Showing 381001 words to 384000 words out of 388641 words
wata matar cikin ƴaƴan family ɗinsu, hakanma zai taimaka mana, sai dai sam Jawaad yaƙi hakan, mun buga ta kowanne fanni babu nasara, tun daga wannan lokacin komai na ƙungiyarmu ya ringa samun tangarɗa da ruɗani, ciki harda shigowar wani maharbi rayuwarmu, sai dai daga baya shi munyi maganinsa ta hanyar salwantar da rayuwar duka iyalansa dashi kansa. Ƙwatsam muna a wannan ruɗanin kuma sai ga Bilkisu ta shigo rayuwata a bazata, inda naci karo da ita a gidan ƴar uwata. Banyi sakaciba na ɗakkota, a washe gari kuma nakai sunanta ga bokanya kamar yanda mukeyi akan budurwar da duk muke buƙatar budurcinta, sai dai kuma Bilkisu sai tazo da banbanci ga sauran, dan bokanya tamin alƙawarin inhar na mallaki budurcin Bilkisu na cika dukkan sharuɗan ƙungiya, dukiyata zata sake haɓaka, zan kuma samu nutsuwa akan komaina. Tamin alƙawura da dama game da yarinyar, sai dai kuma komai bai yuwuba, dan yarinyar tana tattare da wasu sirruka da muka gaza ganewa har zuwa yau, ta zama sanadin rushewar abubuwa masu yawa a garemu ciki harda aurenta da Jawaad, tashin hankalin da muka fahimci yana tunkaromu a dalilinta yasa muka sadaukar da jininta ita da Jawaad.........”
__________________
ZAFAFA 2021
_______________
Masoya naku taurarinfa sun sake dawowa da sabon salo a 2021.
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗
Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗
Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗
Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
09033181070
Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO
TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
________________
“Babban sirrin dake tattare da ita shine amincewar UBANGIJI game da furicin mahaifiyarta game daku”.
Wata murya ta bada amsa ga Dad a bazata. Gaba ɗaya falon suka juya suna kallon mai maganar cike da mamaki da al'ajabi. A bazata Bilkisu ta miƙe zaram tana share hawayenta, jikinta na wani irin tsuma da rawa tace, “Inna! Baba! Firdausi da gaske kune? Kodai gizon da kuka saba yiminne?”.
Fuskar Baba cike da murmushi yace, “Mune ƴata ba gizo muke miki ba, mune tsaye a gabanki bayan rabuwar ƙaddara ta tsahon shekaru, na godema UBANGIJI daya sake haɗamu Bilkisu, na godema ALLAH daya kawoni wannan ranar dazan sauke nauyin da ɗan uwana abokina ya ɗauramin tsahon shekaru”.
Da gudu Bilkisu ta nufesu ta rungume Inna da firdausi tana mai fashewa da matsanancin kuka, suma kuka suka sanya harda Baba. Mai martaba ne yay gyaran muryar da ta sakasu yin tsuru lokaci guda, cikin nutsuwa yace, “Su wanene ku? Mi kuma ya kawoku nan?”. Kafin a cikinsu wani ya samu damar bada amsa Jabeer dake bayansu tsaye yace, “Ranka ya daɗe suna tare da magana mai muhimmanci, tun da sassafe suke a gidan Jay suna jira dan suga matarsa, duk korar da maigadi yaymusu basu tafiba. Kasan yanayin da ake ciki, shinefa drivern sa ya kirani ya sanarmin, da naje bayanin da sukaiminne yasa na gamsu na kawosu nan”.
