Showing 174001 words to 177000 words out of 388641 words

Chapter 59 - KWAI CIKIN KAYA

10 Sep 2025

20687

sai dai nasan ba samu zanba, dan duk waɗanda suke a kaina babu mai irin wannan tunanin. nesa-nesa nake jiyo maganar Yah Qaseem dake cewa Aunty Aamilah mutashi muje mu kwanta, da taimakonta na koma saman gado, sai daifa tace itama anan zata kwana bazata koma ɗakintaba, sannan suma dan ALLAH su kwanta anan ɓangaren basai sun koma nasuba. Bansan amsar da suka bataba saboda idona ya rufe ruf da barci.

★★★

           Kiran sallar farko na asubahi na farka, sai dai abin mamaki da al'ajabi na mance kaso mafi yawa na abinda ya faru jiya a gidan, na tashi zaune ina kallon Aunty Aamilah dake mamuƙe dani alamar a tsorace tai barci, ajiyar zuciya na sauke a hankali inason tuno koda wani abune kaɗan, sai dai sam ƙwaƙwalwata ta gaza aiki, tamkar ansa murfi an toshe bututun dake kai saƙo tsaka

nin ƙwaƙwalwa da zuciyata, addu'a na shiga karantowa kozan sami sassaucin da nakeji dangane da ƙuncin da zuciyata ta shiga da zafin da nakeji a cikinta.

اَللَّهُمَّ رَحْمَتَكَ أَرْجُوفَلا تَكِلْنِي إِلَى نَفْسِي طَرْفَةَ عَيْن، وَأَصْلِحْ لِي شَأْنِي كُلَّهُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أنْتَ.
“Allahumma rahmataka arjoo fala takilnee ila nafsee tarfata 'ayn, wa-aslih lee sha'nee kullah, la ilaha illa ant”.
        Ya ALLAH! Rahamarka nake kauna, don haka kar ka kyale ni da kaina ko da kiftawar ido ne, kuma ka kyautata mini sha'ainina dukkansa; babu abin bautawa da gaskiya sai kai.
         Sai da aka fara kiran salla ta biyu sannan na samu ƙarfin sakkowa daga gadon, banda ƙuncin zuciya babu abinda nakeji a jikina, sai kaina dake ɗan ciwo kaɗan-kaɗan da marata, ban ɗauki hakan komaiba, dan nasan hakan alamun zuwan period ɗinane, da sam bana ciwon mara idan zanyi al'ada, amma a shekararnan gaba ɗaya haka nake fama dukda bawai yanamin tsanani baneba. Saida na duba na tabbatar babu alamar zuwansa ciwon mararne kawai sannan nai wanka dan na samu ƙwarin jikina, daga nan nayo alwala na fito. Nayi ƙoƙarin tada aunty Aamilah amma sam taƙi koda motsi, haka na haƙura na barta nai sallata ganin nima lokaci na neman ƙwace mani. Bayan nayi azkar karatun alkur'ani nayi har zuwa 7am sannan na tashi, shirin office nayi abina, harna kammala aunty Aamilah batako motsaba har lokacin, nakuma ƙoƙarin tadata salla amma taƙi tashi, ƙyaleta nayi na fita kicin danna samu koɗan tea na sha dukda banajin cin komai.

★★★★★★★

           Tunda suka shigo gidan daga asibiti daƙyar ya iya dauriyar yin wanka saboda barcin da yakeji, ya samu yay shafa'i da wutiri a daddafe ya haye gadonsa, ya fara addu'a, amma bashi da tabbacin ya kammalata barci yay awan gaba dashi. Can tsakkiyar dare ya farka a matuƙar razane saboda mummunan mafarkin da yayi.
         ‘Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un’. 

أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّاتِ مِنْ غَضَبِهِ وَعِقَابِهِ، وَشَرِّ عِبَادِهِ وَمِنْ هَمَزَاتِ الشَّيَاطِينِ وَأَنْ يَحْضُرُونَ.
“A'oozu bikalimatil-lahit-tammat min ghadabih,wa'iqabih, washarri 'ibadih, wamin hamazatish-shayateen, wa-an yahduroon”.
      Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga fushinsa, da ukubarsa, da sharrin bayinsa, da kuma wasuwasin shaidanu, da kuma kada su zo mini (a cikin al'amurana).
أَعُوذُ بِاللهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ ثَلاَثٍ مَرَّاتٍ.
a'uzu bi-l-lahi mina shaytani r-rajeem’. ya faɗa sau uku, yay addu'a ya tofa gefen haggunsa da dama sau uku, sannan ya sauka a gadon, alwala yayo yazo yay salla raka'a biyu saboda idonsa cike yake da barci, yay addu'a sama-sama ya koma saman gadon ya kwanta, sai dai ya canja sashen da yay mafarkin dashi ɗazun. Babu jimawa barcin ya sake awan gaba dashi.
      Ana kiran sallar shiga massalaci ya farka, hakan ya sakashi ɗaura al'wala ya fita massalaci dan har an tada sallah. Koda aka idar bai wuce motsa jikiba yau sai ya shigo gida duk da yana buƙata saboda jikinsa yayi nauyi, gyara ɗakinsa yay ya shiga wanka, bayan ya fito yay shirin office. Ƙarfe bakwai da kwata Gimba ya ɗaukesa suka fice daga gidan..............✍



Gaskiya an fara sakama boss ido a gidannan fa😑, yana koyama yarinya aiki anacewa yayi🤐🙄 nayi nan, karkuma ace na koma team Beejay ne🚴🏼.


ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[11/30/2020, 12:56 PM] HASNA✍🏻: Typing📲

ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK TWO

Page 17

................Bayan na kammala shan tea ɗin dana sakama suga kaɗan sai na fito daga kicin ɗin, a falo na iske Yah Qaseem zaune yana waya da Dad, da alama abinda ya faru a daren jiya yake bashi labari, sai dai yanda naji yana faɗama Dad ɗin shima wai ba komai zai iya tunawaba, shidai kawai an bamu tsoro jiya a gidan. Bansan mi Dad ya faɗa masaba, nadaiji ya amsa masa da cewar, “To Dad ALLAH ya kawoka lafiya, itama yanzu zamuje asibitin muji yaya jikin nata”. Yaɗanyi shiru yana sauraren mi Dad ɗin ke faɗa daga can, sai yace, ”Okey gata”. Wayan ya bani, muka gaisa da Dad, daga can yace, “Ɗiyata yaya jikin naki?”. Muryata a sanyaye da har yanzu nakejin jikina wani iri nace, “Alhmdllh Dad, banajin ciwon komai sai na kai, gashima nayi shirin Office ”. “To ALLAH ya kiyaye gaba ya ƙara sauƙi kinji, nima insha ALLAHU ina tafe, anjima kaɗan zan iso”. Nace, “To Dad ALLAH ya kawoka lafiya”. “Amin” ya faɗa mukai sallama, na miƙama Yah Qaseem wayarsa. Miƙewa yay yana faɗin, “Muje dan mu samu mubiya asibitin”. Kaina na jinjina masa, har mun fara tafiya nace, “Yah Qaseem bazakasha ko tea ba?”. Kansa ya girgizamin a sanyaye, haka kawai na samu kaina da tsura masa idanu, gani nai fuskarsa tai jazur kasancewarsa farin mutum, idanunsama haka, duk ya wani fita hayyacinsa, gashi tamkar a firgice yake. Cikin katseni yace, “Bilkisu lafiya?”. Firgigit na dawo hayyacina, saina girgiza masa kai kawai nai gaba ya biyoni a baya.
Tunda muka fice daga gidan babu mai iya cema ɗan uwansa komai, yau ko redio bai kunnaba, sannan sam baya gudu kamar yanda ya saba, duk yanda naso tuno wani abu na daren jiya na kasa hakan a yanzunma, iyakar firgitar da mukai kadaice ban mantaba da abinda ya biyo bayanta, amma miye musabbabin hakan? Amsar itace ban saniba ba, tamkar anma ƙwaƙwalwarta formatting ɗin komai lokaci ɗaya, haƙura nai dason tunawar na cigaba da maimaita ‘Hasbinallahu wa ni'imal wakil’ a cikin zuciyata.
Motar Jawaad na fita daga asibitin bayan yasa gimba ya biyo sun duba Shahudah su Bilkisu na shigowa, shi Qaseem yaga fitarsu Jawaad, amma bily bata luraba dan hankalinta baya tare da duniyar mutane.
Shiga suma sukai suka duba Shahudah, har yanzu barci take, sundai leƙata ta Window suka fito, gudun karsu makara yasa sukaima Mom sallama suka wuce office.
★★★★★★
Koda muka iso yau ban samu damar yima Yah Qaseem rakkiyaba, shima bai nema hakanba, da kansa ya kwashi kayansa ya wuce office nima na wuce. Sama-sama nai gaisuwa da kowa na zauna a mazaunina, Ummie kanta yau takula bani da walwala, koda ta dameni da tambaya sai nace mata aunty Shahudah ce bata da lafiya tana asibiti. “ALLAH ya bata lafiya” kawai tace cikin rashin ɗaukar abun da muhimmanci.
Ban iya cewa da ita komaiba na cigaba da aikin gabana, kusan sha ɗaya akai kiran wayar landline ɗin office ɗin namu, Ada dake kusa ta ɗaga, da hannu taimin nuni nazo. Na ajiye biron hannuna na nufeta, miƙamin kan wayar tayi tabar wajen, na saka a kunne nace, “Hello”. “Ki sameni a office” kawai akace aka yanke. kamar nayi kuka haka naji, da inada dama dana roƙesa ya ɗagan ƙafa zuwa ɗan anjima, dan marata a ƙulle take tamau ga wani azababben ciwon kai dake cina tamkar jijiyoyin kan zasu katse. Mazaunina na koma na ɗauki ATM ɗinsa dana manta jiya ban bashiba na saka a aljihu na fita, ina kallon su Ada na gulmata, na girgiza kai kawai na fice abina dan banida lokacinsu.
