasowa Hafiz yay ya dawo gabansa, ya zauna a ɗaya daga kujerun gaban tebirin yana mai amsar takardar, nazarin mintuna biyu ya ɗago kai yana kallonsa, “Akan case ɗin yaron nan da aka samu makamai a shagonsu ne, Aliyu ne akan binciken kuma”.
Jawaad ya maida kallonsa ga Aliyu, hakan ne ya saka Aliyun tasowa ya nufosu shima.
__________★★__________
BILKEESU
_________________________________
Wani irin mayataccen ƙamshi ya shiga rige-rigen zirarawa cikin ƙofofin hancinanmu yayinda muke shiga motar da boss ya turo ɗaukarmu, batare da kowannenmu ya fargaba muka tsinci kawunanmu da lumshe idanu muna sake buɗe hancunan namu sosai. A haka yaja motar muka bar asibitin, tabbas wannan ƙamshine daya cancanci ajiyeshi a ma'ajin zuciya da ƙwaƙwalwa saboda ya kasance na musamman, bansan miyasa na kirashi na musammanba, sai dai kawai zan iya fassara hakan da kasancewarsa na musamman a duk lokacin da hanci ya shaƙa koda ba namuba. Naji tamkarma kar motar ta tsaya ace na daina shaƙar wannan ƙamshin, sai dai babu yanda zanyi dan hakan tilasne. A wannan yanayin muka isa gida, ya ajiyemu a gate ya juya, mukuma muka shiga ciki bayan mun masa godiya.
Mun iske gidan babu kowa, suna gidan rasuwa su duka, dan haka mukai zamanmu dagani sai Ummie da tace boss ya bata umarnin ta zauna dani harna warke tun a jiya. Ban tambayeta daliliba, kamar yanda itama bata kawo komai a rantaba game da hakan, sai dan tana ganin ya fahimci bani da wadda nakeda kusanci da shi sama da ita a station ɗin namu.
__★.:.★__________★.:.★__
JAWAAD
_____★.:.★__________★.:.★_____
Suna tsaka da cigaba da magana shi da su Aliyu kira ya riskesa daga office ɗin B.G, duk da kiran ya bashi mamaki daga shi harsu Jabeer ɗin hakan bai hanashi fita domin cika umarni ba.
Galala nai da baki ina kallon haɗuwa da tsari na office ɗin da Jawaad ya shiga, komai yaji babu algus. Banma kaina buƙuluba nabi ko'ina daki-daki da kallo a office ɗin, kafin na sauke idanu ga mai ikon faɗa aji na hukumar tasu. Danƙari, na ambata a zuciyata dan kuwa munzo ƙarshen zance, sam babu alamun fara'a balle sassauci tattare dashi, Jay ya miƙa gaisuwa cikin girmamawa kafin ya samu izinin zama daga gareshi.
“Sir Ance kana kirana” Jawaad ya faɗa cike da girmamawa.
A cikin maƙoshi ya bashi amsa da cewar, “Uhhm” daga haka yaja bakinsa yay tsit. Gani nai shima Jawaad ɗin ya sake kame kansa ba tare daya sake tankawa ba, kusan mintuna huɗu suna a haka kafin ya ɗago kai tare da juyama Jawaad fuskar lap-top ɗin dake gabansa, hotone mai motsi (video), Bilkisu ta bayyana tana harbi da bindiga har guda biyu a rikicin jiya, gaba ɗaya bidiyon bai wuce na minti ɗaya da wasu sakanni ba, saboda iya itaɗin kawai aka nuna, ƙarewarsa ce ta saka Jawaad kallonsa cikin rashin fahimta.
Cikin zafin rai da fusata ya zazzaroma Jawaad ɗin idanunsa jajaye, “Wannan yarinyar tanada izinin yin harbi ne kamar haka dama?”.
Jawaad da ya tsuke fuska shima ya girgiza kansa kawai.
“Ya akai tayi kuma?”.
Sai da Jay ya furzar da huci kaɗan kafin yace, “Sir bamu da wani zaɓine bayan hakan, domin musayar wutace, idan kuma bata da makamin kare kanta a hannu rayuwarta na cikin haɗari, musamman daya kasance da taimakonta muka riski masu laifin”.
“Hakan yana nufin shine matakin ƙarshe da kuke da mafita kawai?”.
