Showing 78001 words to 81000 words out of 388641 words
gidansa.
Ya tuna maganar kakansa daya taɓa faɗa masa lokacin aurensa da Shahudah.
*_“Jawaad naso ka auri irin wadda rayuwarka keda buƙata, amma tunda haka ALLAH ya tsara muna maka fatan alkairi, sai dai ka sanifa shi ubu mai ƙyau abin san kowane, sai dai ba kowanne ƙyaƙyƙyawa bane kake samunsa ciki da waje mai amfani da amfanarwa, dakamar wuya asamu cikakken farin ciki tattare dashi inhar akwai tangarɗa tun fil azal, wani lokacin daga yanayin ginin abunne a zuciya da kuma rayuwa, wani lokacin kuma tun usul akwai rashin nagarta musamman idan anci karo da sakacin iyaye wajen rashin yin ginin da addini ya koyar, bazaka fahimci komai daga zantukana ba Jawaad sai nan gaba kaɗan, irin waɗannan yaran abinda zaku haifane abin tausayi dakai kanka da za'a jefa cikin garari ba suba, amma dai ALLAH ya sanya albarka da alkairi a ciki, ALLAH yasa muce gamma da akayi”._*
Nannauyan numfashi Jawaad ya sauke yana rumtse idanu da ƙarfi, wato irin waɗannan tashin hankalin da jahilcin ne kakansa ya hango masa tattare da auren Shahudah, wanda shi a baya tunaninsa bai kawo kan hakaba, kawai yafi kallon rashin isashshiyar tarbiyyarta zai tsayane ga taɓara kawai, kuma zai iya canjata da wuri tunda tana sonsa.
A irin kima da nagartar Dad ɗinsu bai ƙyautu ace zuri'arsa ce a wannan yanayin yahudancinba da sunan wai ƴancin kai, shikenan dan ƙaddara ta shigar dakai cikin wata rayuwar da ba takaba saika mantar da kanka da zuri'arka tushensu da addininsu da al'adunsu?, ansan a shekarun da suka ɗauka cikinsu dolene a samu raunin al'adunsu, dan yau da gobe ta wuce wasa, ballema ba zuwa gidan sukeba su, to amma bai dace a duk inda ka tsinci kanka ya zam ka manta da addininka da koyarwarsa ba, dan ako ina kake ALLAH ya wajabta maka yinsa da kuma neman ilimin sani a kansa.
Lallai yana ganin anzo gaɓar da zai tunatar da Dad da Mummy abinda suka mantan kokuma son zuciya ya sakasu maidashi baya saboda son ƴaƴa ko sakacinsu.
Haka Jawaad yayta tunani bai fargaba sai kiran sallar asubahi yaji, nannauyan numfashi ya sauke tare da kallon agogon dake a tsintsiyar hannunsa.
Ya ɗan matse idanunsa da sukai masa nauyin buƙatar barci, da ƙyar ya yunƙura ya tashi zaune sosai, ya buɗe motar ya fita ya nufi ciki.
Ji yake tamkar yabar gidannan gaba ɗaya yau ɗinnan.
_________________________
BILKEESU
_________________________
Sosai na samu nutsuwar zuciyar zama dasu Ummie, dama can ni a rayuwata inahar zaka nunamin ni mutumce kamar kowa mai daraja tuni nake sakar maka jiki, to yanda su Ummie suka amsheni sai hakan ya dasamin ƙaunarsu.
Nazifa ce dai har yanzu muna sama-sama ne, niko halinta bai dameniba ko kusa, abinda ya kawoni ma nafi son maida hankali kansa ba matsalar wani ba.
Dan na tabbata a halin yanzu wannan ilimin dazan nutsu na samune babbar katangata kuma gatana koda anan gaba idan ALLAH yasa muna a cikin masu tsahon rai.
Su dukansu babu mugunta suke nunamin karatu, hatta da Nazifa da batayina tunda na fahimci mayyar mathematic ce sai nake raɓarta ta koyan abinda ban fahimtaba.
Zakusha mamaki yanda takan zauna ta koyamin dukda anayine ana dizgani.
Ahankali sai na fara fahimtar halin kowanne a cikinsu har ita Nazifar kuwa, tunda na fahimci yanda halin kowannensu yake saina ƙara ɗaura ɗammarar zama dashi a yanda yaken danna ribantu da hakan.
Bani da lokacin hatta tunani a yanzu, na maida dukkan hankalina ga karatun sai ko bautar ALLAH dake a gaban komai, kullum kuwa ina ƙoƙarin miƙama UBANGIJI kukana.
Abinda ya kuma sakamin nutsuwa da Nazifa sam bata wasa da salla, lokuta da dama ma ita kema su Ummie faɗa akan su tashi suyi akan lokaci, idan har zan tashi da daddare da taji motsina itama zakaga ta tashi tayo alwala tazo kusa dani ta shinfiɗa abin salla.
