Showing 294001 words to 297000 words out of 388641 words

Chapter 99 - KWAI CIKIN KAYA

10 Sep 2025

20676

ya juyo ya kalleni, “Zo nan naji mike damunki ne?”. Mamaki ya kamani, ya akai ya fahimta? Saurin gyara yanayina nai da cewa, “Babu abinda ke damuna sai barci”. yaɗan tsuramin idanu sannan ya janye, “Tunda yau na fara saninki ko?. Taso nace”. Tashi nai zuwa inda yake ina kumbura fuska, ya fisgoni da ƙarfi na faɗa saman cinyarsa, ƴar ƙara na saki wadda ni kaina nasan ta shagwaɓace, “Shiiii” ya faɗa yana saka kankana a baki, bakinsa ya ɗora kan nawa ya sakamin kankanar dake bakin nasa cikin nawa. Na yamutse fuska kaɗan a raina ina faɗin ‘ƙazanta’. Ɗallar bakina da yay ya sakani sake ɓata fuska dan naji zafi, ya ɗage gira ɗaya da faɗin, “Nasan ai gulmata kikai a zuciyarki”. Saida na shanye sannan nace, “Nidai nasan banyiba ai”. Bai tanka minba ya cigaba da bani fruit ɗin shima yana sha, saida nace masa na ƙoshi sannan ya barni. Zameni yay na kwanta a kujerar kaina na saman cinyarsa, wannan damar dana samuce ta bani damar faɗin, “boss wai dan ALLAH wane laifi Dad yay makane?”. Kallona yay cikin ido ya watsar, ya maidama hankakinsa ga kallon labaransa hankali kwance. Iya kaiwa ƙarshe nakai da haushi, hakan yasa na sake maimaita tambayar kozai fusata ya bani amsa, amma nanma saiya shareni, aifa nakai ƙarshen harzuƙa, na fashe masa da kuka, “Wai miye laifin Dad ne da Yah Qaseem a gareka? Bayan tarin ƙauna da kulawa da suka nuna maka dagasu har Momy, ƴa fa suka ɗauka sukutum suka baka ka aura, basu ji komaiba suka sake bakani duk da kuwa ɗansu jininsune ya dace na aura, sannan ƴarsu da ke tsananin sonka ya dace ka aura kaima, boss bai kamata ace ka maida alkairi ta wannan sigarba, suɗin ƴan uwanane fa waɗanda sukaimin gatan da kowa ya gaza yimin, sune suka maidani mutum harna zama abin sha'awa ga irink.......” ruf ya rufemin baki da nashi, ya ɗagan

i cak batare daya sakimin bakiba yay bedroom dani, duk ƙoƙarin son ƙwacewar da nake ko gezau baiyi ba, dama ya kashe fitilar ɗakin sai na gefen gado kawai, dan haka sai kawai jina nai bisa gado, babu wani ɓata lokaci ya shiga juyani da zafi-zafi yanda yake so, gashi ya hana bakina damar neman ɗauki, yanda yake bi danine ya tadamin hankali, dan sam babu wani bi a hankali kamar ranar, sai dai kuma hakan bai hanashi kasancewa cikin nutsuwaba da min abinda zai gusarmin da hankali. Idan nace muku na gurzu fiye da ranar farko to ku ɗauka gurzuwa nai irin ta ƙarshen nan da faɗarta kawai takai a tausayamin, dan al'amarin ya zama kamar famine daga baƙar azabar dana sha a daren shekaranjiya. Muryata harta dasashe saboda kuka, ya kuma ƙi lallashina kosau ɗaya.
         Kamar ranar yauma shine ya taimakamin na gyara jikina, ya kuma sakani a ruwan zafi sosai sannan ya maidoni saman gadon ya kwantar batare da yace dani uffan ba, yamayi tamkar baijin kukan nawa, komawa yay bayin yaje yayo wanka shima, har lokacin ina shashshekar kuka na, muryarsa a dadushe kamar mai mura yace, “ALLAH idan bakimin shiruba na hawo gadon nan saina sake banbance miki aya da tsakkuwa, daga yau kuma dan ALLAH ki sake ahiga abinda babu ruwanki kinji ko”. Yana gama faɗa ya ficewarsa a ɗakin.
      Kukan na sake fashewa dashi ina danna kaina cikin filos dan karya ji, kusan mintuna goma da fitarsa naji ya dawo ɗakin, haɗiye kukan nayi na koma sauke ajiyar zuciya, bai tankaminba naji dai yanata kai kawonsa har na wasu mintuna kafin ya hawo gadon. A jikinsa ya sakani ya rungume batare da yace ƙala ba, mintuna kaɗan barci yay gaba dashi bayan yaymana addu'a, nima ajiyar zuciyata na cigaba da saukewa har barcin yay awon gaba dani.