Halin da nake ciki ya sake haddasama tafiyata sanyi, ga fuskata a cinkushe sosai, wadda harni kaina nasan bana cikin yanayin farin ciki gaba ɗaya yau, abinne ya haɗemin da yawa, zuwan period kan sakama mace ɓacin rai na babu gaira babu sabar, tausayin aunty Shahudah da ganinta yau ya sake ɗagan hankali, damuwar abinda ya faru a daren jiya dason tuna koda ƙanƙanin abune amma hakan ya gagara, ciwon kai ga mara dakan saka mutum takura yaji baya buƙatar yin koda magana ma.
Nai knocking ƙofar a hankali tamkar banaso, shirun da naji ya sakani sake ƙwanƙwasawa, umarnin shigowar da aka bani daga cikine ya sakani tura ƙofar na shiga.
Ƙamshin dana shaƙa a office ɗin ya sakani jin ɗan sanyi a raina, na ƙarasa inda yake ina mai satar kallonsa, sanye yake da suit yau, sun masa ƙyau sosai kamar koda yaushe, bai ɗagoba tunda na shigo, yanata rubuce-rubuce a takarda. nace, “Ina kwana sir” bai amsa minba, hakanne ya sakani kallonsa da haushi, sai da na kalli abinda ke a kunnensa na fahimci waya yakeyi, yaɗan ɗago ido ya kalleni yana faɗin, “Okey Sir” cikin jinjina kai. Da hannu yaymin nuni da kujera, kaina na gyaɗa masa kawai na zauna, cigaba da abinda yakeyi yayi. Bawani sauraren abinda yake nakeba balle na fahimta saboda halin da nake ciki, kusan mintuna bakwai kafin suyi sallama ya cigaba da rubuce-rubucensa baice dani uffanba.
Cikin dauriya na kumace masa “Ina kwana”. “Lafiya” kawai yacemin yana cigaba da sabgarsa. Ɓoyayyen numfashi na sauke ina ƙoƙarin son daidaita gudun zuciyata, na ɗora masa ATM ɗinsa saman table ɗin nace, “Gashi nagode, ALLAH ya ƙara buɗi mai albarka”.
Karon farko da tunda bilkisu ta shigo office ɗin Jawaad ya ɗago ya kalleta.
Yanda ya zubamin idanun ne ya sakani saurin duƙar da kaina, baiyi maganaba ya maida kansa ga abinda yakeyi yana ɗan lumshe idanu. sai kuma ya ɗago kansa, takardun dake gefen hannun damarsa ya ɗakko, buɗesu ya shigayi na wasu mintuna sannan ya miƙomin yana kafeni da muggan idanunsa, “Ki fara tattare dukanin bayanan wannan case ɗin a file ɗinnan, komai dake aka farashi, ki nutsu kiyi abinda ya dace”. Kaina na jinjina masa, ya sake miƙomin hotuna guda biyu, batare da ya kalleni ba yace, “Ki sakasu a ciki” suma amsar nai na buɗe na saka a farkon takardun ina cije lip saboda wani mugun katsawa da marata tayi. Babu shiri na ajiyesu na kwantar da kaina jikin tebirin ina ambaton sunan ALLAH da ɗaura hannuna na haggu bisa cikina.
Idanu Jawaad ya zuba mata na wasu sakanni, sai kuma ya ɗauke kansa, duk yanda yaso basarwar sai ya kasa, a hankali yace, “Miemaa” shiru Bilkisu bata amsaba, bakuma ta motsaba, ya zuba mata ido a karo na biyu, ganin taƙi ɗagowa sai ya miƙe ya zagaya inda take. Kujerar dake kallon wadda take zaune yaja baya kaɗan ya zauna, nanma idanunsa a kanta, dan yarasa kuma mizai mata, sunanta ya kuma kira yanzunma a hankali.
Ƙwallan da suka cikamin ido na share sannan na ɗago kaina ina amsawa da “Na'am” Ganin idonsa a kaina suke ya sakani maida nawa na risinar ƙasa. yace,
“Lafiya?”
Kaina na jinjina masa alamar eh babu komai, dan ko giyar wake nasha bazan iya cemasa marata ke ciwoba, fatana kawai ya sallameni na koma.
Ƙaramin tsaki naji yayi, cikin ɗan kausasa murya yace, “K kalleni”. Ɗagowa nai na kallesa danjin babu wasa a furucinsa, yanda ya zuba idanunsa cikin nawa bazan iya jurewaba, naɗan risinar da nawa ina haɗiye busashshen yawun dana tattaro daga bakina da ƙyar.
