Showing 282001 words to 285000 words out of 388641 words
basuda wata alaƙar zahiri dake a bayyane su duka huɗun kuma”.
Aliyu ne yay ƙarfin halin cewa, “To boss indai basu da alaƙar zahiri tayaya zamuyi tunanin haɗasu a kamanceceniyar laifi?”.
“Ƙyaƙyƙyawar tambaya Aliy” Jawaad ya faɗa yana fuskantarsa da ƙyau, hannayensa duka biyu ya zura cikin aljihun wandon sa ya zagayo ya sake zama a kujerarsa. suma duk komawa sukai suka zauna.
Jay ya ɗauki coffee ɗin da Hafiz ya ajiye masa yakai baki yana faɗin, “Akwai kamanceceniya mai yawa Aliy, musamman idan muka saka abubuwa da yawa da suka faru a tsakanin nan a mizani guda, babu abinda yafi ɗaukar hankalina wajen kamantasu sai maganar fyaɗen nan, dan haka zamuyi amfani da wannan damar mu canja salon bincikenmu. Fyaɗen da akaima Amina, Matar Jabeer, Nazifa, yayar Ummie, da ƴar mai aikin gidansu Nazifa daya faru kwanannan duk basu da banbanci, a tunani na hankali da yazo a zahirance zai bama mai nazari wahala wajen fahimta musamman daya kasance ba'a guri ɗaya al'amarin ya faruba, hasalima ba lokaci gudaba, idan har zamuyi aki da hankali kuma amsar ƙarshe itace ba mutum ɗaya ke aikatawa ba kenan. Da akwai aikin dana shirya dunƙule yaran suyi da, dan a jiya harma na sakasu zuwa gidana zamuyi magana sai ban koma gida akan lokaciba, to yanzu zamuyi amfani da wannan damarne, saboda su abin ya faru da wasunsu, sunsan zafi da raɗaɗin da akeji”.
Cikin farin ciki Hafiz yace, “Wannan tsarin yayi wlhy Boss, amma nima ga tawa shawaran”. Gaba ɗayansu hankalinsu suka maida ga Hafiz ɗin, ya gyara zamansa sosai yanda zai faɗi komai dalla-dalla. “Kunsan a yanzu bazai yuwu kai tsaye mu iya binciko waɗanda akaima fyaɗe irin nasu ba, fitowarma fili zaisa masu aikatawar su ɗauki mataki suma, haka bayyanar yaran kai tsaye zai dawo da hankalin masu aikatawar kansu”.
“Ƙwarai kuwa hakane Hafiz”.
“Yauwa to mizai hana mu taimakama yaran su buɗe wata ƙungiya haka ta ƙarɓar ƙorafin waɗanda akaima fyaɗen koma a wane yanayine, matanmu su zama sune masu ƙungiyar a bayyane, mukuma mu koma ta bayan fage wajen tsayawa tsayin daka ga masu shari'a su ringa yanke hukuncin daya dace cikin ƙanƙanin lokaci, na tabbata hakan zaisa mu sami dukkan damar da muke buƙata kodan sakacinma da kotuna keyi akan wannan matsalar, kunga mun jefi tsuntsu biyu da dutse guda, zamu sami abinda muke buƙata, zakuma mu taimaki yaran da ake zalinta musamman waɗanda iyayensu basu da ƙarfi akan tsaya masu bayan an cutar musu da ƴaƴansu”.
Tafama Hafiz suka shigayi dan shawarar tashi tamusu yanda suke buƙata. A take kuma suka tsara komai yanda ya kamata. Suna cikin tattaunawar su Zuhrah suka iso office ɗin kamar yanda Jay yay kirasu tunkan ya baro gida akan su samesa nan.
Ummie ce tai musu jagora har office ɗin na Jay, Sai da suka gaishesu duk cikin girmamawa kafin su basu izinin zama. Shine ya fara magana cikin dakewar nan tasa da
kowa ya sani musamman akan abinda ya shafi aiki, “Inason ku bani dukkan hankalinku nan”. A take duk suka sake nutsuwa garesa fiye ma da yanda yake buƙata.
