Showing 231001 words to 234000 words out of 388641 words

Chapter 78 - KWAI CIKIN KAYA

10 Sep 2025

20692

ya farayi shine bige-bigen waya, a kiran farko Umarni ya bada a nemo masa gidan da Bilkisu ta sanar masa sun zauna da iyayenta a Anguwar Bankaura, tare da ainahin maigidan da halin da gidan yake ciki yanzun. Kira na biyu kuwa Ainahin gidansu Baba makaho inda aka haufesa yasa a binciko masa shikuma a Anguwar Tudin Jarƙasa.
       Sunyi zaman awa biyu shida su Aliyu, duk da yaga ɗacin ran da Rose takeyi baibi takanta ba, bayan sun kammala ta buƙaci yin magana dashi, ca yay mata bashi da lokaci yanzun kam saita bari wani lokacin. Cike da takaici ta riga kowa fita. Haka ya cigaba da rage akainin gabansa.
         Misalin sha biyu yabar station zuwa Barrack ɗin sojoji da suka fara zuwa jiya kafin su tai jejin nan, ya samu ganawa da Lieutenant General a tsaitsaye dan ya iskesa yana shirin fita, ya sanarmasa wajen baba ƙaura yazo. Lieut G ya saka wani soja yayma Jay rakkiya har gidan da baba ƙaura yake zaune a cikin Barrack ɗin.
           Baba ƙaura ya tarbi Jay da murmushinsa mai tsayawa mutum a rai, bayan sun gaisa ya sake yima Jawaad ta'aziyya. Jawaad yay masa godiya akan gudunmawar da ya basu jiya. Fuska ɗauke da murmushi baba ƙaura yace, “Yaro bani nayiba ALLAH ne yayi”. “Hakane baba” Jawaad ya faɗa cikin sake tabbatarwa. shiru suka ɗanyi na wasu sakanni, baba ƙaura yace, “Mike tafe da kai?”. Ɗagowa Jay yay ya kallesa da ƙyau, ya tsufa sosai sai dai yana tare da ƙarfinsa, bashi da tsaho sosai sannan shiba wada bane, ya risinar da idanunsa yana faɗin, “Maganganunka na jiya baba na kwana juyasu a rai, sai dai har safiyar yau ban iya samo amsar ko guda ba, baba mika sani a kanmu?”. Murmushi baba ƙaura yay idonsa akan Jawaad, yace, “Yaro bansan komai a kanku ba, hasalima jiya na fara ganinku a iya tsahon rayuwata, kowane irin mutum a duniya yanada baiwarsa, ni tawa baiwar kenan, fahimtar wasu abubuwa daga mutane, akwai mutane masu irin wannan baiwar tawa da yawa a duniya, sai dai mafi yawansu sunfi zaɓar aikata saɓon ALLAH da tasu damar, sai kaga mutum ya zama ɗan tsubbu ko naɗama kansa wani girman da zai halakar da mutane daga barin ALLAH, ko ya maida baiwar tasa ga zalunci da neman duniya. wlhy kaji na rantse maka bansan komai daya shafekuba face abinda UBANGIJI ya bama idanuna ikon gani tattare daku jiya.....”
      Cikin jinjina al'amarin baba ƙaura Jay yace, “baba ko zamu iya sanin abinda ka fahimta ɗin?”
       Murmushi Baba yay da faɗin,  “Yaro minene sunanka?”. Jay yace, “Jawaad”. “Masha ALLAH, malam Jawaad bawani abune na gani a rayuwar kuba, domin kuwa ƙaddarar da duk ke cikin rayuwar kowanne ɗan adam wannan ɓoyayyen sirrine daga taskar ALLAH, abinda ALLAH ya bani ikon gani tattare daku kawai shine rayuwarku na ɗaure da wani al'amari mai girma, sannan kunada taurari masu ƙarfin haske da suka hana duhun dake zagaye daku tasiri, dan har na waccan yarinyar sunfi nakama haske, abinda nazarina ya bani bayan faruwar abubuwa a dajin nan shine akwai sihiri mai ƙarfin gaske jingine da jininku, su wanene sukai muku? Miye dalili? Saboda mi? Daga yaushe ne? Shine ban saniba sai abunda ALLAH yasio sanar daku nan gaba”.

