Showing 210001 words to 213000 words out of 388641 words
abu akan kunne.
Wata mahaukaciyar dariya aka sanya mai dogon zango daga cikin abinda basirarsa ta ankarar dashi wayace, daƙyar mai dariyar ya tsagaita daga can, kafin ya fara magana a kausashe. “Yaro ashe kaima tsagerane ban saniba, kai wanene daka isa tono abinda ke ɓoye? Ƙaramin naman daji abincin karnuka dakai har kakejin kakai zarra wajen yimana kutse a al'amuranmu? Banida lokacin doguwar magana dakai, yanzu za'a sakeka kai gudun mutuwarka kafin jininka ya zama halattacce ga bakandamiyarmu, wanda kakema aikinma bai isaba balle kai direbansa hhhhhhhhhhhhhh!!!!!”.
Wata dariya gimba ya kwashe da ita shima, a kausashe yace, “Faɗan sunƙuru alamace tamai tsoro, idan kuncika maza kufito filin yaƙi mai nasara saiya ɗauki kambu, boss kainuwane dashen ALLAH, zakine mai yagalgala mazan da suke kiran kansu mazanma balle ku mata maza masu ɓuya a rumfar..........
Kafin Gimba yakai ƙarshen zancensa an cire wayar daga kunnensa, taune leɓensa yay da ƙarfi. Kafin a maida masa baki a rufe, Bai sake jin motsin kowaba har yammaci, yana nan ɗaure babuci babu sha tun safiyar jiya rabonsa da abinci, garama ruwa yasha bayan fitowarsu massallacin juma'a, tun yana samun garkuwa daga yawu har shima yay tifƙewar da harshe bai iya juyashi ya zama abun mai gudana, ƙishirwa abune dake saurin illata mafi yawan halitta mai rai, balle irinshi mutum mai matuƙar son ruwa. Alamun duhun magriba da hasashe ne nashi yaji ya sake ɗaure garin, a wannan lokaci yaji an fara kuncesa, har aka gama tas bai motsaba bai kumace ƙalaba. Jansa aka shigayi keeeyyyy har zuwa waje, bashi da ƙarfin kare kansa dan haka ya salama bakinsa ɗauke da addu'a, tafiyar kusan mintuna uku kafin ai wurgi dashi.
Numfarfashi ya shiga saukewa a gwame, yakai hannunsa da ƙyar ya janye ƙyallen da aka ɗaura masa a fuska, baya ganin komai da ƙyau saboda idanunsa sun kwana sun yini a rufe, ga duhun magriba, saidai ya fahimci dajine yake. Da sauri ya shiga laluban wayarsa dake aljihu wadda suka gaza gani bisa kariyar ALLAH, ya kasance mai saka waya silent saboda baison takurama Boss ɗinsa da shigowar kira, a hankali ya saba da hakan har takai bayama buɗeta koda basa tare, tun ɗazun yakejin sautin shigowar kira dama, daƙyar ya iya ganin Number boss saboda idanunsa basa gani sosai sun masa nauyi ainun. Kai tsaye WhatsApp ya shiga, yay azamar danna recording ya fara magana a galabaice.
“Boss banjin zankai labari, dan basu kamani dansu barniba, akwai babbar ƙura a gabanka da bazan iya buɗe maka haske a kantaba yanzu saboda ƙarancin lokacin daya ragemin a duya, itace musabbabin shigowata rayuwarka tun fil'azal ka gafarceni da ɓoyewa, dama nabari ka fita daga wannan matsalar rikicin aurenne idan nadawo muyi magana, saidai ALLAH bai ƙaddara hakanba, amma nagodema ALLAH da wadda zata baka abinda yafi nawa tana raye, kai ƙoƙarin zuwa gidan Alh al..alhaji............ Ya kasa ƙarasawa saboda rawar da jikinsa ya fara na tunkarowar wata muguwar halitta garesa maiban tsoro. Jifa yay da wayar bayan ya ɗaga ɗanyatsansa saƙon ya tafi
kasancewar baya rufe data shi dama can. Baya ya fara jan jikinsa yana karanto duk addu'ar data zo masa, yayinda shikuma wannan halitta ke biyosa danƙyas-danƙyas tana buɗe baki da lashewa alamar dai taga abinci. Babu zato gimba yaji yay baya, ashe wajen gaccine mai zurfin gaske dan akan tsauni suke. Wata irin wahalalliyar ƙara ya saki data bada amsa kuwwa a dajin yay ƙasa.......