Hakan dasu Ummie sukaga munayi sai suma ya fara tasiri a ransu, sai suka fara cewa suma mu tashesu dan ALLAH.
Daga nan sai muke tashinsu, itama Rebecca sai take tashi taita addu'oinsu, dan bata iya barcin da muma mun tashi, fatanmu dai ALLAH ya tabbatar da nasara a garemu akan wannan jarabawa.
Kusan halin ƙuruciya, a irin wannan shekarun namu dama zakaga daga harkar makaranta saina samari ke tasiri a rayuwarmu, dan idan mun zauna hira su Zuhrah kanta hirar samarinsu, nidai bani da abin faɗa, dan ko'a mafarki ban taɓa saurayiba, na tuna sanda ina gidanmu na haya har habaici akema innata akan banda farin jinine, bata cewa komai, iyakarta murmushi kawai.
Sai zuwa yanzunne nima nake gasgata maganarsu, lallai banida farin jinin, dan nidai ba'a taɓa cewa ana sonaba, ko irin soyayyar nan ta ƙuruciya ban taɓa yiba, sai dai naga ƙawayena nayi harma a bani saƙon musayar wasiƙar soyayya na kai.............✍🏻
*_ZAFAFA SABON KAFCE SUN DAWO GAREKU_*
_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_
_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_
_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_
_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_
_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_
_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_
_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_
_GUDA DAYA DARI BIYU_
_GUDA BIYU DARI UKU_
_GUDA UKU DARI HUDU_
_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_
_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻
_Sannan akwai tashoshinmu na Youtobe da zasu fara kawo muku daɗaɗan labarai bisa tsaftataccen karatu, kuyu azamar garzayawa tashar *ALƘALAMI TV & MANHA HAUSA NOVELS* domin samun wannan gara ɓasa, a danna mana subscribing domin nuna ƙauna ta musamman masoyan gaskiya.😃🥰🥰💃🏻👌🏻_.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*_Typing📲_*
*_🧺ƘWAI_* _cikin_ *_ƘAYA!!🧺_*
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_Wattpad:-_* _BilynAbdull😉_
*_____________________________________*
*_BOOK ONE_*
_Shafi na ashirin da biyar_
*_____________________________________*
*_Yau babi editing kuyi manage⛹♀😒._*
.............Wanka ya samu yayi da ruwan ɗumi danya rage nauyin jikin, sannan yay alwala ya fito, jallabiya kawai ya saka ya fito zuwa massallacin gidan dake a ƙofar kiga.
Ana idar da salla ya fice abinsa, dama yau a makare yazo, dan haka yay sallar a ƙofa-ƙofa, bai yarda tsayawa gaisuwa da kowa ba har kawunansa, ya gudo gida ya kwanta.
Duk yanda tunanin yaso masa tasiri barcin da ya keji sai yaci ƙarfinsa, kafin kace mi ya fara sauke numfashi a hankali alamar dai yayi nisa cikin barcin.
A makare ya tashi zuwa office, dan haka yayta komai cikin hanzari harya samu ya kimtsa, yayi ƙyau sosai, ya fito yanata baza ƙamshi kamar ko yaushe.
Gimba da tun ɗazun yake gewayensa da tunanin ko lafiya?, yay saurin miƙewa daga wajensu mai gadi ya nufosa.
Sam babu walwala a fuskarsa, ɗaure take tamau babu sauƙi, kusan biyar daga matasan ƴammatan gidan da suka fito zasu wuce makaranta suka shiga gaishesa kowacce zuciyarta a narke da ƙaunarsa.
Hannu kawai ya ɗaga musu dan baijin zaima iya motsa bakin balle aje ga magana, da sauri Gimba ya buɗe masa motar saboda yau dai yasan babu wargi a wajen boss.
Shima sai da ya zagaya mazaunin direba sannan ya fara gaishesa.
Shiru Jawaad ɗin bai amsaba, Gimba ya kallesa ta mirror, yanda ya gansa kwance a jikin kujera idanu a lumshe ya tabbatar masa lallai akwai matsala.
Bai sake cewa komaiba ya tada motar suka fice daga gidan.
Sai lokacinne Jawaad ya amsa masa gaisuwar, tare da faɗa masa inda zasuje kafin Office.
Jin asibiti ya saka gimba tunanin ko baida lafiya ne?.
A ƙofar gida sukaci karo da motar yaran da aka bama Jawaad ɗin yanzu a Office saboda tsaro su huɗu, gilas ɗin motar kawai Gimba ya sauke suka matso suna gaisheda Jawaad ɗin cikin girmamawa.
Idanunsa ya buɗe yana ɗaga musu hannu, bayani ɗaya yay masa akan Sir Ahmad yace yau zasu fara gudanar da aikinsu, daga yanzu duk inda zai saka ƙafa dolene sai da su.
