Showing 129001 words to 132000 words out of 388641 words
nai uban tagumi harta dawo.
Na miƙa mata kayanta, ta amsa tana min godiya, harta tafi sai kuma ta dawo da baya idonta a kaina.
“Ƴar uwa kozaki taso muje muyi sallane? Naga kowa na harama amma ke koma motsi bakiyba, ko dai kina hutune?”.
Murmushin yaƙe naimata, sai dai ban motsaba, nace, “Karki damu zan nema waɗanda mukazo tare sai nayi a wajensu”.
Tai ɗan shiru tana kallona, kamar bazata tankaba, dan harna fara murnar ta barni, sai na tsinkayi muryarta tana faɗin, “Yanda mutane ke cike a gidannan kafin ki ganosun ai kin wahala, sannan duk inda zakiy salla a gidannan yau bazai kai nutsuwar inda zamujeba, dan sashen yaya ne kawai nasan babu mutane, indai ba kina tsoron karna saidaki bane”.
Ta bani dariya, amma sai banyiba saboda yanayin da ake ciki, sai kawai na miƙe batare danace komaiba, dan na lura akwaita da surutu.
Tun shigowarmu sashen na yarda da zancenta, dankuwa tsit yake babu wata hayaniya anan, tamjar ba cikin gidan yakeba. Sai wani daddaɗan ƙamshi daya shige mini hanci, batare dana shiryaba na shaƙa na haɗiyeshi cikin maƙoshina, karon farko a rayuwata da naga falon da yafi na gidan Dad ƙyau da tsari, ada tunanina yana bani babu gidan da yakai na Dad haɗuwa da tsaruwar kayan alatu, dan dukkan gidajen iyayen su Ummie basu kai na Dad ba, amma a yau dana tsinci kaina cikin wannan aljannar duniyar duk sai na raina wancan alfaharin nawa, yanda aka ƙawata matattakalar benen dake falon kawai abar kalloce ga mai kallo duk wayewarsa kuwa. Ban gama bama idona abinciba budurwar taja hannuna zuwa wani ɗaki, mun iske mutum uku suna salla, sai ɗaya data fito daga bayi da alama alwalar itama tayo, sai wata kwance a kan gadon dake ɗakin da yara biyu suna kallon waya. Duk suka zubomin ido na rashin sani, wadda ta fito daga bayice tace, “Wai ina kikajene haka Nabeelah? an aika Ammar ya kiraki amma yace bai gankiba”.
Hannuna ta saki tana saɓule jakkarta dake a kafaɗa, “Babu inda najefa Aunty Hanifah, ina can jikin sashen Uncle Sulaiman zaune, nima yanzu saida na leƙo naga kuna nan sannan ai na taho”.
Batace mata komaiba, hakanne ya sakani gaisheta dan naga babbace ta girmeni, na juya ga wadda ke a saman gadon tare da yara itama zan gaisheta sai tai saurin gaisheni. Murmushi kawai nayi, dan ita zan iya girmarta, suma yaran sai suka gaidani, na amsa musu da kulawa ina tambayar sunayensu. Namijin yace Ammar, macen kuma Islam. Yaran sun birgeni, gasu masu ƙyau. Wadda muka shigo tare da aka kira da Nabeelah ce tace min na shiga bayin nayo alwala, cikin tsokana take faɗin “Karnayi abin kunya gashi bansan sunan ƙawar tawabama”.
Ƴar dariya nai babu shiri, ina ƙoƙarin shigewa nace mata sunana Bilkisu. A tare naga duk sun kalleni suna ɗora hannu a bakunansu, hakama biyu a masu sallar da suka idar suma suka juyo suna kallona. Yanda naɗanyi diri-diri na alamar shakkune ya saka ɗaya a cikin waɗanda suka idar da sallar babbar mace tai murmushi da cewa “Mai babban sunace ashe”. Numfashi na sauke a hankali kafin na gaisheta cikin risinawa, ta amsamin tana sake faɗaɗa dara'ar fuskarta, kafin tace naje nai alwalar kar lokaci ya ƙure. Shigewa nayi bayin nima da tunanin ko sunan waye nasu Bilkisun? Daga gani kam dai suna girmama mai sunan sosai.
Ina fitowa Nabeelah ta shiga, suma duk sun tashi daga abin sallar alamar sun bamu waje, sai wadda muka iske tayo alwala kawaice ke salla a wajen, na gaida sauran biyun da bamu gaisaba suma sannan na kabbara sallata.