Umarnin ƙarasawa ciki aka basu, sai da suka zauna da mika gaisuwa Bilkisu na maƙale da inna sannan takawa ya bama baba damar yin bayani akan abinda ke tafe da su. Baba ya sauke nannauyan numfashi yana mai duban Bilkisu da Inna ke sharema hawaye, sai kuma ya duƙar da kansa ƙasa ya fara magana da rawar murya. “Sunana Abdullahi, babban amini ga malam Adamu makaho. Abotarmu ta farane tun lokacin daya kama haya a gidan da nake, tun muna iya gaisawa da mutunci sama-sama tsakanin iyalanmu har muka zama aminai, matanmu ma haka. Kamar yanda na daɗe ban samu haihuwa ba Adamu ma hakane, cikin hikimar ALLAH sai ga ciki a jikin matanmu kusan lokaci guda ni da shi. Matata itace ta fara haihuwar ɗiya mace, ga tanan (ya nuna Firdausi) dan dama ta riga matar Adamu samun ciki da kusan watanni biyu zuwa uku. Kamar yanda al'adarmu take matata ta tafi wankan jego ƙauye, bayan tafiyarta da kusan wata ɗaya matar Adamu ta wayi gari da naƙuda, hankalinmu ya tashi dan ba watan haihuwarta bane, a haka muka ɗauketa zuwa asibiti, ƴan kuɗin sana'arsa ya ƙundume ya miƙa akai mata duk abinda ya dace, sai dai daga ƙarshe likita yace sai an mata aiki, dan ɗan dake cikinta ya ruɓe, ma'ana yadai mutu ma, barinsa itama zai zamarwa tata rayuwar barazana. Hakan ba ƙaramin tada mana hankali ya sake yi ba, gashi ƴan kuɗaɗen hannunmu sun ƙare, kuma suna buƙatar kuɗi kafin su mata aiki. Adamu ya barni a asibiti ya hau acaɓa ya kaisa can anguwarsu gidan iyayensa dana sani, dukda dai ya sanarmin mahaifiyarsa aka haifa a gidan (Alokacin Adamu na gani da ido ɗaya fa) sai dai kuma bai wuce awa biyuba sai gashi ya dawo rai a ɓace alamar bai samo komaiba. A gabana ya labartama Asiya komai, dukda halin ciwo da take ciki saita kwantar masa da hankali, tace yaje wajen yayanta Alhaji Ali (Dad) tasan zai taimaka musu. Baiyi musubu ya jani muka tafi tare, gidane katafaren gaske mai ƙyau da gate, a lokacinma duk gidan da kaga gate to lallai maishi ya tara, munta ƙwanƙwasawa amma ba'a buɗe mana ba, Adamu ya tura ƙofar cikin haushi sai gata ta buɗe a bazata, sai da muka lalleƙa babu kowa sannan muka shige cikin gidan batare da tunanin komaiba. Munta sallama a ƙofa nanma dai bamuji motsin kowaba, sai wani irin nishi da gurnanin kuka. Babu tunanin komai Adamu ya nema cusa kansa, na riƙesa ina girgiza masa kai akan karya aikata haka, tunda ba gidanmu baneba, kuma akwai mace a ciki. Hankalinsa dake a tashe na halin da asiya ke a ciki yasa bai saurareniba, ya fisge hanunsa ya shige ciki babu ko sallama. Duk da a tsorace nake banida zaɓin daya wuce bin bayansa nima. Sanda muka shigo cikin falon sai mukaji kukan ya yawaita, gashi ana kukan ne da addu'ar fatan neman ɗauki daga ALLAH, Adamu ya kalleni na kallesa, sai kuma duk muka kalli ƙofar da muke jiyo kukan. Kukan jinjiri ya sakamu dawowa a hayyacinmu batare da mun shiryaba, Adamu ya matsa jikin ƙofar da sauri yana magana. Daga ciki aka amsa da faɗin “ko wanene ya shigo dan ALLAH” kamar bazai shigaba sai kuma ya afka kansa tsaye, duk kiransa da nake famanyi bai saurareniba. Haka nabisa na leƙa sai dai ban shigaba, daga ƙofa na hango mace durƙushe tana naɗe jariri dake cikin jinin hauhuwa a zane, ita kanta inda take durƙushen duk jinine. Adamu na tsaye hankalinsa a tashe yana kallonta. Ɗagowa tai ta miƙa masa jinjirar jikinta na rawa, sai kuma tai cak tana kallonsa, kallo irin na kamar na sanka kokuma ina nasanka? Da rawar baki tace, “Mai kama da Baba!”