Numfashi kawai ya basu, yay musu nuni su shiga mota kawai.
Umarninsa sukabi, su ka rabu biyu kowacce mota mutum uku, ɗaya a gaba ɗaya a baya, ta Jawaad tana a tsakkiya.
Shi sam baya buƙatar wasu securitys tare dashi, amma Sir Ahmad ya matsa sosai akan yabar barin Jawaad ɗin na yawo haka tun randa abin nan ya faru tsakaninsa da Qaseem.
Shigarsu asibitin suka samu waje sukai fakin, kasa daurewa Gimba yay ya juyo a ɗarare yace, “Boss ko baka da lafiya ne?”.
Idanu Jawaad ya buɗe a hankali kan gimba, sai kuma yay masa guntun murmushi yana girgiza kai alamar (a'a).
Duk da Gimba bai gamsu ba haka ya fito, Security ɗaya kuma ya buɗema Jawaad ɗin motar, yaja kusan seconds ashirin sannan ya zuro ƙafarsa ƙasa ya fito.
Baƙin eyeglasess ɗinsa ya ɗora saman ido alamar dai babu sassauci kenan, yana tafe suna take masa baya cikin bajinta mai nuna alamun fushi tattare dashi.
Ganinsu kawai ya isa ya baka tsoro, gasu duk sunsha baƙaƙen suits da eyeglasses, fuskoki kam ba'a cewa komai saboda ɗaurewa.
Sun samu girmamawar mutane musamman ma'aikatan asibitin, duk da fuskarsa ɓoyayyar fuskace da ba kowa yasan matsayinta ba, amma yanayinsa da kwarijininsa sun saka mutane ganin girmansa a idanunsu, sannan yanayinsa ya tabbatar da ba ƙaramin mutum bane koda a hasashe saboda mazajen dake rufe da bayansa harda masu binduga a hannu su uku.
Sai ƙalilan da ba'a rasaba da zasu iya sanin fuskar, musamman tsananin kamar da yake da mahaifinsa.
Tsaye yay dai-dai saitin matar da ke a reception ɗin, duk sai ta rikice, Jawaad ya kalli gimba dake gefensa a ƙasan maƙoshi yace, “Office ɗin Doctor Tayyeb”.
Gimba ya juya ga matar yana maimaita mata.
Kai ta shiga gyaɗa masa baki na rawa tana faɗin, “Ok ok Sir” tai maganar tana ƙoƙarin kiran wayar ogan nata Doctor Tayyeb.
Basu san mi ake cemata daga canba, tanata dai ƙoƙarin masa bayanin dazai fa himta amma da alama cewa yake bazai samu ganinsu ba....
Tsawa ɗaya daga securitys ɗin Jawaad ɗin wani ya daka mata, hakanne ya sakata sakin wayar jikinta na tsuma, Gimba yace ta haɗasu da wanda zai kaisu Office ɗin ko ita ta fito ta rakasu.
Duk fa wannan dambarwar da ake Jawaad na tsayene yana saurarensu hannayensa duka biyu a cikin aljihu, nazarin asibitin da mutanen dake kaikawo a cikinsa kawai yakeyi, duk da ma tun shigowarsu kowa ya nutsu waje guda dan yanayinsu ya nunama kowa dama ba ababen wasa bane balle a gansu a ɗauke kai.
Wata Nurse ce tai musu rakkiya har Office ɗin, tana ƙoƙarin yin knocking Jawaad ya ɗaga mata hannu alamar kar tayi.
Ja baya tai kanta a rissine alamar girmamawa a garesa.
Gimba ya tura ƙofar Jawaad ya shige kansa tsaye, yayinda yaransa suka jeru a ƙofar kamar waɗanda sukazo kama ɓarawo😂.
Takun takalman Jawaad suka saka Doctor Tayyeb saurin matsawa daga jikin budurwar daya ƙwakume a Office ɗin yana lalubewa, itama Nurse ce, sanye takema da Uniform ɗin asibitin.
Wani wawan tsaki Jawaad yaja yana ɗauke kai daga garesu, Budurwar dukta ruɗe sai duƙar da kai take cikin alamun jin kunya da firgici, shi kansa Doctor Tayyeb ɗin a firgice yake, ganin Jawaad a asibitinsa da kuma abinda yaga yanayi da ƴar mutane.
Sai faman sinne kai yake yazo ya zauna a mazauninsa yanama Jawaad ɗin barka da zuwa.
Jawaad da bai tankashiba ya jeho masa tambaya mai rikitarwa,
“Wannan shine abinda kakeyi da ƴaƴan al'umma shiyyasa ka salwantar min da ciki?!!”.