★★★★★

         Da asuba shine ya tadani, kafinma na sakko a gadon yayi ficewarsa, na rakasa da harara sannan na sakko da ƙyar, wani irin zafi naji ya ratsani a wajen, sai ga hawaye shar, nasa hannuna na share ina jinjina muguntar maza a raina, idan dai haka za'a dingaji to miye abin daɗi anan da har mata suke zuwa suyi iskanci dan ALLAH?. Sai da na shiga ruwan zafi yanzunma sannan nai alwala na fito, naji daɗi sosai yanzun kam harda nutsuwa, ficewa nai daga ɗakin na koma nawa, sai fitilar waya na kunna dan sun ɗauke wutarsu. Ina idar da salla gado na haye nai kwanciyata ko azkar banyiba, banason yazo ya iskeni zaune, barci yaɗan fara fisgata naji ya buɗe ƙofar, ban motsaba balle yasan idanuna biyu, sai da ya maida ya rufe sannan naɗan buɗe kaɗan naga bayanan, ajiyar zuciya na sauke na gyara kwanciya abina.

         Taƙwas saura na farka, na sakko daga saman gadon ina matse fuska saboda ciwon da jikina kemin ta ko ina, bama dole nai ciwon jikiba kodan muguntar da akaimin, wanka nayi na fito nai shiri cikin wando da riga na parkistan da sukaimin ƙyau, nai ƴar kwalliya dai-dai misali sannan nasa turare da yafa ɗan gyalen kamar yanda sukeyi. Fitowa nai dan nema mana breakfast tunda ya roƙi Ummah akan a daina kawo abinci, a bazata na iskesa a babban falo zaune yana aiki. ‘Agogo sarkin aiki’ na faɗa a zuciyata cike da gulma. Ɗagowa yay ya tsatstsareni da mayun idanunsa, hakan yasa nai ƙasa da nawa, saida na rissina ina gaishesa sannan ya ɗauke kansa daga kallona, amsamin yay da tambayata wai ya jiki. “Ni lafiyata lau”. Na faɗa ina ɓata fuska “Haka akeso ai”. ya bani amsa a taƙaice. Miƙewa nai ina satar kallon kofin dake a centre table ɗin alamar coffee ya haɗa da kansa yasha kenan? Bance komaiba na nufi kicin, inaji a jikina kallona yake harna shige.
       Idanunsa ya lumshe da sakin murmushi yana ɗauke kansa daga binta da kallo da yayi, a fili ya furta, “Masu dangi, yauma ki ƙaramin maganarsu kiga yanda zamu kwashe anan gidan sarkin son ƴan uwa”.
             Gyaɗar dana jiƙa da farar shinkafa tun da daddare na wanke, na ɗakko farar kwakwa da dama na fasa na yayyankata itama na haɗesu waje guda da citta ɗanya da kayan ƙamshi dai-dai buƙatata na markaɗesu kasancewar akwai wutar da naita addu'a da fatan su kawo tunda nai sallar asuba, sai da sukai laushi sosai sannan na tace tsaf na ɗauraye tukunya na zuba, ban kunna gas ɗinba tukunna na ɗib