Shiru Jawaad yay bai motsaba, sai maƙogwaronsa ne keta kai kawo a cikin wuyansa, yayi kicin-kicin da fuska.
“Da kai nake magana Captain!”.
“Sir nasan munyi kuskure, amma a duba uzirinmu muma, musamman na isa wajen a ƙurarren lokaci, sannan a duba irin rawar da yarinyar ta taka, duk da kasancewarta ƙaramar ma'aikaciya, wadda ta shigo jiya-jiya cikin wannan hukumar tamu, ta nuna ƙwazon da ya kamata a jinjinama ƙoƙarinta ba ƙalubalantar taba, domin kuwa ita bata da laifi, nine mai laifi dana bata bindigar”.
“Uhyim, kana nufin yanzu dai ka kareta?, sannan dukkan hukuncin da zai biyo baya zaka ɗauka kuma?”.
Shiru tamkar bazai amsaba, sai kuma ya ɗago idanunsa harsun kaɗa da ɓacin rai, a kasaushe yace, “Aimin duk hukuncin da za'ai matan babu damuwa”.
Shiru B.G yay kawai yana kallon Jawaad ɗin, yasan yaron dama akwai taurin kai, dan tun shigowarsa hukumar ƴan sanda ma da tsaurin ido ya shigo, kasancewar wanene mahaifinsa yasa aka hana kowa nuna masa yatsa, himmarsa da zafin nama ne ya saka aka maidoshi cikin hukuma DSS, shi kuma har cikin ransa yaron bai masaba, sanin dalilin kuwa wannan sirrinsane....
“Kaje zamu nemeka” B.G ya faɗa a daƙile.
Uffan Jawaad baice ba, ya miƙe kawai tare da yin salute nashi ya fice abinsa yana haɗiyar zuciya, duk wanda zai iya ganinsa a wannan lokacin dolene ya fahimci ransa a matuƙar ɓace yake, mai makon ya wuce office ɗinsa sai ya nufi office ɗin L.C, wato sir Ahmad barewa, canne kawai zai kai damuwarsa ya samo mafitar da yake buƙata.
Bayan yay knocking ƙofar aka bashi izinin shiga, ya riga da yasan ya gansa ta cctv, tunda ya turo ƙofar ya shigo sir Ahmad ya fahimci akwai damuwa, ya kafeshi da idanu kuwa, yayinda shi kuma Jawaad ɗin yaƙi yarda su haɗa idanu.
Sai da ya miƙa gaisuwa Sir Ahmad yay masa nuni da kujera alamar ya zauna.
Koda Jay ya zauna sai baice uffanba, sai ajiyar zuciya kawai yake faman yi, sir Ahmad yay murmushi irin nasu na manya masu kaifin tunani, kafin ya miƙe daga mazauninsa ya nufi firij ɗin dake a office ɗin, goran ruwa ya ɗakko ya miƙa masa batare da yayi magana ba, babu musu ya amsa, ya ɓalle murfin yana kai goran bakinsa, sai da ya shanye fin rabi sannan ya ajiye yana sauke numfashi a jajjere.
Wani murmushin Sir Ahmad ya kumayi, sannan ya zauna a kujerar dake kusa da Jawaad ɗin suna kallon juna “Captain! Lafiya kuwa? Waya zinguro mazajene?”.
Idanu Jay ya ɗago ya kalli Sir Ahmad, sai kuma ya janye yana shaƙar numfashi da zafi.....
“Jay!”
Sir Ahmad ya kirayi sunansa yana ɗora hannunsa bisa kafaɗarsa.
A karo na Biyu Jawaad ya sake kallon Sir Ahmad barewa, ya cije leɓensa da ƙarfi yana faɗin, “Daga office ɗin B.G nake Sir”.
“Na sani ai” cewar sir Ahmad yana murmushi.
Cikin sauri da tsagwaron mamaki Jawaad ya kalli Sir Ahmad, kallo irin na tuhuma.