      Cikin ɗaurewar kai Jawaad yace, “Amma miyasa kanema sanin sunan mahaifinta?”. “Saboda duhun dana gani biye da bayanta yafi naka rintsi”. “Duhu kuma baba?”. “Ƙwarai duhu ɗana, amma da sannu zai yaye insha ALLAHU bisa rahamar ALLAH, shawarar dazan baku shine ku dage da addu'a da sadaka musamman a cikin wannan watan mai albarka na Ramadhan da zamu shiga nanda kwanaki uku idan munada rabon kaiwa. Kunika ciyar da bayin ALLAH fiye da yanda kukeyi a baya, ku saka dubunnan marayu farin ciki fiye da yanda kukeyi a baya, ku kaima UBANGIJI kukanku fiye da yanda kukeyi a baya, sannan a daren jiya naga wani haske dake nesa da kai na tunkaroka, sai dai yana nesa dakaine, bansan tayaya zakaje garesaba koshi yazo gareka”. Da sauri Jay ya kalli baba ƙaura, “Baba ko hakan nada nasaba da mafarkin da nake mai sarƙaƙiya?”. “ALLAH kaɗai yasan gaibu Jawaad, amma tun yaushe ka fara mafarkin?”. Jimmm Jay yay alamar tunanin, yace, “Baba idan har ban mantaba na farayinsa a daren da muka dawo daga wata horaswa daga ƙasar America ne, shekara kusa ɗaya kenan, sai da danayi sau ɗaya ban sakeba sai a watanan nan naketa maimaitawa, bayan ɗaurin aurena da ita sai kuma ya canja salo”. “Ikon ALLAH,to shidai mafarki sirrine yaro, sannan akwai abinda yake ishara daga UBANGIJI a cikinsa, akwai wanda shaiɗanu ke jinginuwa a cikinsa, akwai wanda keda alaƙa da saka abu a rai, to amma kozan iya jin wani abu daga mafarkinka?”. Babu musu Jay ya faɗa masa na farko da wanda yay a ƙarshe washe garin ɗaurin aurensa da Bilkisu bayan sallar la'asar. Baba ƙaura ya daɗe baice komaiba, yanata juya abun a ransa amma bai samu wani hasken da yake buƙataba, ya ɗago ido ya zubama Jay na tsahon lokaci kafin ya janye, “Alƙar jini a cikin jini yanada nasaba da kamar kun haɗa jini kenan nidai a nawa ɗan sanin da UBANGIJI ya banifa, amma sanin gaibu sai ALLAH”. Sam Jawaad bai fahimci komai daga kalaman baba ƙauraba, dan a iya saninsa babu ta inda yakeda dangantaka da Bilkisu sai ta wajen su Hudah..... Baba ƙaura ya katse masa tunani da cewar, “Sarƙaƙiyar dake ɗaure da rayuwarku tanada nasaba da wani zalincin mai tushe daga wasu jininku, UBANGIJI shikaɗai yasan sirrin dake ɓoye dai, amma a mafarkinka mutum kake gani yana sanar dakai kokuwa?”.
      “Da farko dai bana ganin kowa, amma daga bayan nan mace nake gani, gashi na santa a mafarkin, sai dai dana tashi fuskarta saita ɓacemin, duk iya hasashena bana tunota”.
      “To UBANGIJI shi kaɗai yasan dalilin sirranta maka ita a zahirin taswurar zuciya, kuje kucigaba da addu'a, ALLAH bai manta da al'amarinku ba. Ga wannan gadalin (maganin), karkaji komai sanine daga abinda ALLAH ya sanar dani nima, saboda bibiyarta da ake ana tsoratar da ita dalilin abinda ke hannunta nasu ALLAH bazai basu damaba insha ALLAH, a zubashi a Abu mai tsafta, a karanta Ayatul kursiyyu (itace aya ta 255 a suratul baƙara), suratul Yunus aya ta 79~82, Suratul Ɗaha aya ta 65~70, Suratul Kafirun, Al-Ikhlas, Al-Falaq, An-Nas, a tofa ciki,  A shafe jiki da shi akuma ringa sha safe da yamma, sannan ai turare da wannan. Insha ALLAHU duk wani baƙin aljani da aka haɗata dashi zai gusa, zaku samu haske mai yawa akan al'amarin cikin amincin ALLAH, sihirin dake jikinku zai warware da izinin UBANGIJIN al'arshi.
       Ada Jawaad ya tsani irin waɗanan abubuwan, amma jin baba ƙaura ya ambata harda ayoyin ALLAH saiya amsa yay godiya, sunɗan ƙara tattaunawa yay masa sallama ya tafi.
       Daga Barrack ɗinan tasha ya nufa inda gimba ke hawa motar garinsu idan zaije gida weekend.................✍

😉🤫👍🏻😘.

ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
        ƊAURIN ƁOYE
      ALƘAWARIN ALLAH.