“Ni zakima ƙarya?”
Da sauri na girgiza kaina. Ya sake cewa ”Mi akai miki?”. Saboda ya barni nace, “Kaina ke ciwo”. Shiru yay baice komaiba, hakan yasa na ɗago kaina a tunanina bani yake kalloba. Sai dai anyi rashin sa'a idanunsa ƙyam suke a kaina. Ɗauke nawa nai ina kumbura fuska danni banason wannan kallon takuramin yakeyi.
Huci naji yaɗan fitar kaɗan mai kama da ajiyar zuciya, yace, “Tashi kije ki kwanta”. Kallonsa nai da mamakin maganarsa, ni ina zani na kwanta to?. Doguwar kujerar dake rukunin kujerun office ɗin a gefe ya nunamin fuskarsa a matuƙar ɗaure babu wasa.. Gabana ya faɗi, na kallesa cikin waro idanu da rawar baki dan nakasa cewa komai. Harara ya zubamin, a ɗan tsawace yace, “Na fara wasa da kene?”. Saurin girgiza kaina nayi na miƙe.
Kasancewar dama kwanciyar nake buƙata saina shiga sauke tagwayen ajiyar zuciya lokacin dana kwanta, na takure waje ɗaya saboda azabar da nakeji, bammasan hawaye nabin kumatunaba, kusan mintuna uku kafin ta lafamin, na buɗe idanuna a hankali na saukesu akan Boss dake zaune saman centre table ɗin rukunin kujerar ya zubamin idanu, saurin maidawa nai na rufe ina ƙoƙarin haɗiye kukana. Baice dani komaiba, amma inajin yanda idanunsa ke yawo a jikina har yanzun. Yunƙurawa nai zan tashi yace, “Koma ki kwanta”. cikin marairaice fuska nace, “Ya daina ai, zan koma nacigaba da aikina”. Yanda yay kicin-kicin da fuska ya tilasta min komawa na kwanta yanda yake buƙata. “Mike miki ciwo?” ya jehomin tambayar a kausashe. Bansan sanda na tura baki gaba ba nace, “Nifa kainane kawai sir”. Bai tanka minba yamiƙe yabar wajen, ban sake sanin mi yakeyiba saboda ciwon ya dawo. Saida ya lafamin ne na buɗe ido naga Ummie durƙushe a gabana tanamin sannu, hannunta na kama na riƙe ina hawaye, “Ummie ki taimakeni kiyi masa dabara mubar office ɗin nan dan ALLAH”. Kanta ta jinjinamin tana gogen hawayen, tace, “Mararki ke ciwo ne?” da sauri na ɗaga mata kaina ina cije baki. Nace, “Koda yaushe zai iya fitowa wlhy Ummie”. Cikin ƙara rage murya ƙasa Ummie tace karki damu bara nai masa magana”.
Jawaad da duk ke saurarensu daga inda yake zaune ya girgiza kai kawai. Mutum ne shi da ALLAH yayma baiwar jii, dukda ahankali suke maganar yana jiyosu batare da sunyi tunanin hakanba. Koda Ummie ta miƙe zuwa inda yake domin ta tsarashi kamar yanda Bilyn ta buƙata sai yace ta tafi. Babu ƙofar yimasa musu, dan haka tabi umarni ta fice tana waigen bilyn. Waya ya ɗauka shikuma ya tura saƙo. Cigaba yay da aikinsa kamar ya manta da Bilkisu a office ɗin, lokaci-lokaci yakan amsa waya koshi ya kira. Kusan mintuna ashirin da tura saƙonsa aka kawo masa abinda ya buƙata, Gimba ne ya shigo ya ajiye ledan hannunsa bayan ya gaishesa.
Sama-sama nake jin muryar gimba a office ɗin, kafin kuma naji alamar fitarsa. Ƙamshin turaren Boss da naji a akaina ya sakani buɗe idanu, yace, “Tashi zaune” babu musu na tashi, a raina ina murna zai barni na tafi, abinda ke cikin ledar ya fiddo sai naga magunguna ne, batare da ya kalleniba yace, “Kinci abinci?”