Showing 309001 words to 312000 words out of 388641 words

Chapter 104 - KWAI CIKIN KAYA

10 Sep 2025

20730

da jini, ji yake a duk duniya yau babu kamarsa a cikin masu nasara, jinsa yake tamkarma su kaɗaine a cikin duniyar babu wani mahaluki mai numfashi da ya rage bayansu ɗin, wani sanyi mai sanyaya kuzari na shiga cikin tsokar jikinsa tana ratsa dukkan ɓargonsa da jijiya.
Cikin dasashshiyar murya Umm-Anum tace, “Tabbas niɗin na taɓa aure, bankuma taɓa tuna hakanba sai a daren jiya, na auri wanda yake matsayin yayana a gidanmu dukda ba iyayenmu ɗaya ba, matar babanmu ce da ya aura bayan rasuwar innarmu ce mahaifiyarsa, itama kuma mijinta ya rasune, shine iyayenmu sukai aure, suka kuma haɗemu suka riƙe tamkar tare suka haifemu, Auren soyayya mukayi da Abdul-aziz, shiɗin mutumne mai himma wajen neman nakansa, sannan mutumne mara hayaniya da damuwa da gudun ƙyale-ƙyalen duniya, mutum ne ma'abocin son noma da kiwo, mai tsananin son ƴan uwa da zuminci, shine auta a gidansu kaf, shi kaɗai kuma mama maryam ta haifa a gidan, baida wa baida ƙani dan haka yay mana gata sosai ni da ƙannena lokacin da mahaifiyarsa ta dawo aure gidanmu. Bayan aurenmu mun samu jarabawar rashin samun haihuwa na tsahon wasu shekaru harma dana abubuwan more rayuwa, kafin na fara haihuwar kuma yaran su rasu, sai daga baya harma mun fidda rai da wata haihuwar sannan ALLAH ya azurtamu da samunsa (ta nuna Jawaad) lokacin da muka samesa Abdu-aziz ya bunƙasa, dan harkokinsa na noma da kiwo sun kaisa har ƙasar turai dalilin zaman mutunci da wasu turawa da sukai aikin dam ɗin ƙauyen garinsu, abinda kawai zan iya tunawa bayan wannan game da rayuwata shine, sunana BILKEESU, sai mahaifina, sai ƙannena uku mata, Mariya, Rahmah, Wasila, sai Mama maryam, saiko shi dana bari, sai Abbansa dana tabbatar ya rasu, wannan shine kaɗai abinda zan iya tunawa game dani da rayuwata ta baya kafin gushewar komai”. Ta ƙare maganar hawaye na ziraro mata.
Jawaad da shima ke hawayen ya saka hannu ya share mata yana girgiza mata kai alamar ta bari, muryarsa a ɗashe yace, “Na godema ALLAH da yasa kika tunani Ummuna, na kwana da tsananin fargabar kar kice baki tunani ba koma baki sanni ba gaba ɗaya, da hakan ta kasance na tabbata sai dai ku binne gawata a yau Ummuna, na godema ALLAH da yasa kina raye, na godema ALLAH da ya ƙaddara sake haɗuwarmu a duniyar nan, na godema ALLAH daya jarabceni da son wadda ta silarta yau nake a jikinki Ummuna, (yay maganar yana nuna Bilkisu) na godema ALLAH daya haɗa dangantakarta da zuri'ar Takawa har nima nakai ga zuwa garesu, su ɗin shugabannine da adalcinsu yakai kowanne yanki, kowacce ƙabila, suyi fatan zamowa masu mulkinsu Ummuna, mutanen nan uku haskene babba a gareni da suka haskamin hanyata zuwa gareki”.