“Ku dukanku a yanzu zaku kasance wajen aiki ɗayane, ina mai gargaɗarku da bama buƙatar wasa, daga yau zaku ajiye wani ƙawancenku gefe kuyi aiki tamkar bakusan kankuba, zaku fito a ƙungiyance domin karɓar kukan iyayen da akaima ƴaƴansu fyaɗe. Wannan itace hanya ta farko da zaku iya fahimtar dukkan abinda kukai buri. Sunan ƙungiyarku, lauyoyin da zasu taimaka muku, harma da alƙalai mun tanada, ku naku kawai sauraren duk waɗanda matsalar ta shafa. Baku kaɗai bane a ƙungiyar, akwai matan su Jabeer, dan irin matsalar data faru da ke Nazifa da sister ɗin Ummie data rasu da Amina itace irin hanyar da akabi akaima matar Jabeer fyaɗe kafin aurensu da wasu ƙawayenta biyu data sani”.
Duk kallonsa sukai cike da ɗunbin mamaki, Nazifa dake sharar hawaye tace, “Yaya kuma suma ba'a gane wanda yay musunba har yanzun?”.
Cikin tsananin takaici Jay yace, “Ba'a ganeba, hasalima daga ƙarshe a lalace shari'ar ta ƙare tunda babu wasu hujjoji da zasu tabbatar da wanda ya aikata ɗin. Abinda yasa mukai tunanin kufito a ƙungiyancan dan bazai yuwu mu iya gane waɗanda akaima irin wannan kalar fyaɗen ba saita siyasa, suma waɗanda akayima ɗin ta wasu hanyoyi wasu rashin gata ya sakasu sunyi shiru, wasu kuwa sakacin shari'a yasaka zancen wucewa tamkar ba'ayiba. Ku jami'an tsarone shiyyasa muke fatan ƙungiyar da zata fito daga ƙarƙashinku ta banbanta da sauran ƙungiyoyin, mukuma zamu tsaya a bayanku mu baku dukkan gudunmawa ta ɓangaren shari'a dan acanne ake ruguza komi da make ƙwarin gwiwar ƙungiyoyin dake faɗi tashi akan wannan matsalar. Dan haka aikinku zai kasance da manufa biyu....”
Kasancewar hakan burinsune sai duk suka amsa cike da farin ciki da zumuɗi.
A nutse Jay ya ƙarayi musu bayani suma su Aliyu suka ƙara musu da nasu.
★★★★★★★
Ring ɗin wayatane yasa na farka, na buɗe idanuna da ƙyar ina tashi zaune, saman mirror ɗinsa na hango wayar, dan haka na sauka a kan gadon ina cije baki, duk da Alhmdllh naji daɗin jikina bakamar a daren jiya ba da ɗazun da safe, ganin Ummu ce da kanta tai kirana na ɗan zaro ido waje na ɗauki wayar da har ta katse, ina ƙoƙarin kiranta kiran ya ƙara shigowa, cikin ladabi na ɗaga tamkar ina a gabanta na gaisheta Ina hawaye.
Daga can gimbiya tai murmushi tana gyara kishingiɗar da tayi jikin mai martaba, “Haba ɗiyata, miye kuma abin kukan, baki da lafiyane naji muryarki haka? Ayi haƙuri to, shiyyasa naƙi kiranki ai sai yau, duk kuna lafiya ko?”. Kaina na ɗaga tamkar ina gabanta nace, “Lafiya lau Ummu, barci na tashi ne, sai kaina dake ciwo kaɗan, inasu Safah? Tun jiya naketa zuba idon zuwansu amma shiru”. “kisha magani to, ALLAH ya ƙara sauƙi, Karki damu zasuzo insha ALLAHU, yanzuma na kirakine akan zuwansu Anuwar anjima kaɗan dan zasu wuce gobe idan ALLAH ya kaimu”. Cikin jin daɗi na share hawayena Ina faɗin, “ALLAH ya kawosu lafiya Ummu, to suzonan su kwana dan ALLAH”. “A'a babu batun kwana ɗiyata, ai ba'a kwana gidan amarya, zasuzo dai zuwa dare su dawo, ki tabbatar mijinki da Anuwar sun haɗu dan munyi waya dashi ɗazun yace baya gida”. “Insha ALLAHU Ummu zanyi ƙoƙari”. “To shikenan, sai anjima na kiraki kinji, kidage da shiga ruwan zafi karkiyi son jiki”. Kunyace ta kamani, a raina ina tunanin kodai shine ya sanar mata..... “Kina jina” magarta ta maidoni hankalina. “Eh Ummu”. “Bawai ina nufin ki shiga ruwan zafi idan babu abinda ya faru ba, tunda nasan kina fashin salla, bakuma saina buɗe miki abinda nake nufiba, ayita haƙuri danshi zaman aure haƙurine, allah yay miki albarka”. Hawayena na share nace, “Amin Ummu nagode”.