Bayan mun idar da sallar a cikinsu babu wanda ya tambayeni game dani, sai dai sunata ƙoƙarin sakoni cikin hirarsu wadda duk ta karkata ga mai irin sunana danaji manyan na ambata da Yaya Bilki, yaran kuma na kiranta Mah-mah Yanda suke hira akanta cikin damuwa da kewane ya sakani tunanin ko bata da raine? Bani da mai bani wannan amsar, dan haka na haɗiye abina cikin rai ina cigaba da saurarensu....
Kusan mintuna talatin ina sauraren hirarsu mai cike da birgewar kasancewarsu ahali ɗaya, kafin na miƙe domin tafiya, dan ya kamata naje na binciki inda su Mom suke koda su basu damu da nemanaba.
Duk kallona sukai cike da alamar tambaya.
Murmushi nayi, nace, “Zanjene kar abokan tafiyata suyita nemana”.
Suma duk murmushin sukaimin, Nabeelah ta miƙomin wayarta tana faɗin, “To sakamin Number ki muke zuminci, danni dai nayi ƙawa daga yau”. Ban musaba na amsa wayar tata fuskata har lokacin da murmushi, na saka mata Number ta ina miƙa mata wayar, wadda naji suna kira Aunty Batool tace, “Lallai kin jajubarma kanki kuma Ummien mu, dan shegen surutun Nabeelah takai a guji ƙawance da ita, gaki keman daga gani bakida yawan magana”.
Sanin dani take yasani faɗin, “Aunty ai sunfi daɗin ƙawance irinsu Nabeelah”.
Atake kowa ya shiga faɗin a'a-a'a, yayinda Nabeelah keta ƙoƙarin kare kanta, niko ina musu dariya. Godiya na sake musu kafin nai musu sallama.
Zuciyata tai wani irin harbawa lokacin da akai knocking ƙofar ɗakin tare da sallama cikin wata irin sassanyar murya dake nuna mai ita yana a matuƙar gajiye, tattare da tsagwaron damuwa. Akusan tare suka amsa, nikuma na janye hannuna dana ɗora akan mariƙin ƙofar cike da fargaba, ban gama tattara fahimtata waje gudaba aka turo ƙofar aka shigo, kaɗan ya rage ya bugeni, nai saurin ja baya kaɗan dan na bashi hanya sosai.
Idanunane suka fara sauka akan ƙyaƙyƙyawar ƙafar da baƙin wandon jeans ya sake haskawa, jijjigar da zuciyata keyine ya dasamin tsoron yarda da hasashena, dan haka na kasa ɗago idona naga wanene? Dukda ƙamshin turarensa ya nema saka zuciyata faso ƙirjina ta fito......
Ganin yaƙi shigewa ya bani hanyane ya sakani ɗago idanuna a hankali nakai dubana gareshi, a lokaci ɗaya idanunmu suka shige na juna saboda shima dai-dai ya kalleni. Naɗan sake ja da baya na alamun mamakin sake ganinsa anan, amma shi a mamakina sai naga ya janye nasa idanun babu wani alamar mamakin ganina da ya nuna.
Yanda naji su Nabeelah na rige-rigen gaishesane ya sakani aro jarumta nima nabi layinsu na gaidashi, sau ɗaya ya amsa mana tare da amsa ta'azziyar da mukai masa ya ƙarasa ga iyayensu Nabeelah, hakanne ni kuma ya bani damar saurin ficewa cike da sassarfa daga ɗakin..........
ALLAH ka gafartama iyayenmu .
4 hrs · Public
Save · More
36Bilqeesa Ibraheem Bilyn Abdull Ce:
Alhmdllh inama kowa fatan alkairi, nakumaji daɗin wannan tarba, naso ace zan iya jurewa na biku ɗai-ɗai na amsama kowa Comments ɗinsa, sai dai nace kuyi haƙuri, kamar yanda matsalan ido ta dakatar dani da typing dolene yanzuma na ringa lallaɓawa saboda kunada ɗunbin yawa, akwai group insha ALLAHU da aka buɗe a shafin manhajar Telegram, masu amfani da wannan shafi su maza su garzaya idan suna buƙata, domin canne zai zama dandalin tattaunawa akan littfin ƙwai cikin ƙaya da sada zuminci, duk mai karatu yana buƙatar dandali na tattaunawa akan littafi, dan da yawanmu hakan na bamu nishaɗi da sake fahimtar da mu abinda bamu fahimtaba, kuma yana ƙarama writer ƙarfin gwiwar typing koda batai niyyar hakanba, ku maza kar a baku labari. Zakuna samuna koda yaushe a can domin ku tabbatar ina tare daku, masoyan bily kuma na isar da saƙonku gareta akan ta daina tsoron jay😂, masoyan Shahudah tana miƙo muku gaisuwa itama🤓.
https://t.me/joinchat/TIsXYRvhtri2kQ9E4x7w6g
Wannan shine link ɗin group namu mai suna MASARAUTAR BILYN ABDULL A manhajar Telegram😘😘.
