Showing 123001 words to 126000 words out of 388641 words

Chapter 42 - KWAI CIKIN KAYA

10 Sep 2025

20717

cemin komaiba.
Shiru na mintuna kusan biyu ya biyo tsakaninmu, ita tana cigaba da tsintar shinkafarta ni kuma ina buɗe littafin da nazo dashi gidan, ɗagowa nai na kalleta, itama sai ta kallenin.
“Amina nazone mu fara magana akan wancan abun da ya faru a waccan ranar, ina fata ban shiga uzirinkiba?”.
Murmushi tayimin, “Kai Bilkisu, ni wane uziri gareni, kimin duk tambayar da kikeso, ni kuma zan baki amsa inhar na sani”.
Kaina na jinjina mata, kafin na jeho mata tambaya, “A waccan ranar da abin ya faru, kowa yana gidan?”.
Shiru Amina tayi na kusan sakanni goma, kafin tace, “Eh to, lokacin dana shiga kowa yana nan, dan kinsan da zaran nayi sallar asuba nake shiga, sai kuma azhar na dawo gida, na koma bayan sallar la'asar sai goma nake dawowa gida, sai idan Alhaji na nanne yakan ce da nayi sallar magriba naje gida na huta, to a waccan ranarma ina idar da salla na shiga gidan, bayan mun gaisa da baba mai gadi ya tsokaneni kamar yanda ya saba, sai na wuce ciki, na fara gamo driver yana wankema Yah Qaseem mota, shima muka gaisa na shige. Ban iske kowa a falonba sai motsin kuku a kicin, na shiga muka gaisa da shi, shima ya tsokaneni tamkar yanda ya saba mukai dariya kafin na fito na fara ƙoƙarin gyaran falo.
Harma na kammala gyarawar ina morping Yah Qaseem ya shigo, duk da bansan lokacin daya shigoba ma dan jinai kawai tamkar kallona ake, shine na juya na gansa tsaye, a ɗan rikice na gaishesa dan bansan dalilin kallonba, shima ya amsa yana wucewa kicin ba tare da ya sake kallon nawa ba. Nai ajiyar zuciya ina cigaba da aikina, harna kammala na hau sama shima na gyaro, lokacin dana sakko na iske Yah Qaseem ya fita”.
Ta sauke numfashi tana share hawaye, kafin ta cigaba da faɗin,
“Kinsan sai sun tsashi nake samun damar ƙarasa aikin? To ranarma saina wuce kicin tamkar yanda na saba na zauna muna hira da kuku ina karyawa, banfi zaman mintuna gomaba Mummy ta ƙwalan kira, na amsa ina ajiye filet ɗin hannuna ina fita. Na isketa cikin shirin fita, na gaisheta cikin risinawa, tana laluben abu a jakka take amsamin, ta bani umarnin zuwa na taso mata Yah Salman. Da to na amsa ina ficewa.
Nayi sallama a ƙofar ɗakinsa yafi sau biyar, sai dai babu amsa, sanin halinsa ya sani tura ƙofar na shiga kawai, yana kwance ɗai-ɗai a gado da ga shi sai guntun wando, nai ƙasa da kaina ina kiran sunansa. Kamar yanda ya saba ya tashi a fusace yana mai zagina akan ubanmi nazoyi?. Amsa na bashi da cewar Mummy ce tace na tasoshi, wawan tsaki yaja nidai na fice abina naje na sanar mata cewar gashinan”.
“Bayan na sanar mata ta cemin zata fitane, idan Aunty Aamilah ta tashi na sanar mata taje can ta sameta inda sukai magana jiya, na amsa da to na nufi sama dan ƙarasa aikina”.
“Bansan fitar Mummy ba, dan inacan ina aiki, bayan na kammala na sako na nufi kicin, ina ƙoƙarin shiga Yah Salman zai fito, dan jaka mukai karo da juna harna faɗa jikinsa, muguwar mamuƙar da yaymin ba ƙaramin tsoro ta baniba, dan bilhaƙƙi da gaskiya ya rungumeni tare da matseni tsam a jikinsa, nai saurin turesa ina hawaye.......”
Ta kasa ƙarasawa tana sharar hawayen yanzunma, ni kaina idona ya cika da ƙwalla, handkherchief ɗin hannuna na miƙa mata, ta girgiza min kanta da cewar, “Kona goge waɗanda suka fisu zasu zubo, tuni alƙalamin ƙaddara ya fahimtar dani share hawaye a gareni bashi da wani amfani Bilkisu”.