Wata irin mahaukaciyar dariya dahar saukarta ke kamar ƙasar dajin na girgiza ce ta fara ratsa tsaunika, anyita da tsayi kusan na mintuna biyar kafin ta lafa wani irin yare ya biyo baya da muryoyin mutane masu yawa. Duk wanda zai iya nutsuwar saurarar yaren zai fahimci kalaman cikinsa shirkace kawai ake ambato. (Wa'iyazubillah 😭ya ALLAH kasa mufi ƙarfin zukatanmu, ya rabbi ka saka duniya a tafukan hannayenmu karka sata a zukatanmu, kaiconmu, kaicon burikanmu kaicon son duniyarmu).
_________________________________
Ana sallar magriba su Momy suka koma gida akan su Uncle Nasir zasu zauna da Jawaad domin yasa ɗan-fir'auna ya saki hudah.
Momy da Shahudah ciki suka shige sukabar Aamilah na waya a barandar shiga falonsu.
Da mamaki Aamilah ke kallon akwatinan da aka jibge a harabar gidan gaban motar Qaseem, ƙiyyy!! Sautin jawo abu ya karate kunnuwanta, kallon wajen da ƙarar ke zuwa tayi, Qaseem ne jaye da jikkan gana must go irin ƙatuwarnan sabuwa dal, amma tsabar yanda yasa ƙarfi wajen janta har hannu ɗaya ya fincike yana lililo, duk dai ya ganta yiyai tamkar basan da zamantaba, baba maigadi dai tun ɗazun yana hangen Qaseem ɗin daga ɗakinsa, tsabar baison yafito ya gansa ya sakashi aikin tayashine ya sakashi maƙalewa cikin ɗakin yana leƙensa ta Window. Jikkar ya dangwarar ya sake juyawa zuwa sashensu, daga shi sai gajeren wamdo da baƙar singlet datai mugun fidda masa siffarsa ta ƙaƙƙarfan namijin dake cin ƙarfe. Saida taga ya shige kafin ta juya da gudu gulma na cinta har saura kaɗan ta faɗi, ALLAH dai ya ara mata damar dafe ƙarfen da aka ƙawata barandar ƙofar falon nasu dashi, ƙara kwasa tai a gujen ta shiga tana ƙwala kiran Momy dake sama abin duniya ya isheta ga Shahudah tsaye kanta tana ribzar kuka da mata fitsara. Sosai kiran da Aamilah ke mata ya firgitata, ta miƙe zumbur ta fito tanabi matakalar benan da gudu-gudu. “Haba auta wannan wane irin kirane haka kamar wata baƙauya, miya farune shin kikemin kiran mafarauta?”. Baki Aamilah ta cuno bayan ta murguɗama Momy kamar wata sa'arta, kafin cikin taɓara tace, “Kajimin Momyn nan, dama kika samu na taimakeki na kawo miki labarin da ɗuminsa, toga ɗankican yana haɗa kaya da alama barin gidan zaiyi”. Sosai gaban mom ya faɗi, batama tsaya saurararta wanne a cikiba ta fice daga falon da sauri, dafa mata baya Aamila tayi tare da Shahudah data fito idanu a kumbure.
Qaseem dake ta faman lodama ƙatuwar motarsa kayan yayma momy dake masa magana kallo ɗaya ya ɗauke kai batare da yace da ita ko ci kanki ba. Muryarta har zuga take na alamun ɓacin rai tace, “Qaseem wai badakai nake maganaba? Shin mikukeson maidanine a gidannan kai da Shahudah? shin bazaka nutsu kai ka fahimci uzirinmuba, Na shiga uku ni Aysha, wane irin mugun asiri wannan yarinyar ta haɗaku da shine kaida yaronan Jawaad da kuke ɗaukar kowa ɗan iska akan lamarinta?”. Cikin zafin murya Qaseem yace, “Nifa kin bala'in cikani da surutu hajiya, Please ki barni nai aikin gabana Mtsooww!!”. Ya ƙare maganar dajan wani wawan tsaki yana ɗauke kansa ya cigaba da loda kayansa a motar. Mutuwar tsaye kawai Momy tai tana kallonsa, Aamilah ta kwashe da dariya tana kallonsu, “Faɗan Uwa da ɗa abin birgewa, kucigaba da gashi guys”. Baki Shahudah ta taɓe tana mai juya manyan idanunta alamar zubama Qaseem harara, tace, “Ɗan jaraba duk bakai kaja manaba, wani iyayi da ƙwala kai a farantinne ya kaika nacema banzar yarinyarnan ƙazamiya mara gata, idan da baka maƙale matanba ta gidan uwarwa aurena da naka zasu haɗu ballema har bb ya aikata haka, asararre kawai mai baƙar zuciyar tsiy.....”
