Showing 222001 words to 225000 words out of 388641 words
godiyarsa ga ALLAH kafin ya nufi su Jay da duk suke kan Bilkisu kowa na ƙoƙarin faɗama Jawaad taimakon da zai bata kozata farfaɗo, masu cewa ya murza hannu nayi, masu cewa ya murza ƙafa nayi, masu jajen ina za'a samu ruwa a zuba mata nayi. Shikuma sai faman girgizata yake yana faɗin ainahin sunanta na yanka wato BILKEESU!!.
Murmushi baba ƙaura yayi tare da katsesu baki ɗaya, “Bazata taɓa farfaɗowa a hakaba ko zaku kwana kanta”. Gaba ɗayansu shi suka juyo suna kallo, sai dai babu wanda ya iya cewa wani abu a cikinsu. Shima bai sake faɗar komanba, sai nuna musu su koma gefe da yay da hannunsa, babu musu sukabi umarninsa aka barshi daga shi sai su Jawaad ɗin. durƙusawa yay kusa da Jawaad murya ƙasa-ƙasa yace, “Iskar numfashinka ce kawai zai taimaki nata dawowa gangar jikinta ɗan saurayi, ka ɗaura bakinka kan nata ka zuƙo insha ALLAHU zata farfaɗo”.
A hankali Jawaad ya lumshe idanunsa tare da ranƙwafawa bisa fiskar Bilkisu ya aza bakinsa saman tattausan lips ɗinta, numfashin dake fita ta hancinsa yana sauka akan fuskarta, ya tura harshensa cikin bakinta dake ɗan buɗe kaɗan ya shiga hura mata iska tare da shanye yawun bakinta babu ko ƙyankyami, wani irin numfashi mai ƙarfi ta kawo tare da ƙanƙame hanunsa dake cikin nata ta damƙe laɓɓansa itama. Da sauri Baba Ƙaura yace ta farfaɗo?”. Yay maganar da bubbuga bayan Jawaad ƙaɗan.
Jay ya janye bakinsa dake cikin na Bilkisu da ƙyar yana sauke numfargashi da sauri-sauri, wani irin tsitstsinkewa jinin jikinsa keyi, baba ƙaura yay murmushi tare da ɗora hanunsa akan na Jawaad da ƙofofin gashi duk suka buɗe. A hankali Jay ya buɗe lumsassun idanunsa yana kallon Baba ƙaura kamar yanda itama Bilkisu ta buɗe nata a hankali akan fuskar Jawaad. “Da bakajin sha'awarta a matsayin mata ko?”. Gaban Jawaad ya faɗi yana mai al'ajabin ya akai tsohon ya sani?. Murmushi baba ƙaura yay yana ɗauke kansa ya maida ga bilkisu, “Yanda bakajin sha'awarta itama haka batajin komai game dakai dama kowane namiji a duniya, sai wanda sukaso yimata wasa da hankali a kansa, ada ita kaɗaice da wannan matsalar, amma dalilin aurenku kaima hakan ta shafeka, sun riga sinci buri mai tsanani a kanta, wanda hakan bamai yuwuwa bane a garesu cikin sauki sai idan ALLAH ya ƙaddara hakan, akwai al'amari mai sarƙaƙiyar gaske tsakaninku, sai dai inaji a jikina komai yana gab da warwarewa dalilin abu uku wanda nima ALLAH bai bani ikon saniba, ka jajurce wajen tsananta bincike zaka fahimci komai da yake komai dangane daku. Bazan ɓoye makaba, wanda kukazo nema a wannan Jejin baya raye, sai dai jininsa shine jini mafi haɗari dazai zamarma duk wanda tsiyayar dashi tauraruwa mai wutsiya, ki adana wannan tsintuwar ta hannunki tamkar yanda kika adana ta farko, sai dai zasu cigaba da tsorataki domin bibiyar kayansu dan kin raunanasu sosai, duk randa ta uku tazo gareki suka zama huɗu dana hannun mijinki komai zai buɗe”. Baba ƙaura ya miƙe yana ɗan murmushi da binsu da kallo tamkar yanda suma suke kallonsa har Bilkisu, ya sake cewa “ƘWI CIKIN ƘAYA AJIYAR ALLAH”. ya juya ya barsu.
Da ƙyar Jawaad ya iya maida kallonsa ga Bilkisu, ya kamo hannunta dake rumtse ya buɗe a cikin nashi, Wurine baƙi mai girma tamkar wanda ta taɓa tsinta a ɗakinta. Zumbur ta tashi zaune jikinta har yana rawa, dan sai yanzu ta fargafa a jikin boss take kwance. Wasu hawaye masu zafi suka fara zirara a kumatunta suna sauka bisa fuskarta.