HAFSAT RANO tazo muku da;
         SAUYIN ƘADDARA
        ƊAURIN GORO

MAMU GEE tazo muku da;
           BURI ƊAYA
         ƘAUNAR MU.

MISS XOXO tazo muku da;
           KAIMIN HALACCI
           IGIYAR ZATO.

BILYN ABDULL tazo muku da;
          WUTSIYAR RAƘUMI...
         GUDU DA WAIWAYE....

abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya

500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.

Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899

sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.

Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300

Sai kunzo😍😍😍😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[12/21/2020, 3:47 PM] HASNA✍🏻: ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK TWO

Page 33

...............A ɓangaren gidan Dad komai ya ƙara caƙuɗewa, yakasa barin ƙasar koda kuwa zuwa Niger ne, komai Shahudah batayi yanzu banda aikin kuka da kiran Jawaad, ta tabbatar musu indai basu rabata da Habib sun maidata gidan Jawaad ba saita kashe kanta, kullum cikin lallaɓata suke da mata alƙawarin samun Jawaad duk rintsi kuma har ƙarshen rayuwa, zakuma su rabashi da bily koda tsiya dan ita kaɗai ta mallakesa, acewarsu tabari ya gama hayaƙin rashin mutuncinsa yanzun sunada hanyar maganinsa ne.
Qaseem kan tun bayan barin Jay asibiti da Bilkisu ya shiga wankama Doctor mari akan ya buɗe masa ƙofa, cikin gigitar azaba Doctor ya buɗemasa ƙofar ya fita, koda ya fito sai bai iske su Jawaad ba, cike da mahaukacin gudu ya ɗauka motarsa ya fice daga asibitin. Marukan da yayma Doctor ne yasaka sauran Doctors ɗin asibitin alwashin ɗaukar mataki, atake suka kira police, ko jinin dake fita ta hancin Doctor basu tsaida masaba saida ƴan-sandan sukazo suka gani.
Qaseem daya fita yana can yana bilayin neman su Jawaad titi-titi bayan yaje gidansu ance Jay baizo nanba, ya nufi gidan Jay na A.Y street ne ƴan-sandan da aka tura kamashi da yawun hukumar lafiya ta ƙasa sukai ram dashi, duk yanda yaso musu taurin kai da nuna musu shiɗin wanene ɗan wanene sunƙi saurarensa. Dan kuwa dai shima Doctor ɗin da ya mara ɗan wani ƙusane a ƙasar, gashi ma'aikaci a asibitin gwamnati, shiyyasa kamun Qaseem ya taho tun daga sama.
Yau tsahon kwanakin Qaseem biyu kenan a police station batare dasu Dad sunma saniba, su duk tunaninsu Qaseem na gidansa ne tunda fushi yake dasu bazasu ganshi a yanzuba.
Salman ma dai daƙyar suka lallashesa ya haƙura da batun barin ƙasar, dan yacefa shi lokacin mutuwarsa baiyiba da zai tsaya ɗan-fir'auna ya sakashi cikin jerin waɗanda zai watandarsu kamar kajin salla, da farko Mom masifa ta fara masa, da dai taga babu ci sai ta koma lallaɓashi har Dad ɗinma, da ƙyar ya haƙura akan shifa da yaga wani motsi zai ware abinsa, da wannan ajandar tasa suka yarda, ba komai yasa basason yay nesa dasuba sai sanin halinsa musamman akan shaye-shaye, shiyyasa basason yay nesa dasu, ALLAH dai yasosu abin bai nisaba suka tsaya kansa ya haƙura.