Da ƙyar na iya haɗiye yawun daya tokare min maƙoshi, nace, “Sai mi ya faru kuma bayan hakan?”.
Ta ɗan taɓe bakinta tana ajiye tiren shinkafar da take tsinta, tace, “Tsaki yaymin ya fice a binsa, nima sai na samu kaina da jan tsakin ina shigewa, dama da shirin fita aiki na gansa, dan haka muna daga kicin ɗin mukaji fitar motarsa, itama Aamilah bata jimaba ta tashi a barcinta ta karya tabi bayan Mummy, ya rage gidan daga ni sai kuku da baba mai gadi”.
Can baya na koma nai zamana a wajen ni kaɗai tamkar yanda na saba, da ga baya da naji na takura saima na fita a gidan na dawo gida, sai dai na iske mama bata nan itama, dama kuma ta faɗamin zataje gaisuwa, jinai nan ɗinma babu daɗi, na sake fita na koma can gidan, na kwanta a falo, anan barci ya kwasheni, ban farkaba sai ana kiran sallar zuhur”.
Bayan na idar da salla ne na shiga kicin na samu abinda zanci, banga kuku ba, bankumaji motsinsa ba sam, abinci na ɗiba na zauna naci, tsautsayi ya sakani ɗaukar lemo nasha, abindama bai cika damunaba, duk da kuwa ba'aimin iyaka da dukkan wani nau'in abinci dake gidanba, duk abinda masu gidan zasuci Dad ya bani umarnin nima na ɗaukesa naci, kuma sam dukda halayar Mummy bata da ƙyau tanan ɓangaren dolene a yaba mata, ko wanene kai bata ƙyashin kaci komi zasuci, dan duk abinda sukaci shine ma'aikatan gidan keci, kuma za'a baka yanda zai isheka kaci ka ƙoshi”.
“Wannan lemo shine sanadin komai, daga shansa ban sake sanin ina hankalina yake ba, sai dai tashi nai na ganni a mawuyacin hali a gidannan.....”
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”, naketa maimaitawa, na share hawayen dake zubamin a ido ina riƙo hannun Amina.
“Amma Amina wa kike zargi a cikin gidannan da aikata miki wannan abun?”.
Hawayenta ta share tana murmushi mai ciwo, “Bilkisu ni bana zargin kowa, sannan kuma duk ina ƙyautata musu zato”.
“Humm Amina su kuma basa ƙyautata miki zaton, dan da suna miki ƙyaƙyƙyawan zato da basu biyema son ƴaƴansu ba da zuciyarsu wajen kasa fahimtar an cuta miki, tabbas a wannan gaɓar abin yazo mini da ruɗani, dan zuwa yanzu hatta kuku da baba mai gadi suna cikin zargina”.
Amina ta zaro idanu tana kallona, hakama mama daketa aikinta tana saurarenmu sai da ta kalleni, sai dai babu wanda ya iya cewa uffan a cikinsu.
Nace, “Karku damu, shi laifi kowama yana iya aikatashi, musamman ma irin wannan”.
Dukansu kai suka jinjinamin alamar gamsuwa, na miƙe zan tafi mama tace babu inda zanje sai naci abinci, dan yau ɗanwake takeyi.
Dole nabi Umarninta na koma na zauna ina murmushi, ganin Amina tana tattare da damuwa na fama mata ciwon da nayi sai na shiga bata labarin wajen aikinmu, musamman inda na nuna ragwantaka a wajen trianing, aiko taita kwasar dariya mama na tayata.
Bansan yaya akaiba har abinda ya faru dani a airport akan mutuminnan sai da na bata labari.
Aiko taita kwasar dariya harda hawaye, wai mazari sunga mazaje.
Ganin ta shiga cikin farin ciki nima sai naji sanyi a raina, koda mama ta kammala tare mukaci abinci mu uku a kwano ɗaya munatama mama santin ɗan waken da yaji daddaɗan yaji daketa ƙamshin tafarnuwa da kayan kamshi.
Ban bar gidanba har sai da kiran yah Qaseem ya shigo wayata, ina tunanin ya dawo gidane, dan shi yau ya fita akan wani aiki da yakeyi.
Sallama nai musu na tafi ina jera musu godiya suma sunamin tare da addu'ar fata alkairi...........✍🏻





