Showing 261001 words to 264000 words out of 388641 words
sanyaye yake, tunani da fargaba duk sun cika zuciyata, yau ni Bilkisu nice za'a ɗauka akai gidan boss matsayin matarsa ta aure, aure ba yawo ba, idan naje shike nan natafi din din din, duk da nasan ba sonsa nakeba, shima kuma bason nawa ya keba na ɗaura ɗammarar masa biyyayya insha ALLAH, zanyi haƙuri tamkar yanda kowa ke faɗamin zaman aure haƙurine, zanyi biyayya a garesa matsayinsa na mijina shugabana, zanyi aiki da dukkan dabarun Umm-Anum da gambiya suka ɗorani akai domin samun zaman lafiya a gidana koda ace bazai soni ba. tausayinsa nakeji har cikin raina yanzun, dan a daren jiya munyi zama na musamman da Ummu inda muka tattauna game da kamanninsa da Anuwar harma da Umm-Anum ta abubuwa da dama. Ta tabbatar min nice ya dace nai wannan aikin na bincikar abinda ya shafesa ko tanan zasu iya fahimtar idan akwai alaƙar da duk muke zargi dan kamannin sun wuce kama akwai dangantakar jini dole, bansan komai na abinda ya shafi family nasa ba, sai ɗan abinda ba'a rasaba shima iyakarsa daga wajen su Mom ne da da rashin jituwa tsakaninsa da Yah Qaseem, amma a raina nima tunda muka haɗu da Umm-Anum nakeji abubuwa da dama nazomin a rai game da shi......... Da wannan tunane-tunanen na tsaftace jikina na fito, kasancewar ba salla zanyiba zaman min kwalliya akayi.
Tun ina jiyo hayaniyar ƙawayena dake ɗakin su Amaturrahman suna shiryawa har naji tsit, alamar dai sun fice dan zuwa yanzu har anyi sallar isha'i. Basan yaya zan musalta muku irin ƙyawun da nayiba yauma, amma na bama kowa damar ya hasasoni cikin zuciyarsa, kwalliyata ta yau ta kasance harda alƙyabar da Mommah ta bani matsayin ƙyautarta, basai an faɗaba, a gani da ido kaɗai ya isa amsa ga mai kallo cewar an sayeta da kuɗaɗe masu nauyi da darajar gaske. Suna cikin gyaramin alƙyabbar da santin ƙyawun da nayi aunty Samha ta shigo.
“Wow, masha ALLAH amaryar ƙamshi” ta faɗa tana rungumeni, ta ɗagoni tana kallona da cigaba da faɗin, “Wannan ai saiki rikita angon yace an fasa dinner ɗin”. Dariya waɗanda sukaimin kwalliyar sukayi, ni dai kaina a ƙasa ban yarda na kalleta bama dan tasa naji kunya, gashi kukane keta ƙoƙarin tasomin ina dannewa. Itace ta kama hannuna muka fice, ganin ba'a kaini wajen Ummu ba sai nayi tunanin za'a sake dawo dani nan kenan, ƙilama sai gobe idan ALLAH ya kaimu. A take naji farin ciki ya wani lulluɓeni. Ko ina ƙwanyar yake da haske a masarauta shiyyasa koda muka fito dukda kaina a ƙasa yake ina kallon inda muka nufa.
Mun tsaya dai-dai motar da na hango Oga Jabeer jingine yana waya tun fitowarmu, yana sanye da shadda ƴar ubansu ruwan madara. Yana ganin mun ƙaraso ya ajiye wayar yana murmushi da faɗin, “Aunty Samha aini da har ina shirin bin bayanku, dan naga baƙwa son bamu amaryarnan kamar”.
Murmushi tayi mai sauti tana gyaramin hular alƙyabar, “To gaskiya badan munasoba zamu baku, dan bamu gaji da ɗiyarmu ba, amma yaya muka iya, wannan shine girman”. Oga Jabeer na ƴar dariya ya buɗe ƙofar motar da cewa, “Aure yaƙin mata”. Tace, “Har mazan ma”.