. A hankali nace, “Nasha tea tun a gida”. Baice komaiba ya miƙe. Naɗan bisa da kallo sai kuma na janye idanuna ganin ba fita zaiyi daga office ɗinba, bansan mi yakeyiba saboda ya juyamin baya, a ɗan ƙanƙanin lokaci ya juyo ɗauke da kofi, ya zauna a table ɗin tamkar ɗazun yana miƙomin tea ɗin daketa turiri, sai cake, yanda yay da fuskane ya tabbatarmin babu wasa, ya miƙe yana faɗin, “minti biyar na baki kuma”. Bance komaiba nidai sai fuska dana kumbura. Dayake yunwar nakeji kuma tea ɗin ya haɗashi dai-dai yanda zan iyasha gashi babu suga sai gashi na shanye naci cake ɗin, ina ajiye kofin yana dawowa wajen hannunsa ɗauke da ruwa, nidai kaina a ƙasa naƙi kallonsa, dan dauriya kawai nakeyi kar yaga na cika raki, sai haɗiye kukan dake tahomin nakeyi da sauri-sauri, da kansa ya ɓalla maganin ya miƙamin. Amsa nai babu musu na zuba a baki, ya miƙamin ruwan shima, na kammala sha ya amsa yana min nuni dana kwanta. Ban musaba dan babuma damar yin musun na koma na kwanta kamar ɗazun, shikuma ya miƙe zaibar wajen. Bansan lokacin da harshena ya suɓuce nace, “Sir dan ALLAH kai min addu'a a ruwa ka bani nasha, sannan ka tofamin, jinake jikina kamar ana kunna garwashin wuta”. Cak ya tsaya, sai kuma ya juyo a hankali tamkar mai ciwon wuya ya zuba min idanu. Lumshe nawa nai hawayen da nake maƙalewa suka silalo.
Wani irin bugu ƙirjin Jawaad yake da sauri-sauri, ga wani irin sanyi na ratsashi daga saman kai har yatsan ƙafa tamkar wanda ake tsundumawa cikin ƙanƙara, mafarkinsane na daren jiya yake rige-rigen dawo masa a kwaƙwalwa. Bayan gushewar kuwwar halittu masu ban tsoro da ya samu damar yin addu'a ta koresu, sai furucin ƙarshe na cikin mafarkin daya fito daga bakin wata murya mai amo da baisan daga ina ta ɓulloba ita kuma, yay masa tsaye cak a zuciya yakuma kasa fashin baƙi a kai harya iso office ɗin nan, {Ƙaddarar haɗuwar Jini a cikin jini da zai zama jini ta tabbata, rashin gaggawa zai tabbatar da zubewar jinane, hhhhhhhhh karku manta! Karku manta!! Karku manta!! Hhhhhhhhhhh!!!!}......... “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” ya shiga ambata lokacin da yaji gilmawar abu shuuu ta bayan kunnensa, da dawowar maganar tamkar a yanzu ake mai ambatonta ke faɗinta, hankalinsa ne ya dawo jikinsa. ya kalli inda bilkisu take kwance har barci ya fara fisgarta, samun kansa yay da tsira mata idanu a zahiri, a baɗini kuma taurarin cikin mafarkinsa ne daya koma barci bayan yayi addu'a da nafila ne suke masa kaikawo, yay ƙoƙarin tuno furicin mahaifinsa aka taurari huɗu da sukafi kowaɗanne haske acikin taurarin da ya gani, sai guda ɗaya shima mai tsananin haske amma ya matsa nesa dasu sosai, ya kasa tuna komai da Abba ya faɗa masa akan taurarin, kansa ya shiga yamutsawa cikin wani irin yanayi, a fili ya furta, “Jiya wace irin ranace?”. “Ranar da zata zama cikin ranakun tunawa daga nan har ƙarshen numfashi”. Bily da idanunta ke rufe har tana sauke numfashin tabbatuwar barci ta faɗa cikin motsa labɓanta da sauti mai sanyi, badan ALLAH ya yisa mai jii ba da bazai taɓa fahimta ba. Dukda yaji wani abu a ransa game da amsar tata sai ya tureshi da tunanin ai a fili yay magana shima, tajisane shiyyasa ta bashi wannan amsar, to amma abin tambaya anan miyasa ta bashi amsar a haka?. Ƙirjimsa yay wani irin motsawa, kiran sunata ya shigayi amma ko motsi bataiba alamar barcinta yayi ƙarfi. Ƙwaƙwalwarsa ma saita gaza tunanin komai, samun kansa yay da fara mata addu'ar data buƙata kawai ya shiga tofa mata akan fuska, gani yay ta saki wani lallausan murmushi tana motsa laɓɓanta, yay saurin kai kunnensa amma bayajin komai, ɗagowa yay ya kalleta sai kuma yaga ta yamutsa fusaka ta maida fuskarta ta haɗe.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login