Shidai Jay kallonta kawai yakeyi, ɓullowar su baba ƙaura ya sashi faɗin. “Shiii!!!” yana mai ɗora yatsansa akan bakinsa. Saurin kallon inda yake kallo tayi itama, su Jabeer ne ɗau da mutum bisa buzu. Atare suka miƙe ita da Jay harsu Hafiz suka iso inda suke suka ajiye gawar Gimba da duk fuskarsa tai kaca-kaca da raunuka tamkar yakushi. Durƙushewa Jawaad ya koma yayi gaban gawar, hanunsa na rawa yakai kan fuskar Gimba ya shafa, idanunsa sun sake kaɗawa sunyi masifar yin jazurr, jijiyoyin kansa sunyi ruɗu-ruɗu. Su Hafiz sai sharar ƙwalla sukeyi suma.
Ɗagowa Jay yay yana kallonsu, dagani kasan shima kukan zuci yakeyi, ya maida duba
nsa ga Baba ƙaura dake riƙe da farin ƙyalle a hannu. Baba ƙaura ya girgiza masa kai da lumshe ido alamar ban haƙuri. Juyawa yay yana kallon Bilkisu dake kusa dashi tsaye tana kuka iya ƙarfinta. Ya dafe goshinsa yana murzashi da ƙarfin gaske, soyake yayi hawaye tamkar yanda suma sukeyi kozaiji daɗi, sai dai sunƙi fitowa, sai zuciyarsa dake wani irin zafi mai azabartar da gangar jiki da ƙwaƙwalwa. Miƙewa yay daga gaban gawar ya kamo Bilkisu dake tsaye. Jikinsa ta faɗa tare da sake fashewa da kuka mai huda zuciyar mai sauraro.
Baba ƙaura sai basu baki yake da nuna musu muhimmancin ƙaddara da karɓarta a duk yanda tazoma bawa, sannan mutuwa alƙawarin ALLAH ce ga kowane mai rai dake doron ƙasa, shi da ya tafi ba gaggawa yayba, mu da muke raye bamuyi jinkiriba, ALLAH yay alƙawarin kwanansa ya ƙare, waɗanda suka kashesha sanadi suka zama, da sunyi haƙuri ma aranar zai bar musu duniyar dama. Da waɗan nan kalaman hikima Baba ƙaura ya shawo kansu har suka ɗakko ledan da sojoji kan saka gawa kafin a kaita inda ya dace idan har basu da damar binneta a wajen yaƙi. Haka aka saka gawar Gimba da cikin hikimar UBANGIJI babu abinda tayi tamkar yanzune ya rasu.
Bily bata iya shiga cikin jirginba saida taimakon Jawaad, yanzunkam kusa dashi ya zaunar da ita, dan shima yana buƙatar jin ɗuminta.
Dukda halin da ake ciki hakan ba ƙaramin zafi yayma Rose ba, har cewa Jay take munafuki a cikin zuciya, a ganinta shida yake gudun taɓa macen daba matarsa ba yau wane gulma ta kaisa mamuƙar wannan yarinyar kuma? Taja tsaki a cikin ranta tana ɗauke kai, ta tsani yarinyarnan wlhy, kuma itama tana gab da salwantar mata da rayuwa inhar bata fita rayuwar boss na, yarinya ƙarama sai baƙin karuwanci?.
Wannan zantuntuka sune Rose taita tattaunawa da zuciyarta har jirginsu mai saukar angulu ya sauka a garin su gimba tamjar yanda Jawaad ya yanke shawarar suyi kawai. Ya kuma kira Sir Ahmad ya sanar masa halin da ake ciki, hakama Alhaji Babba.
______________________
Tunda Jawaad ya kira Alhaji babba ya sanar masa inda zasuje da rokon a tayasu addu'a sai ya kasa zaune ya kasa tsaye, haka ya tara tsoffin anguwarsu sukai shawara akan subi makarantu yanzunan a dasa saukar Alkur'ani mai girma, tare da masallatai idan lokacin sallar zuhur yayi, ya kira Ummah babba da ƙarama ya umarcesu da yin abincin sadaka su bada a fitar a rabama mabuƙata.
lokacin dasu Jawaad ke cikin wancan mawuyacin halin addu'oin bayin ALLAH ne dana ƙananun yara keta riskarsu, tareda farin cikin mabuƙata da aketa rabama lafiyayyen abinci harda abin sha.