a wake gwangwani biyu da rabi shima nai zaman dakawa aɗan turmina, sai da yaymin yanda nakeso sannan na cire na wanke shima nai markaɗan ƙosai, saida na tabbatar na haɗa komai sannan na kunna gas, ban rufeba tukunyar kunun ba gudun karya taso ya zube saboda gafin gyaɗa, na saka ludayi ina motsawa a hankali har yay zafi ya fara kauri, cikin amincin ALLAH baiyi ƙurnu ba yay ƙyau abinsa sai ƙamshin gyaɗa da kwakwa ke tashi, na sauke tukunyar a ƙasa danya ɗan huce kafin na saka madarar dana dama. Suyar ƙosan na fara wanda dandanan na gama kasancewar bawani yawane da shiba, na zuba madarar a kunun sannan na zuba ma maigadi muma na juye mana namu, saida na gyara komai tsaf sannan na fito da namu a Dining na maigadi ma na fito dashi na ajiye gefe. Baya a falon, dan haka naɗan gyara tunda babu wani datti na azo a gani na saka turaren wuta. Ina kammalawa yana fitowa, yay tsaf cikin ƙananun kaya sai baza ƙamshi yakeyi.
            Baice dani komaiba ya ɗauki abincin maigadi ya fita, babu jimawa sai gashi ya dawo, lokacin ina a Dining ɗin ina ƙoƙarin haɗa masa nasa, kujera yaja ya zauna idonsa akan hannuna da har yanzu yake raɗam da ƙunshi.
      “Duk a yaushe kikai wannan?” na tsinkayi muryarsa a bazata. Kallonsa nai na janye idanuna, nace, “Yanzun”. “Kinyi ƙoƙari, ALLAH yay miki albarka”. Murmushin daban niyyaba na saki sai naji duk fushin nawa yay ƙasa, a hankali nace, “Nagode”. Shima murmusawa yayi kaɗan da ɗaukar ƙosan yakai bakinsa, ya lumshe idanu da faɗin, “Uhhhmm”. Kallonsa nai dariya na cina, na ɗauki cokali nasa gefensa alamar waiji. “Yarinya ai ba santi nakeba” ya faɗa yana jan kofin kunun dana ajiye masa a gabansa sosai. “Nima ai bance santi kake ba”. “Kin taimaki kanki to”.
         Murmushin na sakeyi ina ƙoƙarin haɗa nawa nima.
     Nayi mamakin yanda yaci sosai, ya ɗauki tissue yana goge bakinsa damin almar komai zamm da hannu👌🏼. “Nagode to” nafaɗa ina murmushi. Zagayowa yay ta bayan kujerar da nake ya ranƙwafo ya sumbaci kumatuna duka biyu sannan yace, “Kin gama mallake Jay da komansa Miemaa”.
          Hannu nakai na shafi fuskarsa ina faɗaɗa murmushina, dan naji yanda ya nuna jin daɗinsa da abincin.
      ya zagayo ta gabana ya nunamin kuncinsa alamar na sumbata. Dukda inajin kunya haka na daure na sumbacesan kamar yanda yake buƙata. Sassanyan numfashi ya sauke da juyamin ɗayan, nanma dai yi nayi ina mamakin rashin kunyarsa. “Jazakhillah bi jannah” ya faɗa yana kamo fuskata cikin tafukan hannayensa, kafin nace wani abu ya manne bakinsa da nawa.
       Yana saki na saka hannu na rufe fuska. yace, “Daga baya kenan. Bara naje Alhaji Babba na jirana zamuje wani waje”.
     Miƙewa nai tsaye nima, “To dan ALLAH ka kira Nabeelah tazo ta tayani zama, ALLAH babu daɗi kaɗaicin”. “Baga wuta ba, kuma nima aiba daɗewa zanyiba”. Cikin marairaicewa nace, “Idan suka ɗauke fa, kumafa ni tsoro nakeji”. “Jami'ar tsaro da tsoro”. Ya faɗa yana jan hancina. Bai jira amsataba ya fice yana faɗin “Aimana addu'a”.
     Da “ALLAH ya tsare” na rakasa inajin duk babu daɗi...................✍

Jiya kam Wattpad yay muku buƙulu, nayi typing tun dare zan baku na nemesa na rasa, wlhy sai sake wannan page ɗin nai cike da haushi, gashi dai sai dai kuyi maneji da shi😥.


ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.

HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO

MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.

MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.

BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....

abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.

Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899

sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.

Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300

Sai kunzo😍😍😍😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[1/12, 4:57 PM] HASNA✍🏻: Typing📲

ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK TWO


Page 47



..................A harabar gidan suka iske Alhaji babba zaune alamar isowarsu daman yake jira, kafin ma Sadiq ya fito ya buɗema Jay shi harya buɗe da kansa ya fita, fuskarsa ɗauke da murmushi ya ƙarisa ga kakan nasa da tun shigowar motar gidan ya ajiye jaridar dake hannunsa. Cike da zolaya Alhaji babba yace, “Kai angon nanfa kamin wayo, gaskiya nima azo a nomin ƴar bana bakwai auren nan zanyi ko kaurin wuya na ƙara da jar fata”. Sosai Jay ya ƙyalƙyale da dariya, ya zauna akujerar robar dake gefen Alhaji babba yana faɗin, “Duk gasarka dai ba zaka samo cancaɗeɗiya kamar tawaba Alhaji, domin tawa fa ta musamman ce”. “Ni dai banason cika baki, kar nan da wata biyu inga ka faramin zarya a gida ehe”. “Ai bama zanyin ba, sai dai kai ka ringa mana saboda zuwa cin tuwo”. Dariya suka sanya a tare, Jay ya rissina ya gaidashi cikin girmamawa, kafin su miƙe cike da farin ciki. Sadiq da shima tuni ya fito a motar ya rissina ya gaida Alhaji babba. Cike da kulawa ya amsa masa tare da sanya masa albarka. Jawaad ya buɗema kakansa mota da kansa, sai da ya shiga ya maida ya rufe sannan ya zagaya inda Sadiq shima ya buɗe masa. Kasancewar tun fitowarsu Jay ya bama Sadiq address ɗin inda suka nufa sai kawai kaka da jika suka cigaba da hirarsu, yayinda Sadiq keta aikin tuƙi abinsa.
Tun a farkon shigowa layin Sadiq yay tambayar gidan Malam ɗan inna. Kasancewar sanannen gidane kuma anga mota mai ƙyau dan danan suka samu rakkiya har ƙofar gidan. Gidane irin da ɗin nan, dan daga ƙofar gidan zaka iya kallon babban zaure dake da ƙatan murfi ja wanda wahaka ta sakashi komawa mai roɗi-roɗin baƙi. Sadiq ne kawai ya fita, cikin alnajiran dake zazzaune bisa dakalin gidan wasu na karatu wasu na rubutu a alluna wasuma hirarsu sukeyi ya ƙarisa. Duk idanu suka zuro masa, ya ɗaga musu hannu alamar sannu sannan yace, “Ƙannena dan ALLAH ko malam ɗan inna na nan?”. Babban gardi dake karatu da sauri-sauri tamkar zai haɗiye harshensa ya dakata yana kallon Sadiq ɗin. “Malam baya nan, amma ba nisa yayiba”. Sadiq dake saurarensa yace, “To masha ALLAH, dama baƙine muke tare dasu gasu a mota, idan babu damuwa ko za'a aika wani ya kira mana shi ne?”. Gardin baice komaiba ya gyara zaman allonsa ya sakko daga dakalin, zauren gidan ya shiga, babu jimawa sai gashi ya dawo. “Ku shigo” ya faɗa kawai yana kallon Sadiq. Sadiq baice komaiba ya juya ga motar, a saitin Jay yay knocking glass ɗin, Jawaad da gaba ɗaya hankalinsa na'a tattaunawa da Alhaji babba ya juyi tare da sauke gilashin motar. “Oga yaronsa yace baya nan amma bai nisaba, yace kushiga ciki inaga zaije ya kirashi ne”. “Okay” Jawaad ya faɗa a taƙaice yana maida kallonsa ga Alhaji babba dake saurarensu.
Kusan a tare suka fito, a take dukkan almajiran dake wajen suka zubo musu idanu, sannu kawai suke musu babu batun gaisuwa, su dai suka shige cikin zauren dake ƙaton gaske, sai dai ko'ina mulmule yake da suminti, sai alluna masu yawan gaske dake jijjingine da kowacce kusurwa ta bangon zauren. Zama sukai a tabarmar da aka shinfiɗa, Sadiq dai dama bai biyosu ba sai Gaddin nan kawai. Saida yaga sun zauna sannan ya shige wata ƙofa alamar cikin gidanne, babu jimawa sai gashi ɗauke da kofin silba babba. ya ajiye a gabansu sannan ya gaishesu. “Bara naje na kirashi yana nan ƙasan layi suba wata mata mara lafiya”. Alhaji babba ne kawai ya amsa masa, ahi Jay ma dai kallon Gaddin yake cike da nazari.