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻https://youtu.be/T8bCANmJA5E

*_MANHA HAUSA NOVELS_*


https://youtu.be/xUINNiDdeH0

*_AL-ƘALAMI TV_*


*_Facebook_* _Bilyn Abdull_ 😉

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=102039014953186&id=100054412625125


*_Typing📲_*



*_🧺ƘWAI_* _cikin_ *_ƘAYA!!🧺_*


*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_Wattpad:-_* _BilynAbdull😉_



*_________________________________*
*_BOOK ONE END_*
_Shafi na arba'in😌_
*__________________________________*



.............Ina ƙoƙarin shiga gida kiransa ya sake shigo mani, ɗagawa nai da nufin faɗa masa ganinan zuwa gidan, amma sai naji yana magana mai alamar ba'a gidan yakeba..
Ya bani umarnine akan na duba ɗakinsa akwai wasu takardu ɗaya daga cikin jami'inmu zaizo ya amsa, na amsa masa da to kafin na yanke wayar na ida shiga da hanzari.
Kamar yanda ya umarta hakan nayi, ina fitowa na iske wanda aka turo ɗin yazo, shima yana sama dani, dan haka nai masa gaisuwar girmamawa kafin bashi takardun na koma ciki.
Duk da na iske su Mummy a falo ban iya zama ba, gashesu kawai nayi na shige ɗaki abuna, dan ina buƙatar samun filin yin tunani akan abinda muka tattauna da Amina.
Sosai komai yake neman ɗaure kaina, duk da kuwa Alhmdllh yanzu na samu ilimi sosai game da bincike, dan ko a wajen horaswa da muka samu, nafi maida hankalina anan sosai, alamu sun nuna Qaseem da Salman basa gida, shin akwai wanda ya dawo daga baya kenan s cikinsu? Ko kuwa kuku zan zarga kai tsaye ne? Baba mai gadi tsoho ne, duk da dai tsufansa bai kai ace bazai iya aikata makamancin hakanba, to amma miyasa zan zargesa ne? Lallai ya dace nama fara bincikarsa akan shiga da fitar kowa a wannan ranar.
Da wannan tunanin naɗan samu nutsuwa, amma koda nai shirin barci na kwanta sai ya gagara, babu abinda nake sai saƙawa da kwancewa tare da tunanin iyayena.

_______________________________

Washe gari litinin muka tashi da shirin aiki, tunda na gama shiri naga harna shiga kicin ina shan tea Yah Qaseem bai shigoba nasan bai kwana gidaba jiya kenan?.
Tea ɗin kawai na iya sha na fito, babu wanda ya tashi har yanzu a mutanen gidan.
Nai addu'a na fita tamkar yanda na saba. Yau kam sai driver nabi, muna isa tamkar jira na samu saƙon kira.
Na nufi inda ake kiran namune na haɗu da Yah Qaseem, murmushi mukaima juna, na gaishesa cikin girmamawa tamkar yanda na saba.
Shima ya amsamin da kulawa yana tambayata yaya gidan?.
“Alhmdllh Yah Qaseem, yaya aikin naka? Ai ni bansan baka kwana gidaba sai yanzu da safennan?”.
Yace, “Oh, wannan wace irin matace dani? Ban kwana a gidaba amma sam bama ta saniba”.
Haka kawai sai maganarsa ta sakani jin kunya, naja baby hijjab ɗina na rufe muskata ina murmushi, matsowa yay kusa dani gab tamkar zai shige mini jiki, ya kai bakinsa dai-dai saitin kunnene yana faɗin, “Baƙauya”.
Baya na ɗan ja saboda kusancin da muka samu yayi yawa, na janye hijjabin zan bashi amsa karaf idona akan mutumin ga, gabana yay wata masifaffiyar faɗuwa saboda cin karo da wata shegiyar harara daya watsomin, tuni fara'ar fuskata ta ɗauke baki ɗaya saboda bugun da ƙirjina yakeyi.
“K lafiya?”
Ƴah Qaseem ya faɗa cikin tsareni da idanu.
Cikin rawar baki da hadiye yawu da ƙyar nace, “B..babu k..omai”.
Idanunsa ya ɗauke da ga kaina ya maida saitin inda nake kallo, sai dai yana juyawa shi kuma yana shigewa Office.
Sake juyowa yay gareni, “Wai haushi kikaji dan nace miki baƙauya?”.
Murmushin ƙarfin hali nai masa ina girgiza kai, nace, “A'a yayana”.
Ƙaramar dariya yayi ya dungure min kai tare da zagayeni ya wuce abinsa da faɗin, yaje gida sai ya dawo.
Ko a dawo lafiyar ban iya ce masaba, na kuma kasa ɗaga koda ƙafata a wajen saboda tsabar yanayin dana tsinci kaina.
“Haba Bilkisu! Ke kin cika matsala wlhy, tsayuwarmi kuma kike anan?”.
Nannauyan numfashi na sauke jin muryar Ummie a kusa dani, taja hannuna ba tare da ta sake magana ba zuwa inda ake jiranmu.

