Showing 57001 words to 60000 words out of 388641 words

Chapter 20 - KWAI CIKIN KAYA

10 Sep 2025

20703

ta turawan ce, sai hoton namiji again da bazai wuce shekaru goma sha biyarba, hoton dai da gani tsohon hotone.
Na sake waigawa ko zanga inda yake babba sai dai babu.
Tunda muka shigo kawu saman bene ya haye, hakan ya saka hajiya binsa itama.
Suma duk sai suka shige ɗakunansu aka barni ni kaɗai a falon tamkar mayya, hakan baisa naji rashin daɗiba, koba komai nasamu damar yima falon kallon tsaf ai.

Sakkowar hajiya daga saman bene ranta a ɓace ne ya sakani kallonta, sai kuma na duƙar da kaina saboda mugun kallon data jefeni dashi, kafin tace wani abu sai ga Kawu ma ya sakko fuskarsa babu walwala.
Ni dai dama a ƙasa nake zaune, sai na ƙara ladabtuwa domin girmamawa a garesu.
Kawu yace, “Ɗiyata taso muje kiga ɗakinki kinji”.
Cikin girmamawa na amsa da “to” ina miƙewa, yana gaba ina biye har ɗan lungun dake falon, ɗakuna ne a jere guda biyu, muka isa har gaban na ƙarshen ya buɗe ya shiga, nima shigar dai nayi.
Ɗakine babba sosai, akwai komai a ciki na amfani tamkar ɗakin matar aure, matar aurenma ƴar gata ta gaske.
Da ƴar ƙura a cikinsa kaɗan, alamun dai ba amfani ake dashiba, komai na ciki kuwa kalar ja da fari ne.......
“Bilkisu nan ne zai zama ɗakin ki kinji, shi ɗin ɗakin ƴar uwarkice datai aure kusan wata tara kenan, yanzu kinga saiki maye gurbinta, inason ki kwantar da hankalinki a gidan nan, ki ɗauki kanki tamkar kowa na cikinsa, yanzu dai idan kin huta zuwa dare zamu zauna dan ki san kowa da sunansa kinji”.
“To kawu nagode sosai, ALLAH ya ƙara buɗi da haske na alkairi”.
Fuskarsa faɗaɗe da murmushi yace, “Amin ɗiyata, amma daga yau ba kawu ba, ki kirani Dad kamar yanda ƴan uwanki suke kirana dashi, kema yanzu baki da banbanci dasu a gareni kinji”.
kaina na ɗaga masa nima ina murmushin jin daɗin dajin tsantsar ƙaunarsa a raina, shine mutum na shida da arayuwa bazan manta da suba, domin sunji tausayina a lokacin da nake buƙatar hakan ga kowa, sun ƙyautata mani lokacin da jama'ar duniya suke guduna, na share hawayen da suka ziraromin a fuska.
Jinai kawai an kama hannuna, na ɗago na kallesa aɗan firgice, “Haba ɗiyata, banason na sake ganin waɗannan hawayen a fuskarki dan ALLAH, nasan bazan iya ɗauke miki dukkan matsalarki ba a rayuwa, amma insha ALLAHU zan kamanta kinji, ki daure ki saki jikinki, zanji daɗin hakan”.
Murmushi nai masa, “Insha ALLAHU Dad bazaka sake ganiba”.
“To Alhmdllh ƴar gidan dad” yay maganar yana rungumeni.
Duk saina rikice, miye hakan kuma kawun yay min?, nashiga ukuna.
Shima fuskantar abun yazomin wani iri ya sakashi sakina yana faɗin, “muje na nuna miki yanda zaki amfani da banɗaki”.

Komai sai da ya nuna min shi, yakuma tabbatar na fahimta sannan ya fita ya barni ina ƙara gwada fahimtar komai yanda bazan manta ba.
Daga baya kuma na zage na gyara ɗakin tsaf, sai naga ya sake ƙyau saboda gyara na musamman daya samu sosai.


★★★★★★★★

A daren ranar wajen cin abinci na sake sanin kowa na gidan, dan kuwa duk Dad yaymin bayani a kansu da sunansu.
Duk na fahimta, duk da dai na kula shi kaɗaine ke ra'ayin zamana a gidan, dan ko babban ɗansu da alama ban cikin tsarinsa shima, sai kallon ƙurilla yake bina dashi a yatsine, wanda hakan ya tunomin da Jazuga a zuciyata, koda na koma ɗaki sai da na zubda hawaye saboda tuno firdausi da su inna da nayi, ina kewarsu sosai, inason sanin halin da suke ciki kuma.
Naci kuka a wannan daren har na rasa hawayen tsiyayarwa, dukkannin komaina na baya ya shiga dawomin daki-daki, ganin ina neman cinye daren da tunani sai na tashi na ɗauro alwala nazo naita nafilfilina ina miƙama ALLAH godiya da kukana game da sabuwar rayuwar dana sake shigowa.