Kusan mintuna talatin da fitar gaddin nan sai gashi ya dawo tare da Dattijo, daka gansa kasan akwai wahalar rayuwa tattare da shi, dan tsufan nasa yafi shekarun yawa a zahiri. Tun shigowarsa Alhaji babba ya shaidashi tsaf, dan kamanninsa na ƙuruciya duk suna a tare dashi, ya ɗan murmusa yana sake girmama buwayar UBANGIJI.
Sannu da zuwa shi dai malam ɗan inna keta zuba musu, ya zauna saman buzunsa dake fuskantar su Jawaad, shima dai kallon sani yakema Alhaji babba, sai dai ya rasa a ina yasan fuskar ne?. Hannu ya fara bama Alhaji babba suka far gaisawa, sannan ya miƙama Jawaad shima suka gaisa. Cikin ɗan tsantseni yace, “Sai dai kuma ban gane baƙin nawa ba duk da ina musu kallon sani sai dai na rasa a ina?”.
Murmushi Alhaji babba yayi yana gyara zamansa, yace, “To bazan musa makaba, sai dai nasan ƙila kamanni kake gani kawai. Da farko dai sunana Nuhu. wannan jikanane sunansa Jawaad, munzo neman wani bawan ALLAH ne mai suna Adamu”.
Malam ɗan inna ya kafe Alhaji babba da kallo, dan yanzukam ya gano ta inda ya kema Alhaji babban kallon sani, to amma abin tambaya shi wanene? Haɗiye wannan tambayar yayi a ransa, a fili yace, “To Adamu dai biyu ke garemu, ɗaya muna kiransa Ado, yanzu haka yana can balaguro kudu damu, shiɗin babban ɗanane, yanada iyalinsa duk suna man cikin gida tare damu, sai kuma ɗan ƴar uwata shima sunansa Adamu, amma ana kiransa Adamu makaho, shikam dai ALLAH yay masa rasuwa shekara kusan ta takwas kenan, matarsa ma ta rasu kafin shi”.
Su jay suna jira suji yace yana da ƴa sai sukaji yay shiru.
Alhaji babba daya haɗiye mamakinsa ya gyara zama yana faɗin, “Masha ALLAH, mu munzo neman Adamu makahon ne, ashema ALLAH yay masa rasuwa?”. “Tabbas ya rasu dalilin mota data bigesa”. Ƙwallar data cika idon Alhaji babba yasa bakin rigarsa ya share yana ɗan murmushi, “ALLAH ya gafarta masa shi da matar tasa”. Amin ya rabbi, da Alhaji ɗan inna suka faɗa a tare.
“Mahaifiyarsa fa ko ita tana raye? Sannan shi baibar zuri'a ba ne?”. Alhaji babba ya faɗa cikin ƙarfin hali.
Alhaji ɗan inna ya jinjina kansa, “Mahaifiyarsa ta jima da rasuwa, dan dalilin jinyane ma ya maidota gida saboda shekaru da dama ba'asan inda takeba ita da ɗan nata, sai kawai rana tsaka muka ganta tare dashi, adalilin jinya ya matsa suka dawo gida, dan shi makanta ta samesa ta idi ɗaya tun ƙuruciya dalilin ƙyanda, to ganin inda suke babu mataimaki sai ALLAH ya matsa mata harta faɗa masa tushenta suka dawo, kowa ƙin yarda ta raɓesa yay a cikin dangi, sai nine na bata masauki a gidana, na kuma riƙe shi Adamun tamkar sauran ƴaƴana har nai masa aure, bayan aurensa da shekara kusan huɗu ALLAH yay ma yaya Sa'a rasuwa. Shi adamun da anan cikin gidan nawa suke zaune shi da matar tasa mai suna Asiya, itama tanada nakasar ƙafa dan gurguwa ce. Daga baya kuma sai suka tashi”.
Kafin Alhaji babba yay magana Jay yay saurin faɗan, “Miye dalilin tashin nashi? Sannan kuma basu da yarane? Naji baka amsa wannan tambayarba”.
Malam ɗan inna yaja fasali yana sake gyara zamansa a karo na babu adadi. “Mudai a saninmu Adamu baida wasu ƴaƴa, amma kuma al'amarinsu dalilin wata ƴa ƙwallin ƙwal yazo ma mutane da ruɗani musamman lokacin da tai girma kamanninta da nashi suka fita. Tun aurensa da Asiya bata taɓa ko ɓatan wata ba a gidanan, danni da kaina nan nasha basu taimako akan hakan ko za'a dace, amma har bayan rasuwa yaya Sa'a da kusan shekaru uku babu wani bayani daga matarsa, hakanne ya saka muka fara masa kwaɗayin kozai ƙara aure. Amma ya murje idonsa yace baisan wannan zanceba shi yana son matarsa. Munta lallaɓashi akan inma kuɗin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login