Share masa hawayen shima tayi tana miƙama Bilkisu dake kuka hannu alamar itama tazo, da ƙyar BILKEESU ta miƙe zuwa garesu tana haɗa hanya, Umm-Anum ta sakata a jikinta tana maijin ƙaunarta har ƙarƙashin ruhinta, “Ɗiyata ashe ƙaunar da nake miki tun ganinki na farko bata wasa bace, ALLAH yay miki albarka kinji, ALLAH ya ɗaukaka rayuwarki ya saka mata albarka ya baibaiyeki da alkairi da rahamarsa mai tarin yawa”. Gaba ɗaya falon aka amsa da amin.
Ummu dake murmushi tace, “Haka rayuwa take, ƙanƙanin abu sai yazama silar warware babba, kunga dai yanda aka ɗauki tsahon shekaru wajen addu'oi da neman ahalin Umm-Anum, amma sai gashi cikin sauƙi Wallet ta zama silar komai......” Ta shiga bama su Umm-Anum labarin komai game da haɗuwar Bilkisu da su Safah a Ladies mirror, da dagewar Safah akan saita tafi da Wallet ɗin bilkisu masarauta, har silar komawarta hannunsu...
Sosai al'ajabi ya kama su Umm-Anum sukaita sake jinjina al'amarin da girmama hukuncin UBANGIJI mai shirya yanda yaso a lokacin da yaso ga wanda yaso cikin hikimarsa.
Duk godiya suka shiga sake jera ma su takawa da addu'oin fatan alkairi, dasu Abbu ma kansu suma har saida takawa da Abbu sukace ya isa haka sannan. Akwai sauran magana sosai a bakin Takawa dan ya fahimci akwai wasu abubuwan da yawa dake a ɓoye wanda Umm-Anum bata iya tunawa ba, shima kansa Jawaad dai akwai magana a bakinsa musamman game da haukar mahaifiyarsa da abubuwa ma da dama, sai dai yayi shiru ya barma ransa, so yake ya samu nutsuwar zama sake nazari da fashin baƙi akan komai, su kuma keɓe da matarsa su tattauna kozai ƙara samun haske daga gareta dan kowa da irin baiwarsa. To yanda duk tunaninsu yake hakama na Abbu da Abu-Siddiq yake, su kuma sunason su keɓe ne da Jawaad sumasa tambayoyi game da family ɗinsa, dan sunji Umm-Anum bata tambayi komaiba akan komai ma, alamomi da yawa kuma sun nuna akwai abinda ke binne, bazasu fahimci hakanba sai sun sami sanin ainahin tarihin komai tun daga tushe sannan.

Kiran sallar zuhur ne ya tashesu daga wannan zama, matan suka shige cikin gida sukuma mazan suka fita massallaci.
Bayan an idar suka dawo akaci abincin rana, Jawaad dai tsakura yay tayi yanzun ma, baici na kirki ba, hakama Bilkisu, Umm-Anum da take jinta sakayau yau tanata lura dasu sai dai batace komaiba har aka kammala aka tashi.
Takawa, Abbu, Abu-Siddiq suka fice masaukin su takawa dan su masa rakkiya yaje ya huta. Bilkisu kuma Umm-Anum ta tsareta ta kwanta barci, acewarta yanayin bily ya nuna barci takeji, kasa mata musu tayi ta kwanta, itako ta ɗaura kan bily saman cinyarta tana shafa mata kai har barcin mai nauyi kuwa yay awan gaba da Bilkisun, Anum dake ta tsegumi Umm-Anum tabar yayinta itama tazo ta raɓa bayan Bilkisun ta kwanta da yake a ɗakin Umm-Anum ɗinne. Ummu da Aunty Mahfuzah kuwa sun tafi can gidan aunty Mahfuzah ɗin suma.