Tabbas rayuwar wannan gida tasha banban da duk inda na rayu, ba'a ɓangaren jindaɗiba kawai harda yanayin zamantakewa da tarbiyya.
Gashi dai ina samun komai na buƙata, dan ko sutura kwana na ɗaya a gidan dad ya kawomin masu yawa, sai dai kumafa duk ƙananune, dan babu ko ƙyallen atanfa.
Abincin da kowa zaici nima shi nakeci, babu wani banbanci tanan ɓangarenma.
Sannan bana aikin komai a gidan, kamar yanda yaran gidan suma basa komai sai ƴan aiki, ko gyaran ɗakina ma sai da nai magana mai aikin gidan ta daina min.
Yanayin tarbiyyar gidan ce dai sai addu'a, dan kuwa na kula dai tsantsar rayuwar turaice da ɗabi'unsu ke wanzuwa ga jama'ar gidan.
Duk kayan daga gadama zaka saka babu ruwan wani da kai, babu mai maka faɗan rashin dacewarsu, rungumar juna tsakanin mazan da matan hakan ba komai bane, shima Dad ɗin dazai tsawatar rungumemu yake, rashin girmama na gaba matsayin na yayanka wannan sam babu shi, ɓangaren ibada ba damunsu tayiba idan har ka cire Dad da ba kullum yake zama gidanba, bazan ce maka arana suna cika salla biyar babu tsallake ba har Mommy ɗin, maganar Qur'an ma ban gansa a gidanba tunda na shigo, amma akwai ɗaki na musamman domin karatu, cike yake da kowanne nau'in littafin daya shafi boko harma dana labaran turanci, komai kayi a gidan sunansa ƴanci kawai, babu mai cemaka akwai kuskure a ciki.

Duk ɗabi'un nasu sunmin girma, na kasa kwaikwayon ko guda ɗaya a ciki balle na riƙesa matsayin cigaba.
Hakan yasa a kullum suke hantarata da suna baƙauya ko bagidajiya, bana damuwa dan bana samun sakewar fuska daga kowannensu dama idan ka cire Dad, idan baya gida babu maimun magana sai hantara da harara.
Iyakar nan dai tsananin ya tsaya min, shiyyasa bai cika damuna ba sosai.
A ƴan kwanakin dana samu a gidan jikina harya fara nuna alamun canji, dan kuwa fatata ta fara gogewa, sannan jikinma dai da alama ƙiba zai fara, baƙina da kullum suke zagina a kansa ya fara korewa, dan duk sanda Yah Qaseem zai hantareni yakan kirani da suna baƙar banza.
A kwai ranarda Yah Salman ke faɗin wai dama na taimaki kaina nazo ya kaini asibiti anmin allurar da zan koma fara ko nayi ƙyan gani, danshi wlhy har kunya yakeji suzo suyi baƙi aga ɓaƙar fuskata a cikinsu, ni da kwalta ta titi bamu da maraba.
Dariya Aamila da Mummy sukaita tuntsurawa akan wannan zance, harma Mummy ke faɗin, “karka damu, sonake mu fita shopping ai na haɗo mata mayukan da zata kore wannan mugun baƙin, ni kaina baƙin nan nata har tayarmin da tsigar jikina yakeyi, anya Bilkisu nama taɓa ganin mai baƙinki kuwa?”.
Murmushi kawai nayi ina haɗiye kukan da yake shirin taho mani.
Yah Qaseem yaja tsaki shima daga inda yake zaune yana cewa, “Ku baƙin kawai kuke gani, ni wlhy nafi tsanar naniƙaƙƙen hancin yarinyarnan, sai kace tana gudu aka saka mata, wannan ko farin tayi an faɗa muku fasali zatayi? Indama ALLAH ya sota ya bata jiki mai ƙyau, gashi dan jaraba kullum tana fama da wannan hijjabin sai kace akanta aka fara addini, idanma zaki sauƙaƙama kanki ki sauƙaƙa yarinya, larabawanma tushen musuluncin sha'aninsu sukesha balle ke jinin wahala”.
Nan ɗinma dariyar sukayi, hakan ya sakani kasa jurewa sai da yawayen da nake riƙewa dai suka zubo, hijjab na saka na share kawai.
“Tofa, wai kuka kikeyi dan an faɗa miki gaskiya? Tab kinada aiki wlhy” Yah Salman ne mai maganar yana miƙewa zai fice.
Haka suka cigaba da cimin fuska kowa na faɗin albarkacin bakinsa, dawowar Dad ce ta ceceni na samu sukuni, shikuma ganin yanayina ya sakashi tsareni da tambayar lafiya?.
Nace masa babu komai daga barci na tashi