Jikake tasss!! Qaseem da babu wanda ya lura da isowarsa gaban Shahudah ya sauke mata wani wawan mari, ƙasa ta zube tana garsheƙ
ar kuka daja masa ALLAH ya isa, to daman zuciyar ƴan mazan a kusa take, neman wanda zai amayarwa yakeyi, gashi ya samu cikin sauƙi, dan haka ya shigar tamkar an aikosa. Duk ihun da Aamilah keyi da Momy bai sauraresuba, sai ma tsarabar mari Aamilah ta samu itama, Momy kuwa ya hankaɗeta. Qaseem yanada Masifaffiyar zuciya irin wadda idan ta yunƙuro ɗinan sam bayajin bari, dan tamjar zugasama yake, sannan shifa cinnakane baisan na gidaba. Wanna. mugun zuciyan da ALLAH ya basu shida Jawaad itace ta hanasu zama ƙarƙashin inuwa ɗaya, dan kowa yanaji da kalar tasa, kawai shi Qaseem yafi Jawaad saurin fushine, dan Jawaad na dannewa yay kawaici har saika kaisa ƙarshe, amma ga Qaseem sam ba haka bane, sha yanzu magani yanzu, ga kuma ɗanbanzan riƙo saikace dangin kutare🤦🏻.
Iya gwargwadon iko babu algus Shahudah ta daku harma da Aamilah daya koma haɗawa daga ƙarshe, dama yanajin haushinsu akan abu biyu, dukan Bilkisu da jimata ciwo, saikuma gudunmawar da suka bada akan ai masa aure da Azeema. Daƙyar da suɗin goshi baba mai gadi da kuku suka amshi Shahudah da Aamilah a hannunsa, dan yay musu kaca-kaca abinka da farar fata, Shahudah harda fasa mata baki akai jini sai ɗiga yake. Yace, “ƙananun marasa kunya, daga yau idan harku kun cika tsagerune dan ALLAH kusake shiga cikin al'amurana”. Kuka kawai suke daga su har Momy, babu wanda ya iya tanka masa har kuku da baba mai gadi suka gama loda masa kayansa a motar, sashensu ya koma ya ɗakko sauran tarkacensa ya shige mota ya fice batare da ya sakebi takantaba.
Kai tsaye gidansa ya zarce, dama harya ajiye mai gadi tun jiya, kodaga waje kasan gidan ya haɗu, ya mugun ƙawatuwa da shukoki masu ƙamshi da daɗi, ga ƙamshin sabon fentima na tashi. Dakansa yayta shiga da kayan, da yake ALLAH yayisa mutum mai hanzari da zafin nama sai gashi ya gama sakasu ciki tas.
★★★★★
Bayan barin Qaseem gidan babu jimawa Dad ya dawo, iske Momy yay zaune ta zabga tagumi, Shahudah na kwance barcin wahala yay gaba da ita ta ɗora kanta a cinyar momyn. sai Salman da Aamilah dake lido a d/table. duk sannu sukai masa, ya amsa yana zama kusa da momy tare da kamo hannunta cikin nashi. “Humairah mike faruwane?”. Muryarta na rawa tace, “Qaseem ne ya tafi?”. “Ya tafi? Ina ya tafi to?”. “Muma bamu saniba, ya kwashe duk kayansa na gidannan”. Cikin taune leɓe Dad yace, “Bari dai zamuyi magana, yanzu tare nake dasu Alhaji Nasir suna falon baƙi, mun kira yaronan ne da aka ɗaura aurensa da mamana zaizo”. Zumbur Momy ta miƙe jikinta har rawa yake ta ture kan Shahudah batare data tuna tana jikinta tana barciba, tace, “Ya yarda ɗin zaizo Dadynsu?”. Fuskarsa ɗauke da murmushi yace, “Eh ya amince, drivern Alhaji Nasir ma yaje ɗakkosa”.