Anuwar da Jawaad kuwa suna can sashen baƙi suma, Anuwar ya tsare Jay akan ya bashi labarin Abban su, sai shagwaɓa yake masa. Jawaad dake kwance cikin doguwar kujera yay murmushi idanunsa akan Anuwar dake zaune a ƙasan darduma jikin kujerar da yake a kwance hannunsu sarƙe dana juna. Cikin muryarsa dake a sanyaye yace, “Dear nima bansan Abba ba sosai, abubuwan da zan iya tunawa game da shi basu da yawa, dan banfi shekara bakwai ba ya rasu, sai dai kakanrmu mama maryam bata gusaba sai da ta maidamin tarihinsa tamkar karatu, dan sai da na haddacesa a cikin kaina tsaf, daga ni har kai da shi muke tsananin kama, musamman ma kai daka biyo har hasken sa, abubuwa ƙalilanne muka ɗakko Ummuna. Inada videos da dama da akayi lokacin da yake shugabancin ƙasarmu, ta hakane nakejin kamar na rayu da shi rayuwa mai tsaho...........”
Da sauri Anuwar ya ƙara ƙanƙame hannun Jawaad dake a cikin nashi yana faɗin, “Suna tare da kai yanzu?”. Murmushi Jawaad yayi ya kai hannu ya shafi kan Anuwar, “Da ganinka ɗan karan gaggawa ne da kai da rashin haƙuri yaron nan”. Yanda yay maganar da jan hancin Anuwar a ƙarshe ya saka Anuwar ɗin ƙyalƙyalewa da dariya, shima Jay murmushin sa ya sake faɗaɗawa yana maijin daɗin ganin Anuwar ɗin cikin nishaɗi. Wayarsa ya ɗauka ya lalubo folder da ta kasance duk hotunan Umm-Anum ne da Abban su sai shi. Miƙama Anuwar yay, jikinsa har ɓari yake wajen son amsar wayar abin tausayi, kallo ya shigayi yana hawaye sosai, hakan yasa Jawaad lumshe idonsa yana haɗiye abinda ya tarar masa a ƙirji na tausayinsu musamman ma Anuwar ɗin. Saurin buɗe idanu Jay yayi danjin yanda Anuwar ya fashe da kuka, ya kafesa da ido shima yana ƙoƙarin danne tasa zuciyar, “Haba my sweet Darling kamar ba namiji ba, kukan ya isa haka kaji lilly na”. Yay maganar da tashi zaune ya rungume Anuwar ɗin yana mai shafa masa baya, har saida yaji yayi shiru ya koma sauke ajiyar zuciya sannan ya barsa. Labarin ahalinsu da mahaifinsu ya cigaba da bashi cikin kulawa, wani gurin Anuwar yay kuka wani gurin yay dariya, haka suka kasance har akai kiran sallar la'asar, wanka Jawaad ya sakeyi da gaggawa suka fita massallaci.
Umm-Anum ma ta tada su Bilkisu sukayi tasu, bayan sun idarne ta saka mai aikinsu ta kawo abinci, zaunar da Bilkisu tayi tana faɗin, “Zauna na baki abincin nan da kaina, kwana biyu da zuwanku duk kun fara ramewa ke da mijin naki saboda rashin cin abinci, ina dalili”. Murmushi nayi cike dajin kunyarta, yanda take ƙoƙarin yin hausa sai abin keban dariya dan hausar kamar bata bahaushiya ba, wani wajenma kakarewa take ta kasa faɗa.
Duk yanda nakejin kunyarta haka na ringa amsar abincin da take bani da hannunta, sallamar su boss ta sakamu maida hankalinmu garesu, idanunsa a kaina dan haka nai azamar ɗauke nawa na maida ƙasa. “Kaima zo ka zauna” Umm-Anum ta faɗa idanunta akan Jawaad dake kallonsu cike da sha'awa dajin daɗi. Hannunsa ta riƙo ta zaunar ɗayan gefenta, ta ɗiba abincin takai bakinsa, “Haa!” ta faɗa kamar yanda akema yara. Ƙwallane suka cika idanun Jawaad ya buɗe bakinsa a hankali ta zuba masa, taunawa ya shigayi yana kallon yanda take sakama Bilkisu itama, gabansu Anuwar yazo ya durƙusa shima ya buɗe baki wai a basa. Umm-Anum ta zuba masa tare da dungure kansa. Anum ma zuwa tai ta tsugunna tana faɗin, “ALLAH nima sai an bani to, anma manta dani kamar banice autar ba”. Sosai abin ya bama Jawaad nishaɗi, su Bilkisu suka shiga yima Anum dariyar tsokana.