. Sai kuma ta girgiza kai da sauri tana hawaye. “Wannan ba lokacin tunanin hakan baneba, bawan ALLAH koma miya kawoka gidannan nasan UBANGIJI ne ya aikomin kai danka taimaki wannan baiwa da batasan komai ba sai iskar duniya data shaƙa a yanzun. Dan ALLAH ka ɗauketa, ka nisantata da gidannan, itaɗin ɗiyatace, mijina ke neman kasheta saboda matsafine, kaimin alfarmar saka mata suna BILKEESU, karka taɓa faɗa mata bakai ka haifetaba dan girman ALLAH har sai takai shekaru ashirin a duniya, ka binciki ɗan gidan tsohon shugaban ƙasa daya rasu, JAWAAD ABDUL-AZIZ ka haɗata dashi, ka sanar masa suɗin ƴan uwan junane, ɗiyar Rahama ƙanwar mahaifiyarsa Bilkisu ce. Suyi ƙoƙari su haɗa hannu wajen binciken mai gidannan da duk abokan da yake mu'amula dasu, babu isashen lokacin dazan maka bayani aka kaina da abinda ya faru, amma nasan komin daren daɗewa lokaci zai fiddo komai dan sharri baya ɓoyuwa a duniya. Ka ɗauki wancan akwatin akwai kuɗi da kayanta a ciki na baka halak malak, dan ALLAH ka bata tarbiyya irin ta addini, karka bar rayuwarta ta tarwatse da ruɗanin duniya, ka faɗa mata ina tsananin ƙaunarta fiye da komai dana mallaka a duniyarnan. Kai maza ka fita, suna gab da dawowa, idan suka iskoka zasu halaka ka da ita da ni baki ɗaya, ni kuma bana fatan hakan”. Ta ƙare maganar da wani irin kuka mai cin rai da zuciya. Motsin buɗe gate da mukaji ya sakamu fita da gudu, kafin mukai ƙofa mukaji ana shirin buɗewa, wani ɗaki muka shige da gudu muka ɓuya muna leƙen masu shigowar ta taga, a gaban idanmu Wannan (Uncle Nasir) da wannan (Dad) suka shiga ɗakin da matarnan take, duk maganganun da sukai ita dasu muna saurarensu, har lokacin da suka fita da ita daga gidan. Da ga ni har Adamu kuka muke rurus, sai dai bamu da wani ƙarfin ikon sakawa ko hanawa, sannan muna son cika mata alƙawarin fita da ƴarta daga gidan cikin aminci. Sai da muka tabbatar motarsu ta fice a gidan sannan muka fito muma muka fice da gudu, cikin amincin ALLAH mai gadin gidan yanzunma bai ganmuba ya shige cikin ɗakinsa kamar ɗazun da muka shigo yana ciki.
Da kuɗin da matarnan ta bama Adamu akaima Asiya aiki, aka cire ɗanta mara rai, bayan an kamala mata aiki aka kaita ɗakin hutu. Adamu yakai jaririya da ya roƙa wata nos ta gyara ya kwantar kusa da Asiya. Bayan ta farfaɗo cikin dare bai ɓoye mata komai game da bilkisu ba, ita kuma saita amsa da daraja ta rungume tana kuka, dan koba komai ai ɗiyar ɗan uwantane. Abinda kawai Adamu ya ɓoye ga Asiya shine ɗan uwanta matsafine, bai faɗa mata wannanba, ya kuma roƙeni na ɓoye wannan sirrin dan ALLAH har sai lokacin da jaririya Bilkisu takai mizanin shekarun da mahaifiyarta ta roƙa kafin mu bayyana komai ga kowa. Na masa alƙawari da karɓar amanarsa, na rufe wannan zance a raina tamkar yanda shima ya rufesa ga kowa nasa suka cigaba da rainon bilkisu, har ALLAH yasa takai shekarun girma, sai dai kafin lokacin da Adamu ya cika alƙawarin sanar mata ita wacece ALLAH yay masa rasuwa sakamakon bigesa da mota tayi, itama kuma Asiya ALLAH yay mata rasuwa kafin shi. Musan ƴan uwan Adamu bazasu ɗauki Bilkisu ba, dan sun saka wasiwasi a ransu game da ita tun tana jinjira. Na ɗauki Bilkisu na cigaba da kulawa da ita kamar yanda Adamu yayta roƙona gab da numfashinsa zaibar jikinsa. Sai dai kuma na gaza cika alƙawarin lokacin da taƙadin yaron mai gidanmu ya shigo rayuwar gidan............” ya ƙarashe labarinsa da zaman Jazuga a gidansu, har faruwar komai na abinda bilkisu tai musu, da maidasu ƙauyensu da Alhaji Lado yayi, tare da gargaɗi da baza abokan Jazuga a ƙauyen suyi gadinsu. Doguwar jiyyar Firdausi da sukasha wadda tai kamar bazata rayuba har tsahon shekara kusan guda kafin ta warke ayi bikinta da ɗan uwanta, gashi a yanzu sunada yara uku, Musa (Fharhan), Abbas, sai bilkisu da firdausi taima bily takwara saboda ƙauna da soyayya haɗe da ɗunbin bege a gareta.