(Duk wanda yace ALLAH ya tsira wlhy, bawa saki kowa ka kama ALLAH shine shugaba mai kallon motsin kowa hatta da ƙwaron da idanu basa gani, mai bada kariya ga kowa ta inda bakai zatoba, mubar zagin shugabanni na duniya da suka zama wakilanmu akan san zuciyarmu, mubar ɗaukarsu matsayin waɗanda zasu bamu kariya ko farin cikin duniya domin suma mutanene tamjarmu, basu isa sanin abinda yake ɓoyeba sai wanda ALLAH yaso su sani, mu aje shirmen siyasa gefe muyima ƙasashenmu addu'a da shuwagabanninmu wannan shine nasararmu).
________________________
Su Jawaad sun isa da gawar Gimba ƙauyensu, inda helicopter ɗin da suke ciki ya sauka a filin makarantar primary ɗin dake gab da gidansu gimban, daga nanne aka ƙarasa da gawar bayan su Baba ƙaura sun fara isa gidansu Gimba sun isar da saƙo maiban tashin hankali.
Faɗa muku yanda abubuwa suka cabe a wannan lokaci abune mai wahala, dan matarsama suma tayi saida aka zuba mata ruwa, haka ƴan anguwa da danginsa sunata kuka dan gimba mutumne na mutane, sannan yanada son zuminci, duk alkairin da yake samu ga Jawaad bai yarda yaci shi kaɗaiba hatta da wanda ba nasabama ci suke shima.
Gimba shi kaɗaine ɗa namiji wajen iyayensa, babansa ya rasu tun suna yara, mahaifiyarsu itace taita ɗawainiya dasu har girma, sai ƙanwarta dake aure birni da bata gajiyawa da taimakonta da marayun ƴaƴanta har suka girma, yayi karatunsa har zuwa diploma saɓanin ƴan uwansa mata da ke tsayawa iyakar secondary ake musu aure, shine ɗa na farko, sa
i ƙannensa shida duk mata, huɗu sunyi aure harda zuri'a sai biyu na nan suna karatu, harma Jawaad ya ɗauka alƙawarin zuwa ya roƙa mahaifiyar su gimban dan suci gaba da jami'a idan sun kammala sakandiri ɗin da suke aji shida yanzu, a lokacin gimba yata murna dan dama burinsa kenan. Matar gimba ɗaya da yara uku duk maza, yaronsa na ƙarshe sunan Jawaad ya saka masa yana kiransa da suna yayana. Adalilin Hajiya Safara'u ƙanwar mahaifiyarsu dake zaune birni ya samu aiki a ƙarƙashin Jawaad, (zuwa gaba lokaci zai fiddo mana wacece Hajiya Safara'u).
Mahaifiyar Gimba mace mai haƙuri da sam batai kukaba saina zuci itace tace Jawaad ne zaima gimba wanka tare da ƙaninta mai suna Ibrahim wanda ya kasance dattijo ne sosai.
Su Jawaad suna can suna ƙimtsa gawar Gimba su Alhaji Babba suka iso kusan mota huɗu, harda jama'ar gidansu Jawaad wato kawunnansa.
Jawaad da kawu Ibrahim sun suturta gawar gimba tamkar yanda shari'a ta koyar, kafin mahaifiyarsa da ƴaƴansa harma da ƙannensa su shiga suyi sallama da gawar, daganan aka fito dashi domin miƙasa maƙwancinsa na gaskiya. Kuka sosai ya tashi a gidan maiban tashin hankali har aka fice da gawar daga gidan zuwa ƙofar gida inda su Alhaji babba da mutanen gari suka haɗu wajen sallatarta.
Masha ALLAH yayi jama'a kam har abin ya bama mutane mamaki, sai dai UBANGIJI shiyasan ajiyar da yay a wannan waje. (ALLAH ya gafartama gimba da iyayenmu da dukkan musulmai da suka rugamu tafiya😭🙏🏻).
Bayan an dawo daga kaisa su Jawaad basu tafiba, suna a cikin garin har gabanin magriba ana amsar gaisuwa dasu shi dasu Hafiz, Jabeer, Aliyu, sai Bilkisu. Sojojin da sukai musu rakkiya da Baba ƙaura sun wuce tun bayan da aka dawo daga binnesa. Rose ma lokacin da su Sir Ahmad zasu tafi dasu Alhaji babba bayan sallar la'asar Jay yace ta bisu. Bilkisu kuwa tana ciki tare da matar Gimba, batasan yaya akai sukasan ita matar Jawaad baceba, sai kawai ganitai anata nunata da faɗin itace matar ogan marigayi Gimba. Haka zasuyita jera mata addu'a da yabon halin Jawaad bisa ɗawainiya da taimakon da ƙauyen yake samu daga Jawaad ɗin ta dalilin gimba. Haka sukaita mata komai a girmame tamkar tafi kowa. Ita harma kunya ta komaji akan yanda suke matan.