2
..............Koda na fito daga ɗakin saida na huta a falon saboda yanda zuciyata ke mutsu-mutsu a cikin ƙirjina, ina matuƙar mamakin wannan al'amari dake yawan faruwa tsakanina da mutumin nan, na kuma rasa wazan tunkara da maganar halin da nake tsintar kaina akansa kozan samu fashin baƙin saɓanin wanda zuciyata ke kissima min, nidai nasan ba tsoronsa nakeba, to minene dalili? Wannan amsar nake neman mai bani.
Gwiwa a sage naja ƙafafuna na fice daga sashen zuwa harabar gidan. Yanzunma dai ban sami ko ɗaya daga cikin su aunty Aamilah ba, gashi banida Number kowa a cikinsu. Dole na sake nemar guri na zauna inda babu yawan hayaniyar mutane, sai jefi-jefi nakan ɗanga sun gittani.
★★★★★
Yanda Jawaad ya nuna halin ko in kula da ganin na Bilkisu bazaka taɓa tunanin yama santaba, sai dai harta fice daga ɗakin yana kallontane ta wutsiyar ido, acan ƙasan zuciyarsa na raya masa “Ita kuma miya kawota nan?” sai dai a fili bazaka taɓa fahimtar komaiba.
Zama yay a saman ƴar dirowar dake farkon shigowa ɗakin, cikin girmamawa ya gaisa da iyayensa, sukai masa gaisuwar ta'aziyyah tare da jero addu'ar neman gafara ga mamacin, har suka cigaba da ɗan tattaunawa akan rasuwar wadda ta jasu tunowa da rasuwar mahaifin Jawaad ɗin shima da ɓatan mahaifiyarsa.
Haɗiyar zuciya kawai Jawaad yake famanyi, amma bakinsa ya kasa furta komai, daga ƙarshema saiya miƙe yana faɗa musu zaije ya ɗan kwanta, gimba zai kawo musu abincin da zasu ci.
Basu hanashi tafiyaba, dan yanayinsa ya nuna yana buƙatar hutun sosai.
★..::..★
Sai kusan ƙarfe biyar na hangi Mom suna gaisawa da wasu gungun baƙi da sukazo musu gaisuwa, da sauri na miƙe na nufeta karta sake ɓacemin, dan matuƙar gajiya na gaji da zaman ni kaɗai, danma naɗanyi cheating dasu Rebecca ne a group ɗin da muka buɗe iya mu biyar kawai na rage kaɗaici. Daga gefe na tsaya harta gama gaisuwa da mutanen suka tafi kafin na ƙaraso gareta, gaidata na farayi a ɗarare, tunda nasan bani da wata fawa a gareta, amma a mamakina sai naji ta amsa harda tambayata ina na shiga tun ɗazun bata ganniba? wani sanyi ya ratsa zuciyata, kasancewata marainiya ina matuƙar buƙatar kulawar mahaifiya koda kaɗanne, rashin samu kuma na sakani a ƙunci sosai, sai dai ina ƙoƙarin shanyewa ba kowa ke fahimtar hakanba. Cikin girmamawa na bata amsar tambayarta, saita bani umarni akan muje ciki naci abinci.
Ban sake sakashi a idonaba har zuwa dare bayan sallar isha'i da muka fito domin tafiya gida, ƙiri da muzu Aamilah da aunty Shahudah suketa ƙoƙarin zamewa haɗa tafiya dani, duk da basu fito fili sun faɗaba na fahimci haka da kaina, dan kafin nagama kimtsawa harsun fice daga sashen na Mama Atika, sai tare muka fito da Mom, sai muka iske harsun tafi wai tare da Yah Salman.
Banji haushiba, saima murmushi da nayi kawai, driver ne zai tafi da Mom, dan haka nima su zanbi dole. Mom ta tsaya gaisuwa da wasu mata da suma zasu tafi, ƴan gayune sosai da kallo ɗaya zakai musu ka fahimci naira ta zauna musu, nidai bayan na gaishesu jikin mota na koma na
jingina kawai ina kallonsu da mamakin yanda naga Mom ta sake dasu sosai, yanda na santa da wulaƙanci, koda yake masu iya magana kance wata gaban tafi gaban raini ai.