________________________________
Bayan Jawaad ya dawo daga sallar magriba shiryawa yay ya amsa kiran da Alhaji babba yay masa, kansa ciwo yake masa, amma bashi da ikon bijirema kiran kakan nasa, ballema yaji muryarsa wani iri kamar yana tare da damuwa, tun da ranama ya fahimci hakan, ya haƙurane kawai ya barsa da yace masa babu komai..
Fitowa yay yanata baza ƙamshi, sai dai fuskarnan a cinkushe babu walwala. ya tsaya suka gaisa da mai-gadi har yake tambayarsa gimba bai shigo bane?. mai-gadi yace, “Aiko bai isoba Oga, ni harma na fara tunanin ko lafiya? Dan tunda ya tafi bamuyi wayaba kuma kaga har lokacin daya saba dawowa ya shige amma shiru”. Jimm Jawaad yay alamar tunani, dan shima dai tunda gimba ya tafi basuyi wayarba kam, to wannan hargitsicinne ya ɗauke masa hankali gaba ɗaya har bai ɗauki hakan komaiba. Ya ɗan sauke numfashi yana kallon mai-gadin. baba bara dai naje na dawo, idan har lokacin bai shigeba saina nemesa naji mike faruwa?”. Mai gadi yace, “To to ba laifi oga, ALLAH ya maidoka lafiya”. “Amin” Jawaad ya faɗa yana ficewa, sai dai acan ƙasan zuciyar tasa maganar gimba taƙi gushewa.
A ƙofar gida ya iske Alhaji babba zai shiga massallaci, dan haka yay fakin anan waje ya fito suka shiga tare, bayan sun fito Alhaji baba yay sallama da mutane maƙwaftansa da ragowar ƴan anguwa masu salla anan kamar yanda ya saba, kafin ya kama
hannun Jawaad dake masa shagwaɓan shifa fura zaisha, Alhaji babba ya bada a siyo masa. Alhaji babba dake murmushi ya tsaya yana dungure masa kai, “Kai miyasa idan rikicinka ya motsa babu wanda ka raina saini? Kaje kaima su Mariya mana”. Fuska Jawaad ya yatsine saboda ciwon da kansa ke masa yace, “Nidai ka daina sawa gaban mamana na faɗuwa a darenan, kabama Tanimu ya sayo mani inba hakaba bazan sake zuwa kwana gidanka ba”. Dariya Alhaji babba yay da jan hannunsa suka cigaba da tafiya, yace, “Yoni ALLAH na tuba aina yayeka da zuwa kwanarmin gida, matarka ta jajiba nima na huta da rigimarka hakanan”. Jawaad yace, “Basai na ɗakkota muke kwana anan ɗin tareba”. “Bana gayya, ku zauna gidanku nima aure zanyo”. Ciki dauriya Jawaad ya ƙyalƙyale da dariya, koba komai yarage nauyin da zuciyarsa tayi da tattaunawa da kakan nasa, shi kansa Alhaji baba sai yaji damuwarsa ta sassauta.
Bayan sun zauna Alhaji baba ya zubama Jawaad fura mai ƙyau da daɗin gaske da bai rabo da ita ya dubesa, cike da jin daɗi yake shan furan sanyinta na ratsa masa zuciya da ƙirji. “Muhammad kasan miyasa na kiraka kuwa?”. Kallonsa Jay yayi ya girgiza kansa batare da yace komaiba. Alhaji baba ya ɗan sauke numfashi, murya a sanyaye yace, “Akan matarkane” Saida Jawaad ya haɗiye furan daya sha kafin yace, “Matata kuma?”...............✍
Ƙyan alƙawari cikawa, sai dai wanda na ɗauka ni ya gagara cikar dalilin birkicewar wattpad, harna fara canja page ɗinma sai ALLAH ya taimakeni ya dai-dai ta🤦🏻, page ɗinnan kaɗai gareni babu nagobe saboda matsalar wattpad ɗinan ta ɗauki hankalina banyi typing ba, ƴan telegram sunce a turo muku kawai, amma da wuya kujini gobe idan ALLAH ya kaimu zan samu nayi typing ɗin jibi idan munada rabon kaiwa. Gaisuwa ga kowa da fatan alkairi😍😍😘😘.
ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.
HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO
MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.
MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300
Sai kunzo😍😍😍😘.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻
[12/15/2020, 2:54 PM] HASNA✍🏻: Billy Abdul, [12/15/20, 12:50 PM]
Page 28
................Alhaji babba ya gyaɗama Jawaad kai alamar eh ita. Cike da mamaki Jay ya ajiye kofin hannunsa yana tsatstsare kakan nasa da idanunsa cike da sonjin ƙarin bayani.
Murmushi Alhaji Babba yay masa tare da kamo hanunsa, “Daina tsareni da waɗanan idanun naka ba wani abu bameba, kawai inason sanin dangin mahaifinta ne”. Sassanyar ajiyar zuciya Jawaad ya ɗan sauke, kafin shima ya riƙe hanun Alhaji Babba da ƙyau a cikin nashi, “Baba nima inason saninsu, sonake kawai wannan ƙurar ta lafa itama ta sakejin sauƙine”. Alhaji babba yace, “Kayi tunani mai ƙyau, inason kayi ƙoƙari ka bincika, sannan yaya maganarka da mutanen gidanku? Da kuma maganar shi wanda kasa ya auri yarinyarnan ta wajen Ali?”.
Murmushi Jawaad ya ɗanyi ya ɗauki furarsa zai cigaba da sha, ganin zai basar da zance Alhaji babba yace, “Nasanfa ka jini”. Ƴar dariya Jay yayi yakai kofin bakinsa, “ALLAH ka iya rigima kaima tsohon nan, karka damu ina sane da komai”. “Nasan kana sane da komai Muhammad, sai dai hankalina ya tashi matuƙa jin ba mutumin kirki bane habibun, kajifa wani suna da Nasiru ya kirashi dashi ranar”.
Jay yay murmushi kawai batare da yace komaiba.
Sun cigaba da hirarsu har zuwa ƙarfe tara ya fita, yaso zuwa asibiti, amma ganin dare yayi sai ya haƙura ya nufi gida abinsa. A gate ya tsaya ya tambayi mai-gadi ko gimban ya dawo?. mai-gadi ya tabbatar masa da bai dawoba, ya kira wayarsa kuma gashi tana ring amma ba'a ɗagaba.
Sosai abin ya ɗaurema Jawaad kai, daga baya kuma ya ajiye tunaninsa akan inhar da safe bai dawoba zaisa abi bayansa garin nasu aga ko lafiya?. Da wannan tunanin yay shirin barci ya kwanta.
_________________________________
Su Dady sun karɓi baƙuncin surikinsu habib, duk yanda Dad yaso su Momy su zauna basai sunzo falon baƙiba hakan ya gagara, dole ya barsu sukabi bayansa, ba ƙaramin tashin hankali Shahudah ta shigaba da ganin wanda ake kira wai matsayin mijinta, daka gansa kaga cikakken tantiri marajin magana, cike da isa ya zauna a kujerar da aka nuna masa sai wani cika yake da batsewa.
Ya kafe Aamilah da Shahudah da kallo yana wani lasar laɓɓa tamkar tsohon maye, ko kunyar su Dad bayaji, dama daya shigo babu wanda ya gaida, bama su ishesa kallon arziƙiba.
“Wace cikar tawa anan?” yay maganar cike da gadara. Babu wanda ya tanka masa a cikinsu, sai Shahudah da Aamilah da suka zuba masa wata shegiyar harara. Ya bushe da dariyarsa mara daɗin ji yana faɗin, “Dama ace ana auren yaya da ƙanwa wlhy da duk haɗawa zanyi hhhhh! Dana kwashi gara aradu...” cike da tsiwa Aamilah da tafi Shahudah jin hausa tace, “Uwarkane garan shege mai suffan aljanu.....” wata wuta data gitta ta idanunta mai stars ce ta hanata kaiwa ƙarshe, lokaci ɗaya jinta da ganinta ya ɗauke baki ɗaya ta zube a jikin Dad daya tarota. Babu wanda yaga sanda Ɗan-fir'auna ya ƙarasa gaban Aamilah sai ƙarar maruka sukaji kawai.
A fusace Dad yace, “Kai ƙaramin ɗan tsagera, wanene ubanka da har zaka mararmin yarinya a gabana?”. Kallon dad ɗan fir'auna yay ya watsar, kafin cike da gadara yace, “Sanin ubana a gareka dattijo ai tamkar yankewar numfashinka ne, dama kun kiranine domin kuci zarafina komi? kunga dalla malamai ku bani matata na wuce na fasa zaman....” da sauri Uncle Uwaisu ya taresa