Momy dake haɗama Dad tea takai dubanta garesa, yay shiru tamkar babushi a d/table ɗin, gaba ɗaya rikicewar da gidan yayi yasa sun fita hayyacinsu daga ita harshi, wani irin jin ƙarin tsanar Bilkisu tai a ranta, dan kuwa a ganinta duk itace sanadin komai, shigowarta rayuwarsu ne ya tarwatsa musu gida, da Dad bai jajubo musu itaba da yanzu suna zaune cikin kwanciyar hankalinsu, siririn tsaki taja tana mai dangwarar masa da kofin tea ɗin gabansa. Kallonta yay da mamaki, yace, “Lafiya kike tsaki? Bayan kinsan abinda nafi tsana kenan a rayuwata?”.
Momy ta kuma jan wani tsakin tana cigaba da zuba masa farfesun bindin sa ɗin da takeyi, “Bakai nakema tsakiba nikan Dadynsu, sanadin tarwatsewar gidana na tuna, lokacin da zaka ɗako yarinyarnan dana nuna ɓacin raina fushi kaitayi dani, ka ringa nunamin batada maraba da ƴaƴanmu jininmu a wajenka, gashi kaga sakamakon daya biyo baya ai, ka ɗakkota daga inuwa ita ta turamu rana, ranarma mafi munin zafi da ƙuna, nikam dai wannan zuminci naku ai ALLAH ya tsine mar (Wa'iyazubillah, Mom zuminci ya wuce tsinuwa, dan yana ɗaya daga cikin hanyoyin shiga aljannah🙄).
Dad yace, “Humm, wlhy kuma kingafa Aysha duk da wannan abun daya faru sai ban daina jinta a rainaba, a ganina yarinyarnan bata da laifi akan rikicinan, daga gidanku aka harɗa komai, kekuma gashi bakison laifin danginki sai nawane sakarkaru ko?!”. Yanda yay maganar da zafi-zafi ya saka Momy kallonsa da mamaki fuska a yatsine tace, “Ikon ALLAH, kaifa nagama sammun yarinyarnan yafi cinka fiye da kowa a gidannan kai da wannan shashashan Qaseem, to wlhy inma ban ɗauki matakin ƙarshe akan yarinyarnanba kuce ba sunana Aysha Humaira ba Mtsowww!!” ta ƙare maganar da buge table ɗin ta tashi tabar wajen.
Duk wannan abu dake faruwafa tsakanin Dad da Mom Shahudah da Aamilah na zaune a D/table ɗin suma, Aamilah dai earpiece ne a kunnenta tanajin waƙa, shiyyasa batasan mi tsoffin nata je tattaunawa ba, Shahudah kam cikin damuwa take mai gusar da hankali, zuciyarta gaba ɗaya tana ga Jawaad da tunanin ina Bilkisu?, dan a yanzu dai wannan matsalar tafi cin zuciyarta fiye da komai, ɗan-fir'auna tasan ko kotune Dad sai ya kaisa ya saketa, inmafa bai saketanba ita ahaka zatai aurenta tunda ai bada soyayya tsakaninsu aka ɗauraba, a ganinta tunda babu soyayya ai auren bai ɗauruba kenan (Hudah Kai a tukunya😖😂 lol).
Buga table ɗin da Mom tayine ya maido hankalinsu kansu, duk suka bita da kallo kafin su kalli Dad da shima kallon Momyn nasu yake rai a matuƙar ɓace.
Aamilah dai baki ta taɓe ta cigaba da sauraren waƙarta dacin abinci, Shahudah ce dai ta kalli Dad ɗin bayan ɓacewar Mom a idanunsu. “Dad wai faɗa kukeyi ne?”. Huda tai maganar tana mai tsatstsare Dad da manyan idanunta da suka koma ƙanana a yanzun saboda tsabar yawan kuka. Kansa ya girgiza mata yaja bowl ɗin data saka masa farfesun ya fara shan romon kawai dan kauda hankalin Shahudah daga abinda take zargin.