Zuciyata ta motsa da ƙarfi a cikin ƙirjina, hakan ya saka tsoro ziyartar raina, koban faɗaba nasan hakan na nufin Dodona ya kusanto wajen koma yana wajen, zuwa yanzu nafara sabawa da wannan SABON AL'AMARIN namu.
Ilai kuwa ina ɗago idanu akansa na sauke, tsaye yake ɗan nesa damu kaɗan, hannunsa ɗaya cikin aljihun wando, ɗayan kuma ya riƙe waya dake kunnensa, wadda ke nuna alamar yana magana da wanine, ɗan taku yake ɗaya biyu cike da nutsuwa da cikar haiba, ba kayan ɗazun bane a jikinsa, daga wando har rigar jikinsa na yanzu duk fararene tas, gefe wando na duka ƙafar biyu akwai ratsin dogon zare jaa daga sama har ƙasa, sai agaban rigar shima anyi rubutu da ja, hasken dake ƙwanyar a tsakar gidanne ya sani ganin abinda aka rubuta, sai silifas fari shima, sosai kayan sukai masa ƙyau, har na iya kasa janye idona a kansa dukda wutsilniyar da zuciyata keyi kuwa.
Haka kawai Jawaad dake waya da Jabeer yaji a jikinsa kallonsa akeyi, kallon kuma irinna wanda keda kaifin gani da baiwar ƙarfin kwarjinin idanu, duk yanda yaso basarwa tamkar yanda ya saba hakan sai ya gagara, dole ya fara wulƙita nasa fararen idanun kozai samu nasarar cafko wannan mayen idon dake neman saukar masa da gajiya. Karaf kuwa idanunsa suka sauka akanta, shima ƙirjinsa ya motsa alamar harbawar zuciyarsa. Tabbas yaji a ransa itace ke kallonsa, amma a mamakinsa sam idanunta da hankalinta basa kansa, karon farko da miskilancin yarinyarnan ya motsa zuciyarsa, tun ganinsa da ita na farko a airport ya fahimci miskilace ta bugawa a jarida, kasancewar ALLAH ya azurtashi da ilimin karantar hallayyar ɗan adam cikin lokaci ƙanƙani, zuwa yanzu mamakin ganinta yabar ransa, dan ya kula akwai alaƙa tsakaninta da Qaseem.......
“Hello...hello...” Da Jabeer keta ambatane ya sakashi dawowa hayyacinsa, dan tuni ya saki wayar da suke ya kama sabgar bilkisu, abinda bayayi sam a rayuwarsa (wato shiga abinda bai shafesa ba), yaja siririn tsaki yana murza goshinsa da hannunsa daya ciro daga cikin aljihu.
Dai-dai lokacin da Bilkisu ta buɗe gaban mota ta shiga ta zauna, dan Mom harta shige baya itama.
Wani irin harɗaɗɗen numfashi ya sauke har Jabeer na tambayarsa “ko lafiya?”.
Gutun tsaki yaja yana yanke wayar batare daya bashi amsaba, yakuma jan wani tsakin har sau biyu yana takaicin kansa da shiga hurumin da ba nasaba.
___________________________
Washe gari ban biyosuba, dan inama barci suka fice, babu wanda yace a tasoni, nima koda na tashi kuku ke sanarmin sun tafi banji komaiba a raina saima daɗi, tunda nasan zuwana bazai ƙara komaiba koya hana, hasalima banason gamuwa da Dodona.
Bayan na karya ɗaki na koma nai wanka, nai shiri cikin doguwar riga ta atanfa data samu zaunannen ɗinki, bawata kwalliya naiba, nasaka turare sama-sama na fito bayan na yafa ƙarmin gyale.
Kai tsaye gate na nufa wajen baba maigadi dake zaune shida mai bayin filawar gidan suna hira, suna ganina suka shiga gaisheni cikin girmamawa, sam banason hakan da sukemin, dan kuwa niba kowa bace a gidan face maicin alfarma, sannan duk sun girmeni, baba maigadi ma a haife ya haifeni, shima mai bayin fulawar kobai haifi kamata ba nasan yanada manyan ƴaƴa.....
“Hajiya fita zakiyine?”.
Baba mai gadi ya katsemin tunanina, kaina na girgiza masa ina murmushi. “A'a baba ba fita zanyiba, hasalima wajenka nazo muyi magana idan ban takura makaba dan ALLAH”.