Hannunsa Jay ya ɗauraye, shima ya ɗiba ya kai bakin Umm-Anum, amsa tai tana murmushi ta shafa kansa da ƙoƙarin haɗiye hawayen da suke neman taho mata, murmushi Jay yayi ya ɗiba ya bama Anuwar shima, sannan ya bama Bilkisu da kunya ta kusan halakawa, Anum itace ƙarshe. Daka gansu kasan suna cikin farin ciki mai tsanani.
Haka suka ƙarasa wannan yini tare, har zuwa dare dan Abbu yau a gidan Uwargidansa ma yake ba nanba, hakan ne ya ƙara bama Umm-Anum damar sakewa da ƴaƴanta har dare ya farayi, daƙyar ta daure tace suje su kwanta haka nan gobe idan ALLAH ya kaimuma ranace ai. Da wannan kowa ya nufi makwancinsa badan sun gaji da kasancewa tare ba.



Sai da muka gama shirin barci muka kwanta, ina jikinsa a lafe kamar wata mage yana shafa bayana a hankali, fitar numfashinmu yana dai-daitane da sautin bugun zuciyarmu, “Miema kinyi barci?” ya faɗa a hankali cikin kunne na. Kaina na girgiza masa da ɗago fuskata dake cikin ƙirjinsa na kalli fuskarsa, shima kallona yakeyi. Murmushi mukaima juna, ya ɗan sumbaci goshina kafin ya sake maida idanunsa cikin nawa. Maida nawa nai na lumshe dan nakasa jurar cigaba da kallon cikin idanun nasa. Baice komaiba sai sake turani da yay jikinsa ya rungume da ƙyau. A haka barci yay awon gaba damu.
★★★★★★★
Mun cigaba da kasancewa a cikin Saudia tare dasu Umm-Anum cike da tsaftatacciyar soyayya da tarin ƙauna mai daraja daga garesu, tattalinmu take tamkar wasu ƙananun yara ni da boss, yayinda a koda yaushe ƙannensa ke nane da shi, yanayin waya sosai dasu Oga Hafiz musamman akan aikin da a yanzu mukasa gaba na ƴan fyaɗe, a yanzu haka dai su Jabeer suna ƙoƙarin miƙa wasu samari kusan goma sha uku kotu akan case ɗin fyaɗen, sannan sunce sun samu case huɗu masu kamanceceniya da nasu Amina. Duk da muna nan saudia muma aikin mukeyi musamman ma boss, danni wataranma A wajen Umm-Anum nake yini komu tafi makarantarta. Har gidan Uwargidanta an kaimu, abin ya birgeni sosai yanda aka tarbemu tamkar ba kishiyoyi ba, a raina nace ‘kaga inda ake kishin ilimi, ba irin na ƴan ƙasarmu ba na hauka’.
Randa muka cika kwanaki bakwai a saudiya boss ya fara samun kira daga wajen aiki, dan mun wuce ƙa'idar kwanakin da aka bamu na hutu, duk yanda yake da son aiki da ƙwazo saina fahimci bayason komawa yanzun, nima dai bason komawar nakeba sam, amma yaya zamuyi hakan tilasne a garemu kodan ɗunbin ayyukan da muka baro.
A ranar yayma Umm-Anum magana akan binmu, sai dai abin mamaki da al'ajabi a take ta nuna ɓacin ranta akan bazataje ba, shiru mukai kawai duk muna kallonta, yayinda fuskar Boss da Anuwar ta nuna tsantsar ɓacin rai akan hakan. Kafin suce wani abu akan hakan Abbu yaja hannunsu suka fice daga gidanma gaba ɗaya.