Jin wannan labari daga bakin Baba ya saka falon sake ruɗewa da koke-koke, Bilkisu kuwa data gigice tamkar wadda ciwon hauka ya sama lokaci guda ta miƙe zaram tana nuna Dad jikinta na wani bala'in karkarwa. “Baba kana nufin shine Mahaifina?”.
“Tabbas Bilkisu shine mahaifinki?”. Ai ganin Bilkisu kawai akai ƙasa wanwar ta sume. Dad kuma ya fashe da wani irin gigitaccen kuka da ƙwalla ƙara, ya shiga buga kansa jikin bango yana ihu maiban tashin hankali da faɗin “Tabbas Rahmah maganar ki ta zama gaskiya, Alaƙar ƙaddarar jiji dake cikin jini ta tabbata.....”. Ƙoƙarin riƙesa ƴansanda sukeyi, yayinda can kuma aka rufu kan Bilkisu ciki harda Jawaad daya ƙwace daga riƙon da Alhaji Babba yay masa.
Bayyana muku tashin hankalin da waɗanan mutane ke a ciki a wannan lokaci zaici tsahon lokaci bamu gamaba, komai ya sake hargitsewa da ruɗewa, dole ƴan-sandan dake a waje suka shigo cikin gidan tare da dogarawan sarki wanda shi yama rasa abin faɗa tsabar mamaki, a da gani yake babu wata ruɗaɗɗiyar rayuwa irin tasa, sai a yau yaga wadda tafi tasa muni da tashin hankali.
Da ƙyar aka iya fita dasu Dad daga gidan, suna kuka da roƙon a yafe musu amma babu wanda ya sauraresu, sai ma tsinuwa da sukesha daga bakin kowa harda ƴaƴansu kansu da matansu. An shiga ƙoƙarin yayyafama waɗanda suka suma ruwa harda Shahudah da Bilkisu, da Mama Atika. Wadda itakam da alama ma dai faɗuwar da tayi tazo da sakamakon paralysis, dan ta gaza motsa komai nata sai ido takebin mutane da shi kawai tana kuka.
______________
Komai fa ya sake rikicewa, gari ya ɗauki magana da ba'asan tayaya ta fita daga gidan Alhaji babba ba, sai daga baya aka fahimci camera aka saka jikin su Dad da ba'asan wanene ya sakaba, ta naɗe komai daya faru a gidan Alhaji babba, lokacin da aka maidasu office kuma a take aka fidda komai ta kafafen yaɗa labarai.
Lokacin da takawa ya baro gidan Alhaji babba zuwa inda ake jiransa zasuyi meeting da ƙyar suka kai saboda hargitsewar da garin yayi, matasa ta ko'ina sun fara fitowa zanga-zanga da makamai akan sufa sai an basu su Dad sun kashe. Kamar wasafa saiga zanga-zanga ta fara faɗaɗa, dan harda ƴammata da zawarawa a cewarsu suma sunabin kadin haƙƙin ƴan uwansu dasu Dad suka lalatama rayuwa ta hanyar fyaɗe. Idan ba'a basu su Uncle Nasir ba zasu bankama station ɗin da aka ajiyesu wuta.
Sai kuma rukunin magidanta da tasu zanga-zangar ta ɗauki manufa akan kisan tsohon shugabanƙasa Abdul-aziz Yousif Tafida, a cewarsu sumafa sai sunbi kadin jinin adalin shugabansu. Tofa jama'a sun fusata ainun, kowane titi ka zagaya mutane ke tittiɗowa zuwa station ɗinsu Jawaad da aka ajiye su Alhaji Kokino, tun jami'an tsaro na ƙoƙarin kwantar da tarzomar dake nemans harfa al'amarin ya nema gagararsu sai da aka kawo wasu jami'an tsaron kala-kala. Amma duk da haka al'amarin ya gagara. daga ƙarshema sai suka zagaye hall ɗin dasu Takawa sukai zaman meeting, acewarsu su fito su bada damar a fiddo musu dasu Kokino kokuma su haɗa dasu. Dan bazasu taɓa yarda sai ankai su Dad Kotu ba, su duk duniya basuga alƙalin da zai iya yima su Dad shari'a ba sam. Gara kawai su kashesu a haɗu a kotun UBANGIJI kawai.