Daddaɗan ƙamshin turarensa da na sani daine ya fara tarbata da sallama, na shaƙa na lumshe idanu ina ƙoƙarin dai-daita bugun zuciyata da kalato yawun da zan jiƙa maƙoshina da ya bushe, sai da na zauna da ƙyau Mah-mah ta gyaramin alƙyabar sannan na tsinkayi muryarsa yana gaisheta cike da mutun tawa, sai da suka gama gaisuwar s
annan Oga Jabeer ya rufe motar ya shigo shima, itama motar da zasu tafi a ciki ta nufa ta shiga.
“Ina yini?”. Na faɗa a hankali har banyi zaton zaima jini ba. Shiru banji ya amsaba, kuma tabbas inaji a jikina idonsa a kaina suke, dan ina jinsu har cikin ɓargona. kaɗan juya na kalli sashen da yake dan in tabbatar da bai jinin ba kokuwa ƴan wulaƙancinne a kusa.....
Ina ɗagowa idanuna na shigewa cikin nasa, saurin maida kaina ƙasa nai ina ɗan ƙunƙuni a cikin raina batare da nasan bakina naɗan motsawaba ashe, ‘mutum babu abinda ya iya sai kallo, har sai an hango maka muni’.
Jawaad dake kallon yanda bakinta dake ta shining na ɗan lipstick ɗin da aka sanya mata ya lumshe idanu a hankali yana sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya, maida kansa yay jikin sit ya kwantar yana maijin takaicin yarda da yay da zuwan wannan dinner ɗin banzar, yanzufa kowa sai yaga wannan ƙyawun da tai ko?. Ware idanunsa ya sakeyi a kanta yana binta da wani irin sassanyar kallo, gaba ɗaya ƙamshin turarenta ya saukarma gaɓɓansa da kasala.........
“Ehhgy egeehhmm!”. Jabeer yay gyaran murya. Haɗe fuska jay yayi ya balla masa harara tare da ɗauke kansa ya maida gefe bai dai ce komaiba. Jabeer ya haɗiye dariyar dake cinsa daƙyar sannan ya tada motar suka fice.
Shiru motar tayi bakajin motsin komai sai na ac da ƙamshin turarukanmu, tunda na gaida Oga Jabeer nima ban sake ko ɗaga kai na kalli inda sukeba, dodon nawa kam tun gaisuwarsa da aunty Samha ban sakejin ya firta komai ba shima, anata kiran wayarsama yayi kunnen uwar shegu tamkar ba yaji ana kiran. Mintuna ƙalilan muka iso wajen taron, inda muka taras da abokansa dasu Ummie tsaitsaye alamar isowarmu suke jira.
Jabeer da yay fakin ya juyo ya kalli Jay. “ku zama cikin shiri boss, bara na musu magana”. Kai kawai ya ɗaga masa, shi kuma ya fice. Kusan sakanni ashirin da fitar Oga Jabeer babu wanda ya motsa a cikinmu daga ni har shi, inata ɗan juya zoben yatsana ne dan gaba ɗaya a takure nakejin zaman namu kusa da juna.
“Bana son rawa” na tsinkayi muryarsa ƙasa-ƙasa saitin kunnena, da sauri na juya garesa dan a bazata maganar tazomin. A karo na biyu muka sake haɗa ido, sai dai yanzun duk yanda naso janye nawa kamar ɗazun hakan ya gagara, kallo yakemin irin na tsakkiyar idonnan tamkar zai haɗiyeni dasu, bazan iya jurewa ba, amma na kasa janyewa dan tamkar yamin ɗaurin goro ne da mayun idanun nasa da a yau suke farare tas babu sirkin ja alamar dai baya tattare da ɓacin rai. Da ƙyar na samu nai ƙoƙarin yin ƙasa da kaina zuciyata na wani tsitstsinkewa tare da jinin jikina. Amma a bazata saijin tattausan hannunsa nai ya taro haɓata ya sake ɗago fuskar, tuni zuciyata ta sake wani zallo tamjar zata faso ƙirji ta fito, Farfar na farayi da idanuna da suka cika taf da ƙwalla lokacin da ya matso da fuskarsa daf da tawa har munajin saukar numfashin juna, lumshe idanun kawai nayi ganin bani da wata mafita kuma, ya kawo bakinsa daf da nawa.