Wajen ƙarfe shida saƙo ya iso mata akan ta fito inji boss zasu wuce. Haka ta tashi ta kimtsa jiki a saɓule dan ta amshi hijjab ɗin matar gimba ta saka tun ɗazun saɓanin da da take da baby hijjab kawai. Sunata mata godiya da addu'a, ƙannensa suka rakota har waje inda motar da zasu tafi take.
Sau ɗaya na kalli Boss na ɗauke idanuna saboda wani irin tausayi yake bani, na ƙaraso inda yake tsaye na gaishesu tare da sake musu gaisuwa, murya cike da damuwa ya amsa mani yana min nuni dana shiga motar daya buɗemin. Ni da shi da Jabeer ne a baya, ina jikin ƙofa yana tsakkiya Jabeer kuma a ƙarshe, sai Aliyu da zai ja motar Hafiz na gefensa. Haka muka wuce sunata mana addu'oin sauka gida lafiya.
Sosai Aliyu ke sharara gudu kasancewar garin yay wani irin ɗaurewar hadarin farkon damina mai cike da iska a ciki, babu mai magana a motar sai zancen zuci, cikin awa ɗaya da mintunan da bazasu gaza ashirin da bakwaiba muka iso cikin gari, zuwa lokacin garin ya sake yin duhu, gana hadari gana magriba, anata salloli a masallatai. Nayi zaton masarauta zasu kaini, sai naga an nufi gidansu Boss, koda mukazo gate sai yace basai Aliyu ya shiga da motarba bara mu sauka anan su wuce kar hadarinan ya riskesu..................✍
(Dolene koda zai halaka da izinin ALLAH sai ya gano suwaye suka kashe ɗan fir'auna, miyasa suka kasheshi?, minene a binne da rayuwarsa da ɗan-fir'auna yaso sanar masa, yanaji a jikinsa kisan ɗan fir'auna nada nasaba da abinda ya shafesa, minene shi? Wannan ne bai saniba.)
dolene jiya kushiga ruɗani akan mutuwar ɗan fir'auna bayan farkon page na nuna bai mutuba, nima sai a Comments ɗinku na fahimci kuskuren danayi na koma na duba page ɗin, wlhy hankalina sam bai kaiba ko'a wajen editing, rayuwace abubuwa sunma ƙwaƙwale yawa, kana gabas tunaninka na yamma, amin afuwa ɗan fir'auna bai mutuba🤦🏻. anahin abinda naso sakawa a
wajen shine (Dolene koda zai halaka da izinin ALLAH sai ya gano suwaye suka so kashe ɗan fir'auna, miyasa sukaso kasheshi?, minene a binne da rayuwarsa da ɗan-fir'auna yaso sanar masa, yanaji a jikinsa masu son kisan ɗan fir'auna nada nasaba da abinda ya shafesa, minene shi? Wannan ne bai saniba).🤗🙏🏻
ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[12/18/2020, 3:57 PM] HASNA✍🏻: +234 909 304 4460:
Page 31
...............“Muje”. Ya faɗa a hankali. Babu shiri nai azamar ɗago idanuna na kallesa, duk da ni yake kallo ban janyeba, cikin harɗewar harshe nace, “Anan zan... zan kwana?”. Tamkar baiji abinda naceba ya ɗauke kansa, dubansa yakai ga sararin samaniya daketa sake caƙuɗewa da duhu, batare da yace min uffanba ya raɓani ya nufi gate. Hawayen da nake maƙalewa suka silalomin a kumatu, a fili nace, ‘Dan ALLAH kar kaimin haka nidai’. Kamar yasan mi nake faɗe ya juyo yayinda ya buɗe ƙofar gate ɗin zai shige, “Karki bari na dawo na sameki a nan gurin”. Yafaɗa yana nunoni da ɗanyatsa alamar gargaɗi. Hannu nasa na share hawayen fuskar tawa kafin na taka nima zuwa gate ɗin. Maigadine kawai ke bin jam'i a bakin gate ɗin da yake anaji daga cikin gida. Ganin yayi tsaye yana kallon maigadin ne yasa nima naja na tsaya, sai da aka sallame sallar da dama zaman tahiyar ƙarshe suke. Kamar jira, ana yin sallama maigadi na miƙewa ya nufosa. Fuska a haɗe Jay ke kallon maigadi, baiko amsa gaisuwar da yake masaba da sannu dazuwa yace, “Ka bautama UBANGIJI tamkar kana ganinsa, dan idan kai baka ganinsa shi yana ganinka, MANZON ALLAH ya horemu da zuwa masallaci muyi sallah cikin jam'i, miyasa kai kafi zaɓar yinta kai kaɗai a cikin gida? Shin tsaron gate dan kar wani ya shigo yafi maka muhimmanci akan zuwa ka samo cikakkiyar ladar da mahaliccinka kaɗai ke badata? Daga yau ina mai baka shawara a kowanne lokacin salla ka kulle gate ɗin nan idan yazama dole saika zama mai tsaron mutanen cikin gidan kaje kai sallah cikin jam'i”. Kan maigadi a ƙasa yace, “Nagode sosai Alhaji, ALLAH ya saka da alkairi ya kareka kaima, ya ƙarin haƙuri?”. Cikin lumshe ido Jay yace, “Alhmdllh, abokinku ya tafi ya barmu”. Hawayene suka ziraro a fuskar maigadi, hakan yasa Jay yin gaba shima yana haɗiye abinda ya tokare maƙoshinsa.