Ƴar dariya sir Ahmad yayi, ya kuma kai hannu ya bubbuga kafaɗar Jawaad ɗin a hankali, “Kar kai fushi yarona, karkuma ka shiga ruɗani, banason ka manta kanka a cikin mutane masu kaifin basira, za'ai amfani da yarinyarne kawai ai wasa da hankalinka, kaga kenan an samo lagwonka da damar bama maƙiyanka yin wasoso a saman mutuncinka, kar kaga laifin B.G, shima sashi akayi, domin bana tantama umarni ya samu daga sama, sai dai wanene? Akan minene? Shine ban saniba”.
“Zuutt!” wani abu dake tsaye a maƙoshin Jawaad ya faɗa cikin cikinsa, ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, saboda dai Sir Ahmad ya dawo dashi a hayyacinsa da wuri...
Sir Ahmad ya miƙe yana murmushinsa na kamilallun mutane, ainahin kujerar zamansa ya koma ya zauna..
“Abin bai baka mamakiba ace iya inda take harbin kawai aka kawo masa, sannan kuma ita kaɗai, bayan kuma batakashin da kuka gwabza a wajen ku kusan goma ne”.
“Sir ai abinda ya matuƙar ɓatamin rai kenan, taya za'ai ace itace kawai za'a ɗauka?....”
“Saboda ita kaɗai tazo da salon da ya ajiye ruɗani a zukatan masu fargaba akan jajircewarka”.
“Salo kuma sir?!”.
“Yes! Jawaad, salo mai ƙayatarwama kuwa, andaɗe ba'a samu mai ƙaracin shekaru irinta da wannan ƙwazonba, abin ƙarin mamakin kuma gata mace, yarinyar da alama zata ajiye tarihi a wannan hukumar, dan alamomin hakan sun farane daga jiya”.
“Sir! to amma su wanene ke ganin hakan matsayin ƙalubale garesu? Miyasa kuma....?”.
“Nima ban saniba Jay”.
Shiru Jawaad yay na wasu sakanni kafin yace, “Saboda mi suka zaɓi hukuntata bayan karramawa ta cancanta dashi sir?”.
Sir Ahmad yay gajeruwar dariya idonsa akan Jay, yace, “Saboda ƙwazonta abin dubawane ga mai hankali, sannan abin tunani ga irin waɗanda basa buƙatarta, wannan shine aiki na farko da yarinyar tayi, kuma ba sakata akayiba, sai dai ƙwazonta ya girmi matsayinta da gogewarta a aikin, hakanne ya sakasu saka maka alamar tambaya (?), musamman daya kasance tare da kai aka fara ganin baiwar ta ta”.
Karan farko da Jawaad ya ƙyalƙyale da dariya harda dukan tebir ɗin gabansu, Sir Ahmad dake kallonsa shima murmushinsa ya faɗaɗa, ya juyo sosai yana fuskantarsa, har yanzu kuma fuskar tasa da sauran dariyarsa irin wadda kafin yayita akan kai ruwa rana,
“Sir kasan minene kuwa?”.
“Saika faɗa Jawaad”.
“Sun bani dariya ALLAH, danni Ko sunanta ban saniba fa”.
Dariya shima sir Ahmad ya shiga ƙyalƙyalawa, kafin yace, “Cakwakiya kenan, to tabbas kuwa daga masu wannan ƙullin abun ba haka bane ba Jawaad, kallon ƘWAI CIKIN ƘAYA sukema lamarin”.
“Nima na fahimci hakan a yanzu sir”.
“Yayi ƙyau. Miya faru jiya?”.
Tun daga farkon zuwansu inda abun ya faru har ƙarshe Jawaad ya bama Sir Ahmad labarin komai bai ɓoye masaba.
Kai kawai Sir Ahmad yake jinjinawa har Jawaad yakai ƙarshen jawabinsa, ya sauke numfashi kaɗan yana faɗin, “Zamu shiga meeting anjima, kuma nasan akan wannan maganarne, shawara ɗaya dazan baka yanzu shine, kai ƙoƙarin gano wanda ya ɗauki wannan bidiyon, sannan kayi gaggawar samo bidiyon da yafi wannan na wajensu tsaho, ka kumayi saurin rubuta bayanai akan komai ka tura office ɗin L.G tare da bidiyo ɗin daka samo ɗin”.
Kamar Jawaad zaice wani abu, sai kuma yay shiru yana miƙewa da faɗin, “Okey sir, zanyi ƙoƙari insha ALLAH”.
★★★★
Gaba ɗaya kan Jawaad ya kulle