Sosai mamaki ya kamani ganin inda ta kawo mu, zan iya kiransa Office kai tsaye, amma mazauna cikinsa da zasuyi amfani da shi aƙalla mutane goma cif.
Tunda naji zuciyata ta dai-daita nasan baya wajen, dan haka nakai dubana ga kowa, iya dai mune da aka tara ranar, tare da yallaɓai Hafiz.
Ya gyara tsaiwarsa yana mana bayani yanda zamu fahimta sosai.
“Wannan Office ne da zai kasance na musamman ga waɗanda boss ya aminta da ƙwazonsu, dan haka sai kowa ya duba, idan kaga sunanka to kana cikin waɗanda ya zaɓa, idan baka ganiba to ba hakan yana nufin bazai iya aiki da kai bane ko bai yabama ƙoƙarin kaba, kawai dai kasan a ranka hakanne mafi alkairi a gareka”.
Duk cikin girmamawa muka amsa masa.
Ni kasama dubawar nayi, sai Ummie ce tabi sauran itama tana dubawa, inajin wasunsu suna murna, alamar dai sunga sunayensu.
Nima a bazata naji Ummie ta rungumeni tana faɗamin ni da ita duk muna ciki.
Ban san miya saba, banji baƙin cikiba, kuma banji wani murnaba, kawai dai nayi murmushi ne dan karta zargi wani abu..
A cikin mu goma ɗinan bakwai mazane, mu uku mata, ni Ummie sai ɗayar mai suna Divine.
Komai na wajen an yisane da tsari, dan an saka mana shingai da kowa bazaiga abinda ɗan uwansa keyi a sashensaba sai idan yaso hakan.
Naji daɗin yanda aka saka Ummie kusa dani, duk da ba'a layi ɗaya mukeba wajen zamanta yana kallon nawa, sannan mune ƙarshen bangon wajen.
Duk wanda yake cikin wannan tafiya yayi farinciki, saɓanin ni da bansan manufar zaɓin da zuciyata ta ɗauka ba.

Shigowar Yah Qaseem station ɗin ya samu labari, bansan dalilinsaba naga ya fara faɗa tamkar zai cinyeni ɗanya, ta inda yake shiga ba tanan yake fitaba.
Tun ina saurarensa da mamaki na koma al'ajab, daga al'ajabi nakoma ban haushi, har takai abin ya bani tsoro, danni bansan minene laifina a cikiba? Kuma ince nan wajen aikine, bamu da dalilin cewar sai inda muke buƙata za'a zaɓamana.
A cikin masifarsa ta yau ne nakeji cikakken suna mutumin nan, wato *_Jawaad Abdul-aziz yusif_*.
Ni dai bance ƙalaba har yaci jarabarsa ya tsire, daga ƙarshe yace na fitar masa a office.
Na fito ina share hawayen da suka ziraromin babu shiri, sai shi kuma naci karo da shi.
Tafiya yake a fusace tamkar wani ingarman doki, yana ƙoƙarin saka bindiga a aljihun wandonsa na baya, yayinda su yallaɓai Jabeer ke take masa baya suma fuskarsu babu walwala.
Yana ƙoƙarin shiga motar da aka buɗe masa ne ya ɗago, sai ko idanunmu cikin na juna.
Saurin janye nawa nayi ina kauda kai, a ƙasan zuciyata ina mamakin miya fusatashi har hakane?.
Bani da mai bani amsa, dan haka sai ma tashin motarsu na jiyo.

Har na bar Office ban kuma sakashi idona ba, hakan na nufin dai basu dawoba daga fitar da naga sunyi ɗazun kenan.
Sai kuma har naje gida abin na damuna, haka kawai naji na damu da tsagwaron damuwar dana karanto a fuskarsa, ranar da wannan abun na kwana a raina.


______________________________


Washe garin safiyar talata muka tashi da dawowar aunty Shahudah ƙasar haihuwarta tamkar yanda naji a bakin su Aunty Aamilah, danni dai babu wanda ya sanarmin hakan.
Ban damuba, dan nasan koba'a faɗaba bani da muhimmancin sanin irin waɗanan abubuwan tunda basu ɗaukeni dai-dai da suba har yanzu, Dad ne kawai yakemin kallon na mutum mai muhimmanci a cikinsu, sai ko Ya Qaseem da shima nake ƙyautata masa zato akaina.
To ni daima aiki nai ficewata abina, dan shine mai muhimmanci a gareni a yanzu, nabar saƙon sannu da zuwa a faɗa mata wajen Aunty Aamilah, dukda dai a ɗage ta amsamin ban damuba nai wucewata driver ma yau ya ɗaukeni, dan Yah Qaseem ma yau bai kwana gidaba.
Na fiskanci akwai aiki mai mihimmancin gaske da yakeyi a kwanakinnan, musamman ma yanda ya maida kansa busy ko'a Office bai cika zamaba sosai.


____________________________


Ƙarfe biyar na yamma jirgin su Shahudah zai sauka, dan haka tun ƙarfe biyu su Mummy suketa shirin tarbarta, ansa kuku ya shirya mata abinci na musamman kala-kala tamkar ba cikinta kaɗai zai ciba.
Tsabar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login