★★★★

Ina sati na huɗu a gidan da safe kowa ya fice, daga ni sai Aunty Aamila da mummy ne a gidan, kuma duk suna ɗakunansu suna barci, niko bana iya dogon barcin nan hakan ya sakani fitowa falo na zauna ina kallo a tv, ɗauke wutar da sukaine ya saka ni miƙewa, ga shirin gidan kuma yasaka naji duk kaɗaici ya taso mani, tashi nai na koma ɗaki na kwanta duk da nasan ba barcin zanyiba.


★★★★

Da ƙyar Shahudah ta iya isa gidansu saboda rashin jin ƙarfin jikinta, tai hon mai gadi ya buɗe mata, yana ma gaisheta amma bata sauraresa ba ta shige, koda tai fakin ma kanta ta kwantar a sitiyari tai shiru na wani lokaci, kusan mintunanta biyar sannan ta samu ta fito zuwa cikin gidan.
Yanda gidan yake shiru tasan su mummy basu tashi barciba, gashi tana buƙatar hutawa, tsohon ɗakinta ta wuce danta samu ta hutama ranta, dama inhar tazo gidan takan zauna acannane.

Takun takalman da najine ya sakani kallon ƙofa, har aka buɗe aka shigo.
Idanuna suka saukakan ƙyaƙyƙyawar matashiyar mace cikin ado na ainahin zubin wayewa ta shigo ɗakin babu ko sallama.
Tozali dani ya sakata zare baƙin glasess ɗin idonta da ya rufe kusan rabin fuskarta tana min kallon sama da ƙasa, nason sanin ke kuma wacece haka?.
Nikuma cire glasess ɗin natane ya bani damar ganeta duk da a hoto na taɓa ganinta, ɗiyarsu Dad da aka bani ɗakintace mai suna Shahudah kamar yanda ya sanarmin ce, yauce ranar farko dana ganta a zahiri, dan kuwa tunda nazo gidan bata zoba, dama Dad ya sanarmin batajin daɗin jikintane tana fama da ƙaramin ciki shiyyasa, amma ita bata iya sati ɗayama batazo gidanba.
Takun takalminta ya sakani dawowa hayyacina, ƙoƙarin fita take tana sake bina da kallo, sai yamushe fuska take tamkar taga wani kashi ko abin ƙyanƙyami.
Da ƙyar na iya fusgo magana a harshena nace, “Sannu da zuwa aunty”.
Banyi tunanin ta amsa mani ba, ta dai fice da ɗan gudu kamar cikin fushi ko tunanin takalmin ƙafarta zai iya kadata bataiba kuwa.