★★★★★★★
Har dare gari yaƙi lafiya, tamkarma ƙara ƴan zanga-zangar akeyi. Jawaad na gida tare da ƴan uwansa dake cike da ruɗani da tashin hankali wannan al'amari har yanzu kira ya samesa daga office. Duk yanda yaso ƙin fitar Alhaji babba sai da ya takurashi, acewarsa babufa yanda zasuyi, wannan al'amarin su barma ALLAH kawai shine zaiyi maganin waɗannan mutanen bawai ƙarfinsuba ko dabararsu. Haka ya fita jikinsa duk babu wani daɗi, ya sumbaci goshin bilkisu daketa barci yana haɗiye hawayen da suka cika masa ido, tausayin kansu yakeji daga shi har ita, musamman ma ita da nata al'amarin yazo a yanda basuyi zato ko tsammaniba, kenan Shahudah da Bilkisu ubansu ɗaya fa kenan? Bilkisu jininsa ce, jini mafi kusanci da muhimmanci a garesu, jinin wadda take da daraja a garesa, wadda ta yarda ta rasa ranta da farin cikinta a dalilin salwantar da mahaifinsa.
Bai iya jan motarba sai Hafiz ne yazo har gida ya ɗaukesa, shi kansa halin da yaga garin yake ciki ba ƙaramin sake tada masa da hankali al'amarin yayiba, dare harya rufa amma mutane basu da niyya komawa gidajensu. Da ƙyar motarsu ta samu hanyar shiga station ɗinsu.
Sun sami su Sir Ahmad cikin tsananin tashin hankali da damuwa, sune sukaimasa bayanin yanda akai komai ya fita har jama'a sukayo wannan gangamin na farautar rayukan su Dad. Ajiyar zuciya kawai Jawaad keta saukewa, tausayin su Qaseem da sauran iyalan waɗanan mutane kawai yakeji, dan haka ya bada shawarar a fita dasu Dad ta ɓarauniyar hanya abar station ɗin dasu zuwa cikin prison dasu ko hakan zaisa a samu sassaucin da hankulan mutane.
Da wannan shawara ta Jawaad akai amfani, sannan D.G da kansa ya fita yayma jama'a bayani daban haƙuri akan su bari suga idan ba'a yankema su Dad hukuncin daya daceba sai su ɗauki matakin da duk sukai niyya, amma dan ALLAH yanzu su kwantar da hankulansu kodan dare.
Da ƙyar suka amince akan safiyar gobe su farka da batun shigar su Kokino kotu, kokuma su su ɗauki doka a hannunsu game dasu. Garin baiyi lafiyaba sai da aka sake baza jami'an tsaro, duk yanda su Jay sukaso kwana a gidajensu yau kam ta gagaresu, sunata kai kawo akan mutane har garin ALLAH ya waye.
_________________
Tunda na farka kallon kowa kawai nake, jinake tamkar an kwashemin ƙwaƙwalwa da zuciya an jefar gefe, kukan zuci zanyi kona zahiri? Wane kalar tunani zanyi akan wannan juyayyen al'amari ruɗaɗɗe? Iyayen dana tashi na gani ƙaddara ta juyasu sun zama ba nawa ba, waɗanda ban taɓa kawowa a tunanin hankali da ƙwaƙwalwa ba sune suka zama iyaye na gaskiya. Dad fa? Jama'a kuji wani batu tamkar a tatsuniyiyi da hikayoyin marubuta. Ashe shiyyasa nakejinsa a raina tun lokacin dana fara tozali dashi matsayin yayan innata? Shin murna ya kamata nayi shin kokuwa kuka? Baƙinciki kokuwa takaicin kasancewarsa Ubana ni jininsa? Wane hukunci ya dace dashi game da mahaifiyata da sauran al'ummar da suka cutar suka zalinta saboda son zuciya da ƙwaɗayi da burin duniya da kayan cikinta? Anya badan kalmomin bakina sunyi nauyin da zasu iya zama tuntuɓen harshe wajen aikata zunubiba da ban zazzagesu ga azzalumin uba irin nawaba kodan duniya taji tasan na tsanesa. Inama gaskiya bata fitaba na ciga da kallonsa matsayin yayan inna ba Mahaifina ba, inama ace banga wannan ranarba Mamana ta bari yayi tsafin dani nima. Inama.... Inama..... Inama.....?
Bilkisu ta faɗa a fili tana rushewa