Yanda jikina ke tsuma zai tabbatar maka a matsanancin tsoro nake da yanayin, tsigar jikina duk ta miƙe.
Jay dake kallon yanda bily ta rikice ya saki lallausan murmushi tare da goga hancinsa kan nata, murya can ƙasan maƙoshi yace, “Matsoraciya kawai, darajar matata tafi ƙarfin nayi kissing ɗinta anan wajen yariya, hakan bazai taɓa yuwuba sai a fadata insha ALLAH. badan girman alƙawari ba da bazan taɓa bari ki shiga wajen nanba, ni kaɗai yafi cancanta na shaida wannan ƙyawu naki a cikin gidana. Ina ƙara maimaita miki bana son rawa”. Ya ƙare maganar da ɗaura yatsansa babba saman lips ɗina ya kwashe ɗan lipstick ɗin da aka samin.
Wata irin kunya naji ta lulluɓeni mai haɗe da tsoro da ɗan haushin gogen lipstick da yayi, nai ƙasa da kaina ina ɗan kumbura da faɗin, “Toni nama iya rawan ne ma.........”
Saukar ɗalli kawai naji a saman laɓɓana mai azabar zafin, na ɗago idanuna da suka cika da ƙwalla a kansa. sassanyan murmushin mugunta ya sakarmin har dimples ɗinsa duka biyu na loɓawa, ya ɗage kafaɗunsa yana ɗage gira ɗaya da taɓe baki alamar ni naja.
Kafin wani ya ƙara magana a ciki
nmu akai knocking glass ɗin motar, sauke gilas ɗin yayi, oga Hafiz ne yay masa magana akan mu fito. Banji amsar da ya bashiba, baice min komaiba nima ya fice, ina ƙoƙarin gyara alƙyabata nima na fita naji an buɗe ƙofar ɓangarena, na ɗago dan ganin wanene muka haɗa ido ashe shine ya zagayo tanan, hannunsa na dama ya miƙomin yana wani ɓata fuska da kallona ƙasa-ƙasa, a kunyace na ɗora nawa ya taimakamin na fita nima, hannunsa na haggu yasa yaja hular alƙyabar ya sake rufemin fuska da ƙyau.
Ina jiyo wani cikin baƙin abokansa na faɗin, “Sarakin kishi muma ba kalla zamuyiba ai bar wahalar rurrufe mata fuska”. banji ya bashi amsaba sai dariyar da sauran sukayi. Inajin irin zafin da nakeji a duk lokacin da ya raɓu jikina, sai dai yau kaɗan nakejinsa cikin amincin ALLAH, dan haka nai jarumtar daurewa tamkar banajin komai ina addu'a cikin raina har muka shige abokansa da ƙawayena na biye damu a baya cikin ƙyaƙyƙyawan tsari babu wata hayaniya.
Muna shiga da aunty Batool dake ƙofar tsaye tana jiranmu muka fara cin karo, ta shiga feso mana wani farin abu mai ƙyalƙyali da ƙamshi, masu hotuna kuwa nata ƙyalla mu.
Sauran mutanen duk suka miƙe idanun kowa na kan amarya da ango dake cike da birgewa, yayinda ƴanmatan family ɗin su Jay sukejin zafi a zukatansu dajin takaicin bilkisu da tazo daga sama tai musu wuf da shi, sai irinsu Rose da kallo ɗaya zakai musu ka hango tsagwaron kishi da tsanar bilkisun a cikin idanunsu. MC kuwa na zubama amarya da ango kirari. yayinda Ali jita ya sake gyara maƙogwaron nan nasa na zinari ya fara baitocin girma ga amaryar ƙamshi bilkisu mai gadon zinari cikin waƙarsa mai taken Bilkisu gimbiya.
(Bara naɗan raira muku kaɗan saura wani yace ban iyaba😣😚. lol)
🎸🎸🎶🎶BILKEESU zan faɗa dan ALLAH, mata ku bani dama duka.
bilkisu gimbiya.