______________________
JAWAAD
______________________

Ɓangaren Jawaad kuwa yau gidan Alhaji Kokino ya sake kai ziyara, inda ya samu damar ganawa da dattijuwar nan da wancan zuwan ta kawo musu kayan breakfast.
Wannan karon ma itace ta kawo masa ruwan sha, dan shi kaɗai ya zo sai gimba.
Koda ta ajiye ruwan bayan gaisuwa sai tai yunƙurin juyawa zata fice abinta.
“Da alama dai a ranar sha uku ga watan bakwai, dai-dai da washe garin rasa Alhaji wani abu ya faru wanda ganinsa ko jinsa ya jawo Accident ɗin faɗuwa a gareki har kika samu ciwon da har yanzu kike jinsa a jikinki, kuma tabbas wannan abun da kikaji ko kika gani yana da nasaba da Alhajin”.
Cak ta tsaya, ita bata fitaba bakuma ta dawo da baya ba, ba komai ne ya jawo hakanba sai kalaman Jawaad masu saka rikici ga duk mai alaƙa dasu.....
Jawaad dake ƙoƙarin zubama kansa ruwa a kofi ya sake katseta da faɗin, “Abin bana dogon tunani bane mama, abin kawai na sani zan cigaba da riƙe Yazeed har sai nasan dalilin faɗuwarki a wannan ranar, miya tsorataki?, abu na gaba ki taimaki kanki kije asibiti a duba ƙafarki, dan naga har yanzu kina ɗangyasata”.
Ya kai ƙarshen maganar yana takowa inda take a tsaye.
Hakanne ya sakata kallonsa ta kauda kanta da ƙoƙarin haɗiye hawayenta, tace,
“Miyasa zaka sakamin yaro cikin al'amarin da baisaniba?”.
“Mama idan har kina buƙatar na sanar masa komai a yanzu ai bamu makara ba”.
Idanunta jajur ta ɗago ta kallesa, shima kallon nata yake, amma sai ya janye nasa idanun ganin tana neman rikicewa, yay murmushi yana sake matse kofin hannunsa na glass, rashin ƙwarinsa ne ya saka kofin tarwatsewa sauran ruwan ciki ya jiƙe masa hannu ya zuba a ƙasa, guntayen kofin kuma sukai ɗai-ɗai a ƙasan suma.
Dattijuwa ta sauke idonta akan hannun Jawaad har zuwa kofin da yaya kuci-kuci a saman tayis tamkar ba shiba, sake maida kallonta tayi gareshi a wani yanayi mai nuni da tsantsar damuwarta.
Jawaad ya zaro handkherchief a aljihunsa ya goge hannunsa tas sannan ya turasu a aljihu duka biyun yana ja da baya fuskarsa na ƙara tsukewa.
“A duk lokacin da aka zuba ruwa a glasscup yana da matuƙar ƙayatarwa, har kakanji bakason ɗauke idonka wajen kallonsa koda zaka kwana a haka, amma da tsautsayi zaisa wannan kofin fashewa a hannunka zaka iya gamo da haɗarin yanka maisa aji zafi, shi kuma ruwan dake ciki idan har ya zuba a jikinka ƙoƙarinka kawai ka goge, damshin da ya rage iskace kawai ka iya busar maka dashi, wanda yake a ƙasa kuwa sai kaga dukansa ya zama haɗarine, musamman akan abu mai santsi irin tayis. Na tabbata duk wanda zai shigo falon nan a yanzu zaiyi ƙokarin ganin bai taka wannan ruwan da glasess ɗin nanba, yaron da hankali bai gama bin jikinsa bane kawai zai maidashi abun wasa. Mama bansan yaya zaki rarraba zantukana a jujuwan da suka cancantaba, ni dai kawai abinda raina ya bani komai tsanani zansan gaskiyar zancen....”
Ya raɓata ta gefe zai fice, yana saka ƙafarsa ɗaya a waje yajiyo sautin dariyarta.
Dakatawa yay tare da juyowa yana kallonta.
Tace, “Yarona idan kwalba ta fashe a hannun mutum zafinta kawai zaiji saiko fitar jini da zai gani, amma idan zuciya ta samu suka har abadan wannan tabon baya gogewa komi adadin shekarun da aka ɗauka bayan jin wannan ciwon, ruwan da zai zuba a jiki a goge iska ta busar bashi da banbanci da hawayen dake kwarara daga idaniya zuwa fuska a goge iska ta busar da sauran, inda ake samun banbancin kawai shi wannan ruwane, daya zube labarinsa ya shuɗe, suko waɗannan hawayene koda sun bushe ba'a daina iya ƙididdige su a tsarin da sukazo na farin ciki ko akasinsa har ranarda fitar numfashi zata yanke, ka cancanci a kiraka da suna *Ƙwai cikin ƙaya* sannan kuma lallai ka cancanta a kiraka da suna *Yaro ɓata hankalin dare kayi suna*, duk abinda kake buƙata daga gareni zaka samu, amma ba'a nan gidanba, mu haɗu a gidan daka ɗauki yarona Yazeed.............✍🏻




*_ZAFAFA SABON KAFCE SUN DAWO GAREKU_*


_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_


_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*


_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻



_Sannan akwai tashoshinmu na Youtobe da zasu fara kawo muku daɗaɗan labarai bisa tsaftataccen karatu, kuyu azamar garzayawa tashar *ALƘALAMI TV & MANHA HAUSA NOVELS* domin samun wannan gara ɓasa, a danna mana subscribing domin nuna ƙauna ta musamman masoyan gaskiya.😃🥰🥰💃🏻👌🏻_.





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*_Typing📲_*




*_🧺ƘWAI_* _cikin_ *_ƘAYA!!🧺_*


*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_Wattpad:-_* _BilynAbdull😉_


*______________________________________*
*_BOOK ONE_*
_Shafi na ahirin ciff😜_
*______________________________________*



............Tunda suka baro gidan Alhaji kokino maganganun tsohuwar ne kawai ke yawo a zuciyar Jawaad, gaba ɗaya ya kasa fahimtar alaƙar ɓatan Alhaji kokino da kalamanta, ya rarrabasu ajujuwa daban-daban amma basa bashi ainahin abinda ya dace, yay guntun tsoki yana cigaba da shafa gemunsa a hankali, yayinda idanunsa ke kallon hada-hadar jama'ar gari.
Daga nan office ya koma, inda ya tarar da baƙuwa zaune tana jiransa.
Rose da tunda Jawaad ya fito a mota ta dasa masa idanu ko ƙyaftawa batayi ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login