___________________________________
Jawaad kam daga wajen baba ƙaura tashar da Gimba ke shiga mota idan zai tafi gida ya nufa. Wajen bawani babban tsasha baneba, dan motocin garin su Gimban ne kawai sai masu ƙarisawa cikin ƙauyikan dake maƙwaftaka dasu. Kowa na sabgar gabansa daga masu talla har matafiya da masu sauka, sai ƴan mashinan Napep dake ɗaukar masu shiga cikin gari idan an saukesu a tashar. Sai da ya gama ƙarema wajen kallo daga cikin motarsa kafin ya ɗauki glasess ɗinsa baƙi ya toshe idanunsa dashi, baya wani cikin mood ɗin farin ciki, hakan yasa sam fuskar babu alamun sauƙi balle rangwame. Tamkar zakin dake taƙama bayan yaci ya ƙoshi haka ya fito daga motar, dama tun fakawarsa mafi yawan jama'ar dake kai kawo a wajen suka zubama motar ido da tsumayen waye zai fito daga cikinta, dan kuwa dai taci ta ƙoshi ita kanta motar balle kuma mamallakinta a ganinsu dole ya zama abin kallo. Yako zama abin kallon dan shi kansa saida ya takura dajin yanda idanu ke yawo a kansa har jinin jikinsa na tsitstsinkewa. Guntun tsaki yay yana sake ɗaure fuska, ya fara taku a hankali yana tunkarosu kansa tsaye.
Tuni da masu kallon nasa da masu gulma suka nutsu, aka shiga gaishesa da tambayarsa ko akwai abinda yake buƙata?. Ta cikin glasess ɗinsa yake ƙare musu kallo ɗai-ɗai, sukam sam basa ganin idanun nasa, sai ƙyawun da glass ɗin yayma fuskarsa ba ƙaramin ɗaukar hankalinsu yayba. Jawaad ya shiga ƙarema saurayin dake gabansa tamkar zai duƙa kallo, nuni yay masa da hannu alamar ya miƙe da ƙyau. Babu musu kuwa ya miƙe. “Inason ganin shugaban wajen nan naku ne”. Jay yay maganar yana maida hannunsa guda cikin aljihun wandonsa. Kafinma saurayin yace wani abu wani dattijo da kallo ɗaya zakai masa ka fahimci wahalace ba tsufaba ya ƙaraso wajen yana mai amsa maganar Jay data shiga kunnensa. “Gani nan Alhaji, barka da zuwa, naɗan zagayane kama ruwa shiyyasa”.
Shi dai jay kallonsa kawai yake harya dasa aya. Dattijon ya kuma faɗin, “Muje daga cikin runfa Alhaji nan kaga rana na dukanka”. Babu musu Jay ya bisa suka shiga rumfar da ƙuda keta faman bi saboda sanyinta, ga robobin abinci da sukaci harda na fura duk ƙudan ya baibaye, gefe kuma masu saida abincinne ƴammata da yara ƙanana abin gwanin ban tausayi. Shi kallonsu yake da tausayawa sukuma suna kallonsa da birgewa da sha'awa. Duk da Jay yaji ƙyanƙyamin tebiran dake wajen matsayin abun zama haka yay shirin zaunawa akai da farin wandonsa tas daketa ɗaukar ido. Da sauri dattijon nan ya dakatar dashi, abin sallar dake can kan babbar tabarma shimfiɗe ya ɗakko bayan ya bugata ƙura ta tashi, yazo ya saka masa kan bench ɗin. Jay baice komaiba ya zauna duk da itama dai sallayan sai a hankali.
Dattijo yace, “Alhaji bara a kawo maka ruwa ko fura”. Da sauri Jay yace, “A'a nagode karka damu, tambaya nazo yi”. Dattijo yace, “ALLAH yasa na sani to Alhaji. Jay yaɗan gyara zamansa, idanunsa dake cikin glass kafe akan Dattijo, yace, “Akwai wani yaro saurayi da bazai wuce shekaru talatin da ɗaya ba mai suna Gimba, duk ƙarshen mako yake zuwa nan ya shiga mota ko kun sanshi?”. Cike da jimami Dattijo yace, “Tabbas munsan Gimba, ai a wajenan kaf Alhaji babu wani driver da zai ce maka baisan marigayiba, danshi mutum ne na mutane ga barkwanci ga alkairi”. Jay Cikin nuna alamun kamar bai sani gimban ba yace, “Naji kace marigayi; kana nufin ya rasu ne?”. Zama Dattijo ya gyara yana matsar ƴan ƙwalla, “Alhaji ashe bakasan ya rasuba? Ai jiya-jiya akai zana'idarsa ma, muma yau labari yake zuwa mana akan duk yanda abun ya faru, ance ogansa da yakema aikine yajasa cikin ƙungiyar asiri, dama anata ƙananun magana akan yanda Gimban kema mutane ɓarin abin arziƙi a garin musamman a irin wannan watan na Ramadhan dazai kama, to dai kasan mutanenmu da kwaɗayi, dukda anajin tsoro dai haka ake amsa a lashe, sai ya gusa kaji anayi dashi, saifa yanzunne da suka tsotse jinsa zance keta fitowa abubuwa gasu nandai barkatai babu daɗin ji”. Tunda Dattijo ya fara magana jikin Jay ke wani yaamm na mamaki, haka kuma aka maida zancen rasuwar gimban ahi baida labari?, kai ɗan adam sai dai ka gansa ka barsa da halinsa kawai, baiji komai a ransaba tunda yasan ba hakan bane, abinda kawai ya ɗauka jahilci ne ke aiki cikin ƙwaƙwalen kansu. Ya gyara zamansa cike da ƙwarewa cikin salon aiki yace, “Ai nima akan batun mai gidan nasa nazo daman, yanzu haka mun kamashi a hannu bincike mukeyi, idan ka bamu haɗinkai kaima kanada naira dubu hamsin sabbi ƙar a takarda. Jimm Dattijo yayi yana ninƙaya a nazari, mikuma ya tuna sai ya kalli Jay yace, “Nikuwa mina sani akan wannan zance Alhaji?”. A karan farkio Jay yay murmushi, “Ba canai ka saniba daman ai,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login