BILKEESU mai gadon zinari waƙarki ta fita haka.🎸🎶🎶
BILKEESU sai gani sai nuni, kowa ya tabbata duka.🎸🎸🎸🎺🎺
BILKEESU gimbiya an baki, mata su dakata duka.🎸🎸🎺
BILKEESU sanya alƙyabar ki kaya mayalwata haka.🎸
Bilkisu gimbiya.
BILKEESU za'a yiwa fada, ai mata fifita haka. 🎸
Jita kaja muje nai waƙar Bilkisu masu girma haka.🎸
Mata ku rausaya Ali jita nine na baku dama haka🎸🎶🎶
Komai yanada rana a gane dama tanada dama haka, Bilkisu gimbiya.
Giwa ki rausaya BILKEESU ALLAH ya ƙara baiwa haka.🎸🎷🎷
Komai yaje ya dawo BILKEESU ku za'a tabbatarwa haka🎸
Ganga irin ta girma a miki waccan a mata garwa haka.🎸
BILKEESU za'a baiwa Number komai daren daɗewa duka
Bilkisu gimbiya
BILKEESU sannu mata irin na zamanin ɗebe kewa duka.🎸🎸
Kinsha aradu kinsha yasin, kin samu arziƙi duka.🎸🎷🎸🎷
Kin tsallakema tarkon maƙiya, ga ɗan abin biki haka.🎸
Kinzam sarauniya a cikin mata bar munafuka haka.
Bilkisu gimbiya🎸
Ga zamani da daɗi wannan al'amarinkine duka🎸🎸🎸
Tsarki na zuciya bilkisu ya baki ɗaukaka haka.
Kinsa kara a hanya BILKEESU wazata tsallakane🎸
Komai kina tunani Bilkisu baƙya abu daka haka🎸
Bilkisu gimbiya
Ga ilimi da halin girma, ALLAH ya ɗaukaka haka.........🎸🎷🎸🎷🎸🎺🎺🎺🎺
(Kunema sauran kuji na gaji😂😜)
“Mawaƙin nan dolene yaci ƙyautar mota”. Oga Aliyu dake bayanmu shida matarsa ya faɗa yana ƴar dariya.
Murmushi naga boss yayi a hankali lokacin da yake kama kafaɗuna yana zaunar da ni a ɗaya daga kujerar guda biyu da aka tanada danmu. Ni kaina waƙar tamin daɗi sosai, hakan ya sakani sakin murmushi da banyi niyyaba. Jay yaɗan lumshe idanu ya sake buɗewa a kanta sannan ya zauna a nashi mazaunin shima.
Babu ɓata lokaci aka fara gudanar da abinda ya tara mutane, an buɗe taro da addu'a kafin ai kiran Ummie tazo ta bada tarihin amarya a taƙaice, Hafiz ma ya bada tarihin ango tare da ɗorawa da shaƙiyancin randa suka fara gane Jawaad ya kamu da son amaryar tasa. Yanda yake faɗar wajen dole ya saka mutane dariya, masu baƙin ciki kuwa suka shiga zuba tsaki suna haɗiyar zuciya. Bily kanta sai da ta murmusa dukda tasan ba haka bane tunda ita
dai bai taɓa ce mata yana son nata ba, ɗagowa tai da nufin satar kallonsa sai suka haɗa ido, dan shima kallonta yake ƙasa-ƙasa idanu a narke.
Cike da salo ya wani ɗagemin girarsa ɗaya, maida kaina nai ƙasa zuciyata na motsawa. Ban sake gigin kallon sashen da yakeba nima na maida hankalina ga kallon mawaƙa da suketa baje fasaharsu cikin daɗaɗan waƙoƙi da duk an raira baitocinsune da sunayenmu. Umar m shariff, Ado gwanja, Nura m inuwa, Naziru Ahmad, Hamisu breaker, Isa ayagi, Abdul D one, kai abunfa ba'a magana, ƴan uwa da ƙawaye da abokan ango nata casar rawa, duk yanda mc keta magiya da roƙon amarya da ango su fito filin rawa ya hanani ko motsi, duk wanda ke buƙatar mana liƙi sai daifa yazo nan inda muke zaune ya liƙa mana ɗin, amma ko sau ɗaya bamu shiga filin rawarba.