Rashin ganinsa a ɗakin ya sakani jin daɗi bayan na ajiye wayar, cikin dauriya na gyara ɗakin tsaf, na fito ɗaukar kayan shara naga Nabeelah, sosai naji daɗin ganin nata, itace tace nabar sharar ita zatayi, ban musa mataba na shiga nai wanka da sake gasa jikina sosai, hakan ba karamin nutsuwa ya ƙaraminba. Koda na fito saina koma ɗakina nai shiri, ina cikin shirin Nabeel
ah ta kawomin abinci, dan tunda taga yanayina ta tambayeni lafiya nace mata banida lafiya duk sai naga jikinta yayi sanyi. Yunwa nakeji sosai shiyyasa na zauna naci abincin. ɗakinsa na sake komawa ɗaukar maganin dan naji daɗinsa, ina buɗe box ɗinne Nabeelah ta shigo da sallama da waya a hannu, a kunne kawai ta sakamin batare da tayi maganaba. Ɗagowa nai zan tambayeta wanene? Muryarsa ta shiga dodon kunnena.
Saida na lumshe idanu na buɗe sannan na amsa masa sallamar tasa,
“Amarsu kin tashi?”. Ya faɗa cikin zolaya.
Jinai tamkar na nutse dan kunya, dukda bana gabansa, nai saurin saka hannuna na rufe fuskata ina murmushi da faɗin, “Nidai ALLAH a'a”. Ina jiyo sautin murmushinsa shima, yace, “Nidai nasan amaryata amaryace ƴar gaske, yaya jikin naki?”. Batare dana buɗe fuskarba nace, “Da sauƙi”. “Alhmdllh ai haka akeso, kinci abinci ko?”.
“Uhm naci”.
“Tom kisha magani ki sake kwanciya ki huta karki biyema surutun Nabeelah, Gimbiya ta kirani akan baƙi zasuzo kuyi sallama, zanyi ƙoƙari na dawo da wuri nima insha ALLAH. ga Sadiq nan zai kawo cefane Nabeelah tayi girki”.
“ALLAH ya dawo dakai lafiya to”.
“To nagode, amma mizan ɗan samune Noor-Jahan?”. A marairaice nace, “Mi kake so?”. yace, “Komai aka bani inaso mana”. Duk da ina tsananin jin kunya nace, “To rufe idonka”. “Na rufe ruf Matar Jay”. Yay maganar cikin sanyin murya kamar ba shiba. da saurin na yanke kiran ina dariya, ina gani ya sake kira naƙi ɗagawa, saima maganin na ɗauka na fita falo wajen Nabeelah.
Babu jimawa da zamanmu Sadiq ya kawo cefanan da yace, karon farko da zan fara girki a gidana dukda Nabeelah tace na barmata zatayi kar yazo ya gani yay faɗa, ban sauraretaba dan nima inason ƙarfafa jikina ai. Tare mukai girkin cikin nutsuwa da salon da Umm-Anum ta sake koyar dani, dan danan gidan ya kaure da ƙamshi, muka kammala tsaf muka gyara kitchen ɗin sannan.
Kusan ƙarfe uku na rana saiga su Anum, Anuwar, Abdul-Rahman, Abdur-raheem, Ameen, Meenal, Amaturrahman, Amatullah. Tuni muka rungume juna dasu Amaturrahman kamar mun shekara da rabuwa, su dai su Abdur-raheem dariya suketa mana.............✍
Inacan ina muku dogon page, kunanan kuna ƙwalama sunana kira😣😫, ku baku ganeba ne, duk randa nai posting da wuri to nayi typing ɗin dare ne ya kwana, idan kuma ban samu damar yiba dole sai randa zan tura nakeyi, ga aikin gida ga uzurorin rayuwa🤦🏻😓, gashi yanzu anzo gangara typing ɗin na buƙatar nutsuwata sosai, amma idan naga wani Comments ɗin har mamakin mai rubutashi nakeyi wlhy. ALLAH dai ya dafa mana kawai, duk ƙoƙarinka baka isa yima kowa yanda ya dace ba, ALLAH kaɗai ka iyama ɗan adam da halinsa wlhy😂🚶🏻🚴🏼.
ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.
HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO
MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.
MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300
Sai kunzo😍😍😍😘.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[1/6, 9:21 PM] HASNA✍🏻: Bilyn Abdull 📚:
Page 44
Auntyn Alfindiki saƙonki ya iso gareni, alkairin ALLAH ya kai gareki a duk duniyar da kike, kema ALLAH ya tabbatar da addu'arnan da kikaimin a gareki, yanda kika soni domin ALLAH, kema ina roƙon ALLAH ya soki haka dear.