Da sauri yace, “Haba wace takura kuma” yay maganar yana miƙewa da sauri, babu jimawa sai gashi da farar kujera, ajiyemin yay gefensu alamar na zauna, mai bayin fulawa kuwa yay mana sallama akan zaije gida yakai cefane.
Sake gaisawa mukai da baba maigadi, yay min ta'aziyyar rasuwar da akayi, nako amsa masa tare da tambayar lafiyar iyalansa, bayan amsamin da yay muka ɗanyi shiru, tunani nake ta ina zan fara abinda ya kawoni garesa?. Zuwa wasu ƴan mintuna sai dabara ta faɗomin, nai murmushi ina sake maida hankalina ga
reshi da kunna voice recorder dan na samu damar kwashe dukkan abinda zamu tattauna nayi nazari a tsanake a kansu.
“Uhm... Baba dan ALLAH niko wata tambayace dani?”.
Fuskarsa faɗaɗe da murmushi yace, “ALLAH Yasa na sani hajiya”.
Murmushi naɗan masa, nace, “Insha ALLAHU inada tabbacin kama sani ɗin”.
Baice komaiba sai hankalinsa daya maido kaina baki ɗaya, nima sai na sake nutsuwa sosai.
“Baba dan ALLAH ko zaka iya tuna ranar da abinnan ya faru da Amina a gidannan da wanda ba'asan ko waneneba?”.
A bazata maganar tazo masa, dan haka kawai saiya hau tari babu shiri. A rikice na shiga masa sannu, na jawo ruwan dana fito dashi daga ciki na miƙa masa da sauri bayan na ɓalle murfin, amsa yay har hannunsa na rawa ya kafa goran a baki ya ɓaɓɓaka, saida yasha kusan rabi kafin ya sauke, idanunsa harsun kaɗa sunyi jajur, sai naji tausayinsa ya kamani, koda ya dawo dai-dai shiru nai ban sake masa tambayarba har tsawon wasu mintuna.
Na sake jeho masa tambayar a karo na biyu, yanzunkam a mamakinawa shiru yay bai tanka minba, sai dai yanata ƴan kalle-kalle tamkar mai tsoron a ganmu ko wani ya jimu. Jin bashi da niyyar bani amsa ya sakani kallonsa, a karo na uku na sake maimaita masa tambayar da sigar kwantar da kai.........
“Ɗi!! Ɗi!!! Ɗi!!...” mukaji horn ɗin mota daga waje, hakanne ya sakashi tashi da sauri ya nufi gate ɗin, na tabbatar dama hanyar da zai gudu yake nema, sai kawai na samu kaina da ƙura masa idanu ganin yanda har yanzu jikinsa ke mazarin rawa.
Hancin motar Dad ne ya danno kai cikin gidan, na sauke ajiyar zuciya ina miƙewa tsaye, saboda tsayawar da driver yayi a saitin da nake zaune, shi kuma Dad ya sauke glass ɗin ɓangarensa yana mani murmushi.
Nima murmushin nake masa ina miƙewa na nufesa, da hannu yaymin nuni nazo, dole nabi motar da direba yaja zuwa ciki inda zaiyi fakin.
Tare da Dad muka shige cikin falo yana tambayata miyyasa banbi su Mom ba can gida?, cikin girmamawa na bashi amsa akan sun wucene ina barci lokacin. Nayi zaton zaiyi faɗa, amma sai naji kawai yay ƙaramar dariya. Mun yada zango a falon ƙasa, ya bani Umarnin naje nasa kuku ya haɗa masa abinci mara nauyi yunwa ya keji, ya fita bai karyabane.
Koda naje kicin ɗin sai ban fitoba na zauna mukayi abu mai sauƙi wa Dad ɗin ni da kuku, dan zuwa yanzunkam Alhmdllh hannuna yay masifar faɗawa akan girki kala-kala na zamani, na gargajiya kuwa dama bani da matsala a kansa, innata tarigada tayi min wannan horon tun ban gama fahimtar muhimmancin girki ga ɗiya mace ba.
Bayan mun kammala nice da kaina na kawoma Dad, lokacin yana waya, na ɗora tiren bisa tebir ɗin tsakkiyar falon na jasa gabansa, buɗe masa komai nayi tare da tsiyaya masa ruwa a kofi sannan na koma gefe na zauna, a haka ya faracin abincin yana cigaba da wayarsa data jashi tsayin lokaci, sai yazam yanacin abincinne kawai a shiririce. Dan harya kammala wayar baici ko kashi ɗayaba bisa uku, ya ajiye wayar yana