Lokacin da Anum da Nabeelah suka hawo domin yima su Jay liƙi ba ƙaramin faɗuwa gabansa yayiba, itama ɗin dai sai da ta ɗora hannunta a ƙirji alamar gaban nata faɗuwar ya keyi, dama tun sanda su bilkisu suka shigo saida gabanta ya faɗi, jikinta a sanyaye ta liƙa masa kuɗin shi da bilyn suka sauka ko jin surutun da Nabeelah keyi bataiba. Duk bilkisu na kula da yanayin da boss da Anum ɗin suka shiga, dan harta sauka yana binta da kallone.
Tun ɗazun nake wuwwula idanu ko zanga Yah Anuwar, haka kawai nakeji a raina bana son su haɗu da boss yanzu anan, to bammaga su Abdur-raheem bama. Da hannu na yafito Anum, ta taso zuwa gareni. Cikin magana ƙasa-ƙasa nace, “Ina Yah Anuwar?”. Tace, “Tab aishi bayason bidi'a, da wahala idan zaizo wajen nan, amma bakiga yanda mijinki ke kama da Yah Anuwar ba? Nifa dana kallesa gabana sai ya faɗi wlhy bilkisu”. Murmushi na mata da cewa, “Karki damu zamuyi magana amma ba anan ba”. Kanta ta ɗagamin ta koma wajen zamanta. Ina kallon irin kallon tuhumar da boss kemin nai kamar ban ganiba, dan rashin zuwar Anuwat ɗin yasa naji hankalina ya kwanta.
An buƙaci mu fito domin yanka cake. Ganin bai motsaba nima nai zamana, Ina jiyo fitar guntun tsakinsa alamar bayason yi, ni kaina bason nakeba, dan duk a takure nake matuƙa. Sai da Jabeer yazo yayta roƙonsa da ƙyar ya amince muka miƙe zuwa gaban cake ɗin da yay masifar ƙyau.
Mun yanka cake tamkar yanda tsarin yake, ni na fara cira ɗan guntu da zan saka masa a baki cike da jin matsananciyar kunya, dan da ƙyar na iya control ɗin tsumar da jikina keyi nakai hannuna bakinsa, hannun nawa ya riƙe shima muka saka masa gaba ɗaya wanda na ciroɗin kasancewar ɗan ƙaramine a baki. Ina ƙoƙarin janye hannun ya maidashi cikin bakinsa ya tsotse yatsun biyu dana ɗauki cake ɗin dasu suka ɗan ɓaci kaɗan. tafi hall ɗin ya ɗauka. Jinai tamkar na nutse dan kunya.
Shi kam Maimakon ya ciro ya bani kamar yanda nai masa sai ya lakato ya samin a saman hanci kawai dan wulaƙanci, ban gama fita daga takaicin salon nasaba naji saukar numfashinsa kan fuskata, kafin na sami damar magana ya lashe wanda ya lakatamin ɗin da bakinsa. tafin yanzun kam har yafi na ɗazu, dan yanzu harda waƙar Ali jita aka sake saki ta Bilkisu gimbiya. Ƙasa nai niyyar duƙewa dan kunya yay azamar riƙoni jikinsa, sai kawai na ɗora kaina saman ƙirjinsa ina sakin murmushin jin kunya, shima ya ɗaura hannunsa ɗaya saman bayana yana ɗan bubbugawa.
Da ƙyar mc ya samu hayaniyar ta lafa, zamu koma wajen zamanmu aka dakatar damu. Jabeer ya fara bayani kamar haka....
“To jama'a kowa sai ya buɗe idanu domin dai zamuga wasan manya ne, kunsan daga amaryar har angon jarumaine a filin daga”. Ya nuna bindigu guda biyu dake saman wani table duk an buɗesu, “Kuna dai ganin bindiga guda biyu ajiye ko? To munason ango da amarya su