Godiya irin trillions dinan 😍😍😍😘😘😘😘
....................Duk yanda zan musalta muku kalar daɗin da naji na zuwansu bazaku fahimtaba, irina da suke gararanbar rayuwane kawai zasu fahimci kalar jin daɗin da mukanji idan mutane irin haka da baka haɗa komai da suba suna nuna maka soyayyar da naka dangin basa nuna maka irinta, abinda ya ƙarama farin cikin nawa armashi kuwa ganin harda matasan samarin ƴaƴan sarki masu zamani da lokacinsu a cikin gidana, kuma sun sake dani tamkar jininsu kona rayu a cikinsu ne. Abdul-raheem ne dai baida yawan fara'a da magana, amma shima bashi da wulaƙanci. Abincin kuma da aka jera musu zama sukai sukaci sosai har ana santi, Abdur-Rahaman harda cewa dama yunwarsa ya tara dan yazo yaci girkin amarya. Amaturrahman ta ɗauki filo ta saka masa waiji wai santi yakeyi. Nan take faɗa ya kaure tsakaninsu, ni wlhy dariyama suka bani, idan kana tare da triple ɗin Ummu dolene drama ɗinsu take baka dariya, shi Abdul-raheem baya magana, amma idan ya mulmulo baƙar magana ɗaya sai tayi kamar ta kar mutum dan takaici, shikuma Abdur-raham babu haƙuri saiya rama, Amaturrahman kuma zuga. Gefe kuma Ameenullah da Meenal ma cashewa akeyi, hakama Anum da Anuwar. Wannan caskalen nasu ne ya sake ƙara armashin hirar tamu da nishaɗi sosai. Kiran sallar la'asar ya saka samarin fita salla, mukuma mukayi a gida.
★★★★★★
Ana idar da sallar la'asar Jawaad ya baro station, kai tsaye anguwar su Hudah ya nufa, sadiq yay fakin dai-dai ƙofar gidansu Amina inda Jay ya bashi umarnin tsayawa. Jay daketa rubuce-rubuce batare da ya ɗagoba yace, “Sadiq yimin sallama a gidan nan”. “To Oga” Sadiq ya faɗa yana buɗe motar ya fita. Ƙofar gidan su Amina ya ƙwanƙwasa tare da yin sallama. Kusan mintuna uku Aminar ta fito sanye da hijjab tana amsa masa. “Assalamu alikum. Malam lafiya kuwa?”. Amsa mata sallamar Sadiq yayi, sannan ya nuna motar, “Dama oga ne yace aimasa sallama”. Cikin rashin fahimta Amina tace, “Oga kuma? Wanene kuma oga?”. Batajira amsar Sadiq ba ta fito zuwa motar, knocking glass ɗin tayi har sau uku, Jawaad da har yanzun hankalinsa na akan rubuce-rubucensa ya saka hannu ya sauke glass ɗin batare da ya ɗagoba. Amina taɗan zaro ido da ɗora hannunta saman baki, “Oh wlhy bansan kai bane Yaya Jawaad, ina yini?”. Ɗagowa yay ya kalleta da amsa mata, duk da fuskar dai babu walwala bai ɗaureta tamauba, “Mama na nan?”. Kanta ta jinjina masa, “Eh tana nan ka shigo”. “Okey” ya faɗa yana maida kansa ga abinda yakeyi. Juyawa tayi ciki ita kuma domin sanarma maman.
Sai da Jay yaja kusan mintuna huɗu sannan Sadiq ya buɗe masa motar ya fito. yana fitowa Amina na leƙowa dan sunji shiru, itace tai masa iso har cikin gidan, mama na zaune daga ƙofar ɗaki gefenta da tabarmar da aka shinfiɗa masa.
“Lale marhabin, yau angone a gidanmu?”. Ɗan murmushi Jawaad yay ya zauna a tabarmar yana faɗin, “Ayi haƙuri Mama bamuzo mun muki ya gajiya ba”. “A'a nikam ku riƙe ban gajiyar ku, dan an mana babban ya gajiya, ɗawainiya kan ɗawainiya Jawaad baka gajiya? Anyi hidimar azumi akayi ta salla shekaranjiya kuma saiga saƙo, ALLAH ya saka da alkairi ya jiƙan mahaifa kaji, ALLAH ya azurtaku da zuri'a tagari mai albarka”. Kan Jay a ƙasa yana ɗan murmushi yace, ”Amin mama”. Amina ta ajiye masa kunun ayar da sukayi ta sake gaishesa da tambayar Bilkisu.