Wannan al'amari ya tsaya min a zuciya, dan yinin ranar gaba ɗaya wuni Umm-Anum tai cikin ɓacin rai, yayinda na yini nikuma cikin nazarin komai da fashin baƙi a kai.
★•°•★°•°★•°•★°•°★•°•★
A ɓangare su Jawaad suna fita daga nan wucewa Abbu yay dasu masaukin takawa, tattaunawa suka shigayi game da abubuwa masu dama, Abbu yace, “kuyi haƙuri kubar ɓacin rai kunji, itama ba laifinta bane, babu yanda za'ai taƙi son zuwa ƙasarta kodan shekarun data ɗauka bata cikinta, al'amarin bai baku mamakiba yanda har yanzu bata iya tambayar kowa daga ahalin nata ba, tunfa washe garin zuwanku har yanzu bamu sake zaman tattauna komaiba, tama ƙi ƙara nuna tana buƙatar jin komai, hatta da yanda ka rayuwu bayan barinta gida bata tambayeka ba Jawaad. Wannan babban al'amarine daya dace ace an zauna anyi dogon nazari a kansa. Shi sihiri a jikin ɗan adam abune mai wahalar yakicewa, musamman irin nata da ba'asan dalilinsa ba ma da sarƙaƙiyar sa, shifa mai sihiri baya gajiyawa da ƙoƙarin ɗaura wani akan wani, dan ya riga yayi imani da yin wannan shirkar itace ƙarfin ikonsa, har yanzu akwai sihiri tattare da mahaifiyarku, wanda inaji a raina akwai wani abu da aka binne wanda saimun tonosane komai dake jikinta zai iya warwarewa harmu fuskanci matsalar gaba ɗaya, bakuma wai dan addu'oin da muke basa ƙarɓuwa bane, ita rahamar UBANGIJI da kariyarsa bata taɓa gushewa ga wanda ya dogara da shi kuma yayi imani ya riƙe gaskiya, gaskiyar ɗan adam bata taɓa ƙarewa sai dai ace ƙaryar wane ta ƙare, dan haka mucigaba da bin komai mataki-mataki insha ALLAHU komai zai zama labari ne, Jawaad idan babu damuwa ka bamu haske dangane da family ɗinku ko zamu samu wani haske”.
Duk sun gamsu da maganar Abbu, dan haka Jay ya shiga basu tarihin rayuwar mahaifinsa da Umm-Anum kamar yanda kakarsa mama maryam ta shaida masa komai bata ɓoye masa ba. Ya cigaba da faɗin, “Ban taɓa zargin kowa a zuri'ata game da iyayena ba, dan babu wani alamun cutarwa dana taɓaji ya shiga tsakaninsu da mahaifina harya bar duniya, sai dai maganar gaskiya lalurar hauka da Ummuna ta gamu da shi a ranar rasuwarsa abin tambaya ce, ada ban taɓa ɗaukar hakan komaiba sai kwanannan da matata tai wata magana data kasa barin raina, na cewar a al'amarin Ummuna akwai alamomin sihiri, dan mutuwar Abba bai kai ace ta kasa jure ƙaddara ba har ta kaita da ciwon hauka, ciwo ma irin wanda mutum baison zaman gida, bayan duk musulmi yasan mutuwa wajibine ga mai rai. Abinda kuma naji daga gareku a yau da wanda ya faru ranar ya tabbatar min akwai abinda bamu saniba dake a ɓoye tabbas”.