Jiki a saɓule nabi bayansa mukabar maigadi na kuka, sai naji nima hawayen nawa na sake gangarowa, dukda bawani sanin gimba nai sosai ba mutuwarsa ta taɓani ainun, mutum mai fara'a dason mutane.
Yana gama buɗe ƙofar da keys ɗin daya ciro a aljihu iskar na tasowa, hakan yasa muka shige da sauri saboda irin mai ƙasarnan ce sosai, da sauri na maida ƙofar na rufe na jingina jikinta ina sauke numfashi da share fuskata da hijjab ɗin gudun kar wadda ta hau ta shigarmin ido.
Boss kam ya kunna fitilar falon saboda an kunna Gen..., a take haske ya gauraye ko ina, baice dani komaiba ya nufi sama abinsa. Tafiyarsa kawai zaka kalla zaka fuskanci yana cikin damuwa, dan a sanyaye yakeyinta. da kallo na bisa har saida ya ɓacemin, na sauke ajiyar zuciya ina lumshe idanuna, a ƙasan raina addu'a nake ALLAH yasa idan iskarnan ta lafa yace zai maidani Masarauta.
Tunda ya shiga bedroom ɗin sai ya shiga yatsina fuska, shaf yama manta ko gadonsa bai samu arziƙin gyaraba yau, duk yanda yake jinsa a matuƙar gajiye haka ya daure ya shiga kakkaɓe gadon, ya gyarashi tsaf kamar ba yanzu za'a kwanta a kansaba, fitowa yay ɗaukar tsintsiya, duk da sarai yaga Bilkisu dake tsaye jikin ƙofa har yanzu yay tamkar bai gantaba yaje ya ɗakko kwandon da kayan sharan ke ciki yazo ya sake hayewa sama.
Da kallo na bisa, haka kawai sai naga kamar bai daceba, dan da alama shara zaiyi da kansa, bayansa nabi jikina duk a saɓule, ga kaina namin wani irin ciwo ƙasa-ƙasa, ga yunwa dan rabona da abincin kirki tun breakfast ɗin safe, a garinsu marigayi fura kawai nasha rabin kofi itama sai da aka takuramin. Duk da sallamar da nayi bai ɗago daga abinda yakeba, nasan salon amsa sallamarsa a ciki-cikine hakan yasan ban damuba dan nasan dai ya amsani, nace, “Bara in share”. Kamar bazai kulani ba, sai kuma ya miƙamin tsintsiyar ya fice.
Ajiyar zuciya na sauke na cigaba da sharan a sake ganin ya fita saini kaɗai. Tsaf na kammala sannan na nufi toilet, shima dai yana buƙatar wankin dukda bawani datti yayba na tashin hankali, tsaf na gyarashi cike da ƙarfin hali. Ina fitowa daga bayin shima yana shigowa ɗakin, saurin ɗauke kaina nayi daga garesa saboda ganinsa a tuɓe babu riga sai dogon wando kawai da farar singlet yana waya, ya zauna a bakin gado
n yana cigaba da wayarsa, kusan mintuna biyu ya juyo inda nake tsaye, yatsunsa biyu ya murza sukai ƙara, hakan yasa na ɗago kaina garesa, alamar nazo yaymin. Ahankali na taka zuwa garesa, ya miƙamin wayar batare da yace komaiba ya bar wajen. Duk da bansan ko