Zama Jawaad ya gyara ya fuskanci mama sosai, “Mama wani taimako nazo kimin Please”. “Inajinka Jawaad, ka faɗa kanka tsaye, inhar baifi ƙarfinaba zan maka da izinin ALLAH”. “To nagode sosai Mama, nasan tun dawowar su Hudah ƙasarnan kike aiki a gidansu bayan rasuwar mijinki, sannan kaf anguwarnan da ƴan gidan nan suke mu'amularsu kawai, a zaman da kikai dasu nasan dolene zaki san abubuwa masu yawa dangane dasu, musanman ma akan duk wani ma'aikaci da yake aiki a gidan”. “Wannan gaskiyane Jawaad, dan mijina kansa kafin ya kwanta jiyyar ajali
Alhaji Ali ne ya koma masa kamar amini”. “Alhmdllh, inason sanin maigadin nan nasu ke da shi waye ya riga wani fara aiki?”. “Ya rigani farawa, danshi tunma ana gina gidan shine maigadinsa har aka gama suka tare”. “Okey, yanada mata ne?”. “Tunda nake da shi ban taɓa ganin iyalinsa ba, sannan ban taɓa jin ance yau ya tafi ganin gidaba, dan har tambayarsa nama taɓayi game da hakan lokacin inason bada wasu kaya sai nake tuntuɓarsa ko yanada iyali na haɗasu ya kai musu?. Sai cayaymin ai suna gida, daga wannan amsar ya shiriritar da zancenma gaba ɗaya. Nikuma ban sake tuntuɓarsa game da suba gaskiya”. Shiru Jawaad yayi yana nazarin maganganun Mama, kafin yaɗan huro iska da gyara zamansa. “Amma mama kin taɓa ganin wani abu dangane dashi na rashin gaskiya haka”. “Gaskiya ban taɓa ganiba, saboda shifa mutumne ma da baida yawan magana sam, kafin kaga firarsa da mutum tai tsawo akan daɗe, kodan ba abokina hirar nawa bane oho”. “Kukun gidanfa, yakai shekara nawa shikuma yana aiki dasu?”. “Shima tunda suka tare yake, a gidan na sanshi”. “Mai bayin fulawa fa?”. “Eto shine dai kafin shi kusan mutum uku sukai aiki”. “Miyasa suka bari to? Ko ba'a baku albashin daya dace ne?”. “Ai Jawaad idan ta yawan albashine babu wani mai aiki da zaiso barin aiki gidan Alhaji Ali, zan iya rantse maka a cikin dubu irinsa dake fita haƙƙin ma'aikacin gidansa da albashi mai tsoka sai an tona, sannan duk abinda masu gida zasuci kaima mai aiki zakaci, wulaƙanci da rashin tarbiyyar ƴaƴansa ne kawai matsalar ma'aikatan gidan, amma masu bayin fulawarnan da suka taɓa ajiye aiki wlhy bansan dalilinsu ba, dan daina ganinsu kawai mukai mudai koma sallama basuyi damuba”. “To amma baƙwa zaman mutuncine dasu har zasu ajiye aiki baku saniba?”. “Sosai ake zaman mutunci wlhy, dan wanda na tararma a gidan idan kaga yanda ya ɗaukeni tamkar uwa, amma daga zuwa ganin gida bamu sake ganinsaba sai wani mukaga an kawo”. “Zan iya sanin garinsu su duka biyun?”. “To gaskiya anan gizo ke saƙar dan na manta, amma zanyi ƙoƙari na tinano insha ALLAH”. “ALLAH ya bada iko to, drivern su fa?”. “Shima basu taɓa canjawaba”. “Kafin ku wasu sun taɓa musu aiki ne?”. “Akwai ƴammata biyu da suka fara musu aiki kafin mai gidana ya rasu mu fara”. “Miyasa suka bari? Kodan an sameku?”. “Wannan bansaniba kam Jawaad, nidai kawai nasan kafinmu wasu sunyi musu aiki, amma ai nasan kaima kasan duk waɗanan abubuwan tunda kana zuwa gidan”. Murmushi Jawaad yayi, “Sanin dazan musu bazai kai na wanda yake rayuwa dasu yini da kwana ba, Mama inason naji wani abu dangane da fyaɗen Amina, tana ina?”. Mama tai ɗan murmushi, “Oh ni, yanzunan Bilkisu bazata haƙura da maganarnanba? Abinda ya faru ya riga ya faru ai sai haƙuri kuma”. “Karki