Yanda Jawaad yay maganar a matuƙar kausashe ya saka jikin Doctor Tayyeb ɓari, bakinsa na rawa yace, “Yal...Yallaɓai wl... Wlhy kaji na rantse ban san komai akan maganar nanba, matarka ba zubar da cikinta taib.....”
Da ƙarfi Jawaad ya buga tebir ɗin gaban Doctor, wasu abubuwan suka zube, wasuko tsalle sukai suka canjama kansu muhallin zama.
“Mara mutunci, zaka cigaba damin wasan kwaikwayone kokuwa zaka sanarmin gaskiyar batu kafin na fasa ƙwalwarka da bindiga?!”.
Doctor Tayyeb daya manne da bayan kujera zufa na karyo masa ya share gumin goshinsa, “Yallaɓai please Calm dawn, wlhy bansan komaiba, yanda na musu bayani shine gaskiyar magana, mahaifartace bata da ƙwarin riƙe ciki.....”
Miƙewa Jawaad yayi yana wata ƴar dariya da tafa hannayensa, ya tako zuwa gaban kujerar da Dr Tayyeb yake, a saman tebir ɗin ya zauna suna fuskantar juna, ya ajiye ƴar ƙaramar bindigarsa daya ciro a aljihu ya ajiye gefrnsa.
Wani mugun yawu Dr Tayeeb ya haɗiya idonsa akan bindigar, Jawaad ya katsesa da faɗin, “Wannan itace tambayar ƙarshe dazan maka, ya rage naka ka bani amsa dai-dai kokuma ka sakemin ƙarya. Miyasa kabi ra'ayinta ka zubarmin da ciki?”.
Doctor dake lafe jikin kujera tamkar magen datai karo da kura a daji ya haɗiye wani yawu mai kauri idonsa akan bindigar Jawaad daya ɗauka yake jujjuyata a hannu, tabbas yasan Jawaad zai iya aikata komai, shiko da baida laifi gara ya fidda kansa a cikin wannan bala'in tunkan kwaɓarsa tai ruwa, saboda kuɗin Aamilah bazai halaka kansa ba a wofi.
“Yallaɓai kayi haƙuri ka ajiye bindugar na rantse duk abinda kake buƙata zan sanar maka shi”.
Cikin wani salo da murmushin mugunta Jawaad yasa ɗanyatsa ya tura eyeglasess ɗinsa sosai yana faɗin, “Good boy, ashe kasan dokar”.
“Sosaima kuwa yallaɓai” Dr Tayyeb ya faɗa yana jinjina kai tamkar ƙadangaren jangwala gwaja yaga shinkafar manja🤪.
Ajiye bindigar Jawaad yay yana ranƙwafowa kaɗan hannayensa harɗe a cinyarsa da yake zaune da ita a tebir ɗin, ɗayar kuwa tana ƙasane a jiye, “Ina saurarenka”.
Nanma kai Doctor ya jinjina masa, “Maganar gaskiya yallaɓai lafiyar mahaifarta ƙalau, zubar da cikin akai, sai dai wlhy kaji na rantse maka bani nai mata aikinba, andai kiranine kawai na ceto rayuwarta”.
Sosai zuciyar Jawaad ke tsitstsinkewa, ya zare glasess din idonsa yana zuba ma Doctor wani hargitsatstsen kalo, “Uhmyim, wato zubarwa akai? Amma miyasa ka zaɓi faɗar abinda ba haka yakeba? Haka aikinka ya koya maka?”.
“Wlhy A'a yallaɓai, kuskurene ka gafarceni”.
Sauka Jawaad yay daga saman tebir ɗin yana taku a hankali yana faɗin, “Maybe na iya yin hakan idan na tabbatar babu saka hannunka a ciki”.
“Wlhy da gaske nake babu hannuna, bankuma san komai a kaiba”.
Komawa Jawaad yay ainahin kujerar daya fara zama ya zauna, ƙafarsa ɗaya kan ɗaya yana aza hannunsa ɗaya a tebir ɗin yace, “Doctor Tayyeb ka sanni na sanka tun lokacin daka fara aiki gidan Alhaji Ali, karka kuskura a wannan karon ka tsinci kanka a harƙallata, dan wlhy bazan maka ragiba, na kamaka da ƙaryar farko ta faɗar sakamakon abinda ba haka yakeba, kasa a ranka ba'a min ƙarya a shani a banza, yanzu zan tafi, a koda yaushe kuma zan iya nemanka a office ɗina, zaɓin kane kazo akan lokaci koka ɓatamin lokacin”.
“Insha ALLAH zanzo yallaɓai, kuma bazan sake kuskuren maka ƙaryaba akan duk abinda zaka tuhumeni a kansa”.
“Good” Jawaad ya faɗa yana miƙewa da ƙoƙarin tura bindigarsa ta baya, bai kuma tankama Doctor Tayyeb ba ya fice