Abbu ne ya sauke ajiyar zuciya yana gyara zamansa, yace, “Tabbas kamar yanda ka faɗa Muhammad akwai ababen tambaya masu yawan gaske akan al'amarin, ko sunanta sai a jiya na taɓaji, kai tsaye bamu da damar zarigin kowa akan wannan al'amarin, musamman idan mukai dubu da marigayi yayi shugabanci na ƙasa, ƙasarma babba irin taku, bazai yuwu ace baida maƙiyaba koda kuwa suna a kusa da shine. Sihiri gaskiyane, hakama addu'a waraka ce, sai dai wani lokacin sai kaga kamar ka ɗauki lokaci kana addu'ar babu biyan buƙata, ba haka bane, UBANGIJI maijin kukanmune a koda yaushe, mai kuma magance mana damuwarmu ne a koda yaushe, wani lokacin ita addu'a idan kayita takan jinkirta da ga abinda ka roƙo a kansa, saita zama kariyane ga wani al'amarinka ɓoyayye da kai kanka baka san da shi ba, mahaifiyarku ta jima cikin wani hali na jarabawa, mun kuma ɗauki lokaci muna gayama UBANGIJI, bamu taɓajin mun ƙosa ba, domin mun tabbatar shi kaɗaine mai badawa, yana jinmu, kuma yana ganinmu, yana kuma sane damu, jinkirtawar warwarewar komai ba yana nufin bai karɓi kukanmu ba. a yanda kuma nakeji a raina addu'armu ta kasance da kai, kai kanka, dan duk waɗanda suka iya tauyeta kaima abune mai sauƙi su ɓaddaka, inaga damuwa akan saita biku ba shine ya kamata ba, bincike akan ainahin miya faru shine ya dace domin mu samu bakin zaren, dan ko Anuwar bai kamata ya biku ba”.
Kallon Abbu Anuwar yayi cikin tsagwaron tashin hankali, kafin yace wani abu Takawa yace, “Wannan tunanin shine a raina nima Abu-Sufyan, Anuwar kayi haƙuri kaji, indai ƙasarmu ce zakaje ka rayu har saika gaji ma, amma ba a irin wannan lokacin ya dace ba, dan abubuwa da yawan gaske na zuwarmin a zuciya game da al'amarin nan, sai dai banason furta komai nafison matsayin Jawaad na jami'in tsaro shi yay wannan tunani, zuwan Umm-Anum da Anuwar ba shine abu mai muhimmanci ba a yanzu ƙwarai da gaske, dan komai ma zai iya faruwa inhar azzaluman da suka ƙulla al'amarin suna tare dasu ne, kai koma nesa da su suke suna bibiyar al'amarin komai dan nima nayi makamancin wannan rayuwar nasan sarƙaƙiyar cikinta, amma kai Jawaad minene a ranka?”.
Zama Jawaad ya gyara cike da kaifin basirar da ALLAH ya azurtashi da ita shima yace, “Na gamsu da duk abinda kuka faɗa, dan nima a kwanakin nan sune suka zama abin nazarina, rashin tambaya ta komai da Ummuna batai ba yafi komai tsayawa a raina sosai, ni a yanzu shirina na farko shine lallaɓata naji waɗanda sukai rayuwa dasu kamar ma'aikatan gidan da sauransu”.
“Tunani mai ƙyau” cewar Takawa da Abu-Siddiq. Jawaad ya cigaba da faɗin, “Sai abokai makusanta da Abbah ya rayu da su kafin shigarsa siyasa da hawansa mulki, abu na uku ne bamu da dama a kansa, dan a wajen Ummuna ne kawai zamu iya jin wasu sirrika game da rayuwar Abba da ƴan uwansa a lokacin da yake mulki, dan haka wannan na ajiyesa gefe zanyi anfani da waɗancan damar guda biyu mugani ko za'a dace, amma nima na gamsu da basai sun bimu ɗinba kam yanzun”.
“ALLAH yay maka albarka” cewar Abbu yana dafa kafaɗar Jawaad dake a kusa da shi. A tare suka amsa da amin. Abbu ya cigaba da faɗin, “Nima nanda sati guda zan biyo bayanku dan inason ganawa da Abba (Alhaji Babba). Kai Jawaad ya jinjina masa yana ɗan murmushi da faɗin, “ALLAH ya tabbatar Abbu”. Da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login